har za ki ce na shj
madafi na diba, ta juya, darling rabu da wannan
matar duk bakin kishi ne ya ke damunta, kuma a
haka zata kare. Shema'u ta ci gaba da canja tashoshi
ba ta sake kula su ba, yana tsaye ranshi ya dada baci
yaje ya kashe TV din to ba zai yiwu ba, Shema'u na
ga kina son kawo min matsala gidana ki shiga
hankalinki ban da abunki ai Ummu yarinya ce kuma
naga kina so ki saya wa kanki raini amma zan yi
maganin ki, ya juya zai koma dakinshi ta dubi
6
ummu ta ce ki kuma kiji tsoron Allah, nan na fito da
abinci na kira ki amma kika cc min ba yanzu ba, shi
ne yanzu don makirci za ki ce na hana ki abinci?
Nan Ummu tasa kuka wa Shen a'u da zage ta ya fito
ranshi a 6accd ya cc "mujc Mr. Biggs." Ta shiga
dakinta ta dauko gyalen da shi da babu duk daya,
irin gyalen da mazan da ba sa kishin matansu su ke
saya musu ta sa takalmi masu tsini zai fita Shema'u
ta cc ga abincinka can fa ya cc sai ya dawo su ka
fita.
Bayan dawowar su nc Ummu ta cc, ai wannan
abincin Shema'u ta saka magani kuma idan ya ci
gaskiya ranta ba zai mata dadi ba. Nan ya hakura
kasancewar baya iko da kanshi a takaice duk sanda
Shema'u ta yi girki Nazir ba ya ci, wai ana saka
masa magani bai san yana kwana cikin magani ba,
karewa ma ba ci ba.
Kullum kwanan duniya Ummu ba ta san yau
kwanta ne ko na 'yar uwarta ba, don kafin ya shiga
dakin Shema'u sai ya gama komai da Ummu sannan
ya shiga dakin Shema'u, wataran sai ya kai karfe
daya sannan ya fito daga dakin (ta musamman) ya
shiga in da ba ya son, wataran kam sai ya dau
kwanaki bai leka dakin Shema'u ba, Shema'u ta bi
ta lalace duk ta rame ta rasa yadda zata yi.
Yau ta na dakinta kwance da baby dinta tana
tunanin yau nice Nazir ya ke gasa wa gyada a
7
hannu, alhalin da kyar ya yarda ya aurı Ummu, duk
da 'yar uwarshi ce amma da cewa ya yi mcyc zai yi
da wannan mace ba wani diri ba komai sai kace
(tabarya) amma yanzu ka shi mai kama da tabarya
ta fita mutunci a gun miji amma sai dai komin daren
dadewa gaskiya zata yi halinta, karya furc take
kuma komai na duniya ya na da iyaka.
Ummu ta fito ta iske baby Nur tana zaunc akan
keken yara na koyan zama, tana zuwa tra fara mata
wasa tana tura ta akan keken da yake baby yarinya
cc nan ta fara 6al6ala dariya. Nazir ya na shigowa
yaga Umu na yi wa 'yarshi wasa, nan ya ji dadi ya
ziyarce shi a take ya sake jin son Ummu a ranshi,
sai ya shiga tsokanar su ya na yiwa babyn wasa ya
dauki baby su ka shige dakin Ummu, nan da nan
bakin ciki ya ziyarce ta ta 6ata fuska ta karbi babyn
ta aje ta ta ce gyara na maka tausa, don yanzu
lokacina ne ba na baby na ba dariya ya yi ya ce (ina
son haka tawan) nan ta shiga yi mashi kissa da
kisisina, shi ko dadi ya ke ji.
Duk wani dangin Nazir Ummu ta gama dasu
duk sun fi sonta akan Shema'u duk in da ta zauna
sai ta yi ta bakanta Shema'u kasancewar Ummu 'yar
uwa ce a gidan su Nazir amma ta wajen Hajiyar
Nazir.
Kullum idan ta shiga gidansu Nazir abun da
zata ce shi ne, gaskiya ita fa idan tana bacci takan yi
mafarkin abun tsoro har wani yana zuwa mat ata
windonta yana cewa ta fita nan ba gidan zamanta ba
ne, to anan fa gurmi ya farfa tashi wai a ne ma mata
taimako kada yar uwarta ta haukatata ko ta yi mata
lahani, Allah Sarki.
Ita ko Shema'u da take zaune a gida ita da
babu dun daya bata son ma me ke faruwa ba ashe
dangin Nazir har cewa suka yi Ummu ta daina
amfani da ruwan famfon gidan da abu ya yi abu har
ta daina shan ruwan gidansa (pure water) ko maltina
ko swan. Kasancewar Nazir Business ya ke daga
Yola zuwa (Dubai), a duk san da zai tafi to kudin
kashe ko na dawainiyar gida yana hannun
Ummulkulthun, gaba daya dangin mijin sai su ka.
fara (Respicting) dinta don duk wanda ya ce ga
bukatarshi to zata dau kudin Nazir ta yi musu ko
nawa ne, shi kuma ba shi da bakin yin magana, ba a
kwana uku sai mahaifiyar Ummu ta aiko a karba
mata kudi sai ka ce (bank).
Kuma koda Nazir ya tashi yin tafiya dole sai
yaje ya sallami mahaifiyar Ummu don dolen shi ne
ya je in ba haka ba ya gamu da bacin ran Ummu.
Kawar Ummu tazo gidanta ta kawo mata
ziyara suna cikin daki sai Hani ta dubi Ummu ta ce
Anutynki bata nanne? Ummu ta yatsina fuska ta
tura baki tana dakinta kinsan yanzu falon ya mata
zafi don ba na ragar mata. Hani ta ce gaski, ba kya
9
kyautawa don Allah ki dinga ragar matga kada wata
rana kashinki ya bushe, Ummu ta yi dariya ta ce,
wallahi karya take yi, domin naje fa ba cafe kuma a
haka zata kare sai bakin cikin ya kashe ta tunda
dani zata ja, kuma na riga na zame mata kadangaran
bakin tulu a karni akar tulu a barni na 6ata ruwa.
Hani ta yi dariya tace "To Allah ya shirye ki
Ummu." Ta tabe baki dama can a shirye nake, Hani
ta ce "To amma dai wannan takun saka ya yi yawa
ku dan sassauta ke fa kece karama, hum zancen
kishi fa ba wata waye-waye, kuma kishiya ba abun
yarda ba ce ko kanwarka ne ta zama kishiyar ka to
sunanta kishiya, Hani ta katse ta, to sarkin kwaba
me ya kawo maganar kanwar ka ta zama kishiyarki
in ban da shirmen ki, Ummu ta yi dariya ta ce, to ai
ke kin zake da yawa irin wannan ketente ne gida
haka, azo garin ku a fiku iya rawa, hum ke ma kin
san kowa samu rana...dole ta yi shanya, in ji
Tani.
Ummu ta nisa ta ce, to ai ni ba ki sani ba wai
jibi Nazir zai tafi (Kwatano) kuma wallahi ni yanzu
bana so ya yi nisa dani da kullujm idan ba na tare
dashi bana jin dadi kuma gashi ya riga ya sabar min
da wasu abubuwa...Iye? Ummu me kike fada?
Lallai na yarda shiru-shiru a layi amma yanzu d
akika yi aure duk sai ki ka zama iwa uwar mata su
ka wakwashe da dariya su ka tafa, Hani ta ce to
10
Allah ya shirye ki Ummu ta ce dama can a shirye
nake.
ASALIN LABARI
Nazir da na ga Alh. Yusuf amma ba shi ba ne
babban dan shi, shi ne kusan dan shi na shida amma
a gun mahaifiyarshi shi ne na uku mata, Alh. Yusuf
uku ne H. Aisha ita ce uwargida sai H. Halima sai
amaryar su Hauwa amma ita b ai kai ta Makka ba,
Alh. Yusuf dan kasuwa ne kuma shahararren mai
kudi amm ba ya nuna wa duniya wai shi mai kudi
ne sabanin sauran masu kudi.
Alh. Yusuf mutumin Zaria ne a wani kauye da
ake kira (Hunkuyi), ba zazzage ne na asali amma
sai Allah ya sa arzikinsa yana garin (Yola) a nan ya
auri Aisha 'ya'yansu biyu ya auro Halima su ka fara
jera haihuwa da uwargidanta Aisha har Allah ya
kawo Hauwa. Nazir ya na da yayu maza uku mata
biyu Rakiya da suwaiba sai Ibrahim, adam Nura, sai
kanne Abdullahi, Khadija, da kuma Halima,
takwarar Hajiya karama wato Hajiyar su Nazir,
Nazir dangata ne a gun mahaifiyarsu amma shi fari
ne, sauran yayun shi da ya ke bi masu bakeke ne
babbar 'yarshi Hajara ta na aure a Zaria sai 'ya'yanshi Abbakar sai sauran kannenshi to
kasancewar shi ne ya karanci Business sai
mahaifinshi ya dora shi akan dukiyarshi tun suna
11
safara tarc har Alh. Yusuf ya daina komai Nazir ne
mai yi ya na tafiya Kotono, Fatakol, da sauransu to
kasancewar shi ne dan zirga-zirga a garuruwa, sai
ya samu daukaka a gidan don komai shi ne mai yin
hidima a gidan sabanin yayunshi, Nazir irin
mutanen nan ne masu kamun kai ba shi da
hayaniya, nutsattse ne.
Nazir ya na da wata yarinya da su ke soyayya
Jamila, kowa ya san su tare kwatsam Malam Jibrin
aminin mahaifin su Nazir ya na zaune tare da
1yalansa gwanin ban sha'awa suna dan taba hira ya
dubi matarsa ya ce "Ya kamata yan wannan yaro
Zakariyya ya fito a gama magana da yarinyan nan
don ina so ta yi azumi a dakinta. Nana Bilki ta dube
shi wato matarsa ta ce "Hum, ai an ba shi
'yar'uwarsa wai hadin gida zasu yi amma shi ya ce
baya sonta, Malam Jibrin yayi dariya ya ce yaro
kenan, lallai zamani ya canja har iyaye su ce ga
wacce za su ba ka amma don taurin kai irin na yaran
zamani sai su ce ba haka ba. Gaskiya bai kamata ba,
an sai dai Musulunci ya ba da dama ka zabi matar
da ka ke so to amma dole ne ayi musu biyayya ko
dan samun kyakkyawan karshe, Nana ta ce kai ma
dai kasan yaro idan ya kafe sai dai addu'a ya ce to
Allah ya rufa asiri.
Su na cikin hirar su yaro ya yi sallama, wai
Shema'u tazo in ji Zakariyya da ma ta na daki Baba
12
nc ya ce wa yaron je ka cc ya shigo, Zakari ya shigo
msu ka gaisa Baba ya cc Zakariyya ba mahaifinka
ya yi maka mata ba? Kanshi a sunkuye ya ce Baba
ai ba mu daidaita da ita ba, Baba ya yi dariya ya ce
ba mahaifinka ba ne ya zaba maka ita ba? Shi ne,
sai Baba ya fara mar nasiha kamar haka.
"Ina so ka kasancc mai biyayya ga iyayenka
kayi hakuri ka karbi tayin da su ka yi maka, insha
Allahu ba za ka tabe ba, kuma ka zama mai yarda
da kaddara kairi wa sharri (mai kyau ko
mummuna), kayi hakuri kuma insha Allahu idan
Shema'u rabon ka ce sia kaga ka aura idan kuma ba
rabon ka ba ne to Allah ya sa haka shi ya fi alheri,
Zakariyya na tsugune ido sun kada har tausayinshi
ya kama ni saboda nasan ciwon so.
Da Baba ya gama yi mashi nasiha, ya mike jiki
babu laka ya yi zauren mu, gurin da muke hira,
Baba ya ce "Shema'u ga Zakariyya ya na jiranki,
Nana Bilki ta ce ko akwance ta ke, Shema'u ta fita
jiki babu kwari tashi ta yi hanyardakin zaure wato
dakin Kabiru yayanta, ta shiga da sallama ya na
une kan kujera a sanyaye ya amsa kasancewar
asan halin da ya ke ciki bai nuna masa komai ba, ta
ya zakariya sannu da zuwa, ya dube tga da kyau ya
kare mata kallo a zuciyarshi ya ce zan yi missing
dinki amma a fili ya ce da girman kujerar ki, ta yi
dariya yaya kake? Ya yi tsaki mits, babu yadda nake
13
Shema'u ta zaro ido mc ya faru? Ajiyar zuciya ya yi
ya cc, "kina nufin ba ki san komai ba ne, a game da
halin da nake ciki? Ranta ya dan baci da ya tuna
mata wannan takkin orber da ake shirin yi musu, ta
dan kanne damuwar ta ta ce, to meye what? Kina
nufin ke bai dame ki ba? ashe dai ni kadai nake
haukana? Please Zakariyya ba haka ba ne kasan
komai mukaddari ne to amma tunda da abu ya zo
haka ina mai baka shawara komai ka gani daga
Allah ne, so dan haka kayi fatan alheri a game da
wannan lamari, ni kam Allah ya na gani ba ni na ki
ka ba......dakata Shema'u wannan yarinyar da aka
ba ni fa tafi ni a haife kusan sa'ar uwatayes
ana haka ai, tunda Annabi Muhammad (S.A.W) ya
auri matar da ta fi shi shekaru, so ashe don ka aure
ta ba laifi ba ne, ranshi ya dagule ya mike zai fita ta
tsaya a bakin kofar kayi hakuri idan ranka ya baci
ba wai na fada da wata manufa ba ne bai saurare ta
ba ya fice ran maza ya 6асі.
**
Hadiza ce ta shigo da sallama Shema'u zo ki
raka ni School dinmu na karbo testimonial dina
nayi nayi yaya ya kaini ya ki na ced ki fada wa
Nana Hadiza ta shiga daki ta gaida Nana Bilki,
Nana Bilki ta tambaye ta su Hajiya da sauran yara,
ta ce duk lafiyarsu kalau, suna gaishe ku muna
14
amsawa idan kin tashi tafiya ga sako zan ba ki ki
kaiwa Hajiya Babba, to dama ina son Shema'u ta
raka ni School ne zan kar6o takardana naji 'yan
ajinmu sun ce wai an fara raba (testimonial) Nana
Bilki ta ce to kada kudaďe Baba zai muku fada ku
dawo da wuri su ka cc to Nana mun gode suna
murna su ka fita a hanyar su ta tafiya ne su ka hadu
da Zakariyya Hadiza ta tsaya suna gaisawa Shema'u
kuwa ta wuce ba ta tsaya ba Hadiza ta ce, ranka ya
dade yaya yau nagan ka beari lazyhate me ya faru?
Ya yi dariya ya ce babu komai kawarki ce take
waina ni ta yi dariya ta ce mc ka mata take
wainaka? Yo ina na sani kinsan ku mata da mulki
my bc mulkin ce yau ta motsa, a'a Zakariyya ruwa
ba ya tsami banza amma dai ka bari mu dawo kada
mu yi latti ina zaku je haka? Wallahi zamu school
din mu ne naji an ce wai 'yan JSCE ana raba musu
(testimonial) dinsu shi nr zan jc na karba, to ko
nazo na kai ku ne? A'a bari kawai yanzu zamu
dawo, to sai kun dawo zan jira ku ta ce to Hadiza ba
ta samu Shema'u anan kusa ba sai da ta yi nisa
sannan ta ji rata ta iso ta same ta, amma kin ban
kunya mutum ya hadu da masoyinshi amma ko ya
kula shi yau an gan ku a rana, Shema'u ta ce, share
shi kinsan meye? Sai kin fada." In ji Hadiza,
Shema'u ta karkata kai ta ce ai tun da naga kin tsaya
kuna ta wani surutai nasan ba ki san komai ba a
15
game da lamarin shi ba, ni kam faďa min don Allah
ba na son wani dogon sharhi, hum "Zakariyya
ammashi mata, wai aure dangi za'ayi mashi Hadiza
ta zaro ido da gaske wallahi ke kinsan waye matar
shi? Hadiza ta ce a'a sai kin fada ta tabe baki ta cс
wai Ruky, Rukaiya zai aura wannan 'yarshi ce da
gaske kike ko da wasa? Da gaske nake miki wannan
zance to amma shi ya nuna min wai ba ya son
wannan aure ni kuma duk jinshi nake kinsan su
maza su na ba sa son mace amma da zaran an yi
biki za ki ji su shiru Hadiza ta ce to 'yan keya ya ku
ka yi? mtsi....ta yi tsaki wai yanzun ina tausar
zuciyata ne tun daga yanzu na fara hakuri da son sa
kin san ma meye? wai yanzu yazo ya na ce min wai
shi me zai yi da Rukayya da sauransu ni kuma na ce
masa ai komai nufin Allah ne.
Sun dawo sun iske Baba a gidan Alh. Yusuf ya
na ta yi mana fada wai mun dade ranar a gidan su
Hadiza mu ka kwana saboda nasan Zakariyya zai zo
gidanmu sai na tura Hadiza taje ta fadi wa Nana
Bilkisu.
A washe gari da safe kawai sai ga Nazir ya
shigo, muka gaisa da shi sai na ji su Hajiya su na
cewa yaushe ka dawo? Ya ce shigowar dare mu ka
yi aka kwance tsaraba mu ne yan fasa kwakwa,
muna cikin yin haka aka kawo abarba mu ka hau
yankawa, muna ta sha na dubi Hadiza na ce "Hadiza
16
ina ma acc na auri Nazir ya yi ta kawo min tsaraba,
Hadiza ta dauko min kujera ta sa a bayana muna ta
dariya wai santin zakin abarba nake yi muka yi
dariya son ranmu har su Hajiya su na cewa wannan
dariyar haka ai sai ace kunyi gamo ne. Da ya ke
Hadiza ta fi ni wayo, ko a haife ma ta dan fini sai ta
yi ta zuga ni wai wallahi na fada wa Baba ni har na
manta sai ta ce wai na fada ni kuma da ya ke bani
da wayo sosai, don duka-duka shekaruna sha hudü
ne, ranar mu na zaune ni da Baba na ce "Baba
wallahi ni kam ina son Nazir din gidan Alhaji, Baba
ya yi dariya ya ce "Allah Shema'u? Da gaske kina
son sa?" Na ce "Wallahi Baba ina sonsa."
Baba yazo ya- samu Alhaji Yusuf a gida bayan
sun gaisa ya sanar da shi na ba wa dana Nazir
Shema'u, Alh. Yusuf ya yi murna ya ji dadi sosai,
ya ce Allah ya saka da alheri na gode, Allah ya dada
girma, Allah ya sa a yi damu. Baba ya ce "Babu
komai, Allah ya ba su zama lafiya."
Alh. Yusuf ya shiga gida ya shaidawa matansa,
ai kuwa kowa ya yi murna da farin ciki Alh. Yusuf
ya kira danshi ya shaida masa, nan Nazir ya rude
saboda ya ji abu ba zata gashi kuma ya na da tashi
masoyiyar wacce su ke soyayya unguwar su daya
ya ce Alhaji ina da wacce na ke so, kuma mun yi
alkawari, to ka yi hakuri tunda ga wanda mu ka
zaba maka, tashi kaje.
17
Dakin Hajiyarshi ya shige ya sanar da ita
komai, ta ce to meye ne don an baka Shema'u?
Gaskiya ni Hajiya ba na sonta, ina da wacce nake so
kowa ya sani a gidan nan, Jamila na ke so shi kanshi
Alhaji ya sani, to kuma shi ne yanzu a ce na auri
Shema'u, ni kam ba na sonta, Hajiy. ta harare shi
tunda ba ka sonta sai ka je ka samu Alb ji ko Baban
ku Jibrin ka fadi mashi, tashi ka bani guri ya na
tsugune bai tashi ba ta share shi ta ci gaba da
gararinta.
Nazir kai ya dau zafi, ya rasa meye abun yi ya
samu Sulaiman abokinsa ya sanar dashi halin da ya
ke ciki, Sulaiman ya bashi hakuri, Nazir wannan
zabi da iyayanka su ka yi maka insha Allahu ba za
ka yi deegreating ba, so don haka ka yi hakuri ka
karba me laifin Shema'u? Mace ce har mace duk in
da ka ke son haduwar mace Shema'u iyaka cе.
Nazir ya katse shi cafanen Likita ce fa? Meye
abun sha'awa ga farar mace? Na ji ban ga abun
sha'awa ba, amma dai ya zama dole kayi biyayya ga
iyayenka, me ka gani? Nazir ya na shiru bai kula shi
ba, can ya nisa ya ce "Sulaiman ina son Jamilash
don babe din ta hadu sosai, Sulaiman ya ce to ka yi
hakuri dai mu mika lamarin mu ga Allah Ubangiji
ya zaba mana abun da ya fi alkairi, Nazir ya nisa ya
ce amin.
18
Nazir ya samu Hajiyarsu a daki ya gaishc ta ya
na tsugunc a gurin bai ce kala ba, ta dubc shi ta ce
lafiya? Ya sunkuyar da kai kasa ya ce Hajiya ni fa
gaskiya ki fada wa Alhaji wannan magana na
Shema'u a barta, tsawa ta daka mashi ba ka isa ba,
ai mu mukia haifc ba ba kai ka haife mu ba, kuma
na ji ka ce za ka bar garin, to duk in da kaje za ka
dawo kuma ka same ta don haka dabara ta rage
naka, aure babu fashi nan da sati biyu tashi ka bani
waje.
A rude ya shiga dakin Sulaiman ya yi bala'in
gigicewa ya fada wa Sulaiman duk abin da ake ciki,
Sulaiman ya ce don Allah ka nitsu ka kwantar da
hankalinka komai ya yi farko zai yi karshc, Nazir ya
katse shi wallahi Sulaiman na tsani Shema'u, kai
duk wani dangidan......Sulaiman ya katse shi ya isa
haka, ka kwantar da hankalinka yanzu meye abin
yi? Sulaiman ya tambaye shi Nazir ya nisa ya ce ka
je ka samu Alhaji ka ce ba na son ta ina da wacce na
ke so.
Sulaiman ya kwashe da dariya, ya cc saboda ni
ne tsagera? Sai na je na soke aure ko, to bari ka ji,
ni dai nasan meye soyayya, kuma na taba yinta naji
yadda take, nasan zakin ta na kuma san dacinta, don
haka ina mai ba ka shawara ka karbi zabin da iyaye
su ka maka, Allah ka samu ka rabo, kuma kaima
'ya'yanka za su yi maka biyayya, please Sulaiman
19
sati biyu fa su ka ce two wecks fa yanzu mc Jamila
zata daukc ni? Kuma tasan ina sonta, kai dai yanzu
duk wannan ba ta taso ba, kai dai kawai kajc ka
samu Jamila kayi ma ta bayanin duk halin da ka kc
ciki, kada ta ji a bakin wani ta ce ka munafurce va,
kasan su mata ba a musu gwaninta bai ce komai ba
ya yi tagumi kamar wani mutum-mutumi, haka
Sulaiman ya lallashe shi su ka dunguma gidan su
Jamila, kasancewar bayan layinsu ne ba wani nisa
ba ne dasu, sun ci sa'a kuwa sun same ta amma tana
fitowa su ka gane ta ji labari, amma ta dan boye
damuwarta, su ka gaisa ta dubi Nazir ta ce "Ango da
ma ka na ganuwa? Ya kwakwalo dariyar karfin hali
ya ce gani kuwa? Ta dubi Sulaiman ta ce ku ana
shirin angwanci ana kiba amma ku sai ka ce kudin
guzuri.
Sulaiman ya yi dari ya ce, kinsan mutun zaj
shiga sabuwar rayuwa dama haka ne, amma dai ga
ki ga Nazir, za ki ji komai daga gare shi."
Nazir ya dube ta cike da sha'awar irin dressing
din da ta yi, ya karkata kai ya ce, Jamila da farko
ina son ki sani komai nufin Allah ne, kuma duk iya
kokarin ka ga ka samu abu idan Allah bai nufa ba to
babu mahalukin da zai ba ka komin yaya.....ta katse
shi wai duk wannan dogon sharhin na menene
Nazir? Ka fadi abin da zaka fada, ya yi shiru bai ce
komai ba, can ya nisa ya ce "Jamila sanin kanki ne
20
kinsan ina Kaunarki, to amma wai yau an wayi ga
an cc za a min auren dole da wacce ko kusa dani in
nace tazo zata ji tsoron zuwa, amma wai yau ita za'a
aura min, sai ka ce mata sun kare? Jamila ta ce na ji
labari amma sai na musa saboda Shema'u ba ajinka
ba ce, amma sai naji da kunnena kai da kanka kana
cewa za a maka auren dole to ai sai ka so tunda kai
ne me auranta ba ita ce mai auranka ba. yanzu dama
Nazir duk fata min lokaci da ka yi ya tashi a banza
kenan? Ka sa na kore samarina waton ita Shema'un
da aka yi mata snaching din saurayi shi nc ta rama
akaina? Yanzu kai kana nufin shi kenan mun rabu
kenan?"
"No, ba mu rabu ba, kinsan ba zan iya rabuwa
da ke ba, in Allah ya yarda za ki shigo gidan nan
nawa kuma kece first lady dina kin dai gane? Ya
dube ta, yes na gane amma gaski......sai ta yi shiru,
ya sake dubanta gaskiya meye?
"Babu komai." Ta fada
**
Ana saura sati bikin Shema'u da Nazir, Nazir
bai taba zuwa hira ba kuma ko sun hadu idan ta
gaishe shi bai cika amsawa ba, ranta ya dan Gaci
kadan amma sai ta share. Idan ta hadu da Jamila sai
bakaken maganganu, gashi uwar Jamila irin
21
matannan ne 'yan duniya wanda ba ta ji ba ta gani
wajan nema wa 'ya'yanta 'yanci in ji ta.
Mun dawo unguwa ni da Hadizan su Nazir, mu
ka yo kwanar gidan mu sai mu ka ga Nazir su na
tsaye da Jamila su na hira, raina ya dan sosu amma
na dakc naki kula su, muka wuce Hadiza ta cе
Shema'u don Allah kiyi hakuri nasan dole ne ranki
ya baci, na kalli Hadiza na ce ai duk kc ki ka cисe
ni kika zuga ni har naje na fada wa Baba ina son
Nazir, kuma ni kam da zai yiwu da na je na ce wa
Baba na fasa. Hadiza ta ce "Wallahi kada ki kuskura
ki fasa, ai in kunyi aure zai daina wuya ne dai ku
zama mallakin juna, kuma sai ya zama tarihi.
Ana bikin wata Haule duk kawaye ne da
Hadiza da su Jamila to kasancewar Shema'u ba
tsarar su ba ce saurin girma dai kawai ta yi Hadiza
ta sa haule ta gaiyaci Shema'u suin je wajan
(Deener) kowacce ta ci kwalliya da ya ke Jamila
tana da rawar kai da kwadi ita kuma Shema'u ta na
da miskilanci don har jama'a suna cewa ta fiye jin
kai kuma ba haka abun ya ke ba, (natural) dinta ne
haka, gaskiya kuma Shcma'u fara ce kyakkyawa ga
diri gaba dayansu sun hallara a ball din can sai ga
Jamila sun isò ita da saurayin da ya ke nema ya
zama mallakin wata.
Jamila ta kalli haduwar da Shema'u ta yi ta ja
tsaki duk sauran kawayenta sai da su ka juyo,
22
Hadiza ranta ya baci sai Nazir ya yi mata alama da
su zauna su ka nemi waje su ka zauna, Jamila ta
sake jan tsaki Nazir ya tambayc ta lafiya? Ta
muskuta ta cc babu komai su ka ci gaba da
harkokinsu, Shema'u ta ce Hadiza ni kam zan tafi
gida dan mc? Tа сс "Babu komai Hadiza ta gane
dalilin da ya sa ta cc zata ta fi gida, sai itama ta
mike "Mu tafi Shema'u." Ta cc 'a'a kiyi zamanki ai
ba a gama ba tunda ko farawa ba ayi ba, No, muje
kawai su ka dau jakarsu za su fita Jamila ta cc
Hadiza ina zuwa? Hadiza ta yi kamar ba ta ji ba ta
fice ta iske Shema'u a waje su ka tsayar da masu
mashin kasancewar babu masu tasi motocin 'yan
biki kuwa ba su fara diban jama'a ba.
Su na isa gida Shema'u gidansu ta wuce, kowa
ya shiga nasu gidan Hadiza komawa gida ta fadi
komai duk abun da Nazir ya ke yi wa Shema'u,
Hajiya ranta ya 6aci sosai.
Ita kuwa Shema'u ta na shiga gida randa ta
nufa ta debi ruwa mai sanyi wai dan taji sanyi
zuciyarta, Nana ta kalle ta ta ce lafiya a'a babu