din aka yi masa kwalliya kai abin gwanin
sha'awa Nazir bai zo da abokansa ba sai bayan
magariba, ganin yadda ta gyara tebur din kawai ya
dau hankalinsa ya gayyace su cin abinci ya na
budewa ya yi arba da rogo, kai duk kular da ya
bude rogo ne dai aka sarrafa shi. Bakin ciki ya
kama shi ya ce, mata, mata ga bakinsa dai
Larabawa ne ya ce musu ba za ku iya cin wannan
abin ba, abincin gargajiya ne wasu a cikin su sun
so ci amma ba za su iya ba ya ce su tashi su je su
45
1
1
ci a in da ya yi musu masauki, kafin su tafi su ka
ce ya yi kiranta su gaisa, su ka yi mata gift su ka
tafi.
Shiru-shiru taji Nazir ya yi mata magana
akan abin da ta yi masa amma bai yi ba.
Yau Asabar tun safe ya yi kiran kaninsa
Anas ya ce ya shiga store dinsa duk abin da ke
ciki ya fito dashi ya kuma share, Anas ya yi yadda
aka sa shi, ya ce maza Anas karasa kayan store
biyu can ya dawo ya ce ya raba ka kira yara kace
sukai store din cikin gida nan da nan yara su ka
gama ya ce dayan ya sa ke raba shi biyu ya raba
ya ce shima a dauka akai store din Ya Abubakar,
dayan kuma akai gidan su Shema'u aka rabe
kayan abinci ba tare da Shema'u ta sani ba, don
taje makaranta mota daya yasa aka yi ta rogo ya
zuba shi cikin store ga kuli-kuli shi ma ya zuba.
Washe gari ya daga zuwa Dubai ko sisinsa bai ba
ta ba, ranar ba ta nemi komai cikin store ba
saboda haka ba ta san me Nazir ya yi ma ta ba.
Sai bayan ya tafi ne bai ba ta komai ba,
hankalinta ya tashi saboda kudin motar zuwa
makaranta da aiki, kuma duk kudaden ta na
wajanta har wanda ta ke ajiya a banki, ta kwasa
don ta sayi wani gida flat me kyau har 'yan haya
ma sun shiga, ta sayi wani fili da ta ke burin Allah
46
ya taimake ta itama ta bude makaranta dan ganin
makaranta ta ke son yi a filin wannan shi ya kawo
ma ta rashin kudi a hannunta, ga shi farkon wata
ne bare ta sa rai a albashi amma bai kyauta ma ta
ba wato shi kuma da haka zai hukuntata da
wannan tunani ta nufi store don ta dobo kayan
shayi ta jera kan tebir me zata gani? Store a
makare da rogo gefe ga buhun kuli ga garwar mai
fa magi dunkule da onga ga kuma barkono, wasu
zazzafan hawayen takaici su ka zubo ma ta, ta
goge. Haka ta hakura ya zata yi, kullum rogo shi
ya zama abincinta ta ringa sarrafa shi kala-kala da
safe in ta je gaida Alhaji abin da ya ba ta shi ta ke
kudin mota har 'yan bukatunta. Wannan tafiyar ya
dade ko da ta dau albashinta sai ta siyi kayan tea
da kwai da dankali ta kaiwa Hajiya abinci
sakwara ce amma fa da rogo gami ya sai budada
kamshi ta ke, Hajiya ta buded ta ce Shema'u
wannan cin rogon na ki fa na lafiya ne, rana rogo
safe rogo, murmushi kawai ta yi.
Ta na zaune handset dinta ta soma fidda
kiran Muhammadurrasulullah, tasan calling ne ta
na dauka taga Nazir ne da murnarta ta ce "Yayana
kwana biyu na ji ka shiru lafiya.?"
47
"Lafiya kalau gobe ina nan tafe, ina so ki yi
min hadin rogo mai dadi, dan naga kin fi
gwanancewa a nan."
Тa се "To Allah ya dawo da kai lafiya." Nan
da nan ta sa aka fidda rogo daga store ana bi gidagida a unguwar ana rabarwa washe gari ya sauka
sai da ya cika cikinsa gurin Hajiyarsa sannan ya
shiga ya bubbuda abincinta amma ko tabawa bai
yi ba, da daddare ne ta same shi falon Hajiya ya
na cin abinci ta ce "Yayana ga abincin ka can a
falo." Ya ce "Kai ni ba zan iya cin rogo ba,
wannan sai ke." Hajiya ta ce "Ni wannan cin rogo
na ta ya na damuna." Ya kalli Shema'u ta zuba
masa ido ya ce "Hajiya kinsan masu abin nan sai
abun da su ke so ake ba su." Hajiya ta washe baki
ta ce "Haba ko da naji, ni fa cin rogon nan nata
har ya soma damuna, amma wannan maigida
nawa ko kishiya tawa ba su kyautaba ace su hana
min 'ya cin komai sai rogo ai Shema'u ba ta san
san da tabar falon Hajiya ba.
Da safe sun karya ya ce "Ke wa ya kawo
kayan tea?" Ta сe "Ni na siya da na dauki
albashi." Ya ce "okey." Yayana ta fada ta na wasa
da awarwaronía ya ce ya aka yi Shema ta? Та се
"Babu kayan abinci a store, ya ce kai Shema
kincinye motar rogo guda, lallai kinyi aiki, kar ki
48
damu, yau zan zuba sabo wannan karan ma dai
rogon ya zuba illa iyaka da banbanci domin ya
kawo kayhan shayi da kifi da dama da kuma
naman kaji duk an zuba a firij kamar yadda ya
saba. Da Shema'u ta shiga store gani rogon ya
sake daga ma ta hankali in hukunci ne ai hukuncin
da ya yi ma ta ya isa, ita kuma ta dauki alkawarin
ba za ta ce ya daina ajiye ma ta rogo ba, illa iyaka
in ta na sha'awar wani abu ta siya da kudinta da
zai koma Dubai wannan karon ma ko sisi ko da ya
ke ba bai dade ba satinsa biyu tunda kuwa ya tafi
kullum cikin ciwo ta ke dan wani lokacin ko zuwa
makaranta ba ta yi.
Ta na zauned falo abin ka da fari ta kara
dashewa ta na zaune a falonta, Anas ya shigo ya
ce "Antina ya jikin naki.?" Ta ce "Da sauki." Ya
ce, yau kanwarki ko in ce amaryarki zata zo duba
ki, na ce na gode, ya ce to anti me ki ka tanadar
mata? komai ma Anas duk abin da ka ke so sai da
ya gama lissafa abin da za'a dafa ma ta ta ce to
megidan sai ka shiga kicin dan ni ina kishi ba zan
iya dafa ma ta ba, haba Anty bakuwarki ce,
kasancewar jikin nata ya yi sauki ta ce shi kenan
zan shirya ya ce Anty komai ai kina dashi ko
akwai wanda babu? Sai in siyo, E, to Anas
gaskiya duk sai ka siyo don abin da muke da shi
49
kadan ne in kuma ta na cin rogo in sarrafa mata ya yi dariya ya ce cin rogo ai sai ke Anty ya fita yin
siyayya maigidan ya shigo ya tsorata da ramar da
tayi, wanka kawai ya yi ya ce su zo su ga Likita ita kuma ta ce babu wani Likita da zata gani dan
ta warke, ganin ta yi kicin-kicin ya hakura ya
samu falo ya zauna ya zubawa rigimammiya ido.
Anas na shigowa ta mike ta shiga kicin ta shirya
girki Anas din ne ya taimaka ma ta wajan shirya
tebir ya na zaune ya na karatun Jaridar Leadership
hankalin sa na kan su sai da su ka kammala ta
shiga wanka kafin ta fito ya na zaune ya na
hattamawa, wani gululun bakin ciki ya tsaya ma
ta wuya ta karaso ta dafa kujerar da ya ke kai ta
ce, Yayana abincin bakin Anas ne, ko ma waye
mu kinsan ko ba ayi mana tayi ba ci muke, to
Allah ya kyauta, ta bude taga kadan-kadan ya ci
ta gyara ya ce kwalliyar ki ta birge ni zo ki raka ni
Mr. Biggs, ta ce amma dai kasan hijab zan sa da
nikaf, ya ce E, na sani ki zo ki raka ni ta ce bakin
da za su zo masu mahummanci ne dan ni zasu zo
dubawa, bai kamata ace ba na nan ba, yanzu fa
zamu dawo, dole dai ta bishi su ka tafi, ashe wayo
ya yi mata asibiti za su, Likitan da su ka gani ya
yi mata tambayoyin daga karshe dai scarnning aka
yi matga nan su ka tabbatar da ciki har na wata
50
biyar shi kansa Likitan ya yi mamakin sakarcin da
tayi ba ta gane ba sai dai kuma da ya ke na fari ne
kuma har yanzu da ta ke da cikin tana yin messes
murnar da Nazir ya yi abin gwanin sha'awa don
tun a gaban Likitan ya ringa nuna mata murnarsa
daga nan sai Mr. Biggs sun suyo snack sannan ya
shiga da ita wani store nan ma dai kudi ya kashe
sannan su ka nufi gidca ta ci sa'a bakin nata sai da
ta dawo su ka zo.
Washe gari Nazir da kansa ya ringa fita da
rogo a ranar aka zuba kayan abinci wannan cikin
ya sa Nazir ya ringa tarairayarta ita abin har
mamaki ya ke ba ta, saboda wani irin zazzafan so
da ya ke nuna ma ta, ko da ya koma Dubai satinsa
bi biyu da ya dawo kuwa babu abin da bai zo da
shi ba na baby, ai kuwa aiki ma hana ta ya yi ya
ce sai ta haihu kafin ta haihu ne ya ke fada mata
zai soma ginin sa dan gidan da zai gina zuwansu
London ta nuna sha'awarta da gidan shi kuma ya
sa aka zana masa gidan cikin satin da ya fada
mata aka soma gini.
Cikin Shema'u ya isa haihuwa faf Laraba
da asuba Allah ya sauke ta ta sarnu 'yarta mace
mai kama da ubanta sak! Ranar da ta kainu komal
kan idanun Nazir eka yi don duk korar da akayi
masa kin tita ya yi da ya fita zai dawo, yarinyar
51
kuwa da an karfe ta sai ce kawo ta tun ya na bai
wa Hajiya haushi har ta hakura.
Ranar suna yarinya ta amsa sunanta Halima,
sunan Hajiyarsa saboda haka muke ce mata Nur, a
gaskiya sunan Nur dangin Hajiya sun zo da yawa
akwai wata 'yar kanwar Hajiya wai ita
Ummulkulthum wacce tazo suna tun da aka yi
suna ba ta koma ba, ko da ya ked ba na ce mata
yarinya ba don a haife ta girman ga ta dama ita
irin mutanan nan ce ga girman jiki ga tsayi sannan
kirjinta a shafe ya ke, uwa uba babu mazaune ko
da ya ke ba za ka sa ta sahun farare ba haka ba za
ka ce ma ta baka ba, amma sam ba ta da fasali,
don ko ni mace ba ta yi min ba ba re kuma da
namiji, Ummu irin 'yan gayun nan ce ma su iya
yin fasi fa ga shi karatu ta ke dan medicen ta ke
karanta, amma fa kwakwalwarta fanko ce don dai
irin 'yan dumama kujera, turanci kuwa ko na
minti biyar ba za ta iya ba, ga shi mahaifinta ya
dauki burin ganin sai ta zama Likita, dan shi
mahaifinta ba mazauniba ne hakan mahaifinta ya
rabu da mahaifiyarta saboda mugun halinta
Ummu tasha raba cahaifinta dda matarsa dan sam
ba t ada hali ga shi mahaifiyarta na matukar sonta
don ita kadai ce da ita ba ta san' 6acin ranta, duk
dacewar mahaifinta na yin rawar gani wajan
52
tarbiyarta da karatunta don ita ko note ba ta yti sai
inDady ta ya yo waya ya ce zai dawo zata yi
saboda dole ya duba littattafan ta duk da in ya
duba ba ya gamsuwa don mafi akasari in ya yi
mata tambayoyi babu amsa, shi ne ya ce wai mr
isa ba ta sa Date cikin note dinta shi ne yanzu in
zata yi kwafin sai ta sa Date saboda ya kan bi date
ne ya duba.
Zuwan Ummu gidan ya kawo sabon canji
saboda bala'in iyayanta duk samarin gidan babu
mai sakar mata fuska da ma shi Nazir ba ya kasar
sai Abubakar shima saboda ita ya daina hira falon
Hajiya, tun kafin na haihu Alhaji Yusif baya nan
sai dai an sanar masa ta waya don ya na Cairo to
yau Allah ya dawo da shi har falona ya shigo abin
da ban taba gani ba, kayan barka kuwa masha
Allah har da dubu goma akai, da safe kamar
yadda kowa ya saba zuwa gaishe shi nima sai da
naje don jego bai hana ni zuwa ba, to hakan ce ta
kasance Ummukulthum itama taje ya amsa
gaisuwar ta ya ce bakuwa muka yi? Ta ce "Ba ka
gane ta ba.?" Та се 'yar gidan Hajiya Hauwa ce
Ummu ya ce au! Ita ce, i ai tun suna ba ta tafi ba
ya ce bazawara cem haba Alhaji budurwa ce fa ya
yi salati ya sanar da Ubangiji, ya ce yanzu shi
mahaifinta ya zauna da wannan sangamemiyar a
53
matsayin budurwa, ba ya tsoron kar duniya ta
zage shi yanzu in ya shiga gida zai iya gane wace
uwar wace 'yar? Gaskiya ya yi mata aure, Hajiya
ta hade girar sama da ta kasa saboda tana ganin
kamar ya ba da ita cikin kishiyoyinta, Alhaji
karatu fa ta ke Likita ce ya ce Allah isa ita ce
ABCD in ban da shashanci ka zauna da ya yi
wannan girman ba ka tsoron haduwar ka da Allah
ko ko sai ya dauko abin kunya ka dora masa laifi?
To wallahi aure zan mata ke daga nan ma wajen
mahaifinta zanje, in karasa mai gaya maka
gaskiya kayi asara yana cikin fadan sai ga Anas
da Abubakar sun shigo.
Ya kalli Anas ya ce kasan Ummu 'yar
uwarka? Ya ce "E." Alhaji na santa wani abu ya
faru? A'a na baka ita wata biyu masu zuwa biki,
ya yi wata irin dariya ya ce Allah na gode na gode
sai dai ni wallahi ina da wacce zan aura mun yi
kuma alkawari kuma kai ka ke daďa tunasar damu
kan mahimmancin alkawari, sai dai ga dan uwana
nan Yaya Abubakar ko zai yi kari, Alhaji ya ba
wa Abubakar shima ya yi godiya ya ce a'a amma
bai sani ba ko Umar zai karba tunda dama wacce
ya ke so ta yi auran ta, nan fa Hajiya ta yi ta fada
wai an wulakanta 'yar kanwarta duk su ka zuge,
saboda a gaskiya irin sigar Ummu ba ita maza ke
54
yayi a yanzu ba saboda ita ko saurayi ba ta taба yi
ba a rayuwarta, daga ita har uwarta ba su da burin
da ya fi ace yau an sami mai sonta, to gaba daya
dai sun zuge wannan abu bai wa Hajiya dadi ba,
Nazir ya da wo daga Dubai, gida ya dauki murna
kamar yadda aka saba, ana ta shan alawoyi kalakala da bisket da dai sauran tarkace, tun da ya
dawo idanun Ummu na kansa kamar tsohuwar
mayya, yadda taga ya na tarairayar matarsa sai t
ake ganin ina ma ita ta samu haka har ta kuduri
niyyar fidda Shema'u ita ta zama madadinta.
Nazir ya shiga falon Hajiyansa hannunsa
dauke da Nur, ya na tafe ya na yi ma ta wasa kaı
ka ce da wata me wayon ya ke, Hajiya ta kalle s}
ta ce "Kai dai ba ka jin kunya diyar fari kake wa
wasa, Hajiya kawo miki ita fa nayi, ina uwarta?
Wanka ta ke ni kuma sai na ce bari in kawo ta
gurin Hajiyarmu ta goyata a bayanta, kai raba ni
da goyon 'ya'yan mutane ai ni yanzu na ce na
daina goyon jika, subul ta sako baki Ummu kenan
ta ce, kawo in goya ta mu iyaye bama gajiya da
goya 'ya'yanmu. Hajiya ta ce E, ku yi ta goya su
da ma naku ne, amma ni ba zan goya wannan
katuwar ta karya ni ba, ba Husna da ke zaune tana
jin su itama ta tofa tata ta ce kinga kuma Alhaji ya
saba da ita dan naji ya na cewa gidanta da ban da
55
ba anan kasar za su zauna ba sai Saudiyya ba ki ji
sunanta ba Nur, haske fa ake nufi ai wannan ta fi
su ce, Ummu ta karbi Nur ta goyata ta juya ta fita
daga falo Nazir ya ce Hajiya ina kika samu
wannan zankalar ta ce ba ka gane Ummulkulthum
din ba? Au! 'yar gidan Umma Hajiya ce ra ce i ya
ce zaman me take a gidan nan ina gidan mijinta ta
ce ai budurwa ce karatun Likita ta ke kai Hajiya gaskiya ya kamata ayi mata aure, ta ce ai kai
muke jira kai ne mijin ya ce kai wallahi wannan
ko a kafa aka daure min ita sai na kwance na
gudu, ina zan kai wannan? Hajiya ta bata rai ta
sake salon hirar ta su, ashe duk Ummu tana jin su.
Da yamma ta shirya ta tafi gida in da ta fada
wa mahaifiyarta ita fa Nazir shi ne choosing dinta
saboda haka mahaifiyarta ta ce ka r ki ji komai
kamar an yi an gama.
Da safe Nazir shi da Shema'u su ka shiga
gaida Alhaji anan shima aka yi masa tayin Ummu
kamar yadda aka yi wa 'yan'uwansa amma ya ce
me zai yi da ita, can dai ba ta da fasali har su ka
dawo wajansu ya na ta mita wai shi an cuceshi
hada shi ma kawai da aka yi.
Kafin Nazir ya koma Dubai sai da ya je
gidan Umma Hajiya don shi ba ya zuwa sai
Sallah, amma sai ga shi can ne gurin cin abincinsa
56
kwata-kwata ya sallama na Shema'u abin zai ba ka
mamaki kina ce Nazir ya rikice kan Umınu dan
yanda ya ke musu barin kudi abin da mamaki, ana
zaune tsakar gida Hajiya take ce da kishiyoyinta
wai Nazir zai auri Ummu amma ita kwata-kwata
ta fi sha'awar Anas ya aure ta saboda shi ne ba shi
da aure haba Hajiya wannan wace irin magana ce
kina ganin yadda matarsa ta sake sosai duk cikin
yayanmu mata wa ya samu yadda Shema'u ta
samu ki godewa Allah tunda da kansa ya dawo ya
ce ya na sonta, ai da yanzu ki a garin wasu gara a
garinku a garin ku ma a gidanku a gidanku ma a
dakinku a dakinku na kuma a hannunka, duk ina
za ki so Shema'u ya yi E, Ummu 'yar 'yar'uwarki
ai wallahi gwanda ya aure ta itama ta ji dadi yo
irin wannan 6arnar da kudi da ya ke ma ta, ai
wallahi Hajiya kar ki sassauta sai an yi ayi nan da
nan a gama, au ya ce sai ya gama gininsa, nan dai
su ka zige Hajiya tas.
Ta 6angaren Nazir kuwa yanzu soyayya ce
mai karfi ta kullu shi da Ummu, in kuwa zai tafi
Dubai dole ne iya adadin kwanakin da zai yi sai
ya yi list dan kudin zancen kwanakin ya bayar in
kuma ya na nan to ta na gaban motarsa su na zaga
gari kwata-kwata Shema'u tun ta na girki da shi
har ta hakura tun tana san jin dalili har ta zuba wa
57
sarau ar Allah ido kuma duk wannan zancen auran
da ake kwata-kwata ba ta sani ba, dan babu wanda
ya fada mata duk abin da ake na aure babu abin da
ba akai ba wanda ya zama al'ada amma ba ta sani
ba, ko ya fada ma ta ya gama gini bai yi ba illah
yaje ya dauki Umma Hajiya da amaryarsa Ummu
ya kai su gidan sun dimauce da ganin gidan ya се
su zabi daki su ka ce to biki ya rage saura sati
uku.
Aysha matar Abubakar ta rasa yadda zata tari
Shema'u da zancen da ya karshe ta shiga falonta
ta zame ta a zaune ta yi shirin fita zuwa in da ta ke
koyarwa su ka gaisa ta ce dama wata magana nake
so muyi, ta ce ina jin ki Ukti dan haka ta ke ce
mata, to abin da zan fada maki ba mai dadi ba ne,
amma ina so ki nutsu ki kuma yi tawakkali don
nasan dole ne ki sani yanzun ma abin da ya sa na
fada miki dan ki yi wasu gyare-gyare, Ukti ina
jinki don Allah ki fada min ko hankalina ya
kwanta, ta ce to ba wani abu ba ne illa ina son in
tambaye ki kinsan Nazir zai yi aure? Har yau
saura sati uku tini ma anje an yi jeren amarya tun
jiya jikin Shema'u ya hau tsuma ta ce Ukti fada
min gaskiya Nazir dina Yayana shi ne zai min
kishiya shi ne zai haďa ni da wata, don Allah Ukti
kice min April full ki ked min dan zuciyata bazan
58
haska wasu Kona kanka ni da nake ganin ko uku
zai yi kina da hikimar da za ki zauna da kowacce,
nima abin da ya sa na fada miki don kiyi
kyararrakin da mu kan yi a al'ada in za ayi mana
kishiya, kiyi zamanki in da bai gaya miki ba kar
ki nuna kin sani ke dai yi gyaranki nan dai ta
zauna ta yi ta bata baki har ta yarda ta fasa tafiya
yau aikin da bata fita ba.
Nazir bai dawo ba sai ana i jibi daurin
aurensa da Ummu ni duk a tunanina Jamila zai
aura ashe wai Ummul kai namiji sai a barshi shi
da ya ce ko a kafa aka dora masa ita zai kwance
ya yar sai gashi an wayi gari ya na kiran ta da (Ta
musamman) kai namiji dan kansa ne ana i gobe za
a daura aure kuma washe gari kenan kai amarya а
ranar ya zo mun da zance gobe daurin auransa zai
auri Ummulkulthum, kanwarsa gobe za a kaita a
yau dai ya ke so in kwashe kayana in koma sabon
gida, ji nayi kamar in shake shi ya mutu don
takaici na ce a'a Nazir ka barni a nan Allah ya
baku zaman lafiya da na ji zai dame ni kawai na
fice na yi 6angaran Ukti, ji na yi an ce in zo
babana ya zo na fita na gaishe shi ya ce min maza
hada kayanki ki koma sabon gidan ku Allah kuma
ya baku zaman lafiya, haba yar albarka Shema'u
ki sani duk in da kike albarka na tare da ke tunda
60
na aurar da ke ban taba samun matala ba, kullum
sai na yi miki addu'a mai kishiya zata tsinta a
wanda ke baki tsinta ba, nan fa ya ringa yi mata
wa'azi ta tashi ta na kuka ta hada kayanta aka
zuba a mota sai sabon gida ta yi sallama da mutan
gidaduk anje rakata.
Kuma sai maigida da ya gyare ya ke tas falo
yasha gyara da wasu irin kujeru dun dum dum
dum ga irin shegun kayan kalo dining table din ku
abin a gani ne ga wata hadaddiyar show glass an
jera wasu irin kirinset labulayan kawai sun ba wa
dubu dari baya, Shema'u ta gigice da wannan
shegen gyara master room shima wani Italian bed
ne aka shimfida masa wani arnen bedshirt gidan
all of then dinsa an cika shi da kayan kudi room
da ya kawai aka bari babu komai a ciki kuma
babu in da aka rufe ko ina a bude ya ke kicin ma
abin gwanin sha'awa Nazir ne ya shigo ke
Shema'u har dakin da babu kowa shi ne naki duk
nan da kike gani kayan amarya ne ta kalle shi ta
girgiza kai ta ce, to, ta kalli Aysha ta ce Ukti ku
saka min gado dan nasan babu gurinsa sif a jeran
akwati na ragowar kayan a saka min su a gareji,
hakan kuma aka yi.
Da daddare wanta ya kawo mahaifiyarta tazo
ta yi mata nasiha mai ratsa zuciya, ta ce kiyi
61
hakuri duk wanda yaga take-taken auran nan tun farko to an san da wata manufa aka yi shi, to
amma ki sani hakuri ba ya 6aci duk rintsi duk
wuya kiyi biyayyar aure wataran sai labari nasan kina da ilimin Islama kin san tarihin manyan bayin Allah mata wadanda suka yi biyayyar aure da irin rabon da su ka samu kina da tarihin
Rabi'atul Adawiyya, haka tarihin Nana Fadimatu,
Bintu Muhammad da irin biyayyar da tayi, ku 'ya'yan yanzu ne ku ka dauki aure gurin holewa da jin dadi amma ai shima bautar Allah ne
mahaifinki ya ce ya na yi miki fatan alheri, ya na
kuma kara tausarki duk abin da za su yi miki ki
mika lamarinki ga Allah don yanzu idanun kowa
da kunnen jama'a ya na kanki duk wani yunkuri
da zaki yi sai a ce kishi ne to kishi halal ne, ki san
irin wanda za ki, wallahi Shema'u nasan kina da
zafin kishi to kiyi hakuri tunda naji maganar
auren mijinki nake miki addu'ar Allah ya
rangwanta miki haka da ta yi tayi mata nasiha har
ta ji zuciyarta ta lafa sannan ta tafi.
Washe gari aka daura auran Ummu da Nazir
ko yanki bai bani ba bare wasu kayan fadar kishiya.
Bayan sallar Isha aka kawo amarya tunda
'yan kawo ta su ka zo suke yar da magana ice ko
62
ba ayi musu sata ba ko kuma a barbade musu
kaya da magani don sun san aikina ne yau kwanan
gidan amarya duk a nan aka kwana amma haka
Ummu ta tsallake jama'ar da su ka kawo ra tayi
master room a nan ta kwana ita da miji kun ji
amaryar zamani, har sha daya ba su fito ba su na
can ana zuba amarci nan kuwa tsofaffi duk an
shanya su duk da uwar 'yan uwanta ne sai da su ka
nuna ba su ji dadin yanda ta zake ba haka na
danne kishina na kula da duk jama'ar da su ka zo
sai da Suleman yazo muka gaisa ya ce ya na son
ganin Ango na ce, to bara in je in kira shi na je n
ayi nocking din kofar tun kan in shiga na jiyo
mitarta wai shi kamar bai da mata ya fiye damu
naji dariyarsa, nan da nan na ji wani abu ya soki
kahon zuciyata, na ce Yayana Suleman na ji wai
duk sun hadu ango bai fito ba, ya ce to bari muyi
wanka sai mu fito na ce, to haka dai har aka gama
budar kai kowa ya watse daga ni sai amarya sai
maigidan da 'yar babynmu Nur.
Ango Nazir dai bai shigo dakina ba sai da ya
kwana tara dakin amarya wanda ni nasan addini
da al'ada sati daya ya ba shi a matsayinta na
budurwa ban nuna masa na ji haushi ba dan nasan
shi ba jahili ba ne ya sani sarai, babban abin da ya
takura min shi ne rashin sukuni a gidan, don ko
63
Yau tun da gari ya waye