wani
abu da ki ta shiga ta kwanta zuciyarta na fidda wani
sauti wanda a zahiri ta rasa mene nc kafin ta ankara
wani zazzafan hawaye ya wanke fuskarta, babu
wanda ya cutar da ni illar Hadiza wuf kamar wacce
aka je fo Hadiza ce ta shigo ta kamo hannunta ta
23
dago ta ya aka yi ne mutuniyar haushi ya kama ta ta
ji kamar ta shake ta baki da kalmar da za ki cc min
dan kin cutar da rayuwata a yanzu na soma hango
wa kaina irin kurkukun da nake niyyar cusa kaina
ciki don na fahimci irin zunzurutun kin da Yayanki
ya ke min yayin da ta dafe kirjinta tana cewa
Hadiza danna min kirjina kinga ji nake kamar zaj
fashe Hadiza ta fashe da dariya ta ce lallai Shema'u
wato ke kishin naki mai zafi ne! Cikin rashin
fahimta ta ce, an ce miki kishi nake kwarai da gaske
kishi ki ke dan ba kya kishin Yaya Nazir da hakan
ba ta faru ba, kuma a yanzu na tabbatar da irin son
da kike masa, so na hakika ne, ina kuma ba ki
goyan bayan kar ki sausauta masa don nasan zai so
ki don kin fi Jamila komai nesa ba kusa ba, ina son
ki tabbatar min ke macece.
Nazir shi da abokinsa Sulaiman su ka shiga
gida, Hajiya na zaune ta na yankan alayyahu su ka
yi mata sannu, kallon in da su ke ba ta yi ba su ka yi
tsugune a gun sun kasa tashi illah wannan ya
zunguri wannan, wannan ya zunguri wannan,
Sulaiman ya yi karfin halin cewa, "Hajiya muna
neman afuwa a bisa laifin mu." Haushi ya kama
Hajiya ta cc "Sulemanu me kuka yi mun iyaka
kunnunawa duniya ccwa mu muka haife amma ba
mu isa da ku ba, tunda kuwa haka ne me zamu ce
daku illa muyi muku addu'ar shiriya."
24
"Hajiya mun tuba mun amshi tayinku a yanzu
ma duk wani shirye-shirye mun kusan kammala
shi."
Hajiya ta ji dadi cikin zuciyarta, to kuwa in
haka ne daga yau har zuwa ranar da za'a kammala
bikin ina so kullum kaje ku ringa gaisawa da
Shema'u don ku fuskanci juna gaba daya, wannan
karfan su ka amsa.
Irin dinkin nan na doguwar riga wanda 'yan
birni suke kira da gosulo shi ne a jikinta, ya matse
kirjinta tsam shi ya bayyana sirrin kirjinta ga shi
karamin hannu ne damatsanta duk sun fito waje, da
su ka je Kano biki tayo dinki don ya na matukar
birge ta, wani ni'imtaccen kamshi ke fita a jikinta,
wani karamin mayafi ne ta sakalo shi a wuyanta ta
fito daga gidansu da zummar shiga gidan su Hadiza,
ji ta yi an ce ran amarya ya dade, ta yi saurin
juyowa saboda jin muryar bakuwa ce a gare ta, ta
kalli Sulaiman gefensa abokinsa ne Ango Nazir,
haushi ya kama ta tumba da ta kalli fuskarsa taga
babu annuri, itama sai ta dada shan kunu ta ci gaba
da tafiya tana amsa gaisuwar Suleman din a'a ranki
ya dade ba za ki tsaya ki saurare ni ba, wajanki fa
mu ka zo, oh ai ban sani ba ga shi kuma kun yi
rashin sa'a don yau ban ji yin zance da ku tattara
koma tsanku kuyi wajan Jamila don ita ce daidai ku
amma ni yanzu bani da lokacin ku.
25
Haushi ya kama Nazcer wai wannan 'yar
ficiciyar yarinyar zai zauna ta na yaba musu
maganar da ranta ke so, bai san sanda ya tattaka
zuwa gabanta ba ya kare mata kallo daga sama har
Kasa, shi kansa yasan akwai kyan diri illa iyaka tayi
masa kankanta, yarinyar da ko irin cikar nan ta
budurci ba ta gama ba, a hankali ya ke fitar da
sautinsa tamkar me rada don ko Suleman ba na jin
ya ji abin da ya ke fada ma ta.
"Ke ki shiga hankalinki, ki san da wa ki ke
magana, ki kuma san waye a gabanki ke kanki
kinsan ba girman kujera ta ba ce ace ina tsayawa da
kwaila kamarki, ina so ki sani biyayya zata sa in
tsaya da ke ba wai so-ba, kin gane."
"Kai an fada maka sanka na ke hadi ne kawai
irin na iyaye tunda ba shawara su ke da mu ba, don
da sun yi shawara da mu kai kanka kasan ba kalata
ba ne."
Jin kalaman ta ya yi tamkar dirar aradu, kafin
ya farga ta fada cikin gidansu, dakin su Hadiza ta
shiga tare da annushuwa cikin zuciyarta ta dan ko
ba komai ta rama don tum tayan kewa kanta wannan
shawarar ko ganin haka zai sa iyaye a fasa.
Dangantakar Nazir da Shema'u ba wai
'yan'ujwa ba ne na jini ba, illa aminci irin na da da
iyayansu abokan juna ne tare su ka tashi don shi
Alhaji Jibrin mahaifin Shema'u dan asalin garin
26
Yola nc, yayin da shi Alhaji Yusuf bazazzage ne
tunda kasuwanci ya hada su har Allah ya sa shi
Alhaji Yusuf ya dawo Yola ga gida ga gida su ke
wannan dangantakar shi ya sa su ka zama tamkar
'yan'uwa na jini don irin wadanda ba su sani ba gani
su ke wa da kani ne.
don Nazir Yusuf ya bi maganar mahaifiyarsa
kullum zai zo sai dai fa ba wai zance ake mai dadi
ba, illa in ya fada ma ta magana za ta rama, ana
igobe daurin aure ne ya na zaune kan motarsa ya
aika kiranta, cikin yanga ta karaso in da ya ke ko
kallonsa ba ta yi ba, daga Sallah ma ta tsuke baki,
ke ba ki iya gaisuwa ba ne, ba tare da ta kalle shi ba
ta ce ni ban san in da ake yin ta ba, cikin murmushi
ya ce zan koya miki yanda akc yin ta kawa, dan
kinsan gobe za su daura a kuma goben za akai ki ina
so ki sa wa ranki da zuciyarki za ki je yin gadi ne ba
wai zaman aure ba, don kin san matsayin maigadi
shi ne matsayinki, amfanin ki ki jire min gidana da
dukiyata kin ji 'yar kyakkyawa." Ya fada ya na
murmushi, ta yi tsaki an gaya maka zama zanje yin gidanka? Ta juya don jin yanda kwalla ta ke neman
subuce ma ta, kafin ta ankara ta zubo hannu ya sa
ya rike ma ta mayafi ai ban gama ba ki ka juya za ki
tafi." Ta so goge hawayen kafin ya gani amma ta
makara, don ya gani.
27
"A'a, tun yanzu? Kin ban kunya tunda kin
soma karaya." Cikin tsiwa ta ce "An gaya ma ka
saboda kai nake hawaye, never wallahi, in yi
hawaye domin ka just kwaro ne ya fada min ido."
"Ya kamata ki gyara bakinki in ba haka ba ran
da duk kika zo hannu sai wannan bakin ya raina
kansa."
"Kanka ake ji." Ta juya ta yi tafiyarta.
**
Biki ya yi biki, ta fangaren su Nazeer Yusif
biki ne na masu 'ya'yan banki, amma ta bangaren su
Shema'u biki ne na masu rufin asiri. Gidan su ango
sun kashe makudan kudi don lefenta ma abin kallo
ne, dan mahaifinta da kin karba ya yi, amma Alhaji
Yusif ya nuna masa sittira ita ce mutum, kuma
Musulunci ya amine da ka yi wa iyalinka suttura
yayin da sadakinta dubu hamsin, shima mahaifinta
yayi rawar gani wajen fitar da 'yarsa kunya, dan ya
yi ma ta furniture na fita kunya, a ka'idar Nazir ya
so zama a wani karamin gidan sa da ke bayan
layinsu, amma mahaifinsa ya ki ya ce shi da ba
mazauni ba ya na tare da su don a nan cikin gidansu
aka ware ma ta 6angare daban.
Ta bangaren abokansa kuwa, sun shirya masa
party ya kai kala takwas yadda bikin ya kayatu ya
jefa zuciyar Jamila cikin wasi-wasi dan gani ta ke
28
ya na so yaudararta kawai ya yi don ganin yadda
hoton Calender su ka yi matukar kyau in da ya na
rungume da ita ita kanta tasan sun yi macing da
juna, haka jakar bikinsu ta birge ta wannan shi ya
dada tabbatar ma ta da cewa ta rasa Nazeer don
tasan ya auri mace wacce ta amsa sunanta.
Bisa al'adarsu randa aka daura aure to a ranar
ake kai amarya washe gari ayi budar kai, to haka
aka yi wa amarya Shema'u, ita haka aka kaita don
yawancin fatin da aka yi tana gidanta ta ringa
halattar sa, haka nan an yi lacca wacce ta ratsa
zukatan al'umma wacce fitacciyar Malamar nan ta
yi ni kaina ba karamar karuwa na yi ba wajen
saurarar laccarta haka dai biki ya kammalu aka
watse.
Su na zaune ita da yaran gidan cikin falonta,
har ma da matar wansa Abubakar sun mai da
hankalisu wajan kallon kaset din biki a gaskiya
kaset din ya yi kyau akwatin TV din ya nuna ango
ya yanko cake ya sa wa amarya a baki, waje ya
dauki tafi falon na ta jin su ka dauka su na fadin sai
metar Yaya ta harari Hadiza ta ce, Hadiza ba na so."
shigowar Nazeer ta katse su yayin da gaba daya su
ka mike su ka fice, ya ce "ku yi zamanku mana." su
ka ce a'a mun gani koda gobe nę su ka fice itama
kashe kayan kallon ta yi, ta yi dakinta ba ita ta fito
ba sai da gari ya waye, ta yi wanka ta shirya cikin
29
kyakkyawar shiga ta shirya abinci kan tebur ya па
fitowa daga dakinsa kamshin abincin ne ya daki
hancinsa ta na falo ta harde ko kallonsa ba ta yi ba
ya fito yajc kan tebir ya duba abinci ya ce mu ko b
ayi mana ta yi ba ci zamu yi ta yi tsaki ba tare da
ce komai ba, ya kai dubanta kan fuskarta ya ce "Kat
ki kuskura in kara magana kiyi min tsaki, ba ta
tanka ba sai da ya kammala cin abincinsa ya kalle ta
ya ce sai ki dauko mayafi muje gaida su Hajiya ko
ta ce tun dazu naje ya tsare ta da ido kinje da wacce
hujjar, ni dama ce ba tare da wani nake zuwa ba
saboda haka yanzu ma ba mai takura min, ya tsare
ta da idanunsa har sai da ta ji tsoró sannan ya ce ki
bude kunnenki ki saurare sharudda-na in kunne ya ji
jiki ya tsira abu na farko shi ne ba na son raini dan
ni mutum ne wanda nake son a bani respecting
dina, ke bari in tambaye ki tunda ki ka zo gidan nan
kin taba gaishe ni daga yau dole ne ki ringa gaishe
ni a matsayina na abokin zamanki, sannan nasan
kinsan ina da olsa dole ne ki kula da abincina kin ga
can dakina ne ya nuna ma ta da hannu ban gayyace
ki ko wucewa ki je yi ta dakin ba balle ki shigar min
in gyara ne zan gyara abina sannan zancen zuwa
gaida su Hajiya dole ne ki jira ni in dai ina gari dan
muje tare, kamar yadda Yaya Abubakar ke yi da
matarsa Aysha, kin dai ji abin da na ce." Ya baza
ma ta kamshinsa ya fice gaida iyayansa.
30
د
Ajiyar zuciya ta yi ta cc, "Allah gani gare ka
Ubangiji ni dai nazo yin bautar aure nc ba wai
bautarwa kamar yadda ya ke son bautar dani ba,
Allah ka bani rinjaye a kansa in da rabon zama a
tarc da mu Allah in babu rabon zama ka kawo
hanyar rabuwa ba tare da amincin iyayenmu ya
wargajc ba, Allah ka sassauta min zuciyata ka bani
juriya da hakuri da dangana akan duk irin yadda zan
tsinci rayuwata, ji ta yi hawaye na bin fuskarta ta
kuma yi alkawarin babu mai jin irin zaman da su ke
ko da kuwa mahaifiyarta ce bare Hadiza da take
ganin ita ce sila.
Shigowarsa ce ta sa ta share hawayenta ya
shige dakinsa can kuma ya fito da hula a hannu
alama ce ta fita zai yi, muryarta na rawa ta ce a
dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya ta yi alkawari
tunda mutum ne mai son girma ta yi aikawarin zata
girmama shi fiye da tunaninsa.
Gidan su Nazir cike ya ke da yara saboda haka
koda yaushe in sun ta fi School zata ji gidan ya yi
ma ta wani iri, hatta Hadiza ta koma School don ta
shiga SS1 ga shi ita ba zancen ci gaba da JS an yi
ma ta aure, takaici yakan isheta ita kenan kullum
kirkirar girki saboda Nazir amma zai cinye ne ba
tare da ya nuna ma ta jin dadinsa ba, kullum cikin
kwalliya ta ke amma a banza yadda ta ke ba shi
girma abin ba magana idan ya ta fi Dubai ya kan yi
31
wata daya wani lokacin ya haura amma in ya dawo
sati daya nc ko biyu zai juya, abinci kuwa ba ya
yanke ma ta haka kudi don duk sanda zai tafi dubu
talatin ce zai ba ta, ta 6angaren abinci kuwa babu
abin da za ta nema daman su iyayen mijinsu ba su
amince da hadin girki ba, daga ita har matar wansa
kowa nasa ya ke yi, saboda haka ba ta da matsala
haka kuma in dai Nazir baya nan Alhaji Yusif
kullum in ta je gaishe shi zai ba ta kudin kashewa,
nan da nan ta yi mulmul abinta ta yi kyau ta dada
girma.
Abin da ta kula da shi, shi ne Nazeer bai rabu
da Jamila ba, sabodá duk randa ya dawo daga Dubai
ta kula tsarabar da zai ba ta guda biyu ake yi iri
daya, sannan duk randa ya dawo sai an kawo masa
danbun nama fal dish tasan daga gurin Jamila ya ke
saboda haka ita dai kullum fada wa Allah ta ke ya yi
ma ta zabin alheri.
Sun zauna falon Hajiya ta ji ihun yara su na ga
Yaya Nazeer, ga Yaya Nazeer, gaba daya 'yan falon
su ka fita tsakar gida aka yi ma sa sannu da zuwa
nima nabi sahunmsu na yi masa sannu da zuwa.
Mun shiga gurinmu na sa ke gaida shi tare da yi
masa sannu da zuwa, Yayana ya na ganka kwatsam
babu wuya, haka na zaba ga shi ban tanadar ma ka
komai ba, ya ce ba na tare da yunwa, ta ce amma
duk da haka ya kamata in yi ma dan special dish ko,
32
ya ce ganin damar ki ne, ta mike ta shiga kitchen ta
shiga sarrafa nau'in abinci kala-kala, kamshi kuwa
ya cika gidan shi kansa maigidan ya matsu a bashi
rabonsa, ta shirya tebir taje ta yi wanka ta tsala
kwalliya cikin wani material wani baki ya na da
sirkin kyalli riga da ya dace da kayan, ni kaina ta
birge ni don ta yi kyau ta yi amfani da turaruka don
mijinta gwanin turare ne, bai rage ta da shi ba, don
ita kanta ba ta san iya adadin turarukan ta da ke kan
dressing mirror din ta ba, ta fito cikin yanga da kada
jiki wanda wannan halitta ne haka Allah ya yi ta, ta
zauna shi ma da cikin kwalliyar ya ke tamkar mai
zuwa fati, sai dai shi Kananan kaya ne ta yi saving
dinsa ya na cin abincin wayarsa ta soma fidda sauti
tasan calling dinsa ake yi, saboda haka taje kan
kujera ta dauko ta kalli sunan da ke jikin wayar taga
an rubuta my love amma sai ta dake ta hadiye
fushinta ta durkusa ta mika masa ya daga ya yi
sallama tare da cewa, ran my love dina ya dade, ba
ta san me aka ce masa ba, amma ta ji ya ba ta hakuri
tare da rantsuwar dazu ya dawo yanzu ma ya ke cin
uci, daga karshe dai ta ji ya na alkawarin ga shi
Lan zuwa daga nan zuwa awa daya da rabi, ta hada
kai da tebir ba ta san sanda ta ringa fidda sautin
kuka ba, ya kashe wayar ya bi ta da kallo amma
cikin ransa ba ya jin dadin kukanta, ya bita da kallo
ya ce, "SHEMAH!" Yadda ya fadi sunan sai ta ji
33
kamar duk duniya babu wnada ya iya fadın sunanta kamarshi, kai ita tunda ta ke ma bai taba fadin
sunan ta ba sai yau, lafiya kike kuka? Haba Yayana
ya za ka fadi haka bayan kasan abin da kayi min,
ina matsayin matarka ka ringa hira da wata a gabana
ka na tsammanin ba zan ji kishi a raina ba, ka na
sanc da Hadisin da ya ke tabbatar mana duk matar
da ba ta kishin mijinta ba za ta shiga aljanna ba,
haka duk mijin da ba ya kishin matarsa shima ba zai
shiga Aljanna ba, Yaya na bika na bika wai ya ka ke
so da rayuwata? Ka tuna ni amana ce a wajanka,
nasan ba ka sona to amma ya kamata kayi min
adalci ka maida ni hannun mahaifina tunda shi ne ya
ba ka abin da ba ka so, in yaso sai ka kawo Jamila ta
zama matarka ina so in sanar maka nima mutunci
wacce a iya dan nawa sanin nasan illar irin zaman
da muke tunda nasan ko Musulunci zai iya raba
aurenmu, ina son in tabbatar ma ka da cewa ci da
sha da sittira ba shi ne aure ba, bayan wannan akwai
wani abu ina so Yayana ka taimaki kuruciyata ka da
ta kare ban mori komai ba, wani irin kuka ya kwace
ma ta, shi kansa ya na son matarsa illar girman kai
da tsoron kar ya yarda girman kujerarsa, (ko ina
girman kujera a gurin da namiji in yaje hannun
mace) ya shiga rarrashinta tare da cewa zai dauki
matakin karshe hannu ta ya kama wai tazo sujе
dakinsa ya dauko ma ta tsarabarsa, zungur-zungur
34
su ka kama hanyar dakinsa sai da su ka je kofa ta
turje wai ba za ta shiga ba, don ta na bin
umarninsa ya yi dam, shima ya ce ai yanzun ma
kina bisa umarnina ne ta ce a'a Yayana shiga ka
kawon ina nan ya dan jima da shiga ya fito su ka
zauna falo ya shiga fidda tsaraba ya na cewa kinga
wadannan ke na sayowa, ya ba ta zobuna da sarka
kirar Dubai, ya ce kinga wadannan ma na ki ne,
dadi ya cikata ta ringa murna ta na fadin godiya
na ke Yayana, ya ci gaba da fidda dogayen riguna
da mayafan ta zaro ido Yayana wadannan duk
nawa ne? Domin ki na siyo saboda dama ina son
in shiga cikin sahun mazan da suke kyautatawa
iyali.
Tun daga wannan lokaci ya shiga kyautata
ma ta, ba ji ba gani, komai ya samu ita, ilarshi
daya ba ya barin ta fita babu in da ta ke zuwa ko
da so ta ke ta fita to lallai sai dai ta tambayi
Hajiya, ita kuma ta tilasta masa, ganin haka ya sa
ta yanke shawarar shiga Islamiyya da ke cikin
unguwarsu. Ba karamar rigima su ka yi ba akan
shigar ta makaranta, don sai da Yayansa
Abubakar ya yi ruwa ya yi tsaki ya ce sa ringa
tafiya ita da matarsa, ta shiga makaranta cikin
nasara domin dama tayi nisa sosai saboda haka sai
ta shiga aji 'yan high Islam, nan da nan sunan ta
35
ya yi fice cikin makaranta da ya ke da wuya
Malami ya fita ba ta yi masa tambaya ba, wacce ta
shafi addini in kuwa lacca aka yi dole ne ka ji ta
na watso tambayoyin da kowa zai karu.
Nazeer ya kamu da son Shema'u bil hakki,
ya rasa ta in da zai nuna ma ta kaunarsa, domin ita
tuni ta yanke kaunar zai so ta duk hanyar da taga
ya na bi dan a sasanta to ita kuma sai ta hau dokin
naki, abin ya na damunsa musamman in yaje
gidan Suleman yaga yadda matarsa ke tarerayarsa,
amma shi in ya shigo gida sai dai ya tarar da tasa
matar tsakiyar takardu ta fi ba wa karatunta
mahimmanci akan komai.
Yau ma saukarsa kenan ya shiga bangaren su
ya same ta ta yi nisa cikin bacci, gefenta kan
kujera ga doguwar rigarta nan da hijab har da
nikaf a jikinta, kuwa daga ita sai unders da bes
karar TV ta cika falon don da alama lacca ta ke
saurara wacce su ka gabatar a makaranta mai
taken 'HAKKIN AURE AKAN AL'UMMA' ya na
sauraran yadda Shema'u ke bayani dalla-dalla ya
ce oh dube ta kamar gaske, juyin da zata yi su ka
yi ido biyu tamkar a mafarki ta ganshi, ta yi
zumbur taja jihab ta na kokarin rufe jikinta ya yi
dariya ya ce kinsan tun sanda nake a nan ai da na
36
yi niyyar sace ki da tuni sai dai ki farka ki ganki a
duniyar masoya."
"Haba Yayana kawai sai ka shigo ka zauna
wa mutane cikin falonsu, ba ka ga yadda bacci ya
sace ni ba."
"Oh! Nima nayi mamaki don bai kamata in
same ki a haka ba, dan kin san yanayin gidan nan
da yadda falonki ba ya rabuwa da samarin gidan
nan."
"Ni kaina na yi mamakin ganinka, don sai da
na rufe kofa yadda na san babu mai shigo min."
"Ai ta kofar baya na shigo don cikin gida ma
babu wanda yasan na dawo." Ta kwashi kayanta
ta yi gaba, ya bi ta da ido ya na yaba kyan tsarinta.
Ta yi shirin kwanciya ta yi addu'o'i kamar
yadda Manzo (S.A.W) ya koyar damu, tunani
barkatai ya ringa zuwar ma ta don sun haura
shekara da aure ita da Nazeer, ya kamata ace
itama tasan dadin aure don ko ba komai ta na
sha'awar ta ganta da baby, tayi saurin fatattakar
tunanin ba zai yuwu ba, ba zan mallakawa wanda
oai sona jikina ba, bai san zafin so ba, illa daya
Nazeer ya yi ma ta ba ta san 6acin ransa tana
matukar sonsa, ta ko'ina ya yi ma ta ba ta san
sanda gwanin iya satar ya bizeta ba ita dai ta farka
cikin duniyar rikicin da ta saba, yadda yau Nazir
37
ya ke neman hakkinsa shi ya karyar ma ta da zuciya, don yau ya fallashi zuciyarsa da yawa ya
fada mata maganganu masu dadi da taushi wadanda ba zata taba mabce su ba, saboda yadda
take jin dadin su, ai kuwa ayau Nazir ya yi nasarar
mallakar matarsa yadda ya ke bukata, ya yaba d
yadda iyayenta su ka yi ma ta tarbiya in da ya
ringa yi ma ta addu'a daga ita har iyayenta.
Son da Nazir ke nuna wa matarsa bai
6oyuwa don duk wanda ya ke ciki ya sani, duk
gidan ba su mai facaka kamarta sittira kuwa sai ta
wata shifa ba ta maimaita zani ba shi kuwa Alhaji
Yusif ya na son surukarsa sosai, haka Hajiya
domin duk in da zata fita ba ta nuna kwalliyarta
sai a gida musamman in aka ce Nazir ya na gari,
tun daga Yola har Kano ta ke aiken dinki duk
wani sitayal na dinki a jikinta ake fara gani hakan
bai ya sa ta nunawa mutanan gari kwalliyarta dan
muddin zata fita cikin nikaf take idan ka shigo
gidanta sai ka raina kanka saboda gayu don 'yar
gayu ce ta kece raini.
Saboda haka duk dangin miji idanunsu na
kanta saboda ga ni su ke ta samu Nazir yadda ta
ke so, matsalarsu daya ita ce har yanzu Allah bai
nufe ta da haihuwa ba, dan ga shi har ta kammala
Secondary a Islamiyyarsu, har ta shiga yin
38
Diploma ga shi su Hadiza 'yan bayansu ga shi har
ta haihu wannan ya na damun Nazir saboda shi
mutum ne mai son haihuwa, babban abin da ya ke
daga masa hankali shi ne ciwon marar da ta ke yi
na tashin hankali an nemu magani an nemi
magani Allah bai kawo karshensa ba.
Suleman ne ya ke ba shi shawara ya kaita ayi
ma ta wankin ciki dan shima matarsa ta samu irin
wannan matsalar, tunda ga wankin ciki Allah ya
yaye mata.
Nazeer ya yi niyyar fita da matarsa outsite ya
fada wa mahaifinsa ya kuma amince, sun fita
zuwa London sun samu ganin wani fitaccen Likita
kan al'amuran mata, ya yi musu bincike sosai
shima dai shawarar wankin mahaifa ya bayar, an
yi cikin nasara sun yawata don sun mji amarci
yadda ya kamata, daga nan sai da su ka je kasashe
hudu sannan su ka dawo.
Bayan dawowarta ne ya koma Dubai in da ya
ke business dinsa.
Shema'u ta ci gaba da karatunta don yanzu
ma ta na koyarwa cikin wata Islamic School da
wani Malaminsu ya bude wanda ya nemi ta ringa
koyarwa da ya ke School din Privet ce ta na
daukar alnashi mai tsoka, ta na kuma taimakawa
iyayanta sosai, dan har uban mijinta ba ta barshi
39
haka ba, duk da kasancewarsa mai hannu da shuni
wannan shi ya daga darajar Shema'u a gidan, duk
wani matashi a gidan ya na neman wani abu gurin
ta zai zo, ko da irin ziyarar nan da 'yan matansu su
ke kawowa dakinta ne gurin saukarsu, ba su kara
babu hantara ta 6angaran matar wan mijinta kuwa
Ayshat. babu wanda zai ce ya taba jin kansu da su
kishin tsauri sai dai su ji labarinsa dan ba su
sanshi ba.
Nazir ya dawo daga Dubai cikin nasara dan
duk kayan da ya saro tuni ma su sara sun sare, ya
kuma samu riba fiye da yadda ya zata saboda haka
shima sai ya kara kyautatawa iyalinsa.
Kwanansa biyu da dawowa ne ya yi shiri
cikin kyawawan kananan kaya ya yi matukar
kyau dan har Shema'u na tsokanarsa.
"Yayana ka ganka kuwa, sai ka ce irin
matashin saurayin nan dan shekaru 22 zuwa da
25, nan kuwa cus ne."
Ya yi murmushi ya ce "Ai kin san namiji ba
ya tsufa, zan iya kaiwa shekaru 80 in zo in auri
sa'ar jikata." Ta yi shewa ta ce "Amma kuwa da
girma ya fadi." Ya mike.
"Sauri na ke kinsan ina ta cin lokacina."
"Af! Yayana zamu gaisuwa gidan Hajiya
Dije." Ta tambaye shi 40
tun da magaribar fari, ihun dai take gami da neman agaji,
gaba daya fa ta birkice tamkar wace ta sami tabin hankali,
fadi take, ko me kake so ko me ka nema ban da wannan
Dady na zai ba ka ko duka dukiyarsa ne.... Finciko ta ya yi
a lokacin. da ya wanke mata fuska da 'mari, "ke ko
nahaifinki baku da ko abin đa za ku ba ne. Me kuke da
shi? Ku su wanene? Talakawa 'yan kauye, ko waye uban
naki ki gaya masa ba shi da abin da zai iya bawa dan
Genera Abdallah Usman, kin fahimta?
Kokawa ta karkemusu, kokarin kaita kasa yake ita
kuma na kokarin mikewa, dariya yake sannu a hankali
yarinya wane ke? wane ja da Wahced? ashe rashin kunyar
taki duk