da ya ke muna
jarabawar karshe ina sauri saboda yau muna da
gasa karatu ga shi ina daga cikin daliban da
jaharmu ta dauki nauyin mu zuwa Misira kowa ya
na ta ya ni murna amma Ummu ko kallo. ban
isheta ba, dama ita tunda ta debi kayan kicin dinta
sai ya zama koda ta yi sha'awar yin girki sai ta yi
a falo ko a jikina domin ban da tsinke cikin falon
balle wani akasin ya faru a sha dani na yi shiri dan
har na goya Nur zan tafi na samu Nazir da Ummu
za su fita na ce Yayana don Allah in hanya daya
zamu yi ku rage min hanya, ya kalli Ummu ya се
Tamusamman kina jin abin da Shema ta fada, tana
yatsina ta bude jakar ta ta dauko naira dari wai in
shiga taxi, su sauri suke, takaici ya kama ni Nur
ta sa kuka ta na mika wa mahaifinta hannu ya
kalli Ummu ta ce ka dauke ta ta raka mu, yasa
hannu zai fige ta a bayana na ce uh'um makaranta
zani ka bar min yarinyata, ta kalle ni sannu me
'ya, ko kunyar fada ba ki ji ba ya fige yarinyar ya
mika ba ta wani rungume ta kamar gaske, ta kalle
ni ta ce awon kaninta zamu kinga kuwa ya kamata
tayi mana rakiya, su ka ja mota su ka tafi nima ta
tafi ni dai haka na kammala pepar nan amma bani
da natsuwa ina kammalawa na dawo gida har na
dawo ba su dawo ba, kwanciya nayi saboda a
65
gajiye nake. Sai La'asar na farka, ina tashi na fito
falo, a falo na same ta tana wasa ita kadai na juya
na shiga wanka ina fitowa na tada Sallah.
Nur da ke wasa a falo ta nufi show glass din
Ummu ta na wasa, daidai lokacin Ummu ta shigo
falon, ke ke ta daka mata tsawa kaga shegiyar
yarinya za ki cuce ni ki fasa min kaya 'yan uwa
kar ku manta Nur fa a lokacin shekarar ta daya, iri
ta soma tafiyar nan dan ko kwari bata yi ba ba ku
ga fincikar da ta yi ma ta ba, taja ma ta kunne ki
ka kara zuwa gaban show glass dina sai na ci
ubanki ko kayan uwarki ne yarinyar ta kwalla
kuka wanda ina Sallah ya gigita ni, duk da dai ban
san yadda aka yi na sallame sallar ba na tsince ni
ne a hanyar falo a daidai lokacin da ta ke wannan
fadan shi kuma Nazir shi dá kaninsa Anas sun
shigo falon nima na kawo falon da niyyar in zo in
dauke 'yata ganin na taho da hanzarina ya sa ta
dauke yarinyar da mari, kafin in kai in da su ke
yarinyar ta kife akar ko motsi ba ta yi, kafin in je
Nazir da gudu ya dauki yarinyar ya na fadin kina
da hankali kuwa, shi kuwa Anas bai yi wata-wata
ba ya dauke ta da mari ji kake tas! ya sake kifa
mata ta wani 6arin, shi dai Nazir ko ta kanta bai
biya ba ya na ta girgiza Nur amma ko motsi, ya
rikice gaba daya sai mikawa Anas ya ke ya na
66
cewa kaga ni ta mutu ko Anas ya karbe ta ya saba
a kafada ya fita shima ya bi bayansa na kasa
komai sai kuka saboda nasan yarinyar ta mutu ne
ko ni Ummu ta daka sai naji jikina balle 'yar
shekara daya.
Ba su su ka dawo ba sai bayan Sallar Isha.
fuskar nan tata gaba daya ta kumbura aka dawo
min da ita Anas sai ban hakuri ya ke shi kuwa
uban gayyar ya kasa magana cikin dare jikin Nur
ya yi tsananin zafi saboda zazzabi na jika tawul
ina goga ma ta can yarinya ta ringa fisge-fisge na
rása in da zan yi da raina na tashi na yi master
room ina nocking din kofar kuma ina jin surutan
su amma an ki a bani damar shiga, ganin halin da
Nur ta ke ciki yasa ni danna kai cikin dakin na yi
nadamar abin da na gani, kuma nasan a yau nice da
girki koda ya ke ni kaina bazan iya tuna ranar da
Nazir ya kwana a dakina ba ya na tashi ya zabgan
mari wai ni wacce irin mahaukaciya ce na nuna
masa Nur da ta ke a sume na ce ka gani Nazir ka
gani zata mutu kuma in ta mutu matarka ta kashe
min yarinya ya ce to ta mutu mana ina ruwana ko an
ce miki na damu na dawo daki ina ta tofa mata
addu'o'in da su ka sauwaka a gare ni. Gari na
wayewa ko wanka ban yi ba salla kawai na yi na
goye Nur a bayana ina fitowa a falo na same su na
durkusa na gaishe shi na ce Nazir ga Nur fa ciwon
67
ta yayi zafi ka taimaka ka kaita asibiti ya ce na gaya
miki ba damuwata ba ce, kije ki kaita mana in ta
mutu Allah ya jikanta, hawaye yha biyo fuskata na
mike jiki babu kwari yayin da Ummu ta rinka jifana
da wani matsiyacin kallo takaici ya kama ni saboda
yau da gobe sai Allah na duba ma'ajiyata ko ficika
bani da ita, ga shi daga nan zuwa gidanmu tafiya ce
mai yawa, haka na daure na fito, tafiya nake ba ta
wasa ba saboda na gaji ai ni naji ana yi min hani na
duba sai naga Anas ne ina zaki ne? Na je duba Nur
aka ce ba kya nan, zan je gida ne a kasa kike nufin
za ki tafi, na girgiza kai kasan safiya ce motoci suna
wahala mai ya hana mijinki fita da ke na ce yau
baya jin fita shigo in kaiki na shiga baya tun muna
mota tana goye a bayana na ji tana wannan fisgefisge ya na tsaida mota tun kafin ya yi magana nayi
fid na fice da gudu na shiga gida na kunto Nur tana
fisge-fisge mahaifiyata tana tambaya ta lafiya? Ina
kuka na ke fada ma ta abin da ya faru, ta juyo da
niyyar zuwa gun mahaifina ashe ya na tsaye ya na
jinmu ta ce Malam bari in shirya mu ta fi asibiti
baba na cikin fushi ya ce ba zai yuwu ba ba
hakkinmu ba ne mu kai ta asibiti tunda ya na da
iyaye bani yarinyar in kai wa mahaifansa in suma
sunga ba za su kaita ba to a lokacin mu ke da
'yancin kaita wannan wane irin rashin imani ne,
Baba na ya karbi Nur a hannun Nana ya juya da
68
niyyar kaita gidan su Nazir da kansa, kawai sai mu
ka ga Anas a tsaye ashe tun da na shigo da gudu
shima ya biyo ni baba don Allah kuyi hakuri ni na
dauko ta a hanya wallahi da ta fada min ba zan
kawo ta ba, asibiti zamu tafi ya karbi Nur ya ce taho
muje mu kaita mu ka tafi kai ta har da mahaifiyata.
Munje mun sami ganin Likitar yara Doctor Fiddausi
ta shiga kula da yarinyar ta ce zafin zazzabi shi ya
haifar da jijjigar nan da nan aka yi ma ta wata allura
sai kuma ta samu bacci gado su ka ba mu ma'ana
dai an kwantar damu mahaifiyata ta ce bari ta kawo
mana abin da muke bukata, Anas ya ce bari in kaiki
in yaso nima sai in kawo abin da suke so su ka fita
tare.
Na kife kan gado ina kuka saboda bakin cikin
kishiya da na miji yanzu ni Nazir ya ke
wulakantawa haka bai ga abun da matarsa ta yi wa
'yarsa ba wai Nur din da Nazir ya ke raba dare ya na
kallonta saboda dadewar da muka yi ba mu samu
haihuwa ba ita ce wacce bai damu da ita ba, yanzu
haka rayuwata zata kasance? Amma fa ina ganin
laifina ne tunda ni ce wacce na nuna ina sonsa har
aka kai ga hada auranmu, to ai Nazir ya so ni so ba
na wasa ba, babban takaicin ban iya son wani in ba
shi ba shi kadai zuciyata ke so, Allah ka yaye min
son Nazir don sonsa ba shi da wani amfani a gurina.
69
Doctor Fiddausi ce ta ce, ke bacci kikc har drip
din da aka sa ma ta ya kare, jinr har ya soma shiga
rabo na dago idanu a kode na ce wallahi ba bacci
nake ba, ta kalle ni ta ce haba 'yar uwa ki daina
damun kanki za ta warke yanzu abun da kananan
yara suke fama da shi kenan, ta kalle ni ta ce sai dai
na rasa dalilin kumburin fuskarta ko wani abu ya
fado ma ta, saboda bakin ciki ya na cin zuciyata ban
san sanda na ce ma ta marinta aka yi. Dr. ta zaro ido
ta ce mari dan rashin Imani wanne yaron ne ya yi
mata wannan marin? Abikiyar zamana matar
mahaifinta, kuka ya kwace min ta tsaya kawai tana
kallona can ta ce ni sai naga kamar na sanki ko
kuma in ce ana nuno ki cikin TV kina wa'azi kuma
kenan kuna samun matsala ita dcai ba ta kara
magana ba ta ci gaba da sharar hawayenta.
Bayan Anas ya kai Nana gida kai tsaye gidan
Nazir ya zarce su na falo su na kallo ya yi sallama
shi kadai ya amsa ya samu tsarabar harara wajan
Ummu, kai ashe kana da lokacin kallo gudar jininka
wacce matsiyaciyar matarka ke son halakawa ta na
can asibiti rai ga hannun Allah yanzu kai ba ka jin
tsoron haduwar ka da Allah? Ka tuna fa Nur
amanace a gare ka, kukan da Ummu take yi shi ya
katse Anas yayin da ya kuma tunzura Nazir yanzu
darling kana kallo kaninka ya na ce min
matsiyaciya bayan jiya a gabanka ya mare ni ba ka
70
dauki mataki ba to wallahi ni bazan zauna wani
kato na shigowa har gidan mijina ya na ci min
mutunci ba, dole ne Anas ya daina shigowa tunda
ba gidansa ba ne, takaici ya kama Anas ya rasa
bakin magana, shi kuma ganin ta dauko mayafi tana
kuka wai gidansu zata tafi bai san sanda ya yi kan
Anas yana zuba masa ruwan bala'i, Anas bai tanka
ba ganin ya kawo masa mari yasa ya rike hannu ya
ce kar ka yi kuskuran marina, dan wallahi sai nayi
maka dukan da zan kunyata ka gaban matar, so
gidanka in dai ni Anas ne na daina zuwa ka sani
Allah ba ya bacci hakkin Shema'u Allah ba zai
kyale ku ba, ke kuma kiji tsoron ganin karshenki ya
juya ya fita idanunsa na zubar hawaye.
Daga nan gida ya zarce yaje ya sa wa matarsa
ubar ni yai girkin da za'a kai asibiti dan bai dade da
aure matar tasa ba ta fi watanni uku a gidan ba.
Yanzu Anas shi ne a 6angaren da Nazir ya tashi,
Aina'u matar Anas ta ce waye a asibiti ya ce Anty
Shema'u ce Nur ce babu lafiya ta ya Allah ya
sauwake amma dan honey tare zamu kai abincin ko
ya ce yadda kike so haka za a yi, ta yi murmushi ta
shige kicin ta na kokarin dora girki. Anas dakin
Alhaji ya yi, yayi sa'ar samunsa lafiya na ganka
haka dan Alhaji mutum ne mai lura ya ce Alhaji
gaskiya ba lau ba, nan dai ya labarta masa komai,
ran Alhaji ya бaci, ya ce abin da ya ke min kenan
71
har ya na neman hada ni da aminina wanda bani da
tamkarsa wayc silar zuwana Yola yanzu ka ce yana
gida nan ya dauki waya ya kira shi ya ce maza yazo
gida ya na nemansa. Anas ya ce yadda tsarin gidan
Nazir ya ke kana zuwa za ka san Shema'u a takure
take, ya ce to ni Hajiya ta fada min cewar Shema'u
ke azabtar da kishiyarta, dan kwanaki can cewa ta yi
dole in yi wa mahaifinta magana yaja kunnan 'yarsa
to amma ka san mata shi yasa ban dauki maganar
ba, Anas ya ce duk girman gidan Nazir Shema'u
daki daya ne da ita sauran kayanta na zube a gare ji
ko ina da ka sani na gidan Alhaji kayan
Ummukulthum ne. Su na cikin tattaunawa Nazir ya
shigo ta in da Alhaji ya shiga ba tanan ya ke fita ba,
Nazir sai haku ri ya ke bayarwa daga nan asibitin su
ka nufa koda su ka je yarinyar na ta fisge-fisge anan
san diban ruwan kashin gado bayanta amma
Shema'u ta kasa rike ta Alhaji ne ya dauke ta ya na
ta yi mata tofi, ya rike ta aka diba jikin Nazir ya yi
sanyi shi kansa Alhaji bai za ci ciwon ya zafafa
haka ba, kullum Alhaji zai dauko mahaifin Shema'u
su zo su ga jikin Nur duk kuma abin da ake bukata
Anas ne ke yi, don Nazir tun wannan zuwan bai
kara ba, ita kanta Ummu ba ta zo ba da ya ke uwarta
'yar siyasa ce zuwan ta nawa, kullum muna tare da
mahaifiyarta da Aysha da Aina'u matan 'yan uwansa
kullum sai sun zo gaishe ta har Nur ta ji sauki
72
kwanan mu ishirin da takwas aka sallame mu,
gidan mu na fara zuwa sannan dare naje washe
gari Alhaji ya zo gidan ya sa daga ya hada mu ya
yi mana fada ya ce kuma in daina zaman daki in
fito falo duk abin da zan yi in yi gida gidan mijina
ne babu wacce aka yi wa get to farko farkon
dawowata daga asibiti abin kamar gaske, dan duk
me girki a dakinta zai kwana to amma fa daga
karshe abin sai nake ganin kamar ya zarce da.
Na shirya zan tafi makarantar da na ke
koyarwa na same su a falo suna yin lido ya kalle
ni Maman Nur sai ina na ce Yayana zan ta
koyarwa Ummu ta yi tsaki ta ce ni dai kalma nan
ta Yayana ta na bakanta min rai domin ai wannan
shishshigi ne darling ta yaya ka zama yayanta ai
wannan kalmar daga bakina ya kamata ta fito wai
wani Yayanta har wani kashe murya kike darling
daga yau na soke, ya kalle ni ya ce kina ji daga
yau ki sake min suna wannan bai yiwa
Tamusamman ba, haushi da takaici su ka sa na ce
na ki din ai tun kafin kizo na ke fada masa bare
kice yau nasa saboda haka ba ki isa ba, ke kin san
abin da kike cewa ni ce fa ishashshiya a gidan nan
sai na ga dama ake komai kanki ake ji ni na tafi
gurin samun lada, darling wai don Allah saboda
me ka batarta take koyarwa wai ba kudi ta ke
73
nema ba kai ka abin kunya ne aced wai kamar ka
matarka na fita neman kudi ka tuna mahimmancin
karatuna Likita fa amma na hakura saboda in tsare
mutuncinka a idanun al'umma gaskiya ya kamata
ta daina duk wannan surutun da ta ke yi kafofin
yada labarai ra ta daina wata fi sanin Allah, kamar
me jiran umarninta ai kuma ya ce ke Shema'u
daga yau na soke zuwa koyarwa ko wani yawon
lacca da sauransu, ta juyo zata shigo Ummu ta
kaikaci idanunta ta yi mata gwalo ta ce ni ce fa,
sai fa naga karshen na ci gidan nan sai kin barshi
ta shige dakinta.
Washe gari taje ta samu mahaifin mijinta
akan cewa ita gaskiya tana son ta ringa koyarwan
nan amma da ya yi kiran Nazir fur ya ki da yaga
za a takurfa masa shima sai yaje ya fada wa
mahaifinta, mahaifinta ya bata hakuri ya ce ta yi
zaman aure wanda ta yi da, Allah ya ba ta lada
haka ta hakura ta zauna a gida ta zama 'yar girki
kuma in ta yi ma ace ta bade shi da magani, kai
tana ji tana gani Nazir fin sai ya bar kasar ya
dawo iya kacinta da shi ido, sai ta yi sati ko wata
ba ta da kwandala daya, duk ta bi ta lalace ta rame
abin gwanin tausayi, daga ita har 'yarta Nur duk fa
wannan ba dakala da ake me karatu kar ya manta
amarya Ummulkulthum watannin ta shida a gidan
74
ake wannan takun sakar da ita. a yanzu tana
dauke da ciki na wata shida.
Wannan tafiyar da Ummu aka yi ta don da
zai ta fi Dubai tare su ka ta fi don zata je siyayyar
kayan baby babu kunya mahaifiyarta ta dawo
gidan wai jiran dukiyarsu ta ke.
Duk da cewar Ummu ba ta ne turaren magani
ba daina ba a gudan da ace zan daka ta wannan
tsohuwar sai mun ba wa hammata iska, shi yasa
ba na zama sai in tafi gidanmu in zauna in bar
mata gidan, amma in na dawo haka zan ga an fade
min kofar daki da magani iri-iri.
Satin su biyu su ka dawo kayan baby sai da
aka yi daki guda da su dan wani abin haushi har
kirana aka yi in gani aka bude min komai na gani
na saka albarka to wannan karon Nur ta samu
tsarabar akwati guda na kayan da zata yi fitar suna
wai in an yi mata kani domin dan tunkan ta haife
shi aka ce min namiji ne kai ita dama ta ce min ita
maza ta tazo haihuwa ba mata ba, wai haihuwar
mace ko wahala me zata gada.
Lokacin tafiyata Misira yazo ina ta murna
dan dama un yi da Nana Nur a wajanta zata zauna,
kowa na taya mu murna sai shirye-shirye nake
saboda Allah ya taimake mu babu abin da
gwamnatin jiharmu ba ta yi mana ba, haka
75
mahaifina da mahaifiyata tunda sun san irin
zaman da na ke babu mai tunanin Nazir zai iya
taimaka min hatta mahaifinsa ya ban kudi masu
tsoka sai shirye-shirye nake sai da ranar tafiya ta
yi 'yan uwa kowa na taya ni murna amma me sai
me gida Nazir ya ce wai shi bai san da tafiyar ba
da mahaifinsa ya ce haba Nazir ya zaka ce haka
buda idanbunsa ya yi tar ya ce abu na farko yanzu
shi ne Ummu ta kusa haihuwa in ta tafi wa zai
ringa taimaka mata, sannan kuma wai na nuna shi
bai isa ba don ko kwabonsa ban nema ba, sai taje
wadanda su ka bata kudin su bata izinin tafiya,
mahaifin sa ya yi ya yi ya amince ta tafi ya ki
daga karshe dai ya ce ta zabi daya ta tafi karatu
Masar ko kuma auranta.
Mahaifinta ya ce ta yi zaman aure idan kina
da rabo gaba kije ta yi kuka ta yi kuka don da ita
ce karatunta zata zasa wannan aure ko kai ya
babu.
Dadi ya cika Ummu dan makiyar ta bata
samu abin da take so ba don tasan in har ta saka ta
tafi to wallahi in ta dawo ta yi mata zarra yanzun
ma yaya bare taje Masar takaici sai da ya kwantar
da ita don sai da ta yi rashin lafiya duk me son ta
sai da ya ji mata takaici mahaifin mijinta ya biya
mata Hajji don ta ji sanyi a zuciyarta amma shima
76
da lokacin tafiya ya yi sai da aka yi rikıci da
Ummu da Nazir dan Alhaji bai sanar ba sai da ya
zama saura sati ta tafi nan fa daga ji zata yaye Nur
ta tafi ya yi tsalle ya dire shi ba za ta yaye masa
ya ta tafi ba sai dai ta hakura wata shekarar saje
da Tamusamman ran Alhaji ya бaci ya ce yaya ne
dai ba ka so sai yanzu kasan Nur 'yarka ce Alhaji
ya ce Hajji ne Allah ya kirawo ta sai kuma zata
tafi da 'yarka ba zata yaye ta ba shi kenan.
Ummu ranar kwana tayi tana kuka saboda
Shema'u zata tafi Makka ga shi cikinta wata
bakwai ne amma ka ce yau zata haihu saboda
girma, da lokacin tafiya ya yi ko Allah ya kiyaye
ba ta ce da Shema'u ba ita kuwa su ka nu fi kasa
mai tsarki don saukr farali.
Da lokacin dawowa ya yi ta dawo cikin
koshin lafiya ita da 'yarta ga shi ta yi siyayya
sosai abun gwanin sha'awa da ta dawo ta ba wa
Ummu tsaraba ta ce ta ki karba wai ta wuce nan
ita kuwa ko a jikinta shi kuwa Nazir da ta kawo
masa ya karba.
Haka dai su ka ci gaba da shimfida rayuwar
kishi a cikin gidan dan yanzu Shema ta dan yi
baki wani lokaci takan rama abin da ta yi mata
tunda ta dawo Nazir ya shimfida dokar yi mata
girki irin wanda ta ke so saboda cikinta ya ısufa
77
da kyar ta ke tashi ga wani uban kumburi da
kafafunta su ka yi ga shi asibiti an hana ta cin
gishiri yanzu da ya ke cikinta ya tsufa in dai ranar
girkin Shema'u ne in ya raba dare a can zai sulalo
ya gudo nan ya kwana abin ma nasa in ya sa wa
Shema'u haushi wani lokaci sai yaba ta tausayi.
Yau dai tun safe Ummu ke neman fitina don
ko ogan ba ta barshi ya fita ba su na master room
a jibge yau tunda na tashi ya ke sani girki ya ce in
dafo wannan in na kawo ta ce ba ta so takaici
kuwa kamar in yi ihu illa daya ba na iya yiwa
Nazir musu ko me ya sani zan yi.
Bayan sallar Isha aka dauke wuta baby Nur
ta ringa rigima saboda zafi na leka master room
na same shi ya na zaune ta ce baban Nur kasa a
kunna mana inji ya ce babu mai an tafi siyowa ta
fito daga wani daki da ta ke ta ce nima candled na
kunna kema ki kunna nace Nur ke jin zafi saboda
in kunna mata AC ko fanka, cikin gadara ta ce to
ba za a kunna injin ba yau in yaso ta mutu tana
kada kaina zuwa kicin ina goyo da Nur na zubo
abincin na kawo in da su ke ta ringa budewa a
yatsine sannan ta ce gaskiya darling ni ba zan ci
ba ka rasa fada ba na ji ta hankadani ta fita da
gudu gaba daya muka bi bayanta ashe ta kasan
kofa ta hango wuta tana ci kafin muyi wani
78
yunkuri gidan gaba daya wuta ta kama, da kyar
mu ka soma laluben fita saboda yanda wutar ta ke
ci BA BA BA BA amma ina mun rasa hanya.
Mu hadu a kashi na biyu
MAMAN SHUREEM
Allahumma salli ala Muhammad, wa'ala ali
Muhammad, kama sallaita ala Ibrahim, wa'ala ahli
Ibrahim innaka hamidul majid.
TUNATARWA
Dan Allah maza ku daina yo min waya,
domin ni matar aure ce muryata haramunce a gare
ku, in kuna da wata tambaya kwa iya aiko da ita ta
text message.
Mai kaunarku:
ZAHRA'U BABA YAKASAI
79
LITATTAFAN MARUBUCIYAR
UWAR MIJI KO KSHIYA? 1 & 2
BAN SAN HAKA KAKE BA! 1 & 2
HADIYYA 1, 2 & 3
TARKON SO 1, 2, 3 & 4
FUREN KAN JUJI 1, 2 & 3
ZUMUNCI KO ANINCI 1,2&3
HATTARA MATA 1,2&3
HUDUBAR MAZA 1, 2 & 3
HUZAYYA 1 & 2
GANI GA WANE...
AWARWARO
PRINTED BY:
AL-AMIN B/PRINTING & PUBLISHING COMPANY
No.; 156 S/TITIN MANDAWARI KANO CITY. 08028411703Gani Ga
Wanest
NA
ZAHRAU BABA YAKASA!
(Mrs. Dan Ringim)
GANI GA WANE.
1
NA
ZAHRA'U BABA YAKASAI
(Maman Shurcem)
08020863615
1
GODIYA
Ga Allah Subahanahu wata'alah, wanda cikin
yardarsa da ikonsa muke baza muku irin baiwar da
ya yi mana.
SAKON TAYA MURNA
Ga Uncle dina da Allah ya sauki Auntyna lafiya,
Allah ya raya mana MARIYATUL KIFDIYA
Tasi'u D. Yakasai (Baba Wali)
INA TAYA KA MURNA ALLAH YA RAYA
MANA
Hauwa'u Ibrahim Umar Makaruma
(Malam Sabo)
GORON AMARCI
Kinsha kamshi tsohuwar gidanmu.
SAFIYA DAHIRU YAKASAI UMMI
da Angonta
NURA ABUSAKA YAKASAI
Allah ya kawo kazantar daki.
INA SANE DA KAI
Bashir Sa'id Kyautah
2
MASOYA NA GARI, ALHERIN
ALLAH YA KAI MUKU
Hauwa K. Umar College of Education Minna.
Hussaina B. SKK
Hauwa Ali Gwambe
Abubakar Haruna Albasu
Asiha Ishak 'Yar Magaji
Ibrahim A. Bauchi
Maryam Suleman Giade (Ummce)
Hadiza Adam
Hajara Abdullah Baba Sokoto
Hadiza Usman (Hadee Queen)
Zahra Ahmad
Babangida Kumo
Bello M.
Hauwa Mohd Loddo (Maman Ukasha)
Suwaiba Musa
Faruk Umar Gamawa
Fa'iza Moh'd Gaya MJB
Hauwa Usaini Bichi
Maimuna Musa Soja
Abdurrashid Abdun kwallo
Amina Abdullah Ghana
Ahmad Paris Bookshop
Samirf Sha'aibu Jangulu Kazaure
Fatima Adamu Yana
Rukayya Mai dinki D/Kaigama
3
Deeni Alasan Yana
Mudansuri A. Badamasi
Hadiza Ali Sokoto
Aysha Sokoto
H.J.A
Sumayya Mohd Sury (Maman Fadila)
Ahmad Tijjani (Abban Mohd)
Abdullah Dalhatu (Abban Humaira).
GAISUWA TA MUSAMMAN GA MASOYANA
Na kasashan ketare kamar:
Kamaru, Ghana, Abijan, sannan Saudiyya, Paris, da
kuma Libiya.
4
SHIMFIDA
ota cc kirar Jeep baka kirin sai M
daukar ido takc kamar wanda aka
shafc ta da mai (oil), ya fito daga
cikin wannan mota, abisa dukkan alamu da akwai
masu gidan rana (kudi), dogo ne fari mai dan kauri
irin mazan da akc kiran su tall man din nan ne
fuskar shi ta kunshi annuri kasancewarshi mai
sakakkan fuska.
Cikin iko da takama irin na ma su akwai, ya
fito ya rufe motarshi, ya doshi cikin gidan. Gida ne
hadadde flat irin ginin zamani wanda aka dauko
hotonshi daga London, gida ne wanda ya kunshi
kayan more rayuwa na bil-Adama domin tsayawa
misalta wannan gida 6ata lokaci ne sai dai ku biyo
ni a sannu ku ji komai.
Ya na shigowa cikin gida kwatsam ya yi for
cyes da wacce ya tsana ko kuma in ce aka cusa
mashi tsanarta don ba wai a son shi ba ne.
"Sannu da zuwa." Ta fada mashi amma ko ya
kulata, sai shigewa bedroom dinshi ya yi, kulawa
Mà yabawa ne in ji Hausawa.
Ya danna inter come ya kira ta musamman
kamar yadda ya ke kiran amaryarshi wato (ta
musamman) a maimakon sunanta na yanka wato
Ummulthum, ta fito cikin yanga da jinkai a daidai
falo ta hadu da wacce ta tsana kuma ta ki jinin ta
5
Fafi ido ta ganta harara ta sakar matga ta shiga
dakinshi cike da kwarkwasa da kissa, shi kuwa tuni
va rude nan ya rungumo ta jikinshi ya fara
sumbatarta nan da nan su ka manta a wace duniya
suke.
Bayan sun nutsu ne ta dube shi cikin kashe ido
ta ce "Darling yunwa nake ji." Ya zaro ido, Shema'u
ba ta baki abinci ba ne.?" Jikinshi na 6ari bai jira
amsarta ba ya fito falo ya iske ta na kallon TV
tashan Aljazeera ya dube ta "Ke me yasa ba ki ba
wa Ummu abinci ba? Ta dago kai ta dube shi da
kyau, ta ce a baki zan bata ko me? Ran shi ya бaci
wane irin zancen banza ne kike min haka? Cewa ta
yi tana jin yunwa sai ta ajiye remote din hannunta
ta kara ganinshi da kyhau cike da mamaki da
al'ajabi ta ce to ai sai ta shiga kitchen din ta duba ko
anyi mata dokar shiga ne? Sai Ummu ta fito amma
kin san ba a nuna wa ido bacci da