Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 10
dangidan......Sulaiman ya katse shi ya isa haka, ka kwantar da hankalinka yanzu meye abin yi? Sulaiman ya tambaye shi Nazir ya nisa ya ce ka je ka samu Alhaji ka ce ba na son ta ina da wacce na ke so. Sulaiman ya kwashe da dariya, ya cc saboda ni ne tsagera? Sai na je na soke aure ko, to bari ka ji, ni dai nasan meye soyayya, kuma na taba yinta naji yadda take, nasan zakin ta na kuma san dacinta, don haka ina mai ba ka shawara ka karbi zabin da iyaye su ka maka, Allah ka samu ka rabo, kuma kaima 'ya'yanka za su yi maka biyayya, please Sulaiman 19 sati biyu fa su ka ce two wecks fa yanzu mc Jamila zata daukc ni? Kuma tasan ina sonta, kai dai yanzu duk wannan ba ta taso ba, kai dai kawai kajc ka samu Jamila kayi ma ta bayanin duk halin da ka kc ciki, kada ta ji a bakin wani ta ce ka munafurce va, kasan su mata ba a musu gwaninta bai ce komai ba ya yi tagumi kamar wani mutum-mutumi, haka Sulaiman ya lallashe shi su ka dunguma gidan su Jamila, kasancewar bayan layinsu ne ba wani nisa ba ne dasu, sun ci sa'a kuwa sun same ta amma tana fitowa su ka gane ta ji labari, amma ta dan boye damuwarta, su ka gaisa ta dubi Nazir ta ce "Ango da ma ka na ganuwa? Ya kwakwalo dariyar karfin hali ya ce gani kuwa? Ta dubi Sulaiman ta ce ku ana shirin angwanci ana kiba amma ku sai ka ce kudin guzuri. Sulaiman ya yi dari ya ce, kinsan mutun zaj shiga sabuwar rayuwa dama haka ne, amma dai ga ki ga Nazir, za ki ji komai daga gare shi." Nazir ya dube ta cike da sha'awar irin dressing din da ta yi, ya karkata kai ya ce, Jamila da farko ina son ki sani komai nufin Allah ne, kuma duk iya kokarin ka ga ka samu abu idan Allah bai nufa ba to babu mahalukin da zai ba ka komin yaya.....ta katse shi wai duk wannan dogon sharhin na menene Nazir? Ka fadi abin da zaka fada, ya yi shiru bai ce komai ba, can ya nisa ya ce "Jamila sanin kanki ne 20 kinsan ina Kaunarki, to amma wai yau an wayi ga an cc za a min auren dole da wacce ko kusa dani in nace tazo zata ji tsoron zuwa, amma wai yau ita za'a aura min, sai ka ce mata sun kare? Jamila ta ce na ji labari amma sai na musa saboda Shema'u ba ajinka ba ce, amma sai naji da kunnena kai da kanka kana cewa za a maka auren dole to ai sai ka so tunda kai ne me auranta ba ita ce mai auranka ba. yanzu dama Nazir duk fata min lokaci da ka yi ya tashi a banza kenan? Ka sa na kore samarina waton ita Shema'un da aka yi mata snaching din saurayi shi nc ta rama akaina? Yanzu kai kana nufin shi kenan mun rabu kenan?" "No, ba mu rabu ba, kinsan ba zan iya rabuwa da ke ba, in Allah ya yarda za ki shigo gidan nan nawa kuma kece first lady dina kin dai gane? Ya dube ta, yes na gane amma gaski......sai ta yi shiru, ya sake dubanta gaskiya meye? "Babu komai." Ta fada ** Ana saura sati bikin Shema'u da Nazir, Nazir bai taba zuwa hira ba kuma ko sun hadu idan ta gaishe shi bai cika amsawa ba, ranta ya dan Gaci kadan amma sai ta share. Idan ta hadu da Jamila sai bakaken maganganu, gashi uwar Jamila irin 21 matannan ne 'yan duniya wanda ba ta ji ba ta gani wajan nema wa 'ya'yanta 'yanci in ji ta. Mun dawo unguwa ni da Hadizan su Nazir, mu ka yo kwanar gidan mu sai mu ka ga Nazir su na tsaye da Jamila su na hira, raina ya dan sosu amma na dakc naki kula su, muka wuce Hadiza ta cе Shema'u don Allah kiyi hakuri nasan dole ne ranki ya baci, na kalli Hadiza na ce ai duk kc ki ka cисe ni kika zuga ni har naje na fada wa Baba ina son Nazir, kuma ni kam da zai yiwu da na je na ce wa Baba na fasa. Hadiza ta ce "Wallahi kada ki kuskura ki fasa, ai in kunyi aure zai daina wuya ne dai ku zama mallakin juna, kuma sai ya zama tarihi. Ana bikin wata Haule duk kawaye ne da Hadiza da su Jamila to kasancewar Shema'u ba tsarar su ba ce saurin girma dai kawai ta yi Hadiza ta sa haule ta gaiyaci Shema'u suin je wajan (Deener) kowacce ta ci kwalliya da ya ke Jamila tana da rawar kai da kwadi ita kuma Shema'u ta na da miskilanci don har jama'a suna cewa ta fiye jin kai kuma ba haka abun ya ke ba, (natural) dinta ne haka, gaskiya kuma Shcma'u fara ce kyakkyawa ga diri gaba dayansu sun hallara a ball din can sai ga Jamila sun isò ita da saurayin da ya ke nema ya zama mallakin wata. Jamila ta kalli haduwar da Shema'u ta yi ta ja tsaki duk sauran kawayenta sai da su ka juyo, 22 Hadiza ranta ya baci sai Nazir ya yi mata alama da su zauna su ka nemi waje su ka zauna, Jamila ta sake jan tsaki Nazir ya tambayc ta lafiya? Ta muskuta ta cc babu komai su ka ci gaba da harkokinsu, Shema'u ta ce Hadiza ni kam zan tafi gida dan mc? Tа сс "Babu komai Hadiza ta gane dalilin da ya sa ta cc zata ta fi gida, sai itama ta mike "Mu tafi Shema'u." Ta cc 'a'a kiyi zamanki ai ba a gama ba tunda ko farawa ba ayi ba, No, muje kawai su ka dau jakarsu za su fita Jamila ta cc Hadiza ina zuwa? Hadiza ta yi kamar ba ta ji ba ta fice ta iske Shema'u a waje su ka tsayar da masu mashin kasancewar babu masu tasi motocin 'yan biki kuwa ba su fara diban jama'a ba. Su na isa gida Shema'u gidansu ta wuce, kowa ya shiga nasu gidan Hadiza komawa gida ta fadi komai duk abun da Nazir ya ke yi wa Shema'u, Hajiya ranta ya 6aci sosai. Ita kuwa Shema'u ta na shiga gida randa ta nufa ta debi ruwa mai sanyi wai dan taji sanyi zuciyarta, Nana ta kalle ta ta ce lafiya a'a babu wani abu da ki ta shiga ta kwanta zuciyarta na fidda wani sauti wanda a zahiri ta rasa mene nc kafin ta ankara wani zazzafan hawaye ya wanke fuskarta, babu wanda ya cutar da ni illar Hadiza wuf kamar wacce aka je fo Hadiza ce ta shigo ta kamo hannunta ta 23 dago ta ya aka yi ne mutuniyar haushi ya kama ta ta ji kamar ta shake ta baki da kalmar da za ki cc min dan kin cutar da rayuwata a yanzu na soma hango wa kaina irin kurkukun da nake niyyar cusa kaina ciki don na fahimci irin zunzurutun kin da Yayanki ya ke min yayin da ta dafe kirjinta tana cewa Hadiza danna min kirjina kinga ji nake kamar zaj fashe Hadiza ta fashe da dariya ta ce lallai Shema'u wato ke kishin naki mai zafi ne! Cikin rashin fahimta ta ce, an ce miki kishi nake kwarai da gaske kishi ki ke dan ba kya kishin Yaya Nazir da hakan ba ta faru ba, kuma a yanzu na tabbatar da irin son da kike masa, so na hakika ne, ina kuma ba ki goyan bayan kar ki sausauta masa don nasan zai so ki don kin fi Jamila komai nesa ba kusa ba, ina son ki tabbatar min ke macece. Nazir shi da abokinsa Sulaiman su ka shiga gida, Hajiya na zaune ta na yankan alayyahu su ka yi mata sannu, kallon in da su ke ba ta yi ba su ka yi tsugune a gun sun kasa tashi illah wannan ya zunguri wannan, wannan ya zunguri wannan, Sulaiman ya yi karfin halin cewa, "Hajiya muna neman afuwa a bisa laifin mu." Haushi ya kama Hajiya ta cc "Sulemanu me kuka yi mun iyaka kunnunawa duniya ccwa mu muka haife amma ba mu isa da ku ba, tunda kuwa haka ne me zamu ce daku illa muyi muku addu'ar shiriya." 24 "Hajiya mun tuba mun amshi tayinku a yanzu ma duk wani shirye-shirye mun kusan kammala shi." Hajiya ta ji dadi cikin zuciyarta, to kuwa in haka ne daga yau har zuwa ranar da za'a kammala bikin ina so kullum kaje ku ringa gaisawa da Shema'u don ku fuskanci juna gaba daya, wannan karfan su ka amsa. Irin dinkin nan na doguwar riga wanda 'yan birni suke kira da gosulo shi ne a jikinta, ya matse kirjinta tsam shi ya bayyana sirrin kirjinta ga shi karamin hannu ne damatsanta duk sun fito waje, da su ka je Kano biki tayo dinki don ya na matukar birge ta, wani ni'imtaccen kamshi ke fita a jikinta, wani karamin mayafi ne ta sakalo shi a wuyanta ta fito daga gidansu da zummar shiga gidan su Hadiza, ji ta yi an ce ran amarya ya dade, ta yi saurin juyowa saboda jin muryar bakuwa ce a gare ta, ta kalli Sulaiman gefensa abokinsa ne Ango Nazir, haushi ya kama ta tumba da ta kalli fuskarsa taga babu annuri, itama sai ta dada shan kunu ta ci gaba da tafiya tana amsa gaisuwar Suleman din a'a ranki ya dade ba za ki tsaya ki saurare ni ba, wajanki fa mu ka zo, oh ai ban sani ba ga shi kuma kun yi rashin sa'a don yau ban ji yin zance da ku tattara koma tsanku kuyi wajan Jamila don ita ce daidai ku amma ni yanzu bani da lokacin ku. 25 Haushi ya kama Nazcer wai wannan 'yar ficiciyar yarinyar zai zauna ta na yaba musu maganar da ranta ke so, bai san sanda ya tattaka zuwa gabanta ba ya kare mata kallo daga sama har Kasa, shi kansa yasan akwai kyan diri illa iyaka tayi masa kankanta, yarinyar da ko irin cikar nan ta budurci ba ta gama ba, a hankali ya ke fitar da sautinsa tamkar me rada don ko Suleman ba na jin ya ji abin da ya ke fada ma ta. "Ke ki shiga hankalinki, ki san da wa ki ke magana, ki kuma san waye a gabanki ke kanki kinsan ba girman kujera ta ba ce ace ina tsayawa da kwaila kamarki, ina so ki sani biyayya zata sa in tsaya da ke ba wai so-ba, kin gane." "Kai an fada maka sanka na ke hadi ne kawai irin na iyaye tunda ba shawara su ke da mu ba, don da sun yi shawara da mu kai kanka kasan ba kalata ba ne." Jin kalaman ta ya yi tamkar dirar aradu, kafin ya farga ta fada cikin gidansu, dakin su Hadiza ta shiga tare da annushuwa cikin zuciyarta ta dan ko ba komai ta rama don tum tayan kewa kanta wannan shawarar ko ganin haka zai sa iyaye a fasa. Dangantakar Nazir da Shema'u ba wai 'yan'ujwa ba ne na jini ba, illa aminci irin na da da iyayansu abokan juna ne tare su ka tashi don shi Alhaji Jibrin mahaifin Shema'u dan asalin garin 26 Yola nc, yayin da shi Alhaji Yusuf bazazzage ne tunda kasuwanci ya hada su har Allah ya sa shi Alhaji Yusuf ya dawo Yola ga gida ga gida su ke wannan dangantakar shi ya sa su ka zama tamkar 'yan'uwa na jini don irin wadanda ba su sani ba gani su ke wa da kani ne. don Nazir Yusuf ya bi maganar mahaifiyarsa kullum zai zo sai dai fa ba wai zance ake mai dadi ba, illa in ya fada ma ta magana za ta rama, ana igobe daurin aure ne ya na zaune kan motarsa ya aika kiranta, cikin yanga ta karaso in da ya ke ko kallonsa ba ta yi ba, daga Sallah ma ta tsuke baki, ke ba ki iya gaisuwa ba ne, ba tare da ta kalle shi ba ta ce ni ban san in da ake yin ta ba, cikin murmushi ya ce zan koya miki yanda akc yin ta kawa, dan kinsan gobe za su daura a kuma goben za akai ki ina so ki sa wa ranki da zuciyarki za ki je yin gadi ne ba wai zaman aure ba, don kin san matsayin maigadi shi ne matsayinki, amfanin ki ki jire min gidana da dukiyata kin ji 'yar kyakkyawa." Ya fada ya na murmushi, ta yi tsaki an gaya maka zama zanje yin gidanka? Ta juya don jin yanda kwalla ta ke neman subuce ma ta, kafin ta ankara ta zubo hannu ya sa ya rike ma ta mayafi ai ban gama ba ki ka juya za ki tafi." Ta so goge hawayen kafin ya gani amma ta makara, don ya gani. 27 "A'a, tun yanzu? Kin ban kunya tunda kin soma karaya." Cikin tsiwa ta ce "An gaya ma ka saboda kai nake hawaye, never wallahi, in yi hawaye domin ka just kwaro ne ya fada min ido." "Ya kamata ki gyara bakinki in ba haka ba ran da duk kika zo hannu sai wannan bakin ya raina kansa." "Kanka ake ji." Ta juya ta yi tafiyarta. ** Biki ya yi biki, ta fangaren su Nazeer Yusif biki ne na masu 'ya'yan banki, amma ta bangaren su Shema'u biki ne na masu rufin asiri. Gidan su ango sun kashe makudan kudi don lefenta ma abin kallo ne, dan mahaifinta da kin karba ya yi, amma Alhaji Yusif ya nuna masa sittira ita ce mutum, kuma Musulunci ya amine da ka yi wa iyalinka suttura yayin da sadakinta dubu hamsin, shima mahaifinta yayi rawar gani wajen fitar da 'yarsa kunya, dan ya yi ma ta furniture na fita kunya, a ka'idar Nazir ya so zama a wani karamin gidan sa da ke bayan layinsu, amma mahaifinsa ya ki ya ce shi da ba mazauni ba ya na tare da su don a nan cikin gidansu aka ware ma ta 6angare daban. Ta bangaren abokansa kuwa, sun shirya masa party ya kai kala takwas yadda bikin ya kayatu ya jefa zuciyar Jamila cikin wasi-wasi dan gani ta ke 28 ya na so yaudararta kawai ya yi don ganin yadda hoton Calender su ka yi matukar kyau in da ya na rungume da ita ita kanta tasan sun yi macing da juna, haka jakar bikinsu ta birge ta wannan shi ya dada tabbatar ma ta da cewa ta rasa Nazeer don tasan ya auri mace wacce ta amsa sunanta. Bisa al'adarsu randa aka daura aure to a ranar ake kai amarya washe gari ayi budar kai, to haka aka yi wa amarya Shema'u, ita haka aka kaita don yawancin fatin da aka yi tana gidanta ta ringa halattar sa, haka nan an yi lacca wacce ta ratsa zukatan al'umma wacce fitacciyar Malamar nan ta yi ni kaina ba karamar karuwa na yi ba wajen saurarar laccarta haka dai biki ya kammalu aka watse. Su na zaune ita da yaran gidan cikin falonta, har ma da matar wansa Abubakar sun mai da hankalisu wajan kallon kaset din biki a gaskiya kaset din ya yi kyau akwatin TV din ya nuna ango ya yanko cake ya sa wa amarya a baki, waje ya dauki tafi falon na ta jin su ka dauka su na fadin sai metar Yaya ta harari Hadiza ta ce, Hadiza ba na so." shigowar Nazeer ta katse su yayin da gaba daya su ka mike su ka fice, ya ce "ku yi zamanku mana." su ka ce a'a mun gani koda gobe nę su ka fice itama kashe kayan kallon ta yi, ta yi dakinta ba ita ta fito ba sai da gari ya waye, ta yi wanka ta shirya cikin 29 kyakkyawar shiga ta shirya abinci kan tebur ya па fitowa daga dakinsa kamshin abincin ne ya daki hancinsa ta na falo ta harde ko kallonsa ba ta yi ba ya fito yajc kan tebir ya duba abinci ya ce mu ko b ayi mana ta yi ba ci zamu yi ta yi tsaki ba tare da ce komai ba, ya kai dubanta kan fuskarta ya ce "Kat ki kuskura in kara magana kiyi min tsaki, ba ta tanka ba sai da ya kammala cin abincinsa ya kalle ta ya ce sai ki dauko mayafi muje gaida su Hajiya ko ta ce tun dazu naje ya tsare ta da ido kinje da wacce hujjar, ni dama ce ba tare da wani nake zuwa ba saboda haka yanzu ma ba mai takura min, ya tsare ta da idanunsa har sai da ta ji tsoró sannan ya ce ki bude kunnenki ki saurare sharudda-na in kunne ya ji jiki ya tsira abu na farko shi ne ba na son raini dan ni mutum ne wanda nake son a bani respecting dina, ke bari in tambaye ki tunda ki ka zo gidan nan kin taba gaishe ni daga yau dole ne ki ringa gaishe ni a matsayina na abokin zamanki, sannan nasan kinsan ina da olsa dole ne ki kula da abincina kin ga can dakina ne ya nuna ma ta da hannu ban gayyace ki ko wucewa ki je yi ta dakin ba balle ki shigar min in gyara ne zan gyara abina sannan zancen zuwa gaida su Hajiya dole ne ki jira ni in dai ina gari dan muje tare, kamar yadda Yaya Abubakar ke yi da matarsa Aysha, kin dai ji abin da na ce." Ya baza ma ta kamshinsa ya fice gaida iyayansa. 30 د Ajiyar zuciya ta yi ta cc, "Allah gani gare ka Ubangiji ni dai nazo yin bautar aure nc ba wai bautarwa kamar yadda ya ke son bautar dani ba, Allah ka bani rinjaye a kansa in da rabon zama a tarc da mu Allah in babu rabon zama ka kawo hanyar rabuwa ba tare da amincin iyayenmu ya wargajc ba, Allah ka sassauta min zuciyata ka bani juriya da hakuri da dangana akan duk irin yadda zan tsinci rayuwata, ji ta yi hawaye na bin fuskarta ta kuma yi alkawarin babu mai jin irin zaman da su ke ko da kuwa mahaifiyarta ce bare Hadiza da take ganin ita ce sila. Shigowarsa ce ta sa ta share hawayenta ya shige dakinsa can kuma ya fito da hula a hannu alama ce ta fita zai yi, muryarta na rawa ta ce a dawo lafiya Allah ya kiyaye hanya ta yi alkawari tunda mutum ne mai son girma ta yi aikawarin zata girmama shi fiye da tunaninsa. Gidan su Nazir cike ya ke da yara saboda haka koda yaushe in sun ta fi School zata ji gidan ya yi ma ta wani iri, hatta Hadiza ta koma School don ta shiga SS1 ga shi ita ba zancen ci gaba da JS an yi ma ta aure, takaici yakan isheta ita kenan kullum kirkirar girki saboda Nazir amma zai cinye ne ba tare da ya nuna ma ta jin dadinsa ba, kullum cikin kwalliya ta ke amma a banza yadda ta ke ba shi girma abin ba magana idan ya ta fi Dubai ya kan yi 31 wata daya wani lokacin ya haura amma in ya dawo sati daya nc ko biyu zai juya, abinci kuwa ba ya yanke ma ta haka kudi don duk sanda zai tafi dubu talatin ce zai ba ta, ta 6angaren abinci kuwa babu abin da za ta nema daman su iyayen mijinsu ba su amince da hadin girki ba, daga ita har matar wansa kowa nasa ya ke yi, saboda haka ba ta da matsala haka kuma in dai Nazir baya nan Alhaji Yusif kullum in ta je gaishe shi zai ba ta kudin kashewa, nan da nan ta yi mulmul abinta ta yi kyau ta dada girma. Abin da ta kula da shi, shi ne Nazeer bai rabu da Jamila ba, sabodá duk randa ya dawo daga Dubai ta kula tsarabar da zai ba ta guda biyu ake yi iri daya, sannan duk randa ya dawo sai an kawo masa danbun nama fal dish tasan daga gurin Jamila ya ke saboda haka ita dai kullum fada wa Allah ta ke ya yi ma ta zabin alheri. Sun zauna falon Hajiya ta ji ihun yara su na ga Yaya Nazeer, ga Yaya Nazeer, gaba daya 'yan falon su ka fita tsakar gida aka yi ma sa sannu da zuwa nima nabi sahunmsu na yi masa sannu da zuwa. Mun shiga gurinmu na sa ke gaida shi tare da yi masa sannu da zuwa, Yayana ya na ganka kwatsam babu wuya, haka na zaba ga shi ban tanadar ma ka komai ba, ya ce ba na tare da yunwa, ta ce amma duk da haka ya kamata in yi ma dan special dish ko, 32 ya ce ganin damar ki ne, ta mike ta shiga kitchen ta shiga sarrafa nau'in abinci kala-kala, kamshi kuwa ya cika gidan shi kansa maigidan ya matsu a bashi rabonsa, ta shirya tebir taje ta yi wanka ta tsala kwalliya cikin wani material wani baki ya na da sirkin kyalli riga da ya dace da kayan, ni kaina ta birge ni don ta yi kyau ta yi amfani da turaruka don mijinta gwanin turare ne, bai rage ta da shi ba, don ita kanta ba ta san iya adadin turarukan ta da ke kan dressing mirror din ta ba, ta fito cikin yanga da kada jiki wanda wannan halitta ne haka Allah ya yi ta, ta zauna shi ma da cikin kwalliyar ya ke tamkar mai zuwa fati, sai dai shi Kananan kaya ne ta yi saving dinsa ya na cin abincin wayarsa ta soma fidda sauti tasan calling dinsa ake yi, saboda haka taje kan kujera ta dauko ta kalli sunan da ke jikin wayar taga an rubuta my love amma sai ta dake ta hadiye fushinta ta durkusa ta mika masa ya daga ya yi sallama tare da cewa, ran my love dina ya dade, ba ta san me aka ce masa ba, amma ta ji ya ba ta hakuri tare da rantsuwar dazu ya dawo yanzu ma ya ke cin uci, daga karshe dai ta ji ya na alkawarin ga shi Lan zuwa daga nan zuwa awa daya da rabi, ta hada kai da tebir ba ta san sanda ta ringa fidda sautin kuka ba, ya kashe wayar ya bi ta da kallo amma cikin ransa ba ya jin dadin kukanta, ya bita da kallo ya ce, "SHEMAH!" Yadda ya fadi sunan sai ta ji 33 kamar duk duniya babu wnada ya iya fadın sunanta kamarshi, kai ita tunda ta ke ma bai taba fadin sunan ta ba sai yau, lafiya kike kuka? Haba Yayana ya za ka fadi haka bayan kasan abin da kayi min, ina matsayin matarka ka ringa hira da wata a gabana ka na tsammanin ba zan ji kishi a raina ba, ka na sanc da Hadisin da ya ke tabbatar mana duk matar da ba ta kishin mijinta ba za ta shiga aljanna ba, haka duk mijin da ba ya kishin matarsa shima ba zai shiga Aljanna ba, Yaya na bika na bika wai ya ka ke so da rayuwata? Ka tuna ni amana ce a wajanka, nasan ba ka sona to amma ya kamata kayi min adalci ka maida ni hannun mahaifina tunda shi ne ya ba ka abin da ba ka so, in yaso sai ka kawo Jamila ta zama matarka ina so in sanar maka nima mutunci wacce a iya dan nawa sanin nasan illar irin zaman da muke tunda nasan ko Musulunci zai iya raba aurenmu, ina son in tabbatar ma ka da cewa ci da sha da sittira ba shi ne aure ba, bayan wannan akwai wani abu ina so Yayana ka taimaki kuruciyata ka da ta kare ban mori komai ba, wani irin kuka ya kwace ma ta, shi kansa ya na son matarsa illar girman kai da tsoron kar ya yarda girman kujerarsa, (ko ina girman kujera a gurin da namiji in yaje hannun mace) ya shiga rarrashinta tare da cewa zai dauki matakin karshe hannu ta ya kama wai tazo sujе dakinsa ya dauko ma ta tsarabarsa, zungur-zungur 34 su ka kama hanyar dakinsa sai da su ka je kofa ta turje wai ba za ta shiga ba, don ta na bin umarninsa ya yi dam, shima ya ce ai yanzun ma kina bisa umarnina ne ta ce a'a Yayana shiga ka kawon ina nan ya dan jima da shiga ya fito su ka zauna falo ya shiga fidda tsaraba ya na cewa kinga wadannan ke na sayowa, ya ba ta zobuna da sarka kirar Dubai, ya ce kinga wadannan ma na ki ne, dadi ya cikata ta ringa murna ta na fadin godiya na ke Yayana, ya ci gaba da fidda dogayen riguna da mayafan ta zaro ido Yayana wadannan duk nawa ne? Domin ki na siyo saboda dama ina son in shiga cikin sahun mazan da suke kyautatawa iyali. Tun daga wannan lokaci ya shiga kyautata ma ta, ba ji ba gani, komai ya samu ita, ilarshi daya ba ya barin ta fita babu in da ta ke zuwa ko da so ta ke ta fita to lallai sai dai ta tambayi Hajiya, ita kuma ta tilasta masa, ganin haka ya sa ta yanke shawarar shiga Islamiyya da ke cikin unguwarsu. Ba karamar rigima su ka yi ba akan shigar ta makaranta, don sai da Yayansa Abubakar ya yi ruwa ya yi tsaki ya ce sa ringa tafiya ita da matarsa, ta shiga makaranta cikin nasara domin dama tayi nisa sosai saboda haka sai ta shiga aji 'yan high Islam, nan da nan sunan ta 35 ya yi fice cikin makaranta da ya ke da wuya Malami ya fita ba ta yi masa tambaya ba, wacce ta shafi addini in kuwa lacca aka yi dole ne ka ji ta na watso tambayoyin da kowa zai karu. Nazeer ya kamu da son Shema'u bil hakki, ya rasa ta in da zai nuna ma ta kaunarsa, domin ita tuni ta yanke kaunar zai so ta duk hanyar da taga ya na bi dan a sasanta to ita kuma sai ta hau dokin naki, abin ya na damunsa musamman in yaje gidan Suleman yaga yadda matarsa ke tarerayarsa, amma shi in ya shigo gida sai dai ya tarar da tasa matar tsakiyar takardu ta fi ba wa karatunta mahimmanci akan komai. Yau ma saukarsa kenan ya shiga bangaren su ya same ta ta yi nisa cikin bacci, gefenta kan kujera ga doguwar rigarta nan da hijab har da nikaf a jikinta, kuwa daga ita sai unders da bes karar TV ta cika falon don da

Chapter 2 of 10