sanar yadda Amrah ta
dinga kiran Sunan Iyayen-nata da sauri ya mike, cikin
muryarsa mai dadi yace da nurse din, ku kula da ita minti
kadan dan dawo.
****
Yana fita daga asibitin ana kiran sallar magriba, direct
hanyar gidansu ya dauka, abinda yake bukata first canda kayan
jikinsa da jini ya bata kafin komai, hannunshi daya yasa ya
dauki wayarshi dake saman Dash -board din motar, ga
mamakin shi missed calls ne rututu daga na Mom and Dad sai
na yan sanda wanda kiran su yafi kowanne yawa.
93
AKWAI KURA 2
Har da wasu numbers din ma da bai san su ba, Saleem ya
danna kiran Dad bugu daya Dad ya daga kiran kamar daman
shi yake jira, Son kana ina Dad ya fada cikin sanyin murya, da
alamun yana cikin damuwa Saleem Cikin Gajiya yace Dad
gani a hanyar gida, Owkhey Son kayi sauri, tom Dad Saleem
ya fada.
Kiran Dad ya kashe tare da sake danna wata Number, cikin
sauri aka daga, daya daga cikin yaran shi ya fara magana Oga I
hope kana cikin koshin lafiya ? Saleem ya amsa yes, Oga
Gawa biyun mun kai su Asibiti suna cikin mutuware, sauran
kuma suna tsare a hannun mu Sai kazo, Hakan ya yi Saleem
ya fada tare da cigaba da magana ku cigaba da tsaron su Nayi
muku umarni kafin in do ku sassaba musu kamanni ku tabbtar
sun fadi hujjarsu ta sace mata ta kafin In zo da kaina
Oga Akwai fa matsala What Saleem ya fada tare da rage gudu
yaron ya cigaba da magana mun samu lbr daga Oga Ahmad
cewa ita yarinya nan da ka kai Asibiti ita ce ta Kashe mutane
biyun da suke mutuwari So Oga ka kula may b she is
criminal..... wait Saleem ya fada cikin ihu dan uwarka matar
tawa ita ce criminal ? Har abada Matata ba data taba zama
criminal ba uban wa ya baka damar yi mun surutu da har daka
Aibata min Matata? cikin rawar murya ya shiga bawa ogan na
shi hakuri tare da neman afuwar ba dai sake ba Mtsweeee
Saleem yaja tsaki tare da kashe wayar yana huci.
****
Ummy da Granny tare da dukkan yan uwa na kusa suna
cikin tashin hankali, musamman yadda suka ga Saleem ya bar
gidan cikin rudanu,Tun barin Saleem gidan Mummy ta kasa
daune ta kasa tsaye, sosai rashin mijin nata ya taba ranta koba
komai da dai lallashe ta.
94
AKWAI KURA 2
Haka Granny saboda kuka idonta ya kumbura suntum abunka
da tsufa tuni hawan jinin ta ya tashi, karshe sai da Ummy ta
dangana da kiran family Doctor din su ya duba lya, Ita kanta
Ummyn karfin hali take ba dan tana jin dadin jikin nata ba,
Damuwa goma da ishirin ga rashin diyarta ga kuma mijinta a
hannun hukuma.
Awa hudu kacal da kama Abban Amlah maganar ta isa ga
inanyan shi na wurin aiki, ba tare da bata lokaci ba Babban
nasu da kanshi yaje Ga yan sanda, kasancewar sa babban
mutum ne cikin lokaci kankani suka bada Belin Abban Amlah
ba tare da sun tuntubi Masu karan ba, fada da hukuma ai sai
hukuma.
Abban Amlah bai bar wajen ba Sai da Ya karbi belin Zahra
da Maheer tare da alkawarin in har Bukatar neman su ta tashi
zasu zo dukka a tare.
Kamar daga sama Ummy taga Abban Amlah ya dawo
abunka da mata da miji sai Allah sosai taji dadin dawowarshi,
cikin kuka ta sanar da shi abinda ya faru da safe, Abban Amlah
bai yi kasa a guiwa ba, ya nemi Maheer a waya kan ya bashi
Numbern Saleem-ba tare da-bata lokaci ba ya tura masa sai dai
tun lokacin yake kiran Saleem ba'a daukaba.
Karshe tedt message ya turawa Saleem kan dan Allah ya
dauka still ba'a dauka ba, Ummy ta share hawayen Abban
Amlah, Mu barwa Allah komai shiyasan Yadda dai yi damu
ni kam yandu na sare bani daton yarinyar nan tana raye ta fada
tare da sake fashewa da kuka mai karfi.
****
Zahra ta ci kuka sosai a office din yan sanda, Tun da take
a rayuwar ta bata taba duwa station ba bare a kai ga kulleta a
cikin cell, Sai dai wannan baisa zahra ko-kadan ta yi fushi da
bestyn na taba illama karin kukan nata kan rashin sanin inda
95
AKWAI KURA 2
bestyn ta ta kene domin ta allaka batan besty kan laifin ta inda Mahcer dan da basu je Sun dauke ta har gida ba da yandu babu maganar batan Amrah.
Maheer Gareshi Abinda Saleem ya yi sam bai bashi mamaki ba sabida ya san abokin nashi tuni akan gaskia da tsayawa akan ta, Tun fil adal wannan tsayuwar daka da Saleem yake akan aikin shi, sune suka sanya masa kauna ga
manyan su har ma da yawan Mutanen gari. Koda yan sanda suka sake shi da yawan mutane suna zagin Saleem kan Rike Maheer din da yasa aka yi da matar da dai aura, Cikin su ko har da masu zigi kan Maheer din ya daina
abota da Saleem saboda todarcin da Saleem yai masa,-sai dai- Kallo basu ishi- Maheer ba gareshi babu haushin Saleem a
ranshi ko kadan dan hakan shine dai dai ya yi imanin in shine
hakan ya faru tabbas dole dai yi abinda Saleem ya yi.
A mota hanyar mai da Zahra gida Zahran kuka take sosai
kan rashin Amrah hakan ya kara taba duciyar Maheer cikin
rarrashi ya kai Dahra gida bai tsaya wata wata ba ya mata
sallama da niyyar za suyi waya cikin sauri yaja mota duciyarsa
cike da daukan Alkawarin yau babsai gobe ba za'ayi wasan ya
kare.
Direct Office din yan sanda ya wuce cikin tsananin bacin
rai Wanda yan sanda da kansu sunji tsoron yanayin da yazo, da
sauri yan sandan suka rufa masa baya wajen wanda suke rufe
cikin bacin rai Maheer ya ce da su a kai su dakin horo na ga
kuna wasa, da gaggawa Suka tusa keyarsu zuwa dakin duhu.
Maheer cikin rashin imani ya fara Dukan Security nasu da
aka kama kamar Allah ne ya aiko su tare da musu horo mai
tsanani, Ganin Maheer na son kashe su tuni su ka ce dasu fadi gaskiya, bai saurara ba ya cigaba da musu horo sai da yaga
sun jiga ta kafin ya fara sauraron abinda suke fada, inda tuni
96
AKWAI KURA 2
wanda yake da alhaki kan laifin ya fara yiwa Maheer bayani ya yin
******
da daya daga cikin yan sandan yake nadewa a recoding.
Motar Saleem tana shigowa get, daga daki Dad ya hangoshi ta saman benc bai jira Saleem ya shigo ba da hanzari
Dad ya sauko Mom da itama taji karar motar da sauri ta fito
daga daki sanye da hijabi da alamar sallah ta idar.
Saleem ya bude mota ya fito karaf idonshi ya sauka akan
iyayen na shi dake rigen isowa gareshi, Da sauri ya karasa
gabadayan su ya hada ya rungumesu tare da sake murmushin
jin dadi, Dad ya nuna jikinshi Son lafiya ? I hope ba wata
babbar matsala? Mom ta-zaro-ido Son Jini-fa! Jinin waye a
jikin ka ta fada tana shirin kuka, Saleem ya yi gajeriyar dariya
cry cry Mommy kwantar da hankalinki diyar ki Ta fito cikin
yardar Allah an sameta, mum ta daka tsalle kamar yarinya-tana
murna tare da furta kalmar Alhamdulillah.
Dad shi ma dariya ya taya Mum yana godewa Allah,
Saleem ya kallesu cikin kauna Tnz Mom tnz dad d special care,
No Son In bamu baka kulawa ba wa zamu bawa, Saleem ya
daga kafada tare dayin-murmushi babu-ni din dai-ni daya babu
wani gabadayan su suka fashe da dariya.
Mum tace Son wato an warke an fara-tsokana ko ?Saleem
yad aga gira yes Mah jinin jikina ta samu ai sai Rigima, mum
ta kalleshi Son ina diyar tawa ina kewart, Saleem ya runtse ido
Tare da kallon iyayen nashi Mum Tana asibiti Subhanallah
suka fada gaba daya Muje ciki ya fada tare da fara yin gaba da
sauri suka rufa masa baya cike da alamar tambaya.
Falon Saleem suka wuce Saleem ya kalli mum ya langwabar
da kai Mom kidan nemawa Matata abu-mai ruwa ruwa ba rinyi
wanka in wuce da shi asibiti, Mum tabata rai Son ba lokacin
wasa bane meya faru? Saleem ya fara balle maballin rigar shi
97
AKWAI KURA 2
mum wannan sai an samu nutsuwa yandu dai tana " Ansar Hospital " akwai ciwuka a jikinta ciki har da harbi a kafa, Innalillahi wa inna ilaihirrajiun duka suka fada Saleem tuni ya barsu suna sallamewa ya shiga bandaki wanka.
****
Da sallama ta haura saman Ummyce ta leko tare da sake fuska Ah ah hajiya kece a daran nan, Mum ta yi murmushi nice hajiya ai ba muga ta zama ba, damuwar tamu ce duka. Ummy ta kalleta cikin jindadi tace ngd sosai hajiya kuma na yaba da kulawar ku ga Amrah Allah y akara zumunci, Mum ta yi dariya Amrah abar so ce ga kowa ba gani kadai ba sai dai wanda yake da hassada,-mum ta nuna kanta tun da na fara
ganin Amrah zuciyata ke kaunarta ba gani kadai abun ya tsaya ba, yayana duka suna kaunar Amrah musamman Meera,
yanzu haka tun da ta samu labarin batan Amrah take cikin
tashin hankali jibi in shaa Allah tana tafe zuwa KADUNA.
Ayya Ummy ta fada tare da jin Sanyi a ran ta gami da farin
ciki maras misaltuwa, Hajiya-mun-gode da kauna, Allah -yakara dumunci, na barki tsaye muje ki samu gurin dama wallahi
kakar Amrah ce babu lafiya jikin ya motsa saboda damuwa,
mom tace to ai sai ta warke Domin Allah ya amshi addu'armu
anga Amrah,
Ummy ta dafe kirji tace da gaske hajiya ko dai mafarki
nake ? Kamar yadda na saba Mum ta yi dariya yanzu hakan na
zo ne muje gareta Son yana falon kasa yana jiranmu, Ummy
ta daka tsalle Alhamdulillahi rabbil alamin.
Da gudu ta bar mum a tsaye tai dakin Iya, cikin kukan dadi
take fadin Iya tashi Anga Amrah Tashi muje Iya kiga Amrar ki,
Iya dake kwance tun safe ta kasa tashi saboda ciwo, da sauri ta
mike tana ware idanu Zainabu kika cemin an ga jikata ?
Ummy ta fashe da kuka bata san lokacin da ta rungume mijin
98
AKWAI KURA 2
F
그
taba, cikin kuka take magana Abban Amlah muje anga Amtah,
da sauri ya furta Alhamdulillah mun godewa Allah bai tsaya
wata wata ba ya dauki key din mota muje Ummyn yan uku,
Iya da tuni ta ware kamar ba itace ke jinya rai a hannun Allah
ba.
Muje Usmanu muje inga Jikata, Ummy da sauri ta ra rumi
danin gado ta yafa aj ikinta muje Abban Amlah, Abban Amlah
cikin sauri ya koma daki bai jima ba ya dawo da hijabi da sauri
Ummy ta karba ta sanya da sauri Bata jira shi ba ta yi falo ya
yin da Iya ta rufa mata baya cikin jindadi, Abban Amlah ya
kwalawa mai aiki kira da gudu tazo ta durkusa yauwa sadiya ki
kula da yaran nan za muje mu dawo to ta fada cikin-ladabi.
Mum tun saukowar Iya ta ganeta cikin mamaki take kare
mata kallo tare da kara tabbatarwa ita ce ?. Wani dadi ne ya
lullubeta cikin sauri ta karasa gareta-Iya ! Sannu da gida- İya
ashe rai kanga rai ? Mum ta fada sai dai Iya hankalinta naga
jikarta ita ma kallo daya ta yiwa mum ta gane itace matar data
kusa kashe ta da mota.
Mum cikin ladabi ta fara gaishe da Iya sai dai Iya bata amsa
ba-harara ta- dannawa-Mum ke ajiye gaisuwar ki niba Ta ita
⚫nake-ba damuwa ta kawai inga lafiyar Zainabu na, bata tsaya
wata wata ba ta. rufawa Saleem-baya ya yin da gabadayan su
suka fito dan zuwa ganin Amrah.
Mom ta shiga motar da suka zo day ita fa Saleem Abban
Amlah yaja tashi motar wanda yake dauke da su Iya da sauri
maigadi ya wangale musu get din da gudu motoci biyun sika
fice daga gidan Abban Amlah...
****
A tare Motocin nasu suka shigo asibitin Ansar Hospita
Saleem a gaba Sai motar Abban Amlah a baya, Saleem ya
nemi wajen parking cikin sauri yafito daga motar, bayan motar
99
AKWAI KURA 2
ya bude cikin Nutsuwa Mommy ta sanya kafarta ta fito, Abban Amlah shima wajen ajiye mota ya nema bayan ta Saleem ya yi parking cikin sauri shima ya fito daga motar. Ummy dake gaban Motar ta fito da sauri bata yi wata wata ba ta rufawa Saleem baya, shima Abban Amlah bayan su yabi
ya yin da Saleem yake gaba, Granny biye a bayansu burinta
kawai taga Amrah, Saleem ya dan saurara da tafiyar ta hanyar
tsayuwa dalilin jin Horn na motar Maheer aiko idon sa Ya
sauka akan motar Maheer din dake wajen get, Gabadayan su
suka tsaya ganin Saleem ya tsaya Granny ta bata rai bayan ta
gane saboda kallon Mota ya tsaya cikin masifa take magana
Kai mai jan kunne kaimu dakin sai ka dawo ka cigaba da
kallon motar ni bani son kauyanci yo mota wacce kazo cikin
tama ta fi waccan din da kake kallo kyau Amma da ke ka
cigaba gulma gashi ka barmu tsaye kallon Mota.
Saleem ya yi murmushi bai ce komai ba Mommy ta yi dariya
saboda maganar iya ko kadan Iya bata laifi gareta Tsohuwar
tana burgeta cikin harshen turanci ta cewa Saleem muje mana
dan ta gane Maheer ya tsaya jira.
Saleem Ya juya yana murmushin masifar kakarsu lolz, tare
da daga hannu yana alamu wa Maheer kan ya yi parking ya
biyo su, a dai dai lokacin Motar Maheer ya gama shigowa
asibitin da sauri yanemi wajen parking bai tsaya bata lokaci ba
ya rufawa su Saleem baya.
Direct dakin da Amrah ke kwance Saleem ya nufa, a hanya
sai sannu nurse da likotocin suke masa wasu ya amsa wasu
daga hannu, dakin ya nufa aiko Iya tana gane nan ne in da da
sauri ta daga kafa ta ru gasu bude dakin ya yin da Sauran
matan suka rufawa Iya baya.
****
100
AKWAI KURA 2
Sosai Iya ta razana ganin yadda Amrah take kwance kamar
babu rai a jikinta sai na'ura dake amfani a jikinta wani ke
amfani saboda dakin, Iya ta fashe da kuka tana fadin Yar
marainiyar Allah waya miki wannan Abun ?me kika tsarewa
mutane haka har suke baradanar kashe mun ke?
Na shiga uku ni hapsatu, Allah ya saka miki Zainabu na
Allah ya tona asirin duk azzaluman da suka miki haka wallahi
ba zamu yafe ba ko waye sai mun dau mataki, ita Ummy tun
da ta yi arba da Amrah cikin mawuyacin hali take kuka
Musamman da duwa yandu fuskar ta ya kara kunbura ga bakin
ya hau sosai saboda ciwukan dake jikin bakin, kafarta daure da
bandage saboda harbin day yake kafarta, Gabadaya kuka-suke
yi babu mai bawa wani hakuri hatta Mommy- kukan take
saboda ganin Amrah cikin wannnan halin, Shi kan sa Saleem
duk yadda yake daurewa saida ya share hawaye saboda ganin
yadda kamannin Amrah ya canza-lokaci-daya uwa uba doctor
ta sanar da shi an mata dukan mutuwa, Saleem yaja numfashi
ya fesar kasan duciyarshi tana dafi sosai tabbas ba dai kyale
kowaye keda alhakin taba masa mata ba, tuni fuskarsa ta eanda.
Sosai tsananin bakin cikin halin da-Amrah take yake taba
zuciyarshi cikin bakin ciki ya cigaba da share hawaye, a haka
Maheer ya shigo dakin, subhanallah ya fada yana Sassauta
murya Haka abun ya kasance-? Am sorry-abokina ya- fada tare
da dafa kafadar Saleem, -cikin Lallashi ya fara magana Hajiya
kuyi hakuri dan Allah ku bar kukan nan tun da mun auna arziki
an sameta.
Granny ta danna masa harara ba da'ayi shirun ba ja'iri maras
Tausayi In banda rashin tausayi wa zai ga Zainabuna a cikin
wannan halin bai yi kuka ba? Aiko ba ture da bai san tausayi
ba sai da ya dubar da hawaye bare ni fa take jikan Ahmaduna,
to ba da muyi shirun ba dole muyi kuka in ba ka da imani kai
101
AKWAI KURA 2
mana shiru ni bani son Kichifi, ta fada tare da kara karfin
kukanta.
Abban Amlah dake tsayc tun shigowar shi dakin baiyi
magana ba illa kallon Amrah da yake yi cikin tausayawa, sai
awan nan karon ya sa baki Iya yaron nan yana da gaskia dan
Allah kuyi hakuri kuyi shiru ba'a hanaku kukan ba sai dai kuyi
a hankali saboda bacci take kuma a cikin baccin ake samun
sauki kukan naku zai iya tashin ta daga baccin dan Allah İya
kuyi hakuri.
****
Uhuuu! Uhuuu ! Amrah ta fara tari tare da juyi kamar
data fado daga kan gadon, da sauri Saleem ya danna abin kiran
likita, bai yi kasa a guiwa ba ya rigasu duwa gareta ya yin da
Sauran ma suka yi rubdugu suna mata sannu, doctor Ta yi
sallama ta shigo da hanzari ta karasa jikin gadon cikin
kwarewa take duba Amrah.
Alhamdulillah ta fada tana kallon Amrah jikin an fara samun
cigaba Yaya kike jin kan naki Amrah tabude ido a hankali sai
dai idon bai bude duka ba saboda kumburi, a hankali tace da
sauki masha Allah-doctor-ta fada-tare da--kallon Saleem,
Controller hamkalin ka ya kwanta matar taka mun ga cigaba
sosai kan dazu daka kawota, Gabadaya suka kalli Saleem har
da Amrah dake kwance jin ance matarshi, Saleem ya murmusa
yana sunkuyar da kai saboda Ummy dake dakin Ngd Doctor.
Yawwa daku iya bata abunci sai dai abu mai ruwa ruwa in
tana bukata saboda drip da ta sha akwai abinci a cikinsa bana
daton da ta ji yunwa, Doctor ta kalli Amrah barin je duba
marasa lafiya anjima dan juyo sai dai banda magana da yawa
saboda ciwon karki fama Amrah ta Gyada kai doctor ta dauki
kayan aikinta tai musu sallama ta fita.
102
AKWAI KURA 2
Fitar doctor keda wuya Amrah ta kuma bude ido a karo na
biyu sai dai wannab lokacin bata rufe ba a hankali take bin
kowa na dakin da kallo, A hankali ta sauke ido kan Granny
cikin karfin hali ta yi murmushi tare da daga hannu a hankali ta
mikawa granny da sauri ta karaso jikin gadon ta rike hannun
Amrah cikin dariyar jindadin samun jkarta.
Amra ta kalli Ummy ta yi murmushi a hankali ta mai da kanta
kan mommy cikin dan mamakin ganin mommyn ta yi dariya
maras sauti Mommy taji dadi sosai da Amrah ta nuna mata
kulawa hakan Saleem ya ji dadi sosai da Amrah ta nuna Mom
nada kima a wajenta.
Gabadaya sai sannu suke wa Amrah ya yin da take amsawa
da kai Abban Amlah dake waje amsa waya a hankali ya bude
kofar tare da sallama ya shigo dakin, Amrah Ta yi murmushi
Cikin murya mai karfi tace Abban Amlah Ur work is done,
Kallon kallo suke gabadayansu yan dakin na rashin-sanin
manufar abinda Amrah take nufi Abban Amlah ya hadiye
miyau mai daci kutttt eikin kasala yake kallon Amrah tare da
satar kallon iya ta gefen-ido aiko da sauri-ya sunkuyar da-kai
saboda gabadaya dakinHatta Saleem ido ya tsura musu yana kallon Abban Amlah
zuciyarsa cike da zargi.
Amrah ta yi murmushi a kaikaice take kallon kowa amma a
dahiri daku dauka bacci take saboda kunburin idonta sai ta
ware sosai ake kallon kwayar idonta, Dariyar gefen baki ta yi
bayan ta kare musu kallo tabbas ta san kallon tuhuma suke
masa Washhh Amrah ta fada dan san kauda shirun dakin.
AI ko da sauri kowa ya kalleta tare da tambayar meya faru?
Amrah ta fara kokarin zama a hankali Ummy ta taimaka mata
cikin karfin hali ta daga hannunta na dama A hankali tanfara
warware ribon din dake kanta wanda ta kunshe gashin kanta
103
AKWAI KURA 2
kamar a cuci mada sai ka dan dasuke dube a bayanta saboda
always hakan ta ke yi ta fi gane daurin gashi haka, Da sauri
Ummy ta fara taimaka mata Wajen kwance ribon din a daton
ta tako ribon din Yamata nauyi ne, Amrah Ta dakata saboda
ciwo da hannunta ya ke mata sai dai hankalinta naga Ummy
dake warware gashin kan Gabadaya Ummy ta cire ribon din
Ya yin da gashin kanta ya zubo a gadon bayan ta Saleem da
Maheer da basu san haka yawan gashin Amrah yakebba tuni suka saki baki suna kallo cike da sha'awa.
Abun mamaki sai ga karamin na'urar daukar magana ta
fado daga cikin gashin Amrah wanda girmansa bai fi girman
Bluetooth na waya ba, Da-sauri Saleem yamaida hankali wajen
fa haji karar faduwar abu a kasa cikin nutsuwa ya tsuguna tare
da dauko abun a hamkali yake kare masa kallo tare da juyawa
a hannunsa, cikin second biyu ya fahinci-abinda take hannunsa
bakinsa a bude da mamaki tare da nazari Me Amrah take da
shi, Amrah ta kalleshi cikin daure fuska ta mika hannu bani
aba ta Saleem ya kalleta ido cikin ido yana Murmushi anki a
bayar din abun mu dai.
Amrah ta bata rai tare da turo-baki-kamar-da ta yi kuka cikin shagwaba tace Mom kin ga yana sani magana ko, Mom ta
kaiwa Saleem duka bata abun ta Bani son neman magana
yarinya babu lafiya kana damunta da kai data ji koda ciwon jikinta, Saleem ya yi karamin dariya a hankali ya matsa jikin gadon Hannun Amrah ya kama ya sanya mata Abunta a
hankali ya furta inada kishi a rufe min gashi na kafin in fama
ciwon mutum, Amrah ta ji shi sarai amma ta share saboda
abun mamaki yake bata inda yake mata wani irin maganganu
tun lokacin daya taimake ta, wani abunda yake bata mamaki
shine sosai maganganun Saleem suke burgeta ko kadan kalmar bai taba bata haushi ba tofa akwai chakwakiya Kenan.
104
3
AKWAI KURA 2
Da hannu ta ya fito Abban Amlah wanda tun dazu ya yi
mutuwar tsaye kwakkwaran motsi, ya kasa a dakin tun da ya
lura da kallon tuhuma da Kowa yake masa a cikin dakin.
Ummy dake kallon ta ta sanya baki Abban tan uku Karaso
ina ga daughter na son magana da kai, Abban Amlah cikin
mutuwar jiki ya matso wajen tare da kir kirar murmushi
daughter ya jikin? Abban Amlah ya fada yana kallon Amrah,
Amrah ta kauda kai a hankali ta amsa da sauki.
Hannun ta ta dago cikin dauriya saboda ciwo a hankali ta
nemo Murmushi akan fuskarta, cikin nutsuwa tamika masa
na:urar cikin murya mai dan karfi-take maganar yadda-kowa-nadakin zai iya jinta, Ta-lumshe ido ta bude baka bukatar bayani
daga bakina Duk wasu bayanai suna cikin nan ta nuna na'urar
data bashi, Alhamdulillah ko yau na mutu nayi abunda ya
gagari mada da yawa nayi abunda a duniyar mafarki kawai ake
iya gani sai gashi ni na yi shi a zahirance.
Duk da hatsari da firrgicin dana fuskanta da gatana-na
damo boyi boyi, wani gurin a ci mutumcina wani gurin a
kaunace ni daga karshe ina gode-maka-Koba-komai Abbana
Ya haifi mace mai kamar mada wanda burin kowane uba ne,
Daga karshe yadda na sadaukar da raina ka tabbbata-duniya ta
sanni ta hanyar jarumta ka tabbata An manna Tarihin
jarumtaka ta a cikin kowane tarihi na kasata Najeriya.
Amrah ta daga hannun hagunta cikin cije labba ta sakewa
Abban Amlah na'urar tare da gyara kwanciya ta lumshe ido
kamar mai bacci.
Kamar anyi mutuwa hakan dakin ya kasance, Saleem ji ya yi
dufa na dubar masa duk-da sanyin AC dake dakin -Ummy
granny kallonsu suke cike da Nadari Ya yin da Abban Amlah
ya fara tafa hannu cikin dariya wadda ya-manta rabonshi da ya
105
AKWAI KURA 2
yi tun batan Amrah, Bery Good Amrah ! nasan daki Iya
Alhamdulillah Allah ngd maka da ka futar da diya ta cikin
Lafiya Da sauri ya bude kofa ya bar dakin cikin tsananin farin
ciki.
*****
Washegari da safe tun karfe 7 dai dai Maherr ya taras da
Saleem a gida basu tsaya bata lokaci ba suka dunguma zuwa
wajen da aka ajiye masu laifin; Tare suka shiga wajen daya
daga cikin yaran Saleem shi ne yai musu jagora har duwa inda
suka ajiye masu laifin.
Gammm karararrawar kan Maheer ya buga sakamakon ganin
Ahmad a daure a cikin jini saboda dukan da yaran Saleem su
kai masa saboda umarni ne daga Saleem din, Da sauri Maherr
ya bude baki yana kallon Saleem abokina kar dai inda kasa aka
daureni haka ka daure Ahmad? in haka ne me yasa akai masa
wannan hukuncin.
Saleem ya kalli Maheer da idonsa da ya fara ja saboda
bacin rai cikin dafin nama ya gaurawa Ahmad mari hagu fa
dam-bai tsaya ba, ya cigaba da Kai masa duka-ta ko ina fun
Ahmad yana ihu har ya kasa sai dai jini dake futa baki da hanci
Saleem yas hake makogoran shi kan wani dalili ba yan ka
saceta daka taba jikinta me taimaka da dafi da dakai mata irin
wannan dukan?
Dan ubanka dan uwarka kan wani dalili daka kai kanka
hurumin daba naka ba ? In kudi kakeso kama daga kudin
Najeriya har kudin America Dollars zan iya baka Domin na
fanshi ran matata me yasa baka fadi kudin fansaba ? Meyasa
ka taba mun jikinta! Bayan jikin ta mallaki na ne ni kadai.
Yau sai na kashe ka daga kan matata ka daina iskanci, a
hankali Maheer ya fara ramfo dancen aiko shima cikin dafin
106
AKWAI KURA 2
rai ya fara kaiwa Ahmad duka tare da huce Zafin daurin da
akai musu shida Zahra kan abunda basu ji basu gani ba Sosai
Mahcer din yake kaiwas Ahmad duka ya yin da Makogwaron
shi yake cakume a hannun Saleem yana kokarin aikawa da shi
lahira, Cikin lokaci kadan Ahmad ya suma Saleem ko a
jikinsa naushi kawai yake kaiwa Ahmad a marainan shi cikin
bacin rai ya juya ya bar wajen ya yin da Maheer ya biyo
bayanshi cikin Dafin rai shima.
****
Da sauri Maheer ya shiga wajen direba ya yin da Saleem ya
shiga gaban motar yana sauke ajiyar duciya ran shi a
dugunzume saboda bacin rai, Maheer-ya kalli Saleem cikin
Sassauta bacin rai ya fara lallashin sa dan yasan in bai yi-haka
ba Saleem din ba dai taba saukowa ba a hakali kamar ya dare
ya fara magana.
Tun last time, da kananun yan-iskan nan suka yi yunkurin
harbi na nayi kwakkwaran bincike, ban zauna ba har sai da na
gane kowaye yake kokarin kawo min hari, koda na gane ban
dauki mataki ba saboda nai-masa uduri-karo na farko ne na
barshi tare da sanya-ido ko dai tuba sai dai kash abun mamaki
wannan karon Matata ya taba, wannan karon Sai na aika