Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
10 / 10
kalmar da Saleem yake ta maimaitawa a ranshi da yaga baiwar kyawun da Allah ya baiwa Amrah, sosai-tai masa kyau ji yake kamar ya mai data-eiki saboda-kauna in son shine-ko kuda bai son ya taba masa Amrah. Wow wow wow gabadaya suka fada Ya yin da Meerah ta ciro wayarta ta fara daukar Amrah photo Zahra ta matso da sauri ta hada kanta da Amrah sis cigaba da dauka Ya yin da Meerah ta cigaba da Dauka Dariya sosai Amrah take yi na jindadi sam ta manta akwai Maheer da Saleem dakin Shi ko Maheer tun da ta fito yake hamdala a ranshi tare da taya abokinsa murna kan Amrah tabbas duk namijin da ya samu Amrah ya more mace komai ta hada Amrah ta cika goma cip a wajen kyawun dirin halittar da Allah ya yi mata irin wadda duk namijin daya kalleta sai ya hadiyi yawu lolz. ***** AKWAI KURA 2 Mamah cma Affan ya fada yana daga hannu alamun a dauke shi, shima ayi Hoton da shi Mera ta dakata da daukan hoton cikin dariya tace tofa kinji yaronki na fadin shima, Amrah ta kwashe da dariya Ah ah yaro na do ai aifin anty Zahra ne tasa nake shirin mantawa da dana. Amrah ta dauki Affan tare da gyara tsayuwa Meerah ta cigaba da Daukan su hoto, Salcem sosai suka burgeshi ganin madarar kaunar da family din shi sukewa matar sa, Shima cikin dabara ya fara daukan Amrah photo, Masha Allah ya fada ganin yafda-ta yi kyau a hoton tamkar sabuwar amarya da sauri ya yi sanya shi a Lock Screen wallpaper din wayarsa. Mikewa ya yi ya kalli Maheer daya shagala da kallon Amrah cikin tabe yace muje waje mu jira su kafin su fito ko, kar a cinyemin mata da kallo lolz Maheer ya yi karamar dariya yana jinjina kishi irin na Saleem tare da fadin Sorry abokina ai matar taka ce ta cika........ ya yi shiru-sanadin bandan kallon da Zahrah ta jefa masa shi ko ya bata fuska dama da biyu ya fada bai kalleta ba ya rufawa Saleem baya suka bar-dakin. Granny ta dauki Jakarta ta saba Zainabu in kingama shegen daukan hoton ku sameni a gida ni ba dan tsaya idona na kallomin tambada ba Ummy kam dama tun farkon daukan hoton ta fice daga dakin saboda tana jin kunyar Saleem sosai. Amrah ta yi dariya haba my Granny- hoton ne tambada! Ta bata rai saboda yaro na nayi fa dan in nuna masa murnar na yaba da gift din daya bani, Granny ba tace komai ba ta sanya kai ta fita tana mai fadin ja ira daki taras da ni gida ai. Zahrah Da ranta ke bace sanadin yaba kyau da Maheer ya yi ita ma cikin sauri ta dauki jakarta da ta fita amma sai Anty Meeerah ta tsayar da ita Swt bestynmu zoki mana hoton nima in dana ta fada tana mai mikawa Zahra wayar. 136 AKWAI KURA 2 Badan ta so ba ta karbi wayar ta fara daukarsu hoto daga bisani Amrah tace Besty juya camera din muyi selfie dukkanmu saboda tarihi, Zahran Mommy tace aikuwa Anty Meerah ta karbi wayar ungo Maman Affan yi mana tun da kin fimu tsayi duka, Amrah ta karbi wayar ta koma gaba ya yin da ta fara kashe musu hoton itama bestyn tuni ta ware tana iya yin styl dan Zahra gwana ce wajen kaunar hoto, sai da Ummy ta dawo dakin tai musu magana sannan suka fito da sauri suna dariya. Gabadaya mota suka shiga harda su. Meerah dan raka Amrah gida, nan fa granny ta tubure kan cewa lallai yau data wuce da jikarta gida, Ummy ba dan taso ba tace shikenan a wuce gidan Iya, Tuni taja motar ta gaba wanda daga ita sai Iya a ciki ya yin da Motar Maheer bestyn sa ce kadai a ciki ta kame a gidan Gaba, Motar Saleem Amrah ce daune a gaba sai Meerah a baya da Zahran mommy tuni suka dauki hanyar gidan Granny. **** Gidan İya gabadaya suka yada-dango harda-mazan, domin lya cewa ta yi su shigo tun da waje akwai rana, tuni sun ware dan duk sun dauki iya kakarsu sosai Saleem da kannen shi-suke kaunar Iya, tun dawowar su daga asibitin suke baje a falon Iya, Iya tana duba musu comedy, ita ko Ummy dakin Amrah ta wuce saboda tahuce gajiya dan badata iya zama cikinsu ba tana kunyar yar fari. Iya ta mike tana tauna goro kun wani baje mun falo sai kace na gidan uwayenku, mada ku tashi ku wuce dan nace ku shigo ba ina nufin ku addabeni bane, ku tashi dan ina bukatar in huta ku tafr wajen ayyukan ku kar kuci kudin haram, yo kudin haram mana kun ki duwa aiki kun zo kuna neman magana anan. 137 AKWAI KURA 2 ku kuma matan babu inda da ku je sai kun daura min girki kuma yau fatan tsaki nake burin sha Mada ku tashi kuyi ni ba zan daurawa kowace ja'ira sanwa ba, ta gutsiri goro Zainabu ki basu kayan aiki ni bari in runtsa hahahahaha suka bushe da dariya Sai Granny! Besty ta fada tana kyalkyala dariya. Maheer ya kara gyara dama kan kujera. Iya ai yau babu inda damu sai munci girkin gidanki, Dan nima ina kaunar fate, Iya ta kama baki to almuri kaji da kinibibinka to fate na dai dai cikina da ayi min in ma ciki gareka sai dai ya dube, haba Kyal kyal suka fashe da dariya Saleem ya yi murmushi tare da mikewa tashi muje kar tsohuwar nan tafasa-mana ciki da dariya. Aiko nan iya ta koma kansa kai kuma mai bilitin ubanwa ya sa da kai, kai nifa naga bature ma nan ya ganni ya barni bare kai dan haure farin na ka ma da gani na bilitin ne ai farin Allah da Annabi-sai diyar arziki Zainabu na, Hahahaha Suka kara karfin dariya suna ihu Saleem bai ce komai ba ya fita daga dakin tana turo baki an tafi ki cinye gida ya yin da Maheer yake kyal kyala dariya yana bin bayanshi. Ita ma Amrah dariya sosai take tana hararar iya kai granny ke kan baki bar kowa ba wallahi, Iya ta kai mata duka har amadu ban bari ba dan haka badan bar uban kowa ba dan ma kin samu anya baki ai kema...... ta sauri ta kashe iya pld Iya dan Allah kiyi hakuri dan kar iya ta baro wata maganar aiko sosai suka fashe da dariya. **** Yau Kwanan Amrag uku da dawowa gida alhmdullh ta warke sosai, ya yin da ko yaushe Meerah da Zahra suke hanyar gidan Granny wajen Amrah haka besty-ba a barta-a baya ba kullum tana hanya wajen Amrah, yau takama Ranar alhamis tun safe 138 AKWAI KURA 2 Saleem bai do gidan lyaba har magriba ya yin da Mera tazo tun azahar sai bayan la'asar ta wuce gida. Affan kuwa kuka ya yi ta yiwa Meerah kan ta barshi Wajen Amrah, Amrah ta marairaice fuska uAnty dan Allah ki bar min yarona ya kwana, Meerah tace to shikenan gobe in nado dan bar miki shi kin ga yau bamu tawo da kayan shi ba, Iya dake daune tana cin abinci ta- dakawa Amrah harara to ance bada abar miki shi ba dole ne. Tun da gidan namu mayu ne muna cin mutane ai dole aki barin yaro, Meerah takama baki Ohhhh! Iya yau naga ta kai na Allah ya huci duciyarki Maman Affan tafi haka a gareni in kyauta tace in bar mata Affan-zan bar mata shi Halak Malak. Wallahi na yarda da tarbiyarta sannan na yarda da kaunar da takewa Affan, Meerah ta ajiye Affan tana murmushi zan wuce kanwata direba dai kawo kayanshi, Amrah ta rufe ido duk Iya ta bata kunya cikin jin kunya tace am sorry aunty, Meerah ta yi dariya a'a ai ni da iya ba yau muka fara ba Gud night kanwata t afada tana shirin barin dakin, ya yin da Affan ya fara tsallen murna Maman-Affan Yau Mommy ta barni a gidanki. Bayan Sallar Isha'i, karfe 8 na dare Baki su kado Iya cikin mamakin ganinsu ta tarbesu-cikin mutumci, Bayan yan-gaishe gaishe tare da tambayar jikin Amrah a-hankali Amrah ta mike ta koma dakinta dan bawa Iya waje su tattauna da bakinta. Baba Auwalu da Baba Haruna suka Dakata da surutu cikiu nutsuwa Baba Auwalu yake sanar da-shi wayar da Su kayi da mahaifin Anas kan neman alfarmar a rage yawan kwanakin auren inda hali suna bukatar ayi nan da wata 1 tak, Iya ta kama baki tana salati cikin fada take maganar kan wane dalili? Yar ta muce ko tasu ?to in sun shirya mu bamu shirya ba Jikata yanzu jinya take nida nake maganar ma ko da a kara 139 AKWAI KURA 2 auren kafin ta gama murmurewa, To ahir ni ban yarda ba dan buduri da burede sosai da muyi auren diyar Amaduna. Kiyi hakuri Iya bansan da kiyi musu ba ganin yadda farkon zuwan su kika nuna farin ciki, maganar da nake miki na yarda na Amince musu kan nan da wata daya ayi bikin, kuma insha Allah abunda da a rufa asiri ba dai gagara ba damuyi iyakar kokarin mu ai mata abinda ya dace wanda ba da'a ji kunya ba. Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un! Iya ta fada tana tafa hannu wanda yasa Amrah dake daki ta futo da gudu a datonta ko mutuwa aka yi sai dai jin maganar da iya ta cigaba yasa Amrah taja burki tare da tsayawa dan jin karashen maganar. Auwalu yanzu auren Zainabun tawa za'ayi nan da kwana 29, sai kace auren kaza? a'a ni-kam shiri na ba-dai-kammalu nan da wata daya ba dominn munyi magana da kanwar uwarta Raliya kan cewa auren nan saura wata biyu da tazo ta tafi da diyarta barno gidan kamshi a yiwa Zainabu gyaran amare na kece raini saboda masu abu da abin su, amma kwatsam auren wata ukun sai a mai da shi kwana 29. Auwalu da sake nifa in basu kaunar auren nan gara a hakura dan Zainabuna matsayin ta ya ninka da yo an fada maka inda kafin al'amarin nan ya faru ta samu wannan daukaka ai sadakin nan sai sun kara eheee, Baba Auwalu ya sassauta murya cikin lallashi ya fara Magana haba Uwarmu maganin kukan mu Manya basa magana biyu kamar yadda muka gada a wajenku Iyayen kwarai, Iya ki taimakeni tabbas nayi kuskuren amsawa babu izinin-ki sai dai nayi hakan-dan gadara da diyata kuma ina ganin aure iyaye mada sune gaba. 140 AKWAI KURA 2 lya taja numfashi Iya ki taimaka kar a damo kananun mutane kan maganar nan ki amimce a daura aure in yaso tarewar sai a dauna a kuma tsaida rana ya fada yana kara sassauta murya, yo yanzu naji magana amma da sai ace da ayi min auren jikar Ahmadu na salim alim babu buduri, Shikenan hakan ya yi na amince yanzu sai a sanar da uwarta da manya wanda suka dace da wuri tun da abun ma ai yazo kwana 29 al kamar yau ne a gun Allah kwanakin yanzu sauri garesu. Baba Auwalu ya washe baki yana jin dadin saukowar tsohuwar cikin Jin dadi yake addu'ar fatan Alkairi ga Iya tare da ajiye mata kilishin daya shigo mata da shi cikin ladabi yai mata sallama to iya damu wuce Iya tace agaida gida nagode Awwalu kai baka gajiya da abun arziki. ***** Jin motsin fitarsu da sauri Amrah ta juya dakinta, Cike da tsananin radana take ta fara jin jiri yana shirin dibanta, bata yi aune ba ta jita kasa kan katifa ta fadi, Wahayene yafara sintiri afuskanta take taji gabanta yatsananta fadi, Cikin kunshe baki tafashe da kuka mai dafi, wanda-jitake-kamar-ansanya-wuta cikin zuciyarta. Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un take maimaitawa tare da dafe kirjinta hannu, cikin tashin hankali take kuka hawaye tuni ya cika katifar in da tasanya kanta, Wht is wrong wt mie ta fada tana kuka? Ido ta runtse tana tariyo maganar iya da bakin da suka fita su baba Auwalu da Baba Haruna, Tukukin bakin ciki ne ya kara tokare kirjinta Tare da wani matsanancin tsanar Anas a ranta, Ji take in har aka daura mata aure da Anas data iya mutuwa saboda bakin ciki, Amrah ta cigaba da kuka wanda ita kanta bata san dalilin sa ba.. 141 AKWAI KURA 2 Cak tunaninta ya tsaya idan ta runtse ido Salcern take gani cikin Salonsa mai daukan hankali tare da muryar shi mai taushi cikin nutsuwa, Tuni ta fara hango Tsarinshi a cikin kwanyarta. Sai dai ba tsarin na shi ne damuwar taba irin yanda take ji game da shi ne fitinar, Wash ta fada tare da kara danne kirjinta da yake baradanar fashewa menene wannan abun da take ji ? ita kanta bata da Amsa, ta runtse ido a karo na uku Zahra ita ce data bata wannan amsar sai dai tana tsoron tunkarar bestyn ta saboda kwarai ta gano kwana biyun ta canda mata fuska, sarai Amrah ta gane saboda kishin dan uwanta ne shiyasa ma tai mata uzuri dan ta san bestyn ta ta tana kaunar ta gaba-da baya. ***** Da sauri ta dauko wayarta ta bude facebook, cikin sa'a ta samu wanda take nema a online da sauri ta hau kan sunansa duk da bata taba magana da shi ba sai dai kullum tana ganin posting dinsa akan soyayya sai dai ko comment bata taba yi ba sai dai time to time ta kan danna masa like, Amrah ta yi masa sallama cikin second daya ya bata-amsa-hyege-yaga-er budurwa, da sauri ta fara rubutu. An saka ranar Aurena sai dai abun mamaki Sam bana farinciki da Auren, kwata kwata babu soyayya a tsakaninmu sai dai abun mamaki ina jin a raina ina ma ya zamo mijin aurena duk da yafi karfina ta kowani fanni, dasauri ta tura masa sakon, aiko cikin minti 6 ta ga ya fara typing Amrah ta rike waya tana jiran Amsar shi sa dai ga abunda yace. MISS AMRAH Labarin Soyayyar taki akwai sarkakiya a cikinta ga numbern wayata ki nemeni ta waya bani da lokaci enough da miki typing na gaji sosai. **** 142 - AKWAI KURA 2 Wayar takashe bayan tadauki no nashi sosai kanta yake mata ciwo badata iya amsa call yanzuba, Aikokamar daga sama tatsinci muryan granny tana kwala mata kira, Amrah tamike kan gado bandaki na dakin nata tabude tashiga cikin sauri ta wanke fiskanta saidai stil jiri na damunta kamar kwai yafashe mata aciki tafuta adakin dan amsa kiran Granny. Amrah tashiga dakin.ko sallama babu domin- arude take, granny ta kalleta Dawo nan kizauna kusa da ni, Amrah ta tabe baki barni nan komai zakice ina jinki, granny ta kalleta tare da kare mata kallo Zainabuna - Meyasamu idonki? Yo wato kinmana labe kin saurari maganar tamu ko?Amrah da tuni iya takara tundura duciyarta batasan lokacin da kuka ya kufce mataba, Iya takama salati tana tafa hannu Yo muma hakan mukayi muka bari gashi yadamo tarihi aidaman duk rashin kunyar amarya da lokaci yazo dole tadamo akoke, Iya tajawo Amrah jikinta dan taga kukan na Amrah yana kara sauti, ya isa Zainabuna Aure hakan yake yakin matane. Maganar da damuyi namiki ita abaya saidai naga baki yi abunda naceba to Alhmdullh kinga lokaci nakara matsowa nasan kin saurari duk tattauna war da mukayi da Iyayenki Su Auwalu, Dan hakan saiki nemi yaron nan Saleemu ki... Iya ta dakata da maganar sakama kon Saleem dake tsaye bakin kofa yana kwala musu sallama, Tuni Amrah takara kuka sakamako n jin sautin muryansa wani kibiyace ta yi tsalle ta huda duciyarta wanda take baradanar karasa- sauran numfashinta tuni taji tsananin tausayinsa yarufe zuciyarta. Iya tadaga murya bismillah dan halak kaki ambato shigo Saleemu, Saleem yadaga labulen falon yashigo saidai tun kafin yashigo yakejin sautin kukan Amrah saka makon hakan tuni ya ji gabansa yafara fadi wanda baisan daliliba, cikin nutsuwa 143 AKWAI KURA 2 yashigo falon tare da neman kasa yadauna kamar yadda yasaba inyashigo falon cikin ladabi yake gaida Iya tarc da maida idonshi kan Amrah yana jin dafin kukan da Takeyi, Iya ta dungure Amrah badaki bar kukan nanba iye tun da badaki iya fada masaba ni nan bani jin kunyarsa dan sanar da shi, dammm gaban Salcem yakara faduwa cikin tsananin tsorо yakalli AMRAH baby meke faruwa, Amrah saboda tausayi ga Tsoronn dake bugun zuciyarta da gudu tamike tabar falon tare da fashewa da wani kuka mai karfi. Masha'Allah na godewa Allh da Ya bani ikon gama littafi na biyu, a nan na kawo karshen labari na biyu. Ku saurare ni cikin littafi na uku nan ba da jimawa ba don cigaban labarin. Tabbas 'Akwai Kura yanzu aka fara. Taku har kullum Sayyada Taheer.. 08100044786 Ba zan rufe littafin nan ba, har sai na yi miki fatan alkhairi uwa mafi uba ko da-uban sarki ne; Hajiya Khadija-Musa Bukur. Allah Ya ja kwana Hajiyata, Allah Ya ba ki aljanna ba tare da hisabi ba, Amin. Ina Kaunar ki Mamata. 144 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 10 of 10