safe gidan Iya ya/fara cika da Yan uwan
Iya, itama Ummyn Amrah da wuri tazo gidan Iyan saboda
aikin taryan bakin, Girki sosai suka shiryawa baki tare da
abun sha kala kala, da-misalin karfe- 4pm dai dai iyayen
Anas suka iso gidan Iya, Abban-Amlah-da Baba Auwalu
Wanda yake Dan uwa, makusanci sosai ga a marigayi Mijin
Iya, sai Yayan Baba Auwalu guda biyu Sani Da Nasiru
Sune suka karbi bakin, Suma bangaren Anas Maza ne
dattijai biyu sai Samari biyu, bayan gaishe gaishe tsakanin
su daga bi sani, mata suka fito da abinci Kala kala tare da
kayan sha daga cikin Gidan Iya, Bismillah Abban Amlah
yace dasu tare da dan basu guri domin suci abinci, Amma
sai daya daga cikin dattijan yace Ah ah ai tare daku za muci,
Abban Amlah yace wannan na kune namu yana cikin gida
zamu je mu taras, Amma sai Dattijan nan ya tubure har
saida Su Abban Amlah suka hadu tare da su suka ci Abincin
tare da hira a tsakaninsu, Sosai suke hirar kamar sun san
juna, gabadayan su Bangare biyun kowa ya ji dadin yadda
lyayen suka kasance masu mutumci, Musamman Iyayen
33
AKWAI KURA 2
Anas sun yi na'am da tarbar karamcin da aka yi musu sosai
suke Taya Anas murnar samun surukai nagari, ba tare da
bata lokaci ba suka gabatar da kudurin su na nema wa Anas
dansu Neman Auren Amrah.
Baba Auwalu yace A matsayinsa na waliyin Amrah, ya
bawa Anas auren Yarsu Amrah, Ma shaa Allah
gabadayansu suka fada tare da godiya, Daya daga cikin
dattijan yace Nawa kuka yanke wa yar ku sadaki? Kuma
mu naso in har babu damuwa a sanya mana auren anan kusa
dan yaron yana bukatar abun da wuri Abban Amlah yace Ba
komai bazai gagara ba Allah yasa abokiyar zaman sa ce,
Alhaji Auwalu Bismillah Sai abinda kace, Baba Auwalu ya
yi dariya tare da shafa gemun shi Da alaman ustaz ne, yace
na yankewa Anas sadaki Naira 50,000 kacal, domin Anmabi
s.a.w. yace mafi karancin sadaki an fi samun-albarkar aure a
cikinsa.
Sosai Iyayen- Anas suka ji dadin Maganar-Baba-Auwalu a
take suka bada sadaki Naira Dubu Hamsin tare da kudin
gaisuwa shima dubu hamsin, sai katan - katan na minti dana
alawa sai huhun goro manya guda 5, Cikin mutunci da
dattako aka gama komai na Karban sadakin take Baba
Auwalu yace ya sanya rana wata 5 chif, lokacin ita Amrah
tagama skl Sosai Bakin suka yi farin ciki Tare da sanya
albarka wa auren cikin jindadi suka yi sallama da junansu,
har jikin Mota Abban Amlah da Baba Auwalu suka rakasu
suna musu godiya har sai da suka ga tashin su a mota.
34
AKWAI KURA 2
tafiyar bakin keda wuya Baba Auwalu, suka shigo cikin
gidan Iya, Dakin Iya suka yada zango Iya ta hakimce akan
kujera ta sha kwalliya kamar yaune bikin na Amrah, Dakin
Matane da yawa yan uwanta na kusa, Sai Ummyn Amrah
dake daune kan Sallaya ta idar Da sallar la'asar, da sallama
suka shigo dakin Iya, Aiko Iya tana ganin su ta hau washe
baki tare da fadin An gama, komai Auwalu ? Baba Auwalu
yace sosai Iya ga sadaki an karóa, kuma mun tsaida rana
aure nan da watan Babar Sallah in shaa Allah, Iya ta kama
hanci ta yi guda "Ayyiriri! Zainabuna Lokaci yazo kaiii
Allah yai muku Albarka, Allah ya kara zumunchi sannun ku
da kokari.
****
Zahra tana kwance a dakinta, ta kasa bacci sai juyi take
akan gado, zuciyarta cike da-farin ciki, gama wayarta kenan
da Maheer din ta, ba dan sun gaji ba sai dan dare ya yi akalla
karfe 12 na dare, sun sha lobe sosai ta waya ita da bbynta
Maheer, gabadayan su ita da shi kowa murna yake
kasancewanr Iyayensu sun yarda suyi aure.
Uwa uba tana da labarin jiya an kai sadakin dan uwanta
Anas, wa babbar Aminiyarta na rai da rai Amrah, tun jiyan
take kiran Bestyn nata a waya dan su taya junansu murna,
Amma wayar a kashe, saboda ita ma cikin satin nata sadakin
na zuwa daga gidansu masoyinnata Maheer.
Sai dai yau kwana biyu kenan take kiran wayan Wayar
Amrah shiru karshe ta kira Mommy, sai Mommyn tace da
ita Amrah ta wuce gurin aiki. Sako ta turawa Bestyn nata
kan cewa tana kewarta musamman da suka kwana 6 basu ji
muryar juna a waya ba please in ta kunna wayar ta kirata
35
AKWAI KURA 2
akwai labari tare da mata shakiyanci amaryan yayana Kin
sha kamshi.
WhatsApp ta bude ta yi making hotunansu da Amrah Masy
yawa, wanda kowanne Amrah ta sha kyau sosai, akalla sun
kai kala 15, cikin su har da wanda Amrah ta dauka sanye da
babyn nata Maheer Abaya kanta babu dan kwali gashin
kanta ya zubo, har gadon bayanta a jikin photon ta yi kyau
sosai kamar diyar larabawa, rubutu Zahrah ta yi a kasan
photon, Amaryan Big bro kin sha kamshi, ko madara bai kai
ki fari ba lolz.
Bai fi minti uku da sanya photon ba Frnds na Zahrah da
yawa suka fara comment akan photon na Amrah, wow
-beautiful, Fantastic, Wow Hurul en, Sune ire iren da mafi
yawan abokan na Zahra suke fada wajen comment, daya
bayan daya Zahran ta rubuta musu tnz.
Maheer dake kwance kan gado yana Tunanin- Zahra da
sauri ya rubuta mata sako Babyna Mu hadu a whatsapp.na
kasa bacci, Tare da kunna datan shi abun mamaki Zahra din
tana online, sabbin status ya gani Zahra tasa da sauri ya fara
budewa, a tunanin shi na Zahran ne.
Dasauri ya yi zooming photon yana kare mata kallo, Ko
tantama babu wannan gashin irin shi ne ya gani a bayanta
ranar da ta cece su shida Abokinshi, Daya bayan daya-yake
kallon photon yana zooming, Tabbas fuskan nan ya santa
sai dai a inah ???.
****
Yau laraba satin ta guda cur a gidan Ahmad, duk da Wannan
gida Ahmad ya saye shi ne saboda ta'addancin sa, ya kan fita
yaje harkar sa ya dawo sau da yawa ba kodayaushe yake
kwanan gidan ba ya kan tafi can gidansu ya kwana saboda
36
AKWAI KURA 2
babu wanda ya san wannan gidan daya saya cikin abokan
aikinshi bare yan uwan sa.
Ahmad ya sanya tsaro sosai a gidan, ko ta ina Yan ta'adda
ne, masu gadin gidan yan jiran ko ta kwana, ba kowa ne
yasan wannan gidan ba sai Abokan harkallar shi a cikin
kwanakin da ta yi a gidan ta yi mamaki sosai, da ganin
manyan mutanan da suke zuwa gurin ahmad kan harkar
hodar iblis wanda mutane, ne masu mutumci a idon Jama'a,
Ahmad duk wani abokin harkan shi da zai zo sai ya gabatar
da Amrah a matsayin Gwana a cikin harkar ya yin da da
yawan abokan harkar shi suka mata maganar bata aiki in ta
gama da aikin Ahmad, hakan ba karamin dadi ya yiwa
Amrah ba, a kasan zuciyarta sam babu dana sanin sace ta da
Ahmad ya yi saboda duk wani sirrin da yakamata ta rike kan
hujja a gidan Ahmd ta same su, wannan lokacin Amrah ta
gano Saleem bayi da laifi ko kadan illa-ma neman-ran sa-da
mahassada suke yi, A karan farko kenan Da Amrah, ta fara
jin tausayin Saleem, Sosai Saleem yake bata tausayi, Amrah
ta kan bata lokaci wajen tunanin Saleem, A duniya bata taba
ganin dan adam daya tara makiya irin Saleem ba, Gareta
yanzu babu burbudin kiyayyar Saleem a ranta sai dai ma
Jinjina da take masa kan gaskiya da rikon Amanar shi.
Ido ta runtse tana tuno kyakkyawar surar shi, Amrah ta rufe
ido kamar yana kallon ta A hankali ta furta Handsome guy i
lyk ur...Da sauri ta bude idonta ganin Ahmad ta yi tsaye
akanta yana murmushi, Ahmad yace yes my baby I knw ni
din kyakykyawa ne sai dai Ban tabbatar da hakan ba sai da
naji a bakin Babyna, sai dai babyna ke din first class ce
wajen kyau nasan kin dara ni a kyau nesa ba kusa ba, Amrah
37
AKWAI KURA 2
ta langwabe kai tana kallonshi tare da cewa really? Ahmd
yace 6ery sure my baby.
Wuri ya samu ya dauna dan nesa da ita Yana murmushi
baby na yaushe za aban kayan dadi ? Rass gaban Amrah ya
fadi, cikin jarumta ta daure Soon dear kasan abun bai dauke
ba Yes babyna aina sani i knw baki wasa da Sallah kota nan
wajen ai zan gane, Amrah ta yi fari da ido Saura 3days.
Ahmad ya kada kai kice in na aure ki dan sha wuya har 9days ?? Amrah ta tabe baki tana Yamutsa fuska dan hirar ta
isheta, Baby barin dan runtsa kaina ciwo, ok babyna ki
kwanta ki huta barin watsa ruwa, Amrah ta rufe ido alaman
bacci Ahmad ya bude bandaki ya shiga.
A hankali Amrah ta bude ido taja karamin tsaki, dan
mahaukaciya, jaki, dakiki, Baka san burina In gama hada
hujjar da- za'ayi ram dakai ba, kafin in-bar -gidan nan,
mtswwweee taja tsaki, zata bar gidan tabbas tasan abu ne
mai wuya sai dai ta shiryawa hakan, Ko ana h amaza ha
mata dole in bar gidan nan kafin in samu tsarki, hyege dan
Iska ta fada tana huchi......
****
MAHEER, yau da wuri ya fito daga gida zuwa office,
sauri yake domin yana Allah - Allah, yaje office ya shafawa
Saleem labari, kasa hakuri ya yi ya karasa office din,
Wayarsa dake gaban Aljihunsa ya ciro.
Lambar Saleem ya kira, sai dai har ta gama ringin ba'a
dauka ba, bai gajiba ya sake dannawa lambar kira, Saleem
dake bacci karar ringing din wayarsa ne ya tashe shi, cikin
bacci ya daga wayar tare da jan karamin tsaki, Maheer ganin
an daga ya sa ya sanya wayar a loudspeaker, Abokina da
38
AKWAI KURA 2
fatan kana office nima gani a hanya ina zuwa maka da
babban labari, Saleem Ya kuma jan tsaki Gaye ina gida fa
wallahi banji dadi ba daren jiya, Subhanallah Mahcer ya
fada barin zo gidan yanzu tare da juya kan motar shi, ya
kama hanyar gidansu Saleem.
Cikin minti kadan ya iso Gidan Masu gadi suka wangale
masa get kasancewar shi dan gida ne a gidansu Saleem, Tare
da mika gaisuwa a gare shi hannu ya dinga daga musu kafin
ya nemi wajen parkin ya ajiye motarsa, da sauri ya shiga
sashin Saleem Dan cimma abokin na shi, sai dai a hanya
suka hadu da mai aikin Saleem Grace tace da shi Oga baya
ciki, Waya Maheer ya ciro ya kira Saleem tare da cewa gani
a side naka.
Saleem kamar ba zai yi magana ba yace kazo Side din Dad,
Da sauri Maheer ya juya bangaren Dad-yana-mamakin Lallai
jikin Abokin nasa ya yi tsanani tun da har ya bar dakin nashi,
Da sallama ya shigo Falon amma babu kowa hakan yasa kai
tsaye ya yi dakin Dad ya kwankwasa kofa ya yi Tare da jiran
ai masa izinin shiga.
Saleem ya daga murya abokina shigo mana, dasauri
Maheer ya bude kofar ya shiga, tare da fadin Abokina
yaushe jikin naka ya kai hakan? Wallahi nayi mamaki da
kace mun wai ba kada lafiya, Saleem ya tabe baki hmmm !
Kai dai bari Beb tana shirin kai ni kabari saboda tsabar
kaunarta, Maheer ya yi dariya kace ciwon lobe kake, ayya har na tausaya maka, MAHEER dafa kafadar shi tashi
abokina tashi kaga abinda nagani.
39
AKWAI KURA 2
Saleem ya tabe baki kai fa dan iska ne ina fama da cuta kana
shirin karamin damuwa, please bar ni in ji da hakurin rashin
dream girl dita.....
****
Sallamar Mommy shi ya katse musu hirar da suka fara,
da sauri Maheer ya durkusa har kasa ya kwashi gaisuwa
wajen Mommy Mommy ta amsa fuskarta cike da fara'a, Ah
ah Maheer yaushe kazo ?
Ai gara da kazo Ko Son zai samu abokin hira na fiso ya
ware, Maheer yace Mommy kwantar da Hankalin ki ai nazo
da maganinsa, kin ganshi tun dazu nake maganar ya tashi
yaga wani Abu Mom yaki wai in bar shi ya huta Mom bara
ki gani ya fada tare da danna wayarsa, Gallery ya shiga yana
duba photo sai da yazo da-idai kan wanda yake so ya mika
mata, Mom Kinga.
-INNALILLAHI WA'INNA ILAIHI RAJIUN! Mom ta fada
tana Washe baki wannan ai Amrah ce, da sauri Saleem ya
tashi akan gado wayar hannun Mom ya sanya hannu ya
kufce tare da kai idanunsa kai dan ganin photon, Saleem
ware ido yana Kare mata kallo Abokina wallahi ita ce,
Maheer ya yi dariya Tare da matsowa kusa da Saleem
Abokina kaje gaba daka ga abinda nayi mamaki, Saleem Ya
zare ido tare da fadin na shiga uku ! My dream grl, Yes !
Maheer ya/fada Mom da sauri ita ma ta matso tana kallon
Wayar, dariya ta yi tana kallon sa ai Amrah akwai gashi, ni
kaina ranar dana fara ganin kan ta nayi mamaki sosai dan ko
ni baturiya bani da yawan gashin ta, Maheer ya kalleta Tare
da Kallon Saleem abokina in har ita ce to fa lallai itac e
Dream grl din ka Wow, 6ery fantastic As how ? Ikon Allah,
Mommy tace kuyi min bayani, kun bar ni a duhu Saleem ya
40
AKWAI KURA 2
kalli Mom da shanyeyyun idanunshi Mom Am totally
comfused ! MAHEER ya yi dariya Abokina ni kaina jiya
kwanan Mamaki nayi Sau daya naganta ranar data ce ce mu
Amma tabbas wannan gashin da farin fuskar ita ce na gani
ranar da aka ce ce mu, Mom ta zare ido Tare da kallon
Saleem Son kuna nufin Amrah itace ranar da ta taimake mu
gabadaya ?? SALEEM ya daga kai yana Jin tsananin farin
ciki, Mom No wonder nake tsananin kaunarta ashe ita ce ta
ce ci rayuwata Wow mum i can't beliebe, she is the one that
help us, for that, please mum i want uh to help me nd get her,
because i started to feel i can't do without her, i lobе her
damn mch mum !
*****
Maheer ya dube shi, abokina Sai dai hanzari ba gudu ba,
In har wannan itace Abar kaunarka to fa, *AKWAI KURA.*
Domin ita ce wadda Anas bro na babyna zai aura, in fact ma
An biya sadaki har rana an saka, shiyasa Dad nasu yace in
turo magabatana domin yana son a hada-Aur...Saleem ya
shako wuyan rigar Maheer tare da daka masa tsawa dan
ubanka matar tawa kake fadin wani banza dai aureta, Daman
ashe kai makiyina ne tun fil adal ban sani-ba ?? to wallahi
sai na harbe duk wanda ya rabi matata koma waye shi, Ina
son Amrah sosai kauna mai-yawa bare yanzu dana ke da
tabbacin ita ce dream grl dina sai dai a mutu ko ayi rai
Amrah tawa ce Ni kadai, ya fada yana kara shako wuyan
Maheer, Maheer kala bai ce ba bai kuma yi yunkurin kwace
kwalar rigarsa a hannun Saleem ba, Dake kallon su ganin
Saleem yaki sakin wuyan Maheer, cikin bacin rai ta yi wa
Saleem Tsawa Son baka da hankali ne? abokin naka kake
kokarin duka Sakar masa wuyan riga tun kafin in saba maka,
41
AKWAI KURA 2
Sai da Saleem ya yi nisa da alama baya cikin hayyacin sa,
yaki sakin Wuyan rigar Maheer da sauri Mommy ta fara
kokarin kwatar Kwalan Mahcer a hannun Saleem.
Ya yin da Maheer ya kasa magana sai bin Abokin nasa yake
da kallon tausayi, ko kadan Maheer bai ji Haushin Saleem
ba sai ma tausayin sa daya cika zuciyarsa, SALEEM ya saki
wuyan Maheer tare da fashewa da kuka mai karfi, Mom
Wht is wrong wt mie am die 4 her.
****
Da sauri Maheer yava karasa gaban Saleem, tare da
rungumeshi a jikinsa, Abokina ba lafiya gareka ba please ka
daina kuka mu bi abin a hankali, Saleem ya fusge a jikin
Maheer yana Nuna shi da yatsa ba za'ayi hakurin ba dake kai
ka samu taka abar kaunar ba, ai dole kace in bi a hankali to
bazan bi a hankali ba akan matar tawa kake-fadan haka to da
karfi dan bi wallahi tallahi koma waye shi sai ya bar mun
matata, domin Amrah rayuwata ce in babu ita babu ni,
Mom dauko mayafi muje gidan su Mom Akwai kudi a
dakina ki bude durowata ki dauko sadaki, yau ba dan dawo
gidan nan ba sai an bani Matata.
Gabadaya Maheer da mom suka yi dariya Jin sumbatun
Saleem, Mom ta share hawayen tausayin dan nata Tare da
kamashi ta rungume a jikinta Son kayi hakuri Magabatanka,
su kai maka sadakin Amma ai mace bata kai sadaki, Saleem
ya langwabe a jikin Mom, tare dacewa No Mom ga abokina
namiji ne ya isa shaida please Mom muje kar lokaci ya kure
kinji ana maganar wani banda yana zuwa wajen matata,
Please Mom kinsan badan jure ganinsu tare ba kawai muje a
daura auren a bani matata, Mom tashiga lallashin Saleem
42
AKWAI KURA 2
tare da fadin Son ai dole sai mun nemi yardar Amrah ko ?
Tun da ai bata san kana yi ba, ya zamo dole ka fara neman soyayarta kafin maganar manya, dan haka Maheer ka sanya ya yi wanka ya shirya sai kuje ku fara ganin ita Amrah in ta
amince sai a sanya manya ciki, Maheer yace haka ne Mom Abokina Shirya mu wuce office daga nan sai in kira babyna
ta bamu address din gidansu dream girl din taka koya? Saleem ya daka masa harara ai sai ka kai ni gurin aikin dan
ubanka, Mom pld shirya muje tare ya fada yana langwabe kai, kinga Mom tana jin maganarki na san data amince, Mom ta harareshi Ah ah maganar soyayya babu alfarma Son, sai dai barin shirya muje saboda ina kewar Daughterna. ****
Fitar Mom keda wuya Saleem-ya takurawa Maheer-ya kira Zahra dan ta basu address din gidansu Amrah kafin ya yi wanka, Maheer yana-dariya tare-da tsokananr Saleem
Uhum -Uhum su ba sa bun ba an fada soyayya haha kai
soyayya bata da hankali, Soyayya-mai sanya babba-kuka,
Saleem ya Galla masa harara kaga zaka kira ta ko sai na ci mutuncin ka, Maheer ya masa gwalo tare da danna kiran Lambar wayar Zahra.
A handsfree, ya sanya wayar yadda Saleem-zai ji komai,
ringin biyu Zahra ta daga wayar, Cikin yanga kamar Maheer
na kallon ta ta Amsa wayar, Hy Abokin rayuwata, ka tashi
lafiya? Bata jira Amsar da zai bata ba ta ci gaba da magana
babynah ! Kamar kasan yanzu nake rubuta maka
Morning text.
Maheer ya amsa Ayya abokiyar rayuwa ta kece always a rai
na hakan yasa na kiraki lokacin da kike cikin tunani na, nida
ke din Abu daya ne soyayya ta sanya mun fara tunani daya,
43
AKWAI KURA 2
Maheer ya kalli Saleem ya kanne ido daya, I lobe yhu so
much babyna ya fada yana lumshe ido.
Saleem da Ransa ya fara bacci ganin Maheer ya manta da
shi a wurin, sai waya yake yana masa tsiya, Duka ya kaiwa
Maheer dan iska bani da lokacin wannan karamar soyayyar
taku bani wayar in tambaye ta labarin Abar kaunata, tun da
kai iskanci ya hanaka tambaya, Maheer ya yi dariya tare da
kara matse wayar a kunnensa, ah ah ban yarda kaji min
muryar mata da sassafe ba, kuma sau nawa ina ce maka gata
ku gaisa amma baka taba karba ba sai yau saboda taka
bukatar.
Zahra dake jin duk abin da suke yi ta waya ta yi dariya
Babyna, kar dai Yau Babban Abokin mu ne ke son magana
da ni ? Maheer ya yi dariya tare da nutsuwa sosai, Babyna
Bestyn mu tana nan kuwa ? Zahra tace da shi wallahi
babyna tun ranar da muka dawo shopping har yau bamu
hadu ba, Maheer yace gaskiya bamu da kirki pld gani nan
zuwa ki shirya zanzo ki kaimu. nida abokina Zahra, tace
Aikuwa ina kewanta gashi bana samun wayarta barin yi
sauri in shirya kafin kuzo.
Tabar ya zuka, tare da busar da hayakin ta sama
*MAIGIDA* daga majiya mai karfi Yarinyar nan Ahmad
*FIYA FIYA* takewa aiki Goje, yace da ni ya ganta jiya a
gidan Ahmad din dan hakan Maigida ina ganin tazo gidan
sauki Tun da duk tafiyar iri daya ce ko ya kace MAIGIDA ??
ya fada yana busa hayakin sigari.
Alhajin ya mike tsaye tare da zaga falon Hakan meke nufi
Kenan? wato Ibrahim ya cu ce ni kenan ya karbi kudina kan
44
AKWAI KURA 2
labarin karya, kaiiii inaaa ba zai yiwu ba Maigida to
magana ta tabbata karyar ya yi dan ya samu rabonsa.
Domin in har yarinyar hukuma ce suka turo ta, lallai ba
zamu ganta a cikin harkokin mu ba bare har mu ganta dumu
dumu a cikinmu, kuma Goje ya sanar da ni har barasа
yarinyar take sha domin jiya a gabansa tasha Goje ya sanar
da ni gari yar hatsabibiyace ta karshe Maigida kaga haka ya
tabbatar yar hannu ce ko ya ka gani Maigida ??
Kiramin Goje ya fada yana hura hanci angama Maigida,
Wayar Goje ya kira tare da sanyawa a kunne a daya
bangaren Goje ya dauki waya tare da fadin sai Mushe Uban
Shaidanu yaya ake cikine? Wanda aka kira da mushe ya yi
dariyar manyan Arna Maigida ne yake son magana da kai,
ta mikawa da mikawa Alhajin wayar.-
"Allah ya taimaki Maigida" Goje ya fada tare da cigaba da
masa kirari irin nasu na-yan iska, ka hada ni confrence call
da Ahmad yanzu wani abu nake son tabbtarwa inna samu
amsa mai kyau kana da kyautar dubu 100,000 Hahhahhhhh
Goje ya yi dariya sai Maigida an gama baka da case yanzu
yanzu ma kuwa, Goje ya danna wayar dan kiran Ahmad,
ringin biyu Ahmad Ya daga Wayar.
****
A hankali ta sai ta nutsuwar ta bayan ta gama, kare masa
kallo ta mirrow, kai ta jinjina tana yaba kyau da Aliah ya
bashi a ranta take fadin duk matar data aureshi ta more, cikin
nutsuwa tace Ina kwana ba tare da ta kama suna ba Maheer
ya amsa lafiya klau.
45
AKWAI KURA 2
Zahra ta harare shi ta cikin Mirrow ta turo baki tace waya
ce da kai nake ? Maheer ya yi murmushi ohh ! Abokina ashe
fa da kai ake, Saleem ya amsa lafiya ba tare da ya juyo ba.
Maheer ya kalle ta Beb naji dazu kin ce Bata gidan granny,
Yes Zahra tace ta bashi amsa da tana gidan Ummy, Ok Ya
fada tare da daukar hanyar Gidan Ummy, a hanya sosai
Mum ke jan Zahra da hira sai dai Zahra a cikin kunya take
amsa wa tare da jin nauyin Mommy.
Tafiyar minti 23 ce ta kawo su bakin get din gidan Ummy,
da sauri Saleem ya kalli Maheer Meye hakan wai sai ka bata
min rai ne kafin ka kai ni gareta mtswwwweeee yaja tsaki,
Na kusa in ci ubanka wallahi dan iska kawai Maheer ya yi
murmushi mai da wukar abokina nan shine gidan.
Da sauri Mom ta kalli Maheer Amrahtu na fa mai aikin
Saleem, Maheer ya kalli Mom yes Mom nan shi ne gidan
Mahaifiyarta sai dai akwai gidan kakan ta da suke tare a
Mando* Ikon Allah Mom tace, tana jinjina kai Son kaga
Abun mamaki ko ?? Saleem ya lumshe ido Mom am eager
to c her.
Horn Maheer ya yi da sauri mai gadi ya zuge musu get ya
futo, jikin motar mai gadi ya kara so tare da dan leka kai
gaban motar, Cikin sauri ya mika musu gaisuwa tare da raba
ido ko ya san su sai dai bai gane kowa a cikin su ba.
Ganin hakan yasa Zahra ta sanya baki ta gaishe shi mai gadi,
bayan motar ya leka in da ake gaishe shi da sauri ya fara
dariya tare da cewa ah ah Fatima Zahra ke ce tafe Zahra tace
eeh nice Baba mai gadi, maza ku wuce ai naga motar
bakuwace dan bantaóa ganinta a wajen bakin hajiya ko
Alhaji ba.
46
AKWAI KURA 2
Da sauri ya koma jikin get tare da wangale musu kofar get din, hancin Motar Mahcer yasa tare da shiga cikin get din ya yi parking din motar a Parking Space din gidan, Tare suka fito gabadayansu Mom, tace ku jira mu anan daughter muje ciki
****
sai ki musu iso in masu gidan sun ba mu izini.
Tabar ya zuka, tare da busar da hayakin ta sama
*MAIGIDA* daga majiya mai karfi Yarinyar nan Ahmad *FIYA FIYA* takewa aiki Goje, yace da ni ya ganta jiya a
gidan Ahmad din dan hakan Maigida ina ganin tazo gidan sauki Tun da duk tafiyar iri daya ce ko ya kace MAIGIDA ?? ya fada yana busa hayakin sigari. Alhajin ya mike tsaye tare da zaga falon Hakan meke nufi
Kenan? wato Ibrahim ya cu ce ni kenan ya karbi kudina kan
labarin karya, kaiiii inaaa ba zai yiwu ba Maigida to
magana ta tabbata karyar ya-yi dan ya samu rabonsa.
Domin in har-yarinyar hukuma ce suka turo ta, lallai ba
zamu ganta a cikin harkokin mu ba bare har mu ganta dumu
dumu a cikinmu, kuma Goje ya sanar da ni har barasa
yarinyar take sha domin jiya a gabansa tasha Goje ya sanar
da ni gari yar hatsabibiyace ta karshe Maigida kaga haka ya
tabbatar yar hannu ce ko ya ka gani Maigida?
Kiramin Goje ya fada yana hura hanci angama Maigida,
Wayar Goje ya kira tare da sanyawa a kunne a daya
bangaren Goje ya dauki waya tare da fadin sai Mushe Uban
Shaidanu yaya ake cikine? Wanda aka kira da mushe ya yi
dariyar manyan Arna Maigida ne yake son magana da kai,
ta mikawa da mikawa Alhajin wayar.
47
AKWAI KURA 2
"Allah ya taimaki Maigida " Goje ya fada tare da cigaba da
masa kırari irin nasu na yan iska, ka hada ni confrence call
da Ahmad yanzu wani abu nake son tabbtarwa inna samu
amsa mai kyau kana da kyautar dubu 100,000 Hahhahhhhh
Goje ya yi dariya sai Maigida an gama baka da case yanzu
yanzu ma kuwa, Goje ya danna wayar dan kiran Ahmad, ringin biyu Ahmad Ya daga Wayar.
****
"Ka jima ka yi karko Oga Allah ya tsone idon Makiyanka,
ba zaka fadi ba sai a gadon baccin ka, Goje ya fada yana
karka da hannu kamar Ahmad din yana kallonsa, a daya
bangaren Ahmad yace an amsa gaisuwarka Goje Meke tafe
da kai? Dan alamu sun nuna bakin ka akwai magana.
Goje yace kwarai kuwa Oga Maigida *DAN CHANJI* ne
yake son magana da kai, Ahmad ya gyara wayar zuwa daya
kunnen nasa saboda jindadin maganar da ya ji tare da sake
tambaya Goje kace me ? sa ke maimaita masa