sam ta ki yadda da hakan bata wuce ya
rungumeta sai kiss daya ke kai wa bakinta kuma shima sau
17
AKWAI KURA 2
daya farkon zuwan ta gidan ta yarda ya mata kiss baki da
baki shima Ahmad din ya shammace ta ne.
Ita da shi sun zamo, aminai su kwana daki daya su tashi tare
tun zuwan al'adarta ta samu salama game da son taba jikinta
dan shi din yana da kyaman mace sosai lokacin da take
al'ada, hakan ya sanya ita kanta Amrah ta samu nutsuwa
dan babu abunda ta tsana irin Ahmad ya taba ta, tun
washegarin zuwan ta ita ke musu girki shi da yaran nashi
duk wani hidiman gidan ita take yi su kansu yaranshi suna
jin dadin kwasan girkinta tu ni suma sun zamo na hannun
damanta cikin dabara Amrah keshan cikin yaran tana sanin
abinda take nema a wajensu, musamman in sun sha kwaya
sun bugu haba tiryan tiryan suke mata bayani cikin maye.
Da misalin Karfe 4pm Gabadayansu zaune suke a falo
Ahmad da yaran suna ta shan Hayaki ya yin da suke hira
suke kyakyata dariya Amrah ita ma da tuni ta koyi irin
maganarsu na yan tasha ta yi babban dariya tare da furta
Oga Babyna,
Meye next plan din mu ne akan Saleem ??
Ahmad ya kalleta babyna Saleem na gab da shiga hadari,
domin Laifin da yake shirin kamani da shi shi ne kaikayi zai
koma kan mashekiya, Domin Yanzu hakan muna da labarin
hukumar DSS dakanta tana tuhumar Saleem da laifin Shigo
da hodar iblis, Saleem ya shigewa mutane da yawa hanci da kudundune bani kadai nake neman daukar fansa ba Daga majiya mai karfi Akwai wanda hukuman bincike na fasa
kauri ta yi ram da shi ganin Saleem shine sila na kama kayan
18
AKWAI KURA 2
sa wannan dalilin yasa ya sanar da hukumar cewa Saleem ne
Mai gidansa ba kowa bane face Alhaji Musa dan chanji, ko kina nufin kice min baki saniba?
Amrah ta yi fari da ido kamar gaske ta sani ta yi ta mike tana
taku a hankali kamar dawisu aini nan dakake gani babu
sirrin daban sani ba ciki har da naka Shiyasa ka godewa
Allah dana zamo taka billahillazi da munjima da gamawa da
kai ni da Maigida dan chanji.
***
Ina kika samu wannan labarin, ya fada cike da tsoro tare da
kokarin rike hannunta, Amrah ta-fisge hannunta tana kare
masa kallo, a bagaren Ahmad yau babu Maganar kyamarta a
gareshi, sai tsananin tashin hankali daya nuna a fuskar shi,
Amrah ta kalle shi ta yi babban dariya, Oga duk sirrinka a
tafin hannunmu yake ni da Oga na. da Sauran yaranshi koda
ka gama da ni, tofa ka kashe-macijine amma baka sare kansa
ba.
Amrah ta Kuma kallonsa,- kana-mamaki-ne-ko-tsoro,- No, ai
tsoro bai dace da hatsabibi irin ka ba, ko ni da nake, mace
babu maganar tsoro a tsari na saboda duk wanda ya-sai
rariya ya san zata zubar da ruwa, in ko haka ne Babu
maganar tsoro, cikin duk wata harka ta dabanci musamman
irin tamu mai dauke da hatsari, Ta fada tare da-juyi tana
girgiza jikinta.
Ahmad ya busar da iska mai zafi daga bakinsa tare da mata
kallo mai cike da ma'ana da yawa, tabbas yau ya kara aminta
da ita musamman da ya hango hatsabibanci a kwayar
idanunta uwa uba da alama dukkan sirrinshi a tafin hannun
19
AKWAI KURA 2
ta suke ita da ogan ta, ta kalleshi da gefen ido ganin yadda
Ahmad ya shiga firgici, cikin tafa hannu ta karaso gareshi,
hannu tasa ta zaunar da shi, kan kujera tare da furta masa
baka da case Oga, tun da kana da ni, ni ba ni da Oga kudi
sune Oga na duk wanda ya bani su, a farashi mai tsoka t ofa
shi ne ubangidana dan haka ka kwantar da hankalinka babu
mai ganin bayanka Matukar zaka bani hadin kai akan duk
kan umarni da hanina.
*****
Sosai Anas ya takurawa iyayen sa kan maganar Son Auren
Amrah, Anas ya damu sosai kwana biyu musamman daya
rasa ta a waya wannan dalilin ya sanya ya kara uzzurawa
kan lallai akai sadaki gidansu Amrah, dan Yana kirge da Da
kwanakin da Amrah ya rage mata Ta kammala school
gabadaya, Mama Ganin damuwar dan nata ya sanya ta yi
Na'am da kudurin sa tare da lallaba Mahaifin nasa kan
maganar lallai ya dace akai sadakin, Ba tare da bata lokaci
ba Aka fara shirin kai kudin gaisuwa gidansu Amrah tare da
maganar sadaki, kamar yadda Angon ya dage, Ganin Ita
ma Zahra ta samu mai sonta da gaske Abban nasu a boye ya
yi bincike kan Halin Maheer din kamar yadda addini ya
koyar damu ayi kafin Tabbatar da maganar aure,
Alhamdulillah Maheer ya samu shaida mai kyau, a gurin
wanda Abban ya wakilta, ba tare da bata lokaci ba wannan
yasa Mahaifin nasu yace Yana bukatar ganin Maheer,
Maheer bai yi kasa a guiwa ba ya amsa kiran na Abba,
Bayan sunyi gaisuwa Abban ya bashi damar turo
magabatansa, tare da masa bayanin, yana son a tsaida rana
dai dai dana dan uwanta jin maganar Abba ba karamin dadi
ya lullube Maheer ba, tuni ya washe
20
baki yana fara'a ya
AKWAI KURA 2
manta ma a gaban Abba yake cikin doki ya kira Mahaifinshi
yana masa Albishir an bashi mata, Abba ya yi gyaran murya
tare da jindadi yadda Maheer ya nuna farinciki kan auren
diyarsa, Mahcer ya yi godiya sosai wa Abba kan karamcin
da ya yi masa Maheer cike da farin ciki ya bar gidansu
Zahra ko jira ganin Zahran na shi bai yi ba ya bar gidan cike
da daukin Auren na sa tare da Babyn tasa.
****
Abban Amlah sam hankalin sa baya kwance na rashin sanin
inda Amrah take duk hanyar da zai bi wajen ganin ya samo
ta kafin Mutane su farga ya yi shi da yaransa na wajen aiki,
sai dai shiru kake ji har yanzu babu kwakkwaran labari kan
Amrah, Abun mamaki shiru kake ji Babu labarin na Amrah,
Numbern ta da ta turo masa sako tuni sun yi tracking Sai dai
inda Hashashen ya kaisu Sun yi binciken duniyar nan babu
Amrah a yankin daga karshe ma har suka cimma inda wayar
take yashe a cikin wata tsohor rijiya.
Ummy a halin yanzu ta yi fushi sosai da diyar tata Ji take in
har Amrah ta dawo lallai ne zata canza salo wajen koyar da
diyar ta ta Tsoronta dan ta yi imanin akwai sakacin ta cikin
raini da Amrah ta yi mata, Tabbas Maraicin Amrah shi ke
sanyawa take daga mata kafa sai dai ita Amrah bata ga
hakan ba.
Ummy ta ci alwashin sake sabon tarbiya wa duyarta dan
baza ta yarda da wannan debewar albarkan ba, Ace diya
mace tabar gida tsawon kwana 6 Babu sanin kowa cikin
magabatanta ai wannan lałacewa ce mai girma.
21
AKWAI KURA 2
Cikin wannan halin, iyaycn Anas suka zo kan maganar
Auren Amrah da Anas......
****
Da hantsi Granny tana zaune kan tabarma kofar dakinta,
tana shan hantsi kasancewar lokaci ne na sanyi, Mama ta yi
sallama a gidan granny ta washe baki tana marhaban da
Hajiya Fatima, kece a tafe da hantsin nan, Mama ce Ech
Wallahi Iya ni ce ta fada tana shigowa cikin gidan, itama
tana barka wa Granny da gida.
Kokarin zama Maman take kan tabarmar da Granny ke
zaune, tace a'a Hajiya fatima mu shiga daga ciki, Mama
tace Iya nan ma, ai ya isa bar ni ni ma in sha hantsin ai garin
akwai sanyi GRANNY ta koma mazauninta ta zauna tana
mata sannu da hanya, bayan yan gaishe gaishe Mama
tasanar da granny in sha Allah gobe Iyayen Anas maza za su
kawo kudin gaisuwar Amrah har ma da sadaki.
Ayiririhhhhh ! Granny ta-fada tare da, kama hanci tuni
fuskarta ya-kara washewa Da tsananin farin ciki, murna
sosai granny ta yi-har sai da ta yi kukan Farin ciki, Mama
tana rarrashinta, granny tace bar ni in yi hajiya Fatima
Lokaci ne Allah ya nufa zan gani banni inyi kukan farin ciki,
yau Jikata Gudan jinin Amaduna, Hasken idanuwana
Zainabu na itace ake maganar Aurar da ita. ai dole inyi
kukan dadi, granny taci gaba da fyace majina tana jan hanci
Sai da ta yi mai isar ta kafin ta yi shiru, Mama ita ma cikin
murna tare Tambayar granny ina diyar nata Amrah Granny
tace ai yau kwananta 13 gidan uwanta tun da ta dawo asibiti
take can, Mama tace ayya Allah yakara sauki in ji ba jinkin
22
AKWAI KURA 2
bane har yanzu ke damun taba, Iya tace tawarke ras gulman
tane yasa ta gujeni ja'ira ai yau kafata kafarta zan je in dauko
ta, gara inji duminta sosai kafin Anas ya dauke mun ita,
Mama ta yi dariya aikuwa gara kam Kodayake ai auren tare
dake Iya zaku tare, Iya ta kama baki ni Hapsatu raba ni da
yaran zamani marasa kunya, Ai in da zamanin mune da
tsohuwa ko da yar gaba ake hadaki Amma wannan zamanin
yaran sam basu da, kunya in yar ga ban aka basu sun ta
muntsine miki ya tare da sanya ta aikin wahala har sai ta
gudo gida, in tsohuwar aka kai, rashin kunya sai ya kore ta.
hahahahaha mama ta yi dariya tare da mata sallama ta bar
gidan.
****
Nan da nan granny dauko wayarta alamun da aka sanya,
mata a jikin kowace Number ta shiga, yan uwan mijin nata
ta fara kira Wanda sukeda alhakin Karban Sadakin na
Amrah, ta sanar da su gobe Su hallara kan maganar auren
Jikar ta ta, Granny kira sosai ta yi yan uwa na nesa dana
kusa duk mai hannu cikin auren Amrah sai da ta sanar daga
karshe gyalenta ta yafa ta rufe gida ta kama hanyar gidan
Ummyn Amrah.
Granny ta sauka akan adaidaita sahu kofar gidan Alhaji
Usman, Da sauri mai gadi ya bude mata get, yana dariyar
ganin ta saboda mutuniyar sa ce yana shan dariya in
tsohuwar tazo, kofar ya bude yana fadi Iya ke ce a tafe, da
ranar nan, Iya ta yi dariya yo Isihu ai dole na Banga ta zama
ba Shalelena Aure ya tashi, Maigadi ya washe bakinsa yana
murna kai ma shaa Allah kice tare da goro na kike tafe
Daman yau ban da kwandalan saya, Iya ta kama baki kaji
23
AKWAI KURA 2
makiri da na ni nake kawo maka goron? to yau sai dai kar
kaci goron sisi na bazan baka ba ja'iri, Maigadi ya bushe da
dariya har yana rike ciki Kai iya aina san ba zaki hanani
Goron Auren jikallen kiba dan nima ina taya murna sosai.
Ta kama hanyar wucewa cikin, gidan tare da fadin
kana da gaskiya Isihu dan haka ka jira naka in sun kawo
Amman kwandala bani baka Dan yau kam ban yi niyya ba.
Da sallama Iya ta shiga falon tana fadin ina Zainabun Fito
kiji abun alkairin da ya same mu Yanzun nan shiyasa na taso
dan ba maganar salula bane, yar aikin Ummy ce ta fito daga
kichin tare da russunawa ta gaida Iya baki ta washe Iyan ta
amsa tare da tambayarta masu gidan, Yar aikin tace Bara in
kirata yi sauri ki je Iyan ta fada, da sauri ta haura saman
bata jima ba ta sauko ta sanar da Iya tana zuwa, Ummy da
Abban Amlah na-zaune-falon-sama Sakon iyan ya riskesu,
da sauri suka kalli ju
****
Ummy ta ajiye tray a gaban Iya, tare da zama kan Carpet
din cup ta dauko-ta. zubawa Iya lemo tare mika mata Iya
sannu da hanya Bismillah ruwa, Ummy ta fada tare da
matso da filet na dambun nama gaban Iya, Iya ta karbi
ruwan lemon ta kurba tana Nagode Zainabu, Ummy ta yi
dariya haba Iya ke da gidan danki ai baki bukatar Godiya,
Iya tace matso nan kusa da ni Zainabu Ummy ta matso tana
dariya.
Alhamdulillah Allah ya kawo mu shekara ta kawo mu,
Ummy ta yi shiru tana sauraran Iya cikin nutsuwa Iya ta
sanar dasu dalilin zuwan nata kan maganar turo magabatan
24
AKWAI KURA 2
Anas gobe, Abban Amlah ya washe-baki Alhamdulillah
fuskarsa cike da farin ciki, Ita ko Ummy kai ta sunkuyar zuciyarta cike da farin ciki Alhamdulillah ta fada a ranta
Gara ma ai mata auren ko za ta yi hankali, afili kuwa ba tace
komai ba ta sunkuyar da kai tana jin kunya saboda nuna- kawaici kan yar Fari.
Iya tace dan haka shiyasa nazo da kaina saboda shirin
zuwan nasu In kuma tafi da Zainabuna dan na gaji da zaman
kadaici, Abban Amlah yace hakane Iya kina da gaskia, ai
kin mayi kokari, ya cigaba da magana kai Ma shaa Allah
nayi murna sosai, Allah ya tabbtar da alkhairi Allah yasa ace
gara da aka yi, Ameen Iya ta fada, ita dai Ummy bata ce
komai ba, Iya ta kalleta ni fa bani son gulma da kini bibi,
Ameen din ma ba zaki fada ba saboda gulma, yo komu 'yan
da masu kunyar gaskiya Ameen kan kan fatar arziki ma
diyarka ai za kace, Abban-Amlah ya yi dariya yana kallon
Matar tasa to kinji Ummyn yan uku Iya fa tace a ce Ameen,
Ummy ta yi dariya, kasa - kasa ba tace komaiba.
Iya ta jawo filet din dambun Nama ta kai bakinta, tare da
fadin kya ji da ka difurinki, Zainabu na dai Aure Allah ya yi
sai dai yan bakin ciki su mutu, Dariya sosai Abban Amlah
ya ya yi har da kwalla Ita ko iya ko a jikinta kamar ba ita ta
yi maganar ba taci gaba da cin dambun ta, Abban Amlah ya
tsagaita da dariyar tare da sassauta murya Iya ina rokon
arzikin, ki bar Mun dota in yaso in har bakin sun zo sun tafi,
ni da kaina zan kawota a cikin satin nan kinga bai dace
amarya tana gida ana maganar auren ta ba, Iya tace yaran
zamani ai ba kunya ce dasu ba wasu ma dasu ake shirin
komai, To Amma ba komai ita Zainabu na ai mai kunyace,
25
AKWAI KURA 2
Na bari Allah Ya kaimu satin ina nan ina jiranku, Iya ta
mike to ni barin wuce tun da babu Zainabuna Ummy tace
haba Iya keda ki ka ce wuni za kiyi, Iya tace na fasa ai
daman ba wani ya sani wunin ba nice nan nace hakan
saboda Zainabuna, kuma tun da Babu ita bazan wunin ba,
Ummy ta yi murmushi Allah ya huci Zuciyarki Iya, Abban
Amlah yace Iya muje in kaiki gida garin akwai rana.
****
Saleem rayuwa ta masa tsanani mafarki ya sanya shi a
gaba, ko yaushe yana cikin mafarkin Yar budurwa -mai
neman taimakon shi, Abun mamaki kullum fuska daya yake
gani wato fuskar yar aikin sa, a wani-bangare ga tsananin
soyayyar Dream girl dinsa dake Addabar rayuwar sa, Duk
Jarumtaka irin ta Saleem ya kasa jure Wannan abu mai
girma dake addabar rayuwarsa.
Saleem tun yana iya danne damuwar har yazo ya kasa, Yau
kwana 5 kenan babu labarin Amrah a gun aikinta, Wayewar
garin na yau tun safe Saleem ya tashi baya jindadin jikinsa
tsananin ciwon kai ke damunsa tare da bugawar zuciya,
wanda shi kansa bai san daliliba, a hakan ya yi shirin-tafiya
aiki, domin yana da abinda zai yi a office mai matukar
muhimmanci, a daddafe ya gama shiri sanye yake da shiga
na suit ya yi kyau sosai kamar bature, Sai dai ga wanda ya
sanshi sosai da ganin fuskarsa zaka gane akwai damuwa a
tattare da shi, cikin Sallama ya shigo falon na Mommy,
Tun shigowarsa kallo daya, tai masa Mommy ta gane Dan
nata yana cikin damuwa, A tsaye yace da ita Mrng Swthrt,
Mommy ta kalle shi da kulawa, tare da mayar masa Mrng
hw yhu my Son? Fine Mom yace da ita, Yana kokarin daura
26
AKWAI KURA 2
agogon hannu Mommy Zan wuce Office, Dawuri haka?
Mommy ta fada yes Mom in Dad ya fito kice masa na wuce
ina saurinc.
Mommy ta kalle shi break fast din-fa? am ok Mom ya fada
yana shirin fita daga falon, wait_Son tace da shi a hankali
Saleem ya juyo yana kallon ta tare da yamutsa fuska, Mommy tana kallon shi amma bata ce komai ba, ta girgiza
kai tare da daukan cup ta zuba masa kunun gyada karba
kasha bani son zaman ka da yunwa, Saleem ya karba tare da
kafa kan sa a hankali ya fara shan kunun yana yatsina fuska
alaman akwai damuwa, Ga Saleem sam baya jin dadin
Kunun daci daci ma yake ji a bakin-sa sai da ya sha rabin
kunun ya daga kai tare da ajiyewa kan table Swthrt sai na
dawo ya fada yana fita daga falon, Mommy ta bishi da ido A
dawo lafiya rabin raina.
****
Da ido Mommy ta bishi har ya fita daga falon kamar kwai
ya fashe masa a ciki, Mommy ta yi murmushi Son zurfin ciki, I knw ur problem.
Wayarta dake kan table din ta dauko ta danna kiran Number
Amrah, sai dai kamar kullum yau ma a kashe Wayar Amrah
take Mommy ta ja karamin tsaki Mtsweee ! rashin Amrah na
damunta Jin ta take kwana biyun nan itama kamar bata da
lafiya, sai daga bisani ta gane kewan Amrah ke damunta,
musamman in ta yi tunanin Watakila jikin Amrah ya kuma
tashi shiyasa bata samu zuwa wajen aiki ba, Ita dai tana
kaunar yarinyar jin Amrah take sosai a ranta, ita kanta tana
mamakin Kaunar yariyar yanda take har cikin zuciyarta.
27
AKWAI KURA 2
Fitowar Abba shiya katsewa Mommy zancen zuci, dariya ta
yiwa Abba tare da bashi wajen zama, Abba ya zauna yana
murmushi Habibty Lafiya irin wannan farin ciki dana gani a
fuskarki? Mommy ta yi dariya Daddyn yara lafiya lau Tare
da fara sabing dinsa.
Saleem tun da ya dawo aiki nan falon Mommyn ya yada
zango anan ya ci abinchi tun da yaci bai fita ba yana nan
dafe dakai, har aka kira sallar Magriba sannan ya tashi ya
tafi sallah a masallacin dake cikin gidan nasu ya wuce dan
gabatar da Sallah, sai da yas allaci isha'i kafin ya mike dan
shigowa cikin gida, sai dai me ? Jirine ya debe shi da sauri
ya koma ya dauna, Daya bayan daya -mutanen dake
masallacin, suka dinga fita har liman ya fita sai Daddy dake
zaune yana lazimi, Saleem Na zaune dafe da kai yana jin
jiri duk da a daune yake Daddy har ya gama Lazimi ya tashi
da niyyar fita Amma Saleem na Zaune dafe da kai, Son
Daddy ya-fada tare da tsayawa yana kallon-shi, A hankali
Saleem ya daga kai ya kalli Daddy Kanshi tuni jijiyoyin sun
tashi idonsa ya yi ja alaman damuwa.
Da sauri daddyn Ya karaso Lafiya Son Saleem, ya ciza
lebba yana son daurewa Dad Ya rungume shi a jikin shi tare
dafa kan shi sosai kan nashi ya dauki zafi, Da sauri dad ya
daga Saleem, tare da masa kyakkyawan riko a hankali suke
takawa Saleem na layi kamar zai fadi Dad yana taroshi,
masu gadin second get sune suka taimakawa Daddy wajen
shigo da Saleem gida direct Falon Mommy suka wuce da shi,
Mommy na zaune tana kallo A falo sai ganin ta yi masu gadi
28
AKWAI KURA 2
tallafe da Saleem a jikinsu -da gudu ta karaso garesu tana
tambayar Lafiya? Kira dr Daddy yace da ita tare da karban
Saleem din ya kwantar da shi a kan 3siter.
****
Gabadaya gidan Hankalin su a tashe yake kama daga masu aiki har Masu gadi da suka shigo da Saleem, Mommy tafi
kowa damuwa baka jin sautin komai a falon sai kukan ta,
tun da aka shigo da Saleem Mommy ta kira Family Doctor dinsu, Amman har yanzu-bai karaso ba a karo na uku
Mommyn ta kuma kara waya a kunnenta ganin numfashin
Saleem din ya na shirin daukewa da sauri tace Daddy ruwa a
guje Yar aikinsu hajara ta dauko ruwa ta mikawa Mommy.
Ruwan Mommy ta karba ta bude tare da zubawa a hannunta
tana shafawa Saleem a fuska bakinta dauke da addu'ar nema
masa sauki a hankali Saleem-ya-ja Numfashi-da alamar ya
dawo daga karamin suman da ya yi a hankali ya furta Mom
kirjina Tare da kai hannun shi ya dafa wajen dake masa
ciwo, yana sauke numfashi mai wahala, Daddy ya kuma
rungume shi yana tofa masa addua, tare da yi masa sannu.
Cikin wannan halin likita ya zo ya same su, Ba tare da bata
lokaci ba ya fara bawa Saleem taimakon gaggawa tsawon
Mintuna 30 Doctor nakan Saleem kafin ya yi nasarar gano
meke damun sa cikin sauri ya yi masa Allurar bacci, Tuni
bacci ya dauke Saleem Tare da Sauke Ajiyar Zuciya na
wahala, Alhamdulillah Dukkan su suka fada, Ganin Saleem
ya samu bacci hakan yasa masu gadi da sauran ma'aikatan
dake cike a falon Mommy saboda rashin lafiyar Saleem
29
AKWAI KURA 2
gabadayansu suka fita tare da yiwa iyayeb na sa fatan
Samun lafiyar Saleem.
Doctor meke damun Dana Daddy ya fada yana kallon
Doctor, Doctor yace, Alhaji garin yaya Saleem ya samu
damuwa haka wanda har yake baradana da rayuwarsa? Nayi
mamakin da naga jinin sa ya hauhawa mai yawa wanda mu
likitoci bama kaunar hakan ga maras lafiya, Subhanallah
Daddy ya fada Hawan jini dai Son din nawa ?? Doctor ya
daga kai tare da tabbatarwa Daddy hakan yake nufi,
MOMMY ta kuma, fashewa da kuka na shiga uku na Son
Ban dauka kayi nisa hakan ba Please Son kar ka bari in
rasaka saboda Soyayya pld Son ta fada tana kuka sosai,
Gabadayansu-suka kalleta Daddy da Doctor-! Mommy ta
cigaba da kuka tana Kiran Saleem kar ka-Mutu kan Soyayya
Daddy ya jawota jikin sa yana rarrshin ta Mommy kuka
take har da sheshsheka ta Kasa yiwa Daddy bayani hakan
yasa Doctor ya ya katse mata kukan Alhaji zan wuce ga
takarda nemo wadannan magungunan kafin ya farka, Alhaji
ina baka shawaran ka dauna da danka kaji-damuwar sa-indahali a bashi abinda ya ke so kar matsalar ta shafi zuciyarshi
Daddy ya gyada kai tare da godiya ga Doctor, sallama suka
yi sannan ya fita dan basu guri su tattauna watakila maganar
su ce ta cikin gida shiyasa Mommy ta kasa sanar da mijinta
a gaban sa.
****
Hankalin Iyayen Saleem ya tashi sosai Musamman
Mommy, da tun da Doctor ya fadi matsalar Saleem take
kuka kamar karamar yarinya, Cikin kuka take fadin Laifi
nane Daddy, tabbas laifina ne gashi yaro na yana shirin rasa
ran sa akanta.
30
AKWAI KURA 2
Wallahi banyi zaton Abun zai yi tsanani haka ba na manta ni
uwace addu'ata karbabbiya ce akan dana, ta cigaba da kuka
ta nuna kirjinta ni da kai na nake rokon Allah ya dorawa Son kaunar Amrah, bakomai ya jawo hakan ba sai kaunarta da Allah ya doramin a cikin raina kullum addu'a ta Son ya sota ban yi la'akari da rokon Allah ita ma Amrah ta so shi ba sai gashi Allah ya karbi Addu'ata kamar yadda na roka wayyoni
na shiga uku Son ka yafe min, Daddy rungumeta a kirjin sa
yana rarrashinta Habibty kukan ya isa haka is okay, uwa ba
za ta taba cutar da danta ba sai dai shashashar uwa.
Mommy ta gyada kai Ban yi da niyyar cutar da dana ba, sai
danna hango Alkairi sosai a tsakanin su, kuma ban tsananta
addu'ar ba har sai da nayi istihara naji na samu nutsuwa akai, Allah sarki Son ashe Addu'ata a matsala-zata jefa-ka ka
yafemin Son ta fada tana-share hawaye, Daddy ya-yi murmushi, Mata kenan sarakan wauta Ai da kin masa
addu'ar zabin Allah, kinga in Amrah alkhairi ce a gareshi sai
kiga da kanss yace ita yake so, but nebertheless, Allah ya
bawa Son lafiya, Allah kuma yasa yadda yake sonta itama ta
so shi haka Ameen in ji Mummy ta fada.
Saleem, bai farka ba sai karfe 11pm na dare a hankali, ya
bude ido Sosai ya ke jindadin jikinsa yana karewa dakin
kallo a halin yanzu babu inda ke masa ciwo sai dai rashin
karfin jikinsa da sauri Mommy dake kan sallaya tana sallar
nafila ta sallame, tare da tashi tazo kan gadon Sannu Son ta
fada tana rike hannunsa, a hankali Saleem yake magana
Mom, meya sameni na ganni a dakin Daddy? Mommy ta
girgiza masa kai tana share hawaye Son soyayyar ta ce sila
31
_
-
AKWAI KURA 2
ko? ta fada tana kallonsa, Saleem runtse ido yabude tuni ya
tuno dalilin da ya kai shi kwanciya a dakin Daddyn nashi, a
hankali kamar bai son magana ya furta Mom I **Lo6e her*
**somuch** but ina ta je Na rasa inda zan ganta ! Mom
kusan duk garin kaduna na kewaya but banganta ba why!
Ya fada yana lumshe ido, Karar bude kofar bandaki shi tasa
Mom ta tsaya bata ce komai ba sai ma idonta data mayar kan
kofar tana kallon Daddy daya fito daga Toilet, Ganin Saleem
ya farka da sauri Daddy ya karaso yana masa sannu Saleem.
ya gyada kai tare da kallon Daddy, Dad ku nemo min ta ina
son ta sosai Dad ji nake dazu kamar zuciyata zata fashe
Saboda kaunarta, Dad Mom in babu ita Mutu...Mom ta rufe
masa baki, baza ka-mutu ba, Son da kaina zanfita in nemota
duk inda ta shiga a garin nan, pld Son ka kwantar da
hankalin ka badan jure ganin ka cikin ciwo-ba, Saleem ya-yi
Murmushi a hankali yace Thakns swthrt.
-Son yakamata-ka ci wani abu ko da shayi ne Daddy ya-fada,
Habibty a hada wa *JARUMINA** Shayi Mommy ta yi
dariya Ah ah yanzu kam ya fita daga layin jarumai, tun da
gashi kwance saboda kauna, Saleem ya turo baki yana
shagwaba Daddy kaji Swthrt ko? Rabu da ita Daddy yace in
dai kan Soyayya ce koni da tsufa na ai sai in kwanta In har
Habibty tace bata yina, Dariya Mommy tana jin kaunar dan
ta da mijinta tana ratsa ruhinta, tace aini ban isa ba mutu ka
raba nida kai, Saleem ya yi murmushi yana jin dadin yanda
Iyayen nasa suka tsufa da soyayyar junansu.
32
AKWAI KURA 2
Daddy ne ya taimaka masa ya tashi zaune, Mommy ta hada
masa shayi a hankali take bashi a baki, cikin shagwaba
Saleem yake sha tare da jaddadawa Mommy lallai fa in bata
so ta rasa shi a nemo masa Amrah, Daddy na musu dariya ai
dolen ta Son kai dai Allah ya kaimu gobe da rai da lafiya.
a dakin Daddy Saleem ya kwana tare daddy saboda tsoron
kar ya kwana shi kadai tunanin Amrah ya hanashi bacci
gashi bai da lafiya, Ita ma Mommy bata bar dakin Daddy ba
Sai Karfe 2am sannan ta koma dakinta Asuba tagari.
****
Ranar Juma'a tun