Daddyn shi, Dad yana daukan wayar kamar yaro
karami Saleem ya fashe da kuka, Dad dake Office ya mike a
radane yana tambayar Son din nasa lafiya ? cikin kuka
Saleem ya sanar da Daddy Matar shi ta bata, Dad daya kasa
gane inda Zancen dan nashi ya nufa, gabadaya hankalin shi
a tashe Yake maimaita Tambayar meke faruwa kawai dad
yake yi.
63
AKWAI KURA 2
Cikin kuka Saleem yake fadin Dad ba a gantaba matata ta
bata Dad koma waye yake da hannu cikin batan Matata sai
na harbeshi, Dad Na rike da waya cikin rarrashi yake
tambayar Saleem me ya faru? Saleem, Ya kasa magana sai
kuka karshe Maheer ne ya karbi wayar cikin alhini ya sanar
da Dad abunda yake faruwa, Dad shi ma take hankalin shi
ya tashi, Cikin damuwa yace da Maheer Please ka kula da
abokin ka ba lafiya yake da its ba ka rarrashe shi kuje gida
ina zuwa gidan yanzu, bawa Son wayar Maheer ya sanya
wayar a kunnen Saleem Cikin rarrashi Dad ke fada masa za
a sameta ya turo masa da hoton ta a WhatsApp zai tura a
fara Bincike yanzu.
A hankali Hankalin sa ya fara dawowa jikinsa sakamakon
rarrashi da Abban ya masa a gefe kuwa-ga Maheer sai
Lallabashi yake, a wayar Maheer suka samu photon Amrah
funi ya turawa Dad a whatsApp, dad yana ganin sakon
shima tuni ya yi forwarding zuwa ga hukumar bincike ta
kasa baki daya
Saleem bai yarda sun koma gida ba direct Office, na yan
sanda suka nufa, cikin awa biyu kacal garin Kaduna ya cika
da jami'an tsaro lungu da sako, kama daga kan Yan-sanda
Sojoji hae Dama Jami'an Costum ba'a bar su a baya ba,
Saleem ya-tura CONVOY din sa neman inda Amrah ta
shiga, shima bai dauna ba wuni surrre suna zaga Kd da
jajinta Neman Amrah, basu dawo gida ba sai bayan sallahr
isha"i shima da kyar Mom ta lallabashi a waya ya dawo gida
kan cewa gobe su daura daga inda suka tsaya, cikin lokaci
kadan da sanin batan Amrah, Tuni Maganar Batan ya bazu
ko ina cikin birnin KADUNA da kewayanta, gidan Radio
da talabijin kowanne sai sanarwa suke na batan ta tare da
64
AKWAI KURA 2
fadar kyauta mai tsoka ga duk Wanda ya fanta ko ya kawo
labarin ta.
******
Da kyar Zahra ta lallaba Granny ta janyc maganar dauko
Sojoji, Zahra da kanta ta tsare keke napep tare da masa
kwatancen inda zai kai Granny, Zahra ta ciro kudin a jakarta
ta cire kudin ta biya mai keke napep, ita kan ta granny kuka
shar shar take tana salati, tare da kiran Sunan Zainabu Ina
zan ganki kamar Zainabun tana gabanta.
Sai da mai Keke napep yaja ya tafi kafin ita ma Zahra ta
hau dan acaba ta yi ta tafi nasu gidan, Mai keke napep yа
ajiye granny a kofar gidan Ummy cikin sauri ta buga get din
gidan, Malam isihu mai-gadi da sauri ya taso ya bude get
tare da fadin ah ah Mutumiyar kece tafe Baki ya bude yana
mamakin me yasa Tsohuwar kuka, ita ko Iya kala ba tace da
shi ba ta sanya kai ta wuce cikin gidan, Ikon Allah mai
gadin ya fada yau dai lafiya meke faruwa a cikin gidan ga?
Iya Ta fada falon Ummy ko sallama babu cikin fada tana
kuka ta fara magana ina Usmanu, fito yau bani ba kai
Azzalimi tun da ka zamo algungumi, fito matsiyaci yau bani barin gidan nan sai ka -fitomin da Jikata Azzałumi
macuci yau mai rabani da kai sai Allah.
Da sauri Ummy ta fito daga daki jin maganar Iya ganin
iya tana kuka Ummy taji kamar Yanzu abun ya faru, bata
san lokacin da itama ta fadi a jikin Iya ta sake fashewa da
kuka ba tare da fadin Iya mun rasa Amrah, Iya yau kwana
10 Amrah bata gida waya sani ma ko an cinye naman ta
wayyo Iya na shiga uku ban rike Amanar Marainiya ba Na
bu da namiji ya batar min da diya, Ummy ta fada tana kara
sautin
65
AKWAI KURA 2
kukan ta tare da kankame Iya.
Iya ta daga murya Ina Usmanun yake ya fito Ya fadamin
inda ya kai min jikata Ni nan zanje in dawo da Jikata, ko
Dajin Sambisa take ni zanje saboda ceto rayuwar diyar
Amaduna, kuma insha Allah mun riga ka munce Allah
jikata bazata mutu a hannun Azzalimai ba.
Alhaji Usman da tun shigowar Iya ya jita amma kunya ta
hana shi fitowa, duk kalar zagin da Iya take a kunnen sa
gareshi san bai zargesu ba saboda ran mutum guda ba abun
wasa bane ace an rasa, Shi kansa tun faruwar abun tsawon
kwana Goma, bai zauna ba yana kan bincike tare da
yaranshi kan inda Amrah take, inta son ranshi nema yaso a
sameta kafin Kowa ya farga saboda gudun irin wannna rana.
Muryar Iya ya dawo da-shi daga tunani Usmanu ka fito ko in
biyo ka daki dan yau babu sauran mutumci a tsakaninmu
Algungumi, Abban Amlah Cikin karfin hali ya fito falon
yana sun sunne kai, kamar munafuki fuskansa dauke da
Tausayi tare da damuwa na ganin halin da Tsohuwar da
matarshi suke ciki, Cikin dauriya ya nemi kasan kafet ya
dauna tare da gaisar da Iya sai dai Iya bata amsa ba illa
harara data doka masa.
Cikin lallashi Abban Amlah ya fara magana Iya ki yafe
min domin Allah, Ni ban da abunda zan kare kaina sai dai
Allah ne shaidata banyi hakan da niyyar cutarwa ga Amrah
ba Ai nima Amrah diya tace Saboda Zainab Amrah ni
Ubanta ne, sai dai baka tara sani da ikon Allah wallahi
tallahi Iya da dana san hakan zai faru da ban fara ba......
Dakata Iya ta fada tana nuna shi da dan yatsa Kulllll nace
maka kul kar in karajin kalmar baka san haka zata faru ba in
hakane me yasa baka sanya yayanka ba. ? da aka samu
66
AKWAI KURA 2
matsala me yasa kamar yadda kazo ka sanar damu kafin
aikin yanzu ma baka sanar damu an samu mishkila ba? To
Azzalimi jinin diyata daci gareshi yafi karfin cin ka ai
daman Masu kudi yanzu bana Allah da annabi banc Kudin
tsafi neWallahi tallahi babu inda zanje saika fitomin da
Jikata.
****
Yau shi ne karo na farko da Granny Ta fara kwana a gidan
Ummy a cewar granny babu inda zata je sai Abban Amlah
ya fito mata da jikarta, Tun data zo bata saurara mishi ba har
sai da ya bar gidan.
tun fitar shi bai kuma waiwayar gidan ba Allah ya taimake
shi ma yau, kwanar gidan Uwargidan dan haka can daya
gidan ya wuce Tabbas ba dan haka ba da ya shiga uku a
wajen granny.
Shi ma koda ya fita bai dauna ba Shige da fice su kayi
sosai shi da yaran sa na office su na neman inda Amrah ta
shiga, bai samu kansa ba-har sai-karfe 11pm na dare kafin
Uwargidan ta ganshi, Abun mamaki Da shigar sa gidan
Uwargidan a zaune ya sameta tana jiran sa cikin tashin
hankali, domin tu ni ita ma ta samu labarin batan Amrah ta
sanadin gidan Radio, Abban Amlah na shigowa falon Hajiya
mariya ta fashe da kuka tare da fadawa jikin mijin ta, tana
tambayar shi ko an dace da ganin Amrah, Abban Amlah
cikin damuwa ya sanar da ita har yanzu ba'a dace ba sai dai
ana kan nema, cikin tashin hankali tana kuka tace da shi ya
koma gidan Ummyn yan uku ita kan yau ta yafe kwanan
saboda tasan Ummyn Uku ita ke bukatar kulawar sa yau,
Amman sai ya yi murmushi tare, da sanar da ita karta damu
Ummyn yan uku tana tare da lya.
67
AKWAI KURA 2
Washegari, family ukun sun tashi cikin tashin hankali na
rashin samun labarin wanda yaga Amrah bare ita kanta
Amrah, Ummy da granny yadda suka ga rana haka suka ga
dare Maganar bacci babu shi cikin gidan Uku.
Saleem Kuka sharshar ya yi wa Mom nd Dad na rashin
ganin Amrah, Ita kanta Mom din tana bukatar mai rarrashi
domin rashin Amrah ya taba ta sosai Mom da Amrah Akwai
shakuwa mai girma a tsakanin su, Mom da kanta ta kira
Mera tasanar da ita batan Amrah, Tare da halin da dan
uwanta Saleem yake ciki na Tarkon Kauna.
Mera ta fashe da kuka cikin tashin hankali Maman Affan
Mun shiga Uku Mom ko masu garkuwa da mutane ne suka
dauke ta, please Mom ko nawa suke bukata nayi alkawarin
dan biya in fanshi ran Maman Affan.
****
Zahra Da kuka ta isa gida, dan achaba yana sauketa a
kofa get da gudu ta shiga gidan su, Mamah Mamah ta dinga
kwala mata kira tana kuka da sauri Mama ta fito daga
Kichin Zahra'u lafiya irin wannan kira hak.
Zahra ta fada a jikin kujera tana kuka Mamah An sace
bestyna Mama Bestyna bestyna Mamah ta fada-tana kuka
sosai, Mamah ta riketa yi min bayani bangane an sace ta ba?
Zahra tana kuka eeh Mamah ranar da naje na dauketa Mu
kaje shopping Ashe Bestyna bata koma gida ba Cikin kuka
ta sanar da Uwarta abunda ya faru, Innalillahi wa inna ilaihirrajiun.
Mamah ta fada tana Dama akan kafet, Mun shiga uku dan
mutum ya bata bat sai kace kaza, Ayya Amrah baiwar Allah
tana mace ko a raye sai Allah a ce yau tsawon kwana goma
da batan mutun amma ba'a sani ba kai Amma anyi sakaci
68
AKWAI KURA 2
ran mutum ai ba ran dabba bane Allah ya baiyana Amrah
Allah yasa tana hannun mutanan kwarai.
Mamah Bani wayarki in kira yaya Anas Wayata na barta
falon Ummy, Mamah tace-ah-ah karki daga masa hankali ya
kasa Tuki a kuma shiga wata matsalar barshi in ya dawo
gida zai ji a tsanake kinsan Yayanku sarai da dimuwa, Zahra
tace ah ah Mamah ki bani in ce yazo kina son ganinshi dan
nasan in ma baiji labari anan gida ba zai ji a waje kuma a
halin yanzu Yaya Anas yana bukatar jin lbrn dan ya dauki
nashi matakin kafin wanda bai da alhaki akanta ya dauki
Hidimar da ba tashi ba.
Mamah ta kalleta waye bai da alhaki akanta Zahra ta yi shiru
tana kifta ido Mamah bani wayar ta fada tana-share hawaye
Mamah tace gata dan Allah ki tabbatar baki sanar da shi ba
saboda dalilin dana fada miki, Zahra-ta karbi waya tana
danna kiran lambar Anas.
*****
A zaune ya kwana yana cikin saboda damuwa daga
karshe Bandaki ya shiga ya dauro alwalah, bayan-ya fito
darduma ya shimfida ya tada sallar Nafila, Saleem da ya kai
karfe Ukun dare yana ibada tare da tsananta addu'a-cikin
sujuda akan Allah ya baiyana Amrah, Karfe uku da rabi na
dare ya kammala sallah, haka kawai ya ji yana kaunar ganin
photon ta wayarshi ya dauka akan T6 tare da shiga Galary
ido ya tsira mata cikin Tsananin *So Da kauna*
Tuni zuciyarshi ta yi nisa wajen shaukin begenta, kamar an
tsikare shi ya mike tare da futa daga dakin Kofa ya bude
direct ma'adanar CCTB camera ya tafi Haka kawai ya ji
yana kaunar yaga All shigarta da fitar daga gidan, Ba tare da
bata lokaciba ya ciro SD card din laptop dinsa ya jawo tare
69
AKWAI KURA 2
da dama akan kafct tuni ya sarrafa komai cikin kwarewa,
Ido ya duba yana kallon Laptop din cikin minti kadan 6ideo
ya fara aiki.
Saleem ya kai minti 18 yana kallo sai dai har yanzu bai ga
abunda yake kaunar ganiba, hakan yasa ya jawo laptop din a
hankali ya fara forwarding dasauri ya tsaya Cikin nutsuwa
ya fara kallon ta tuni ya ji farin cikin ya ziyarci zuciyarshi,
Kallon ya maida hankali kai a sannu yake ganin komai tun
farkon zuwan ta gidan neman aiki cikin local dress.
****
Yadda take komai nata a nutse da yadda take yin aikin nata
cikin kwarewa abun ya burge Saleem, Babu abunda ya
burgeshi irin yanda yake kallon ta da Mom cikin nishadi tare
da Affan Da Meerah, Saleem ya lumshe ido yana jin nishadi
Akwai kauna mai yawa tsakanin Matarsa da parent dinsa
lolz öYTM Murmushi ya yi tare da cigaba da kallon ta a
kichin tana girki.
Amrah mai kyau ce abin son kowa ya fada yana kare
mata kallo cikin kishigarta mai kyau, lsanye take da kayan
girki Riga da skirt iyakarta guiwa ta yi kyau sosai cikin
shigar duk wani baiwar kyau nata, tare da kyan halittar ta ya
bayyana, kanta sanye da hula ya yin da gashin kanta yake
zube a kafadar ta har gadon bayanta.
Saleem ya sanya hannu ya yi screenshort-na gurin saboda
tsananin kyau data masa, a hankali ya yi playing bideo din
ya cigaba da kallo cikin nishadi yake kallon ta Abun ya
burge shi lokacin da yazo inda ta shigo gidan ta labe tana
kallonshi yana motsa jiki Baki Saleem yankama alaman
mamaki, *Wash** ya fada afili yana lumshe ido saka
70
AKWAI KURA 2
makon ganin lokacin da ya take ma ta dan yatsa, a hankali
kamar tana kallonshi ya furta "Sorry My Madam."
Kiran Assalatu shiya fargar da-Saleem daga kallon daya
shagaltar da shi cikin mika ya jawo laptop dai kashe sai dai
me ? da sauri ya tsaya yana kallonsu tare da kankame
Laptop din a jikinsa, cikin second uku Abunda ya faru ya
fara baiyana masa Tun daga lokacin da Uwar da yarta suke
zuwa gurin har lokacin da suka fara tone rami, Sosai Saleem
ya ware ido tare da tsaida Hankalin shi dan ganin me zai
faru, Abun kamar a mafarki Amrah ta tako wajen kunnanta
manne da waya.
Cikin sauri ta boye jikin garu tana leko da kai tana kallonsu,
daga bisani Wayarta ta sai ta tana Bideo, komai daya faru a
gun ya cigaba da gani Inda yaga Kanwar Dad nashi da
diyarta sun ciro manya manyan layoyi, cikin sauri suka
binne a cikin ramin tare da mai da kasar gurin, Da sauri suka
bar wajen hankalin su kwance sun gama aiki.
A hankali ta fito daga maboyarta-komai da ta yi Saleem ya
gani Cikin tsananin mamaki ya gyara dama har saida daukan
ya kare, ikon Allah ya fada yana tuno ranar da ta canda
masa abinci, Wacece ita ?meyasa ban farga da komai ba sai
yanzu? Lallai kinchi sunanki *JARUMA* Ko a films bai
taba ganin kaddara irin tashi ba, da sauri ya mike tare da
kallon Agogo karfe 6:30am na safe Saleem ya kashe laptop
din tare da shiga bandaki dan dauro alwala.
****
Cikin sauri ya gama shiri cikin simple dress Wayoyinsa
ya dauka tare da fita falon Mom, a gurguje suka gaisa cikin
kulawa iyayen nasa suka jajanta wa juna Matsalar tasu, Dad
ya kara masa bayanin in shaa Allah za'a dace.
AKWAI KURA 2
Tnz Dad ya fada yana korarin fita, Mom barinje ana
nema na Office na yan sanda kan case din, Mom ta tsayar da
shi Son ko ruwan tea kasha please kai ma ba lafiya gareka
ba ta fada tana langwabe kai, Dad Ya amsa Ayi hakuri asha
*JARUMINA*
Saleem ya yi murmushi hakan kawai yake jin nishadi tare
da jin kwarin guiwa kan Masoyiyar tasa, Owkhey ! yace da
Su tare da jan kujerar Dinning ya zauna Cikin sauri yake
shan tea din, kirrr wayarshi ta yi kara Cikin hanzari ya
dauka Maheer ne ya kira Hellow abokina kana jina Saleem
lumshe ido tare da fadin uhum Maheer ya cigaba da magana
Yan sanda sun kirani yanzu ni da Madam dita wai Muzo mu
amsa wasu yan tambayoyi banyi kasa a guiwaba naje na
dauketa muka je But suna maganar kulle mu ni da madam
har sai anga Amrah.
Saleem Ya yi shiru yana sauraron Maheer Cikin nutsuwa
ya furta bery good in deed, ashe yanzu sun san aikinsu.
Cikin jindadi ya fara magana akwai farkon Tuhuma ne
bayan kai da Madam dinka? Think tare kuka futa after dat
har yau ba'a ga matata ba dan haka Hukuma suyi aikinsu kan
duk wani mai ruwa da tsaki cikin batan matata bai saurari
amsar Maheer ba ya kashe wayarsa tare da mikewa Baki
Mom ta sake tana kallon Saleem fuskanta cike da zargin shi,
Saleem ya mike yana kauda kai Mom Dad saina dawo ayi
min addu'ar dacewa ya sanya kai ya bar falon. ****
Numfashi ta cigaba da saukewa tare da kallon su, saura
kadan su cimma ta, Amrah ta daga waya tana dan nawa
cikin dace ta samu wayar babu Pasaword, Ita din gwanace
wajen haddace number akanta duk wani contact dake
72
AKWAI KURA 2
wayarta dai dai ne bata dasu a haddace akanta, Amrah bata
yarda da number a wayaba saboda bacin rana irin ta yau,
cikin Jarumta ta yarda da shawarar zuciyarta na ta kirashi
hakan kawai taji a ranta shi din zai taka rawar gani wajen
kubutar ta a hannun Azzalumai...
Ido ta runtse tana kallon number a idon zuciyarta, kamar
yau Mom ta yi dialing, a wayarta Masu karatu in baku manta
ba, last tym Mom ta karbi wayarta ta kira Saleem.
Cikin Sauri ta fara Rubuta Number din a wayar ya yin da
idonta yake kansu suna karasowa cikin gudu, Hannu tasa ta
ciro bindiga a cikin aljihunta tare da sai ta bangaren su tana
numfashi cikin sauri taji an daga wayar Nishi take fitarwa na
wahala cikin muryanta mai Dadi tafara magana *Please help
me OGА J.*
Tas tas tas, ta harba bindiga Cikin nasara ta samu biyu a
cikinsu Gabadayan su suka tsaya daga nesa tare da daga
hannu alamar sunyi saranda, Amrah ta fara magana cikin
wahala duk wanda ya karaso gareni sai dai uwarshi ta haifi
wani, cikin wannan hali Ahmad ya karaso gurin da gudu
Turuss ya tsaya yana kallonsu Kamar a filin yaki Ido ya kai
kan yaransa da suke yashe cikin jini da alamar daf suke da
mutuwa.
Cikin izza ya fara magana kin ci amana Alkawari-bai ce
haka ba Lallai na yarda mata shaidanu ne masu kwandon
sharri, Amrah cikin fada ta fara magana cin amana ya wuce
naka kai in kana da kunya har kana da bakin maganar
Amana in ji amininka abokinka wanda ya sadaukar da
komai nashi akanku shi ka ciwa amana. ? To kasani taka
tazo karshe kai da duk wani azzalumi wallahi tallahi ko dan
rasa raina sai asirinku ya tonu.
73
******
AKWAI KURA 2
Tuni yan sanda suka yi ram da Abu Amlah, bisa ga
umarnin Saleem Ummy ko da ta samu labari ko kadan bata
ji haushi ba hasalima taji dadi abinda matashin saurayin ya
yi duk da bata san shiba batataba ganin sa ba sai akan case
din Amrah.
Tun wayewar garin yau yan uwa da abokan Arziki suke
zarya a gidan Saboda masu mata jeje kan abunda ya faru,
Granny da taci kuka har ta godewa Allah tun faruwar
lamarin bata samu nutsuwa ba ita ma taji dadi sosai na kama
duk wanda yake da alhaki cikin batan Amrah.
Anas shima tun da ya samu labarin batan Amrah yake
cikin tashin hankali Shi ma ba'a barshi a baya ba kasancewar
sa jami'in yan-sanda tuni ya baza nasa yaran kan nemo
Amrah, Daga faruwar lamarin zuwa yandu duk wani
majalisa ta daba a jihar Kaduna hukuma ta yi ram dasu, dai
dai ku ne a cikinsu da suka samu labarin ana kame su sukа
nemi maboya.
Tun da iyayen Zahra suka samu labarin an rike Zahra
hukumar bincike hankalin su yake tashe fiye da batan
Amrah, Dakansu suka je office na yan sanda tare da
jagorancin Anas daya kasance shima babbane cikin
ma'aikatan na Yan sanda, Sai dai sawun giwa ya take na
rakumi wanda yake da alhakin shigar da karar Babbane
cikin ma'aikatan Custom, dan gidan babban Attajiri a kasar
Alhaji Hamza shiyasa duk wani beli babu wanda aka bada
daga Maheer, Zahra Harda Alhaji Usman.
Faruwar wannan abu ya bata ran Iyayen duka musamman
Iyayen Anas basu ji dadi kan abinda aka yiwa diyar suba
ance mai da wawa tun da Dad yasamu labarin Yan sanda
74
AKWAI KURA 2
sun hana beli tuni ran sa ya baci- Cikin Tashin hankali dadamuwa ya kira Anas a waya gabadayan su suka dunguma
gidan Ummy danjin ba'asi.
Saleem Daga gida direct gidan Ummy ya nufa saboda sun
yi mAbaba da yansanda kan ya kawo Ummy domin ta amsa
wasu yan tambayoyi kan dalilin batan Amrah-musamman da
take zargin akwai sanya hannun mijinta, Cikin sa'a da isa rsa
gidan Iyayen Anas suka karaso ya yinda Uwar gidan Alhaji
Usman tuni ta tsufa a gidan Ummy tun da garin Allah ya
waye da Yan sanda suka je suka yu ram da maigidanta.
Tun da Saleem ya fito a mota Anas ya tsura masa ido tare
da mamakin mai ya kawo Young Millonia gidan, haka
Abbansu ido ya tsura yana kallon Saleem fuskanshi cike da
alamun kamar ya sanshi, Saleem bai ce kala garesu-ba-kallo
daya ya yi wa Anas ya hango tsananin kamarsu da Zahra,
take ya ramfo zancen wannan shi ne Anas barawon matarshi
Saleem ya ji ran shi ya baci-tare da tsananin kishi ji yake
kamar yaje ya fasa kan Anas da bindiga....
*****
Mtsw! Ya ja dogon tsaki tare da kama hanyar shiga
falon ko Izini bai jira ba cikin muryar shi mai dadi mai
tattare da damuwa ya yi sallama a falon, yan uku dake zaune
suna cin abincin break da gudu suka rungumeshi kamar sun
sanshi Oyoyo Uncle, Saleem ya ware hannu tare da musu
alamin suzo da gudu Mazan suka fada jikinsa Saleem ya
daga su sama tare da ajiyesu Hannu ya mikawa macen Oya
".come יי
Amlah ta tsuguna har kasa tana gaida shi tare da make
kafada Ummy ta hanamu Tace ba kyau ni mace ce Allah ya
75
AKWAI KURA 2
hana, Saleem ya yi murmushi tare da ya bawa Ummy kan
tarbiyar da take baiwa yayanta.
Bismillah ka dauna Ummy tace da shi tare da Amsa
sallamar Hajiya fatima dake bayan Saleem Cikin nutsuwa
Saleem ya gaida Ummy tare sunne kai wai shi kunya,
Ummy ta amsa cikin sakin fuska tare da jin kaunar dan
saurayin a ranta Duk da bata san waye ba Gareta tun jiya
datai masa kallo daya taji ran yanaa sonshi-Musamman inda
ya tsaya kan tsayin daka game da batan diyar ta.
Mamah ta yi gyaran murya Iya tare muke da Abbansu
Anas suna jiran ai musu idini su shigo, Ummy ta kalli yan
uku Amat jeka shigo da baki da gudu Amat ya fita bai jima
ba ya shigo da Anas da Abbanshi, Bayan gaisuwa tare da
jajantawa juna abin da ya faru.
Abban Anas ya fara magana Anas ya sanar da mu duk
abunda ya faru kafin In daura dalilin zuwan mu, Anas ya
sunkuyar da kai tare da satar kallon Saleem da wutsiyar ido
lalli yau dole ya tona asiri Koda hakan yana nufin Saleem
din zai dau mataki bada komai ba ya zamo dole ya fadi
iyakar gaskiyar daya sani.
****
Gabadaya falon ya yi tsit kamar babu halittar dan adam
a ciki, dikin nutsuwa Anas ya fara sanar dasu tun-farkon
zuwan Amrah har office din sa, kan alfarmar ya koya mata
harbi da farko yaki amincewa Ammaa da Amrah ta rinka
masa magiya ba dan ya so ba ya amince saboda tsananin
kaunar ta da yake bai yi la'akari da risk din da zai jawo masa
a gurin aiki ba.
Ya cigaba da basu labari tun daga lokacin daya fara koya
mata harbi har kawo yau da aka rasa Amrah sama ko kasa
76
AKWAI KURA 2
Anas yakara da fadin, koda kafin hakan ya faru bangajiba
kullum ina cikin tambayar ta meye dalilinta na aikata hakan
sai dai Amsa daya take bani in lokaci ya yi zan sani, da fari
naji tsoro amma daga baya nima na ware saboda itama da
take mace babu shakka ko tsoro a tare da ita sai dai kullum
tana sanar da ni Babu kuskure cikin abunda ta keyi inlokaci
ya yi dan shaida.
Bantaba jin tsoro ba sai ranar da Muna cikin koyan harbi
tsautsayi ya fado kan mu inda Amrah ta harbi assistant
controller na Costum, Anas yaja numfashi tare da nuna
Saleem da hannun shi.
Gabadaya kallo ya koma kan Saleem Musamman Ummy
data yi mamakin Ashe a TB take ganin fuskar Saleeem
musamman da duniya ta yi shaida shidin mai gaskiya ne a
cikin aikin sa., haka Abban Anas shi ma da sauri ya ramfo
inda yasan Saleem, anas ya cigaba da magana.
Na yi kuskure nayi wauta a matsayi-na-na namiji-dana
biye mata ba tare dana san hujjarta na-aikata-hakan ba,
Soyayya ta rufe min ido banyi la'akari da hatsarin da-zamu
shiga daga ni har ita ba, sai jiya dana samu labarin batan
Amrah...
Salati gabadaya falon ya dauka Tare da kukan Ummy,
Anas lallai kayi wauta Mamah ta fada ai wannan ba abun
shiru ba ne gashi sai da abun yafi karfin mu ka fada Ohhh!
Ni Fatima ta ina damu fara neman Wannan yarinya ?
Granny ta fashe da kuka tana fadin Allah ya bayyanaki
Zainabu na, Allah yasa kina hannun mutanen kirki, Ta
nuna Anas da yatsa wannan anyi dan bandan yaro mai
kwalelen kai da gani wannan baki naka har cikin zuciyarka
ne, Ban san kwakwalwar kifi gare ka ba sai yau, ashe baka
77
AKWAI KURA 2
da tunani kai da kake namiji ai kai ne mai laifi da baka sanar
da kowa ba yo inni Tsohuce aiko Uwarta kazo ka sanar mata.
To kalleni da kyau na fasa baka auren Zainabu na koda
Allah ya bayyanar da ita Aure babu shi tun da kaima
shashasha ne ko auren kuka yi ba zaka rinka ganar da ita
hanya madaidaiciya ba, da sauri Anas ya fara bada hakuri
tare da tsiyayan hawaye dan yasan wannan tsohuwar tsab
data iya aikata abunda ta fada, shi ko in ya rasa Amrah ai saidai ya hakura da Aure.
***
Kirır karar kida mai dadi ya karade falon Saleem da
gabadaya ransa ya baci jin Anas yana fadar magana sai kace
mace saboda wauta Lallai ya zamo dole ya daure Anas
domin harda gudunmowar shi wajen Batar-da- Amrah,
Saleem sosai yake jin tsanar Anas da ya dage yana fadin
yana son Amrah, ji yake kamar ya kama Anas ya yi masa dukan kawo wuka.
Saleem cikin gajiya da karan kidan wayar nashi ya daga
wayar tare kallon Number din wayar mtsweee yaja karamin
tsaki tare da yarda wayar kan hannun kujera da yake zaune, Saboda bakuwar Number ce shi kuma baya daukar bakuwar
number, Sai dai tuni duciyarsa ta tunatar da shi Halin da yake ciki na batan sahibar shi kowani Number halak ce a
gareshi ya amsa, hakan kawai ya ji zuciyarshi na gargadinsa
daya dauki wayar, Kamar ba daiyi magana ba yace hye !!
What ya fada da sauri ya mike Gabadaya