maganar
Gojen ya yi, Ahmad ya matse wayar a kunnen sa tare da
Murmushin Mugunta.
A ran sa ya fada dama wannan ranar nake jira dan nasan
zata zo amma a fili sai Ahmad ya bushe da dariya Tare da
furzar da iska daga bakinsa Alhajin Allah na san zaka neme
ni, ba saboda komai ba sai saboda hajar ka da take hannuna
na.
Ahmad ya kuma bushewa da Dariya Sai dai nayi mamakin
da kayi jinkiri wajen nema na dan hakan ina maka Albishir
da ni *Ahmad Fiya-fiya* na rubanya Farashin/ka, Tuni
48
ง
AKWAI KURA 2
hajarja ka ta zamo tawa ma'ana Yarinyar ka Ta Zamo
mallakin Ahmad.
Rasssssss! Gaban Alh. Musa dan chanji ya fadi an zo
wajen ya fada da karfi tare da Neman kujera ya zauna dan
ba zai jure sauraron maganar da suke yi a tsayeba saboda
Firgicin da yake cikinta.
Amrah Tun wayewar garin yau gaban ta yake ta faduwa Ita
kanta bata san me yake damunta ba, sai dai daga bisani ta
Allaka damuwarta akan tsarkin data samu wayewar garin
yau, tuni ta yi na'am da abinda zuciyarta ta tunatar da ita,
tabbas Taji tsoron samun tsarkin nata ba dan komai ba sai
saboda takadirancin Ahmad.
Ita kanta tasan in har ya farga ta samu tsarki to fa Allah ne
kadai zai kare ta daga sharrin Ahmad, daga karshe ta yanke
hukuncin komai rintsi yau zata tsere daga cikin gidan
Ahmad koda baza ta tsira da rayuwar ta ba tabbas za ta yi
yunkurin hakan in ta yi ruwa Rijiya.
Kaurin indomien da ta daura ne ya dawo da ita hayyacinta
da sauri Amrah ta sauke Indomien ta juye a filet din
tangaran, dafaffen Kwai guda uku ta dauko a cikin tukunya
da ta dafa ta hau 6arewa, tana gama-6arewa ta-jera-a gefen
indomie, Flask din ruwan zafi ta dauko tare da neman
madaidacin tray ta jera a kai, cikin nutsuwa ta dauki indomie
din da niyyar kaiwa Ahmad a falo kamar yadda ya yi mata
umarni.
Chak Amrah ta tsaya jin sunan Dan Chanji da Ahmad ya
kira a hankali ta fara komawa da baya Cikin Ikon Allah ta
koma kichin da sauri ta ajiye tray din dake hannun ta
Matattakalar benen ta haura cikin sauri ta kai ga dakin da
yaran shi ko in ce yan daban sa masu masa aiki, cikin ikon
49
AKWAI KURA 2
Allah ta samu dukkan bacci suke da alamar ko sallah babu
wanda ya yi a cikinsu.
Da sauri ta janye kofar window tare da sanya kan ta tana
hango tazarar dake tsakanin ta da Kasan dakin, Amrah ta
runtse ido tabbas in ta fado nan raga raga data kakkarye, da
hanzari taja windon tare da canda tunani, wayoyin su dake
makale jikin charji ta sanya hannu ta dauki daya a ciki.
Tare da fita daga dakin a hankali take takawa har ta iso falo
in da Ahmad ya cigaba da wayarsa yana dariyar mugunta, da
sauri ta shige dakinsa direct kasan gadon ta shige cikin sauri
ta dauki bindiga, Sanyi taji a ranta ganin Akwai harsashi a
ciki da saur ta soke bindigar ajikin wandon, Bata tsaya wani
tunani ba Amrah ta tun kari bakin get din gidan gadan gadan.
****
Cikin bakin ciki tare da kulewa da dariyar da Ahmad yake
masa, Bai san lokacin da ya daka masa tsawa ba Shashasha
ka saurare ni, Dan Chanji ya fada cikin ihun Masifa.
Ahmad dake kyalkyala dariyar mugunta ya ji kalmar *Dan
CHANJI* ta doki dodon kunnuwansa tuni ya ji ran sa ya
baci, wani tukukin bakin ciki ya ziyarci zuciyarsa, shi ma
cikin Fada ya amsa In saurare ka akan me? maganar daya ce
ni da kai gaba ce ta har abada, Ba gudu ba ja da baya ka fito
filin yaki, mu fafata Sai dai alamun nasara sun fara nuna yar
manuniya cewa ni ne da cin gasar, kuma ni ba dan cikin ka
ba ne da zaka dinga daka min tsawa, please Mantain ur self
ya fada tare da kokarin katse wayar.
Shima dan chanji cikin bacin rai ya cire wayar daga
Kunnensa yana kokarin kashe wayar, da sauri Goje ya yanke musu hanzari Oga rike waya Maigida Bata kai ga nan
ba kubani 1 minute Alfarmar Annabi Muhammadu, duk
50
AKWAI KURA 2
maganar da suke tun dazu yana sauraron su kasan cewan shiya hada confrence call din.
Ganin wayar zata kare bai samu Alkawarin Dubu 100 da Dan chanji ya masa Alkawari ba cikin sauri ya yanke
shawaran katse musu hayaniyar, ya damo dole ya sasanta maganar da suke, musamman daya fara hango Ahmad yana
so ya masa asarar dubu dari chas da Dan Chanji ya masa alkawari kafin kiran wayar, cikin muryarsa ta mashaya ya fara Magana.
Oga kaina a kasa kai min alfarmar sauraron Maigida dan
nasan ruwa baya tsami banza fa Oga, Harkallar dayace Mu
duka watarana ai za ai wa juna rana, Oga ka ankare.
Ahmad ya sassauta-murya-ina-jinka -Alhajin Allah *Dan Chanji*.
****
Bakin get din Amrah ta tunkara, cikin jarumta da rashin
tsoro, Amrah ta riga ta kuduri aniyar barin gidan kota halin
kaka musamman da ta san yau karyar ta ta kare, asirin ta yau
ya tonu ga daukacin mazauna gidan Ahmad, Cikin sauri ta
dunfari get din zuciyarta cike da rashin tsoro, ta riga ta
shirya duk abinda zai faru ya faru wajen barin ta gidan.
Cikin ikon Allah babu kowa a bakin get din mamaki sosai
ta yi tare da murnar hakan, a fili ta furta Alhmdulillah,
Cikin sauri ta yi hanyar fita mai gadi kadai ta hango zaune
kan benci yana sauraron kida a wayarsa tare da kada kai
alamar wakar ta yi gaba da imanin sa.
katoton inyamuri ne kakkarfa mai cike da Rashin tsoro
fuskar sa daka gani zaka hango rashin imani a tare da shi,
Amrah ta kuma lekawa da kanta karo na biyu bakin get din
51
AKWAI KURA 2
ta kalla dan nemawa kanta mafita, get na rufe sai dai
karamac kofar shiga da fita a wangale tame Amrah ta yi
murmushi ganin hanyar fita a free lolz ðÝ €.
A hankali ta koma ta labe jikin mota tana hangoshi, mai
gadi yana kada kai yana jin dadin wkaar daga karshe ma
mike wa ya yi ya bar wayar akan benchi ya fara taka rawa,
gabadaya ya shagala yana tikar rawa tare da bin wakar cikin
muryansa mara dadin Sauraro.
kamar kiftawar ido Amrah ta fice daga gidan sam mai gadi
bai lura ba sai da Amrah ta fita daga gidan kafin mai gadi
Yaga alamu kamar giftawar inuwar mutum da sauri ya daina
rawar tare da leka kansa bakin get ta waje sai dai bai ga
komai ba, babu alamar wani a wajen kofar ya rufe ya koma
mazauninsa tare da cigaba da sauraron wakarshi yana kada
kai.
****
Bakin get din Amrah ta tunkara, cikin jarumta da rashin
tsoro, Amrah ta riga ta kuduri aniyar barin gidan kota halin
kaka musamman da ta san yau karyar ta ta kare, asirin ta yau
ya tonu ga daukacin mazauna gidan Ahmad, Cikin sauri ta
dunfari get din zuciyarta cike da rashin tsoro, ta riga ta
shirya duk abinda zai faru ya faru wajen barin ta gidan.
Cikin ikon Allah babu kowa a bakin get din mamaki sosai
ta yi tare da murnar hakan, a fili ta furta Alhmdulillah,
Cikin sauri ta yi hanyar fita mai gadi kadai ta hango zaune
kan benci yana sauraron kida a wayarsa tare da kada kai
alamar wakar ta yi gaba da imanin sa.
katoton inyamuri ne kakkarfa mai cike da Rashin tsoro
fuskar sa daka gani zaka hango rashin imani a tare da shi,
Amrah ta kuma lekawa da kanta karo na biyu bakin get din
52
AKWAI KURA 2
ta kalla dan nemawa kanta mafita, get na rufe sai dai
karamae kofar shiga da fita a wangale tame Amrah ta yi
murmushi ganin hanyar fita a free lolz öYE.
A hankali ta koma ta labe jikin mota tana hangoshi, mai
gadi yana kada kai yana jin dadin wkaar daga karshe ma
mike wa ya yi ya bar wayar akan benchi ya fara taka rawa,
gabadaya ya shagala yana tikar rawa tare da bin wakar cikin
muryansa mara dadin Sauraro.
kamar kiftawar ido Amrah ta fice daga gidan sam mai gadi
bai lura ba sai da Amrah ta fita daga gidan kafiın mai gadi
Yaga alamu kamar giftawar inuwar mutum da sauri ya daina
rawar tare da leka kansa bakin get ta waje sai dai bai ga
komai ba, babu alamar wani a wajen kofar ya rufe ya koma
mazauninsa tare da cigaba da sauraron wakarshi yana kada
kai.
****
Wace haja kake magana kar dai kace min hajar dama ba
taka ba ce? To lallai in har hakane kace AKWAI KURA
Sharrin 'ya mace da yafi na shaidan ta rufta da kai, Ahmad
cikin firgici ya zabura tare da mikewa tsaye ban fahimce ka
ba? Fitar da ni daga duhu domin ina hada abu daya yana
bani dari.
Dan Chanji tuni hankalinsa ya yi bala'in-tashi shi ma cikin
Tsoro yake magana kashin mu-ya bushe ka cuce mu ka
gama damu, asirin mu da ke rufe tsawon shekaru yau ka
buda mun shiga 3, ya cigaba da magana cikin fada kai ne
mafita Ahmad kai ne Zaka warware matsalar cikin ruwan
sanyi, i knw kuna tare da ita yanzu please Ahmad Do
something i will gibe u anytin u want.
53
AKWAI KURA 2
Ida. yarinyar nan tabar gidan ka a raye mun kade har
ganyen mu, ni da kai har duk masu harka damu, Ahmad ya
katse shi dama wai ba yarinyar ka ba ce? No Ahmad Ina da
labarin hukuma sun wakilta mace kan bincike daga majiya
mai karfi, tun lokacin da na samu labarin na bada
kwangilar a kashe ta sai dai kash yara na sun gaza wajen
kawar da ita, a tare da haka kullum suna cikin farautar
rayuwarta.
idan kwakwalwar ka tana ja ba kwakwalwar kifi ce da kai ba
yanzu nasan ka gane lissafin, No Ahmad ya fada yana ihu
No, impossible, She is there i will kill her now now, Bai
saurari amsar da dan chanji zai bashi ba ya kashe wayar tare
da tunkarar kichin cikin zafin nama, sai dai wayam bata
kichin, cikin sauri ya haura sama dakinsa nan ma bata nan
bandaki ya bude ko tana ciki sai dai babu ko alamarta.
karkashin gado ya daga da niyyar daukar bindiga abun
mamaki babu ajiyar ta sa, Cikin zaro ido da damuwa Ahmad
ya dafe kai cikin sauri ya bude durowarsa wata bindigar ya
dauka, ya bar dakin tuni ya gaskata maganar da dan Chanji
ya fada masa akan Amrah, Da gudu ya bude dakin yaransa
bindiga ya harba sama da sauri a tare suka farka daga bacci,
cikin fada yake sanar dasu su fito Akwai damuwa.
****
Tun da Amrah ta samu nasarar fita daga gidan Ahmad da
gudu ta arce, ita kanta ba ta san in da ta nufa ba gaba jeji
baya jeji, A rikice take direct gabas ta nufa tare fatan dacewa
da alkharin dake gabas din, Sosai ta samu balance wajen
gudu kasancewar tun da tazo gidan Ahmad bata da sutura sai
54
AKWAI KURA 2
riga da wando kamar yadda Ahmad din ya fita ya sayo mata,
a cewar sa shigar yake so ya rinka ganinta da shi.
Sai dai abinda bai sani ba dama can ita gwana ce wajen
dress na kananan kaya gashi yau shigar tai mata rana, in zani
ne ko skirt ba ta san ta yaya zata fara gudun ba, kamar daga
sama taji alamun ana biyo bayan ta dan rage gudun ta yi tare
da juyowa bayanta dan ta tabbatar da hakan aiko da sauri ta
kara kaimi wajeb gudun, daga can nesa ta hango alamun ana
biyota a bata.
Gata can Oga daya daga cikin yaransa ya fada Ahmad
cikin karaji yace dasu ku kara gudu Kai Mai malfa in ta
kama ku harbe ta babu matsala, gabadayan su har Ahmad
suka kara kaimin gudu tare da son su cimma ta, Amrah gudu
take falfalawa bata san in da take sanya kafarta-ba-ko kadan
bata damuwa da kaya da take soke tafin kafarta ba wanda
tuni kafar ta ta fara zubar da jini kasancewar jikin ta bai saba
shan wuya ba, sai dai ko a jikinta illa ma kara kaimin gudun
da take burinta daya shine tai misu fintinkau sai dai ina da
alamu sun kusa cinmata.
Abin ka da mace da kuma wahalar gudu da Amrah bata sa
ba ba kafar ta ce ta- fara sarkewa tare da numfashi mai
wahala, tsananin kishin ruwa da gajiya sune suka hadar mata
lokaci daya, A hankali ta fara rage gudun ta fara rage karfin
gudun tari ne ya fara turnike ta Amrah ta rike ciki tana
matsawa kafin kace kwabo t. fara kelaya amai, yi takeyi
sosai babu kakkautawa.....
****
Da sallama Zahra ta ku tsa kanta falon Mommy dake
bayanta ita ma sallamar ta yi tare da bin bayan Zahra cikin
falon Ummy dake daune kan dinning table ita da Abban
55
AKWAI KURA 2
Amlah suna breakfast sai yan uku dake tsaye rataye da jaka
Zasu tafi skul, Ummy ta amsa sallamar fuskanta cike da
fara'a tare da fadin Bismillanku gaskiya kun iya sammako ta
fada cikin wasa, Mum ta yi dariya Alhmdulillah sai da
mukaci muka baro gida, kuyi hakuri mun doka muku
sammako ko breakfast ba ku yi ba mun dirar muku a gida.
Ummy ta yi dariya Wallahi ba komai ai samun bako da
wuya, bismillah ku zauna hajiya Ummy tace, bayan sun
dauna ido ta mayar kan yan uku Oya ku je direba yana jiran
ku. Kuje kada ku makara, Bye Ummy Bye Abba gabadaya
su ukun suka fada kafin suka Fice daga falon domin tafiya
skul.
Mommy da tun shigowarta falon ta yi arba da yaran, sosai
suka burge ta tare da bata sha'awa tabbas kamar su daya da
Abbansu, haka tana kallon matashiyar matar gidan anan taga
kama sosai ita da Amrah ko tantama babu ita ce mahaifiyar
Amrah.
Da sakin fuska Mommy ta gaida Abban Amlah, ya yin da
Ummy ta gaida Mommyn Zahra ce ta mike daga mazauninta,
Ita dawo kujera kusa da Ummy cikin sakalci ta gaida
Ummyn tare da tambayarta, Ummyn mu ina bestyna? yau
fada nazo muyi inji dalilin da yasa ta kashe wayarta ehee,
Ummy taji gabanta ya fadi amman sai mazeee Tare da
kirkiro murmushi tace Zahra ai kunfi kusa da Amrah sai dai
kinyi rashin dace Amrah din tana gurin aiki.
Mommy ta yi dariya tare da sanya musu baki AMRAH bata
gurin aiki wannan shi ne dalilin da yasa nazo takanas ta
kano, gida domin in duba ko lafiya? Saboda last tym, da
bata zo aiki ba ta sanar da ni bata da lafiya, shiyasa yanzu
56
AKWAI KURA 2
da naga ta yi 10 days bata doba na yanke shawarar biyo ta gida inji lafiya?
gabadayan su suka kalli Mommy daga Zahra har Ummy shi
kanshi Abban Amlah da ya kasa tashi akan dinning, tun
shigowar su ya ji gaban sa ya fadi shiyasa bai tashi ya bar
falon ba haka kawai yake jin faduwar gaba na zuwan bakin
musamman daya gansu da sassafe.
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un !! Ummy ta-fada tare da
dafe kirji na shiga Uku, Kuka ta fashe da karfinta Dama
zuciyata bata yarda Amrah tana cikin lafiya ba wayyo ni na
shiga uku na kasa rike amanar marainiya, da gudu ta yi
wajen dinning Abban Amlah daya gama jin komai cikin
tashin hankali ya riketa Amma sai ta fusge sakeni ka fada
min inda ka kaimun 'yata?
Wallahi tallahi Amrah ta rasa ranta kan wannan banzaan
aikin naka Sai nayi shari'a Dakai, Wayyo na shiga uku ta
fada tare da kwalla kara luuu ta yanke jiki ta fadi.....
****
"Subhanallah, Mommy ta fada tare da rike Ummy data
suma, Ihu Zahra tasa tare da fashewa da kuka mai tsuma
zuciya shi ko-Abban Amlah girgiza Ummy yake kamar
mahaukaci da alamar baya cikin hayyacinsa, kiran sunan ta
yake da karfi Zainab karki mun hakan ki taimakeni ki
saurareni Zainab banyi hakan dan in cutar da Gudan jinin ki
ba.
Ni ma ai nasan dadin yara kuma nasan zalunci haramun ne
a musulumci Zainab koda zan cutar da wani to wallahi ke
bazan miki ba, please ki-saurare ni in miki-bayani nasan zaki
fahimta ki saurare ni Ummyn yan uku ta fada tare da kara
jijjigata sai dai Ummy ta yi nisa ba ta san meke faruwa ba.
57
AKWAI KURA 2
Da sauri Mom ta saki Ummy tare da bude firinji ta dauko
ruwa bakin goran ta bude duka tare da watsawa Ummy duka
a jikinta, sai dai Ummy bata farka ba ganin hakan Zahra ta
kuma fashewa da kuka.
Da gudu Zahra ta yi waje tana ihu, wayyo Allah kuzo ku
taimakemu, Saleem da tun dadu yake jin kamar alamae
hayaniya a gidan da sauri ya bude murfin mota ya fito da
sauri shima Maheer ya rufa masa baya, da gudu suka shiga
falon shigar su ya yi dai dai da bude idon Ummy a zabure ta
mike cikin second daya ta tuno da meke faruwa aiko da
gudu ta kuma tunkarar Abbban Amlah tana ihu ka fito min
da yata, Wallahi tallahi Usman ka salwantar mun da ran
Amrah sai na kashe duka yaranka sai nayi shari'a da kai har
kotun koli wayyo na shiga uku.....
*****
Mommy ta yi tari Ummy tana Rarrashin ta sai dai Ummy
ina bata san in da hankalin ta yake ba saboda damuwa, sosai
ta cigaba da kuka iya karfin ta.
Yi take tana fadar maganganu masu kaushi game da Abban
Amlah da alamar bata cikin hayyacinta, Maheer da Saleem
Kallon - kallo suke wa juna fuskar su cike da son karin
bayani, Ummy ko kuka take bata jin lallashi tare da cigaba
da aiba ta mijin nata a cikin surutun da take nan take
Gabadayan su suka fara daukan haske kan inda maganar ta
nufa, Amrah ta bata, Zahra ta fada da karfi, Wayyo na shiga
ukuna besty ina kika shiga? wayyo na banu sautin kukan ta
kara tare da faduwa akan kafet tana burgima.
Can kamar an tsikare ta ta mike da gudu ta karasa gaban
Maheer, hannun shi ta rike tana kuka baby In hakane muna
da alhaki ciki batan bestyna, ranar mune mu kazo har gida
58
AKWAI KURA 2
muka dauki Bestyna da niyyar zuwa shopping baby ranar
Abun ya faru ta fada tana kuka Baby help mie wayyo ni ina
dan saka kaina?"
Salecm ya zare Ido cikin tashin hankali yace ban fahimta
ba matar tawa ce ta bata sai kace Allura? Ban fahimce ku
ba? Maheer ya rike shi ganin yadda yake karkarwa yana
shirin fitina, Zahra ta kalleshi matar ka ta a ina? besty matar
Yaya Anas ce ta fada tare da kara sautin kukan ta, kamar
mutum mutumi Abban Amlah ya damo a falon saboda
tsananin tashin hankali ya rasa ta ina dai fara ya yin da
Zainab take kuka kamar data mutu.
Kamar walkiya Saleem ya yi tsalle ya dira a gaban-Abban
Amlah cikin fitina yake magana Ka fito min da matata ko in
harbe ka bindiga ya ciro tare da shako wuyan abban Amlah,
Maheer ya yi Tsalle ya rike hannun Saleem tare da kokarin
kwace bindigar a hannun shi, Amma ya kasa cikin bacin rai
Mommy ta saki Ummy, ji kake tas - tas ta/gaurawa Saleem
kyawawan mari hagu da dama, Saleem ya saki bindigar yana
kallon Mommy da sauri hawaye ya fara zarya a fuskar
Mommy Son baka da hankali ne ? yaushe ka zama haka?
****
Cikin fada Mommy take magana Son ashe baka da
hankali, da girman ka da wayonka kake abu sai kace jahili,
wannan uba ne ga Wacce kake ikirarin kana so in banda
rashin hankali irin naka maganar ai ta gida ce bata shafe ka
ba muda muka zo neman iri sai kuma mu bige da fada da
manya, Kayi na farko kayi na karshe karka kuma wannan
shirmen.
Ummy ta katse Mommy cikin kuka tare da fadin Hajiya
barshi ya masa rashin mutumci, barshi ya tuhumeshi domin
59
AKWAI KURA 2
yau ya tabbtar min shi ba mahaifin Amrah bane, nayi
imanin uba da yasan darajar haihuwa ba zai kai yarshi ga
halaka ba bare har rayuwarta ta salwanta, to bari kaji a
wannan lokacin ba dan taba daga maka kafa ba Usman
wallahi tallahi duk inda diyata take kayi gaggawar fito min
da ita kafin muje ga hukuma, kuma ina mai tabbatar maka
da cewa duk wani matsala da ya samu Amrah, ba dan barka
ba sai kotu ta karbar mata hakkinta.
Abban Amlah ya katse ta cikin fada Zainabu ni kike fadawa
wannan magangunan ? kin fara shaye shaye ne nine fa
Mijinki uban yayanki, aiko dan darajar yayan dake tsakanin
mu, zaki saurari uzurina wallahi tallahi koni mugune bazan
cutar da Amrah ba koba komai taci darajarki da muke
daman aure harda karuwar ya ya a tsakaninmu dake.
Ummy ta cigaba da kuka tana fyace majina a baya ka
yaudareni da kalamai irin wannan har nayi sakacin yarda da
kai amma fa kasani a wannan lokacin dai dai nake da inyi
sharia da kai har kotun koli akan diyata, inda alkhairin kake
nema mai ya hana ka sanya taka diyar? Sai tawa ce bata da
gata saboda ka ganta marainiya?
*****
To wallahi tun kafin duniya ta jimu ka fito min da diya ta
domin nasan kasan in da Amrah take bisa ga hujjar da kai ka
sanar da ni, wannan karon Abban Amlah bai kara maganaba
sai ido da yake bin Ummy tare da ajiya zuciya na bacin rai
Mamaki tabashi sosai na yadda ta todarta shi a gaban baki,
Sosai Ranshi ya baci na rashin bashi damar kare kanshi da
Ummy ta yi.
Saleem tun da Mom ta yi magana ran shi ya kara baci bai
sake cewa komai ba daga karshe kamar kububuwa fuuu ya
60
AKWAI KURA 2
fita dada falon, Direct mota ya fada yana sauke mumfashi,
Maheer da sauri ya bi bayan Saleem zuciyar sa cike da
damuwar wannan badakala, Salcem yana ganin Maheer ya
fashe da kuka mai cike da tausayi, tare da fadin No wonder
ashe mata ta tana cikin hadari shi yasa Allah ya sanar da ni
ta hanyar mafarki, Abokina wake son ganin bayana da mata
ta?
Tabbas hakuri na ya kare zan iya jure a taba raina sai dai
har abada ba dan daga kafa Ga wanda ya taba iyalina ba;
Oya tada mota muje Koma waye yau Ya tada *KURA* nayi
imani saina buleshi da kasa Mace ko Namiji, Oya Muje ya
fadawa Maheer cikin fada, tamkar Maheer din shi ke da
alhakin laifin.
****
Jin karar tashin mota ya sanya Mummy fitowa da sauri
Mommy ta fito daga falon ga mamakin ta Motar Saleem ita
ce ta futa daga get din, Mom- ta yi-ajiyar zuciya tare da
tausayin danta, Ko bata tambaya ba tasan Saleem na cikin
tashin hamkali.
Tana sa ne ta zage shi tass a gaban mutane dan kaunar da
take ma danta baza ta iya ganin-ya baci ta kau da kai ba, ita
din uwa ce ta gari mai son yayan ta da basu kulawa still
kaunar bata rufe mata ido da data ga hani kan barna ta yi
shiru ba, uwa uba Abun da ta yin shi zai kare kimar ta a gun
Iyayen Amrah, wannan ya nuna Saleem na da tarbiya bacin
rai ya sanya ya aikata abunda ya yi a gidan.
Ita kanta Mommyn tana cikin damuwa na rashin sanin
ainahin inda Amrah take, sosai take cikin dimuwa tun da Ta
farga da Abunda yafaru da Amrah wayar ta ta dauko a jaka
61
AKWAI KURA 2
ta kira Numbern daya daga cikin direban gidansu tare da
masa kwatancen inda zai zo ya dauke ta.
A hankali ta juya cikin gidan dan tai musu sallama, Koda
ta koma falon Ummy bata daina kuka ba hakan Zahra shima
maigidan yana tsaye ki kam kamar Nonon Maza lolz, inda
ta barsu hakan ta kuma tarar dasu, Mommy ta yi gyaran
murya cikin nutsuwa ta fara yiwa Ummy nasiha kan ta
kwantar da hankalin ta, su bi komai a hankali ta wannan
hanya shine zasu Fahimci juna har a kai ga Cimma burin
ganin Amrah.
Haka shima Abban Amlah nasihar tai masa tare da bashi
hakuri kan abinda ya faru, kuma tana bashi shawarar su
zauna su fahimci juna fitinar ba ita ce zata fito musu da
Amrah ba, Daga karshe tai musu sallama tare da alkawarin
itama da danta zasuyi iyakar kokarin su wajen neman
Amrah.
*****
Cikin kuka har da majina ta shigo gidan, da gudu ta fada
dakinta tana kara sautin kukanta, Granny dake zuba zobo a
jarka da sauri ta mike lafiya Zahra'u? Waye ya mutu ta fada
tana zare ido, Zahra ta cigaba da kukan ta tana Ihu kamar
wadda uwarta da ubanta suka mutu.
Granny data gaji da lallashi kan meke faruwa har ranta ya
fara baci, cikin kufula tace kya yi ki bari a koke Ke ni
fitamin a daki kin isheni da ihu tun da bazaki fada min
abinda ya faru ba sai kace gidan mutuwa, Yo inma mutuwar
akayi ai kya sanar da ni, Ni nan da kika ganni tun ina
tsumman goyo Ubana ya mutu haka mijina da yarinta ya bar
duniya, ga Amaduna Ina sonshi mutuwa ta dauke shi,
Mutuwa ai mu mun jima muna ganinta.
62
AKWAI KURA 2
Zahra ta harari Granny tare da share hawaye, Granny ke
mutum ma na cikin damu wa bazaki rarrashe shi ba sai fada,
To naji kin saba ganin mutuwa Amman ai baki taba ganin na
Bestyna ba, Granny ta ajiye jarkar zobon kaji ja'irar yarinya
yau kuma da fatan tsiya kika zo ? Maza zoki fice min daga
daki tun kafin in man gareki, Yo aiko mutuwar ba zata
rabani da Zainabu na yanzu ba sai naga yaya da jikokinta,
Zahra ta kuma fashewa da kuka jin anyi maganar Bestyn ta,
cikin kuka ta sanar da granny abunda ya faru.
Iya ta dafe kirju tana salati Inna lillahi wa inna ilaihirrajiun !.
Tuni ta fashe da kururuwa tana kuka, ya yinda Zahra ke ta
ya ta kukan itama cikin ihu, Usmanu ashe sharrin daya kulla
kenan Abunda Usmanu zai min kenan, Wayyo Ahmadu
Usmanu ya ci amana Allah ya isar mana Allah ka tona
asirinsa Zahra'u, Tashi muje ki rakani barikin sojoji yan
sanda sunyi kadan wajen matse Usmanu ya fito mun da
jikata, maza tashi muje-Yau mai-raba ni da Usmanu sai
Allah.
kai duniya ina zaki damu, ashe makashinka yana tare dakai
Wayyo Yar marainiyar Allah, Allah ya isar mana....
*****
Saleem Da Maheer suna fita daga gidan Ummy, Saleem ya
kira wayar