Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
6 / 10
sauran yan falon suka mike suna tambayar shi ba'asi sai dai da gudu ya bar falon ba tare daya basu amsa ba cikin sauri ya ja mota yabar gidan da mugun gudu na fitar hankali... **** 78 AKWAI KURA 2 Ahmad ya kalli bindigar hannun Amrah, tuni ya gano ta cikin lokaci kankani ya fashe da dariya Tabbas harsashı Biyu tak ya rage a cikin bindigar Lokacin daya ajıye ta, Cikin dariyar mugunta yake tafa hannu Tare da furta ta yaro kyau take bata karkо. Bismillah harba mana harbeni ya fada tare da tunkarar inda take gadan - gadan, Amrah cikin fushi ta daga bindigar tare da saita Kafarshi tas ta saki kunamar bindigar, saı dai me? Ko alamar harsashi bai fita a cikin bindigar ba Tuni ta gane abinda yake shirin faruwa da ita, Ba ta tsaya wata wata ba ta danna da gudu tana kwalla ihun neman taimako. Da sauri sauran yaran suka yi yunkurin rufa mata baya, cikin fada Ahmad ya fara magana ku dakata ! Cikin fushi ya kallesu wa kuka taba gani rike da bindiga yabi mai gudu Empty hannu rabbana? Turus suka tsaya-suna-ajiyan-zuciya, Ahmad cikin bacin rai ya daga bindiga tare da sai ta Amrah cikin second daya ya aake mata kunamar bindigar a kafa, Innalillahi wa inna ilaihirrajiun ta fada tare kwala ihu ta fadi a wajen..... **** "Ku dauko ta," Ahmad ya fada yana Karkada bindiga a hannunsa, da sauri Suka tunkare ta Amrah da take rike da kafarta tuni jini ya wanke mata wando cikin adabar zafin harbi ta fashe da kuka cikin kuka, take magana koda kun kasheni na san kuma ba daku tsira ba, Hyegu ya yan mayu Hyegu makamashin wutar jahannama duk wanda ya tabani saina kashe shi, Dariya suka fara Hajiya ai taki ta kare da wani Ikon daki kashe mu Hhhhhhhh hajiya bari mu fara aikawa dake can in yaso in munzo sai ki dau mataki Mai malfa ya fada tare da kokarin daukarta, Amrah cikin karfin 79 AKWAI KURA 2 hali take dukan su da hannunta tare da kai cizo da yakushi, Ahmad ya daka musu tsawo tafi karfin kune dan ubanku cikin fushi ya karaso gurin kamar faki ya daga Amrah da hannu daya Tare da gaurawa fuskar ta Mari, dan uwarki yau kin tabo ajalinki an fada miki ni din kanwar lasane ? Yau dan nuna miki illar cin amana, Betl ya zare a jikinshi ya fara lafta mata Tare da kai mata duka hannu da kafa, Amrah da zuciyar ta ta bushe kukan ma ta kasa Illah kokarin neman hanyar tsira da takeyi, Ahmad ya cigaba da dukanta yana ball da ita Tare da danna mata duk kalar dagin daya zo bakinsa, Amrah ta galabaita sosai daf take da sumewa saboda Adaba tun da uwarta ta haifeta babu wanda ya taba mata wulakancin da Ahmad yai mata, Ahmad kaca kaca ya mata da riga cikin numfar farshi mai dafi-yake magana Yau dan kasheki bayan na gama dake Badan kashe kiba sai na kashe sha'awata akanki na tsawon kwanaki. Da ido ya yiwa yaran nuni da sauri suka bar gurin Illa Amrah da shi a gurin, Dakata Amrah ta fada masa tana kallonshi da idonta cikin galabaita Ya yinda Jini yake fita cikin bakinta da hanci Koda dan mutu badan taba yarda da raina ka ketamin haddi ba sai dai bayan ka kasheni ka cinma burinka, Ahmad cikin dafin rai ya tunkarota da niyyar keta mada haddi Amrah ta cije lebba tana jiran ikon Allah da dukkan karfinta ta danki kasa a hannunta Kafin Ahmd ya ankara ta watsa masa kasar duka cikin kwayar idonshi Ahmd ya yi taga taga dai fadi tare da kwalla karan adaba Amrah cikin karfin hali ta Dauki bindigarshi cikin dafin nama Da gudu sauran yaran hudu suka karaso wajen, Amrah ta nuna su da bindiga Ku ware ko in aika daku lahira ta fada da karfin wahala. 80 AKWAI KURA 2 Da baya da baya suka fara ja ya yinda Ahmad ke yashe a kasa yana ihun adaba acikin idonshi, cikin azaba da kafar ke mata Amrah ta fara taka kafarta da dingishi take tafiya da baya ya yin da bindiga ke hannunta tana jiran ko ta kwana, sa ida ta yi nisa kafin ta ran ta ana kare. **** Gudu yake sosai a mota kamar zai tashi sama, tafiyar minti 6 ta kawo shi Office da sauri ya fito daga motar ba tare da ya tsaya rufe murfin motar ba, Saleem ne-cikin tashin hankali ya danna kai Office din da sauri ma'aikatan suka mike Moming Sir, Saleem bai amsa ba illah wayarshi da ya ciro cikin Sauri ya furta Jabir Oya sauri it is an Emergency tracking. Wanda ya kira da Jabir cikin sauri shima ya fara danna Kayan aiki cikin kware Saleem cikin tashin Hankali yafara karanto Number waya da sauri Jabir ya fara zabarin nema cikin minti kadan yace yes Oga tare da juya masa kan tare da fadin Oga suna wajen *KADUNA* cikin Kauyen *TURUNKU* tare da juya masa kan computer cikin sauri Saleem ya maida hankali tare da kalla Ohh my God ya furta Cikin damuwa, Jibrin sauri ku fito da mota ka hada yara gani nan fitowa ya fada yana kallon jibrin, da sauri wanda aka kira da jibrin ya kame yes Oga tare da futa a cikin office din. Jabeer ka hanzarta bani son shirme cikin aikin nan rayuwar Matata yana cikin hatsari-Kayi mada kacigaba da Bibiyarsuzan dauki hanyar Turunku yanzu kabturomin da inda location din yake ta waya, Bai jira amsar shi ba ya fita daga cikin Office din da sauri. 81 AKWAI KURA 2 Motoci Biyar ya taras a jere da CONBOY dinsa kowa rike da bindiga suna jiran Fitowarsa da sauri Saleem ya fada mota cikin sauri yaj a ya fita ya yin da sauran Motocin syka rufa masa baya..... ***** Saleem yana fita daga gidan Ummy ta fashe da kuka da gudu tabi bayan shi tana kwala masa kira saidai Kafin ta isa gareshi Saleem yaja mota ya bar gidan, da sauri ta dawo Falon Tana kuka shikenan hala an ga gawar Amrah? Ga dukkan Alamu waya mai tashin hankali ya amsa, Cikin bakin ciki gami da kishi tare da jin zafin Saleem wanda daman da shi yazo a cikin ranshi Anas ya fara fada Saboda Allah ya fita ya barmu wage da baki bamu san dalilin fitarshi ba. Ai hakan zalinci ne ya dace ya sanar damu kafin ya fita, Granny ta kurma ihu tana salati na shiga uku Meke faruwa da Zainabu Granny ta fada tana Tsiyayar hawaye, Kar dai ace Zainabu ta mutu! da sauri Hajiya Mariya uwar gidan Abban Uku Tas higa rarrashin su tare da dubar da wahayen tausayi, Cikin rarrashi take magana Ummyn Uku kukan ya isa dan kukan a barshi hakan kuka baya magani, yanzu kam addu'a ita yakamace mu duka ba kuka ba Da yardar Allah Amrah za a sameta cikin koshin lafiya. Abban Anas shima hakurin yake basu tare da adduar samun Amrah a duk inda take, bai yi kasa a guiwa ba Ya roki Ummy alfarmar a bada Belin Zahra domin ita din macece Ba mutumci bane ace tana hannun hukuma ba, Ummy cikin kuka ta daga kai alamar da'ayi wani abu akai, Sallama ya yiwa Ummy da granny kafin ya umarci Mamah da Anas su same shi a mota su wuce gida. 82 **** AKWAI KURA 2 Cikin daka tsawa Ahmad yace musu ku bita ku tabbtar kun kamota, bani bukatar ta a rayc a mace nake son ganinta dan ubanku in har ta kufce mana ba ni kadai ba garemu duka kashin mu ya bushe, da sauri ukun suka juya Dan cika umurnin Ahmad sai dai cikin Zafin nama Mai malfa ya jawo biyu da karfi Dan mai cin uwarku a haka zamu kare Yarinya kamar Aljana ta yi ta aikawa damu barzahu Ah ah mun san darajar ran mu Oga Sai dai Ayi tafiyar tare Ya fada yana Zare ido, Ahmad Zaune rike da Ido ya kasa budewa, saboda kasar dake cikin Idanunsa cikin bacin rai ya bude idon duk da adabar da ya ke ji cikin idanu, Yana kallon mai malfa Kai harka isa in yi musu umurni ka hana Dan durun uwarka? Naga kanka na rawa kayi hankali da ni yanzu zan fasa kanka da bindiga. Ah Ah Oga mai malfa ya fada yana juya baki bafa zai sa buba wai bindiga a ruwa, wannan yarinya na jima ina ⚫ zargin ko Aljanace ban tabbtsar da hakan ba sai yau Oga ka duba ka gani yanda hyrgiyar yarinya Ta tura *Jan tsiya** barzahu shi ma Na Male yana kwance cikin jini ya kamata ace mun an kare Oga in ba so muke ta kaimu lahira bamu shirya ba, Ckin dafin nama Ahmad ya fauce Bindigar hannun mai malfa Baiyi wata wata ba ya nuna shi da bindiga Kafin ta gama daku ni bari in ga karshen ku Matsiyata masu butulci ya fada tare da kokarin harbawa. No oga ai ba'ayi haka ba Mai malfar ya fada tare da daga hannu alamar neman afuwa Allah ya huci duciyar Oga yandu za'a cika umurninka Afwa Me Gida, Ahmad ya yi murmushi ta gefen baki let's Go ya fada tare da nuna musu 83 AKWAI KURA 2 hanya da gudu suka rufawa Amrah baya dan cika umurnin Oga. **** Gudu Saleem yake Conboy dinsa a jere a bayansa suna take masa, tun da ya dauki hanyar zuwa turunku yake kiran number da Amrah ta kirashi, sai dai wayar tana shiga amma ba'a dagawa tuni hankalin shi ya kara tashi zuciyarshi bakin cikine fal, Sako ne ya shigo wayar ta cikin sauri ya dan rage gudu tare da budewa sakon Jabir ne ya shigo cikin Second biyu ya gane inda yake nufi domin yagane Location din Aiki yataba kaisu wajen shida Oganshi. Saleem zuciyarshi ta harba Tuni ya ji wata Sabuwar *JARUMTA*: yana shigarshi, Murmushin gefen baki ya yi tare da kudurawa a ranshi koma waye ya kama matarshi, tofa kashin sa ya bushe mace ne ko namiji, Ya riga ya yi Alkawari koda Mijin uwarta ne Sai ya dauki mataki ba dai ya fema duk wanda ya yi kidnapping matar shi ba. Kirmmr wayarshi ya yi kara ido ya kai kan wayar Ko Amrah ne sai dai kiran da ofishin yan sanda ne kan Malaman asibiti da security da ake bincike kan mutuwar yan ta:adda biyu da suka mutu, Saleem bai daga ba ya cigaba da sharara gudu burinshi ya kaiga Amrah, a karo na hudu kiran ya kuma shigowa wayarshi cikin jin haushi Saleem ya daga wayar tare da danna handsfree, Allah yataimaki Oga Dan sanda mai alhaki da kula da su ya fada, cikin Haushi Saleem yace yayane ?Oga labari mai dadi Ans amu mai laifin kuma abun dadi mun samu wasu sirri a gurinshi wanda baka sanda suba shiyasa nayi gaggawan kiranka dan in maka Albishir. 84 AKWAI KURA 2 Saleem ya tabe baki tare da dakuwa wayar ta kare Owkhey zan kira anjima yandu ina da uduri, bai jira amsar dan sandan ba Salcem ya kashe wayarshi, dan sanda ya rike waya baki sake yana mamakin Salcem Ikon Allah wannna wani uzurine yafi wannnan ? kai masu kudin nan Wulakanci ya musu yawa mtswwwwweecee yaja tsaki tare da fadin Dan kana da kudi ne zan bika in samu rabona da uwarka zanci lolz...... **** Daga can nesa nesa suka hangota tana takawa da kyar jini na duba a kafarta, Cikin bacin rai mai malfa ya tsaya tare da Umartar sauran ku tsaya cikin Fada, Oga ya raina mana hankali Wato mune ran mu bashi da Amfani sai na shi, ta yaya damu tunkari wanda bindiga ke hannunshi muko hannu rabbana? ina ba dai yiwu ba Ni kam nasare Babu inda dani In ku Zaku je Bismillah 'Ya 'yan mahaukaciya. Gabadayan su suka Daga kai Maganar ka Dutse Oga mai malfa Madallah da ka ankarar damu, Oga kawai muyi daman mu anan anjima mu koma muce ta ware koya ? mai malfa Jinjina kai Alamar-gamsuwa Tare da neman wajen dama tabar wiwi ya kunna ya cigaba da zuka tuni suma yaran suka nemi gurin dama tare da busa wiwi. Cikin sa'a Amrah ta tsere Jiri ne ya fara daukar ta gami datsananin gajiya ga dafin ciwo da kafar ke mata musamman data ta kashi saboda gudun ceton rai, a gajiye Amrah taja tunga ta tsaya Cikin adabar Ciwo ta kwanta a wajen Tananumfashi tare da adduar samun mai taimakonta, Jan ciki ta yi ta koma gefe kasan wata bishiyar Kashu ta boye tana Numfashi sama sama, a hankali baccin gajiya da adaba ya fara daukarta. 85 AKWAI KURA 2 Tafiyar Awa daya tak ya kawosu Inda Suke hasashe ya yin da Waya ke makale a kunnen Saleem Jabir na Sanar da shi sunje wajen cikin sauri Saleem ya faka mota tare da Ciro bindiga cikin Aljihunshi Suma conboy dinsa d asauri suka faka motocinsu Suka rufawa ogan su baya. ****** Kamar a mafarki Amrah taji karar tashin bindiga cikin firgici ta farka daga baccin wahala, ido bude Sosai tana mamakin mafarkin ta, Ikon Allah Mafarki da Oga J. Tabbas shi din ta gani a mafarki yana yana kwala mata kira tare da fadin gashi yazo, Amrah ta tabe baki tana Share siririn hawayen daya dubo akan fuskarta. A karo na farko da taji tausayin kanta tun faruwar abun, ta ja Tsaki kamar banda hankali in rasa taimakon wanda dan nema sai makiyi na? Me yasa ban kira Anas ba bayan ina da numberb shi a kaina? Baki ta tabe tana jin haushin kanta data kira shi gashi bai amfane ta da komai ba. Yawwa dai dai nan Jabir ya fada ah ah koma baya kadan jeka jeka kadan ya fada yana Kallon computer, Saleem yana manne da wayarsa a kunne yana bin umarnin jabir tsaya nan Oga da sauri Saleem ya tsaya *Yes* wayar tana nan Jabir ya fada. Cikin Sauri Saleem ya fara raba ido Yana duba wajen kirjinsa ya dafe sakamakon ganin jini a wajen sai waya dake ya she a gurin cikin sauri ya daga wayar bai yi wata wata ba Ya bude murya yana baiwa yaranshi umarni ku kuyi nan kuma kuyi nan Kaso uku ya musu cikin sauri duka suka bi umarnin shi, da sauri Saleem yace da sauran ku biyoni ya yin da ya dauki daya hanyar yana faman kwalaws Amrah kira Amrah! Amrah !! Amrah !!! 86 AKWAI KURA 2 ***** Da sauri Amrah ta juya bayan ta, Tabbas ba mafarki take ba sunanta taji ana kira, cikin hanzari ta dauki bindiga Tare da tsayawa jiran kota kwana. Amrah, Amrah, ya cigaba da fada tare da shiga dajin, Daya daga cikin yaran nashi yace da Saleem Oga kalli Jini a hanyar nan Alamu sun nuna Akwai wani abu nan, cikin sauri Saleem ya maida hankali kan jinin dake Wajen dumm gabanshi ya fadi Sakamakon arba da ya yi jinin Malale akan ciyawa, Cikin Tashin hankali yace da yaran muje. Da karfi Saleem ya cigaba da kwala mata kira tare da tunkarar wajen fa suka ga jinin, Amrah jin ana ta maimaita kiran sunan ta, cikin cije labba ta yunkura ta mike a hankali take taka kafar tare da rintse ido sakamakon tsami data fara shiyasa zafin da take ji ya karu. A hankali Amrah ta fara daukan muryar shi Cikin mamaki ta kalli inda take jin Kiran daga nesa ta hangoshi cikin Shigar shi mai kyau tare da daukar hankali, take Taji sanyi ya ziyarci cikin duciyarta ba ta yi wata wata ba ta daga murya da karfi sakamakon ganin sun dauki hanyar daba nan take ba, *Oga J*Oga I* Ta fada tana nishi cikin saa iska ya kai muryar kunnen Saleem da sauri ya juyo da kansa bangaren da ya ji Muryar. Washhh Amrah ta fada cikin kara, sakamakon kaya data karce mata kafa, da sauri Saleem ya daga kafa dan isa ga Amrah, haka sauran yaran da tare dasu cikin gudu suka rufa masa baya, Saleem yaja tunga cikin masifa yace da yaran shi ku dakata turus suka tsaya duka ukun suna kallon shi. 87 AKWAI KURA 2 Cikin Tsawa yake magana I say ku juya ko ? Matar tawa za ku gani babu sutura ? Ashe bansan dabbobi nake tare dasu ba? ya fada yana daga murya zuciyarshi cike da kishi, sakamakon tun daga nesa ya hango Nonuwan Amrah a bude saboda ya ga rigarta da Ahmd ya yi. Cikin bin umarnin shi conboy na shi suka juya baya Saleem da sauri ya daga kafa dan karasawa gare ta, Amrah ta daga kai ta kalleshi ido ta runtse sosai taji dadin ganinshi cikin Jarumta ta kuma taka kafar dan ta iskoshi, a tsakiya suka hadu da sauri Saleem ya riketa idonsa akan kafarta Cikin radana yake kallon jinin dake ke duba daga bakinta da hancinta duk a farfashe kamar ta yi fada da zaki. a Saleem bai san lokacin da ya rungume ba, jiya ke kamar mafarki wai Amrah ke cikin halin rai ko mutuwa, bai san time da ya fashe da kuka ba zuciyarsa cike da tausayinta, Abun mamaki Edactly ganin daya mata a mafarki cikin wahala hakan ya ganta a zahiri Saleem ya kuma kankameta a kirjinshi Yana kuka mai shiga rai tare da furta mata I miss yhu *JARUMАТА*. Baki Amrah ta saki tana kallon shi tare da mamakin kalmar daya fada mata imagine, duk da tana cikin ciwo sai da taji shock daya rungumeta Tuni wani shaukin da batasan dalili ba ya diyarci zuciyarta, cikin karfin hali ta fara kokarin tureshi a jikinta, cikin muryan wahala ta furta kafata. Saleem ya sake ta a hankali tare da daga ta kan kafarshi a hankali, bai tsaya bata lokaciba ya cire rigar jikinsa da saurі ya mikawa Amrah ido cikin ido-suka kalli juna Saleem ya.daga mata kai alaman tasa, Amrah da sauri tafara sanya rigar sakamakon an kara data yi jikinta babu riga. 88 AKWAI KURA2 Rigar sosai ya mata kyau a jikinta duk da tana cikin halin wahala Amrah ta sunkuyar da kai tare da kallonshi Saleem Sanye da wandon Aiki sai farar singlet a jikinshi cikin adabar ciwo ta furta Tnz *Oga J* Cak Saleem ya dauke ta a kafada cikin handari yake Yake umurtar yaran da suyi wajen mota, BINDIGA ya ciro ya harba sama Take sauran yaran da suke-daji suka gane meke nufi cikin sauri suka tasa Mai malfa da yaranshi da suka kama a gaba dan zuwa jikin mota, Abun mamaki sai ga daya tawagar dauke da gawa biyu sai Ahmd dake turjewa suna tankada keyarshi, Cikin Sauri Saleem ya bude bayan motarshi a hankali ya shinfida Amrah cikin sauri ya fada motarshi bai jira kowa ba yaja motar ya yi gaba da bala'in gudu. ***** Sosai yake gudu dan son cimma in da zashi, zuciyarshi cike da bakin cikin abinda ya samu Amrah, bai san lokacin da yace Matata ita ce aka yi kidnapping lallai kun taro match koma waye sai na fasa kan shi da bindiga, Amrah dake kwance bayan mota tana ihun wahala duk maganganun da Saleem yake fada tana jinsa, Cikin-jin-haushin-sa a zuciyarta-tace wato bama tani yake ba ta matar shi yake, batasan lokacin da ta ta. karkare da karfi ta sanya ihu ba. Wayyo kafata dan mutu, wayyo Ummy, Ki yafe min Granny, ki gafarta min mutuwa danyi, Cikin tsoron furucin Amrah Saleem ya dawo hayyacin shi kar dai ace da gaske Yarinyar nan mala'ikan mutuwa take gani ? No ya fada a fili sai dai mutuwar ta daukemu tare, i know ba dan iya rayuwa babu ke ba, Amrah ta galla masa harara Tana turo baki ni ka cika ni da surutun matarka wayyo kafata. Saleem ya dan ya rage gudu tare da juyowa ya kalleta Sorry Madam kina bukatar taimakon gaggawa ga likita, please ki 89 AKWAI KURA 2 daure muje akan lokaci bamu da time, Amrah ba tace komai ba ta cigaba da ihun ta tana fadin data mutu. Saleem cikin Dafin nama ya figi motar da gudu sosai kukan Amrah yake taba duciyarshi sai dai ya damo dole suje asibiti akan lokaci dan ya san matsalar harbi mai dubar da jini, tuni motar Saleem ta yi fintin kau wa sauran yaran na shi saboda tsabar gudun da yake yi, tafiyar Awa daya Saleem ya yi ta a cikin minti 43, direct Asibiti ya wuce da Amrah.. **** A guje ya shigar da motar cikin asibitin bai jira nurse ba da sauri ya bude mota Cikin dafin nama ya dauko Amrah cak daga motar da karfi yake kwala kira ina doctors pld sabe my wief life, cikin hanzari Nursse suka rufa masa baya da abun daukar marasa lafiya amma Saleem bai saurare su ba fadi yake ina doctor? Daya daga cikin nurses din tace yallabai akwai likita abcikin Emergency da gudu Saleem ya yi hanyar Emergency kasancewar ya san asibitin sosai. Da kafa ya tokarile kofar dakin bai jira neman izini ba ya fada dakin, cikin damuwa yake magana doctor sabe her a beg, She is my lyf, she is my eberything, cikin sauri doctor Murja ta karbi Amrah kasancewar ta kawar Mommy ta san Saleem ba sanin shanu ba, Ba ta yi wata watabba Ta fara ceto rayuwar Amrah, Daya daga cikin likitocin tace da Saleem yallabai Kadan jira a waje kaga dakin akwai matan mutane da ake dubasu. Saleem ya danna mata kallon uku saura kwata cikin bacin rai yaja tsaki in asibitin na ubanki ne sai ki kore ni babu wanda ya isa ya fidda ni daga dakin nan sai naga lafiyar matata. Saleem ya cigaba da masifa maras mutunci wanda bata san aikin taba daman akwai mata a dakin? Yaja dogon tsaki Mtsewwww Amrah kadai ita ce mace duk kallon mada nake 90 AKWAI KURA 2 muku, Ido sauran Doctors suka sa babu halin magana domin sun san waye uban Saleem a Najeriya gabadaya ita ma wacce ta yi maganar wata kila bata san dan gidan waye ba shiyasa ta yi maganar. Amrah ta kwalla ihun azaba saboda an fara cire mata builet din da take cikin kafarta, Saleem cikin fada yake maganar Doctor kiyi mata a hankali Ihate dubar-hayenta Doctor ta yi murmushi to controller ayi min afuwa..... ***** Ihu sosai Amrah take na wahalar cire mata bullet, saboda ko ina ciwo yake mata sakamakon dukan da Ahmad yai mata, Wayyo a kawo min Ummyna Wayyo zan mutu take fada tana ihu, abun mamaki da dariya ya bawa sauran matan dakin maras lafiya Sai dai babu halin dariya. Saleem yana tsaye yana lallabata-karfi da ya ji yaki fita daga dakin, Doctor ta maida hankalin ta kan Aikinta cikin kwarewa take komai Ya yin da Amrah tsabar kuka har muryar ta ta dashe ajiyar zuciy kawai take saboda wahala. Shi ko Saleem yana tsayea kanta yana ta rarrashin ta sai dai lokacin da Doctor ta fara-kokarin cire wa-Amrah riga,- dan-ta yi mata treatment din inda taji ciwo a jikinta Amrah kuka tasa sosai tana fadin Saleem ya fita, har cikin Zuciyarshi yake jin kukan nata ba dan yana so ba yace is Owkhey Matar Saleem barin fita doctor minti uku kacal dan dawo, -Amrah ta-daka masa harara tana turo baki cikin masifa tace ubanwa ya bawa Saleem ni? Maimakon ya ji haushi amma sai ya yi murmushi wanda har dimple din shi ya fito cikin rada yaje Saitinkunnenra ya furta mata *UBANA** ne ya bani Amrah. Bai jira amsar da zata ba shi ba ya fita daga dakin tare da jaddawa Doctor minti uku kacal dai dawo, Amrah ta bishi da 91 AKWAI KURA 2 kallon mamaki bata ce komai ba ta cigaba da share hawayen wahala. Cikin sauri doctor ta sanyawa dakin key ba ta yi jinkiri ba fara aikin ta dan ta san tun da yabfurta dai dawo tabbaa zai aikata, Cikin lokaci kankani ta gama gyara mata duk inda Ahmad ya ji mata ciwon, Doctor Murja ta yiwa Amrah Allurar bacci tare da rage dafin ciwo, Amrah iyayen tsoron Allura tana gani ta fara zare ido tana girgida kai, please doctor naji sauki wallahi bana so, Doctor ta yi dariya yi hakuri my Dota babdan miki da karfibba cikin lallashi da kyar Amrah ta yarda aka yi Allurar aiko Allurar na shiga jikinta ta kwalla ihu. Da gudu Saleem ya turo kofar sai dai ga mamakin shi, kofar tana rufe cikin jin haushi ya cigaba da buga kofar doctor ki bude ko in balla kofar, Amma doctor da yan dakin babu wanda ya bude sai dariya dansuke yi kasa kasa, cikin tausayin Amrah ya koma gefe ya tsaya zuciyarshi cike da kaunarta. **** Zare Allurar a jkinta keda wuya Amrah ta fara lumshe ido alamar bacci, tuni bacci mai-nauyi ya dauketa Doctor ta gyara mata kwanciya tare da rufe mata jikinta da bluen mayafi na asibiti saboda ciwukan da suke jikinta suna bukatar shan iska, Biyu daga cikin Nurse din ta kalla Ku tura ta zuwa special room number 7, Owkhey Mah suka fada a tare, Gadon maras lafiya da Amrah ke kwance suka nufa. Da sauri Doctor ta bude musu kofa Cikin sauri suka fita daga dakin, Saleem dake tsaye Yana jiran Tsammani da gudu ya bi bayansu cikin tashin hankali ya rike gadon tare da zare ido, а rude, cikin harshen turanci yake tambayar Nurse din meya faru? Daya daga cikinsu tace da shi Normal Sir she gonna b atryt in shaa Allah, dakin hutu za'a kai ta, Saleem ya sauke ajiyar zuciya mai karfi ba karamin tsorata ya yi ba da yaga 92 AKWAI KURA 2 Amrah kwance rufe da dani ya zata mutuwa tati dan bema kula taka numfashi baby. Cikin mutuwar jiki ya rufawa nurses din baya zuwa special room, ya buga kotar daya daga cikin ma'aikatan asibitin ce ta bude kofar tare da basu wuri su wuce da maras lafiyar, Saleem ya dakatar da nurse ya hanyar daga hannu cikin sauri ya shige dakin tare da kare masa kallo ga mamakin shi-kamshi ne mai dadi kamar ba asibiti ba ya fara musu sallama, cikin gamsuwa da kyan dakin ya yi umarni ga nurse din su shigo, dakansa ya daga Amrah kan gadon ya shimfide ta a madaidaicin gadon kwantar da mara lafiyar da ya gani a dakin, sosai Salcem ya burge nurse din ganin yadda yake nunawa-matarshi-kulawa, Daya Daga ciki har ta kasa boye maitar ta cikin Iya yi tace Yallabai MATARKA taji dadi Irin wannan kulawa haka kodayake ai daman ku turawa anyi muku shaidar haka. Mtsweeee Saleem yaja tsaki kala-bai ce dasu ba hankalinsa yana kan Amrah, Idanun shi ya bude sosai yana kałlon baiwar kyau da Allah ya bata ga gashinta kwance har gadon bayanta, cikin tsananin kaunarta ya gyara mata kwanciya, a hankali nutsuwa take shiga-jikinsa-take-ya-fara nazarin-yakamata-ya da Iyayenta halin da ake ciki duba da

Chapter 6 of 10