Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
9 / 9
harbosu sannan suka ji an yi 108 harafi Tafiyar ajali Magana da wata irin murya mai tsananin amo da karsashi muryar ta ce dasu "Hallaka zata tabbata a gareku don daukar fansa akan ku bisa abin da ku ka aikata na hallaka tsohuwa Zaʼazuma tare da wasu daga cikin jama'ar da suke tafe tare da ita a cikin wannan tsibiri domin kai ziyara wajen ibadarmu mai daraja. Dattijo Zarkiyu ya maida raddi ga mai maganar da cewa "Babu wani daga cikin ba'arin la'antattun jama'ar Aljanu da ya isa wanzar da hallaka gare mu har sai wanda ya haliccemu Allah ubangiji ya kaddara wanuwar hakan a garemu, kuma ba mu kasance daga cikin jama'ar da za a sanyawa razani da ambaton kalamai na wanzar da hallaka a gare sub a, idan kuma kana inkari abin da na Ambato to ka bayyana gare mu yanzu ka zamo daga cikin jama'ar da rayyukansu suka taba wanzuwa a doron kasa sukashude babu su. Muryar nan ta sake cewa da shi "Kaiconka da abin da ka ke ambatawa kuma ba zakat aba zamamai rinjaye da samun nasara akaina ba tunda har lalacewar zamani areka a kai ga kasancewar mutum bil'adama ya zamo abokin tafiyarka cikin wannan tsibiri tur da irin wannan hali naka abin kaskantarwa a cikin jama'ar aljan irin ka, kuma zan bayyana garekadomin wanzar da hallaka a kanka da bil'adama da kake tafe tare da shi". Muryar tan agama fadar wannanmaganar sai suka ga wani bakin ifirtu ya bayyana gare su cikin siffar irin ta gogggon biri ma'abocin girma da tsaye 109 Tafiyar ajali yadda muzaffar yake ganinsa tamkar wani katon tsauni mai girma a gabansa, idannunsa ja jawur kamar garwashin wuta, hannunsa rike da wani al'amudi bakin karfe idan yay i karaji kounji sai ka ji dajin gaba daya ya amsa kuwa da wani irin rugugi tamkar faduwar aradu bayan da ya bayyana gare su sai ya daga al'amudin bakin karfe da yake hannunsa ya tunkare su afusace yana wani irin gunji kasar wajen ta rinka girgiza kuma duk inda ya taka da duga-dugansa sai ka ga wajen yay i ramina tukun sahunsa kamar bakin riijiya. Kafin ya karaso gare su, Zarkiyu ya daga takobin say a tare si suka yi arangama da haduwa irin ta zaratan maridan aljanu,, masu ji da kansu a fagen jarumta da sadaukataka,makamansu suka hadu da juna karar faduwarsu ta sanya Muzaffar sai da ya toshe kunnuwasa saboda tsanannin kara da yaji kamar kansa zai fashe, wani farin hayaki ya tashi sama daga jikin makaman nasu suka sake zubura, suka kaiwa juna bara nan fa artabu da bakin gumurzu mai tsananin ya rincabe a tsakaninsu, suka shiga dauki ba dadi da arangama irinta zaratan jarumi aljanu, idan ifiritun nan ya kaiwa Zarkiyu bugu da al'amudun dake hannunsa, Zarkiyu ya goce duk abin da ala'amudun ya sauka a kansa sai ka gay a ragargaje koda kuwa dutsen na daga cikin duwatsun da suke wajen. Suna cikin wannan kafsawa ne Allah ya bawa Zarkiyu sa'a ya kaftawa ifiritun nan sara da kaifin takobinsa a kafada, Ifiritun nan yay i wata irin kuwa kkk kkk harafi 110 Tafiyar ajali saboda azabar da ya ji na shigar saran da Zarkiyu yay i masa, sannan ya yunkura cikin fusatuwa ya kaiwa Zarkiyu wani bahagon duka da al'amudunsa da nufin yi masa bugu daya ya gama dashi, Zarkiyu yayi sauri ya goce al'amudun bais ame shiba, sannan sai ya sunkyar cikin azama da zafin namaya sari kafar .Ifiritun nan ta dama, Ifiritun ya sake yin karaji saboda musiba kafin yayi wani yunkuri ko ya maida martani Zarkiyu ya sake yunkura ya sauke kaifin takobinsa a kan dokin wuyansa, nan take ya raba kan Ifirtun da gangar jikinsa,jini yay i tsartuwa sama tare da wani farin abu mai yauki daga inda Zarkiyu ya sare kansa, gangar jikin Ifiritun ta fadi gefe kansa ya fada gaban Muzaffar dake tsaye a bayan Dattijo Zarkiyu. Daga nan wannan Ifiritu ya hallaka tasa ta kare baiko shuru ba. Da hallakar wannan Ifiritu sai suka ji wata irin kuwwa cikin wata kakkausar murya maikarfi sannan sai suka ji an ci gaba da sakar musu ruwan kibbau kamar yadda aka yi musu da farko. Nan fa suka siga karewa da makaman da suke hannunsu,, sannan sai dattaijo Zarkiyu ya zaro tasa kwari da bakar ya sanya kibiya ya harba a tsakanin wajen da suke ganin ana harbor musu kibiyoyin da kibiyar ta tafi tana ci da wuta akan iska sannan ta fada wajen da ake harbinsu da kibiya.gaba daya itatuwan da ciyayin da suke wajen suka kama da wata tsaunuka da duwatsu suka fashe, kura da bakin hayaki suka turnuke suka tashi sama lokaci guda. 111 Tafiyar ajali Bayan wani lokaci kurar talafa dattijo Zarkiyu da Muzaffar suka jishiru babu motsin komai bare a sake arbo kibiya garesu, nan take Zarkiyu ya tabbatar da cewa duk abin da yake wajen ya hallaka don haka ya maida kwari da baka tare da takobinsa sannan ya dubi Muzaffar y ace da shi. "Duk abinda yake wajen nan ya hallaka babu sauran wani abin cutarwa gare mu, daga nan ya umarce shi da cewa su bar wannan bakin kogin su ci gaba da tafiya. Muzaffar bai ce komai bay a bishi suka kama hanya suka ci gaba da tafiya a cikinw annan daji mai yawan tsaunuka da kwazazzabai. Can kuwa a birnin Ambar bayan da Najiranu ya tashi daga lambu da yaje wajen gimbiya ZUhuriya ya kama hanyar komawa gida da isarsa gidan mahaifinsa ya ganshi cikin bacin rai da alamun rashin samun nasara a tare da shi. Ya taho gare shi ya taryeshiyana mai tambayarsa abin da ya faru.najiranu ya kwashe labarin dukkanin da ya faru tsakaninsa da gimbiya Zuhuriya ya sanar da mahaifinsa, tare da shaidamasa cewa it ace take yin shigar yaki ta tare shi a daji a duk sanda ta ce dashi ya tafi zai hadu da wani jarumi a bayan gari ba wani jarumi bane da ban ba. Da jin wannan labari sai ran Waziri Hawaisu y abaci, zuciyarsa ta harzuka ya fusata da fushi mai tsanani, yayi mamakin faruwar wannan al'amari tare da bakin cikin rashin samun nasara akan dukkanin shirinsu na son su hallaka Sarki Sa'adulgamidi sarautar birnin AMbar ta dawo hannunsa, tunaninsa ya koma kan boka Musailamatu abin dogaronsaya yi nufin nemansa domin ya sanar da shi abin da yake farua, nan takeya 112 harafi Tafiyar ajali murdazoben nan nab akin karfe da yake hannunsa tare da ambaton sunana boka Musaila har sau uku. Ba a dauki lokaci mai tsawo ba sai sukaji wata irin iska mai karfi ta keto ta shigo cikin dakin da suke, iskarta taho ta tsaya a gaban waziri Hawaisu sannan sai wani farin haskeya keto daga cikinta daga cikin hasken sai ga boka Musailaya bayyana a gabansu, fuskarsa a turbine alamar shi mayanacikin bacin rai da bakin ciki. Waziri Hawaisu ya dube shi zai yi masa Magana kafn ya furtawani abu sai Boka Musaila ya dakatar da shi tare da daga masa hannu sannan yace da shi. Ina sane da abin da yasa ka yi kirana da dalilin nemana gareka nay i bincike cikin alkaluman tsafi da sihirina nag a dukkanin abin daya faru tsakaninka danka da Najiranu da gimbiya Zuhuriya, hakika mun aikata babban kuskure kukure mafi girma na rashin yin bincike akan wannan jarumi mu san wane ne shi, tun farko marra idan da mun yi sani da cewa gimbiya Zuhuriya ce take yin wannan shi ta fita bayan gari ba wani jarumi ba, hakika da mun dauki matakin samun nasara akan ta tun kafin lamarin ya kai ga taʼazzara garemu, sai dai a yanzu ma ba mu kasance masu gazawa ba cikin abin da muke muradin wanzar wa na mallakar Sarki 'adulgamidi sauratar birnin AMbar ta dawo hannunk, nayi rantsuwa da girman alkawarin da yake tsakanina da kai tare da rantsuwa da nufina na daukar fansa akan Sarki Sa'adulgamid sai mun cimma nasara akan shirinmu na mallakar Sarautar birnin Ambar kuma sai danka Najiranu ya auri gimbiya Zuhuriya duk da kasancewar wannan al'amari da ya faru tsakaninsu". Da ya gamawannan bayani sai Waziri Hawaisu ya dube shi y ace da shi, "Ban zamo mai nuna karaya ko 113 harafi Tafiyar ajali rashin aminta da abinda ka ambata ba,amma ina son ka sanar dani ta wacce hanya z aka wanzar da wannan al'amari har mu kai ga samun nasara akan Sarki sa'adulgamidi sarautar birnin AMbar ta dawo hannnunka". Boka Misailamatu ya bushe da dariya cikin wata irin kakkausar murya mara dadin sauraro sannan ya dubi Waziri Hawaisu y ace dashi "Wannan shi ne abin da yafi komai sauki cikin al'amarin aikin bokanci da sihirina zan tafi gareshi na sanar da shi cewa na amince da maganar auren danka Najiranu saboda ina kaunarsa idan sarki S'adul gamdi ya ji wanann bayani zai amince da maganar auren danka Najiranu da gimbiya Zuhuriya tunda ta amince tana begensa kamar yaddda ya sanar da kai, kuma zai neme ka akan maganar aure a tsakanin 'ya'yanku daga karshe. Ita kuwa Gimbiya Zuhuriya bayan na aikata hakan ga mahaifinta ita ma zan siffantu da irin surar sarki Sa'adul gamidi na sa ayi kiranta na sanar da ita cewa na bayar da aurenta ga danka Najiranu, idan ta ji wannan bayani ba zata yi musu ko jayayya da abin da n ace ba, kasancewarta mai matukar biyayya da bin umarnin mahaifinta, a kan dukkanin hukuncida ya yanke a kanta, kuma za ta yi hakurin zama tare da shi koda kuw ba ta kaunarsa, domin gudun bacin ran mahaifin ta da yin biyayya gareshi. Yana gama fadar wannan maganar sai ya daga izgar tsafin da take hannunsa ya soma karanta wadans dalasumai irin na aikin bokanci da sihiri nan take sai kamaninsa sukajirkita ya zuwa irin siffar gimbiya Zuhuria da irin kayan da ta sanya a wannan rana kamar yadda Najiranu ya ganta, yay i murmushi irin yadda take yi 114 harafi Tafiyar ajali sannan yay i Magana da irin muryarta ba tare da wani banbanci ba, daga nan sai ya sake jirkita ya koma irin suturar Sarki Sa'adul gamidi cikin shiga irin ta sarauta da rawani akansa tamkar yadda ya zo fada a wannan rana, kamar yadda Waziri Haaisu ya ganshi, yay i gyaran murya kamar yadda Sarki Sa'adul gamidi yakeyi sannan yayi Magana da irin muryarsa ba tare da wani bambanci ba, ba don a gaban Waziri Hawaisu da dansa Najiranu ya rikida ya zuwa wannan siffa ba, da kuwa ba za su tantance ba idan y ace shi ne Sarki Sa'adul gamidi. Bayan boka Musailamatu y agama rikida ya zuwa siffar gimbiya ZUhuriya da mahaifinta Sarki Sa'adul gamidi cikin alkaluuman sihirinsa, sai gashi ya sake daowawa siffarsa ta asali cikin shigar kayan bokanci daure da warki na fatar bakar kura a kugunsa ya dubi waziri Hawaisu ya fashe da dariya irinta mugunta da zalunci sannan ya tsahirta da dariya yace da shi "Wannan ta ce hanyar da zamu samu nasara akan Sarki Sa'adul gamidi da yarsa gimbiya Zuhuriya cikin aikin shirina, kuma zan aikata wannan al'amari ne cikin kwanaki uku don haka ku kasance masu saurare ku ga abin da zai wanzu cikin wannan kwanaki uku masu zuwa". Waziri Hawaisu da dansa Najranu suka cika da matukar murna da farin ciki saboda ganin abin da boka Musaila yace zai aikata domin su samu nasara akan Sarki Sa'adulgamidi,Waziri Hawaisu ya rungume Boka Musaila yanamai yi masa godiya cikin tsananin murna da farin ciki, daga nan sukayi sallama da shi y abaci cikin alkaluman sihirinsa ya kamahanyar komawa bukkarsa ta tsafi dake tsakiyar 115 Tafiyar ajali dajin da ke bayan birnin AMbar. Su kuma su Waziri Hawaisu da dansa suka kasance cikin saurare su ga abin da zai faru cikin kwanaki uku asu zuwa kamar yadda boka Musaila yashaida musu. ** Su kuwa su Muzaffar da dattijo Zarkiyu bayan da suka bar bakin wannan kogi suka ci gaba da tafiya, suka yi tafiya har ta tsawon kwanaki hudu daga nda suka baro bakin kogin ba tare da sun sakehaduwa da komai ba, Sallah da cin abinci ne kawai yake tsayar da su ko kuma idan dare yay i Muzaffar ya gaji su yada zano su kwana kafin gari yaw aye su ci gaba da tafiya. A rana ta biyar daga cikin ranakun tafiyarsu ne daidai lokacin sallar magriba suka iso bain wani katon tsauni ma'abocin girma da fadi daga kasan tsaunin akwai wata kofa da ta shiga da ta shiga cikinsa kamar kogon dutse, har zasu wuce wajen su ci gaba da tafiya ba tare da sun tsaya ba, sai suka hangi wani irin bakin hadari ya bullo daga bangaren mahudar rana, aka soma tsawa da walkiya tare da rugugin aradu mai tsananin karfi da ta gauraye dukkanin dajin baki daya, wata irin bakar guguwa da iska mai karfi suka taso lokaci guda suka soma kada rassan bishiyoyi da duk wasu itatuwa dake wajen karfin iskar tamkar zai dauki su Muzaffar ya tasii sama dasu baki daya. Da dattijo Zarkiyu ya ga haka ya dubi uzaffar y ace da shi "Bai kamata mu yada zango a wannan wajen mu kwana ba, saboda ganin wannan hadari da 116 harafi Tafiyar ajali ya taso dole zamu tsaya a wannan waje mu kwana don haka zamu shiga cikin wannan kogon tsauni mu kwanta a cikinsa kafin gari yaw aye mu ci gaba da tafiya, sai dai kafin mu shiga cikin wannan kogon dutsen zan gargadea da gargadi mafi tsauri da nake so ka ji kuma ka kiyaye da abin da zan sanar da kai, da farko kada ka sake ka yi mantuwa, kuskure kokuma bin son zuciyarka ka taba wani abu daga cikin abin da zamu rika a cikin wannan kogon dutse, sannan ka da ka sake ka aikata wani abu da ban umarceka da aikatawa ba, har mu fita daga cikinsa. Da Zarkiyu y agama yi mas awannan bayani ya sakemaimaita masahar sau uku Muzaffar yace da shi ya ji kuma zai kiyaye da abin da ya umarce shi daga nan suka kamahanya suka shga ckin wannankogon dutsen, kogo dutsen na da tsananin duhu yadda Muzaffar baya iya ganin kda tafin hannunsa bare abin da yake gabansa, suka dan yi tafiya har suka isa wani waje sannan dattijo Zarkiyu ya umarce shi da cewa su zauna a nan su kwana. Bayan sun gabatar da sallar magriba da isha'l Muzaffar ya kwanta bacci domin ya uce gajiyar dake tare da shi, kafin gari yaw aye su ci gaba da tafiya, can da kusan tsakiyar dare bayan Muzaffar ya dade yana barci sai ya ji ya farka daga barcin da yake tamkar wanda aka tashe shi, yana bude idanunsa ya ga cikin kogon dutsen ya gauraye da haske ba kamar lokacin da ya kwanta bacci cikin duhhu ba, ya tashi zaune da sauri sai ya ganshi cikin wata kasaitacciyar fada irin manyan sarakuna da suka shahara a fagen 117 harafi Tafiyar ajali tarin dukiya da karfin mulki,ko ina a jikin bango kogon dutsen an yi masa ado da jan hauhari tare da zane na tambarin gidan sarauta daga gabansa akwai wata kujerar sarautarta azurfa dake ajiye akan wata karaga,an jingina wata sandar sarauta ta zinari a jikin kujerar sarautar kuma akwai wasu takalma na fata da ka yi musu ado da gashin dawisu tare da wasu kananun duwatse na lu'lu'u masu sheik sannan gaba daya kasan wajen a lullube yake da wasu manyan dardumai da kilisai masu taushi har inda Muzaffar yak e zaune. Muzaffar ya cika da matukar mamakin wannan al'amari da yake gani tamkar mafarki a gareshi ya duba gefensa bai ga dattijo Zarkiyu ba ainda ya zauna kafin Muzaffar yay i bacci, don haka sai yayi tunanin ko ya fita waje ne daga cikin kogon dutse, zai je ya dawo, ya tashi daga inda yake zaune ya soma zagayawa a cikin wannan katafariyar fada da bait aba ganin fada mai matukar kyau da tsari irinta ba, nan take ya soma shagala da duban kayan ado da alatun dake cikin fadar ya rika zagayawa yana duban duk abin da ya burge shi har ya isa inda wannan kujera ta sarauta take, ya dubi sandar sarauta ta zinari dake jingine a jikin kujerar kyawunta ya kawatar da shi nan takeya sha'awaantu da son ya dauki sandar ya rike a hannunsa,yadda idan ya koma birninsu ata rana zai bada labarin cewa ya taba rike wata sandar sarauta mafi girmandaraja da bait aba ganin kamarta ba a fadin duniya. 118 harafi C Tafiyar ajali Yanagama annan tunani ya kai hannu zai dauki sandar, kafin ya taba jikinta sai ga dattijo Zarkiyu ya bayyana a gabansa,ya daka masa tsawa cikin madaukakiyarmurya mai karfi, har sai da Muzaffar ya razana, garin ya dauke hannunsa ya ture sandar daga inda takeajiye jingine a jikin kujera ta fadi kasa, da faduwar wannan sanda sai sukaji wata irin karamai tsananin karfi da ban firgici ta gauraye cikin kogon dutsen baki daya, wajen ya soma girgiiza da raurawa kasa ta soma tsagewa, duk abin da yake cikin fadar sai ya fara yin kasa zai nutse a cikin kasa, Muzaffar ya razana da ganin wannan al'amari,ya juya baya sai ya ga babu dattijo Zarkiyu, a wajen da ya bayyana ya bace ya barshi a cikin kogon dutsen yay i kiran sunansa har sau uku bai ji ya amsa ba, alamar ya fice daga kogon dutsen ya bar wajen, kasa ta ci gaba da girgiza tana tsagewa fadar na ci gaba da nutsewa a cikin kasa. Hankalin Muzaffarya kara tashi ya sake shiga halin razana da firgici ya kuma yi nadamar abin da ya aikata na zuwa ga wannan sandar sarauta zai dauketa a cikin halin shagaktuwa, baya ga cewa dattijo Zarkiyu ya haneshi da taba wani abu a cikinsa, ya kuma tuna gargadin da yayi masa a baya cewa idan ya sake aikata wani abu na kuskure da bai umarceshi da aiwatarwa ba, to kuwa karshen rabuarsa da shi ya zo zai tafi ya barshi a cikin wannan tsabiri na Hljusiya ya hallaka ba zai sake taiimaka mas aba. 119 harafi Tafiyar ajali Yana cikin wannan tunani da nadama ya sakejin wata kara mai tsanani karfi wadda ta fi adda ya ji da afarko sannan kasar wajen ta sake a cikin kasa ya rage sauran bangaren da Muzaffaryake tsaye sannan kasar ta cigaba da girgiza tana tsagewa ya zuwa wajen Muzaffaryake tsaye. Shin me zai faru gare shi? Ku yi min afuwa domin jin yadda za ta kasance mu hadu a cikin littafi AJALI KO RAYUWA a ci gaan TAFIYAR AJALI. 120 harafi An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9