kuma ya hadu da wasu jama'amatafiya
yayi tambaya a gare su koza a samu wanda ya san hanyar da
zai bi ya koma birninnsu da zai ci gaba da tafiya sai ya dauki
akushin abinci tare da wannan salkar ruwa dan yin guzuri da
su tunda abincin da ke ciki tare da ruwan basu kare ba, kuma
gas hi baai san inda zai sake samun wani abincin ba a cikin
wannan dajin.
Ya ci gaba da tafiya yana keta duhun itatuwa tsaunuka
da kwazazzabai a cikin wannan bakin daji ba tare daya hadu da
wata halitta dake da rai ba koda dabba bare ya ga mutum
bil'adama a cikin sa da rana ta yi zafi sosai Muzaffar ya sake jin
yunwa ya tsaya a bude akushin nan ya ci abinci ya koshi ba
42 harafi
ka
do
id
bi
y
y
k
k
こ
Tafiyar ajali
tare da abicin ya ragu ba, ya dauki salkar ruwan ya sha itama
kamar da farko ruwan da yake cikin salkar bai ragu ba bare
yayi tunanin zai kare.
Yayi godiya ga Allah sannan ya tashi ya ci gaba da
tafiya tare da wannan salkar ruwa da akushi da yak e ci yake
sha daga gare su. Ba taree da abinda yake ciki yak are ba.
Haka Muzaffar ya ci gaba da tafiya har tsawon kwanaki
uku ba tare da ya hadu da wata halitta da ke da rai ba koda
kuwa tsuntu dake shawagi a sararin samaniya ban da
kasusuwan gawarwakin mutane da suka dade da hallaka babu
abinda yake gani a duk inda ya wuce a cikin wannan daji, ya ci
gaba datafiya sallah da cin abinci ne kawai yake tsayar da shi,
amma bai ga alamar zai riski wani gari gabansa ba, a rana ta
hudu daga cikin ranakun tafiyarsa ne ya isa bakin wani kogon
dutse yana zuwa daidai wajen sai ya ga takun sahu tamkar
takun sahun mutum ya shiga cikin kgon dutsen ya bi wannan
sawu da ya gani ya shiga cikin kogon dutsen, ko zai yi sa'a ya
riski wani mutum bil'adam a cikinsa, da shigarsa cikin kogon
dutsen sai ya tadda wani farin dattijo tsoho tukuf da shi mai
alamun tarin shekaru da dadewa a duniya, zaune akan farin
buzu yana jan tasbaha Muzaffar yayi matukar mamaki da
ganin wannan dattijo dake zaune a cikin wannan kogon dutse
dake tsakiyar daji ba tare da wasu jama'a makusantan sa da
zasu taimaka mas aba, da ya sake dubansa sosai sai ya ga yayi
kama da tsohon nan da ya taba taimakawa ya kubutar da shi
daga hannun Damisa da ta tasarwa hallakashi wata rana a
bakin kogon dake birninsu, ba don a tsakiyar daji ya ga wannan
dattijo ba babu shakka da ya tabbatar da cewa shi ne ya taba
taimakawa a birninsu wata rana.
Bayan ya gamadubansa ya matsa kusada shi yayi masa
sallama. Dattajon ya dago kansa ya amsamasa sannan yay i
masanuni da wata shimfida dake kusa da shi y ace "Zauna"
Muzaffar ya bi umarnin dattijon ya zauna ba tare da
jayayya ba, tsohon nan bai sake yiwa Muzaffa Magana bay aа
43 harafi
Tafiyar ajali
kau da kai ga barin dubansa ya ci gaba dajan casbaharsayayi
addu'a ya shafa ya juyo ga Muzaffar y ace da shi.
"Yaro rayuwarka tana cikin hadari da musiba mara
misaltuwa kasancewarka a cikin wannan tsibiri na Hijusiya da
babu wani mutum bil'adama da ya isa shigowa cikinsa ya
kubuta ba tare da ya hallaka ba".
Muzaffar yayi matukar mamaki da jin maganar
wannan tsohon nan takeya maidamasa da cewa "IDan kuwa
har wannan daji ya kasance mai matukar hadari da musiba a
cikinsa yadda har babu wani bil'adam da zai iya shigowa
cikinsa ya fita ba tare da ya hallaka ba, to kuwa kai meen ya kawo ka cikinsa ka ke zaune ba tare da musibar ta halaka ba?
Kuma ka yi sani cewa duk abin da zai hallaka jarumi kama ta
kuwa zai hallaka dattijon mai tarin shekaru irinka ba batare da adadi ba"
Tsohon nan yayi shiru yana duban Muzaffar sannan ce
da shi "Kai dai ka kasance mutum mai Gadara da jarumta ta
kuruciya da take dibanka b aka san da cewa a cikin halittun da
ke raye a doron kasa akwai da yawa da suka fika tsananin
¡arumta da karfi ba, ka kasance mutum mai yawan tambaya da
rashin tsoro babu abin da z aka ga ni ka kauda kai baka yi
tambaya a kansa ba, ko kuma ka ce zaka je ka taba komai
hadarin da yake tare da shi, kuma ka kasance mutum mai
yawa shu'umanci da rashin nisantar abin da zai cutar da kai.
Wannan shi ne abin da ya jam aka kasancewar a cikin
wannan hali da ka riski rayuwarka acikin,da kana kiyaye
maganar mahaifinka da ya kasance mai yin naisha a gare ka da
hanaka aikata wannan dabi'a taka da baka kasance a cikin
wannan mummunan hali da ka tsinci kanka a ciki ba".
Muzaffar ya sake yin mamaki da jin kalaman wannan
lattijo cikinsari ya sake tambayarsa cewa "Ya aka yi ka san
abarina da abin da ya faru a gare ni amma kai ka kasance daga
ikin mutane ma'abota bincike na alkaluman tsafi da sihiri
,
44 harafi
Tafiyar ajali
wanda aikata hakan shirka ce da bata mabayyani Allah ya
tsare mu da aikatawa".
Dattijo nan y ace da shi "Ban zamo daga cikin
ma'abota bincike na alkaluman sihiri ba, sai dai ni na kasance
ba mutum bane bil'adama irinka kamaryadda ka ke zato,
kasancewar wannan daji da kake cikinsa ba zaka tabaganin
wani mutum bil'adama irinka kamar yadda kake zato,
kasancewar wannan daji da kake ctkinsa, ba z aka taba ganin
wani mutum bil'adama kamar ka a cikinsa ba, koda aljanu sai
wanda suke sadaukai suke iya shigowa wannan tsibiri su fit
aba tare da sun hallaka ba, duk wani bil'adama da kagani a
cikin wannan tsibiri ko kuwa an kawo shi ne don ya hallaka a
cikinsaa kamar yadda ake nufi da kawo ka wannan waje domin
ka halaka saboda wanda suka aikata hakan a gare ka sun
tabbatar da cewa ba zakat aba kubuta daga cikin wannan
tsbiri ka koma birninku ba, har sai ka hallaka, sai dai kada
wannan ya s aka razana ko ka zama mai raunini zuciya ni zan
taimakamakakakubuta daga rikin wannan tsibiri kamar yadda
ka taba taimaka ka kubutar da ni daga hannun Damisa, waa
rana matukar ka kiyaye abin da zan sanar da kai".
Muzaffar yayi shiru yana sauraron dattijon nan ya ci
gaba da cewa da shi.
Da farko dai suna MUBASSHIR BN SHARKIYU ni ne
tsohon da ka taba kubutar da ni daga hannun Damisa, wata
rana a bakin kogin dake birninku wand aba don taimakon daka
yi a gare nib a da kuwa na hallaka,saboda duk sanda na wanzu
cikin siffar mutane bil'adama bani da tasirin kubutar da kaina
daga dukkan abin cutarwa saboda tsufa da yawan shekaruna
har ssai na koma siffata ta aljani, ni ne na tsawatar maka ga
barin taba wannan batta da ka gani a tsakiyar daji ka tafi gare
ta da nufin dauka ka buxe don ganin abin da yakecikinta.idan
da ka bi umarnina ka kiyaye abin da na ambata a gare ka na
san cewa hallaka zata tabbata a garekada kuwa baka kasance
a cikin wannan hali da ka riskikanka a ciki ba, don kuwa wani
tsohon ifiritu ne dake hidima ga wani boka a cikin wannan
45 harafi
Tafiyar ajali
battar da ka gani kumashine ya daukoka ya kawo ka wannan tsibiri na Hujisiya don ka hallaka kamar yadda akenufi da
wanda aka kawo shi wannan waje, sabbin bude wannan batta
da ka yi, kuma an alkata hakan a gareka ne don kada ka auri Gimbiya Zuuriya 'yar Sarki Sa'adul gamidi da aka sanya ranar
aurenka da ita, wanda yasa aka aikata hakan gar shi ne waziri
Hawaisu don yana so dansa ya auri gimbiya ZUhuriya saboda
ya hallaka Sarki Sa'adulgamidi sarautar binin AMbar ta dawo
hannunsa".
Ya kwashe labarin dukkan abin da yake faruwa
tsakanin waziri Hawaisu da Boka Musailamatu na makircin da
suke shiryawa don su hallaka Sarki Sa'ad sarautar birnin
AMbar ta dawo hannunsu ya sanar da Muzaffar sannan ya ci
gaba da cewa.
"Ni ne na hallaka Ifiritun da ya taso gare ka da nufin
hallaka na jefe shi da hasken na addu'a yak one ba don haka
ba da kuwa ka hallaka ni na zuba maka ruwa ka farfad daga
suman da ka yi bayan da ka fadi kasa sakamakon karajin da
wannan ifiritu yay i lokacin hallakarsa,ni ne na kawo maka
akushi da salkar ruwwan da ka gani a usa da kai, a lokacin da
kake cikin halin suma,kuma kake ci kake sha, daga gare su har
Eya zuwa wannan lokaciwanda ba don sub a d akuwa yunwa da
kishirwa sun hallaka ka saboda babu inda z aka samu abinci ko
ruwa a cikin wannan tsibiri da kake ciki, yanzu haka
mahaifanka da sauran yan uwanka suna can suna nemanka a
brnin Ambar basu san inda kake ba,hankalinsu yayi matukar
tashi sosai saboda rashin sanin halin da kake ciki an tsinci
dokinkatare da takobinka ta yaki bayan gari amma ba a ga
koda sahunka ba, ko a san inda kake daga wannan tsibirin na
Hijusiya zuwa birnin Ambar tafiyar shekaru goma ce daidai ga
mutum bil'adam kamar ka, idan bai hadu da wani abin
cutarwa ya hallakashi ba, sai dai zan taimakamaka kakare
awannan tafiyar cikin sauri ka koma brninku a tsakanin kwanaki
¡kalilan idan ka kiyaye abin da zan sanar da kai.
46
Tafiyar ajali
"Da farko dai b azan iya daukarka na fitar da kai daga
wannan tsibiri ba, haka kuma babu wani mahaluki daga jinsin
aljani da zai iya daukarka ya fitar da kai daga wannan
tsibiri said an uwana Zarkiyu don haka zan tura ka gare
shi don ya taimaka makaya maida kai birninku, ka zauna
nan tare da ni har zuwa wayewar gari da safe zan
sanyaka a hanya da z aka tafi gare shi don ya maida kai
birninkи"
Da Muzaffar ya ji wannan bayani sai ya amince da
shawarar dattijo Mubasshir ya zauna tare da shi kamar
yadda ya aumarce shi.
**
Can kuwa a birnin AMbar baya wasu kwanaki da
samun labarin bacewar Muzaffar, sai waziri Hawaisu ya
shirya ya tafi wajen Boka musailamatu don sanar da shi
abin da yake faruwa yay i ta tafiya a cikin daji har ya iso
inda bukkar Boka Musailamatu take a cikin tsakiyar daji.
Da isarssa wajen ya sauka daga kan dokinsa ya
shiga cikin bukkar ya tadda Boka Musaila a zaune a gefe
kafin yay i Magana sai Boka Musaila y ace da shi
"Muna sane da dukkanin abin da yake faruwa da
kuma abin da ya kawo ka gare mu, hakika ka aikata abin
da muka umarceka har ma hadimin dake hidima ga
wannan batta ta aikin sihiri da nab aka.ya dauki wannan
Jarumi ya kaishi tsibirin Hujisiya ya yasar da shi a can ya
dawo gare mu".
Ya nuna masa attar nan ta aikin sihiri da ya bawa
Waziri Hawwaisu a jiya a geensaa ta dawo gare shi ba
tare da Waziri Hawaisu ya dawo da it aba, sannan ya ci
gaba da cewa.
"A duk sanda na tura hadimin dake hidima ga
wannan batta don aikata wani al'amari da zarar ya aikata
47 harafi
Tafiyar ajali
abin da aka umarce shi to kuwa zai dawo gare ni, sannan nay i sani da dukkanin abin da ya aikata"
Ya dauko izga da yakeamfani da ita wajen Surkullensa na aikin siiri ya tsoma ta a cikin ruwan kwatarniyar dake gabansa sannan ya cire ta ya yarfa ruwan a jikinsa farin dutse dake kusa da shi, nan take farin dutsen yay i haske kamar madubi daga jikin hasken sai ga Muzaffar ya bayyana a inda yake cikin tsibirin Hijusiya. A lokacin yana kwance a halin suma sanda tsananin yunwa da kishirwa suka ci karfinsa.
Boka Musaila ya dubi Waziri Hawaisu ya cce da shi "Wannan shi ne tsibirin Hijusiya inda aka kai wannan
arumi aka yasar da shi kuma anan zai hallaka ba zai taba
dawowa wannan birni ba, don babu wani mahaluki daga
insin mutane da ya taba shiga wannan tsibiri ya fit aba
tare da ya hallaka ba, ka yi duba ya zuwa inda yake
akwance z aka ga babu komai sai tarin kasusuwan
gwawarwakin mutane da suka dade da hallaka tun
Emanin mai tsawo kamar yadda shima zai hallaka a
vanzu, don haka shi an gama da lamarinsa ke nan tasa ta
kare".
Waziri Hawaisu yay i matukar murna da farin ciki
da jin wannan bayani sannan y ace da Boka Musailamatu
Godiya nake a gareka abin dogarona cikamakin bokaye
masana alkaluman tsafi da sihiri yanz me ya kamata mu
Bikata don ganin Sarki Sa'ad ya amince da auren dana
Najiranu da yarsa Gimbiya Zuhuriya tunda mun gama da
batun wannan jarumi".
Boka Musaila yayi dariya irin ta mugunta da
calunci sannan ya dubi Waziri hawaisu y ace da shi.
"Wannan shi yafi komai sauki a cikin lamarina zan
aka wata gora dake dauke da ruwan na aikin sihiri a
48 harafi
f
Tafiyar ajali
cikinta idan ka koma gida ka samu wani daga cikin bayi
ko hadimanka ka hallaka shi, ka jefar da gawar a wajen
da aka tsinci dokin wannan Jarumi a bayan gari, sannan
ka zubawa gawar ruwan dakeciki wannan gora da zan
baka, kamanni da siffarsa zasu zama irin na wannan
jarumi ba tare da banbanci ba, idan aka tsinci wannan
gawa za a yi zaton Muzaffar ne ya hallaka babu wanda zai
iya gane cewa bas hi bane daga cikin jama'ar birnin
saboda wannan aikin sihiri dake tare da gawar.
Idan yan uwansa suka daki wannan gawa suka
binne shi kenan an tabbatar da cewa Muzaffar ya hallaka,
maganar aurensa da gimbiya Zuhuriya yar Sarki Sa'ad ta
rushe kena, bayan wasu kwanaki sai ka sake komawa da
maganar neman auren danka da gimbiya ZUhuriya ga
Sarki Sa'ad tunda wannan jarumi ya hallaka, idan bah aka
muka aikata ba, ka san cewa Sarki sa'ad ba zai taba
amincewa da maganar aurar da yarsa ga danka Najiranu
ba duk da cewa Muzaffar ya bata komai yawan shekaru
da za a dauka ba za a ganshi ba, idan kuwa aka tabbatar
da labarn mutuwarsa shi kenan maganar aurensa da
gimbiya zuhuriya ya rushe."
Waziri Hawaisu ya sake cika da matukar farin ciki
da jin wannan bayani na Boka Musailamatu. Boka
Musaila ya kawo wannan gora y aba shi Waziri Huwaisu
ya karba yay i masa godiya sannan ya tashi ya kama
hanyar komawa gida.
Da isar Waziri Hawaisu gida ya kira dansa Najiranu
ya sanar da shi abin da yake faruwa da yadda suka yi da
Boka Musailamatu da abin da ya umarceshi da ya aikata
ya kawo wannan gora ya bawa Najiranu y ace da shi zai
hada shi da daya daga cikin hadimansa su tafi bayan gari
tare da shi, idan sun isa wajn da Ifiritun nan ya dauke
49 harafi
Tafiyar ajali
Muzafar ya tafi da shi aka tsinci dokinsa a wajen ya hallaka wannan hadimin ya jefar da gawar a wajen
sannan ya zuba masa ruwan dake cikin gorar sihirin amar yadda Boka Musaila ya umarce shi.
Najiranu ya karbi wannan gora da mahaifinsa ya
anso daga hannun Boka Musaila sannan Waziri Hawaisu
yay i kiran wani hadiminsa dake sharer wajen da ake
daure dawakai, ya kawo tufafi na alfamarma masu
matukar kyau da ya bashi, sannan y ace da si ya shirya da
yamma ya zo ya raka Najiranu kilisa bayan gari.Hadimin
nan yayi godiya sannan ya tashi ya tafi.
Da yamma ta yi dai-dai lokacin da Waziri Hawaisu
ya umarci Hadimin nan ya zo, sai gashi ya iso sanye da
kayan da Waziri Hawaisu ya bashi, ya tadda Najiranu у
agama shiri suna jiran isowarsa, ya kai gaisuwa gare shi
Waziri ya amsa masa sanan ya sa aka bashi doki yah au,
suka tafi tare da Najiranu suka kama hanyar bayan gari,
suka yi tafiya har suka isa wajen da aka tarar da dokin
Muzaffar bayan da wannan ifiritu dake cikin battar nan ta
aikin sihiri ya dauke shi.
Da isarsu wajen sai Najiranu ya ja linzamin
dokinsa ya tsaya shima wannann Hadimin yaja linzami
dokinsa ya tsaya. Nan take sai Najiranu ya zare takobin
daketare da shi cikin zama da zafin nama, ya kaiwa
Hadimin sara ya same shi a tirken dokin wuya hadimin
nan ya yi karaji da kururuwa mai tsananin karfi sabda
azaba, Najiranu ya sake kafta masa wani saran a kafada
jini yay i tsartuwa sama hadimin ya fadodaga kan dokin da yake kai ya soma shure shure d akakarin mutuwa da
haka har ransa ya fita ya hallaka, daga nan sai Najiranu ya sauko daga kan dokinsa ya bude bakin gorar da
mahaifinsa ya bashi ya juya ruwan dake cikin gorar akan
50 harafi
Tafiyar ajali
gawar wannan Hadimi nan take sai gawar ta soma rikida daga siffar wannan hadimi ya zuwa siffar
Muzaffar har ya zama tamkar gaawar Muzaffar baki
daya shi kansa Najiranu sai da yay i matukar mamaki
faruwar wannan al'amarin ba don shi ne ya zuba
masa ruwan gorar sihirin lamarin ya faru a gabansa
ba da kuwa ya gasgata cewa gawar Muzaffar ce baa
war hadimin da ya hallaka ba,saboda tsananin kama
da siffarsa ta yi da ta Muzafar.
Daga nan ya juya ya koma dokinsa yah au, ya
hada da dokin da Hadmin ya zo a kansa, ya nufi
hanyar komawa gida da isarsa gida ya sanar da
mahaifinsa dukkanin abin da ya faru da yadda
kamain wannan hadii sukarikida ya zuwa irin siffar
Muzaffar ba tare da wani banbanci ba.
Waziri Hawaisu ya cika da matukar murna da
farin ciki na samun cnasara akan dukkanin makircin
da suke shiryawa don ganin sarautar birnin AMbar ta
dawo hannunsa.daga nan suka zauna cikin saurare
su ji labarin cewa an tsinci gawar Muzaffar kamar
yadda Boka Musailamatu ya sanar dasu.
Bayan kwana daya da hallaka wannan Bawa
aka tsinci gawarsa a wajen da Najiranu ya hallakashi,
wani maharbi daga cikin jama'ar birnin ya zo da
labarin ganin gawar a bayan gari ya tafi fadar
Sa'adulgamidi ya sanar da shi abin da yake faruwa
nan take Sarki Sa'ad ya tura baradansa don su dauko
wannan gawar su kawo ta fadarsa don yin cigiya a
nemi dangin mamacin, baradan suka kama hanya
suka tafi suka isa inda wannan gawa take, da zuwasu
51 harafi
Tafiyar ajali
suka duba sai suka ga gawar Muzaffar ne duk wanda
ya sanshi idan ya ga wannan gawa sai ya tabbatar da
cewa shi ne, daga nan suka dauki gawar suka koma
adar Sarki Sa'ad suka sanar da shi abin da yake
aruwa.
Shi kansa Sarki Sa'adulgamidi da ya ga
wannan gawa sai da ya tabbatar da cewar Gawar
Muzaffar ce dan gidan liman Adnan da ya bashi yarsa
Simbiya Zuhuriya, kuma aka ce ya bace tsawon
wanaki masu yaw aba asan inda yake ba, don haka
hima ya shiga cikin jimami da bakin ciki ya kua tura
asanar da mahaifinsa Liman Adnan abin da yake
aruwa.
Kafin yan aike su isa gidan Liman Adnan su
anar da shi abin da yake faruwa tuni labarin tsintar
awar Muzaffar ya isacikin gidan Sarki Sa'ad har ya
ai ga kunnen Gimbiya ZUhuriya,da jin wannan
abara sai ta taso dagadakinta a firgice ta nufi fadar
nahaifinta cikin halin kidima da rudewa tana zuwa
a ga wannan gawa sai ta fashe da kuka irin na
akaici da bakin ciki saboda tsananin kaunar da take
iwa abin begenta Muzaffar, ta yi ta kukamai
sananin har akarasa wanda zai iya rarrashinta, Sarki
a'ad ya bada umarnin amaida ita cikin gida saboda
awan kukan da takewanda ya cikadukkanin fadar.
Da za a maida ita gidata sake duban wannan
awa da aka kawo fadar mahaifinta, sai ta ga babu
hakkaya yi matukar kama da masoyinta Muzaffar
mma sai ta ji zuciyarta na tare da shakku da rashin
adda akan cewa shi ne, ta duba hannunsa ba ta ga
52 harafi
Tafiyar ajali
zoben nan na azurfa da ta bashi ba, wanda a
kodayaushe yana tare da shi a duk inda yake baya
rabuwa da shi hakan ya kara saya wais-wasi da
shakka a cikin zuciyarta, har akafita da ita daga cikin
fadarakamaidaita gida bata gasgatacewa wannan
gawar masoyinta Muzaffarbace. Shi ma mahaifin
Muzaffar Liman adnan da ya samu labarin abin daya
faru na tsintar gawwar dansa da ya bace tsawon
kwanaki masu yaw aba a ganshi ba, ya kama hanya
ya isofadarSarki Sa'ad cikin jimami da bakin ciki
hallakar dansa, da zuwan say a dubi wannan gawa da
aka kawo fadar Sarki Sa'ad ya ga babu shakka yay i
matukar kama da dansa Muzaffar a kamanin na
siffarsa, amma kuma tsayinsabai kai tsayin dansa
Muzaffarba kuma akwai wani tabo na kuna wuta
atsakiyar tafin hannun dansa Muzaffar da yak one
tun yana karamin yaro ya duba bai ga tabon a jikin
wannan gawa ba, nan take sai ya shiga rudani da
rashin tabbas zuciyarsa ta kasa amincewa da cewa
wannan gawar dansa Muzaffarce,duk da tsananin
kama da suka yi da yake ya san bayyana maganar na
iya kawo rudani da rashin fahimta a tsakanin
jama'ar jama'ar birnin kasancewarsa babban
limamin gari, kuma hujjarsa ba zata zamakarbabbiya
abar gasgatawa ba, saboda ganin yada dukkanin
jama'a suka yadda cewa gawar dansa Muzaffar ce sai
ya hakura ya bar maganar a ransaya sa akadauki
wannan gawa aka kaita gidansa aka yi masajana'iza
aka binne gawar.
53 harafi
Tafiyar ajali
Duk abin da yake faruwa a fadar Sarki sa'add
Waziri Hawaisu yana fadar akayi komai a gabansa,
da ya ga dukkanin jama'a sun yadda da cewa garwa
Muzaffar ce aka kawo adar kuma mahaifin
MuzaffarLiman Adnan ya dauki gawar don yi masa jana'iza sai ya sake cika da matkar murna da farin
ciki ya kuma yadda cewa shi mai samun nasara ne
akan makircin da yake shiryawa don sarautar birnin
AMbar ta dawo hannunsa, kamar yadda Boka
Musailamatu ya tabbatar masa.
Labarin rasuwar Muzaffar ya gauraye ko ina
acikin birnin Ambar saboda shahara da yayi a fagen
Jarumta da bajinta,wadanda suka sanshi suka yi ta jimami da yay i masa addu'a babu wanda bai yadda
cewa Muzafffar ya rasu ba a duk daukacin birnin
AMbar ban da mahaifinsa Liman Adnan dakuma
Gimbiya Zuhuriya dake cikin halin shakka da rashin
yaddda sai dai babu wanda ya bayyana abin da yake
zuciyarsa suka bar maganar a ransu, mahaifinsa ya
mikalamarinsa ga ubagiji yana mai addu'ar Allah ya bayyana inda Muzaffar yakeya dawogare su,
matukar yana raye a doron kasa.
**
Shi kuwa Muzzaffarbayan da ya kwana daya
tare da wannan dattijo da ya tarar a cikin kogon dutse kamar yadda ya umarce shi,da gari yaw aye Muzaffar ya kammalashiri don ci gaba datafiya,dattijo Mubasshir ya dube shi ya ce da shi **
54 harafi
Tafiyar ajali
Shi kuwa Muzaffar bayan da ya kwana daya
tare dawannan Dattijoda ya tarar a cikin kogon dutse
kamar yaddaya umarce shi da gari yaw aye Muzaffar
ya kammalashiri don ci gaba da tafiya,dattijo
Mubasshir ya dube shi ya ce da shi.
"Zan sanyaka a hanya da zaka bi har ka riski
inda dan uwana Zarkiyu yake zaune a ckin wannan
daji,shi ne zai daukeka ya fitar da kai daga cikin
wannan tsibiri da kakeciki ya kaida kai
birninku,kuma zaku iyi wannan tafiya ne cikin
kwanaki ashirin da uku ku gamata baki daya,
kasancewarsa mafi sauri daga cikin jinsin aljanu da
suke shigowa cikin wannan tsibiri ko su fita daga
cikinsa, amma sai ka kiyaye da dukkanin abin da zai
sanar da kai ko kuma ya umarce ka da aikataawa
cikin tafiyar da za ku yi tare da shi, ka kasance mai
yin taka-tsantsan da lura cikin lamarisadon zarkiyu
yana da saurin fushi mafi girman Harzuka da
fusatuwa idan ka aikata abin da ransa zai baci babu
shakka zai tafi ya rabu da kai ka hallaka ba zai
taimakamaka ba,kuma idan ka yi kuskure ka rasa shi
ya tafi ya barka babu sauran wanda zai iya daukarka
ya fitar da kai daga cikin wannan tsibiri a cikin tafiyar
kwanaki ashirin da uku sai dai bayan wasu watanni
koma shekaru idan ka yi sa'a wani abin cutarwa bai
salwantar da ruhinka kahallaka ba, don haka ka yi
hattara kuma ka kiyaye gudun bacin ransa".
Da ya gamamasa wannan bayani ya daga
karkashin shimfidar buzun da yake zaune ya dauko
55 harafi
Tafiyar ajali
wata takobi tare da zobe na azurfa ya mika masa
sannan ya ci gaba da cewa da shi.
"Ka rike wannan zobe a tare da kai sai dai
Π kada ka sake ka sanyashi a danyatsanka, kuma kada
ka sake ka rabu da shi, komai rintsi da tsanani a duk
tinda kake haka itama wannan takobi tana da
Imatukar amani gareka cikin wannan tafiya da zaka yi 'kafin a maida kai birninku sai dai b aka da ikon
amfani da ita har sai an sanar da kai yadda za kayi
amfani da ita,don haka kada ka sake ka zareta daga
gidanta har sai an baka umarnin kayi amfani da ita,
sannan z aka ci gaba da tafiya wannan akushi da
salkar ruwa da kake ci kake sha daga gare su a
masayin guzuri, abincin da ruwan da yake cikinsu ba
zai taba karewa ba, har sai ranar da ka koma
birninku ko kuma idan ka yi kuskure zoben nan da na
bakaya bata daga gare k aka rasa shi.
Idan ka fita daga cikin wannan kogon dutse z
aka yi tafiya har ta tsawon kwanaki uku da yini daya
sannan ka isa inda dan uwana Zarkiyu yake saka
riske shi cikin wata bukka a tsakanin wasu manyan
tsaunuka da zaka tarar a gabanka, idan ka riske shi
ka yi masa sallama sannan ka mika masa zoben da
nab aka, da zarar ya karbi zoben ya rike a hannunsa
zai yi sani da cewa ni ne na turo kagareshi tare da
taimakon da zai yi maka ya maida kai birninku ba sai kayi masa Karin bayani ba, daa nan zai dawo maka
da zoben gare ka ya kuma sanar da kai shharudan da yake so ka kiyaye cikin tafiyar da zaku yi tare da shi
idan har kana so ya taimaka maka ka koma birninku,
56 harafi
Tafiyar ajali
kuma shi ne zai sanar da kai yadda za ka yi amfani a
wannan takobi da nab aka da irin amfanin ta gareka
idan ka bi umarninsa, don haka sai ka yi hattara
kuma ka kiyaye da abin da na sanar da kai".
Da ya kare bayaninsa Muzaffar yayi masa
godiya sannan dattijo Mubasshir ya raka shi har
bakin kofar fita daga kogon dutsen ya nuna masa
hanyar da zai bi don risker inda dan uwansa Zarkiyu
yake, daga nan suka yi sallamada bankwana
Muzaffar ya kama hanyar da akaumarceshiya bi,ya ci
gaba da tafiya yana