shi akansa,
nan takedutsen a fashe ya tarwatse ya zamakamar kasa kura ta turnuke ta
tashisama, ta sake fusata ta yunkura kansa tare da wata irin iska mai karfi ta
sure shi ta makashidakasa,itacen da yake hannunsa ya fadi gefe ta sanya
kafarta ta taka kafadarsa ta daga sandar ta za ta narka masa bugu a tsakiyar
kansa ta hallaka shi, Muzaffar yay i kokarin kwacewa daga gareta,ammay aji
ya kasa kodamotsi bare ya ture kafarta daga kansa,yana ganin sanda ta daga
sandar zata hallaka shi amma bashi da ikon gocewa sai dai ya rintse
idanunsa ya saduda yana jiran abin da zai wanzu gare shi, tare da nadamar
abin da ya aikata na mantawa da maganar da dattijo Zarkiyu ya umarce shi
da kiyayewa, nadama mara amfani gare shi a lokacin da takeshirin zuwa a
gareshi.
Kafin sandar ta sauka akansa Dattijo Zarkiyu dake kokarin kawo
masa dauki yay i sauri ya sanya kibiyar cikin azama da zafin namaya harbeta
a tsakiyar kirji,tsinin kibiyar ta huda kashin hakarkarinta ya fito a bayanta,
tsohuwar nan ta yi wata irin kadaitacciyar karamai tsananin karfi da ban
firgici sannan ta yi sama akan iska saboda karfin harbin kibiyarta tarwatse
sassan jikinta ya watsu a kasa yana ci da wuta nan take ta hallaka.
Da ganin abin da ya faru ga wannan tsohuwar sai ragowar ayarin
da suke tafe tare da ita sukayunkuro cikin karaji da gunji fusatuwa suka taso
kan Muzaffar da dattijo Zarkiyu da nufin hallaka su, kamar yadda suka
hallaka wannan tsohuwa Muzaffar yayi sauri ya tashi ya dauki makaminsa
tare da salkar ruwansa dake yashe a kasa ya daureta a damarar ya ja daga
cikin jarumta da karfin zuciya yana mai sauraron karasowar wannan jamaʼ'a
gare shi, shima dattijon zarkiyu ya zare takobinsa ya karaso kusa da Muzaffar
suka tari wadannan tawaga baki daya akasomakafsawa,nan takewaje ya
96 harafi
Tafiyar ajali
hargitse kura ta tunuke ta tokare sararin samaniya, Muzaffar na kai bugu da
fekakke itacen da yakehannunsa duk wanda ya samu koya soke shi da tsinin
itacen sai ka gay a wafcewani sashi daga jikinsakamar saran takobi ya
haklaka shi.
Shii kuwa Dattijo Zarkiyu saransu kawai yake yi da takobinsa cikin
tsananin kwarewa da jarumta duk wanda kaifin takobinsa ya sauka akansa
sai ka gayatsarge shi gida biyu kokuma ya sare wani sashi daga jinsa, ya
hallakashi duk inda yak eta tsakanin wadannan runduna sai dai ka ga
gawarwakinsu suna zuba kasa matattu tamkar busassshen ganyen bishiyar
da guguwa ta zubo da shi kasa.
Haka suka dauki lokaci mai tsawo suna gabza artabu dda bakin
gumurzu mai tsananin a tsakaninsu da wadan nan tawagar jama'ar
aljanu da suka juyo garesu, amma babu alamar zasu kare bare su sa
ran zasu sasmu nasara akansu saboda tsananin yawa tamka ba daga
cikinsu suke hallakawa ba.
Da dattijoZarkiyu ya ga haka sai ya maida takobinsa cikin
kubenta ya fiddo kwari da bakaya sanya kibiya ya harba tsakaninsu
kibiyar ta tafi kan iskatana ci da wuta ta tunkare su,su kuwa da
sukaga hakasai suka tarwatse sukaba ta waje ta wuce ta tafi ta samu
jikin wani katon tsauni dake kusa da wajen ta nutse a cikinsa,tsaunin
yay i wata irin kara mai sananin karfi da ta yi amsa kuwa da amo mai
hauhawa da ya gauraye dukkanin dajin sannan ya fashe kura da wani
irin bakin hayaki suka dunkule suka tashi sama kan iska nan take
wajen ya gauraye da duhu mafi tsaanin daga yankinduhu dare
sannan sai sukadaina jin hayaniya da hargowar tawagar da
suke kafsawa da su.
Bayan ani lokaci kurar da ta turnuke wajen ta lafa sais
u Muzaffar suka ga babu jama'ar aljanu da suke kafsawa da su
a wajen daga su har gawarwakin wadansa su Muzffar suka
hallaka, alamar sun bace daga wajen sun a da baya saboda
razanar da suka yi ta jin karar fashewar wannan tsauni, bayan
wani lokaci da bacewarsu su Muzaffar da Dattio Zarkiy u suna
tsaye a wannan waje basu sake jin motsin komaiba bare su ga
wani daga cikin jama'ar aljanun nan ya bayyana garesu,
alamar sun bar wajen don haka sai Zariyu ya maida kwari da
bakarsa ya juya ya dubi Muzaffar cikin hasala da fusatuwa у
ace da shi.
97 harafi
Tafiyar ajali
Kaicon wanda ya zama mai mantuwa da kauda kai ga
barin abinda aka umarceshi da kiyayewa kai dai ka kasance
daga cikin ma'abota shu'ummanci da wofintar da duk abin da
na umarceka da kiyayewasai da na haneka da yiwa wani
Magana ko kuma sauraron wani daga cikin wadannan jama'a
tun a farkon marra, saboda kasancewar ba jama'ar mutane
bane, kamar yadda kake zato, don babu wani mutum
bil'adama kamar ka da zai iya shiowa cikin wannan tsibiri ya
rayu batare da ya hallaka ba, amma sai ka zamo mai bijirewa
abin da na umarce k aka aikata abin da kake ra'ayi na daga
soye-soye zuciyarka, to ka sani cewa wannanshi ne laifi na
karshe da zan iya yi maka afuwa daga cikin laifukan da ka
aikata gare ni tunda muka fara wannantafiya tare da kai don
haka matukar ka kara aikata kuskure ka bijirewa abin da na
umarceka da aikatawa, to kuwa karshen tafiya tsakanina da
kai yazo zan rabu da kai a cikin wannan tsibiri ka hallaka bа
zan sake taimaka maka ba".
Muzaffar yayi shiru kansa a sunkuya bai ce komai
saboda kasancewarsa mai laifi na aikata abinda aka hanashi da
aikatawa, daga nan dattijo Zarkiyu ya juya ya kama hanya
Muzaffar ya bi bayansa suka ci gaba da tafiya a cikin wannan
tsibiri.
**
Shi kuwa Najiranu dan gidan Waziri Hawaisu tun bayan
ruwan nan na aikin sihiri da yayinufin zubawa Gimbiya
Zuhuriya ya kawo kansa ya zuba a jikinsaya fado daga kan
dokinsa,baisake sanin abin da yake faruwagareshi ba, har
Gimbiya Zuhuriya ta tafi ta bar shi a wanan waje tamkar
sumamme, sai da ya dauki lokaci mai tsawo can da kusan
faduwar rana sannan ya dawo hayyacinsa, ya dubi kansa ya ga
halin dayakeciki ya ganshi yashe a kasa gefe guda takobinsa da
kumagarkuwarsa suma gefe guda ga dokinsa tsaye a
gefe, sannan bai gajarumin da sukekafsawa da shi ba, gashi har
rana ta kusa faduwa alamar ya dade a wannan waje, nan take
ya fahimci abin da yakefaruwa gareshi na rashin samun sa'a
98 harafi
Tafiyar ajali
akan wannan jarumi, bakin cikida takaicimara misaltuwa ya
turnuke zuciyarsa ya tashi ya dauki takobi da garkuwarsa ya
tafi ya kama dokinsa yah au ya kama hanyar komawa gida.
Da isarsa ida ya tafi ga mahaifinsa Waziri Hawaisu ya
sanar da shi abin da ya faru a gare shin a rashin samun nasara
akan wannan jarumi karona biyu, mahaifinsa Waziri Hawaisu
yayi matukar bakin ciki da takaici na jin wannan labari, ya
sunkuyar dakansa kasa yayi shiru yana tunanin wani lokaci ya
dago kansa ya dubi dansa Najiranu y ace da shi.
"Haika mun yi rashin sa'a na kasa samun nasara akan
wannan jarumi sai dai ba zamu zama masu nuna gajiyawa ba
akan abin da muka sag aba har sai mun tabbatar da samun
nasara, don haka zan nemi boka Musaila na sanar da shi abin
da ya faru domin neman shawararsa akan wannan al'amari".
Yana gama wannan bayani sai ya ciro zoben nan na
sihiri da boka Musaila ya bashi, ya sanyashi a danyatsansa ya
urza zoben tare da ambaton sunan Boka Musaila sau uku ba
dadewa ba said akin da suke ciki yayi duhu mafi tsananin daga
yankin duhun dare yadda waziri Hawaisu da dansa Najiranu
bas a iy aganin junansu, bayan wani lokaci sai suka ji iska mai
karfi ta keto cikin dakin ta shigo daga nan kuma sai duhun da
ya gauraye dakin sai ga Boka Musaila ya bayyana a gabansu
zaune akan buzunsa na aikin sihiri tamkar yadda waziri
Hawaisu yake tarar da shi ad uk sanda yaje gare shi cikin
bbukkarsa dake tsakiyar daji.
Najiranu dake zaune kusa da mahaifinsa yay i matukar
mamakin wannan al'amari da yake gani a gabansa tamkar
mafarki,shi kuwa waziri Hawaisu da ya ga Boka Musaila ya
bayyana a gabansu sai ya kai Gaisuwa gare shi riin ta
girmamawa sannan ya ce da shi.
"Girma da martaba ya tabbata gareka yahamshakin
masani na alkaluman sihiri cikamakin bokaye da matsafa na
wannan karni, ka sani cewa na bukaceka ne domin neman
taimako a gareka kasancewarka ne abin dogaro a gareni cikin
wannan lamari.
99 harafi
Tafiyar ajali
Ya kwashe labarin abin da ya faru tsakanin dansa
Najranu da jarmi da ya tafi gareshi domin karbo takobin da
take tare da shin a rashin samun nasara ya sanar dashi, sannan
y ci gaba da cewa "Idan Njranu ya koma wajen Gimbiya ZUhuriya ba tare da wannan takobi bashi kenan maganar aure
a tsakaninsu tarushe kamar yadda sukayi alkawari,kuma idan
Najrau bai auri Gimbiya Zuhuriya ba, burinmu na mallakar
sarautar birnin Ambar ba zai cika ba, don hakana dawo gareka domin neman taimako
Da Boka Musailamatuyaji wannan bayani na waziri
Hawaisu sai yayi shiru ya sunkuyar da kai kasa yana tunanin
bayan wani lokaci ya dago kai ya dube shi y ace da shi "Rashin
samun nasara danka Najiranu akan jarumi ba zai sa mu
zamamarasa samun nasara akan shirin da muka yin a mallakar
sarautar birni Ambar ta dawo hannunka ba, na rantse
dagirman daraja kakana Boka fikilu da ya hallaka a wajen
tabbatar da bautar gumaka da tsafi a doron kasa sai danka
Najiranu ya auri Gimbiya Zuhuriya bisa alkawarin da suka yi
idan ai mata takobin dake hannun wannan jarumi.
Yana gama fadar wannan maganar sai suka ga wani
farin haske maikama da hasken walkiya ya gifta ta gabansu
sannan sai suka nemi boka Musaila suka rasa ya bace tareda
bacewar wannan haske, waziri Hawaisu yay i kiran sunansa
har sau uku baiji ya amsa ba bare ya sake bayyana a gare su
don haka sukajinkirta suna masu sauraron su ga abin da yake
shirin aikatawa.
Bayan wani lokaci da bacewar Boka Musailamatu sai
suka sake ganin farin hasken nan ya keto bangon dakin ya
shigo ya fadi gabansu sannan sai suka ga boka Musaila ya
bayyana a inda hasken ya sauka, har a sannan yana zaune
akan bakin buzunsa na aikin sihiri sai dai ya daga hannayensa
sama idanunsa a rue yana karanta wadansu dalasumai irin na
alkaluman sihiri da tsafi,iskaai kaarfi ta keto ta shigo ta kofar
dakin da suke zaune tare da wani duhu a tsakiyar duhun ya
sauka akan tafin hannun Boka Musaila sannan sai ya daina
100 harafi
Tafiyar ajali
karanta dalasuman aikin bokancin da yake karantawa, duu da
ya sauka akan hannunsa ya bace sai ga takobin wannan jarumi
da Najranu ya kasa samun nasara karbo ta daga gareshi, ta
bayyana kaan tafin hannunsa, marikar takobin tana haske da
sheik saboda adon da aka yi mata na zinare.
Boka Musaila ya buda idanunsa ya dubi takobin
sannan ya dubi waziri hawaisu y ace da shi, wanan itace
takobin da Gimbiya Zuhuirya ta ce da danka Najiranu ya karbo
a hannun wannan jarumi ya kasa samun nasara a kansa, na
sanya ma'abota hidima a garemu sun dauko takobin daga inda
aka ajiye ta sun gabato da ita a gareni, saboda haka danka
Najiranu ya karbi takobin ya tafi da ita ya kaiwa Gimbiya
zuhuriya akan wannan aurensu kamar yadda sukayi alkawari,
koda wannanjarumiya ce Najranu bai samu nasara akansa ba,
hakika bashi da wata hujja tunda gashi ya kawo takobin gare
ta,wadda it ace takobin da take hannunsa.
Tun da takobin ta bayyana a hannun Boka Musaila
Najranu yake dubanta cikin matukarmamaki da al'ajabi ya
kuma tabbatar da cewa it ace takobin da ke hannun wannan
jarumi da yakekarbota daga gare shi, bai samu nasara ba. Shi
ma waziri Hawaisu ya cika da matukar murna farin ciki ya karbi
takobin ya mikawa dansa Najranu.
Najranu ya karba yana mai matukar mamaki tare da
kara yin imani da karfin tsafi da sihirin Boka Musaila, daga nan
waziri yay i masa godiya suka yi saama da shi ya bace cikin
alkaluman sihirinsa ya koma inda bukkkarsa take tsakiyar dajin
dake bayan birnin Ambar.
Bayan tafiyar Boka Musailasai Najranu ya tashi ya
komadakinsa tare da wannan takobi yana mai jiran wayewar
gari ya tafi ga Gimbiya Zuhuriya take fita ambun mahaifinta
tare da kuyanginta domin shakatawa, si Najranu ya shirya ya
dauki wannan takobi ya nannadeta a cikin wnai farin yanki ya
kama dokinsa ya hau ya tafi wannan lambu domin kaiwa
gimbiya Zuhirya takobi.
101 harafi
Tafiyar ajali
Ita kuwa Gimbiya Zuhuriya tun bayan da ta bar
Najiranu a bayan gari inda suke kafsawa ta koma gida, sai ta yi
nufin ta bayyana masa abin da ta ganshi ya aikata na daga
aikin sihiri domin ta tabbatar masa da cewa babu maganar
aure a tsakaninsa da ita,kasancewarsa ma'abocin aikin tsafi da
sihiri wanda shirk ace da bata mabayyana.
Washe gari da yamma da za ta tafi lambun mahaifinta
dominjiran zuwan Najranu gareta sai ta sanya kaya nan da
take sakawa a duk sanda zata fita bayan gari su hadu da
Najiranu sannan ta kawo wani farin mayafi ta rufe jikinta gaba
daya yadda ba za a ga kayan da ta saka daga ciki ba, bata
sanya hular karfe da take rufe fuskata da it aba sai da ta
risketa a hannun sannan ta dauki gorar nan na aikin shiri da ta
dauka daga wajen Najranu tare da zobensa na azurfa ta cire
daga danyatsansa, domin su zama shaida ga abin da da zata
bayana a gare shi, ta duba inda ta ajiye wannan takobi da ta
umarce shi da cewa ya je ya karbo a hannun wannan
jarumi,amma ba ta ganta ba, da yake takobin mahaifinta Sarki
Sa'adulgamidi ce da ya gada a wajen mahaifinsa sai ta yi zaton
cewa shi ne ya dauki takobin domin yin wani amfani da ita,
kamar yadda ya saba don haka ba ta damu ba daga nan ta fita
ta hau dokinta tare da suaran kuyanginta suka tafi wannan
lambu kamar yadda ta saba.
Bayan ta isa lambu ta zauna zaman jiran Najranu bada
jimawa ba sai ga Najiranu ya iso tafe akan dokinsa, yay i shiga
ta alfarma da sutura mai kyau, irin wadda 'ya'yan sarakuna da
'ya'yan attajirai suke sanyawa ya isa wajen da ake daure
dawakai ya daure dokinsa sannan ya karasa gare ta hhannunsa
rike da wannan takobin dake nannade a cikin farin yanki, ya
nemi iso gare ta ta bashi izini zaman akan kujerar dake
fuskantar ta ya zauna sukafuskanci juna ta yi mamakin ganinsa
cikin sakin jiki da nuna rashin damuwa tamkar wanda ya samu
nasarar karbo takobinsa da ta umarce shi da karbowa,kafin ta
yi Magana sai Najranu y ace da ita.
102 harafi
Tafiyar ajali
"Da girman darajarki Gimbiya Zuhuriya tauraruwa a
cikin 'ya'yan manyan sarakunan duniya,yau dai na kasance mai
cika alkawari bisa ga abin da kika umarce ni cewa na je na
karbo takobin da ke hannun Jarumin da ki ka turani gareshi,
domin ki amince da maganar aure a tsakanina da ke don haka
sai ki zama mai cika naki alkawarin da kika dauka tunda ni na
cika nawa"
Yana gama fadar wannan maganar sai ya warware
farin kyallen dake hannunsa ya fito da takobin da take ciki ya
mikamata.
Gimbiya Zuhuriya ta dubi takobin cikin matukar
mamaki tare da mamakin maganar da ya ambaa na cewa ya
samu nasara akan wannan jarumi yakarbo takobin da ta ke
hannunsa, ta karbi takobin ta rike a hannunta sai ta ga babu
shakka takobinta ce da ta neme ta ta rasa a inda ta ajiyeta yau
da za ta zo wannan lambu su hadu da shi, ta sake cika da
matukar mamaki sannan ta kara tabbatar da cewa babu
shakka akwai wani al'amari na aikin sihiri a cikin lamarinsa,
kuma ya samu nasarar dauko takobinne ta hanyar aikin sihiri.
Bayan ta gama duban takobin ta juya ta dubi Najiranu
ta ce da shi "Kai dai ka kasance daga cikinmutane masu
yaudara da ha'inci cikin lamarinsu, kuma ba ka zama mai
samun nasara akan jarumin da na turaka gareshi ka karbo
takobin dake tare da shi ba, sannan akwai alamar wanzuwar
wani al'amarina kunshin aikin sihiri a cikin lamarinka,wanda
aikata hakan shirk ace da bata mabayyani da nake fatan Allah
ya tsare ni da kusanci da masu aikatawa.kuma koda ka samu
nasarar karba takobin ta wannan hanya b azan amince na auri
ma'abocin aikin tsafi da sihiri ba".
Najiranu yay i farat y ace da ita "Ka da ki zama mara
cika alkawari ko juya baya ga abinda kika ambata da farko
bayan na samu nasarar karbo takobin da kika umarce ni da
karbowa akan maganar aure a tsakanina dake kuma kada ki
zama mai yin zato ko yadda da abin a wani zai fada na batanci
da suka a kaina,kuma idan har wannan jarumi ne ya sanar
103 harafi
Tafiyar ajali
dake cewa ban samu nasara a kansa ba,to taw ace hanya na
samu wannan takobin jar na kawota gare ki".
Gimbiya Zuhuriya tace da shi "Ban zamo mai yadda da
abin da wani zai ambata a gare nib a, illa dai abin da na gani da
idanuna, ka sani cewa ba kowa bane jarumin da na turaka ka
karbo takobin da take hannunsa face ni da kaina".
Tana fadar wannan Magana sai ta mike tsaye daga kan
kujerar da take zaune ta warware farin mayafin da ta rufe
jikinta da shi sai ga akaken kayan tare da sulken yakin da take
sanyawa a duk sanda zata fita tare shi idan ta ce da su ya je ya
karbo takobin dake hannunsa wannan jarumi sannan ta dauko
hular karfen nan da take sakawa ta rufe fuskarta yadda ba zai
iya gane cewa mace ce ba ta saka nan take sai gashi ta zama
tamkar yadda yake ganin wannan jarumi a duk sanda suka
hadu da shi.
Najranu yay i matukar razana da karayar zuciya saboda
abin da ya gani, ya kuma tabbatar da cewa babu shakka
gimbiya ZUhuriya ce takeyin wannan shiga ba wani jarumi
daban ba kamar yadda yake zato da farko, nan takejikinsa yay
i sanyi har ya rasa abin cewa saboda rashin gaskiya, ita kuwa
Gimbiya ZUhuriya da ta gay a karaya sai ta cire hular karfen da
take kanta ta ci gaba da cewa.
"Hakika na san da cewa baka gane cewa n ice nake yin
wannan shin a tafi na tare ka a bayan gari shi ayasa ka ambata
cewa kasamu nasarar karbo takobin daga hannun wannan
jarumi,kumasaboda ka daka gane hakan ne yasa bana yi maka
Magana ko na maidamaka raddi aduk sanda mukahadu da kai
ka yi Magana gare ni domin kada ka ji muryata ka gane ni kо
gane cewa mace ce, kuma duk abin da ka aikata na daga cikin
sihiri domin kasamu nasara akaina na gani idanuna ba wwani
ne ya labarta min ba,kuma na taho da shaidar da zata tabbatar
da hakan gareka a duk sand aka zo. Tana fadar wannan
maganar sai ta sake dauko gorar nan na aikin sihiri tare da
zoben azurfa da ta cire a hannun Najiranu sanda ruwan nan na
aikin sihiri ya zuba ajikinsa ya fadi kasa, ya zama tamkar
104
Tafiyar ajali
matacce, ta ajiye masaa gabansa ta ce da shi "Wannan shi ne
shaida".
Najiranu ya sake rudewa saboda rashin gaskiya nan
take gumi ya soma keto masa ta ko ina tamkar wanda akajika
da ruwa ita kuma gimbiya Zuhuriya sai ta ci gaba da cewa da
shi
"Hakika ka kasance mai aikata kuskure na fkawa cikin
aikin sihiri da shirka domin neman samun biyan bukatarka to
son ka aureni,wanda idan b aka nemi gafarar ubangijinka ba
katba to kuwa kana cikin halin hallaka da bata
mabayyani,kuma ka sani babu maganar aure tsakanina da kai
tunda b aka samu nasarar karbo takobin da ta hanyar jarumta
da bajintar k aba, sai ta hanyar aikin sihiri,don haka ka koma
ka sanar da mahaifinka ka janye akan maganar aurena kamar
yadda mukayi da alkawari da kai tunda farko idan har baka
samu nasarar karbo takobin bа".
Tana gama fadar wannan maganar sai ta juya ta bar
wajen ta bar Najiranu a zaune ya kasa ko daga kansa ya
dubeta saboda rashin gaskiya ta koma wajen da sauran
kyanginta suke ta umarce su da cewa su ka kama dawakansu
su hau suka fice daga lambun sukakama hanyar komawa gida.
**
Byan Muzaffar da dattijo Zarkiyu sun ci gaba da tafiya
daga inda sukahadu da wannan jama'ar aljanu a cikin wannan
tsibiri, ba su sake tsayawa ko in aba si da suka kwana suka
wuni suna tafiya sannan suka yada zango domin su huce
gajiya.
Da gari yaw aye a inda sukakwana bayan sun yi sallar
asuba suka yi shiri suka ci gaba da tafiya a cikin wannan tsibiri,
suka yi tafiya mai nisa har rana ta kusa faduwa sannan suka
riski wani katon kogi ma'abocin girma da fadi, ruwan da yake
cikinsa yana ambaliya da toroko idan iska ta ta kada da karfi
sai ka ga ruwan yayi tsiri sama kamar tsauni ya tabo tamkar zai
rufe doron kasa baki daya, sai ya zo gabar kogin sannan sai
yayi kasa ya koma baya.
105 harafi
Tafiyar ajali
Ruwa da yake gabar kogn yayi ambaliya kan
doron kasa, tun kafin su karasa bakin kogin Muzaffar ya
duba iya ganinsa bai hangi gabar karshen kogin ba, da
suka karasa bakin kogin sai suka tadda wasu jiragen ruwa
kwale kwale ababen sassakawa da itace guda biyu a jiye
a bakin kogin daya daga cikin jiragen sabo ne, alamun sa
ba a dade da sassakashi ba, dayan kuwa tsho ne sannan
jikinsa ya tsattsage yadda ruwa zai iya shiga cikinsa idan
ana tafiya da shi a cikin ruwan kogin.
Dattijo Zarkiyu ya dubi ruwan kogn nan sannan ya
dubi Muzaffar y ace da shi "Babu wata hanya da zamu iya
bi mu wuce wannan kogin har sai mun ketara ta cikinsa,
kuma tafiyar kwanaki biyar zamu yi kafin mu ketare
wannan koi, saboda haka za mu hau wannan irgin ruwan
mu ketare wannan kogin a cikinsa, ya nuna daya daga
cikin jeragen ruwan nan wanda ya tsufa tsiyarsu ya tsage
yace da shi za su hau a cikinsa zasu yi wannan tafiya akan
ruwa ta tsawn kwanaki biyar.
Da jin wannan Magana ta dattijo Zarkiyu sai
Muzaffar yadube shicikinmatukar mamakin ganin yadda
wannan tsoho jirgin ruwan ya lalace tsakiyarsa ya tsage
yadda ba zai yiwu su iya tafiya a cikinsa ba har tsawo
kwanaki biyar su ketare wannan kogin matukar dai ba so
suke jirgin ya nutse dasu su hallaka ba, ya dubi Dattijo
Zarkiyu y ace da shi "Me yasa zaka ce mu shiga wannan
tsohon jirgin ruwan wanda ya lalace tsakiyarsa ya tsage
bayan cewa gas abo wanda bashi da wata illa a tare da si
matkar dai ba kana so mu nutse a cikin wannan kogi mu
hallaka ba.
Dattajo Zarkiyu ya dube shi cikin fushi y ace da shi
"Umarni nake baka akan maganar da na ambata ba ina
neman shawara a gare k aba, kuma na hanake da yin
106 harafi
Tafiyar ajali
tambaya a garei akan duk abin da na umarce ka amma
baka zama mai kiyaye wannan sharadi ba, kai dai ka
zamo daga cikin mutane Bil'ada masu yawan tambaya da
rashin kiyaye abin da ake umarta a kowane lokaci".
Muzaffar ya sunkuyar da kai kas ayayi shiru kamar
yadda yake yi a duk sanda ya yiwa dattijo Zarkiyu laifi ko
kuma ya aikata kuskure har dattijo Zarkiyu ya juya ya tafi
bakin kogin ya kama wannan tsohon jirgin ruwa turashi
akan ruwa ya shiga cikinsa, shima Muzaffarya kama ya
shiga dattijo Zarkiyu ya umarce shi da cewa yayi amfani
da fekakken itacen da yake hannunsa ya tuka jirgin su
tafi. Muzaffar bai yi masa musu ba, ko yayi tambaya a
gare shi sai kawai ya aikata abin da aka umarce shi da
aikatawa nan take jirgin ruwa ya soma tafiya da su akan
ruwa suka kama hanya suka ci gaba da tafiya akan ruwan
kogin wata irin sika mai karfi tana kadawa igiyar ruwa ta
murda ruwan kogin yana ambaliya da tsira sama jirgin
ruwan ya rika tangadi da tangal-tangal tamkarzai kife
dasu su hallaka, wani lokacin sukan hangi ruwa yayi tsiri
sama kamar tsauni ya taho ya nufo inda suke kamar zai
rufe su su nutse kasa su hallaka amma idan ya zo usa da
su sai ya dare su ratsa ta cikinsa su wuce ba tare da wani
abu ya faru gare sub a.
Haka suka yi ta tafiya a cikin wanna kogin wannan
kogi ba dare ba ran aidan Muzaffar ya gaji da tuka jirgin
ruwa sai dattijo Zarkiyu ya karbe shi kuma ya zauna ya
huta kuma abin da yabawa Muzaffar mamaki shi ne ko da
digon ruwa bai keto ya shigo cikin jirgin ruwan ba ta
tsakiyar jirgin inda ya tsage har suka shafe tsawon tafiyar
kwanaki biyar suka isa bain gabar kogin.
Da isarsu bakin kogin suka sauka akan tsandauri
kusa da wnai daji mai yawan tsaunuka da kwazazzabai
107 harafi
Tafiyar ajali
kamar wanda suka wuce baya, sai dai wannan yana da
itatuwa da ciyayi da sarkakiya mai duhu da suka gewaye
ko ina. Dattjo zarkiyu ya dubi dajin bangaren hagu dana
damansa sannan ya umarci Muzaffar su bi bangaren
dama su ci gaba da tafiya.
Kafin su bar bakin kogin su fara tafiya sai suka ga
an jefesu da wani irin bakin mashi ma'aboin girma da
tsaye, tsinin mashin da yayi jajawur tamkar karfen da aka
ciro daga wutar makera mashin yana tafe akan iskayana
huci da kugi tamkar ana ruru wuta a jikinsa, dattijo
Zarkiyu yayi sauri ya zare takobinsa ya tari wannan mashi
ya kade shi gefe daya, mashin ya tafi ya fada cikin kogin
nan dake kusa dasu ya nutse a cikinsa, nan take ruwan
kogin nan dake kusa dasu ya nutse a cikinsa,nan take
ruwan kogin ya soma zabalbaala da tafarfasa saboda
musiba.
A ka sake jefansu da wani bakin mashin irin
wanda aka jefesu da shi da farko Zarkiyu ya sake sanya
takobinsa ya kade mashin efe mashin ya fada tsakanin
wasu bishiyoyi dake kusa da wajen nan take bishiyoyin
suka kama da wuta ciyayi da sarkakiyar dake wajen duk
suka kone kasar wajen ta yi baki saboda musiba danga
nan sai suka ji an sakar musu ruwan kibiyoyi ta ko in aba
tare da sun a masu harba kibiyoyiyin ba dattijo Zarkiyu ya
ci gaba da karwa da takobinsa yana kade kibiyoyin suna
faduwa kasa, shi ma Muzaffar ya soma kare kibiyoyin don
kar kansa yana kade su suna faduwa asa da fekakken
itace da yake hannunsa.
Bayan wani wa'adi mai tsawo ana harbinsu da
wannan kibiyoyi ba a samu daya daga cikinsu ba, sai
suka ga an dakata da harbor wadannan kibiyoyi da
basa ganin masu