har sai ya zama cikakken
Jarumi da zai iya gogayya da kowanne irin sadauki a
fadin duniya, kuma wanda yake da ilimin addini,
daga cikin wanda suka bijiro da bukatarsu ta neman
aurena babu namijin da ya kai wannan mataki dan
haka ban fidda ko daya daga cikinsu ba. Ina da
sahihin labara game da kai cewa mahaifinka shi ne
babban limamin birnin nan, kuuma kana da ilimin
addini sannan ga jarumta kamar yadda na tabbatar
don haka kai ne ka dace da irin namijin da
15 harafi
Tafiyar ajali
nakemuradin na aura, kuma zuciya ta ta amince da
kai a matsayin abin bege menene makomarzance na
cikin lammarinka?'
Muzaffar ya ji maganar tamkar bada shi take
ba, dan yana ganin matsayinsa bai kai a ce gimbiya
ZUhuriya za ta so shi ba a matsayinta na yar Sarki, ya
dubeta y ace da ita. "Makomar zancen ki cikin
lamarina shi ne zuciyata ba tare da da makantar da
za ta afka cikin begen abin da baza ta iya mallaka ba.
Na san cewa baki kasance daga cikin matayen da za
su ambata begensu ga kowanne irin namiji yay i
watsi da sub a, amma ni ina da sahihancin baki
kamaci auran namiji kama ta ba don kuwa nib a dan
sarki bane kuma ba attajiri ba....."
Gimbiya Zuhuriya ta tari numfashinsa da cewa
"Bari ga ambaton irin wannan kalami dan kuwa ni
ban kasance daga 'ya'yan Sarakuna da ke dorawa
kansu alfahari da tunkaho cewa sai yayan sarakuna
ko kuma attajira za su aura ba, ka sani cewa sarautar
da dukiya ALlahshi ke ba da su, ga bayinsa kuma bad
an yafi kaunar wanda ya bawa wannan baiwata sa
ba. Sai dan ya ga shugaba da zaiyi adalci ga jama'ar
da yake shugabanta da mai dukiyar da zai kyauyata
ga talakawa mabukata gare shi. Dan haka kai ne
wanda zuciyata ta zaba kuma nake fatan kasancewa
tare da kai ka zamomiji a gare ni,kuma nay i imani
da cewa idan na sanar da mahaifina kai ne wanda
nake so a cikin wanda suka bijiro da bukatarsu ta
neman aurena ba zai ki amincewa da zabina ba,
16 harafi
Tafiyar ajali
kuma zai yi matukar farin ciki da jin hakan zai kuma
amince da kai ka aure ni dan kuwa mahaifinka
mutum ne mai daraja da martaba a wajen mahaifina,
menene ra'ayinka akan haka?"
Muzaffar yayi shiru bai yi Magana ba sai dai
murmushi, ita kuma tana ganin haka sai ta ce da shi
"Na san akwai begenma a cikin zuciyarka dan na gani
kwayar idanunka, dan haka idan na koma gida zan
sanar da mahaifina kai ne wanda nake so duk a cikin
masu neman aurena zai kuma neme ka dan
tabbatarwa".
a
Tana gama wannan Magana sai ta maidahular
karfen da ta cire daga kanta ta rue fuskarta kamar
yadda take tun da farko, sannan ta kada linzamin
dokinta ta juya a sukwane ta kama hanyar komawa
gida Muzaffar ya bita dakallo yana mai mamakin
abin da ya faru tsakaninsu da irin kalaman da ta
ambata a agare shi,na nuna begensa a matsayinta na
yar sarki da bai taba zaton haka zai iya faruwa ga
wani mutum kamarsa ba.\yana tsaye a wannan waje
yana hangenta har sai da ta bace ya daina ganin koda
kurar gudun dokinta, sannan shi ma ya kada linzamin
nasa dokin ya kama hanyar komawa gida.
Gimbiya Zuhuriya tana isa gida ta daure
dokinta, ta tafi ta cire sulki da dukkanin kayan yaki
da yake jikinta, ta sanya wasu tufafin irin na ado
masu matukar kyau ta koma cikin kuyanhinta ta
zauna suka ci gaba da al'amuran sub a tare da wani
ya san cewa ta fita daga gidan ba.
17 harafi
Tafiyar ajali
Da yake mahaifinta Sarki Sa'ad bai dawo daga
tafiyar da yayi ba sai ta yanke shawarar cewa idan
mahaifinta ya dawo za ta sanar da shi cewa ta fidda
Muzaffar a matsayin wanda ta keso ta aura daga
cikin masu neman auranta.
**
Bayan kwanaki uku Sarki Sa'addulgamidi ya
dawo daga tafiyar da yayi ta kai ziyarar birnin
aininsa, bayan yayi kwanaki biyu ya huce gajiyar
tafiya ya soma fitowa fada. Waziri Hawaisu ya shirya
dan zuwa gare shi ya sanar da shi kudirinsa na
neman auran gimbiya Zuhuriya ga dansa Najiranu.
Yana isa fadar ya tadda Sarki Sa'addul gamidi da
sauran yan majalisarsa ana fadanci ya kai gaisuwa ga
Sarki aka amsa masa sannan ya nemi waje ya zauna
aka ci gaba da zaman fada tare da shi.
Da lokacin tashi daga fada yayi yan majalisar
Sarki Sa'ad suka tashi. Waziri Huwaisu ya matsa ga
Sarki Sa'ad y ace yana son ganawa da shi bayan yan
majalisar Sarki sun gama fita suka kadaita su biyu a
cikin fadar Waziri Hwaisu ya dubi Sarki Sa'ad y ace da
shi.
"Allah ya baka nasara daman ina san ganawa
da kai ne dan neman wata alfarma ta neman auran
yarka gimbiya Zuhuriya ga babban dana Najiranu, da
yake daga cikin masu begenta, idan ka amince mas
azan yi matukar farin ciki saboda kusancin da ke
tsakanina da kai, kuma hada auran yayanmu zai kara
dankon zumunci da amintaka a tsakanin Zuri'armu.
18 harafi
Tafiyar ajali
waziri Da Sarki Sa'ad ya ji wannan bayani na
Hawaisu sai y ace da shi, "Hakika nay i matukar farin
ciki da wannan shawarar taka dan kara dankon
amintaka da ke tsakanibmj, sai dai kuma kafin nay i
saurin yanke hukunci, akan al'amarin ka bani lokaci
zan ji daga gimbiya ZUhiriya idan ta kasance tana
begen danka to kuwa zan ba da auranta gare shi, ta
zama matarsa idan kuwa tana da wanda take so ti
kuwa sai mu bar wannan Magana matukar dai
wanda ta zaba bai zamo daga mutanen da shari'a ta
haramta bada auran 'ya a gare sub a.
Da waziri Hwaisu ya ji abin da Sarki y ace, sai
yay i sauri y ace da shi "Allah ya taimaki Sarki ya ja
zaminka, ai ina ganin ba sai ka nemi shawara daga
gare ta ba idan hark a amince da da n aka bas hi
aurenta duk irin ukuncin da ka yanke akanta ba zata
aki amincewa bad an kuwa nay i sani da cewa ita mai
biyayya ce a gareka cikin dukkanin lamarinta"
Sarki Sa'adya ce da shi "babu shakka abin da
ka ambata haka yake, duk irin hukuncin da na yanke
akan gimbiya Zuhuriya ba zata ki amincewa da shi
ba, amma zan bada dama ta dan ta bawa zuciyarta
abin da take muradi matukar dai abin da ta zaba bai
sabawa shari'aba, don haka kayi hakuri daga nan
zuwa kwanaki biyu zaka ji irin hukuncin da na yanke
akan lamarin".
Waziri Hawaisu bai sake cewa komai ba daga
nan suka yi sallamadaSarkiyatashi ya fice daga fadar
ya kama hanyar komawa gidansa, shi kuma Sarki ya
shiga gida.
19 harafi
Tafiyar ajali
A wannan rana da yamma Gimbiya Zuhuriya
tana zaune a dakinta cikin kuyanginta sai ga sako
daga mahaifinta ya turo a kira ta, yana son Magana
da ita ta tashi ta tafi gare shi ta gaishe da shi sannan
ta zauna ta na mai sararann abin da zai ce da ita.
Sarki Sa'adyadubi Gimbiya ZUhuriya y ace da
ita "Yak e yata Zuhuriya na saa kira ki ne saboda na ji
daga gare ki game da maganar wanda za ki aura,
hakka na baki dama ki fidda wanda zuciyarki ta
amince da shi dan na aurar da ke a gare shi, amma
har yanzu ban ji wani sakamako daga gare ki ba, idan
har yanzu babu wanda zuciyarki ta amince da shi to
Najiranu dan gidan Waziri Hawaisu mahaifinsa
bayyana bukatarsa ta neman auran ki ga dansa".
Gimbiya ZUhuriya ta amsa da cewa "Ya
Abbana mafi girman daraja da daukaka a gare ni,
hakika ni mai yin biyayya ce a gare ka bisa ga duk
wani hukunci da ka yankeakaina, ina da wanda nake
bege kuma zuciyatata amince da shi kamar yadda k
aba ni zabi amma idan kana ganin Najiranu dan
waziri Hawaisu shi ne yafi dacewa k aba da aurena
gare shi to kuwa na aimince da zabinka".
Sarki Sa'ad y ace da ita "Ban yankehukunci
akan ki ba, sai abin da kika zabarwa zuciyarki kuma
tun da kina da wanda kike so sanar da ni wane ne shi
idan har bai zamo daga mutanen da shari'a ta
haramta bada aurenki garesu ba, to kuwa zan aurar
da ke a gare shi"
Zuhuriya ta sunkuyar da kai tana mai jin kunya
sannan ta yi Magana da muryar kas-kasa ta ce da
20 harafi
Tafiyar ajali
mahaifinta Muzaffar na zaba dan gidan babban
limamin birnin nan"
Da Sarki Sa'ad ya ji wannan bayani na ta sai
yayi matukar farin ciki, kuma nan take ya amince da
zabinta, saboda yanamartaba babban limamin birnin
mahaifin Muzaffar kumayanadalabarin Muzaffar
game da jarumta da bajintarsa, kamar yadda yakeji a
birnin ana fada. Sannan bai taba jin wani ya ambaci
mummunan hali ko dabi'a da aka ce Muzafar yana
aikatawa bay a dubi Gimbiya ZUhuriya ya ce da ita.
"Hakika na amince da abin da kika yiwa kanki
zabi kuma zan auar da keg a wanda kike so don ban
taba jin an fadi wani abu na aibu ko mummunan hali
daga gare shi ba, sannan kuma mahaifinsa mutumin
kirki ne mai gaskiya da amana, don haka zan sanar
da mahaifinsa abin da yake faruwa dan a tsaida
maganar aure a tsakaninku, tashi ki je Allah yay i
miki albarka".
Gimbiya Zuhuriya ta cika da matukar murna
da farin ciki da ta ji cewar mahaifinta ya amince da
abin da ta zaba ya kuma yadda zai aurar da ita ga
Muzaffar kamar yadda take so ta tashi ta koma cikin
gida tana mai godiya ga Allah tare da farinc
ikimisaltuwa.
Washe gari da aka fita fada Sarki Sa'adul
gamidi ya sa aka kira masa waziri Hawaisu da babban
limamin birnin liman Adnan bayan da suka hallara a
fada tare da sauran yan majalisar Sarki. Sarki yayi
musu ayani da cewa yarsa gimbiya ZUhuriya ta fidda
wanda take so, daga cikin masu neman auranta,
21 harafi
Tafiyar ajali
kuma Muzaffar ta zaba dan babban limamin birnin
dan haka ya amince da shi yakuma bas hi auranta
yan majalisar Sarkisu zama shaida
Da liman Adnan ya ji bayanin Sarki sai yay i
matukar mamaki,saboda bai san cewa dansa yana
daga cikin masoyan gimbiya ZUhuriya ba don bait
aba sanar da shi ba, kuma bai gawata alama ta cewa
dansa yana bege ga wata mace ba, yayi godiua ga
Sarki Sa'adulgamidi bisa ga amincewarsa ta bada
auran yarsa ga dansa Muzaffar.
Shi kuwa Waziri Hawaisu da yajimaganar da
Sarki sa'ad ya ambata ta bada auran yarsa gad an
gidan lima Adnan ba a bawa dansa Najiranu ba,
kamar yadda yake so sai ransa y abaci, zuciyarsa ta
harzuka da ganin cewa shirinsa zai rushe na mallakar
sarautar birnin Ambar. Idan ba dansa aka baawa yar
gidan Sarki Sa'ad auranta ba.
Ya fusata da fushi mara misaluwa bakin ciki ya
yawaita a gare shi, haka ya kasance ciki damuwa yayi
shiru bai yi Magana ba, har lokacin tashi daga fada
yayi Sarki ya salami jama'a kowa ya kama hanyar
komawa gidansa.
Da liman Adnan ya koma gida sai yayi kiran
dansa Muzaffar ya sanar da shi abin da ya faru a fada
da amincewar da Sarki yayi na bashi auranta bayan
da Gimbiya Zuhuriya ta ce ta fidda da shi a matsayin
wanda take so. Muzaffar ya ji wannan Magana
tamkar mafarki duk da cewa gimbiya Zuhuriya ta
fada masa,za ta sanar da mahaifinta,shi ta zaba a
matsayin abin begen da take so ta aura, yayi godiya
22 harafi
Tafiyar ajali
ga Allah a bisa baiwa da ikonsa akan komai ya kuma
yadda da cewa gimbiya ZUhuriya tana kaunarsa da
gaskiya.
**
Shi kuwa waziri Hawaisu da ya koma gida cikin
bacin rai da bakin ciki.ya samu dansa Najiranu ya
sanar da shi abin da ya faru a fada da hukuncin da
Sarki ya yanke na bada auran yarsa gad an gidan
babban limamin birnin Ambar.da Najiranu yaji
wannan labara sai ransa ya baci zuciyarsa ta harzuka
ya fusata da fushi mara misaltuwa, saboda jin Sarki
Sa'ad ya ga wani ba a gare shi ba, ya tashi zai fice
cikin bacin rai sai mahaifinsa waziri Hawaisu ya ce da
shi.
"Ya kai dana Najiranu hakika na san kana cikin
bacin rai da damuwa kamar yadda nima nake ciki
saboda wannan hukunci da Sarki ya yanke sai dai b
azan bari ka rasa auran gimbiya Zuhuriyaba, dan
kadda sharina na son mallakar Sarautar Birnin
AMbar ta dawo hannuna ya rushe, don haka zan
dauki mataki akan wanda Sarki Sa'adya bada auran
yarsa gare shi don ganin bayansa, zan sa a hallaka shi
ruhinsa ya salwanta, idan ya zamana babu shi a
doron kasa, na san daga karshe doe sarki Sa'ad ya
dawo da maganar auran gimbiya gare ka"
Da Najiranu ya ji wanan Magana ta mahaifinsa
sai zuciyarsa, ta yi sanyi yayi farin ciki da matakin da
mahafinsa yayinufi dauka akan al'amarin.
Cikin wannan ranar waziri Hawaisu ya samu
wasu amintattun baradansa da ya yarda dasu, ya
23 harafi
Tafiyar ajali
sanar da suu abin da yake so su aikata masa na
hallaka Muzaffar dan babban limamin birnin a boye
ba tare da wan iya sani ba.
Ya ce da su idan sun hallaka shi su haka rami
su binne si yadda ba za a ga koda gawarsa ba, bare a
samu labarin inda yake ko na mutuwarsa. Ya kuma yi
musu alkawarinsa zai basu dukiya mai tarin yawa ta
zinariya da azurfa idan suka aikata abin da ya umarce
su.
Baradan nan suka yiwa waziri Hawaisu
alkawari za su aikata abin da ya umarce sun a hallaka
Muzaffar kamar yadda ya sa su,daga nan Waziri ya
hada su da dansa Najiranu dan su aikata komai a
gabansa dan tabbatarwa.
Da yakesuna da masaniyar cewa Muzaffar yak
an fita bayan gari kilisa akan dokinsa cikin kowanne
yammacin rana, sai suka yishiri da yamma suka fita
bayan gari kan hanyar da yake wucewa suka nemi
wani waje tsakiyar daji sukalabe dan jran
karasowarsa.
Bayan wani lokaci sai ga muzaffar tafe akan
dokinsa cikin sassarfa yana mai matukar nishadi da
jin dadin fitowarsa kilisa a wannan yammaci saboda
abin farin ciki da ke tare da shin a bada auran
gimbiya Zuhuriya a gare shi, da fidda shi a matsayin
mijin da take muradin ta aura.
Yana tsakiyar tafiya a wannan hanya da ya karaso
daidai inda baradan nan suke boye a cikin duhun itatuwa
sai suka fito gabaki daya akan dawakansu suka zagaye shi
ta ko ina suka yi masa kawanya, hannayensu rike da
24 harafi
Tafiyar ajali
miyagun makamai irin na fada a filin daga, da yake sun
tare shi ne dan neman rayuwarsa basu saurari komai ba,
koda suka tsaya yi masa Magana kawai sai suka yunkura
gabaki daya suka tasar masa. A fusace da nufin gamawa
da shi tun a karon farko su hallaka shi da Muzzaffarya ga
haka sai yayi sauri ya zare takobinsa ya karkata gare su
dank are kansa da ganin wadan nan baradan sun taso
kansa rike da makamai da nufin hallakasi,kuma ba tareda
ya san kosu wanene sub a da dalilinsu na san hallaka shi.
Baradan nan suka isa kansa cikin karaji da gunji
suka far masa da sara da ko ina tamkar saukar ruwan
sama.muzaffar ya tare su aka yi a rangama da kazamar
faduwa mai muni da ta haddasa salwantar rayuka
gawarwaki baradan suka soma silmiyowa daga kan
dawakansu, suna fadowa kasa san da Muzafffar ya
fantsama a tsakaninsu ya soma keta su cikin tsanain
jarumta da kwarewa ta salon iya fada.
Nan take wajen ya hargetse kura ta kuduru a
tsakaninsu ta turnuke ta takore sararin samaniya, duk
inda Muzaffarya kai sara da kaifin takobinsa sai kaga yak
eta duk wanda kaifin takobin ya samu gida biyu, saboda
karfin irin na jarumta da sadaukantaka, da ke tare da shi,
haka yay i ta hallaka baradan nan da suka taso gare shi,
har sai da ya karar da su baki daya, ya ja linzamin dokinsa
ya tsaya akansu huci da haki irin na zaratan sadaukai da
suka gama artabu a gafen fama.
Najiranu dan gidan Waziri Hawaisu da aka turo
don a hallaka Muzaffar a gabansa ya gani,dan tabbatar
da ya ga baradan sun kasa samun nasara akan Muzaffar
ya hallaka su,sai ya sake fusatuwa da harzuka mara
misaltuwa zuciyarsa ta tunzura, ya zare wata bakar
takobi daga damararsa ya rufe fuskarsa da rawai wadda
25 harafi
Tafiyar ajali
Muzaffar ba zai iya gane kowanene shi ba, ya fito daga
cikin duhun itatuwan da yake boye ya saki linzamin
dokinsa ya taso kan Muzaffar cikin karaji da gunji
fusatuwa, da nufin hallaka shi da kansa.
Muzaffar ya ji karaji da takun gudun dokinsa ta
bayansa, ya juyo ya ga wani mahayi ne daga cikin
baradan da suka tare shi yay i saura bai bayyana gare shi
ba, sai yanzu.
Cikin azama da karfin zuciya ya karkata a gare shi
ya tare shi suka yi bahaguwar haduwa irin ta mashahuran
jarumai da suke ji da kansu a fagen fama.
Kaifin takubbansu ya hadu a kan iska suka soma
kaiwa juna sara cikin nuna kwarewa da mugun nufi na
son hallakaabokin karawa.
Artabu ya rincabe a tsakaninsu suka dauki lokaci
mai tsawo suna kafsawa babu wanda ya samu nasara
akan wani, suka zabura akan dawakansu suka kaiwa juna
wafta kaifin takubbansu ya sake haduwa akan iska, suka
rike kaadun juna da hannuwansu marasa rike da makami
suka yunkura gaba daya suka diro daga kan dawakansu,
aka ci gaba da sokekeniya da bugayya fada ya dawo na kasa,
sukayi ta kafsawa har sai dai kaifin takubbansu ya dakushe
haskensu ya dasusashe saboda tsananin yawan kai sara da
haduwa da suke yi.
Suka sake yunkura suka kai dauki ga juna cikin
fusatuwa Muzaffar ya banke Najiranu da kirjinsa da bangaza
irin ta sadaukai. Najiranu ya ji ya ji kamar yayi karo da bakin
dutse saboda karfin kirjin Muzaffar suka rike damtsan juna
suka yi gwajin kwanji babu wanda ya murde wani.muzaffar
yayi masa karo da kai a tsakiyar fuska sai da Najiranu yayi baya taga-taga kamar zai fadi, saboda tsananin buguwa, sannan ya turje ya zaburo a fusace ya suri Muzaffar zai maka da kasa,
Muzaffar ya juye ya dire da kafafunsa, ya yiwa Najiranu dibar
26 harafi
Tafiyar ajali
karan mahaukaciya ya fadi da kasa. Ya zaro wani karamin
gatari daga damararsa cikin tsananin zafin nama da jarumta ya
kaiwa Najiranu sara da shi ya same shi a kafada.
Najiranu yay i karaji da kururuwa mai tsananin karfi
saboda azabar saran da shigar da kaifin gatarin yay i a jikinsa,
Muzaffar ya sake daga gatarin da dukkanin karfinsa ya kai
masa sara a tsakiyar kirjinsa. Kaifin gatarin ya sari wata
damara ta karfe da ke daure a jkin Najiranu wadda bad an it
aba, da kuwa Muzaffar ya ragargaza kashin hakarkarinsa, ya
hallaka shi da kaifin gatarinsa, gatarin yayi tsalle sama ya firge
daga hannun Muzaffar saboda tsananin karfin saran da kuma
haduwarsa da damarar karfe da ke jikin Najiranu.
Kafin Muzaffar ya café gatarin ya sake kai masa sara
Najiranu ya yunkura ya ture Muzafffar daga jikinsa ya tashi
cikin sauri ya tafi da gudu jini na daukarsa ya kama dokinsa
yah au. Ya saki linzamin dokinsa ya kama hanyar komawa
birnin AMbar asukwane dan ya tsira daga hallaka.
Shì ma Muzaffar ya tashi cikin sauri ya tafi kama na sa
dokin yah au yabi bayan Najiranu,da nufin cin masa,ya kama
shi sai dai kafin ya isa gare shi tni Najiranu yay i nisa saboda
tsakanin gudun dokinsa ya barshi a baya sosai, kurar gudun
dokinsa kawai Muzaffar yake hange har ya isa cikin birnin
Ambar ya shiga ya bacewa Muzaffar.
Da Muzaffar ya isa cikin birnin AMbar sai ya rasa
hanyar da baradan nan da ya biyo ya bi a cikin hanyoyin da ke
cikin birnin. Ya dudduba bai ga koda sahun dokinsa ba bare ya
gane inda yabi ya shiga cikin gari, yana yao da zagayawa ko zai
ga wannan jarumi k kuma ya ga dokinsa daure a turke daga
cikin turakun dounan jama'ar amma haka Muzaffaryayi ta
zagayawa har rana ta fadi bai yi sa'ar ganinsa ba. Da ya gaji da
neman wannan barde sai ganshi ba sai ya kada linzamin
dokinsa ya juya ya kama hanyar koma wagida.
Shi kuwa Najiranu bayan da ya tsrewa Muzaffar tun
daga bayan gari yana shigowa cikin birnin Ambar bai tsaya a
ko in aba sai cikin gidansu. Ya sauko daga dokinsa a galabaice
27 harafi
Tafiyar ajali
hadu akan iska tartsatsin wuya ya tashi sama tare da
wata irin tsiwa mai tada tsigar jiki irin ta haduwar
karfe da karfe suka ci aba da kaiwa juna sara da suka
da takubban da ke hannunsu, kura ta turnuke ta
kuduru a tsakaninsu tamkar dandazon barada ne
suke kafsawa a fagen fama.
Ga mamakin Gimbiya ZUhuriya sai ta ji duk
sanda Muzaffar ya kai mata sara ta kare da takobinta
sai ta ji tamkar takobin za ta kufce daga hannunta ta
fadi kasa.saboda tsananin karfin sara karfin damtse
irin na sadaukantaka da ke tare da shi.
Sannan duk da tana takama da kwarewa ta
salon iya fada da ta samu horo daga mahaifinta, sai
ta ga salon fadan da Muzaffar yake amfani da shi ya
zarcce saninta, kuma tun da take ba ta taba ganin
salon fada makamancin nasa ba, ga shi da tsananin
zafin nama da hanzari yadda yake saurin kai sara
tamkar kaduwar iska.
Tun gimbiya zuhuriya tana kokarin mubazara
da shi ta kai mas asara, har ya zamana ba ta iya
maida martani sai dai ta yi kokarin kare kanta, ta yi
amfani da duk saln fadan da ta yi masa wani abu da
za'a ga raunin jaruma da gazawarsa,ita da kanta ta
tabbatar da fifikon da ke tsakaninsu na jarumta da
kwarewa a fagen iya fada, ta kuma yadda cewa
Muzaffar ya cika cikakken jarumi kuma sadauki da
zai iya gogayya da kowanne irin barde a fadin
duniya.
Ta ja da ba baya ta yi turjiya cikin fafatawar da
suke yi sanda ta ga ta soma jigata, ba za ta iya samun
13 harafi
Tafiyar ajali
wannan al'amari suka barmaganar akan cewa su hallaka shi ta
hanyar aikin bokaye masana alkaluman sihiri da tsafi.
Shi kuwa Muzaffar da ya koma gida bai sanar da kowa
abin da ya faru tsakaninsa da wannan barada da suka tsare shi
suka tasar ma hallaka shi ba, sai ya ci gaba da gudanar da
al'amuransa tambar ba wani abu bai faru a gare shi ba"
Bayan kwanaki biyu da faruwar wannan al'amarin aka
saka ranar daurin aren Gimbiya ZUhuriya da Muzaffar, wanda
za a yi tsakanin watanni biyu masu zuwa, tun daga wannan
lokaci Muzaffar yak an ziyarci gimbiya zuhiriya a kowanne
Ikkaci dan su yi hirarsu irin ta maʼabota bege da kaunar juna,
kuma ya kann kasance cikin shiri ko ta kwana a duk sanda ya
fita bayan gari dan bai san masu son fada masa da mugun nufi
na hallaka shi ba, ka da su shammace shi cikin rashin sani su
cutar da shi.
Shi kuwa Waziri Hawaisu da ya samu labarin yin bako
da sanya ranar auran Muzaffar da gimbiya ZUhuriya 'yar Sarki
Sa'adulgamidi sai hankalinsa ya kara tashi. A wannan ranar ya
shirya ya tafi ga wani amintaccen bokansa masanin alkaluman
sihiri da yafi yarda da gasgata maganarsa daga cikin manyamahanya bokaye da yake mu'amulla da shi, don neman sa'a
ya hallaka Sarki Sa'adulgamidi ya gaji sarautar birnin Ambar ta
dawo hannunsa.
Ya yi tafiya mai matukar nisa a tsakiyar daji yana keta
sarkakiya da duhun itatuwa. Ya ketare wasu kwazazzabai ya
shiga tsakanin wasu manyan tsaunuka sannan ya isa inda wata
bukka take ita kadai a tsakiyar dajin wato bukkar da boka
Musaiamau yake zaune a cikinta.
Boka Musaila yana daya daga cikin manya Bokaye
masana aikin sihiri da Sarki Sa'addulhamidi ya kora daga birnin
Ambar don haka Boka Musaila bas hi da wnai abokin gaba da
ya tsana a fadin duniya tamkar Sarki Sa'adul-gamidi kumashi
ne wanda Waziri Hawaisu ya fi yadda da shi da gasgata
maganarsa daga cikin bokaye masana alkaluman sihiri da yake
29 harafi
Tafiyar ajali
neman taimako a gare su, do ya hallaka Sarki Sa'ad sarauta
birnin AMbar ta dawo hannunsa.
Ya tsaya a bakin bukkar ya sauka daga kan dokinsa,
sannan ya tafi ya shiga cikin bukkar kamar yadda ya saba a duk
sanda ya zo are shi, yana shigaya tadda Boka Musaila zaune
akan karaga da aka yi da itace, an shinfida buzun bakar fatar
bauna a kansa,jikinsa babu riga sai fari mayani da ya daura a
kugunsa kamar walki. Tsoho ne tukuf mai tarin shekaru babu
gashi akansa, tamkar dutse, amma yana da dogon gemu da
saje mai tarin yawa da ya zama fari fat, saboda yawan furfura
da ta baibaye shi.
Waziri Hawaisu ya isa gare shi ya fadi yay i gaisuwa
boka Musaila ya amsa masa sannan ya zauna ya soma yi masa
bayanin abin da yaketafe da shi akan maganar Gimbiya
ZUhuriya da yake son aurawa dansa da kuma kudurinsa na son
hallaka Muzaffar ruhinsa ya salwanta kafin a kai ga ranar
auransa.
Da Boka Musailamatu ya ji wannan bayani sai ya
dauko wani kaho irin na barewa, mai matukar tsayi ya kafe shi
a kasa sannan ya dauko wata kwarya ya dora a kan tsanin
kahon ta zauna, ya zuba ruwa a cikin kwaryar har sai da ta cika
ba tare da ta goce daga kan tsinin kahon ta fadi kasa ba, ya
dauko wata izga ta jelar farin doki ya rike a hannunsa, sannan
ya rufe idonsa ya soma karanta wadansu dalalusumaiirin na
aikin sihiri da ilimin bokanci.
Nan take jikin kahon ya turnuke da hayaki sannan
ruwan da ke cikin kwaryar ya soma tiriri yana tafasa tamkar an
dora shi akan wuta.
Bayan wani lokaci boka Musailamatu ya bude
idanunsa sannan ya sanya izgar da ke hannunsa a cikin ruwa
da ke cikin kwaryar ya ciro ta ya yarfa ruwan da yakejikinta a
jikin wannan farin dutse da kekusa da shi, duk inda ruwan ya
zuba a jikin dutsan sai ka ga rubutu irin na aikin sihiri da ilimin
bokanci yana bayyana a jikinsa.
30 harafi
Tafiyar ajali
Bboka Musaila ya soma karanta rubutun tare da
dukkanin bayanan da suka bayyana sai yay i shiru bai ce komai
ba, har zuwa tsawon wani lokaci. Sannan ya dago da kai ya
dubi waziri Hawaisu yace da shi.
"Babu shakka wannan lamari ne mai girma daga cikin
al'amura masu wuyar aikatawa ga duk wani masanin
alkaluman sihiri da ilimin bokanci idan ban i ba, hakika
wannan Jarumi da kake so a hallaka shi dan kadayya auri
gimbiya zuhuiriya yar Sarki Sa'addulgamidi bayanai sun
tabbatar da cewa yana da yawancin kwanaki da ba zai hallaka
lokaci guda ba har saiya kare tsawon wa'adinsa a duniya, babu
sahihancin lokacin mutuwarsa kuma ba a san a inda zai mutu
ba, sai dai duk da bayyanarwadanan bayanai ba zai hana nay i
amfani da karfin tsafi da shirina ba