ya samu damar kufcewa, daga gareta a duk sanda yay i wani kwakkwaran motsi da nufin ya samu damar kubuta sai ya ji kamarmikiya ta kara nutsa farantanta a jikinsa, ta rike shi sosai kada ya kubuce daga gareta nan
take Muzaffar ya kara jigata da galabaita saboda wannan tsanani
riko da mikiyar ta yi masa har ya soa fita daga hayyacinsa
Shi kuwa Zurkiyu yana cikin fafatawa da wadannan
mikiyoyin yana ta hallakasu tun bayan fitowarsa daga kogon
dutsen da ya baro Muzaffara a cikinsa tsawon kwana biyu da
wuni daya yana cikin wannan hali ne sai ya hangi Muzaffar ya
fito daga cikin kogon dutsen da ya hane shi da fitowa daga ciki,
daya daga cikin mikiyoyin nan ta sure shi ta tashi sama da shi
tana shirin hallakashi da ganin haka sai Zurkiyu yayi sauri ya
dauko wata kwari da bakadaga cikin kayan fadan da yake tare
da shi ya sanya kibiya harbi wannan mikiya da ta suri
Muzffarta ke shirin hallakashi, kibiyar ta tafi same ta a kirjin
mikiyar ta yi wata kadaitacciyarkara ta tarwatse asararin
samaniya gashi jikinta ya kama da wuta ya bazu akan iska
Muzaffar ya subuto daga sama ya taho ya fado kasa.
Kafin ya kai ga fadowa kasa wata daga cikin mikiyoyin
ta sake kai masa sura ta tashi sama da shi Zurkiyu ya sake
sanya kibiya ya harbeta ta tarwatse a sararin samaniya, gashi
84
Tafiyar ajali
jikinta ya kama da wuta ya bazu a kan iska Muzaffar ya subuto
daga sama ya taho zai fado kasa.
Kafin ya kai ga fadowa kasa wata daga cikin mikiyoyin
ta sake kai masa sura ta tashi sama da shi Zarkiyu ya sake
sanya kibiya ya harbeta ta tarwatse a sararin samaniya,gashin
jikinta ya kamadawuta, Muzaffarya sake subutowa ya taho
kasa ya fado akan wani kutturen itace dake kusa da wajen ya
bugu da buguwa mai tsananin nan take ya suma,wata daga
cikin mikiyoyin ta sake kai masa sura zata dauke shi ta tashi
sama da shi, Zarkiyu ya sanya kibiya ya harbe ta itama ta
hallaka,tun kafin ta kai ga daukarsa,yay i sauri ya tafi gare shi,
ya girgiza shi ya ga baya motsi alamar ya suma, ya dauke shi ya
maida shi cikin kohon dutsen da y ace masa kada ya fito daga
cikinsa ya kwantar da shi,ya sake fitowa ya ci gaba da hallaka
wadannan mikiyoyi da yake kafsawa da su har sai da ya karar
da su baki daya.
Bayan Zarkiyu y agama hallaka wadannan mikiyoyin ya
duba ya ga babu sauran wata mikiya dake shawagi a sararin
samaniya sannan ya maida takobi da sauran kayan fadansa ya
koma cikin kogon dutsen nan da ya ajiye Muzaffar ya ta dashi
har a wannan lokacin yana cikin halin suma bai farfado ba, ya
matsa kusa da shi ya kwance gorar ruwar dake jikin damarar
Muzaffar ya zuba a hannunsa ya soma shafa masa ruwa a
fuskarsa bayan wani lokaci Muzaffar ya farfado daga suman da
yayi ya bude idanunsa, da y agama dawowa hayyacinsa ya
yunkura ya tashi zaune, da kyar saboda tsannin buguwa da
yayi da kututturen itacen da ya fado a kansa ya duba ya ganshi
a cikin kogon dutsen da Zarkiyu ya hane shida fitowa daga
cikinsa gakuma Zarkiyu zaune a gefensa yana dubansa na take
ya gane cewa Zarkiyu ne ya kubutar da shi daga hannun
mikiyar da ta kusa hallakashi, ya dawo da shi cikin wannan
kogon dutsen.
Bayan Muzaffar y agama dawowa hayyacinsa sosai
Zarkiyu ya dube shi cikin fushi y ace da shi "Kai dai ka kasance
bil'adama mai matukar kafiya da bibiyar son zuciyarka ka
85 harafi
Tafiyar ajali
aikata abin da aka hane ka da aikatawa, sai da na haneka da itowa daga cikin wannan kogon duts har zuwa sand azan dawo
gare ka, ko kuma nab aka umarnin ka fito daga cikinsa, amma
sai ka zama mai bijirewa abin da na umarce k aka fito ba tare
da na umarce k aba, wannan shi ne kuskure na uku da ka
aikata a gare ni cikin tafiyar da muka fara tare da kai, kuma
idan baka zama mai kiyaye abin da na umarce k aba ka ci gaba
da aikata irin wannan kuskure,tokuwa na kusa rabuwa d akai
zan tafi na barka cikin wannan tsibiri ka hallaka b azan taimaka
maka ba”.
Muzaffar yayi shiru yana sauraronsa cikin nadamar
abin da ya aikata sai da Zarkiyu ya gama bayaninsa sannan ya
bash hakuri akan kuskuren da ya aikata, Zarkiyu y ace da shi
wannan ta wuce sai dai ka zama mai kiyaye abin da zan
umarce ka nan gaba matukar kana son tsira daga hallaka ka
fita daga wannan tsibiri ka koma birninku,idan kuwa ba zaka
zama mai kiyayewa ba, hakika hallaka za ta wanzu a gare ka
cikin wannan tsibiri, daga nan ya umarce shi da cewa ya tashi
su ci gaba da tafiya domin su fita daga wannan da'ira kafin
rana ta sake faduwa wata musibar ta sake wanzuwa a gare
su,haka Muzaffar ya tashi suka ci gaba datafiya cikin
wannanrana yana dogarawa da fekakken itacen da Zarkiyu ya
bashi saboda tsanani buguwa da yayi sanda ya fado a kan
kututturen itace.
**
Al'amarin Waziri Huwaisu kuwa bayan da gimbiya
ZUhiriya ta amince da shawarar da ya bawa dansa Najiranu ta
amince da bkatarsa ta sake bashi damar ya koma ga wannan
jarumi dmin karbo takobin dake hannunsa bisa ga sharadin da
ta kafa masa na cewa ian bai samu nasara akan jarumi ba, ba
zai sake neman wata bukata a gare ta ba, da gari ya waye
tunda sanyin safiya waziri Hawaisu ya kama hanyar dajin da
bukkar Boka Musalamatu take ya y tafiya har ya isa bigirensa
yana zuwa sauka da ga kan dokinsa ya shiga cikin bukkar ya
tadda boka Musaila zaune akan bakin buzunsa na aikin
86 harafi
Tafiyar ajali
sihiri,ya fadi gabansa ya kai gaisuwa tare da kirari irin na
girmamawa kamar yadda ya saba a duk sanda ya zo da
watabukata gareshi.
Boka Musaila ya amsa masa tareda tambayarsa cewa
"Me ke tafe da kai ya kai Wziri Hawaisu sanar da ni bukatarka
yanzu na wanzar da ita akan duk abin da kake so".
Waziri Hawaisu yace da shi "Na dawo gareka ne akan
maganar auren dana Najiranu da gimbiya Zuhuriya yar SARKI
Sa'adul gamidi ya kwashe duk labarin abin da ya faru
tsakaninsu ya sanar da shi tare da sharadin da ta kafa masa na
cewa sai ya karbo takobin dake hannun wani jarumi idan yana
so ta amince da maganar aurensa da yadda suka yi da wannan
jarumi a haduwarsa ta farko ya kasa samun nasara akansa
daga karshe y ace da shi "Don haka na zo gare ka ne domin
neman taimako dana Najiranu ya samu nasara akan wannan
jarumi ya karbo takobin dakehannunsa, tunda Gimbiya
ZUhuriya ta sake bas hi damar komawa gareshi don karbo
wannan takobi".
Da Boka Musailamatu ya ji wannan bayani na waziri
Hawaisu sai ransa y abaci zciyarsa ta harzuka ya fusata da fushi
mara misaltuwa, ya dubi Waziri Hawaisu y ace da shi "Yanzu a
duniya akwai wani bul'adama da ya isa wanzar da rashin
nasara a cikin shirin da mukeyi na mallakar sarautar birnin
AMbar ta dawo hannunka, shin da akwai wani jarumi da
jarumtakarsa zata hana danka Najiran ya cimma nasarar
farautarsa zata hana danka Najiranu ya cimma nasarar samun
amincewar Gimbiya Zuhuriya akan maganar aure a tsakaninsu,
nayi rantsuwa da ababen bauta ta tare da karfin tasirin tsafi da
sihirin da na gada a wajen mahaifina, sai na hallaka wannan
jarumi idan hallaka shi ka ke so a yi, ko kuma na kaskantar da
jarumtarsa, danka Najiranu ya samu nasara akansa"
Waziri Hawaisu yay i sauri y ace da shi "Ba na bukatar
ka hallakashi sai dai ka kankantar da jarumtarsa yadda dana
Najiranu zai iya samun nasara akansa, domin kuwa sharadin
da ta kafa masa ta ce da shi kada ya sake ya hallaka wannan
87 harafi
Tafiyar ajali
jarumi koda ya samu nasara akansa, abin da take bukata
kawai shi ne ya karbo takobin dake hannunsa ya kawo
mata domin ta amince da maganar aure a tsakaninsu".
Boka Musailamatu ya ce da shi "Wannan ya fi
komai sauki a cikin lamarina na aikin bokanci da sihiri,
kuma mai wanzuwa ne cikinabin da na kudurta zan aikata
daga alkaluman tsafina" ya daga karkashin bakin buzun
da yake zaune ya daukowani farin garin magani kamar
toka nannade a cikin wani ganye ya mikawa waziri
Hawaisu sannan y ace da shi, Katafi da wannangarin
maganin idan ka komagida sai ka zuba shi ac ikin gorar
nan ta aikin sihhiri da ku ka yi amfani da ita ku kajuye
ruwan da yakecikinta akan bawanka da siffarsata
komairin ta Muaffardan gidan liman Adnan, ka zuba akan
garin maganin ka bawa danka Najiranu ya tafi da shi
wajen da za su hadu da wannan jarumi idan sun fara
kafsawa da shi yayi kokarin ya watsa masa ruwan da ke
cikin gorar sihirin a jikinsa, idan har ruwan ya taba jikin
wannan jarumi duk wata jarumta ko sadaukantaka da ke
tare da shi zata raunana ya kasa aikata komai hard an ka
ya samu nasarar karbar takobin daga gareshi, kuma ba
zai sake dawowa hayyacinsa ba,har sai bayan wani
wa'adi mai tsawo danka Najiranu ya karbi takobin daga
gare shi ya tafi,kuma daga yanzu idan kana da wata
bukata a gare ni, da kake son ganina kada kace sai ka taso
daga cikin birnin AMbar ka taho gareni zan baka wani
zoben azurfa dake tare da dalasumai na aikin sihiri ka
sanya a hannunka,a duk sand aka tashi nemana kake da
bukatar ganina sai kamurza zoben da zan baka tare da
ambaton suna na sau uku, ba dadewa z aka ga na
bayyana gareka domin amsa bukatarka ba sai kasake
tasowa ka taho gare ni ba".
88 harafi
Tafiyar ajali
Da y agama yi masa wannan bayani ya sanya
hannnsa na hagu a cikin katuwar kwatarniyar dake ajiye
a fegensa na dama cike da wani irin bakin ruwa ya tsoma
zoben daga cikinta ya mikawa waziri Hawaisu.
Waziri Hawaisu ya s hannu ya karbi garin maganin
cikin matukar murna da farin ciki, daga nan kumayayi
godiya ga Boka Musaila ya tashi ya kama hanyar komawa
gida.
Da isarsa gida ya kira dansa Najiranu ya sanar da
shi yadda suka yi da Boka Musaila, sannan ya dauko
gorar sihirin nan da suayi amfani da shi wajen zubawa
bawan nan nasa ruwan da yake ciki gorar siffar ta rikida
ta koma irin ta Muzaffar,ya zuba garin maganin a ciki tare
da ruwa kamar yadda Boka Musaila ya umarce shi sannan
ya baiwa Najiranu domin ya tafi da ita ranar da zai koma
wajen wannan jarumi, ya watsa masa ruwan ajikinsa don
samun nasarar akansa ya karbo wannan takobi dake tare
da shi.Najranu ya karbi gorar ya ajiye a wajen da yana
mai sauraron zuwa ranar da suka yi alkawari da gimbiya
Zuhuriya akan cewa ya koma wajen wannan Jarumi don
karbo takobin da take hannunsa.
Bayan cikar kwanaki biyar kamar yadda suka yi
alkawari da Gimbiya Zuhuriya, sai Najranu ya sake yin
shiri don tafiya wajen da suka hadu da wannan jarumi da
nufin karbo takobin dake hannunsa, da yake yay i imani
da maganar mahaifinsa da ta Boka Musaila akan cewar
shi mai samun nasara ne a cikin wannan ranar matukar
ya watsa masa ruwan da ke cikin wannan gora na sihiri,
bai dauki wani makamii ko kayan fadamasu yaw aba, ban
da takobi da garkuwar sa sai wannan gora na aikin sihiri
da aka bashi bayan y agama shiryawa ya tafi ya kama
dokinsa yah au ya nufi hanyar da takefita bayan gari ta
89 harafi
Tafiyar ajali
kofar kudu ya tafi wajen da suka hadu da wannan jarumi
a karawarsu ta farko.
Ita kuwa Gimbiya Zuhuriya a wannan ranr da ta yi
musu alkawarin ya koma wajen wannan Jarumi domin
karbo takobin da take hannunsa, tun kafin Najranu ya
gamashirinsa ya fito daga gida tuni ta gama nata shirin ta
yi irin shigar da take yin a bakaken kaya tare da sulke da
hular bakin kwalkwali da take rufe mata fuska yadda ba
za a iya gane cewa mace ce ba, ta dauki wanann akobi da
aka yi wa marikarta ado da zinare, ta kama dokintata hau
ta fita ta kifar bayan gidan ba tare da kowa ya sani ba, ta
nufi wannan waje da suka hadu da Najranu a karawar da
sukayi da farko tana zuwa wajen ta sau cikin duhun
itatuwa ta shiga ta buya tana jiran isowarsa.
Bayan wani lokaci da zuwanta sai ga Najiranu tafe
akan dokinsa yana sassarfa yana zuwa daidai wajen ya ja
linzamin ya tsaya yana dube duben ya ga ta inda wannan
Jarumi zai bayyana gare shi, ita kuma gimbiya ZUhuriya
da ganin ya iso sai ta fito daga cikin duhu itatuwan da
take boye ta bayyana a gare shi, Najiranu ya dubi wannan
mahayi da ya bayyana gare shi, Nairanu ya dubi wanna
mahayi da ya bayyana gare shi ba tare da ya san cewa
Gimbiya Zuhuriya ce bay a ce da shi.
"Na dawo gareka ya kai wnan bijirarren mutum
makaskancin bawa, domin na karbi takobin da ke
hannunka kamar yadda na sanar da kai tun farkon marra,
samun nasarar da ka yi akaina tun a wancan okaci ya san а
dawo gareka domin na maida ramuwa, tunda har gimbiya
ZUhuriya ta sake bani damar na dawo gareka domin karbar
wannan takobi to kuwa zan tabbatar da isa da karfin ikona
akanka, zan kuma karbi wannan takobi daga gareka domin na
kaiwa Gimbiya ZUhuriya saboda ta amince da maganar aurea
tsakanina da ita".
90 harafi
Tafiyar ajali
Gimbiya tana jin abin da yake fad aba ta dau da
maganarsa b aba tare da ta tanka masa don kada ta yi Magana
ya gane cewa mace ce koma ya gane muryarta, shi kuma
Nairanu da ya ga haka sai yay i sauri ya zare takobin da take
hannunsa ya zaburi dokinsa ya tasar wa wannan mahayi a
fusace da nufin far masa ya karbi takobin daga gare shi, da
Gimbiya Zuhuriya taga haka sai yayi sauri itama ta zare tata
takobin ta tareshi suka soma kafsawa, tun a haduwarsu ta
farko gimbiya Zuhuriya ta kai masa wani gawurtaccen sara,
Najiranu yak are da garkuwar dake tare d ashi, garkuwar ta yi
karamai tsananin karfi irin ta haduwar karfee da karfe
tartsastin wuta ya zubo daga jikinta saboda musibar kaifin
takobin dake hannun gimbiya ZUhuriya.
Najiranu yay i baya taga taga tamkar zai fado dagakan
dokinsa saboda karfin sarar da ta kai masa wanda yayi
matukar gigiza shi ta sake kai masa wani saran ya goce kaifin
takobin ya bi iska ba tare da ta same shi ba, yay i kokarin
maida martani da kai hari da ta sa takobin kafin ta sake kai
masa wani sara Gimbiya Zuhuriya ta kare saran da tata takobin
suka ci gaba da kafaswa cikin arangama da dauko ba dadi mai
tsanani kura ta turnuke ta kuduru a tsakaninsu. Saboda yawan
Zaryada zamiyar da zamyar da dawakansu suke yia wajen
tamkar wata rundunar mayaka ne suke kafsa fada a filin daga.
Sun dauki lokaci mai tsawo suna fafatawa ba tare da
Najiranu ya ga alamar samun nasara akan wannan jarumi ba,
don haka ya soma kokarin dauko gorar nan na aikin sihiri dake
tare da shi yana kwantoshi daga damararsa ya tasarwa
wannan mahayi da nufin watsa masa ruwan dake cikinsa,
domin ya samu nasara akansa,ita kuwa gimbiya Zuhuriya da ta
lura da abin da yake hannunsa tun kafin ya karaso gare ta don
haka yana watso ruwan da yake cikin gorar sai ta yi sauri ta
goce ruwan ya wuce ya zuba a kasa ba tare da ya same ta ba.
Kafin ya sake watso mata ragowar ruwan da yake cikin
gorar sihirin ta yi sauri ta tare shi cikin matukar azama da zafin
nama ta sanya kasan takobinta ta daki gorar dake hannunsa,
91 harafi
Tafiyar ajali
gorar ya kubcedaga hannunsa ya tashi sama akan iska ruwan
da yay i nufin watso mata ya komaya juye a ikinsa baki daya,
nan take Najranu ya wuntsule daga kan dokinsaya fado kasa
yay i wanwar tamkar wanda aka yiwa saran mutuwa da takobi
a fagen daga.
Gimbiya Zuhuriya ta sake daga takobin da niyar kai
masa sara amma sai ta ga tunda ya fado daga kan dkinsa bai
kara komotsawa ba, bare ya samu damar tashi ko kare saran
takobin da zata kai masa, ta fasa kai saran gare shi ta ja
linzamin dokinta ta tsaya a gabansa, ta dube shi ta ga yana
numfashi kuma idanunsa a bude amma bay a iya motsawa ko
dan yatsansa daga inda yakekwance tamkar wanda ya suma,ta
yi matukar mamakin wannan al'amarin da ya faru gareshi,
lokaci guda kuma sai ta fahimci cewa akwai wani abu na aikin
sihiri tatare da wannan ruwan da yayi nufin watsa mata bai
samu nasara ba, ruwa ya koma ya zuba a jikinsa ta yi godiya ga
Allah da ya kiyaye ta daga sharrin da mugun nfin da Najiranu
yay i nufin aikatawa a kanta hadi da aikin sihiri, wanda da ya
zuba mata ruwan da ke cikin gorar nan it ace zata kasance a
cikinw annan al'amarin ya samu nasarar karbar takobin aga
gare ta ta hanyar aikin sihiri ba ta hanyarjarumta ba.
Bayan gimbiya Zuhuriya ta gamawannan tunani
tanashirin sakin linzamin dokinta ta tafi sai ta hangi wani zobe
na azurfa a hannun Najiranu don haka ta sauko dag akan
dokinta ta kama hannunsa ta cire zoben domin ta tafi da shi
tare da gorar ruwan da yay i nufin watsa mata saboda su zama
shaida a gare ta,a duk sanda Najiranuya sake dawowa gare ta
bisa ga alkawarin da suka yi, daga nan ta kma dokinta ta hau
ta nufi hanyar komawa gida tana mai tunanin yadda Najiranu
ya wanzu a cikin aikin sihiri da shirka don kawai ya samu biyan
bukatarsa ta neman aurenta.
**
Su kuwa su Muzaffar da dattijo Zarkiyu dake tafiya a
tsakiyar daji cikin tsibirin Hijusiya bayan da suka bar wajen da
Zarkiyu ya hallakawadannan mikiyoyin suka ci gaba da tafiya,
92 harafi
Tafiyar ajali
basu sake tsayawa a ko in aba sai da suka fita daga cikin
wannan da'irasuka riski wani waje ma matukar kyawun yanayi
a wani karancin tsanuka da kwazazzabai a wajen, haka
kumababu sarkakiya da duhun itatuwa irin na bakn dajin da
suka wuce a baya, ga ciyawa ta yi kore shar tare da furanni
masu dadin kamshi, sassanyar iskatana kadawa tare da wanzar
da ni'ima a cikin wannan yanayi Muzaffar yay i mamaki da
ganin wannan waje a cikin wannan tsibiri mai matukar kunci
da musibu marasa misaltuwa, sai dai tunda suka shigo wannan
waje ya lura da cewa dattijo Zarkiyu yana taka-tsantsan da
kiyayewa a duk inda suka wuce kamarmai fargabar kada wani
abu ya farmake su ya hallaka su.
Haka suka ci gaba da tafiya har rana ta fadi sannan
suka nemi waje suka yada zango domin su kwana kafin gari
yaw aye, su ci gaba da tafiya, da dare yay i bayan sun idar da
sallar magariba da isha'l Muzaffar ya kwanta barci don ya huce
gajiya dake tare da shi, shi kuma dattijo Zarkiyu ya zauna daga
gefe yana jan casbaharsa ya shiga lazimi, kafin wani lokaci
barci mai nauyi ya dauke Muzaffar a cikin barcin nasa ya rika
mafarki mahaifansa tare da yan uwansa da kuma masoyiiyarsa
Gimbiya Zuhuriya wanda a yanzu yay i nisa su cikin wannan
tsibiri na Hujiyasa da aka kawo cikinsa.
Yana cikin wannan bacci ne can da kusan sulasainin
dare sai Muzaffar ya ji dattijon Zarkiyu yana tashinsa daga
bacci tare da umartarsa cewa ya tashi su ci gaba da tafiya,
Muzaffar ya farka daga baccin ba tare da ya so ba, ya dubi
Muzaffar Zarkiyu ya ce da shi.
"Me yasa zaka ce mu ci gaba da tafiya a cikin wannan
dare ba za a bari gari yaw aye ba, hakika na zamo gajiyayye
saboda yawan tafiyar da mua yi ga kuma ciwo na buguwar da
nay i a jikina".
Dattijo Zarkiyu ya dube shi cikin tsawatarwa yace da
shi "Umarni nake baka cikin lamarina ba ina neman shawarar a
gareka ba, kuma na hane ka da yin tambaya a gareni tun a
farkon marra, amma baka zama mai kiyayewa abin da na
93 harafi
Tafiyar ajali
umarce k aba, babu shakka kana cikin kuskre da zai ya
sanyawa na tafi na barka cikin wannan taisbiri ka hallaka
matukar b aka zama mai kiyaye abin da na umarce ka da
kiyayewa ba"
Muzaffar bai sake cewa komai ba, ya tashi ya bi Dattijo
Zarkiyu suka kamahanya suka ci gaba da tafiya cikin wannan
dare, kafin gari yaw aye sun fita daga cikin wannan dausayi
mai maukar ni'ima sun shiga cikin wani lardi ma'abocin
tsaunuka da duwasu, bbu itatuwa ko ciyayi a wajen sai dai
rairayi da ya mamaye ko ina tamkar tsakiyar sahahara da gari
yaw aye, bayan sun idar sa sallar asubahhi suka ci gaba da
tafiya da rana ta keto sai gaba daya da'irar wajen ta dauki zafi
iskar da take kadawa ta rika busowa da dumamar yanayi
tamkar duk wata halitta da ke wajen zata kama da wuta, ta
kone saboda musiba, gashi babu kotsiro na ciyawa bare wata
bishiya da za su samu inuwar da zasu zauna su huta.
Hhaka suka ci gaba da tafiya a cikin wannan lardi mai
tsananin dumamar yanayi da zafi har sukashafe tsawon
kwanaki biyar ba tare da sun fita daga cikinsa ba, a rana a
shida daga cikin ranekun tafiyarsu ne sua tsakiyar tafiya sai
suka hangi wata tawagar jama'a matafiya sun keto ta gabansu
sun tunkaro inda suke, suna dauke da jajayen tutoci a
hannunsa masu tambarin rana, tare d amakamai na yaki iri
daban daban kumababu wanda yake sanye da wata sutura a
jikinsa ban da bante da fata da suka daura.
"Muzaffar yayi matukar mamamki da ganin wannan
tawagar jama'a da suka tunkaro su, saboda ganin sun yi kama
da jama'ar mutane kuma rabon da ya ga wani mutum
bil'adama kamar sat un ranar da ya baro birninsu aka kawo shi
wannan tsibiri, shi kuwa dattijo Zarkiyu da yake ya san cewa
ba jama'ar mutane bil'adama bane kamaryadda Muzaffar yake
zato wasu tawagar bakaken aljanu e ma'abota bautawa rana
suka shigo wannan tsibiri domin gudanar da ayyukansu na
bauta kamar yadda suke yi a kowacce shekara don haka ya
dubi Muzaffar y ace da shi.
94 harafi
Tafiyar ajali
"Zany i gargadi a gare ka bisa ga wannan jama'u da
suka tunkaro inda muke kada ka sake ka yiwa wani Magana
daga cikinsu, kuma koda wnai yayi maka Magana kada ka kula
al'amarinsa ko ka saurare shi, idan ka kiyaye abin da na umarce ka
hakika zamu wuce ta cikin wannan ayarin jama'a ba tare da sun
samu ikon aikata wani al'amari na cutarwa a gare mu ba.
Muzaffar ya amsa da cewa "Zan kiyaye abin da ka umarce ni
da aikatawa, a lokacin da yake maganar hankalinsa yana kan ayarin
jama'ar ba akan dattijo Zarkiyu ba daga nan suka ci gaba da tafiya
har suka karaso inda tawagar jama'ar suke tafe akahadu, suka ratsa
ta cikinsu suna tafiya babu wanda ya yiwa wani Magana a
tsakaninsu, jama'ar bas u ko dubi su Muzaffar ba bare su kula
al'amarinsu tafiya kawai suke yi ya zuwa inda suka sag aba babu
saurarawa daga cikinsu akwai mata da kananun yara da tsofaffi,
amma sashin su baya yiwa sashin su Magana babu mai tausayin yaro
ko tsoho tafiya suke tamkar babu wanda ya damu da wani a
tsakaninsu.
Muzaffar suka ci gaba da tafiya suna ketawa ta tsakanin
wadannan jama'a babu wand aya damu da al'amarinsu da yake
jama'ar sna da matukar yawa sai da rana ta kusa faduwa, sannan
suka kai karshensu bayan wucewar wannan jama'a daga karshe sai
ga wata tsohuwa daga cikinsu da suka barta a baya, tana tafe tana
dogawara da sanda saboda yawan tsufa kuma gas hi ta yi matukar
gajiya da galabaita sannan dafa cikin jama'ar da suke tafe tare da su
babu mai tausayinta bare ya taimaka mata tana isowa wajen da
Muzaffar yak e sai ta dube shi ta yi masa Magana cikin rawar murya irin ta
stufa da galabaita tace da shi.
"Yaaro kataimakamin da ruwa na sha kada kihirwa ta kaini ga
halaka".
Tausayin tsohuwar nan ya kama Muzaffar saboda ganin halin da
takeciki,ya tafi gareta domin ya taimakamata dattijoZarkiyu dake gaba yana
tafiya bai san da cewa Muzaffar ya tsaya ba, sai da ya juyo baya sai ya hange
shi tare da wannan tsohuwa ya kwanto salkar ruwa dake tare da shi ya mika
mata zata karba ta sha, dattijon Zarkiyu ya daka masa tsawa cikin
madaukakiyar murya mai karfi domin kada ya bata salkar ruwa amma kafin
Muzaffar ya ji tuni har tsohuwar ta karbi salkar ruwan ta kai bakinta ta soma
sha.
Da kai ruwan nan bakinta ta sha sai ta yi wani irin karaji da gunji
mai tsananin karfi da ban firgice ta suri Muzaffar ta yi jifa da shi jikin wani
karamin dutse dake kusa da wajen karajin da ta yi ya sanya sauran jama'ar
95 harafi
Tafiyar ajali
dake tafe tare da ita suka dakata da tafiyar da sukeyi suka juyo gare ta, ta sake yin karaji ta daga hannayenta sama nan take sai ta rikayin girma daga
siffar da zaka iya kiranta mutum bil'adam ya zwa wata irin siffa maimatukar
ban tsoroda razanarwa, idanuwanta suka koma ja jawur kamar garwashin
wuta wasu zaro-zaro hakoramasu kama a fike suka fito daga cikin bakinta,
tare da wnai irin gashi da ya lullube dukkanin fatar jikinta.
Muzaffar yai matukar mamakin wannan al'amari ya zabura ya tashi
cikin sauri ya dauki fekakken itace da yakeyin amfani da shi wajen yin fada
ya tare ta kafin ta karaso gare shi,tsohuwar nan tana zuwa ta kaimasa
dukada sandar da take hannunta, Muzafffarya kare da nasa makamin amma
sai da yay i baya taga taga kamar zai fadi saboda karfin bugun da ta kawo
masa nan takeya ji a ransa cewa wannan tsohuwa ba zata zamo daga cikin
jinsin mutane bil'adama ba sai dai ta kasance daga cikin jama'ar aljanu,ya
kuma tuna maganar dattijo Mubasshir da ya sanar da shi cewa duk wanda ya
ganin cikin wannan tsibiri ba utum bane bil'adama irinsa sai dai Aljani domin
jama'ar mutane ba za su iya shigowa ciki wannan tsibiri su rayu ba.
Tsohuwar nan ta sake kai masa duka da sandar da take hannunta
Muzaffar ya goce ta sauka a jikinwani karamin dutse da ta jefa