An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
TAFIYAR AJALI SHEHU USMAN MOHD
Tafiyar ajali
Sa'adul gamidi wani Sarki ne dake sarautar birnin
AMbar can gabas da kogin basara. Allah yay i masa baiwa
da kwarjini da kamala tare da soyayya daga jama'ar da
yake shugbanta, don bin umarnin abin da ya shardanta
musu sabda adalci da kyautatawa mutanensa, mai son
addini tare da tabbatar da an kiyaye hukuncin ubangiji a
dukkanin masarautarsa, tun bayan da ya zama Sarki a
daular AMbar ya kawar da duk wata bidi'ata al'da da
jama'ar birnin suke aikatawa.
Yasa aka fatattaki bokaye yan tsubbu da masu
aikata duk wani nau'l na aikin sihiri a cikin birninsa. Ya
kuma tabbatar da shari'ar musulunci a dukkanin
masarauyun dake karkashin birnin Ambar.
Tun daga wannan lokaci manyan-manya bokaye
ma'abota aikin sihiri da tsafi, wanda Sarki Sa'adya sa aka
atattake su daga birnin AMbar suka shiga yunkurin
daukar fansa a kansa. Dan ganin bayansa su hallakashi ko
kuma su raba shi da sarautar birnin AMbar, amma cikin
hukuncin ubangiji da kiyayewarsa babu wani abu na
cutarwa da ya taba samun Sarki Sa'adul Gamidi bare su
sa ran samun nasara akan hi.
Sarki Sa'ad yana da wata kyakkyawar 'ya mai suna
ZUHURIYA wadda it ace babba c ikin 'ya'yansa.
Kasancewar bayan da aka haife ta Sarki Sa'ad bai sake
samun haihuwa ba, har sai bayan shekaru goma sha
takwas, sannan dukkanin matansa suka ci gaba da
haihuwa. Dan haka Sarki sa'ad bas hi da wani da babba a
gabansa, ban da gimbiya Zuhuriya. Dukkanin sauran
'ya'yansa yara ne kanana masu karancin shekaru.
Gimbiya Zuhuriya ta taso cikin samun tarbiya da
kulawa irinta soyayyar da da mahaifinta Sarki Sa'add
2 harafi
Tafiyar ajali
yake nuna mata kasancewar babbar ya a gare shi ta
farko, da yake tana sha'awar koyan fada da makami da
yadda ake afatawa a fagen fama.
Ta samu horo daga mahaifinta Sarki Sa'ad
kasancewarsa cikakken jarumi kuma sadauki da ya
shahara a fagen iyya fada da kowane irin makami.
Tun bayan da gimbiya Zuhuriya ta tasata kai munzalin
isa aure. Sai masoya suka fara bijiro da bukatarsu ta neman
auranta ga Sarki Sa'adul gamidi 'ya'yan sarakuna da manyan
attajirai masu abin hannu duk wanda ya gabatar da bukatarsa
ta neman auran gimbiya Zuhuriya gare shi sai Sarki Sa'adya
bas hi dama cewa ya tafi ya nemi soyayyar daga gare ta idan
Gimbiya ZUhuriya ta amince tana kaunarsa, shi kuma yayi
masa alkawarin zai bashi auranta. Masoya Gimbiya Zuhuriya
da dama sun gabatar da kansu gare ta dan neman soyayyarta,
amma ita taki mallaka tata soyayyar gare su, saboda tana
ganin babu wanda ya dace da irin mijin da take muradin ta
aura.
A ra'ayin Gimbiya ZUhuruiya ta fi son ta auri namiji
mai ilimi addini kuma cikakken jarumi da zai iya gogąyya da
kowanne irin Sadauki a fadin duniya koda kuwa bad an Sarki
ba ne shi ko kuma attajiri da yawa daga cikin 'ya'yan Sarakuna
da attajirai da suke zuwa gare ta da zummar neman auranta,
babu wanda ya iya koda kwakkwaran rikon takobi irin na
Jarumta, bare ace ga wanda aka taba fita da shi fagen yaki a ka
ga irin jarumta da bajintarsa. Dan haka taki amincewa ta nuna
begen ga daya daga cikin wadannan 'ya'yan sarakuna da
attajirai da suke neman auranta.
Sarki Sa'adul gamidi yana da wani waziri mai suna
HAWAISUL_MUNAN da yake a matsayin waziri tun zamanin
mahaifin Sarki Sa'ad yana sarautar kafin ya rasu a nada Sa'adul
gamidi Sarki.
Waziri Hawaisu mutun ne mai nuna kyakkyawan hali
ga Sarki Sa'ad da sauran jama'ar birnin a zahiri amma a badini
mutanne mai mummunan hali na fajirci da rashin tsron Allah
3 harafi
Tafiyar ajali
babu abin da yake buri a rayuwarsa illa ya ga sarautar birnin
AMbar ta dawo hannunsa tun zamanin mahaifin Sarki Sa'ad
yana Sarauta kafin ya rasu a nada Sa'adul gamidi Sarki.
Bayan rasuwar mahaifin Sarki Sa'ad Waziri Hawaisu ya
so a maida sarautar hannunsa, a nada shi Sarki, amma sai 'yan
majalisar masarautar suka ki amincewa da kudirinsa. Suka
nada sa'adul hamidi Sarki kasancewar shi ne mai gadan
sarautar, Waziri Huwaisu yay i matukar bakin ciki da faruwar
wannan lamari nakin nada shi Sarki da yan majalisar
masarautar suka yi, amma daga baya sai yay i farin ciki da ya
ga cewa Sarki bas hi da wani dan uwa, ko kuma kani da zai
gaje shi, idan ya rasu, hakan kuma bas hi da wani babban da
namiji da zai zama magajinsa bayan ransa. Don haka tilas
Sarautar birnin ta dawo hannunsa da zaran an ce babu ran
Sarki Sa'adulgamidi.
Tun daga wannan lokaci sai waziri Haiwausu ya shiga
bin manyan bokaye. Matsafa da masana aiki sihiri musamman
wanda Sarki Sa'ad ya sa ake fatattake su aka kore su daga
birin. Don neman taimakonsu aka yadda zai samu nasarar
hallaka Sarki Sa'adul gamidi Sarautar birnin ta dawo
hannunsa.
Tsayin kowacce rana Waziri Haiwaisu bas hi da wani
aiki sai shirye-shiryen makirici da kulla yadda za su haklaka
Sarki Sa'adaul gamidi da shi da manyan bokaye da yake neman
taimako daga gare su. Amma cikin kiyayewar ubangiji da
buwayarsa babu wani abu na cutarwa da ya taba samun Sarki
Sa'adbare su saran samun nasara akan kudirinsu na hallaka shi
Manyan-manyan bokaye masana alkaluman sihiri da
dama sun sha sanar da shi cewa dole sarautar birnin Amzar za
ta dawo hannunsa wata rana daga cikin wa'adin rayuwarsa.
Amma har yanzu lamarin yaki tabbata, kuma bai ga wata alama ta samun nasara ba.
Daga ire iren bayanan da bokayen suke yi masa na
bincikensu cikin alkalaman sihiri da suka sanar da shi, tun yana
yarda da maganar bokayan yana gasgata abin da suke sanar da
4 harafi
Tafiyar ajali
shi, har zuciyarsa ta soma rauni ya karaya saboda rashin
samun nasara cikin wannan lamari tsawn lokacin da ya sanya
kudirin hallaka Sarki Sa'adulgamidi a ransa.
Daga cikin masoyan gimbiya Zuhuriya akwai babban
dan waziri Hawaisu mai suna najiranu da yake matukar
kaunarta ammaita gimbiya Zuhuriya daidai da bugawar
numfashi ba ta kaunarsa a zuciyarta, ya gabatar da bukatarsa
ta neman begenta a gare shi amma ta nuna masa rashin
amincewa da karbar soyayyarsa a gare ta dan yay i hakuri da
Najiranu ya fahimci hakasai ya koma ga mahaifinsaWaziri
Hawaisu ya sanar da shi irin begen da yakeyiwa Gimbiya
Zuhuriya yar Sarki Sa'ad da bukatarsa ta ya nema masa
auranta wajen mahaifinta Sarki sa'ad
Da waziri Hawaisu ya ji wannan bayani na dansa
Najiranu sai wani tunani irin na makirci ya fado a ransa, yay i
hangen cewa wannan ma wata hanya ce ta samun nasarar
dawo da sarautar birnin AMbar gare shi, idan har dansa yana
auran Gimbiya ZUhuriya babbar yar Sarki Sa'adul gamidi.
Yana daga abin da zai kara tabbatar da si ya zama Sarki
idan ya samu nasarar hallaka Sarki Sa'ad kuma da yake tsufa
ya fara cin karfinsa dan ya fi Sarki Sa'ad yawan shekaru idan
ma ba'a nadashi Sarki ba dole dansa za a bawa Sarautar tun da
shi ne yake auran babbar yar Sarki dan haka Sarautar dai tana
tare da shi.
Da ya gama wannan tunani sai y ace da dansa Najiranu
'hakika nay i matukar farin ciki da kai yi tunani ka auri Gimbiya
Zuhuriya yar Sarki sa'ad. Dalilina kuwa shi ne na dade ina buri
da muradin nag a na karbi sarautar birni nan ta dawo hannu
na tun zamanin mahaifin Sarki Sa'adyana sarauta kafin ya rasu
a nada sa'ad Sarki dan haka zan nemamaka auran gimbiya
ZUhuriya saboda na kara samun damar mallakar sarautar
birnin nan ta dawo hannuna.
Idan ma yan majalisar masarautar basu yarda na zama
Sarki ba dole dai kai za a nada Sarki a birnin tun da kai ne
kakeauran babbar yar Sarki kuma bas hi da maigadan sarautar
5 harafi
Tafiyar ajali
daga danginsa. Sannan ba zai yuwu a nada mace sarauta a
babbar daular musulunci ba"
Da Najiranu ya ji wannan bayani na mahaifinsa sai ya
cika da matukar murna da farin ciki saboda jin cewa idan ya
auri Gimbiya Zuhiya zai iya zama Sarki a birnin AMbar bayan
rasuwar Sarki Saʼad da yake Sarki Sa'ad yay i tafiya a wannan
lokaci dan kai ziyarar birnin amininsa d ake yamma da kogin
basra sai Waziri Hawaisu y ace da dansa idan Sarki
sa'addulgamidi ya dawo zai gaatar da bukatarsa ta neman
masaauran gimbiya Zuhuriya.
Najiranu ya sake cika damatukar murna da farin ciki
sannan ya tashi ya fita daga dakin mahaifinsayana mai alfahari
da jin dadin abin da mahaifinsa ya ambata tun daga wannan
rana Waziri Hawaisu ya kasance cikin shirin ganin dawowar
Sarki dan ya gabatar da bukatarsa gare shi ta neman
auran gimbiya Zuhuriya ga dansa Najiranu
**
A cikin birnin akwai wani matashin Jarumi, kuma
Sadauki mai suna Muzaffar, mahaifinsa shi ne babban
limamin birnin kuma yanada wadatar ilimi addini.allah ya
halicci Muzaffar kyakkyawan kuma ga jarumta da rashin
tsoro ko fargaba a babu a tare da shi sai dai kuma
Muzaffar yay a kasance hatsabibi, kuma shhu'umin gaske
a cikin lamarin rayuwarsa babu abin da yake so illa ya ga
wani abu da ya addabi jama'a ko kuma yake hallaka
mutane ana tsoron tunkarar inda yake shi kuma ya tafi
gare shi ya haike masa ya hallaka shi.
An taba samun wani gawurtaccen maciji da ake
tunanin yana tare da aljanu a jikinsa. Cikin wata
tsohuwar rijiya tsawan shekaru ashirin ya addabi jama'a,
yak an fito daga rijiyar ya hallaka mai karar kwana.ga duk
wanda ya kuusanci inda yake, amma Muzaffar ya tafi
gare shi ya shiga har cikin rijiyar ya hallaka macijin ya
Π6 harafi
Tafiyar ajali
raba jama'a da musiba. Wannan ne ya sa jarumtrarsa ta
shahara a wajen dukkanin jama'arbirnin aka sanshi. Koda
baka taba ganinsa da idanunka ba z aka ji labarinsa ya
karade ko ina.
Muzaffar yana da matukar karambani da rashin ji,
kasancewar shi ne babban dansa da yake fatan ya gajesi
ya zama babban limamin birnin koda bayan ransa amma
babu abin daya sauya daga dabi'ar Muzaffar da
hatsabibancinsa. Sai dai mahaifin nasa ne ya hakura ya ci
gaba da yi masa addu'a akan Allah ya raba shi da wannan
hali na shi.
Duk abin da yake faruwa a birnin AMbar na
labarin Jarumta da bajintar Muzaffar gimbiya ZUhuriya
tana samun labara sai dai bata taba ganin Muzaffar da
idanunta ba, bare ta a wani abu a jarumta da ya aikata. А
ka yi sa'a wata rana dayammaci Gimbiya Zuhuriya da
kuyanginta suka fita bayan gari dan yawan shakatawa,
irin na nishadi. Suka yi ta tafiyar har suka iso bakin wani
kogi da jama'ar birnin sukedibar ruwa a cikinsa. Gimbiya
Zuhuriya ta sa suka tsaya a nan sukasauka a gindin wata
bishiya da kekusa da kogin. Ta zauna suna hira cikin
kuyanginta
Can da kusn faduwar rana sai ga wata tsohuwar
Damisa a gigice, ciwon hakori ya bazamo ta daga cikin
daji bayan wasu tsaunuka da ke kusa da wannan kogi.
Damisar ta nufo bakin kogin ta taso kan jama'ar da ke
bakin kogin da suka hangi damisar ta nufo inda suke, sai
suka razana suka tarwatse kowanensu yay i ta kansa. Aka
shiga guje guje da neman hanyar tsira, nan take waje ya
hargitse kururuwa da hargowar mutane ta cika wajen
kowa ka gani yana neman hanyar tsira kada Damisar ta
hallaka shi.
7
harafi
Tafiyar ajali
Muzaffar yana bakin kogin yana bawa dokinsa
ruwa yaji haniya da hargowar jama'a ta gauraye bakin
kogin.
Yana dago kansa dan ya ga abin da yake faruwa
sai ya hangi damisa ce ta taso kan jama'a suka razana
suka shiga gudun neman tsira.
Ya ga damisar nan ta tasarwa wani tsoho mai
neman, yawan shekaru da ya kasa guduwa zata hallaka
shi. Nan take Muzaffar ya tashi cikin hanzari da jarumta
ya nufi inda Damisar take dan ya kaiaw wannan tsohon
dauki kada Damisar ta hallaka shi kuma ba tare da wani
makami a hannunsa ba.
Ita ma gimbiya da ke zaune a gefen kogin cikin
kuyanginta. suna hira. Da ta ji hayaniya da ta gauraye
wajen ta juyo ta ga abin da yake faruwa ta hangi damisar
nan ta tasar ma wannan tsohon da ya kasa guduawa za ta
hallaka shi. Da ganin haka saita mike cikin sauri ta nufi
inda suka daure dawakansu ta dauko takobinta da ke
duare a jikin sirdin dokinta. Ta tasar ma wajen da wannan
damisa take cikin tsananin jarumta da karfin zuciya, dan
kaiwa wannan tsoho dauki kada damisar ta halaka shi.
Kafin ta karasa wajen tuni Muzaffar ya isa ga
damisar ya sanya hannu ya fizgeta daga cikin tsohon yam
aka ta da kasa. Damisar ya yunkura a fusace ta rabu da
tsohon ta taso kan Muzffar tana wani irin gurnani da
gunji na masifa. Ta yi tsalle kansa da nufin bangaje shi ya
fadi kasa ta turmushe shi.
Muzaffar ya café Damisar ya sake makata da kasa,
sannan ya turmushe ta ya kama habar bakinta ya sanya
dukkanin karfinsa yak eta bakin gida biyu, ya kuma karya
kashin wuyanta lokaci guda bata ko shuruba.
8
Tafiyar ajali
Yana gama hallaka Damisar gimbiya zuhuriya tana
karasowa wajen rike da takobi azare, da nufin taimakon
say a hallaka damisar amma sai ta tarar da tuni ya hallaka
damisar ba tare da wani makami ba.
Ta yi matukarmamaki da jarumtar wannan jarumi
har abin ya burgeta. Duk da cewa ba ta san shi ne
Muzaffar da ake bada labarin jarumta da bajintarsa baа
dukkanin fadin birnin.
Muzaffar ya dago kansa ya dubi wanda yake tsaye
a kusa da shi bayan ya saki Damisar a kasa matacciya. Ga
mamakinsa sai ya ga mace rike da takobi da ta taho don
taimaka masa a hallaka damisar yayi matukar mamaki na
jarumta da bajintar wanan mace saboda kokarin da ta
nuna na rashin tsaro bayan da mazaje da dama da ke
wajen suka arce da tsira dadaga hallaka.
Suna hada ido sai suka tsaya suna duban juna
gimbiya Zuhuriya ta ga Muzaffar kyakkyawa ga diri da
sura irin na mazaje Sadaukai, zuciyarta ta kasa jurewa har
sai da ta yi masa murmushi ya bayyana jeren fararen
hakoranta.
Shi ma Muzaffar tuni kyawun surarta ya dauki
hankalinsa har sai da yay i kirari da tasbihi ga ubangiji
cikin zuciyarsa da cewa.
"Tsarki ya tabata ga mahaliccin wannan
kyakkyawar mace a duniyar kamarta ba, shi kansa bai san
sanda yay i mata murmushi ba kamar yadda ta yi masa.
Sai dais hi ya fita karfin zuciya yay i auri ya dauke
idanunsa yak au da kai ga barin dubanta. Ya tafi ga
tsohon nan da ya fadi kasa ya tayar da shi ya debo ruwa a
cikin kogin y aba shi ya sha. Ya ci gaba da kula da shi har
tsahon ya dawo hayyacinsa, sannan ya tambaye shi inda
'yan uwansa suke dan ya maida shi gida.
9
harafi
Tafiyar ajali
Da tsohon nan ya gay a kubuta daga hannun
Damisar bai hallakata ba sai yayi NUzaffar godiya tare da
sanya masa albarka. Ya kuma ce da shi ya barshi zai iya
komawa gida da kansa ba sai ya kais hi ba. Ya mike ya dauki sandarsa ya soma dogarawa yakama hanyar
komawa gida. Yana tafe yana yiwa Muzaffar addu'a da
shi masa albarka har ya bar bakin kogin.
Duk abin da yake faruwa Gimbiya ZUhúriya tana
tsaye tana duban Muzaffar, nan take sai ta ji begensa
ya shiga zuciyarta, saboda yawan tausayi da jarumtarsa, da tsohon nan ya tafii Muzaffar ya juyo
sai ya ga wannan mace tana tsaye tana dubbansa,
yay i matukar mamaki da irin kallon da take yi masa.
Ita kuma sai ta yi masa godiya abisa taimakon da
yay i wa wannan tsoho ya kubatar da shi daga
hannun da Damisar ba ta hallaka shi ba.
Da yake Muzaffar bai san cewa ta ce Gimbiya
ZUhuriya yar Sarki Sa'ad da ke sarautar birnin AMbar
ba, sai ya ya amsa godiyar da ta yi masa ya kada
kansa ya tafi ya koma inda dokinsa yake, ita kuma
tana tsaye tana dubansa
Jana'a suka soma dawowa bakin kogin daga
gudun tsira daga hallaka da suka yi.
Saboda ganin Muzaffar ya allaka wannan
Damisar da ta taso kansu.kuyangin Gimbiya ZUhuriya
suka karaso gare ta ta dube su tana mai yin tambaya
a gare su da cewa.
"Shin ko kun sani da wannan jarumi da ya
hallaka Damisar nan a cikin birnin nan? Hakika
jarumtarsa ta yi matakur bani mamaki.
10 harafi
Tafiyar ajali
Daya daga cikin kuyangin ta amsa mata da
cewa "Ranki ya dade ai babu abn mamaki cikin
lamarin Jarumtar wannan Jarumi don kuwa ya aikata
abin da yafi haka, shi ne Muzaffar dan babban
limamin birnin nan wanda labarin Jarumta da
bajintarsa ya gauraye ko'ina saboda karfin zuciya da
rashin fargaba ko tsoro na tunkarar kowanne irin
abin cutarwa komai gagara da shu'umancinsa".
Da Gimbiya ZUhuriya ta ji wannan bayani na
Kuyangarta. Sai ta sake jin begensa ya dada karuwa a
zuciyarta. Ta ga ya dace da irin namijin da take
muradin ya kasance miji a gare ta, sai dai ta yi
tunanin a ranta cewar kafin ta bayyana masa abin da
yake zuciyarta na daga begensa sai ta sake jarrabashi
dan ta ga irin jarumtarsa a fagen iya fada da takobi
da sauran makami da akeamfani da shi a wajen yaki.
Daga nan ta umarci kuyanginta su koma inda
suka daure dawakansu su kama su hau su nufi
hanyar komawa hanyar gida.
**
Bayan kwanaki biyar da faruwar wannan
al'amari gimbiya ZUhuriya tasa aka samo mata
sahihin labarin akan Muzaffar cewa yak an fita kilisa
bayan gari akan dokinsa cikin kowanne yammaci.don
haka ta yi shiri wata rana da yamma ta sanya
sulkedasauran kayan yaki ta rufe kanta da hular yaki
ta bakin karfe wadda ta kare fuskarta yadda ba za a
iya gane kowane ne ba.
Ta dauko takobi, kwari da baka, garkuwa da
sauran kayan fada ta daure a damarta sannan ta tafi
11 harafi
Tafiyar ajali
ta kama dokinta ta hau ta zagaya ta kofar bayan
gidanita ta fita ta kama hanyar bayan gari ita kadai
ba tare da wasu masu yi mata rakiya ba. Idan ka
ganta cikin shirin yaki da ta yi zaka yi zatan wani
hamshakin jarumi ne da ya fito dan karawa da
rundunar barada a fagen fama ba mace ce ba.
Ta yi tafiya mai nisa har ta isa kan mahadar
hanyar da aka ba ta labarin cewa Muzaffar yana
wucewa ta wajen, ta samu cikin duhun wasu itatuwa
ta shiga cikinsu, ta labe tana jiran tahowarsa ya zo
wuce ta wnanan hanya.
Bayan wani lokaci da zuwanta tana tsaye tana
jiransa, sai ga Muzzaffar tafe akan dokinsa ya biyo
wannan hanya zai wuce, yana sassarfa yana karowa
daidai inda Gimbiya Zuhuriya take labe sai ta fito
daga cikin duhun itatuwa ta sha kansa ta tare masa
hanya.
Muzaffar ya cika da matukar mamaki da ya ga
wani mahayi cikin shirin yaki ya bayyana a gabansa,
ya tare masa hanya ba tare da ya san ko wane ne ba,
ya ja linzmin dokinsa ya tsaya suka yi kallon-kallo
sannan sai ya ga mahayin nan ya zare takobinsa ya
taso kansa a fusace da nufin kai masa sara ya hallaka
shi.
Cikin azama da zafin nama Muzaffar yay i
sauri ya zare tasa takobin ya tari mahayin d abai san
kowanene shi ba a tsakanin sanda yake kokarin kai
masa sara. Suka yi arangama irin ta hamshakan
sadauka da sukeji da kansu a fagen jarumta da
kwarewa ta iya fada da makami kafin takubbansu su
12 harafi
Tafiyar ajali
jini yana daukarsa, mahaifinsa Waziri Hawaisu da ke zaman
jiran dawowarsa idan sun samu nasara hallaka Muzaffar ya
ganshi cikin wannan hali, ya taso cikin hanzari da gigita ya tare
shi Najiranu yana zuwa ya fada jikinsa ya suma, saboda
tsananin galabaita. Hankalin Haiwasu ya sake tashi, zuciyarsa
ta kidima ya shiga rudani da gigita, cikin sauri ya dauki dan
nasa Najiranu ya kais hi dakinsa ya kwantar da shi, ya yi kiran
wasu hadimai maza da ke yin hidima a gare shi suka taho gare
shi cikin sauri dan amsa umarninsa. Waziri Hawaisu ya sa su
suka cire sulken yakin da ke jikin Najiranu da rawanin da ke
kansa, aka wanke masa jini da ke jikin raunin dake kafadarsa
inda Muzaffar ya sare shi da gatari, sannan aka sama
masamagani.
Bayan wani lokaci Najiranu ya farfado daga suman da
yayi, ya soma dawowa hayyacinsa Waziri Hawaisu ya dan ji
sanyi a ransa saboda ganin dansa ya farfado daga Suman da
yayi. Da Najiranu y agama dawowa hayyacinsa sai ya kwashe
labarin dukkanin abin da ya faru tsakaninsu Da Muzaffar da
suka tafi gare shi domin hallaka shi, da kasa samun nasara da
suka y a kansa, har ya hallaka baradan da suka farmasa baki
daya.
Da waziri Hawaisu ya ji wannan bayani na dans
Najiranu sai ransa ya kara baci bakin ciki da takaici ya sake
yawaita a zuciyarsa. Ya dubi Najiranu y ace da shi.
Tun da har wadannan baradan sun kas samun nasara
akansa to kuwa zan hada shi da manyan bokaye masna
alkaluman sihiri dan su salwantar min da ruhinsa ya hallaka.
Don kuwa b azan bari ya samu nasarar auran gimbiya Zuhuriya
ba shirina na son mallakar masarata Birnin Ambar ta dawo
hannuna ya rushe, don haka na dauki alwakarin sai nag a
bayan wannan yaro na hallaka shi da salwantar da ruhinsa ko
ta wane irin hali.
Da Najiranu ya ji wannan bayani sai ya sake yin farin
ciki da matakin da mahaifinsa ya ce zai sake dauka akan
28 harafi
Tafiyar ajali
nasara akansa ba. Ta yi sauri ta fiddo da kwari da
baka ta zari kibiya ta saka ta harba masa ita da kanta
sai da ta yi garfabar irin harbin da ta yin a kwarewa
kada kibiyar ta same shi ta yi masa illa.
Amma sai ta ga Muzaffar ya sanya takobinsa
yak ad kibiyar ta tafi ta cake a kasa, ba ta same shi
ba. Ta ci gaa da zarar kibiyoyin tana harba masa shi
kuma Muzaffar yana sanya takobinsa cikin azama da
zafin nama yana kade kibiyoyin har sai da suka kare.
Da Muzaffar ya ga kibiyoyin sun kare sai ya
zabiri dokinsa cikin fusatuwa ya tasarma wannan
mahayi da nufin gamawa da shi, ita kuma gimbiya
Zuhiriya kafin ya iso gare ta sai ta yi sauri ta cire
hular karfen da ke kanta fuskarta ta bayyana. Yana
karasowa inda take sai ya ga wannan mahayi da suke
fafatawa da shi macece kuma wannan kyakkyawar
budurwa da ya taba gani a bakin kogi sanda ya kwaci
wani tsoho daga hannun damisa da tasar masa zata
hallaka shi.
Ya ja linzamin dokinsa yay i tirjiya a gabanta
ya tsaya ya dube ta yana mai mamaki wannan
al'amari ita kuma sai ta yi masa murmushi irin
wanda ya tabayi masa a haduwarsu ta farko da
sannan ta maida takobinta cikin kube da yake har a
wannan lokacin Muzaffar bai san kowacece it aba sai
ya yi mata Magana da cewa "Wacece ke,kuma mene
ne makasudin tunkarata cikin shirin yaki da nufin
hallakani, a hirdinki"
14 harafi
Tafiyar ajali
Cikin wannan batu Muzaffar bai zamo daga
mazajen da mace zata iya yin mubazzara da shi dan
samun nasara akansa ba.
Gimbiya Zuhuriya ta sake masa murmushi
sannan ta ce da shi, Ni ce Gimbiya Zuhuriya yar Sarki
Sa'adul gamidi dake sarautar wannan birni, kuma
ban tareka da nufin hallaka k aba said an na kara
jarrabaka na tabbatar da jarumta da bajintarka,
kamar yadda nake jin labarinka a dukkanin birnin
nan, tun ranar da na fara ganinka a sand aka kubutar
da tsohon da Damisa ta tasar ma hallaka shi a bakin
kogi, na tabbatar da cewa ka cika jarumi sai dai na
sake tareka a wannan waje dan nag a irin
kwarewarka a fagen iya fada da makami kamar
yadda na gani a yanzu.
Ta ciro wani zobe na azurfa daga hannunta ta
mika masa, sai da Muzaffar ya karba sannan ta ci
gaba da cewa.
"Zany i maka wani albishir akaina nay i
alkawarin cewa b azan auri kwanne namiji ba, dan
sarki ne shi ko attajiri