don ganin bayansa. Ва
zamu bari ya auri Gimbiya zuhuriya ba, don kada shirinka na
son mallakar sasautar birnin AMbar ya rushe, saboda haka zan
sanya a dauke shi daga birnin AMbar akai shi tsibirin Hihusiya
a ajiye shi a can baya ya halaka idan nay i imani da cewa idan
aka kais hi ba zai taba dawowa birnin AMbar ba har abada
kuma rayuwarsa ta kare kenan komai nisan kwanansa, saboda
Musaiba da ke tare da wannan tsiburi.
Nahiya ce da ke da matukar nisa daga wannan lardi
zuwa inda take har ma tsawon tafiyar shekaru goma akan
ingarman doki ba tare da yada zango ba. Kuma waje ne da
yake tare da matukar hadari, unci da musiba iri daban daban
yadda babu wani mahaluki daga jinsin mutum ko aljani da zai
iya fitowa daga cikin wannan tsibiri idan aka kais hi ba tare da
ya hallaka ba.
Idan aka kais hi wannan tsibiri aka batar da shi shi
kenan aka samu damar dan kai zai auri Gimbiya Zuhuriya ka
samu nasarar hallaka Sarki Sa'adulgamidi sarautar birnin ta
dawo hannunka"
Ya sa hannu ya dauko wata yar karamar batta an rufe
bakinta da bakar fata ya mikawa waziri Hawaisu y ace da shi.
31 harafi
Tafiyar ajali
"Ka tafi da wannan battar ka ajiye a gefen hanya dai
dai inda wannan Jarumi da kake so a hallaka yake wucewa,
battar tana tare da abubuwa ta a ajibi da ban mamaki na daga
alkaluman sihirina a cikinta, kuma akwai wani bakin ifiritu da
ke yin hidimaa gare ta da ke cikin battar, ka kiyaye kada ka
sake ka bude battar hark a kaita inda wannan jarumi yake
wucewa ka ajiye ta, idan har wannan Jarumi ya ganta babu
shakka zai ce zai je inda take dan ya dauka ya ga abubuwan
al'ajabin da yake tare da ita. Idan har ya sake ya buxe wannan
batta to kuwa bakin ifiritun da ke cikin batttar zai fito daga
cikinta ya dauke shi ya tafi da shi, kuma ba zai aje shi a ko in
aba sai a wannan tsibiri na Hijusiya da zai hallaka a can ba zai
sake dawowa wannan birni ba har abada.
Waziri Hawaisu ya karbi battar cikin matukar murna da
farin ciki tare da yin godia ga boka Musaila sannan ya tambaye
shi abin da yake bukata nadaga dukiya da zai bashi a matsayin
ladan aikinsa.
Boka Musaila ya ce da shi "Bana bukatar komai daga
gareka na daga dujiya a matsayin ladan aikin da zany i maka,
illah dai zan aikata wannan aiki ne dan ka samu nasarar
hallaka Sarki Sa'ad sarautar birni ta dawo hannunka, saboda
kiyayyar da take tsakanina da shi sakamakon cin mutumcin da
yay i min na kora ta daga birnin AMbar da sauran bokaye yan
uwana.
Abin da nakebukata daga gare kakawai shi ne idan danka ya zama sarkia birnin AMbar to kuwa ni zan zama
wazirinsa, kada ka yi hange ga yawan shekarako tsufana,
aikata hakan shi ne zai san a tabbatar da biyayyar jama'ar birnn a gare shi,ta hanyar karfin tsafi da sihiri na, kuma
wannan shi ne kawai abin da nake bukata daga gareka a
matsayin ladan aikina".
Da waziri Hawaisu ya ji wannan bayani babu ayayya sai ya amince da sharadin da boka Musaila ya kafa masa, ya
sake jadda godiyarsa a gare shi sannan ya tashi ya fice daga
Σ
32 harafi
Tafiyar ajali
bukkar ya bar Boka Musaila. Ya tafi ya kamadokinsa ya kama
hanyar komawa gida
Da isarsa gida yayi kiran dansa Najiranu ya sanar da shi
abin da ya faru tsakaninsa da Boka musailamatu, sannan ya
bashi wannan batta da boka ya bashi y ace da shi ya tafi ya
ajiyeta a gefen hanyar da Muzaffar yake wucewa. Najiranu ya
karbi battar cikin matukar murna da farin ciki sannan yay i
shiri don tafiya ya kai battar kan hanyar da Muzafar yake
wucewa idan lokacin wucewarsa yayi.
**
A wannanrana da yammaMuzaffar yay i shiri don
tafiya bayan gari kilasa kamar yadda ya saba, yana fitowa zai
kamadokinsa yah au sai ga mahaifinsa Liman Adnan ya shigo
gidan ya dubi Muzaffar ya ga irin shirin da yay i na fita Kilisa
hadda sulken yaki da takobi tamkar wanda zai tafi kafsa yaki a
faen fama,saboda shirin ko ta kwana da yake yi.
Tun daga ranar da baradan nan suka tare shi a bayan
gari suka tasar masa da niyar hallaka shi da Liman adnan ya ga
irin wannan shiga da yayi, sai yay i kiran Muzaffar dan yi masa
nasiha yanamai cewa da shi.
"Zan yi nasiha a gare ka dank a zama mai kiyaye
rayuwar duniya abin da yake cikinta, ka da ka sake ka shiga
abin da bai shafeka ba matukar ba taimako za kayi gad an
uwanka musulmi ba, ka guji duk wani abin hadari ko na
cutarwa da zai iya kai ka ga hallaka kada jarumta da jin karfi na
kuruciya su rike dibar ka kana tunanin cewa kai mai iya samun
nasara ne akan komai,ka da k ace zakat aba duk abin da baka
san mafarinsa ba, ko ka zama mai yawan tambaya a cikin
lamarin daba shi da nasaba da rayuwarka".
Da ya gama yi masa wannan nasiha sai Muzaffar yayi
godiya ga mahaifinsa, sannan ya tashi ya tafi ya kama dokinsa
yah au ya fita ya kama hanyar fita bayan gari. Yayi iyatafiya
mai nisa akan dokinsa cikin sassarfa har ya iso wani waje da
manyan bishiyu masu wadatar rassa da inuwa mai sanyi
suke.ya hangi wasu kyawawan tsuntsaye suna raira kuka mai
33 harafi
Tafiyar ajali
dadin saurare tare da tashi daga wannan reshe ya zuwa
wancan resi ya ja linzamin dokinsa ya tsaya yana duban
waadan nan tsuntsaye cikin nishadi tare da jin dadin kukan da
suke rairawa. Sannan ya sake sakin linzamin dokinsa ya cigaba
da tafiya.
Bayan yayi tafiya mai nisa daga inda ya fara tsayawa
sai ya hangi wata batta ahiye a gefen hanya kusa da inda zai
wuce, battar tana haske da walwali shekinta yana daukar ido
tamkar madubi, wani Karin abin mamaki shi ne da ya matsa
kusa da battar sai ya ga ba a jiye take akan doron kasa ba, tana
tsaye ne a tsakanin sama da kasa, kan iska ba are da ta dogara
da wani abu ba, kuma bata fado kasa ba. Yaja linzamin dokinsa
yatsaya yana duban battar cikin matukar mamaki da ta'ajjibi
na faruwar wannan al'amarimai kama da aikin sihiri.nan take
sai ya ji zuciyarsa na sha'awantuwa da son ya je ya daukoo
wannan batta ya bude dan ya ga abin da yake cikinta. Ya kuma
san yadda aka yi har take tsaye akan iska ba tare da ta fado
kasa ba.
Ya sauk daga kan dokinsa ya nufi wajen da battar take,
da zuwansa ya kai hanu zai taba battar ba tare da wani tsoro
ko fargaba kamar daga sama sai yaji wat amurya mai matukar
amo da hauhawa tana cewa da shi.
"Kada ka sake kataba wannan batta da ke gabanka
hallaka zata tabbata a gareka matukarka sake ka taba ta".
a Muzaffar ya juyo cikin sauri bai ga mai yin maganar
gare shi ba, ya duba kowannen bangare daga sashin da yake
tsaye bai jikoda motsin wani a kusa da shi ba bare ya ga mai
yin maganar,don haka sai ya sake kai hannu zai taba battar
muryar ta sake cewa da shi "Ka zama mai biyayyar umarnin
don kaucewa abin da zai iya kai ka ga hallaka ka guji tabа
wannan batta idan ba so kake ajali ya gabata a gare k aba".
Muzaffar ya sake dakatawa yana sauraren muryar da
baya ganin mai ambatonta, sannan yayi Magana da cewa "Da
zan iya ganin ma'abocin wannan furuci da na fi yadda da
gasgata abin da yake ambatawa, shin wanene ne kai kuma
シ
34 harafi
2
Tafiyar ajali
daga wane jinsi kakasance mutum ko kuma aljan? Ka sani
cewa nay i imani da Allah mahaliccin rayuwa da muttuwa,
tare da gasgata cewa babu wani abin halitta idan bas hi ba,
saboda haka ban zamo daga mutanen da za a bawa tsoro
korazani da ikirarin tabbatar da hallaka akan sub a".
Yana gama fadar wannan Magana sai ya kai hannu zai
dauki battar muryar ta sake daka masa tsawa, don kada ya
taba amma hakan bai hana shi aikata abin da zuciyarsa ta yi
niyar bay a sa hannu ya daui battar da ke tsaye akan iska
sannan ya bude bakar fatar da ke rufe da bakinta dan ya ga
abin da yakeciki.
Da budewarsa sai ya ji wata irin kara mai tsananin amo
da hauhawa ta gauraye wajen, wani irin bakin hayaki ya taso
daga cikin battar ya turnuke ya rufe ko ina a tsakanin inda
suke, aka sake yin wata tsawa da rugugi mai matukar karfi da
ban firgici sannan daga cikin hayakin sai ga wani bakin ifiritu
ya bayyana a gaban Muzaffar tae da wannan rugugi da yake ji.
Ifiritun na da matukar girmada munin gani idanunsa yayi
jajawur tamkar garwashin wuta, yana da kaho a tsakiyar kansa
wani irin bakin gashi ya lullube fatar jikinsa gaba daya yayi
karaji da gunji mai matukar karfi da ban firgici feshin burbudin
wuta yana fita daga bakinsa.
Dajin yay i amsa kuwa da amo mai hauhawa kasa ta yi
girgiza a raurawa mai karfi tamkar za ta tsage dukkanin abn da
ke wajen ya nutse cikinta.
Muzaffar yaja da baya dan ganin abin da ya bayyana
gare shi,cikin azama da karfin zuciya iri na jarumta ya kai
hannunsa kan damararsa da nufin zare takobinsa amma sai
yaji babu takobinsa ya barota a jikin sirdin dokinsa.ya jyya a
hanzarce da nufin komawa inda dokinsa yake da nufin dauko
takibin sai dai kuma kaddara ta riga yi muradi cikin lamarinsa,
kafin ya kai ga inda dokinsa sa yaketuni bakin ifiritun nan ya
taho gare shi, ya wafci Muzaffar ya daue shida sasari, annan ya
sake yin wani karaji da yafi wanda yayi da farko karfi da amsa
kuwa,duhu mai tsananin ya lullube wajen sannan ifiiritun ya
35 harafi
Tafiyar ajali
suri Muzafar ya tashi da shi sama ya luluka da shi cikin
gajimare ya kama hanyar tsibirin Hljusiya inda aka umarce shi
da ya kai duk wanda ya buxe wannan batta da yake ciki.
Muzaffar yayi iyakacin kokarinsa ya kufce daga daurin
da akayi masa amma yai ya kasa koda motsa sasarin da aka
daure shi da shi bare ya sa ran kubuta. Tun yana iya ganin abin
da yake faruwa gareshi har numfashinsa ya daukebai sake
sanin abin da yake faruwa gare shi ba.
Ifiritun nan yay i tafiya mai nisa da Mzaffar har ta
tsawan kwanaki biyar irin tafiya ta manyan ifirita da suka fi
komai sauri akan iska, sannan ya isa tsibirin Hijusiya inda aka
umarce shi ya kai Muzaffar ya jefar da shi a tsakanin wasu
tsaunukacikin kwazazzabai ya kwance sasarin da ya daure shi
Muzaffar yana cikin halin suma bai san abn da yake faruwa
gare shi ba sannan ya sake tashi sama akan iska ya kama
hanyar komawa inda ya fito
Duk abin da yake faruwa akan Muzaffar lokacin da
Ifiritun nan ya bayyana gare shi, Najiran dan gidan Waziri
Hawaisu yana labe cikin wani duhu itatuwa da ke kusa da
wajen da ya ga Muazaffar ya bude wannan battar Ifiritun nan
ya dauke shi ya tafi da shi sai ya cika da murna d afarin ciki ya
fito daga ida yake boye yah au dokinsa ya kamahanyar
komawa gida.
Yana zuwa ya sanar da mahaifinsa dukkanin abin da ya
gani akan idanunsa. Waziri Hawaisu shi ma yayi matukar
murna da fari ciki saboda ganin sun samu nasara akan
Muzaffar suna masu tunanin cewa ya hallaka har abada Boka
Musalamatu ya sanar da Waziri
**
Shi kuwa muzaffarbai farka daga suman da yayi ba sai
bayan tafiyar wannan ifiritu da ya kawoshi wannan waje, da
kusan sa'a guda da ya farfado ya dawo hayyacinsa ya tashi
zaune ya ganshi a wani bakon waje a gareshi tsakiyar daji da
bai san wajen ba. Sai ya karewa wajen kallo babu komai sai
manyan tsaunuka da kwazazzabai kuma hatta sararin
36 harafi
Tafiyar ajali
samaniyar da ke wajen ya banbanta d airin yadda ya saba
ganin launin sararin samani tsawon rayuwarsa sararin saman
yayi duhu gajimaran dake tafiya akan iska ya yi jajawur tamkar
zai zubo da tafasasshen ruwan zafi. Ya dubi wajen da yake
zaune, nan takeya shiga halin kidima da rudani saboda abin da
ya gani, babu komai a wajen sai tarin kasusuwan gawarwakin
muane da suka dade da hallaka awajen
Muzaffarya mike tsaye cikin sauri yana duban
kasusuwan gawarwakin cikin tsoro da razana hankalinsa yayi
matukar tashi da abin da ya gani, sannan sai yaji wata kurya
mai matukar karsashi da rashin dadin saurare tana cewa da
shi.
Hallaka ta gabata gareka ya kai wannan bil'adama
sababin shigowarka wannan waje, kuma wannan waje da
kake cikinsa shi ne tsibirin Hijusiya inda duk wani ruhi na
bil'adama da ya shiga cikinsa kan salwanta, don haka babu
wani mahaluki bil'adama kamar ka da ya taba shigowa cikinsa
ya fitabatare da ya hallaka ba, ka yi duba zuwa kasusuwan
gawarwakin da zaka ya iya gani a wannan waje na mutane ne
bil'adam kamarka da akakawosu wannan tsibiri suka
hallaka,tun shekaru masu yawa da suka gabata kamar yadda
kai ma zaka hallaka yanzu a cikinsa.
Wannan shi ne karshan mai jin kai da kafiya ta son
aikata abin da zuciyarsa ta kuduru da son aikatawa.hakika da
kabi umarnin mai Ambato da ya haneka da taba wannan
battar da ka taba to da kuwa b aka kasance cikin wannan
al'amari da ka riske kanka a cikinsa ba"
Ana gama fadar wannan Magana sai ya ji an kyakyace
da dariya cikin wata kakkausar murya marasa dadin saurare,
harowar muryar tayi amsa kuwa da amo mai hauhawa da ya
gauraye dukkanin dajin sai da aka dauk lokaci mai tsawo ana
kyakyata wannan dariya sannan muryar ta tsagaita da dariya
daga nan bai sake jin komai ba.
Muzaffar yayi shiru yana tunanin abin da wannan
murya ta ambata a gare shi, ya duba gabad da yamma bai ga
37 harafi
Tafiyar ajali
wata hanya da zai bi ba, ko kuma wata alama da za ta sada shi
da inda zai riki inda gari ko wasu jama'arsuke ya rasa inda zai
nufa daga wajen da yake tsaye. Ya hangi wasu kananun
dawatsu a kusa da ind ayake yayi tunanin ya je yah au kan
daya daga cikinsu ya duba ko zai hangi wani gari ko hanyar da
zata sada shi da wai bigiri da zai riki inda jama'a suke yayi
tambayar a gare su ko zai samu wanda zai sanar da shi hanyar
da zai bi ya koma birnin Ambar.
Ya tafi yah au kan daya daga cikin wannan duwatsu ya
duba iyakacin ganinsa bai ga wata hanya da za ta kaishi inda
zai riski jama'a ba, ko ina ya duba daji ne kawai mai matukar
sarkakiya da duhu mara masaltuwa, wani abu da ya kara sanya
shi fargaba shi ne bai ji ko da kukan tsuntsu ba, bare ya sa ran
akwai wata halitta da ke da rai a cikin dajin.
Ya dade a wannan waje yana tunanin da sake-sake
cikin zuciyarsa, daga karshe sai ya yanke shawarar ya sauko
daga kan dutsan ya bi hanyar da ta yi kudu ya ci gaba da tafiya
cikin hasashe ko zai riski inda wasu jama'a suke zaune cikin
wannan daji, idan kuma bai hadu da kowa bay a ci gaba da
tafiya har zuwa inda hallaka zata rike shi cikin dajin idan Allah
bai nufe shi da komawa gida ba
Yana gama wannan tunani ya sauko dag akan dutsan
ya kama hanya ya bi bangaran kudu ya ci aba da tafiya cikin
sarkakiya da duhun itatuwa babu abin da yake gani sai
kasusuwan gawarwakin mutane da suka dade da hallaka a duk
inda ya ratsa.
Tun da sanyin Safiyar ya soma wannan tafiya, amma har sai da rana ta kusa faduwa bai gama da ko da tsuntsuba
daga cikin halittun da ke rayuwa a dajin ga tsananin yunwa da kishirwa da ya soma addabarsa, kuma bai riki koda rafi ba a
gabansa,bare ya sa ran samun inda zai samu ruwa, sai dai idan lokacin sallah yayiyayi taimama ya gabatar da sallarsa ya ci gaba da tafiya a cikin dokar daji.
San da rana ta gama faduwayunwa da kishirwa sun
gama cikin karfin Muzaffar ga gajiyar tafiya da ta gama
シ
38 harafi
Tafiyar ajali
galabaitar da shi.yana zuwa cikin wasu kwazazzabai sai juwa ta
soma daukarsa saboda jigata daga nan ya fadi kasa ya suma.
**
Can kuwa a birnin AMbar bayan da dare yay i
mahaifan Muzaffar suka ga bai dawo gida ba, sai suka shiga
nemansa an tura yan uwansa duk inda ake zaton za a riske shi
amma ba a samu koda labarin wanda ya ganshi ba, tun bayan
fitarsa da yamma hakamaafan Muzaffar sukakwana cikin
fargaba da zulumin rashin sanin inda ya shiga.
Da gari yaw aye aka saketura yan uwan Muzaffar
nemansa ko za su yi dace a gabansa amma har rana tafadi dare
yayi babu shi babu labarinsa.mahaifinsa ya sake shiga halin
damuwą da fargaba saboda rashin ganinsa, kuma da yake sun
san halin shu'umanci da hatsabibancinsa sai suka rika fargabar
ko wani abu ne na cutarwa ya sameshia fitar da yayibayan gari
cikin wannan yammaci.
Washe gari da safe a rana ta biyu da bacewar Muzaffar
wani matafiya ya zo da labarinsa cewa ya gawani farin doki da
sirdi akansa yana yawo a daji amma bai ga mahayin dokin ba.
Mahaifin Muzaffar ya turo aje a gani ko dokin Muzaffar ne da
zuwan yan uwan Muzaffar suka ga cewa babu shakka dokinsa
ne suka shiga nemansa a dukkanin wajen amma basu ga koda
sahunsa ba, bare ssu san inda yake, suka yi ta nemansa har
rana ta fadi basu ganshi ba. Da suka gaji da nemansa sai suka
kama dokinsa suka tafi da shi gida suka sanar da mahaifinsu
cewa dokin Muzaffar ne, amma sun yi dukkanin nemansa basu
ganshi ba.
Hankalinmahaifin Muzaffar ya kara tashi, suka sake
shiga fargaba da tararradin halin da yake ciki,aka ci gaba da
ttura yan uwansa nemansa har tsawon kwanaki biyar, amma
ba a sam ukoda labarin wanda ya ganshi ba, daga karshe sai
mahaifinsa ya hakura da tura yan uwansa nemansa ya
mikalamarin ga Allah yana mai addu'ar Allah ya bayyana inda
Muzaffar yake idan har yana raye a duniya.
39 harafi
Tafiyar ajali
Bayan wasu kwanaki labarin bacewar Muzaffar ya
cikako'ina a birnin AMbar saboda shaharar da Muzaffar yay i
wajen jarumta da rashin tsaro.maganar bacewar ta tafi ta kai
har unnen Gimbiya ZUhuriya da ta samu wannan labara
hankalinta yay i matukar tashi, ta shiga damuwa da fargabar
halin da masoyinta Muzaffar yake ciki. Daga karshe ta shiga
addu'a da fatan Allah ya bayyanashi a duk inda yake inda har
yana raye.
**
Al'amarin Muzaffar kuwa bayan da ya fadi cikin
wannan kwazazzabai ya suma,bai farka daga suman da yayi ba
sai bayan wayewa gari ya farfad daga suman da yayi, a lokacin
rana ta fito haskenta ya gauraye ko ina, ya yunkura da kyar ya
tashi saboda tsananin yunwa da kishirwa ga kuma galabaita da
yayi, ya tashi ya soma takawa da kyar yana rangaji saboda
jigata.
Can daga gabansa sai ya ji wat airin tsawa tare da
rugugi mai tsananin karfi da ya gauraye dukkanin dajin tamkar
tasowar hadari, wata irin bakar iskadake cudanyeda guguwa
mai karfi suka tasu suka rufe dukkanin wajen duhu ya gauraye
ko'ina mafi tsananin daga yankin duhu dare sannan sai
Muzaffar ya ji kasa ta somagirgiza da raurawa tamkar zata
tsage ya nutse a cikinta. Daga nan kuwa sai ya ga wani irin
bakin ififiitu ya bayyana a gabansa yana da matukar girma da
muni na firgita,duk wani bil'adama da ya ganshi hannunsa rike
da wani almudi nab akin karfe jajawur da shi tamkar karfan da
aka ciro daga wutar makera.
Ifiritun nan ya dubi Muaffar yana wani irin huci da
gunji irin na fusatuwa, iska mai zafi tana fitowa daga cikin
hucin da yake yi tana bugun jikin Muzafffar yana jin tamkar
ana kona shi da wuta, sannan ya daga kansa sama yayi karaji
da kururuwa mai tsananin karfida ban firgici da ta yi masa
kuwa da amo mai hauhawa da ya gauraye dukkanin dajin, ya
daga almudin da ke hannunsa y ataso kan Muzaffar a fusace
yana wannan karaji da gunji wuta daga bakinsa ya nufe shi da
40
Tafiyar ajali
nufin narka masa bugu da wannan almudu da ke hannunsa ya
hallaka shi.
TAFIYAR AJALI @
Muzaffar yay i maukar gigita da razaa da ganin wannan
ifiritu da ya taso gareshi a fusace da nufin hallaka si, gas hi
baya tare da wani makami da zai iya tunkarar wannan ifiritu
da shi bare yayi kokarin karr kansa, yay i nufin juyawa ya gudu
daa inda yake amma sai ya ji ya kasa koda motsi bare ya sami
damar guduwa tamkar wanda kasa ta rike, da ya ga babu
mafita cikin lamarinsa hallaka na shirin tabbata a gare shi sai
yay i Kalmar shahada ya mikalamarinsa ga ubangiji yana mai
saurare da jiran abin da zai wanzu gare shi, na hallaka da yak e
tunanin zai ta kasnace a kansa cikin wannan lokaci.
Ifiritun yana isa gareshi ya kai masa bugu da
al'amudun bakin karfen da ke rike a hannunsa, kafin al'admun
ya sauka a kan Muzfffar sai wani farin haske ya keto daga
tskanin duhun itatuwan da ke kusa da wajen cikin tsananin
sauri mafi sauri daga tafiyar harbin kibiya,ya bugi jikin ifiritun
nan d akarfi tamkar jifa da mashi, Ifiritun yayi wata
kadaitacciyar kara mai tsananin karfi da ban firgici da tayi
amsa kuwa da amo mai hauhawa, gaba daya dajin ya amsa
sannan karfin bugun da hasken yayi masa ya daga shi sama
akan Iska ya jefar da shi gefe, karfin karar da ifiritun yayi ta
sanya shima Muzafar ya yanke jiki ya fadi kasa sumamme.
suman da Bayan wani lokaci Muzaffar ya farfado daga
yayi tamkar wanda aka shafawa ruwa ya duba jikin rigarsa ya
ganta a jike alamar an zuba masa ruwa a lokacin da yake cikin
halin suma. Ya dubi wajen da yake sashi szuwa sashi bai ji
koda motsi ba, bare yay i tunain wani ne ya kawo dauki gare
shi, ya taimaka masa. Ya dubi bangaren da Ifiritun nan ya fadi
ya gay a kama da wuta yak one kurmus ya zama tka, hatta da
al'amudin bakin karfen da yake haunsa ya narke babu shi, ya
duba bangaren da hasken nan ya keto ya bugi jikin Ifiritu ya ga
babu wata alama da zai iya tantance abin da ya hallaka
41 harafi
Tafiyar ajali
wannan Ifiitu, yayi godiya ga Allah da ya kubatar da shi,daga
hallaka duk bai san abin da ya hallaka wannan Ifiritu ba.
Ya juya zai tashi ya ci gaba da tafiya sai ya ji hannunsa
ya taba wani abu a agefensa na dama ya duba wajen sai ya ga
wani karamin akushi tare da salkar ruwa a ajiye a kusa da shi,
mamaki ya wanzu cikin zuciyarsa mafi girman mamaki ya sa
hannu ya bude akushin sai ya ganshi makare da abinci yana
tiriri alamar ba a dade da gama dafashi ba, mamaki yya sake
karuwa a gare shi ya duba dukkan wajen bai ga koda sahun
mutum ba bare yay i tunanin wani bil'adama ne ya gabato da
wannan abinci a gareshi da yake Muzaffar yana cikin halin jin
matsananciyar yunwa da take addabarsa, sai kawai yay i
bismillah ya sa hannu ya soma cin abinci ba tare da wani tsoro
ko fargaba ba.
Ya ci gaba da dibar abincin yana ci amma har sai da ya
koshi, ba tare da abincin ya ragu ba, bare alamar zai kare, ya
dauki salkar ruwa ya shay a koshi itama yana dauketa daga
bakinsa sai ya ga ruwan ya sake cikowa tamkar ba daga cikinta
ya sha ruwan ba, mamaki ya karu gareshi cikin wannan
al'amari yayi ta tunani da sake-sake cikin zuciyarsa.
Bayan wani wa'adi mai tsawo da gama cin wannan
abinci ya huta sosai ya samu nutsuwa sai ya yanke shawarar ya
tashi ya ci gaba da tafiya cikin wannan daji ko zai riski wata
alkarya a gabansa ko kuma ya hadu da wasu jama'amatafiya
yayi tambaya a gare su koza a samu wanda ya san hanyar da
zai bi ya koma birninnsu da zai ci gaba da tafiya sai ya dauki
akushin abinci tare da wannan salkar ruwa dan yin guzuri da
su tunda abincin da ke ciki tare da ruwan basu kare ba, kuma
gas hi baai san inda zai sake samun wani abincin ba a cikin
wannan dajin.
Ya ci gaba da tafiya yana keta duhun itatuwa tsaunuka
da kwazazzabai a cikin wannan bakin daji ba tare daya hadu da
wata halitta dake da rai ba koda dabba bare ya ga mutum
bil'adama a cikin sa da rana ta yi zafi sosai Muzaffar ya sake jin
yunwa ya tsaya a bude akushin nan ya ci abinci ya koshi ba
42 harafi
W
d
Q
O
Z
t
Tafiyar ajali
wannan Ifiitu, yayi godiya ga Allah da ya kubatar da shi,daga
hallaka duk bai san abin da ya hallaka wannan Ifiritu ba.
Ya juya zai tashi ya ci gaba da tafiya sai ya ji hannunsa
ya taba wani abu a agefensa na dama ya duba wajen sai ya ga
wani karamin akushi tare da salkar ruwa a ajiye a kusa da shi,
mamaki ya wanzu cikin zuciyarsa mafi girman mamaki ya sa
hannu ya bude akushin sai ya ganshi makare da abinci yana
tiriri alamar ba a dade da gama dafashi ba, mamaki yya sake
karuwa a gare shi ya duba dukkan wajen bai ga koda sahun
mutum ba bare yay i tunanin wani bil'adama ne ya gabato da
wannan abinci a gareshi da yake Muzaffar yana cikin halin jin
matsananciyar yunwa da take addabarsa, sai kawai yay i
bismillah ya sa hannu ya soma cin abinci ba tare da wani tsoro
ko fargaba ba.
Ya ci gaba da dibar abincin yana ci amma har sai da ya
koshi, ba tare da abincin ya ragu ba, bare alamar zai kare, ya
dauki salkar ruwa ya shay a koshi itama yana dauketa daga
bakinsa sai ya ga ruwan ya sake cikowa tamkar ba daga cikinta
ya sha ruwan ba, mamaki ya karu gareshi cikin wannan
al'amari yayi ta tunani da sake-sake cikin zuciyarsa.
Bayan wani wa'adi mai tsawo da gama cin wannan
abinci ya huta sosai ya samu nutsuwa sai ya yanke shawarar ya
tashi ya ci gaba da tafiya cikin wannan daji ko zai riski wata
alkarya a gabansa ko