mai godiya ga Allah tare da jin
dadin irin taimakon da dattijon Mubashhir yayi masa
wand aba don shi ba da tuni ya hallaka a cikin
wannan tsibiri da aka kawoshi don ya hallaka.
Ya ci gaba da tafiya ya mike hanya
kamaryadda aka umarce shi sallah da cin abinci ne
kawai ke tsayar da shi sai dai wani lokacin idan yay i
matukar gajiya ya yada zango ya kwana da haka har
ya shafe tsawon kwanaki uku da yini daya sannan ya
isa inda wannan Bukka take a tsakanin wasu manyan
tsaunuka kamar yadda Dattijo Mubasshirya sanar da
shi.
Da isar sa wajen sya karasa kusa da bukkar
yay i salama aka amsa masa ba tare da wani jinkiri
ba, yana shiga ya tadda wani dattijo zaune akan
wata karaga yana jan tasbaha, kamar yadda ya tadda
dattijo Mubassshir a cikin kogon dutsen ya sameshi
kuma yayi matukar kama da dattijo Mubashhir
tamkar wa da kani,sai dai bai kais hi tsufa da yawan
shekaru ba, Muzaffar ya matsa kusa da shi ya dauko
57 harafi
Tafiyar ajali
zoben da dattijo Mubasshir ya bashi ya mika masa ba
tare da ya sakeyin Magana ba, Dattijon nan ya karba
ya rikezoben a tafin hannunsa yana dubansa har
zuwa tsawon wani lokaci sannan ya dago kansa ya
dubi Muzaffar y ace da shi.
"Yaro nag a sakonk ada kazoo da shi da abin
da ya kawo ka gare ni,don na taimakamakana fitar
da kai daga wannan tsibiri na maida kaii birninku
kamar yadda dan uwana da ya turo ka gare ni ya
nemi alfarmar na taimaka maka, kuma ka yi sa'a
gobe zanyi tafiya daga wannan tsibiri ya zuwa
alkaryar mutane bil'adam har kusa da birninku don
haka zan taimaka maka na tafi tare da kai na kaika
birninku, idan da ni kadai ne zan yi wannan tafiyar
zan gama ta ne baki daya a cikin kwanaki goma, sai
dai da yake yanzu zamu yi tafiyar tare d akai sai mun
shafe sawon kwanaki saba'in da biyar kafin mu fita
daga wannan tsibir mu isa birninku,saboda ba zai
yiwu na dauke kaa kaina na fitar da kai daga wannan
tsibiri ba, dole ne sai mun yi tafiya da kafa kuma idan
mutum bil'adama ne irin ka zaiyi wannan tafiya shi
kadai sai ya shafe tsawon shekaru goma akan
ingarman doki idan yay i sa'a bai hadu da wani abin
cutarwa ya hallakashi a cikin wannan tsabiri ba,
sannan ya umarce ni cewa na sanar da kai yadda z
aka yi amfani da ita saboda haka z aka zauna a nan
tare da ni kafin gari ya waye, mu fara wannan tafiya
tae da kai sai dai zan gargadekatare da sanar da kai
sharuda da nake so ka kiyaye cikin wannan tafiyada
58 harafi
Tafiyar ajali
zamu yi tare da kai matukar kana son na
taimakamaka na maida kai birninku".
Da farko dai ban a son yawan tambaya cikin
lamarina duk abin da ka ga na aikata ko kuma na
umarce ka da ccewa ka aikata kada ka sake ka
tambaye ni, saboda me yasa za a yi haka kuma ka
kiyaye kada ka sake ka aikata duk wani abu da ban
umarce ka da aikatawa ba, idan ka kiyaye wadannan
sharuda da na sanar da kai cikin tafiyar da zamu yi
tare da kai ta tsawon kwanaki saba'in da biyar. O
kuwa zan taimaka maka na fitar da kai daga cikin
wannan tsibiri na maida kai birnin ku idan kuwa ka
kuskure ka kasa cika sharudan da na sanar d akai to
kuwa zan tafi na rabu da kai ka halaka b azan
taimaka maka ba, said aka yi hattara".
Da y agama yi masa wannan bayani Muzafar
ya amsa da cewa ya amince kuma zai kiyaye da abin
da ya sanar da shi, daga nan ya daowa Muzaffar da
zobensa gare shi,ya kumasanar da shi sunansu
Zarkiyul ambas tare da nuna masa shimfidar da zai
kwanta kafin gari ya waye su fara tafiya.
Da gar yaw aye, bayan sun kamala shirin
tafiya Zarkiyul Ambas ya kawo wani takalmi na gata
ya bawa Muzaffar y ace da shi "Ka sanya wannan a
kafarka da shi ne za mu yi dukkanin tafiyar da zamu
yi har mu isa birninku, kuma kada ka sake ka cire shi
daga kafarka idan ba lokacin kwantawa barci ba, ko
mu ma wani uziri da ya zama dole ka cire shi ba".
Muzaffar ya karbi takalmin ya sanya a kafarsa
daga nan sukafita daga cikin bukkar suka kama
59 harafi
Tafiyar ajali
hanya, suka soma tafiya cikin wannan bakin daji
suna keta duhun itatuwa da sarkakiya, kuma tun da
suka baro inda wannan bukka take basu hadu da
wata halitta da ke da rai ba, daga jinsin dabba
kokuma tsuntsu sannan babu wani abu dake tsayar
da su ban da sallah da cin abinci, sai dai idan dare
yay i Muzaffaryagaji da tafiyar da sukeyi su yada
zango don su kwana, kafin gari yaw aye su ci gaba da
tafiya. Da haka har sukashafe tsawon kwanaki biyar
cikin tafiyar da suka fara ba tare da sun hadu da wani
abin cutarwa ba, ko kuma wanda zai tsayar da su
akan hanyar su.
A rana ta shida cikin ranakun tafiyarsu ne suka
iso wani waje a cikin wannan tsibiri mai matukar
duhu mafi tsaanin daga yankin duhun dare ga hayaki
ya turnuke ko ina daga cikin duhu,da isar su wajen
sai Zarkiyu ya dubi Muzaffarya ce da shi.
"Kana da masaniyar cewa za u hadu da
miyagun halittu a cikin wannan tafiya da muke yi
wanda dole sai mun yi yaki da sum un hallaka su
kafin mu samu damar wucewa don isa birninku?
Kuma daga cikin wannan bakin daji dake
gabanmu ne zamu fara haduwa da s har zuwa ranar
da zamu fita daga cikin wannan tsibiri mu isa
alkaryar mutane bil'adama, kuma ka sani cewa duk
halittar da z aka gani a cikin wannan tsibiri ba irin
halitun dake cikin mutane bil'adamabane don
hakaka kasance cikin shiri kuma ka kiyaye da abin da
na sanar da kai."
60 harafi
Tafiyar ajali
Da y agama yi masa wannan bayani sai ya zaro
wata takobi dake daure a damararsa da akwai
sauran takobi tare da mashi da kuma ragowar
mamai na yin fada a tare da shi Zarkiyu amma bai
baw Muzaffar ko daya daga cikin makaman ba, don
yay i amfani da shi, wajenkare kansa ko yin artabu da
halittun da za su hadu da su a ciikin wannan waje da
zasu shiga sai ya tafi jikin wata bishya da ke kusa da
su ya sanya takobinsa ya saro reshin biyar ya
fekeshi,kamar tsinin mashi sannan ya mikawa
Muzaffar yace da shi "Ka rike wannan itace ka yi
amfani da shi wajen kare kanka da yin fada da
halittun da zamu hadu da su a cikin wannan waje
zamu shiga har zuwwa lokacin da zamu isa inda ya
kamata na sanar da kai yadda z aka fara amfani da
takobin da ke tare da kai".
Muzaffar yay i mamakin wannan al'amari ya
dubi Zarkiyu y ace da shi "Me yasa ba z aka bani
takobi ko kuma daya daga cikin makaman dake tar
da kai ba,don na kare kaina sai dai ka bani wannan
itace da b azan iya kare kaina da shi ba, kamar yadda
zan iya kare kaina da takobi ko kuma daya daga cikin
makaman dake tare da kai".
Zarkiyu ya juya ya dube shi y ace da shi "Ai
dama tun a farkokafin mu ara tafiya na kafa maka
sharadi da gargadinka cewa bana son yawan
tambaya cikin lamarina ko na umace ka aikata wani
abu ka tambaye ni saboda me yasa za a yi haka.
Wannan shi ne kuskure na farko da ka fara aikatawa
a gare ni, kuma idan baka kiyaye b aka ci gaba da
61 harafi
E
i
E
Tafiyar ajali
aikata kuskure makamancin wannan to kuwa zan
tafi na barka kahallaka b azan taimaka maka ba, don
haka ka zama mai aikata abin da na umarce k aba ka
zama mai yin tambaya a gare nib a".
Da Muzaffar ya ji wannan bayani sai ya karbi
wannan sanda ya sunkyar da kai bai sake yin Magana
ba, daga nan Zarkiyu ya juya ya wuce gaba, Muzaffar
yana biye da shi suka shiga cikin wannan bakin daji
dake gabansu, da shigarsu cikin wannan duhun daji
sai Muzaffar ya soma jin wani irin gurnani da gunji
yana tasowa daga can cikin dajin, ska ci gaba d
atafiya suna kara shiga ciki gurnanin yana dada
karuwa alamar suna tunkarar wajen da halittar dake
yin gurnanin take sai da suka yi tafiya mai nisa a cikin
wannan bakin dajin sannan suka iso inda suke jin
wannan gurnani da gunji yana tasowa daga cikin
: duhun wani kogon dutse da yake gabansu.
Da isarsu wajen sai suka ga wasu irin halittu
masu matukar munin kama da rashin kyan gani suna
ketwa daga cikin kogon dutsen suna fitowa su taho
gare su tare da yn wannan gurnani da sukeji tun da
farko.
Halittun suna da kafafu biyu da hannuwa biyu
kuma a tsaye suke tafiya kamar mutane, sai dai suna
da wuya irin na kare tare da kaho a tsakiyar
goshinsu, jikinsu buzu-buzu da gashi kuma a
mimmike kamar kayar beguwa idan suka yi gurnani
ko gunjin da suke yi sai ka ga wani farin abu mai
matukar yauki da kumfa yana zuba daga bakunansu,
Halittun nan suka yi ta fitowa daga cikin kogon
62 harafi
Tafiyar ajali
dutsen suna zagaye su. Muzaffar tamkar ba za su
kare ba, saboda tsananin yawansu suka yiwa
Muzaffar kwawanya ta ko ina yadda ba zas iya
komawa da baya ko kuma su samu mafita daga barin
wajen da wadannan halittun suke, sannan sai
halittun suka yyunkura gaba daya suka taso kansu
cikin gurnani da gunjin da sukeyi da nufin far usu su
hallaka su.
Zarkiyu ya fara zare takobinsa yay i yunkuri ya
tare su, ya fantsama a tsakaninsu yah au su da sara
da kaifin takobinsu, nan take ya fara girbar kawunan
da sassan jikin wadannan halittun yana hallakasu
duk wanda ya sara da kaifin takobinsa sai ka ji yay i
wata kadaitacciyar kara mai kama da haushin kare ya
fadi kasa yana shure shure, idan ya hallaka ransaya
fita daga cikinsa, sai ka ga yana narkewa ya zama jini.
Shima Muzaffar da ya ga yadda Zarkiyu yake
hallaka wadannan halittun sai ya yunkura ya tari
wadanda suka taso gare shi, duk wanda ya kawo
masa sura daga cikin wannan halittu da nufin ya
wafce shi ya hallaka shi sai Muzaffar ya tokare shi da
tsinin itacen da yak e hannunsa ya caka masa tsinin a
wuya ko a kirjinsa ya hallaka shi.
Haka su Muzaffar da zarkiyu suka yi ta hallaka
wadannan Halittu har sai da suka gama da su baki
daya gaba daya kasan wajen yay i jajawu da saboda
yadda halittun nan suka rika narkwwa suna zama jini
idan su Muzaffar sun hallaka su.
Bayan sun gama hallaka wadannan halittu da
suka fara haduwa da su suka yi duba da saurare ba
63 harafi
Tafiyar ajali
tare da sun sake ganin wata halittar ta sake fitowa
daga cikin kogon dutsen ba, daa nan sai Zarkiyu ya
maida takbinsa cikin kufenta sannan yaumari
Muzaffarda cewa su gaba da tafiya ba tare da san
yada zango a cikin wannan bakin daji don su kwana
ba.
**
Al'amarin Waziri Haawaisu kuwa bayan wani
lokaci da tsintar gawar Hadiinsa da suka hallaka da
maida siffarsa irin ta Muzaffar aka kawo si birnin
AMbar akabinne shi amatsayin Muzaffar,sai yay i
shiri ya tafi ga Sarki Sa'ad don sake neman auren
Gimbiya Zuhuriya ga dansa Najiranu, tunda wanda
aka bada aurenta gare shi ya hallaka.
Da isar sa fada ya tadda Sarki da sauran yan
majalisarsa zaune a fadar anafadanci ya isa ga Sarki ya
kai gaisuwa aka amasamasa sannan ya nemi waje ya
zaua aka ci gaba da zaman fad tare dashi da lokacin tashi
daga zaman fada yay i aka yi addu'a aka tashi sauran yan
majalisa suka fita daa fadar Sarki shi kuma aziri Hawaisu
sai ya matsa ga Sarki y ace da shi, yana son Magana da
shi Sarki Sa'adda ya bashi dama Waziri Hawaisu ya fara
da cewa.
"Allah ya baka nasara na dawo gare ka ne akan
maganar neman auren yar ka Gimbiya ZUhuriya ga dana
Najiranu, wanda ya dade yana bege a gareka kasancewar
wand aka bada aurenta gare shi Allah ya kaddara ba za ta
zama mata a agare shi bay a hallaka, sai dai mu yi masa
addu'a Allah yay i masa rahma ya gafarta masa".
Da Sarki Sa'ad ya ji wannan bayani sai ya amsa
masa da cewa "Hakika na ji abin da yake tafe da kai gare
64 harafi
Tafiyar ajali
ni kuma ina sane da cewa ka taba neman auren Gimbiya
ZUhuriya ga danka Najiranu, tun kafin na bada aurenta ga
Muzaffar dan gidan Liman Adnan da ya rasu, sai dai
kamar yadda na sanar da kai tun a farko b azan yi saurin
yanke hukunci akan taba har sai na ji daga gare ta don
haka zan bawa danka damar zuwa gare ta don su
fuskanci juna,idan sukasan kansu ta amince da cewa tana
kaunarsa t kuwa zan bada aurenta gare shi.
Wannan shi ne shawarar da na yanke akan
dukkanin mai neman aure Gimbiya Zuhhuriya".
Waziri Hawaisu yay i godiya da ya ji wannan
bayani na Sarki Sa'ad sannan suka yi sallamaya tashi ya
kamahanyar komawa gida da isar su gida yay i kiran
dansa Najiranu, ya sanar da shi yadda suka yi da Sarki
Sa'adul gamidi akan zai bashi dama ya je su yi hira da
Gimbiya ZUhuriya idan sun fuskanci juna ta amice tana
kaunarsu to kuwa Sarki Sa'ad yay i alkawarin zai bada
aurenta gare shi, Najiranu yay i matukar murna da farin
ciki da jin wannan labarin sannan ya kasance cikin
sauraren lokacin da za a bashi dama ya fara zuwa gareta
don su fahimci una.
Shi kuwa Sarki Sa'ad da ya koma gida sai ya sa
akakira masa yar sa gimbiya ZUhuriya don ya sanar da ita
shawarar da ya yankeakan batun masu neman aurenta
da zuhuriya ta samu sakon mahaifinta ta tafi gae shi ta
Baishe dashi, bayan Sarki Sa'ad ya amsa ya shaida mata
cewa "Na sa an kira ki ne don na sanar da ke shawar da
na yanke akan maganar auren ki zan bawa Najiranu dan
gidan Waziri Hawaisu damar ya zo hira gare ki don ku
fahimci juna, idan Allah ya sa zuciyarki ta amince da shi
kin zabe si ya zama madadin masoyinki wanda ya hallaka
to kuwa zan bada aurenki gare shi, idan kuwa ba kya
65 harafi
Tafiyar ajali
ra'ayinsa kina da zabin ki ki fidda duk wanda kike so na
bada aurenki gare shi matukar dai bai zamo daga cikin
mutanen da shari'a ta haramta aurar da ke a gare sub a,
ina sane da halin da kike ciki na mararin rashin masoyinki
Muzaffar da ya rasu, sai dai zan so ki kasance mai juriya
hakuri da yadda da kaddara ki ci gaba da addu'a Allah
yayi masa rahma ya kuma hadaki da wanza zai zama
madadinsa gare ki".
Da gimbiya zuhuriya ta ji wannan bayani na
mahaifinta sai ta ce ta amince da shawarar da ya yanke
akan maganar aurenta daga nan sai Sarki Sa'ad y ace da
ita "Ta shi ki je Allah yayi miki albarka
Gimbiya zuhuriya ta tashi ta koma dakinta ta
zauna ta shiga tunani da sake sake a ranta game da abin
da yake faruwa cikin rayuwarta, kuma har yanzu ba ta
gasgata cewa masoyinta Muzaffar ya hallaka ba, zucyarta
na hangen cewa wata rana zai dawo gare ta matukar
yana raye a doron kasa don haka ta yanke shawarar ta
dauki matakin da zata kauce daga bada auren a wani har
masoyinta Muzaffar ya dawo kamar yadda take fata da
muradi a cikin zuciyarta.
Bayan kwanaki uku aka bawa Najiranu damar
zuwa ga Gimbiya ZUhuriya don su fahimci juna a ranar da
zzai fara zua Gimiya Zuhirya ta yi ado da kayan adona alfarma irin wanda yayan manyan sarakuna sukekwalliya
dashi wancan zamani, ta tafi lambun mahaifinta ta zauna
tana jiran isowar Najiranu cikin nuna rashin damuwa da
sakiin fuska da cewa bata kaunar Najiranu ko kadan a
ranta kuma ta shirya yadda za ta rabu da shi a cikin zuciyarta, can da yammaci bayan rana ta yi sanyi sai ga Najiranu ya iso wannan lambu da gimbiya Zuhuriya
takezaune tana jiran iowarsa,ya caba ado da sutura ta
66 harafi
Tafiyar ajali
alfarmada manyan attajrai da yayan Sarakuna suke sanya
aka yi masa iso gare ta ya shiga har nda take zaune yay i
mata sallamata amsa masa cikin farin ciki tamkarbabu
wani abu a zuiyarta sannanta yi masa izinin zama kan
kujerar da ke kusa d aita ya zauna suna fuskantar juna.
Bayan Najiranu ya zauna ya dube ta y ace da ita
"Ranki ya dade tauraruwar a cikin 'ya'yan Sarakunan
duniya na san kin yi sani da dalilin zuwana are ki kamar
yadda maaifinki ya sanar d ake, sai dai zan kara yin
tahaliki akan hakan don ki fahimci alkiblata, an turo ni
gare ne domin mu fahimci juna idan kin amince da ni a
matsayin masoyi kamar yadda na dade ina begenki a
cikin zuciyata, to kuwa mahaifinki yay i alkawarin zai
bada aurenki gare ni, na san kna cikin tsananin kewa da
mararin rashin abin begenki da ya hallaka, don haka ina
mai fata da muradin na zamo madadinsa a gare ki, na
maye gurbinsa da yake a cikin zuciyarki da sannu zaki
same ni mutum ne mai kyautata da faranta zuciyarki fiye
da duk wani danamiji da za ki so a cikin zuciyarki mene ne
makomar zance na?"
Gimbiya ZUhuriya ta dubi ajiranu bayan da ta
gamajin bayanin sa sannan ta yi ajiyar zuciya ta amsa
masa da cewa "Hakika ina cikin kewa da mararin abin
begena da na rasa kuma zuciyata na tare da fargabar
rashin samun wanda zai zama madadinsa gare ni cikin
mazajen da suka kasance masu neman aurena a bayan
rashinsa.
Najiranu yay i sauri y ace da ita "Me yasa kika
ambata wannan Magana baya ga cewa bas hi kadai bane
da namiji da ya rage a doron kasa, kuma ya hallaka ba
sannan ace irin daraja da martabar Muzaffar ya fi ni da b
azan iya zama madadinsa a zciyar ki ba, girman nasa ba ta
67 harafi
Tafiyar ajali
sarauta ko kuma tarin dukiya, duk da kasancewar
mahaifina ba Sarki bane amma shi ne wazirin
mahaifinki,don haka na isa girman daraja na aure mace
yar Sarki kamar ki.
Gimbiya Zuhirya ta yi murmushi ta ce da shi
"Dukkanin abin da ka ambata babu wanda Muzaffar ya fi
ka girman daraja dukiya da nasaba da saurauta, sai dai
Muzaffar yana tare da wata baiwa da na kasa riskarta
cikindukkanin mazajen da suka bayyana gare ni da nufin
neman aure na, wannan baiwa it ace jarumta da
bajintarsa wadda dukkanin jama'ar birnin nan sun
tabbatar da haka,ina so na auri namiji jarumi, mai karfin
zuciya da rashin tsaro wanda zai yi alfahari da shi a cikin
dubban dubatar mazaje kuma na rasa samun kamarsa a
cikin mazajen da sukarage suna neman aurena.
Najiranu ya fusata dajin maganarta yayi sauri y
ace da ita, "Ka da ki zamamai nuna kaskanci ko gazawa ga
wanda ya ambata yana kaunarki don kina cikin mararin
rashin sabin begenki wa wnda ya hallakaakan shu'umanci
da hatsabibancinsa, kuma wace irin jarumta da bajinta
Muzaffaryake da ita wadda nib a zan iya aikata kamarta
ba".
Gimbiya Zuhuriya ta ji zfin maganar ad Najiranu ya
ambata akan Muzaffar saboda kaunar da take yimasa,
amma sai ta daure ta danne abin a ranta cikin sakin fuska
ta ce da shi.
"Kada ka zama mai fusatuwa cikin abin da na
ambataban zama mai nuna tozarci ko gazawaa gare k aba
don na yabi jarumta da bajintar Muzaffar,idan kana soka
ka zama madadinsa a gare ni, na amince da maganar
aurenka to ka zama jarumikamarsa, ina son ka tafi bayan
birnin Anbar ta bangaren kofar dake kudu bayan kwanaki
68 harafi
S
Tafiyar ajali
uku massu zuwa, z aka hadu da wani jarumi mahayin doki
sanye da bakaken kaya yana rike da wata takobi abar
yiwa marikarta ado da zinare katunkare shi kayi fada da
shi idan hark a samu nasara akansa to kuwa nay i maka
alkawarin zan aureka".
Shaidar da zata tabbatar da hakan it ace ka dauko
takobin da ke hannun wannan jarumi kakawo ta gare
m,kuma koda ka samu nasara akan wannan Jarumi kada
ka hallakashi kamar yadda shimaidan ya samu nasara
akanka ba zai hallakaka ba, don haka ina sauraronka daga
nan zuwa kwanaki biyar idan hark a kawomin takobin
wanan jarumi da na sanar da kai to kuwa nay i alkawarin
aurenka".
Tana gama fadar wannan maganarta yi masa
sallamata tashi daga inda take zaune ta koma cikin
kuyanginta suka kamahanyar komawa gida, daga nan
shima Najiranu ya tashi ya fita daga cikin lambun ya
kamahanyar komawa gida yana mai tunanin maganar da
gimbiya ZUhuriya ta sanar da shi, tare da daukar alwashin
cewa zai je ya tunkari wannan jarumi da ta sanar da shi
don fafatawa dashi ya karbo takobin da take hannunsa ya
kawo mata kamar yadda ta bukata, cikin wannan tunanin
da yakeyi har ya isa gida yana zuwa ya sanar da
mahaifinsa abin da yake faruwa tare da yadda sukayi da
gimbiya ZUhuriya da kuma alwashin da ya dauka don
tunkarar wannanjarumi ya karbo takobin da take
hannunsa ya kawo mata don ta amince da maganar
aurensa.
**
Al'amarin su Muzaffar da dattijo Zarkiyu kuwa
bayan da suka hallakawadannan halittar da suka fara
haduwa da su a cikin wannan bakin daji da suka shiga
69 harafi
Tafiyar ajali
suka ci gaba da tafiya ba tare da sun ya da zango don su
kwanta barci ba, sai da suka shafe tsawon kwana daya da
wuni daya suna tafiya a cikin wannan daji, sallah da cin
abincine kawaiyake tsayar da su, sannan suka isa wani
waje a tsakanin wasu manyan tsaunuka guda biyu da
saman tsaunukan da yake ci da wuta akwai hanyar
wucewa a bangaren dama da kuma bangaren hagu,
hanyar da take a bangaren habu babu komai tar da ita sai
farin rairayi da fili fetal tun daga farkonta har karshenta,
wadda take a bangaren dama kuwa tana tsakan
wadannan tsaunuka ne guda biyu da samansu yake ci da
wuta, idan iska ta kada da karfi sai ka ga brbudin wuta
yana zubowa kan hanyar daga saman wannan tsaunuka
haka kuma idan wutar ta yi huci da ruri mai karfi da take
yi sai ka ga harshen wutar ya taho har kasa ya lullube
hanyar baki daya.
Da isar su wannan waje suka ja suka tsaya Zarkiyu
ya dubi Muzaffar y ace da shi "Babu wata hanyar wucewa
sai ta cikin wannan hanyoyi guda biyu dake gabanmu,
kuma ta cikin wannan hanya dake bangaren dama da
wuta take zubuwa akanta zamu bi u wuce ba zamu bi
hanyar dake bangaren hagu ba".
Da jin wannan magan ata zarkiyu sai Muzaffar
yayi sauri y ace da shi "Saboda me za mu bi ta kan
wannan hanya da wuta take zuba a kanta mu kai kanmu
ga hallaka tare da cewa ga hanya a bangaren hagu wadda
ba ta tare da wata musiba,kokuma abin cutarwa da zai
iya kai mu ga hallaka".
Zarkiyu ya juyo cikin sauri y ace da si "Umarni
nake baka kana bin da na ambata ba ina neman shawarar
a gare k aba,kuma na hane ka da yin tambaya a gare nit
un a farkon marra kafin mu fara yin wannan tafiya a
70 harafi
Tafiyar ajali
tsakanina da kai, sai dai b aka zama mai kiyaye abin da na
hane ka da aaikatawa baka kasance mai wofinta da
maganata da yin tambaya cikin lamarina, wannan shi ne
kuskure na biyu da ka aikata a gare ni cikin wannan
tafiya, kuma idan baka zama mai kiyayewa ba, ka nisanta
ga barin wannan hali n aka to kuwa zan tfi na bar ka a
cikin wannan tsibiri ka hallaka b azan taimaka maka ba".
Da jin wannan Magana ta Zarkiyu sai Muzaffarya
sunkuyar da kai kasa yay i shiru bai sake cewa komai ba,
zZarkiyu ya ci gaba dacewa da shi "Za mu bi ta kan hanyar
dake bangaren dama mu wuce idan mun isa inda wutar
take zubowa daga sama n wadannan tsanuka kada kaji
tsoron koka razana ka bi ta cikinta mu wuce sai dai id aka
ji wutar tayi ruri da huci mai karfi ka dakata da tafiyar da
kakeyi ka tsaya har sai wutar ta gama hucinta, karhshen
wutar da yakerufe hanyar ya koma sama sannan ka ci
gaba da tafiya, idan kuwa bakakiyaye ba, ka ci gaba da
tafiya a sanda wutar takeui da ruri to kuwa harshen
wutar zai konaka kahallaka kakonekurmus baki daya sai
ka yi hattara".
Zarkiyu yana gamafadar wannan Magana sai ya
juya ya wuce gaba ya nufi hanyar da wutar take zubowa
akanta, Muzaffar ya bi bayansa ba tare da ya sake
zubowa akanta, Muzaffar ya bi bayansa ba tare da ya
sake ambaon wata Magana ba har suka isa inda hanyar
take,suka somatafiya akan wannan hanya dake tsakanin
manyan tsaunuka,idan suka ji hucin wutar dake saman
wadannan tsunuka sai su dakata da tafiyarar da suke yi
har sai harshen wutar y agama rufe kan hanyar ya
komasama sannan su ci gaba da tafia da haka har suka
wuce wannan hanya ba tare da wani abu ya faru gare sub
a,da suka ga sun wuce wannan hanya lafiya sai sukayi
71 harafi
Tafiyar ajali
goddiya ga Allah sannan sukaci aba da tafiya acikin
wannan daji.
Bayan sun yi tafiyar kwanaki biyu daga inda suka
wuce wannan hanya suka sake isowa wani keweaye a
tsakiyar wannan daji,Zarkiyu ya ja ya tsaya ya zare
takobinsa dake tare da shi,sannanya dubi Muzaffarya се
da shi, "Ka kasance cikin shiri domin za mu sake haduwa
da wasu miyagun halittun a cikin wannan kewaye da
zamu shiga kuma sai mun yi yaki da sum un samu nasarar
hallakasu kafin mu samu damar wucewa daga cikin
wannan da ira dondon haka ka yi amfani da wannan it
ace da nab aka don kare kanka da kuma hallaka
wadannan halittu da zamu hadu da su a ciki wannan da
ira.
Muzaffarya amsaba tare da yay i masa tambaya
ba don kiyaye abin da ya umarci kada ya sakeaikata
kuskutedaga nan Zarkiy ya wuce gaba Muzaffaryabi
bayansa sukashiga wannan kewaye da kegabansa.da
shigarsu cikin wannan kewaye sai sukasomahangen wasu
irin halittu masu kama da siffar mutane amma girmansu
ya ta'azzara fiye da girman dan adam suna dadoro a
tsakiyar bayansu kamar tozon rakumi tare da kahonni
guda biyu a tsakiyar kansu, idanunsu guda daya ne a
tsakiyar goshin kuma suna da wasu dogayen hakura guda
biyu da sukafito daga cikin bakinsu zaro zaro kamar
hauren gawa, kuma halittun bas a Magana ko