kuma
ambata wani abu sai gurnani kamar karnuka, muni da
rashin kyawun surarsu ya ta'aza ga idanunsu wanda bai
zamo daga cikin jinsinsu don kuwa halittun su kasancе
ababen ban tsoro da firgitarwa ga dukanin bil'adama da
ya gansu,kuma halittun baki daya suna tafe akan wasu
dabbobi ne masu kama da kura, sai dai girmansu ya wuce
72 harafi
Tafiyar ajali
na ingarman doki abin har ba zai misaltuwa ba, kowacce
dabba daga cikin wadannan dabobibi mahayin ta ya
sanya mata linzami kamaryadda akeiwa doki wasu daga
cikinsu dabbobin mahaya biyu ne akansu wasu kuwa har
uku, kuma hannayensu rike da wasu irin bakaken
takubba wasu daga cikinsu mashi wasu sasari ko
al'amudu da sauna kayan fadatamkar rundaunar
baradanu da zasu tafi fafata yaki a fagen fama.
Da ganin su Muzaffar sun shigo cikin wannan
da'ira sai halittun nan suka karkata gare su baki daya
sukayi gunji da gurnanin da sukeyi suka tasokansu a
harzuke tamkar daman su sukejira su fito yaki ne saboda
su hallakasu. A ganin haka sai zarkiyu ya daga takobin a
take hannunsa ya tare su cikin karaji dagunji irin
najarumta da sadaukantakayafara tafiyar ruwa da
kawunan wadanda suka fara tunkarar sa a karon farko
sannan ya fantsama a tsakaninsu ya farmusu da sara da
kaifin takobinsababu kakkautaa, duk inda ya ratsa a
tsakanin adan nan halittu sai dai ka ga gawarwakinsu da
na dabbobin da suke kai suna zuba kasa matattu tamkar
busasshen ganyen bishiya da iskatake kadowa daga jikin
reshin bishiya, shimaMuzaffar da ganin yadda Zarkiyu
yakehallaka wadan nan halittu sai daga wannan fekeken
işace dake hannunsa ya karkata gare su cikin karfin zuciya
da jarumta irin ta neman tsira daga hallaka, dukwanda ya
tasogare shi daga cikin halittun nan sai ya fara sanya
tsinin itacen dake hannunsa ya soke wuyan dabbar da
yakekanta ta fadi kasa sannan ya sake sanya tsinin itacen
ya halakashi,hakasukayi ta dauki ba dadi da bakin
gumurzu mai tsananin a tsakaninsu, da wadannan halittu
har suka samu nasarar hallakamafi daga cikinsu.
73 harafi
Tafiyar ajali
Suna cikin kafsawa newani daga cikin halittun ya
kaiwa Muzaffar duka da sararin bakin karfen
dakehannunsa Muzaffar ya goce sasarin ya samu jikin
wata bishiya dake bayansa nan take bishiyar ta ratattake
ta zube kasa tamkar wadda aradu ta fada a kanta, saboda
musiba ya sakekaiwa Muzaffar duka da sararin
Muzaffarya kare itacen dake hannunsa nan take ita cen
ya kubce daga hannunsa ya fadi kasa can gefe guda shi
kuma yayi baya taga-taga kamarzai fadi kasa saboda
karfin bugun da wannan halitta ya kawomasa da nufin
hallakashi, halittar nan ya sake tasowa kansa a fusace
yana jan sararin dake hannunsa a kasa, duk ciyawar da
sasarin yabi ta kanta ta kama da wuta ta kone kurmus
saboda musiba da take tare da sasarin wajen ya yi
bakikkirin yana karasowa inda Muzaffaryake ya kai masa
duka da sararin Muzaffar yayi sauri ya goce sararin ya
samu wani daga cikin wadannan halittu dake kusa da
ajen nan take suka yi sama akan iska daga shi har dabbar
da yake kanta sannan suka fado kasa a can gefe suka
kama da wuta suka kone kurmus.
Da Muzaffar ya ga haka sai yayi sauri ya tafi ga
inda itacen da yake yin amfani dashi ajen yin fada ya fadi
kasa, ya sa ahannu ya dauka ya tari wannan halitta cikin
hikimadakwarewa ta salon iya fada, suka ska yi karon
battar karfe da kazamar haduwa maimuni halittar nan
yana kai masa sura da nufin waftarsa ya hallakashi shi
kuma Muzaffarsai ya sunkuyar daya sanya itacen da ke
hannunsa ya harde kafafun dabbar da yakekanta ta
durkushe ta fadi kasa tare da wanda yakekanta, kafin ya
yunkura ya tashi Muzaffar ya isa gare shi yayi tsalle da
majaujawa cikin azama da zafin namayasokamasa tsinin
itacen dake hannunsa har sai da ya huda kan makoshinsa
3
74 harafi
Tafiyar ajali
ya fito ta baya,jini yay i tsartuwa sama ya watsu akan
fuskar Muzaffar halittar nan yayi atakadairacciyar kara
mai tsananin karfi irin ta azabar fitar rai gaba daya da
irirar wajen ta yi amsa kuwa da amo mai hauhaa da ya
garaye koina sasarin da yake hannunsa da ya daga shi da
niyar kai bugu ya dao kansa, nan take ya kama da wwuta
ya konekurmus ya hallaka
Muzaffar yana gamahallaka wannan halittadaya
da ya taso masa shima Zarkiyu yana gamakarasa
hallakahalittun da suka yi saura yana fafatawa da su,
suka tsaya suna duban halittun nan babu sauran wani
mai rai a cikinsu kuma basu sake ganin wasu sun tunkaro
inda suke ba daga nan sai suka yi godiya ga Allah a bisa
nasarar da suka samu na hallaka wadannan halittu da
suka taso gare su baki daya sannan zarkiyuu ya maida
takobinsa cikin kubenta ya umarci Muzaffar da cewa su ci
gaba da tafiya don su fita daga cikin wannan da'ira da za
su tafiya Muzaffar yay i nufin ya dauki daya daga cikin
makaman wadannanhalitu da suka hallaka,amma sai
Zarkiyu ya hane shi da daukar kowane irin makami ko
taba waní abu a cikin wannan da'ira har su fita daga
cikinta, tare da gargadinsa cewa babu wani makami da
zai iya amfani dashi acikinwannn tsibiri ban da fekeken
tacen da ya bashi har sai sun isa inda zai sanar da shi
yadda zai yi amfani da takobin dake tare da shi wannda
dattijoMubasshiru ya bashi,hakaMuzaffar ya hakura bai
dauki komai daga cikin makaman wadannan halittun duk
da cewa zuciyarsa tana so.
suka ci gaba datafiyadon su fita daga cikin wannan
da'irada suke cikinta.
75
**
harafi
Tafiyar ajali
Can kuwa a birnin AMbar bayan kanaki uku da
zuwan Najiranu wajen gimbiya Zuhuirya ta shaida masa
ya fita bayan gari zai hadu da wani jarumi da zai yi fada
da shi ya karbo mata takobin da take hannun wannan
jarumi idan yana so ta amince da maganar aure a
tsakaninsa da ita.
Da ranaku sukacikakwanaki uku Najiranu ya yi
shirin yaki ya dauki duk wani makamida yake amfani da
shi a wajen yin fada ya shirya dokinsa ya kama yah au ya fita
ya kama hanyar fita daga birnin ta kofar dake bangaren kudu
kamar yadda gimbiya Zuhuriya ta umarce shidan ka ga
Najiranu cikin shirin yakin da yay i a lokacin da ya fito zaka yi
zaton wani hamshakinjarumine kokuma gawurtaccen sadauki
ya fito cikin shirin yaki da nufin zuwa ya yaki jama'ar wani
birni shi kadai ba tare da masu taimaka masa ba.
Ita kuwa Gimbiya Zhuriya tun kafin Najiranu y agama
nasa shirin ya fito daga gida tuni ta gama shiryawa da shirin
yaki ta sanya sulke da hular karfea kanta (Kwalkwali) adda ta
rufr mata fuska,ba da idanunta babu abin da ake iya gani
yadda ba za a iya gane cewa mace ce ba, kamar yadda ta yi a
sanda za ta jarraba jarumta, da bajintar Muzaffar, ta tafi ta
kama dokinta ta hau ta fita ta kofar bayan gida, ba tare da
kowa ya sani ba, ta nufi wajen da ta kwantataa Nairanu cewa
zai hadu da wannan jarumi da zai yi fada da shi ya karbo
takobin da take hannunsa ya kawo mata, idan yana so ta
amince da magarsa aure a tsakaninsa d aita, tana zuwa daidai
wajen ta samu wani duhun itatuwa ta shiga ta labe tana jiran
isowar Najiranu.
Bayan wani lokaci da zuwanta wannan waje sai ga
Najiranu tafe akan dokinsa yana sasarfa ya nufo wajen da
gimbiya ZUhuriya take boye cikin duhun itatuwa tana jiran
isowarsa da zuwansa daidai wajen sai ya jalinzamin dokinsa ya
tsaya yana huci da cka irin na fusatattu tamkar wanda ya fito
neman abokin gabar da ya kashe masa mahaifiya don daukar
fansa akansa ita kuma gimbiya ZUhuriya da ta gay a iso wajen
76 harafi
Tafiyar ajali
sai ta fito daga cikin duhun itatuwan da ta labe a cikinsu ta
bayyana a gabansa.
Na jiranu ya dubi wannan mahayin dokin da ya
bayyana gare shi cikin shirin yaki ba tare da ya gane cewa
gimbiya Zuhirya ce ba, ya dubi takobin da take tare da shi ya
ga tana sheki da haske kasancewar anyi marikarya ado da
zinare nan take ya gane cewawannan shi nejarumin da
gimbiya Zuhuriya ta shaida masa cewa zai hadu da shi idan ya
iso wannan waje wanda zai iya fada da shi ya karbi takobin da
take hannunsa ya kai mata idan yana so ta amince da maganar
aurensa da ita, don haka ya dubi annan mahayin da ke
gabansa yace da shi.
"Kai bajirarre, fandararrre,gafalalle makaskancin
bawa, na fito ne domin nemankakuma na zo gare ka ne
saboda na yake kana karbi takobin da takehannunka wadda
zata zama shaidar yadda da amincewar abar begena cikin
lamarin wanzuwar are a tsakaninmu don haka zan afku a
kanka na karbi wannan takobin dake tare da kai ta karfin
jarumta da bajinta don samun biyarn bukatata na auri gimbiya
Zuhuriya, ko kuma ka bani takoin cikin lumana ba tare da na
afku akanka ba, don kaucewa ukuba da azabar kaifin takobina
a gare ka".
Gimbiya ZUhuriya ta yi shiru tana sauraronsa bata
tanka mas aba, ko ta maida masa da Magana shi kuwa
Najiranu da ya ga haka sai ya fusata ya zare takobinsa cikin
karaji da gunjin fusatuwa ya sake linzamin dokinsa ya taso kan
mahayin da nufin gamawa da shi ya karbi takobin daga
hannunsa, Gimbiya ZUhuriya ta yi sauri ta zare wannan takobi
da ke tare da ita, ta tare shi cikin karumta da kwarewa ta
sakon iya fada, suka hadu a tsakanin kaiwa juna sara alokaci
guda, kaifin takubbansu ya hadu akan iska karfin haduar
takubban da kwarewa a kai sara irin na gimbiya Zuhuriya y sa
takobin da take hannun Najirannu ta kusa kufcewa ta fadi kasa
yay i kokarin ya riketa da kyar ba tare da ta subuce daga
77 harafi
Tafiyar ajali
hannunsa ba sukawuce ba tare da wani ya samu abokin
karawarsa ba daga cikinsu.
Suka sake juyoa suka maida kai hari ga juna, da kaifin
takubbansu nan take artabu ya rincabe a tsakaninsu aka soma
zamiya da kai bara akan juna cikin salon nuna kwarewa da
jarumta ga mamakin Najiranu sai ga wannan Jarumi da suke
kafsawa da shi ya fi shi tsananin zafin namada saurin kai sara
akansa,kuma salon fadan da jarumin yake amfani da shi
Najiranu bai taba ganin makamancinsa ba a tsawon
rayuwarsa, tun yana kokarin kare sara da maida martani har
ya gaza kai sara sai dai kokarin kare kansa, ga Gimbiya Zuhirya
ta ga haka sai ta himmatu wajen nusar da shi kuskurensa da
tabbatar da gazawarsa a fagen jarumta da rashin kwarwa ta
salon iya fada.
Ta yunkura ta kai masa wani gawurtacce sara da
takobinta Najiranu ya kasa karewa da takobinsa sai da ya
sanya garkuwar dake rike a hannunsa na hagu yak are
garkuwar tayi wata irin kara mai tsananin karfi saboda karfin
saran da ta kai masa tartsatsin wuya ya tashi sama daga jikin
garkuwa, shi kuma Najiranu yayi baya taba taga-taga kamar
zai fado daga kan dokinsa saboda karfin sara.
Kafin ya warware daga firgicin saran da ta kai masa ya
maida kai hari ta sae jau dayju are sgu cujub azana da zafub
banam ta jau nasa wabu sarab a daudau jafadarsa tana da
daar da za a ta same shi idan ta so amma da ta gay a kasa kaucewa
ko yak are saran kuma ba ta da niyar cutar da shi ko ta hallakashi sai
ta kauda kaifin takobinta daga kansa ta sarai jikin garkuwa dake
hannunsa. Najiranu yayi baya ya tntsiro daga kan dokinsa ya fado
kasa, kansa ya bugi jikin wani kututture itace dake kusa da wajen ya
ji masa ciwo a goshi. Garkuwar da takobin da suke rike a hannunsa
suka fadi kasa gefe daban, kafin ya yunkura ya tashi gimbiya
Zuhuriya ta dao kansa ta sake kai masa sara sai da takobin ta kusa
sauka a kansa sai ta ja linzamin dokinta ta tsaya batare da ta sauke
kaifin takobin a kansa ba.
Najiranu ya rintse idanunsa yana jira ya ji saukar
kaifintakobin a kansa ya hallaka sanda ya ga wannan jarumi da suke
78 harafi
Tafiyar ajali
kafsawa da shi ya kawomasa sara bayan faduwarsa kasa daga kan
dokinsa ammasai ya jib a a saukekaifin takobin a kansa ba, ya bude
idanunsa domin ya ga abin da yake faruwa sai ya ga wannan jarumi
bai dauke kaifin takobinsa daga daidai kansa ba, nan take ya saduda
ya tabbatar da cewa wannan jarumi ya samu nasara akansa, saboda
yana bukatar ya hallakashi da tuni ya mika ruhinsa barzau ta sa ta
kare, daga nan sai ya ga jarummin nan ya dauke takobin daga daidai
kansa ya maida ita cikin kubenta sannan ya kadaliinzamin dokinsa ya
iuya ya bar wajen ya nufi cikin dhun itatuwan da ya fito daga cikinsa
da farko.
Najiranu ya bi shi da kallo har ya shige cikin duhu itatuwan
a bacemasaya tafi ya bar shi anan alamarya samu nasara akansa.
Bayan tafiyar annan mahayi Najiranu yay i ajiyar zuciya
sannan ya yunkura ya tashi ya dauki takobi da garkuwarsa dake a
yashe a kasa ya tafi ya kama dokinsa yah au ya juya ya kama hanyar
komawa gida zuciyarsa cike da bakin ciki na kasa samun nasara akan
wannan jarumi da ya zo gare shi, domin ya karbi takobin da take
hannunsa, ya kaiwa gimbiya Zuhuriya don samun amincewarta akan
maganar aure tsakaninsa da ita, kamar yadda ta sharadanta masa.
Da isarsa gidan mahaifinsa Waziri Hawaisu ya ganshi cikin
matukar jigata da galabaita alamar bai ji dadin karawar da suka yi da
jarumin da ya tafi don karbo takobin da take tare da shi ba, bare
tunanin samun nasarar a kansa, cikin sauri Waziri Hawaisu ya tare shi
ya kama masa ya sauko daga kan dokinsa sannan ya tambaye shi
abin da yake faruwa. Najiranu bai boye masa komai bay a bayyana
masa irin a rangama da artabu da sukayi da wannan jarumi kuma ya
kasa samun nasara akansa ya karbo takobin da take hannunsa.
Waziri Hawaisu yayi matukar bakin ciki da jin wannan labari na
dansa Najiranu ya sunkuyar da kai kasa yay i shiru yana tunanin
bayan wani lokaci ya dago kans aya dubi Najranu ya ce da shi.
'Dukda kasancewar baka samu nasara akan jarumi ba, ka
sake komawaw wajen gimbiya Zuhuriya ka nemi amincewarta akan
ta sake baka dam aka koma wajen wannan jarumi don karbo takobin
da take hannunsa, idan har ta amince maka da cewa ka sake
komawa gare shi don karbo takobin to kuwa zan nemi taimako daga
Boka Musailamatu don kasamu nasara akan wannan jarumi ta
hanyar alkaluman sihiri komai tsananin jarumta da sadaukatakar da
yakeda ita koma ko wanene shi a doron kasa.
79 harafi
Tafiyar ajali
Da Najiranu ya ji wannan bayani sai ya samu karfin zuciya da
himmatuwa ta ya koma ga gimbiya Zuhuriya don sake neman
amincewarta ta bashi damar ya sake komawa don karbo takobin da
take hannun wannan jarumi.
Ita kuwa Gimbiya Zuhuriya bayan da ta samu nasara akan Najiranu ta tafi ta barshi a wajen da suka fafata da ta shige cikin
duhu itauwa ta bace masa sai ta zagaye ta kama hanyar komawa gida da isarta gida ta cite kayan dake jikinta ta koma dakinta ta
zauna ta ci gaba da gudanar da al'amuranta kamar yadda ta sab aba
tare da wani daga cikin jama'ar dake gidan ya san abin da yake
faruwa ba, da gari yaw aye yamma ta karato daidai lokacin tafiyarta
lambun mahaifiinta tare da kuyanginta, kamar yadda ta saba ta
zauna tana jiran isowar Najiranu domin ta ji abin da zai zoya ambata
a gare ta tunda ya kasa samun asara akanta bare ya karbi takobin
dake hannunta ya kawo mata don ta amince da maganar aurensa kamar yadda suka yi yarjejeniya da shi.
Bayan zuwanta lambun ba da dadewa ba sai ga Najiranu ya
iso ya nemi iso daga gare ta akan bahi damar shigowa cikin lambu, ya karasa inda take a
a zaune Gimbiya Zuhuriya ta taryeshi cikin wawala
da sakin fuska tana mai yi masa murmushi da nuna rashin damuwa
da lamarinsa tamkar ba it ace tatare shi a daji suka fafata ba, bayan
Najiranu ya zauna daga gefe suna fuskantar juna gimbiya ZUhuriya ta
dube shit ace da shi.
"Yau dai nag a tamkar baka tare da walwala cikin lamarinka
kuma ban ga takobin da muka yi alkawarin zakakarbo daga hannun
jarumin da na sanar da kai ba, domin na amince da maganar aure a
tsakaninmu, ko kuma ba kasamu nasara akansa b aka dawogare ni
bayan ambaton jarumta da bajinta da kakeikirarin kana tare da ita".
Najranu ya amsa da karfin zuciya yana mai fadin cewa
"Lamarin ya taʼazzara a gare nia farkon marra ban samu nasara akan
wannan jarumi da na je domin na karbo takobin da take annunsa ba,
a karawar da muka yi da shi kamar yadda ki ka umarce ni na kasance
cikin halin rashin lafiya a wannan rana wadda ta tsananta gare ni
amma saboda irin kaunar da nake yi a gare ki ya sa ban kauda kai ga
barin alwakrin da muka yi dake ba, na tafi ga annan jarumi domin
karbo takobin da take hannunsa, wannan shiyasa ban samu nasara
akansa ba balle na karbo takobin da na kawo ta gare ki, saidai
wannan ba yana nufin nuna gazawa ko kuma rashinjaruta a gare nib
a face dai wanzuwar akasi don haka na sake dawowa a gare ki ina
80 harafi
Tafiyar ajali
mai neman izini da yardarki akan ki sake bani daman a koma ga
wannan jarumi na karbo takobin da ke hannunsa, ni kuma nayi miki
alkawarin zan koma gare shin a karbo wannan takobin na kawo ta
gare ki,kamar yadda kika kubata matukar za ki amince d amaganar
aure a tsakaninmu".
Gimbiya Zuhuriyata yi shiru tana saurare da tunanin akan
maganar da ya ambata duk da ta san cewa babu gaskiya cikin
lamarin da zancen da ya ambata a gare ta da yake ta san cewa koda
ta sake bashi dam aba zai iya samun nasara akanta ba, saboda
karancin kwarewa ta salon iya fada kuma ta fishi jarumta da dabara
na iya fada da kowane irin makami sai zuciyarta ta amince da cewa
ta sake bashi dama ya koma ga wannan jarumi kamar yadda ya
bukata. Bayan wani lokaci ta dago kai ta ce da shi "Zan sake baka
dama a koma ga wannan jarumi don karbo takobin da take hannunsa
kamar yadda ka bukata, amma sai ka amince da shauradan da zan
sanar da kai guda biyu a yanzu.
Sharadi na farko shi ne ba z aka sake neman watabukata a
gare nib a matukar b aka samu nasara akan jarumi da z aka tafi gare
shi domin karbo takobin da ke hannunsa, ba tare da ka sake dawowa
gare ni akan maganar aure, sharadi na biyu kuma shi ne za ka sanar
da mahaifinka ya koma ga mahaifina ya sanar da shi ka janye akan
maganar neman aurena, idan kaamince da wannan sharuda to kuwa
na baka dama bayan kwana biyar ka sake komawa ga wannan jarumi
don karbo takobin da take hannunsa, kuma idan hark a samu nasara
akansa zan amince da maganar aure a tsakanina da kai".
Najiranu ya ji wannan bayani sai y ace ya amince da
sharudan data ambata agare shii daganan suka yi sallama ya tashi ya
kamahanyar komawagida cikin murna da farin ciki, cikin samun
amincewarta ita ma gimbiya Zuhuirya ta tashi suka fita daga lambun
tare da kuyanginta suka kam hanyar komawa gida.
Da zuwan Najiranu gida ya sanar da mahaifinsa yadda
sukayi da gimbiya zuhuriya mahaifinsa Hawaisu yay i matukar murna
da farin ciki samun amincewarta sannan ya sanar da Najirannu
cewaidan gari yaw aye tunda farkon safiya zai tafiya ga boka
Musailamatu domin neman taimako a gare shi cikin dalasumai na
aikin sihiri don samun nasara akan wannan jarumi komai tsananin
jarumta da sadaukatarkasa a doron kasa.
**
81 harafi
Tafiyar ajali
Su kuwa su Muzaffar da dattijo Zarkiyu bayan da suka gama
hallaka wadannan halittu da suka hadu da su a cikin wannan da'ira
da suka shiga cikinta, suka ci gaba da tafiya tare da sun yada zango a
ko in aba har suka yi kwana suka wuni suna tafiya acikin wannan
da'ira Muzaffar yayi matukar gajiya da galabaita sabida arabun da
suka yi da wannan halittu suka hallaka su sannan basu zauna sun hut
aba suka ci gaba da tafiya.
Suna cikin wannan tafiya e sai suk ji wata irin tsawa da
rugugin aradu mai tsananin karfi da ban firgici sun gauraye dajin baki
daya, har sai da suka daina jin komai ban da wannan rugugi da tsawar da suka dauki lokaci mai tsawo suna amsa kuwa da
amomaihauhawa, iska mai karfi ta biyo baya tare da wata irin bakar
guguwa da ke cudanye da wani haske mai kama da hasken walkiya a
tsakiyar ta, bayan lafawar iskar da tsawa da rugugin da sukeji sai
suka ga wandasu irin manyan mikiya masu matukar girma da ban
tsoro da Muzaffar bait aba ganin nau'in tsuntsu mai irmansa ba, idan
sukai wani irin kuka mai kama da kakari sai ka ga wuta tana fesowa
daga bakinsu, duk abin da wutar ta zuba a kansa sai ka gay a kone
kurmus cikin dankankanin lokaci ya zamatolka.
Da Zarkiyu ya ga wannan al'amari da yake tare da
wadannan mikiyoyi da sukatunkaro inda suke sai yay i sauri ya nemi
wani kogon dutse dake kusa da wajen da suke y ace da Muzaffar su
yi sauri su shiga cikin kogon dutsen su buya kafin wadannan mikiyoyi
su karaso inda suke suka shiga cikin kogon dutsen suka zauna sai
suka rikajin tsawa da rugugin da suke jinn a dada kauwa da hauhawa har dusten da suke ciki yay a soma girgiza da raurawa tamkar zai fashe ya rufto kansu su hallaka, bayan wani lokaci yana kara
tsananta da munana a agare su suka rika jin wata irin zazzafariskamaikamada tiririn ruwan zafi tana ketowa tana shigowa
cikin wannan kogon dutsen haka suka dauki lokaci numfashi sai ya ji
tamkar zai kama da wuya yak one kurmus saboda musiba.
Da rana ta gama faduwa tare da yay i su Muzaffar suna
zaune cikin wannanmummunan yanayi da suka riski kansu a ciki sai
Zarkiyu ya tashi ya dubi Muzaffarya ce da shi "Zan fita na yaki
wadannan halittu har sai na hallaka su baki dayansu, domin mu
samu damar ci gaba da tafiya mu fita daga cikin wannan da'ira kazauna a cikin kogon dutsen nan har na dawo kada ka sake kace
zaka fita daga cikinsa idan ban i na umarce ka da cewa ka fito ba, kuma babu wani abin cutar da zai iya shigowa cikin wannan kogon
82 harafi
Tafiyar ajali
dutse ya cutar da kai matukar kana cikinsa baka fto ba, idan na samu
nasarar akan wadannanhalittun zan hallaka sun a dawo gare ka kafin
ketowar alfijir".
Da y agama masa wannan bayani sai ya zare takobinsa ya
juya ya fita daga cikin kogon dutsen don zuwa yaki wadannan
mikiyoyin dake waje tun da zarkiyu ya fita sai Muzaffar ya soma jin
kakari da kuka wadannan mikiyoyin ya sake gauraye dajin baki daya,
wani lokaci yak an hango irin feshin wutar da wannan mikiyoyin suke
fitarwa daga bakinsu idan ya zubo kasa daga cikin ogon dutsen da
yake boye, haka a ka shafe tsawon daren wannan rana har gari yaw
aye Zarkiyu bai dawo ba, kuma Muzaffar bai daina jin kuka da
kakarin wadannan halittu ba, aka sake shafe tsawon yini ranar har
dare yayi ana cikin wannan yanayi ba rae da Zarkiyu ya dawo ba
hankalin Muzaffar yay i matukar tashi yashiga fargaba da rashin
tabbas akanhalin da Zarkiyu yake ciki ganin cewa y ace zai dawo
kafin ketowar alfijir gas hi har ya kwana ya wuni bai dawo ba.
Cikin wannan dare sai Muzaffar ya rikajin kakari da
kukanwadannan mikiyoyi ya dada karuwa fiye da yadda yakejinsa
afarkon mara, hankalinsa ya kara tashi ya soma tunanin ko Zarkiyu
ya hadu da wani abin cutarwa da yay i masa illa a bayan ftarsa, don
haka yay i tunanin cewa idan har gari ya sake wayewa Zarkiyu bai
dawo ba to kuwa zai fita don ganin abin da ya faru a gare shi ya
kuma san halin da yake ciki.
Da gari yaw aye Zarkiyu bai dawo ba bayan Muzaffar ya idar
da sallar asubahi sai ya yanke shawarar fita daga kogon dutsen
domin ya ga halin da yake ciki ya dauki fekakken itacen nan da
Zarkiyu ya tashi don ya rika yin amfani da shi wajen yn fada ya nufi
kofar fita daga kogon dutse, ya fara lekawaaaa waje a hankali ya ga
babu komai a wajen ban da gawarwakin wadannan mikiyoyin gasu
nan birjik a kasa tamkarbusassun ganyayyakin bishiya da iska ta zubo
da su kasa kuma gaba daya kasar wajen ta kone ta yi baki saboda
feshin wutar da wannan mikiyoyin suke yi.
Bishiyin da ke kusa da wajen sun kone sun yi baki busasssun
iatuwa kuwa sun zama toka.
Muzaffar ya duba bai ga dattijon Zarkiyu a kusa da wajen
ba, don haka ya fito daga kogon dutsen domin neman inda zai ganshi
da fitowarsa daga cikin kogon dutsen sai ya ji wata irin iska mai karfi
ta taso kansa, ya juyo da sauri domin ya a abin da ya taso masa kafin
ya lura da abin da ya taho gare shi tuni ya ji an sure shi an yi sama da
83 harafi
Tafiyar ajali
shi a cikin wannan iska, sannan ya ji kuka da kakari wanda wannan mikiyoyi suke yi tun a farkon sanda suka fara hangensu karfin sura da daukar da akayi masa ta gigita da firgita shi, sannan ya ji wani abu mai kama da tsinin mashi ya kama jikinsa sosai ga tsininzafi yana ratsa jikinta tamkar ana sukansa da kibiyar da aka zaro ta daga wtar makera
soma
saboda musiba, nan take ya soma fita daga hayyacinsa ya sarkewa.
Muzaffar ya ji an ci gaba da tafiya da shi akan iskacikin
wannan hali na kunci da musiba da yake ciki yun bayan da ya ji an
asure shi an tashi da sama akan iska yay i duba ya zuwa ga abin da yake rike da shi sai yaga daya daga cikin mikiyoyin nan ce ta sure shi ta tashi sama da shi akan iska, yayi kokarin ya kufce daga rikon da ta yi masa don ya kwace kansa daga gare ta amma sai ya ji ya kasa, koda zare faratan da ta kafa masa a jikinsa bare