danna cikin ma'adanar kayansa. Towel ya ɗaura ya fita ya na faɗin.
"Allah Ya sa dai kin bar ruwan zafi a flask yau."
"Eh My king akwai ruwan zafi. Kana buƙatar wani abun ne bayan shi?"
Ba tare da ya kula ta ba ya wuce ya haɗa ruwan wanka ya shige abunsa. Ya na fitowa ɗaure da towel kamar shi kaɗai ne a gidan ya nufi wajen rago,kallonsa ya yi ya ga yanda ya ƙara ramewa. Nan take ya ƙwalawa Fauziyyah kira ya ce ta kai masa wuƙa. Sai da ya yanka ragon sannan ya wanke hannunsa ya koma ɗaki. Mahaucin unguwar su Hajiya da suka saba ya yi wa waya,ya ce ya aika yaro a cikin yaransa a zo gidansa a yi masa fiɗa. Ya na kammala wayar ya hau saka kayansa,kafin ya gama Fauziyyah ta haɗa masa kayan abincinsa ta jera masa. Ya na cin abincin ne take bashi labarin sauran kwana uku su Barirah su tashi. Tsayawa ya yi cak da cin abincin yana yi mata wani irin kallon da ta kasa fassara shi........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨
PAGE 15.
*SANARWA.*
*Masu son su siya kuma ku sanya 500 ta 0006366584 Hamidatu Sanusi Ahmad Ja'iz bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.*
Ruwan dake cikin babban jug ɗin da ya rage ya ɗauka ya kwara mata a fuska. Wani irin dogon numfashi ta ja kafin a hankali ta sake shi ta bakinta. Cikin natsuwa ta ware idanuwanta a saman fuskar Abbas,a yau bata ganin kyawun nan nashi da ke mantar da ita baƙin cikin da yake ƙunsa mata kullum. Haushin shi da take ji ne ya sanya ta ture hannunsa da ya kai jikinta ya na taɓa ta tare da kiran sunan ta. Cikin wata iriyar murya ta ce.
"Kar ka kuskura ka taɓa ni da hannunka mai najasa! Kar ka sake kiran suna na da bakin ka da ya iya furta kalaman iskanci da gafala. Ina so na furta kalmar tsana a gare ka,amma ba zan iya ba,me ka yi wa zuciyata ne Abbas? Wanne irin dabaibayi ka yi wa ruhina da ya sarƙe da matsanancin son ka? Na shiga uku ni Fauziyyah,ina zan saka kai na na ji sanyi? Ashe har yanzu ba ka bar wannan halayyar ta bunsuraye ba? Ashe...."
Wani irin mari Abbas ya sakar mata a kunci wanda ya sa kanta buguwa ya haɗu da gini,hancinta ya fara tararar da jini. Ba tare da ya damu da jinin da ke zuba daga hancinta ba ya miƙe tsaye ransa a matuƙar ɓace ya hau nuna ta da yatsa ya na faɗin.
"Ni kike kira da bunsuru Fauziyyah? Ashe lalacewar tawa har ta kai macen da nake aure,nake ciyarwa na yi wa tufafi sannan na killace a ƙaton gida irin wannan ta kira ni da bunsuru? Yau zan nuna miki ni bunsuru ne na haƙiƙa."
Da ƙarfi ya ja hannunta ya tura ta ɗakin baccin su,tirjewa ta fara yi ta na riƙe bango tare da yi masa magiya akan ya ƙyale ta,wurga ta a saman gadon ya yi sannan ya bita ya taushe mata ciki. Gigitacciyar ƙarar da ta ƙwalla ne ta ankarar da su Barirah abinda ke faruwa. Cikin sauri ta miƙe za ta fita daga ɗakin, Shehu ya riƙe ta ya ce.
"Ina zaki je? Kar ki sake ki saka kan ki a rikicin da za ki ji kunya. Idan yau kin ji kin raba gobe wa zai raba su? Ita ce ya kamata ta dage ta kwaci ƴancinta da kanta,dan haka koma ki zauna."
Zama ta yi ta na ta jijjiga jikinta kamar mai shirin yin dambe. A zuciye ta kalli Shehu ta ce.
"Don Allah mu tashi daga gidan nan,bana son zama anan, na gaji da ji da ganin tashin hankali, ba zan iya jurewa ba...ba zan iya ba..."
Kuka mai tsanani Barirah ta fashe da shi,cike da jimami Shehu ya miƙe ya rungumeta ya na lallashinta. Ta ɓangaren Fauziyyah kuwa ta na can ta dage ba zai kusanceta ba da najasar da ya biya buƙatarsa wajen aikata zinar waya da wata. Shi kuwa goga Abbas ya taushe ta ya zuba mata duk ƙarfinsa tare da kai mata duka ta ko ina yana neman hanyar da zai kusanceta ta ƙarfin tsiya. Kukan Muhseenah da ƙyallowarta bai hana shi cimma burinsa ba. Duk irin dagewar da Fauziyyah take yi sai da Abbas ya samu nasara akanta,saboda ƙarfin nasu ba ɗaya bane. Ganin ba ta samu damar hana shi ba,kawai sai ta saki jikinta ta koma kamar wata matacciya. Shi kaɗai ya gama budirinsa ya tashi ya na tofa mata yawu a fuska ya ce.
"Ga bunsuru nan ya yi miki aikin bunsuraye. Kuma daga yau mun ɗaura ni da ke,ki sake zuwa ki na yi min laɓe ki na ganin abinda nake yi. Idan na sake kama ki kina yi min laɓe na lahira sai ya fiki jin daɗi,jaka kawai. Ki tashi ki ɗauki yarinya ki bata abincinta !"
Abbas ya karasa maganarsa a tsawace. Kasa tashi Fauziyyah ta yi ballantana ta ɗauki yarinyar da ke sheƙa kuka kamar ana zarar tsokar jikinta. Dukan da Abbas ya kai wa Fauziyyah a gefen ciki ne ya sanyata ƙwalla ƙara tare da fashewa da kuka. Cikin azabar ciwon jiki da zuciya ta rarrafa ta ɗauki rigarta za ta saka,a hasale ya fizge rigar ya yi wurgi da ita sannan ya ce.
"Ɗaukan wannan shegiyar rigar ne ya fi maki mahimmanci akan ɗaukar min ƴa ki lallasheta?"
Cikin kuka da disashewar murya Fauziyyah ta ce.
"Rigata fa zan saka kafin na ɗauke ta."
"Ba za ki saka rigar ba to,ki ɗauke ta ki bata ta sha yanzun nan !"
Bata da wani zaɓin da ya wuce na ta ɗauki yarinyar ta na a halin rashin sutura a jikinta,wanda hakan sam bai dace ba a ganinta,gashi ko ba dan rashin sutura bama bata da tsarki, za ta so sai ta tsarkake jikinta kafin ta shayar da ita. Ji ta yi ya dangwara mata yarinyar a jikinta,da sauri ta riƙe ta ta rungumeta a ƙirjinta ta na mai sake fashewa da kuka. Tsaki Abbas ya ja ya ɗauki gajeran wandonsa ya saka ya bar ɗakin. Kai tsaye kitchen ɗin Barirah ya nufa saboda ya ɗebi ruwan zafi ya yi wanka. Sai dai ya na shiga ya tarar da wajen wayam babu ruwan zafi, sai tukunyar da ta ɗora abincin safe dake zaɓaɓɓaka a saman wuta. Haurin wata roba dake wajen ya yi da ƙarfi sai da ta fashe,a guje Barirah ta fita daga ɗakin Shehu na ƙwala mata kira amma ko ta kansa bata bi ba,ta na shiga kitchen ɗin ta rarumi muciyarta ta ƙerawa Abbas a tsakiyar bayansa sai da ya gantsare,ƙarar da ya saki ne ta sanya Fauziyyah saurin ajiye Muhseenah da ke shan mama ta zira rigarta ta na dafa bango ta yi waje,ganin Abbas a duƙe a kasa Barirah riƙe da muciya tana kuka tana yi masa masifa sai ya tsoratata. Barirah na ɗaga kai ta ga Fauziyyah cikin jini,fuskarta ta kumbura,sai ta sake ɗaga muciyar hannunta za ta kwaɗa wa Abbas a tsakiyar kai,Shehu ya isa a guje ya tare,haukacewa Barirah ta yi ta na wani irin surutu mara kan gado,babu wanda ya gane me take faɗa ballantana ya fassarawa Ɗan'uwansa. Banda ihun ta babu abinda ke tashi a gidan,tana yi tana nuna Fauziyyah dake maƙale a jikin labule ta toshe bakinta tana kuka. Da ƙyar Shehu ya ja matarsa suka koma ɗaki, shi ya koma ya kashe gas saboda abincin ya riga ya dahu. Abbas kuwa cike da jin zafin abinda ta yi masa ya hau faɗin.
"Ai dama kuɗin hayar ku saura kwana ɗaya ya ƙare,to ku tattara tsiyar ku ku bar min gidana,ƴan ta'adda kawai. Tsinannu matsiyata masu shiga harkar da ba ta shafe su ba."
A duƙe ya koma ɓangaren su ya ɗebi ruwan sanyi ya yi wanka sannan ya koma ɗaki ya shirya fita. Kallon Fauziyyah da ke zaune rungume da Muhseenah ya yi ya ce.
"Zan fita na dawo da break,ki tabbata kin sama min abinda zan ci,idan ba haka ba abinda zan yi miki sai ya fi na ɗazu."
Gyaɗa masa kai ta yi kawai,domin ta kasa samun ƙwarin guiwar amsa kalaman sa. Cikin ɓacin rai ya fita daga ɗakin yana sake goge takalminsa. Sallamar cousin ɗinsa ce ta sanya shi wurgar da takalmin a ƙasa ya taka ya na faɗin.
"Haydar ya aka yi? Ya mutanen gi.... Haydar me ya faru kake kuka?"
Sake rushewa da kuka yaron ya yi kafin ya ce.
"Yah Abbas ina ka shiga ina ta neman wayarka ɗazu ba a same ka ba har Hajiya ta rasu?"
Zubewa a guiwowinsa Abbas ya yi,wani irin duhu ne ya mamaye shi har baya ganin gabansa,cike da tashin hankali ya hau ƙoƙarin dafa gini domin ya tashi,sai dai kafin ya riƙe ginin kansa ya kai ƙasa,a gigice Fauziyyah ta yi kansa riƙe da Muhseenah a hannunta. Kuka ta fasa ta na kiran Shehu da ƙarfi.
"Yayah ! Yaya ku zo don Allah ku taimaka min Abbas ya faɗi. Na shiga uku na lalace ni Fauziyyah ina zan saka raina? Hajiya ta mutu ta barni,ita kaɗai ce ta rage min da ke iya tanƙwasa Abbas gashi yanzu ta mutu. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un,ina ma a ce ni ce na mutu ba Hajiya ba,wayyoo mutuwa me yasa baki ɗauke ni na huta da baƙin cikin duniya ba?"
Kalamanta sun yi kama da na wadda ta ɗimauce ta gigece sannan ta fita daga hankalinta. Kan dole Barirah ta daure ta fito ta hau lallashinta,tana nuna mata illar abinda take yi. Ɗaki Barirah ta kaita ta shiryata cikin riga da zani ta sanya mata hijabi,sai Shehu ya goya Abbas a bayan babur ɗinsa,ita kuma Haydar ya ɗauke ta a bayan nasa babur ɗin suka tafi gidan Kawu.
Su na zuwa gidan suka tarar da mutane sun cika ƙofar gidan ana zaman makoki,jikin Abbas sake mutuwa ya yi, har sai da Shehu ya taro shi. Da ƙyar ya iya zama a bakin tabarma mutane na ta yi masa ta'aziyya,hawaye ne masu zafi ke zuba daga idanuwansa ya na jin zafin su na ƙona masa kunci. Fauziyyah na isowa Kawu ya ga fuskarta a kumbure hancinta a fashe,sai ya miƙe ya isa wajen Abbas ya damƙi wuyansa ya hau falla masa mari,ko gezau Abbas bai yi ba,ballantana ya hana shi dukan nasa. Cikin matsanancin kuka Kawu juya wajen Babban wansu ya ce.
"Yaya ka ga abinda Addah Hajjo ta ke faɗa ko? Mafarkinta ya tabbata. Baiwar Allah'n nan ko magana bata iya yi,amma da yake da baƙin cikin ka za ta koma ƙiyama,sai da bakinta ya buɗe ta hau zayyana mana mugun mafarkin da ta yi akan kana dukan matarka,sannan ta ce kada mu sake mu bari ka zo saman gawarta,ta yafewa duniya kai. Dan haka muma bama ƙaunar ganinka anan,ka tattara naka ya naka ka bar nan,idan ba haka ba ƴan sanda zan kirawo su tafi da kai,domin ka cancanci hakan. Baƙin mugu azzalumin yaro kawai. Ke kuma kar ki tafi wajen dangin ki,ki zauna zaman soyayya da ƙaunar wanda bakya gabansa,watarana idan ya yi ajalinki fatalwarki ta ce dama Kawu ya faɗa."
Ya na gama faɗar haka ya kalli Haydar ya ce.
"To ɗan iya, ɗan kanzagi,sai ka ɗauke shi ka mayar da shi tinda babu wanda ya aike ka ɗakkosa."
Kan Haydar a ƙasa ya fara ƙoƙarin ɗaga Abbas dake zaune daɓas a ƙasa ya na kwarar da hawaye. Wajen sai ya ɗauki surutu da ra'ayoyin mutane,wasu na ganin gwanda da Kawu ya yi wa Abbas haka. Wasu kuma suna ganin bai kamata ba ya tozarta shi cikin jama'a,ko babu komai mahaifiyarsa ce ta rasu. Shehu ne ya duƙa ya taya Haydar ɗaga Abbas. A machine suka tafi su uku Haydar ya riƙe Abbas a baya. Gida suka mayar da shi,Fauziyyah kuma ta shiga gidan ta'aziyyah ta na ƙunshe fuska a hijabi gudun kar a ga fuskarta. Sai dai ganin kallon da ake binta da shi ne ya tabbatar mata kuskuren da ta yi na shiga gidan ta'aziyyar. Cikin sauri ta juya ta bar gidan. Mai adaidaita sahu ta tare ta faɗa masa inda zai kai ta. Suna zuwa ta ce ya jira ta kawo masa kuɗinsa. A wajen Barirah ta karɓi kuɗin ta sallame shi. Kai tsaye ɗakinsu ta shiga,Abbas ta gani ya takure waje ɗaya ya na kuka kamar wani karamin yaro. Cikin sauri ta isa wajensa ta saka hannayenta biyu ta rungume shi tana hawaye. Sake rungumeta ya yi har sai da ta rintse ido saboda zafin da ta ji a daidai inda ya ɗirka mata duka a ciki. Kuka ya dinga yi yana faɗin.
"Ki yafe min Fauziyyah,ki yafe min duk abubuwan da na yi miki don Allah."
Wani irin sanyi Fauziyyah ta ji ya dira a zuciyarta. Ta jima tana dakon ranar da Abbas zai nemi yafiyarta su zauna lafiya fiye da zaman da suka yi a baya. Sake danna kansa ta yi a tsakiyar ƙirjinta ta na kuka ta ce.
"Na yafe maka My king,yanzu ba lokacin surutu bane,lokaci ne da za mu yi wa Hajiya addu'ar Allah Ya jiƙanta,Ya gafarta mata,Allah Ya sa halayenta na gari su bi ta."
Jiki na rawa Abbas ya hau yi wa Hajiya addu'a yana maimaitawa. A haka suka wuni ko abinci basu nema na. Cikin tausayawa Barirah ta kawo musu abinci da la'asar ta ce su daure su ci. Nan ma Abbas sai da ya nemi yafiyar Barirah,ta kalle shi a sheƙe ta watsar ta bar ɗakin ba tare da ta ce masa komai ba.
Washegari da safe malaman makarantar da Abbas ke koyarwa da ɗalibai ne suka dinga zuwa yi masa ta'aziyya,su Salman na zaune da shi,da an kawo abun sadaka su sa a gaba su lamushe. Sai dare suka yi masa sallama suka tafi. Haka aka ci gaba da zaman makoki har kwana bakwai. A kwana na bakwai su Shehu da Barirah suka gama kwashe kayan su suka yi sallama da maƙota da abokan arziƙi suka koma sabon gidansu. Wannan rana tamkar an sake yi wa Fauziyyah wata mutuwar haka ta zamo angare ta. Ta yi kuka ta yi kuka har hawaye sun daina zuba a idanuwanta. Barirah kanta da kuka ta bar gidan tare da yi wa Fauziyyah addu'ar samun sauƙi a zamantakewarta da Abbas da za ta yi a nan gaba.......
*Hummm to makaranta anan zan tsaya da tura maku free pages. Wanda suka roƙi na ɗan ƙara yawan free page gashi na cika muku alƙawarin ku,sai dai ku sani idan fa ba antayowa kuka yi da ƴan mutsabban ku kuka sayi littafin nan ba,ba zaku san wainar da za a soya ba anan gaba. Ko kuna zaton Abbas ya tuba kenan ya dena halinsa? Kun san wace rayuwa Fauziyyah zata sake fuskanta anan gaba? Wanene Abdullah a rayuwar Fauziyyah? Ina iyayenta suke take shan azabar miji irin wannan? Ya rayuwar Muhseenah za ta kasance a lokacin da ta girma ta buɗe ido ta ga Abbas a matsayin mahaifinta? Ku biyo ni da ɗarin ku biyar ku sha labari.*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨
PAGE 16.
*SANARWA.*
*Masu son su siya ku sanya 500 ta 0006366584 Hamida Sanusi Ahmad Ja'iz Bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.*
Bayan kwana arba'in da rasuwar Hajiya,sai ƴan'uwanta suka kira Abbas suka tasa shi a gaba da nasiha da faɗa akan ya gyara rayuwarsa,ko Allah zai sa a dinga tada Hajiya a ƙabari ana nuna mata ayyukansa na alkhairi ba sharri ba. Abbas kuka ya dinga yi yana nadamar abubuwan da ya aikata a baya,daga ƙarshe suka haɗu sukai ta lallashinsa su na bashi baki,da ƙyar ya yi shiru ya na sunne kai ƙasa kamar na Allah. Daga nan kuma sai suka tattara duk wata dukiya da Hajiya ta bari wadda ya gadata daga wajenta suka bashi abun shi,hatta da takardun gidanta basu riƙe ba sun bashi tinda ya mallaki hankalin kansa. Yana godiya ya yagi abinda zai yaga ya basu,su kuwa sai suka ƙi karɓa sai ya bawa ƙannensa na gida,wato abokan wasansa ya yi musu sallama ya tafi. A hanya haka ya tsaya ya siyi kayan abinci sosai har da doya da ƙwai da nama,da kifi haɗe da kayan miya ya isa gida. Ranar haka suka yi kwanan farinciki shi da Fauziyyah. Washegari ya hau machine ya je gidan Hajiya ya ga kayayyakin dake ciki,manyan fridge guda biyu da take sana'ar sayar da ruwan sanyi a lokacin zafi,sai kujeru da gadaje biyu,da sauran tarkace na amfanin yau da gobe. Waje ya fita ya nemo ɗan sahu ya ɗaukar masa fridge ɗaya ya kai gidansa. Ranar Fauziyyah ta yi murna ta yi farinciki sosai, kwashe kayan miya da kifi da naman da ya siyo ta yi ta saka a ciki. Sai ruwa da ta zuba a gorunan lemon da Abbas ke sha kullum ta zuba ta adana. Kafin wata biyu su cika kyawu da hasken fatar Fauziyyah sun dawo,ta yi wani irin kyau ta yi ɓulɓul gwanin sha'awa. Ƙaramar waya ta roƙi Abbas da ya siya mata,kallon ta ya yi yana murmushi ya ce.
"Ai My Queen yanzu babu ke babu riƙe ƙaramar waya,dan kuwa kin fi ƙarfinta. Babbar waya zan siyo miki kema a dama dake."
Cikin tsananin murna Fauziyyah ta daka tsalle ta rungume Abbas. Da dare kuwa kamar yanda ya yi mata alƙawari,haka ya kawo mata dalleliyar waya me kyau ya damƙa mata a hannunta. Har ƙasa Fauziyyah ta durƙusa tana godiya. Ɗagota ya yi ya rungume ya na shafa ta a hankali,suna nan tsaye suna farantawa juna Fauziyyah ta ce.
"Yauwa My king,ni kuwa ina so na tambaye ka, don Allah me yasa yanzu duk wasannin da za mu yi baka yarda ka kusance ni? Ko dai na yi maka wani abu ne? Ko kuma akwai abinda baka so a tattare da ni ne?"
Ɗan janyeta ya yi a jikinsa ya ja gajeran tsaki,a hankali ya zauna a bakin gado ya na faɗin.
"Don Allah Fauziyyah kar ki kawo maganar da za ta ɓata min rai. Idan baki manta yanda muka faro ba zan tuna miki. Kin sani bana son yawan yara a gida,ba zan iya da hayaniya da ɗawainiyarsu ba...."
"To amma ai gashi na haifa maka Muhseenah,kuma ta zamo abu mafi soyuwa a gare ka a yanzu,baka ganin nan gaba idan..."
"Babu wani gurbin soyayya da ya yi saura a zuciyata da zan iya bawa kowa a yanzu,dan haka kar ki sake yi min maganar haihuwa ko wani abu da ya danganceta bana so. Dama jira nake yi a kwana biyu na kai ki asibiti a ɗora ki akan tsarin iyali,idan kuma ba haka ba,sai dai mu yi ta zama a haka ba tare da saduwa ba. Zaɓi yana gare ki."
Ya na gama magana ya miƙe ya koma ɗakin da su Barirah suka tashi. Ya baza tabarma da pillow ya kwanta. Tsaki ya ja sannan ya ce.
"Dole ne ma gobe na kwaso kayan ɗakin dake gidan Hajiya na gyara nan kawai,ita ta je ta ji da can ɗin dan bana son damuwa."
Abu kamar wasa washegari ya tasa Fauziyyah a gaba akan ta shirya su je asibiti a ɗora su akan tsarin iyali. Duk wata hanya da za ta bi ta kauce wa fitar,ita ta dinga bi. Ganin haka sai ya sanya Abbas ɗaga kafaɗarsa ya fice daga gidan ba tare da ya ce mata komai ba. Tin daga wannan ranar Abbas ya kwaso kayan gado da kujerun parlourn Hajiya Fauziyyah ta shirya masa ɗakin da Barirah ta tashi. Tv da sauran kayan kallo duk ya kwaso ya haɗa a ɗakin. Rayuwarsu sai ta koma daga gaisuwa sai ya ci abinci ya fice,da ya dawo daga aiki ya kwanta ya huta,da yamma ya ɗauki wanka ya fita. Tin Fauziyyah na iya jurewa har ta kasa jurewa,watarana ta roƙe shi akan tana so ta je ta gaishe da su Barirah,tinda suka koma sabon gidan bata je ba,sai dai ta yi ta bata uziri a duk sanda ta kawo musu ziyara. Abbas kafewa ya yi ya ce ya raba tsakaninta da Barirah har abada. Tinda ita ɗin munafuka ce,dama ya kula duk ranar da ta kawo ziyara sai Fauziyyah ta sauya hali,to daga yau kar ya sake ganin ƙafar Barirah a gidansa,idan kuwa ta zo sai ya ci musu mutunci gaba ɗayansu. Kuka Fauziyyah ta dinga yi ta na roƙon sa ya barta ta je amma ya ƙi sam. Ƙarshe ma wanka ya yi ya bar mata gidan.
Haka rayuwarsu ta ci gaba da tafiya har Muhseenah ta kai watanni bakwai a duniya. A wannan lokacin Fauziyyah ta kai maƙura wajen buƙatuwa da son kasancewa da mijinta,har mamakin yanda take jin tsananin ƙauna da sha'awarsa take yi,shi kuwa yana sane da yanda take maitarsa,da dare haka zai hau yawo tsakanin ɗakinta da nasa tsirara-tsirara,haka za ta yi ta binsa da kallo kamar mayya, watarana har da magiya take yi masa,amma haka zai yi burus da ita,gaba ɗaya rayuwa bata yi mata daɗi a gidan,ta kuma rasa yanda za ta yi ta jawo hankalin Abbas zuwa gareta. Sai dai shi a ɓangarensa ko a jikinsa,wai an tsikari kakkausa. Domin kuwa ya jima da samarwa kansa mafita ta hanyar zuwa gidan Babson ya ɗauki macen da ta yi masa ya kai ta gidan Hajiya da dare su sha soyayyarsu,da ya gama abinda zai yi da ita sai ya faki idanuwan mutane ya sallame ta,shi kuma sai ya tabbata ta jima da barin unguwar sai ya fito ya kulle gidan. Duk wannan badaƙalar da yake yi babu wanda ya kula da shi a unguwar, kasancewar idan yamma ta yi unguwar shiru take zamowa. Ba kamar cikin gari bane da yara da manya ke ta kaiwa da komowa. Shawarar da suka yanke na saka ƴan haya a gidan sai ta tashi,domin ba shi kaɗai bama,hatta su Salman idan suna son aron wajen hutawa da ƴan matansu nan suke zuwa.
Idan ya dawo da dare kuma da ya gama cin abinci sai ya kora Fauziyyah ya kunna BF ya yi ta kallo,ko ya kira Nana a waya su yi ta musayar videos da hotunan banza a tsakaninsu tare da hirar banza. Tin Fauziyyah bata sani ba har sai da watarana da daddare ta ji hadari ya taso,sai ta fita kwashe kayan Muhseenah da ta wanke,tana zuwa daidai ɗakin Abbas ɗin sai ta ji abubuwan da yake aikatawa. Kayan da bata kwashe ba kenan ta koma ɗakinta ta na gunjin kuka kamar ranta zai fita daga jikinta. Ta rasa yanda za ta yi ta ja ra'ayin Abbas zuwa gare ta har ya kusanceta. Duk wata kwalliya da ake cewa mata su na yi dan ta ɗauki hankalin miji ya neme su,ko su shafa turare ya tada wa maza sha'awa Fauziyyah ta yi,daga ƙarshe har ta gaji da nemansa ta fara guje masa dan kare kanta daga kwana da mummunan ciwon mara.
Cikin ƙanƙanin lokaci ƙiba da hasken da ta yi na hutu duk ya tafi. Tsananin damuwa da tashin hankali ya maye gurbin farincikin da ta samu na ɗan lokaci. Shawara ta yanke domin bin umarnin Abbas ɗin, dan haka watarana da yamma bayan ta kammala ayyukanta ta kaiwa Abbas abincinsa parlournsa sai ta salla wankanta,ta na fitowa sai ta ɗakko kayan gyaran jikinta na haɗin farar shinkafar da ta jiƙa ta kwana ta markaɗe ta da turmeric,cinnamon,zuma da castor seed( ƴaƴan gelo/ wasu su ce masa babba juji,to wannan ƴaƴan na jiki)sannan ta fasa ƙwai a ciki ta matse lemon tsami dan ya kashe ƙarnin ƙwan sannan ya gyara mata fata,madarar ruwa ta tsiyaya kaɗan ta shafe jikinta da haɗin,murje jikinta ta yi sosai na tsawon minti talatin. Wanka ta koma ta yi da zallan ruwan ɗumi. Ta na fitowa ta shafa skin oil ɗin da Barirah ta bata tin kafin ta tafi na Hamibrah,kallon robar ta yi ta ga sauran kaɗan ya ƙare. Turare ta fesa ta saka wata yaloluwar rigar bacci,sannan ta ɗaura zani ta yi sallar magariba, addu'a ta dinga yi akan Allah Ya yi mata zaɓin alkhairi. Ta na nan zaune aka kira sallar Isha'i,sai ta gabatar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 12