Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
12 / 12
ta inda za ta ga Abdullahnta ya ɓullo. Ganin Mama da Fauziyyah sun shiga a tare ne ya sanya ta sake sakin murmushi ta miƙe tsaye ta na faɗin. 'Ah ah Yayah har dake ake tafe? Bismillah ku shigo.' 'Da alama dai wannan fara'ar ba tawa bace. To kar ki damu ɗan naki na nan shigowa yanzu. Na same ku lafiya?' Sallamar Abdullah ce ta katse musu hirar tasu,cike da maɗaukakin murmushi Mama ta ke kallon ɗan nata da ya zamo babban mutum. Hannunsa ta kama ta na faɗin. 'Oyoyo Abdullahna sannu da zuwa, bismillah shigo ka zauna.' Sai da ya durƙusa ya gaishe ta har ƙasa sannan ya zauna kujerar da ke daf da tata,hira suka dinga yi yana bata labarin kasuwarsa da kuma albishirin sabuwar motar da ya siya. Muryar Abbah ce ta katsewa Ummah addu'o'in da take ta zubawa. Cike da fara'a Abbah ya ce. 'Ai bamu jima da tattaunawa da Yaya ba akan sabuwar motar taka,na ce to an yi sabuwar mota saura kuma sabuwar amarya ko? Wannan karon mun gama yanke shawarar ba za ka koma ba har sai ka samu matar aure. Dan zama kudun nan babu mace bai yi ba a wajen ɗan musulmi.' Kafe Fauziyyah da ido Abdullah ya yi kafin ya ce wa Abbah. 'Abbah ai ni na samu matar aure bana. Addu'ar ku da fatan alkhairi kawai nake buƙata.' Guɗa Ummi ta saki ta miƙe tsaye ta na hamdala,kallon Mama ta yi ta ce. 'Yanzu Yaya dama kin san da wannan albishir ɗin shine baki faɗa min ba?' Ɗaga hannuwa sama Mama ta yi sannan ta ce. 'Haram,sam ban san da wannan labarin ba sai yanzu. Gashi nan kuma ki tambayesa.' 'Ummina ai ni kaina ban san da matar ba,sai yau na ganta da idona,na rasa hankalina ina yake tina da ban gano matata tana kusa dani ba sai yanzu.' Da jin kalamansa sai iyayen nasu suka ɗago abinda yake nufi,nan take kunya kuma ta kama Ummi,cikin sauri ta koma ta zauna,Mama kuwa sai ta hau yi mata dariya ta miƙe ta yi musu sallama ta wuce gida. Fauziyyah da bata gane abinda Abdullah yake nufi ba sai ta dinga murna ta na faɗin. 'Yayahna don Allah ka kaini wajenta na ganta,Allah Ya sa tana da kyau,dan gaskiya ka auro mummuna ba zan yi Auntyn da ita ba' 'Matar da nake so ai tafi kowacce mace kyau a duniyar nan. Ke dai kawai ki shirya shan biki kwanan nan kawai.' Dariya Fauziyyah ta yi sannan ta ce. 'Kai Yayahna da sauri haka kamar dama jira kake ayi maka maganar aure?' 'Ai su Abbah sun jima suna yi min magana akan na yi aure. Ni ne dai na makance ban ga matar tawa ba da wuri,amma yanzu tinda na samu sauƙin makantar tawa komai ya zo ƙarshe.' Ganin surutun Fauziyyah na neman yin yawa ne ya sanya Ummi aiken ta ta ɗakkowa Abdullah abubuwan da suka tanadar masa. Fitar ta ke da wuya Abbah ya yi gyaran murya sannan ya ce. 'Ina so bayan Isha'i ka same mu a babban gida ni da Yaya,akwai maganar da za mu tattauna game da abinda kake faɗa a yanzu,sannan ka tabbatar da gaske kake akan ƙudirin ka,domin bana son a zo ana yin kwan gaba kwan baya a wannan lamarin,ko a yi abinda zai taɓa zumunci.' 'Da gaske nake wannan maganar Abbah, in Allah ya so ba zan yi abinda zai taɓa zumunci ba. Na gode Abbah.' Abinci Fauziyyah ta durƙusa ta na zuba masa tana bashi labarin makarantar su,a haka Abdullah ya gama cin abinci ya ɗauki su Ummi a mota ya zaga da su,har da yi musu ƴar siyayya sannan ya dawo da su gida. Kamar yanda Abbah ya umarce shi da ya je babban gida bayan Isha'i,bai yi ƙasa a guiwa ba,ana idar da sallah ya wuce babban gidan. Ya na zuwa sai ya tarar da iyayensa har da ƙannin kakansu Wato Baba Amadu. Nan suka zauna suka tuntuɓe shi game da wadda ya ce ya samo a matsayin mata,Abdullah bai yi nauyin baki ba ya sanar da su Fauziyyah yake son ya aura. Hamdala suka yi sannan Baba Ilyas ya ce. 'Alhamdu Lillah,wannan shi ake kira da tuwona maina. Allah Ya sa ayi da mu.' 'Amin Yayah,Allah Ya sanya albarka a lamarin.' 'To Amin. Amma wani hanzari ba gudu ba,ina fatan dai ita yarinyar bata da wanda take so ko? Domin sanin kan ku ne,ba zai yu dan muna son mu ƙulla zumunci ba ita kuma a tauye ta.' Baba Amadu ya faɗa ya na ɓantarar goro yana kaiwa bakinsa. Cikin hanzari Abbah ya ce. 'A iya sanina Fauziyyah bata da wani saurayi da take kulawa,dan ita ko sallama aka aika ana yi da ita ma korar yaran take yi,bata kula kowa.' 'Amm don Allah ina neman alfarma,ina so a rufe maganar nan kar a sanar da ita har sai ta shiga aji biyu na sakandire,kafin nan ni kuma na ƙarasa gini na da nake yi anan,suna yin candy sai a yi komai a gama.' 'Meye dalilin ka na ƙin sanar da ita? Ka san fa mace allura ce cikin ruwa,kada ka tsaya kallon ruwa kwaɗo ya yi maka ƙafa fa Audu.' Cike da fara'a Abdullah ya kalli kakan nasu ya ce. 'Haba Kaka,idan dai ba kai ne za ka zagaya ka ƙwace min mata ba,ai kowa ya san ita bata soyayya,wannan dalilin ne ya sa bana son kawo mata cikas a karatun ta na raba mata hankali biyu.' 'To kai ma ka ce wani abu yaro,Allah Ya zaɓa maku abinda ya fi alkhairi.' Da wannan maganar aka rufe zancen Abdullah na son Fauziyyah har sai ta gama aji biyu na sakandire. Dan haka kafin ya tafi sai ya dinga yi mata jirwaye mai kama da wanka,har da waya ya siya mata ya ce za su dinga gaisawa. Fauziyyah ta yi murna sosai tare da farinciki. Bai tafi ba sai da ya sata ta yi masa alƙawarin ba za ta yi soyayya da kowa ba za ta mayar da hankalinta akan karatunta. Shiru ta yi ta na hango kyakkyawar fuskar Abbas a zuciyarta. A hankali ta ce masa. 'In Sha Allahu Yayahna na yi maka alƙawari ba zan yi soyayya da kowa ba,zan mayar da hankalina akan karatuna.' Har bakin mota ta raka shi tana ɗaga masa hannu. Tin daga wannan ranar Fauziyyah ta dena yarda ta keɓe daga ita sai Malam Abbas. Shi kuma Abbas sai ya shiga matsanancin tashin hankali da damuwa. Wanda har Hajiya sai da ta gane yana cikin damuwa mai girma. Duk yanda za ta yi ta kwantar masa da hankali ta yi,amma Abbas na nan jiya i yau. Ga shi Fatimah tinda ta fara samun abinda take so a wajensa ta fara yi masa wulaƙanci kamar ita ce namijin ba shi ba. Duk sanda ta so keɓewa da shi haka za ta ce masa ya same ta a inda suka saba haɗuwa za ta shawo masa kan Fauziyyah,Abbas kuwa kamar soko haka zai je ya sameta su gama sheƙe ayarsu,ta bashi labaran ƙarya akan Fauziyyah na son shi amma ta ce ya bari su gama makaranta sai ya je gidan iyayenta ya nemi aurenta. Cike da damuwa Abbas ya ce mata. 'To ni da ba soyayyar aure nake yi mata ba me zai kai ni ganin iyayenta?' 'Ka manta shawarar da na baka tin farko? Ka aure ta mana ka barji sadakin ka sai ka sake ta daga baya.' Ajiyar zuciya Abbas ya sauke,ba tare da ya ce komai ba ya wuce gida ya na ƙulla ko dai sace Fauziyyah zai yi ya kaita gidan Babson ya gama abinda zai yi da ita sai ya wurgar da ita? Kaɗa kansa ya yi cikin sauri tare da faɗin. 'Inaa idan asirina ya tonu ai sai hakan ya yi ajalin Hajiyata. A yanzu ma fama take da halina ina ga na fara aikata fyaɗe kuma? Kaiii Allah ka kai damo ga harawa,ya ci ya sha ya yi birgima a cikinta.' Duk wannan bidirin da ake yi, Fauziyyah daure zuciyarta kawai take yi,domin kuwa a duk lokacin da Abbas ya shiga ajin su koyarwa sai ta yi fama da jinyar zuciyarta idan ta koma gida. Wani irin azababben so take yi masa mara misali. Alƙawarin da ta yi wa Abdullah ne ke ƙara danne son zuciyarta. Shi yasa ko Fatima ta yi mata maganar Abbas sai ta nuna mata sam ita ba soyayya ce ta kawo ta makaranta ba,idan ya matsu yana son ta ya je gidan iyayenta ya gabatar da kanshi,amma ba ya dinga damun ta a makaranta ba ta na karatunta. Ana haka har suka yi hutun makaranta,rashin ganin Abbas da Fauziyyah bata yi ba a cikin hutun sai ya ƙara rura wutar soyayyarsa a ranta,haka za ta zauna a ɗaki ita ɗaya ta ci kukanta ta gode Allah. Wani lokacin ma har zazzaɓi take yi,sai ta yi da gaske ta yakice damuwarsa a ranta take samun kanta. Suna gab da komawa makaranta Abdullah ya yi mata aiken kuɗi da kayayyakin ƙwalama da kuɗin siyan sabon uniform. Murna sosai Fauziyyah ta dinga yi ta na yi masa godiya. Daga ƙarshe maƙotansu ta kai ɗinkin uniform ɗin aka yi mata mai kyau ya fitar da shape ɗin ta da kyau. Ranar komawa makaranta da ta zagayo ta sa sabon kayanta ta sha gayu ta na zabga ƙamshin turaren da Abdullah ya siya mata ta wuce makaranta. Babban buri da fatanta bai wuce na ta yi tozali da Abbas ba a ranar farko. Sai dai kashh. Mummunan labarin da ya riske ta ne a wajen Fatima ya yi masifar ɗaga mata hankali har ya yi sanadiyyar faɗuwarta ƙasa sumammiya,a guje ɗalibai ƴan'uwanta suka ɗauketa suka kai ta office ɗin da suke karɓar magani,kwantar da ita aka yi a saman benci aka zuba mata ruwa a jikinta,da ƙyar Fauziyyah ta farfaɗo. Ta na buɗe idonta ta zuba shi a kan fuskar Principal ɗin su sai ta rushe da kuka. Cike da tashin hankali principal ya fita waje ya kira mahaifinta a waya ya sanar da shi abinda ke faruwa,wanda sam basu san dalilin faɗuwarta da suman nata ba. Cikin tashin hankali Abbah ya zo makarantar shi da Baba Ilyas,domin suna tare aka kira Abbahn sai kawai suka taho a motar Baba Ilyas ɗin. Gida suka wuce da Fauziyyah dake kuka kamar ranta zai fita daga jikinta,tambayar duniya an yi mata dan ta faɗi abinda ke damunta amma ta ƙi sanar da kowa damuwarta. Haka Abbah ya haƙura ya fita ya barta da Ummi,wadda ta fara hasala sosai akan lamarin Fauziyyar. A tunanin su idan ta kwana ta tashi za ta manta da komai,sai suka ga ashe wasa ma farin girki ne,domin kuwa da safe sai da suka ɗauke ta suka kai ta asibiti likita ya duba ta. Gargaɗinta likita ya yi akan ta rage sanya damuwa a ranta tana da ƙananan shekaru. Daga nan ya bata magungunan da za su saukar da zazzaɓi da zafin jikin da take fama da shi suka koma gida. Sai da Fauziyyah ta cinye sati guda ta na ciwo bata zuwa makaranta. Wata ranar alkhamis da misalin goma na safe ta na zaune ta ji wayarta na ringing,bata so ɗauka ba saboda rashin son yin magana da bata yi. Nacin da aka sa wajen kiran wayar ne ya sanya ta miƙa hannu ta ɗauka. Ganin baƙuwar lamba ne ya sanya ta haɗe girarta ta amsa kiran tare da kara wayar a kunnenta ta ce. 'Assalamu alaikum.' Wata wawuyar ajiyar zuciya Abbas ya sauke mai ƙarfi,da jin haka sai Fauziyyah ta miƙe tsaye da sauri jikinta na rawa ta shige ɗakinta ta tura ƙofa, durƙusawa ta yi a jikin gini ta na zubar da hawaye masu mugun zafi. Cikin sassanyar murya Abbas ya ce. 'Fauzyy.' Shessheƙar kuka ta fara yi wanda ya sake rikita Abbas ya jefe shi shiga damuwa,a hankali ta ce. 'Malam Abbasss ina son ka don Allah ka dawo.' Wani irin tsallen murna Abbas ya daka,har sai da su Salman suka hau tambayarsa da hannu me yake faruwa ko ta amince tana son sa ne? Da kai ya basu amsa sannan ya ci gaba da marairacewa kamar ta na ganinsa ya ce. 'Ah Ah Fauziyyah gwanda kawai na yi nesa da ke,wataƙila hakan ne zai sa na manta da ke da irin soyayyar da nake yi miki,dama bahaushe ya ce son maso wani ƙoshin wahala ne. Gashi ina ta fama da wahalar rashin ki a rayuwata Fauziyyah. Yanzu ma na kira ki ne dan na ji muryar ki ta ƙarshe saboda garin zan bari gaba ɗaya.' 'Idan ka tafi ka bar garin gaba ɗaya na tabbata ni kuma duniyar zan bari Malam Abbas. Don Allah ka dawo ina son ka. Ina yi maka son da ni kaina ban san kalar sa ba,ban san yaushe na yi zurfi a cikinsa ba,bana iya bacci,bana iya cin abincin kirki,bana iya maida hankali akan karatuna. Don Allah kar ka tafi ka barni,zan iya rasa raina.' Wani abu Abbas ya ji mai ƙarfi ya caki zuciyarsa,tinda yake biye-biyen mata bai taɓa haɗuwa da mace me kyau,hankali,natsuwa da kamun kai kamar Fauziyyah ba,sai kuma gashi ta na yi masa soyayya ta gaskiya,ba kamar sauran matan da ke son sa dan iya kyawunsa ba da ƙwarewarsa a bariki. Lallai lokaci ya yi da zai zubar da komai ya yi aure,domin Fauziyya ita ce kalar matar da idan ya aure ta ko abokansa sai sun jinjina wa ƙoƙarin sa na zaɓar kyakkyawa kamarta. Cikin sauri ya ce mata. 'To shikenan na ji zan dawo,amma ki sani saboda ke kawai zan dawo. Ina son ki Fauziyyah. Soyayyar da ba zan iya misalta maki irinta ba,sai ranar da kika zamo mallakina.' Wani irin farinciki ne ya lulluɓe Fauziyyah tare da jin tsananin kunyar Abbas kamar yana ganinta. Da sauri ta kashe wayar ta kwanta a ƙasa ta na birgima tare da ihun murna. Ummi ce ta shiga ɗakin da gudu ta ganta kwance a ƙasa ta na birgima,sai ta hau salati tana faɗin. 'Na shiga uku ni Zuhairah me nake gani haka? An bar kukan yanzu kuma dariya aka koma yi da juye-juye? Malam ! Ma...' Rungumar da Fauziyyah ta yi mata ce ta sanya ta yin shiru,cikin tsananin murna Fauziyyah ta ce. 'Ummina zauna yau na baki labarin abinda ke damuna da na kasa sanar dake a baya. Ummi i am in love..Ummi ina son shi,ina son shi kamar raina. Idan bai aure ni ba Ummi mutuwa kawai zan yi dan...' 'Ke rufe min baki shashashar banza kawai,waye idan bai aure ki ba za ki mutun? Ko an faɗa miki Abdullah soko ne irin ki da zai sauya magana bayan ya riga ya yi ta?' Haɗiye maganar bakinta Fauziyyah ta yi kafin ta ce. 'Wanne kuma Abdullah Ummi? Ina yi miki maganar Malam Abbas ki na maganar Abdullah.' Tsaye Ummi ta miƙe ta na bin Fauziyyah da soyayya ta haukata ta manta da wa take magana da kallo,za ta sake buɗe baki ta yi magana Ummi ta daka mata tsawa,cike da masifa Ummi ta ce 'Wanene kuma Malam Abbas Fauziyyah? Meye a tsakanin k da shi? Ki buɗe baki ki sanar dani abinda ke faruwa yanzun nan ko na yi miki shegen duka.' Jikin Fauziyyah ne ya hau rawa ta fara ja da baya. Finciko ta Ummi ta yi za ta mare ta,da sauri Fauziyyah ta dunƙule waje ɗaya ta ƙwalla ƙara,a tsorace Abbah ya shiga ɗakin ya na faɗin. 'Lafiya nake jin kina ɗaga murya haka?' 'Ina fa lafiya Malam. Yarinyar nan so take ta watsa mana ƙasa a ido,muna yabon ta sallah za ta kasa alwala. Wai soyayya take yi da Malamin makarantar su.' 'Wanne irin soyayya da malamin makarantar su kuma ana zaune ƙalau?.' 'To gata ai sai ka tambaye ta.' Zama Abbah ya yi a gefen gadon Fauziyyah ya riƙe ta a jikinsa,ganin haka sai Ummi ta yi ƙwafa ta bar musu ɗakin cikin ɗacin rai. A hankali da dabara Abbah ya ji labarin Malam Abbas a bakin Fauziyyah,tin daga ranar da ta fara son shi,har ƙoƙarin avoiding ɗinsa da ta dinga yi,har zuwa labarin da ta samu na zai bar koyarwa a makarantar a wajen Fatima ƙawarta,da kuma ciwon da ta yi akan soyayyarsa,kawo zuwa wayar da suka gama yi yanzu. Salati Abbah ya dinga jerawa. Ba tare da ya ce mata komai ba ya miƙe ya zira takalmansa ya bar gidan............ *Abbah zan bika na ji ina zaka je nima😂* RUBUTAWA :HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️ Wannan littafin na kuɗi ne,idan kina son karantawa har ƙarshe biya #500 ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi ko kuma 0006366584 Ja'iz Bank Hamidatu Sanusi Ahmad. Ki tura shaidar biya ta,09031416423. Mutanen Niger kuma za ku iya biya ta 96988833 Soueba sani idi,sai ku tura shaidar biya ta 09031416423. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 12 of 12