Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 12
ce da ta maida ki kamar buhu babu gaba babu baya? Kar ki ji komai,domin kuwa na zo maki da ingantaccen maganin hausa wanda bashi da illa ga lafiyar jiki a farashi mai sauƙi cikin kwana uku zaki fara ganin sauyi,a kwana bakwai kuwa shape ɗin ki zai bayyana ki huta da nauyin jiki.* *4-Kina son ki samu glass skin da an hango ki a ga yanda fatar ki ke haske da walƙiya tare da ɗaukan ido? Kema zo nan kar ki wuce na tanadar maki naki kayan da za su kyautata fatar ki.* *5-Kina fama da matsalar ciwon sanyi mara jin magani? To ki zo na baki maganin da zai wanko maki shi,za ki gansa da idon ki yana fita kamar dusar awara,har ya wanke ruwan ni'imar jikin ki ya bayyana ki mori rayuwar auren ki.* *Gaba ɗaya za ku iya samu na a wannan No 08038086083.* Turus Barirah ta ja ta tsaya a tsakar gidan,ta na aikawa Abbas da abokansa da suke ta lashe hannu kamar tsofaffin mayu harara. Da ƙyar ta iya danne fushinta ta kalli Hajiya dake ta ƙoƙarin haɗa wuta a jiƙaƙen murhun Fauziyyah ta ce. "Hajiya ai da kin bar kunna wannan murhun tinda an jiƙa shi,ga kuma yanayi na damina itacen ma kansa a jiƙe yake." "Wai ai na ga a gas kike ɗora ruwan ne,kar ku yi ta asarar gas ɗin tinda shi dai iskar banza ce,babu wuya ya ƙare." Murmushi Barirah ta yi kafin ta ce. "Ai da yake ya fi sauri ne wajen aiki shi yasa nake jin daɗin aiki da shi,nan da nan sai ya biya miki buƙata ki tashi abunki." "To da wannan dan wannan kuma. Maza ɗebo ruwa ki gani ga wutar nan ta kama ganga-ganga,idan na tafi kun yi a gas ɗin naku na ƴan zamani,yanzu fa sauƙi ya samu ba kamar da ba da mata suka sha wahalar rayuwar gidan miji,shi yasa nake mamaki idan na ga yarinyar nan ta nace ita ba ta son aiki a risho ko gawayin nan me saurin aiki wai ita ta fi son itace,ko meye abun daɗi a girki da itace oho? Ko ni da nake tsohuwa a kurfotina nake girki yanzu,ko na saka kalanzir a risho na ɓararraka abinda zan ɓararraka na tashi." "Humm samu ne fa da bata yi ba Hajiya,domin babu wanda baya son hutu a rayuwarsa,ai na so itama Fauziyyahn na da gas ɗin musamman a lokacin da take da ciki. Tin kafin a kira sallah sai ki ga ta fito kunna wuta,watarana har gari ya yi haske wutar bata kama ba,yanzu kuwa ga yarinya,idan me ƙiwa ce haka fa za ta fito da ita cikin sanyin daminar nan,ta dalilin hakan sai ki ga sanyi ya kama ta." "Wannan gaskiya ne,ya kamata itama a samar mata da gas ɗin nan,domin ta huta. Bari zan yi wa Abbas ɗin magana ai,zuwa ƙarshen wata ko da kuɗinta na wajensa ne sai a siya mata,kin san halinsa yanzu sai ya ce ba shi da kuɗi,to tinda yarinya da dukiyarta ai sai a yi mata abinda ya kamata ko ba haka ba?" Cikin sauri da murmushin mugunta Barirah ta ce. "Sosai ma kuwa. Kuma yanzu yanda abubuwan zamani suka shigo da suke sauƙaƙawa mace ayyuka,tsaf zai iya siya mata injin wankin nan,su blender iron da standing fan,gashi bana muna samun wuta sosai ba kamar da ba da sai a wuni babu wutar." "Ƙwarai da gaske. Kai amma dai wannan yarinya Allah Ya yi miki albarka,ai ni duk ban yi wannan dogon nazarin ba,bari a gama hidimar suna sai mu yi maganar dashi,ba zan barsa ya huta ba har sai ya siya mata ƴan abubuwan da za ta dinga hutawa da ayyukan gida,yanzu zamani ya sauya,mata sun dena wannan wahalhalun ai. Yarinya da uwar kuɗinta ta zauna ta na izar jiƙaƙƙen itace?" "Ah toh, dan a yanayin nan na damina fa sai ta kunna wutar sannan ta tara garwashin da za ta yi guga,lokacin guga da dutsen ƙarfe ai ya wuce. Da ace ma za ki sanar da shi yau ai da kin wa tufkar hanci da wuri,gudun kar ki manta." "Wannan ma shawara ce mai kyau,bari baƙin nasa su tafi na same shi da maganar." Ran Barirah ƙwal ta wuce ɗebo ruwa a babbar tukunya,dan ta san dole aljihun Abbas ya jijjiga. Tana dawowa da ruwan Hajiya ta karɓa ta ɗora a saman murhu,hira suka ci gaba da yi Barirah na ta zuga Hajiya,ita kuwa ta na ta adana maganganu a cikin kwanyarta,Abbas kawai take jira ya zo ta lissafa masa kaf abinda take so ya siyo wa Fauziyyah. Hajiya ce ta yi wa Fauziyyah wankan yamma da kanta,ta yi mata gashi sosai a inda ya dace,sannan ta sanya ta zama a ruwan ɗumi domin ta gasa jikinta da kyau. Hajiya na gamawa da Fauziyyah sai ta karɓi jaririyar ma ta wanke ta tas ta gasa ta sosai,anan ne Fauziyyah da Barirah suka ga yanda ake yi wa jarirai wanka me kyau,ba irin wanda ta jajjaɓa mata da safe ba. Suna zaune Hajiya na ta koya musu abubuwa irin na mutanen da Abbas ya shiga parlourn ya na washe baki,domin ba ƙaramin daɗin abincin suka ji ba shi da abokansa,har suna cewa gobe ma za su dawo su ƙara kwasar gara. Cike da fara'a ya zauna a gefen Hajiyansa da ke sanya wa Yarinya kaya,cikin fara'a Hajiya ta kalle shi ta ce. "Ah ah Ɗan lele Abashen Babansa irin wannan washe baki haka kamar wanda ya samu wata kyauta mai tsoka? To ba wannan ba,wai ni meye sunan yarinyar nan ne? Ko kai ma al'adar mutanen da za ka raya,ba za a faɗi sunan yaro ba sai bakwai ta zagayo?" Kallon Fauziyyah ya yi ya tuna bala'i da masifar da suka kwasa a watannin baya akan cikin jikinta,nan da nan ya yi mursisi ya murje idanuwansa ya ce wa Hajiya. "Ai Muhseena za a saka mata,amma za mu dinga ce mata Ummi." Wata iriyar guɗa Hajiya ta saki,kafin ta koma yin hamdala,cikin tsananin farinciki ta kalli Fauziyyah wadda mamakin Abbas ya gama kashe ta a zaune ta ce. "Ashe kun shirya yi min ba zata shine baki sanar da ni ba? Kaiii yaran nan Allah Ya yi muku albarka. Allah Ya raya mana takwarata Ya albarkaci rayuwarta. Sai dai ina roƙon alfarma a wajen ku,don Allah kar ku ɓoye sunan nan,ku faɗe shi kamar yanda kuke kiran ruwa. Mugunta wa yaro ne kawai bana so,a hau jibgar yaro be yi komai ba,idan kuka yi min haka kun gama min komai." Murmushin yaƙe Fauziyyah ta saki kafin ta zaro kalmomin. "Allah Ya raya mana ita Hajiya." Da ƙyar ta furta. Ta na gama faɗin haka ta tashi ta shiga ɗaki ta damƙe bakinta ta na rusa kuka. Shin Abbas ya manta abinda ya faru ne? Ya manta alƙawarin da ya yi mata? Ko kuwa ya manta halacci da mutuncin da Mahaifiyarta ta yi masa a rayuwa? Lallai a yau ta tabbatar da cewa Abbas baya son ta,ba kuma ya ƙaunarta, yaudarar ta yake yi. A yau ta yarda da sunan da Barirah ke kiransa da shi,wato MUGUN MIJI. Duk wahalar da ta sha akan cikin nan tin daga ɗaukansa,da haihuwa,sai ya karya billensa ya haɗiye kalamansa ya yi wa tashi mahaifiyar takwara. Cikin kuka Fauziyyah ta ce. "Na ɗauka ƴata ce ni kaɗai,na zaci sai abinda na ga damar yankewa akan ta shi zan yanke? Me ya sa ka zamo mai baki biyu?" Muryar Abbas ta ji a saman kanta cike da ɓacin rai ya na faɗin. "Saboda ni ne mijin ba ke ce mijin ba. Ni nake da iko da haƙƙin zaɓarwa ƴata suna,ko za ki hana ne? Sunan uwar tawa ne ya sanya ki zuwa ɗaki saboda baƙin ciki da iskanci ki dinga kuka kamar an yi miki mutuwa?" Idanuwanta da suka rine suka yi jajawur ta zuba masa,har sai da tsigar jikinsa ta miƙe,a hasale ya kai wa kanta ranƙwashi murya ƙasa-ƙasa ya ce. "Bar kallo na da shegun idanuwanki kamar na tsohuwar mujiya don uban ki. Kuma ki tashi yanzun nan ki ɗebarwa Hajiya wancan kayan miyan da na ga an lode a ƙofar kitchen ɗin ki,dan na san tinda aka ajiye a can to naki ne. Ta fara shirin tafiya zan mayar da ita gida yanzu." Kasa cewa komai Fauziyyah ta yi,sai kawai ta hau share hawayenta ta nemi kwalli ta saka,sannan ta fito tsakar gidan. Kai tsaye wajen kayan miya ta nufa ta ɗiba sosai a leda ta koma ɗaki,Barirah na kallonta bata ce mata ci kanki ba,aikin girkin dare kawai take ta yi,zuciyarta fess dan ta san komai bala'in Abbas sai ya siyawa Fauziyyah abubuwan da ta kitsawa Hajiya a sai mata. Cike da jin kunyar Barirah ta gama cika leda da kayan miya ta nufi hanyar ɗakinta. Turus Fauziyyah ta ja ta tsaya a ƙofar shiga ɗakinta saboda jin irin lissafin da Hajiya ke yi wa Abbas,jikinta na rawa ta hau cewa. "Hajiya ai ni na fi son aiki da hannuwana na wanke kaya...ni..ni....ba...ban ma iya amfani da injin wanki ba,sannan blender tsoro take bani,ƙarar firgita ni take yi Hajiya kuma..." Cikin hasala da ɗaga murya Barirah dake jiyo wautar da Fauziyyah ke yi ta ce. "Tana firgita ki kike aron tawa? Ko kuma shi gas ɗin da nake baki ki yi girki idan wutar murhun ta ƙi kunnuwa tsorata ki yake yi? Ke wai wace iriyar yarinya ce Fauziyyah? Banda abinki ma uwa da ɗa suna magana ina ruwanki a ciki da za ki saka musu baki?" Shiru Fauziyyah ta yi ta na rarraba ido,ganin irin azababben kallon da Abbas ke sauke mata,wanda ke ratsa gangar jikinta ya na shigewa har ya yi sanadiyyar da ta sanya ta ajiye ledar hannunta a gaban Hajiya cikin firgici da gigicewa ta ɗauki ƴarta ta shige ɗaki da sauri. Murmushi kawai Hajiya ta saki,domin kuwa duk ɓoyewar da Fauziyyah ta dinga yi ta gano cewa halayyar Abbas ta mugunta na nan babu abinda ya sauya,ashe basaja kawai suke yi mata a ɗazun shi yasa bata gane komai ba. To kuwa ya yi shuka a idanun makwarwa,dole ne ya yi duk abinda ta lissafa masa,tinda ai akwai kuɗin ba babu ba. Sassauta murya Hajiya ta yi,sannan ta dafa kafaɗar Abbas ta ce. "Abashen Babansa ka dai ji abubuwan da na lissafa maka ka siyo mata ko? Na baka daga nan zuwa ƙarshen wata ka siyo ka ajiye mata su,domin ta samu hutu a ayyukanta na yau da kullum. Ba dan hidimar suna ba ma da ke gaban ka ai da na ce ka siyo mata su gobe,amma yanzu ka ji da ragon suna da sauran kunji-kunjin suna da za a buƙata. Allah Ya yi maka albarka,tashi ka mayar dani gida. Wannan kayan kuma a mayar dasu dan babu inda zani da su,ina can da kayan miya na jibgi,dan kuwa ko kafin na fito sai da na tsince wanda suka fara lalacewa na aika maƙota. Maza tashi mu tafi,garin ma kamar akwai hadari,shi yasa zafin ya yi yawa." Abbas bai iya furta komai ba,tsabar yanda zuciyarsa ke tafasa,babban fata da burinsa bai wuce ya kai Hajiya gida ya dawo ya ji shegen da ya kitsawa Fauziyyah ta ce a siya mata abubuwan da Hajiya ta lissafa masa ba. Kamar wadda ke yin duba haka Abbas ya ji muryar Hajiya dake yafa mayafi ta na faɗin. "Babu wanda ya sanar da ni abinda na yi maka lissafi Abbas,ni da kaina na duba na ga abubuwan da bata da su,take kuma da buƙata,wanda ya kamata ace ta jima da mallakar su amma bata da su,bayan ta na da kuɗinta ba wai babu ba. Kai idan ma bata da su ai kai ne ya kamata ka siya mata,tinda duk amfanin ku ne. Dan haka kar ka bari maganar nan ta kai mu ga ɓacin rai Abbas." Sosa kai ya yi yana murmushi ya ce. "Ai Hajiya na yi shiru ne ina tinanin kuɗaɗen da za a samu na wannan watan,ina lissafi ne na ga za su isa ko sai na yi ciko da albashi na? To Alhamdulillah na ga za su isa ma a yi mata komai,har a ci gaba da yin ajiyar da aka saba yi duk wata." "To Alhamdulillah,Allah Ya baka ikon sauke nauyi Abbas." "Amin Hajiyata." Har suka fita Fauziyyah bata san ma sun fita ba tsabar yanda ta matsu su tafi ta tinkari Barirah ta ji ko ita ta kitsawa Hajiya maganganun da ta ji tana yi. To ta ina ma za ta fara tinkarar Barirar tinda bata da wata shaida akan hakan? Dafe kanta da ta ji yana sara mata ta yi,a hankali ta fashe da wani irin kuka mai azabtar da zuciya. Wannan wanne irin sabon bala'i ne ya tinkarota ko hutawa bata gama yi ba daga nishi da wahalar haihuwa da ta yi?........... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI. RUBUTAWA HAMIDAH SUNUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨ PAGE 10. LAST FREE PAGE. *MUHIMMIYAR SANARWA.* *1-Ƴar'uwa ki na fama da mummunar ramar da kike jin kunyar shiga cikin taro gudun kar a dinga tambayar lafiya kike kuwa ramar ta yi yawa? Matso kusa na zo maki da magani ingantacce wanda aka haɗa shi da kayayyaki masu inganci wanda ba sa cutarwa ko da bayan kin gama amfani da shi,za ki murje ki yi ɓulɓul kema ki juya mazaunan ki ki kaɗa ƙirjin ki gaban Oga da sauran mata yanda kike so ba tare da kin cutar da lafiyar jikinki ba. Ana shan wannan magani da Kunu ko fura,ko kuma Yghort.* *2-Ke kuma matsalar zubewar nono da lalacewarsa tare da tamuƙewarsa kamar leda ke damun ki? Kar ki ce kin sha wancan da wannan kin gaji,taho ki gwada products ɗin mu mai abun mamaki domin samun confidence ɗin bayyana jikin ki a gaban oga.* *3-Mummunar ƙiba mai haɗe da ƙaton tumbi da manyan kumatun da suka nitsar maki da hanci ciki ke damun ki? Ko kuwa irin ƙibar nan ce da ta maida ki kamar buhu babu gaba babu baya? Kar ki ji komai,domin kuwa na zo maki da ingantaccen maganin hausa wanda bashi da illa ga lafiyar jiki a farashi mai sauƙi cikin kwana uku zaki fara ganin sauyi,a kwana bakwai kuwa shape ɗin ki zai bayyana ki huta da nauyin jiki.* *4-Kina son ki samu glass skin da an hango ki a ga yanda fatar ki ke haske da walƙiya tare da ɗaukan ido? Kema zo nan kar ki wuce na tanadar maki naki kayan da za su kyautata fatar ki.* *5-Kina fama da matsalar ciwon sanyi mara jin magani? To ki zo na baki maganin da zai wanko maki shi,za ki gansa da idon ki yana fita kamar dusar awara,har ya wanke ruwan ni'imar jikin ki ya bayyana ki mori rayuwar auren ki.* *Gaba ɗaya za ku iya samu na a wannan No 08038086083.* Kasa fita Fauziyyah ta yi,sai ta ƙunshe kanta a ɗaki ta hau kumbura kamar wata shagwaɓaɓɓiyar yarinyar dake fushi da iyayenta. Barirah na kula da take-taken ta,sai ta yi banza da ita,ta ci gaba da sabgar gabanta. Tana gama tuwon dare ta zuba mata ta kai parlour ta dire,ko neman ta bata yi ba,ballantana ta jira sannunta ko kuma godiyar ta. Kafin Shehu ya dawo ta salla wanka ta ɗauki gayu da ƙananan kaya,sai ƙyalli da ƙamshi take bazawa. Kitchen ta je ta kwashe abincin su ta kai ɗaki ta jera sannan ta zauna ta ɗauki ƙur'aninta ta hau karantawa. Hayaniyar Abbas da ta jiyo tin daga tsakar gida baisa ta daina karatunta ba sai ma ƙara ƙarfin muryar ta da ta yi,saboda bata son jin me yake faɗa. Ta riga ta sanyawa ranta ko Fauziyyah ba za ta kula ba ballantana wani Abbas,domin babu wanda ke binta bashin bayani a cikin su,kuɗi ne dai sai ya fitar ya kashewa baiwar Allah,tinda haƙƙinta ne ba na wani ba. Cike da ɓacin rai Abbas ya sake dakawa Fauziyyah tsawa ya ce. "Ba da ke nake magana ba dan uwarki? Uban wa ya sa ki sakin baki ki gayawa Hajiya baki da washing machine da iron da blender? An faɗa maki kuɗin banza ne da ni da zan siya miki duk waɗannan abubuwan da kika lissafa mata?" Barirah na nan zaune jikinta na tsuma domin duk yanda ta so toshe kunnenta hakan bai hana ta jiyo hayaniyarsu ba. Cikin rawar murya Fauziyyah tace. "Haba My king,me yasa kake yi min irin haka ne wai? Anya na cancanci wulaƙanci da cin mutuncin ka kuwa? Ni fa ba ni na faɗa mata komai ba,ita da kanta ta yi wannan tunanin kuma ta sanar da kai abinda take son ka yi min,wanda ya dace a ce ka yi min tin kafin wani ya ce ka yi ɗin. Sannan da ka ke cewa baka da kuɗin banza ba fa da kuɗin ka za ka siya min ba,da kuɗi na za ka yi amfani ka siya. Ina ce hakan dika rufin asirin mu....." A harzuƙe Abbas ya kai wa bakinta duka sai da jini ya fito,yatsansa manuni ya nuna mata ya ce. "Wato gori ma kike yi min har kike sanar dani a kuɗin ki za a siya miki ko? To shikenan zan siya miki duk abinda Hajiya ta lissafa,amma na rantse miki sai na lahira ya fiki jin daɗi a cikin gidan nan,sai kin gwammace kiɗa da karatu,sannan sai kin yi da kin sanin sawa na saya maki kayayyakin nan,idan ma wata ƴar iskar ce ke zuga ki to ki sani na kusan korar shegu daga gidan nan,na gaji da iskancin da matar nan ke yi min da gadara a cikin gidana da na gida da kuɗi na ba da kuɗin uban kowa ba." Wasu irin zafafan hawaye na masifa da bala'in dake cin Barirah ne suka hau zubar mata a kunci. Lallai ba dan kada Shehu ya dawo ya ji labarin ta dambace da mijin wata ba,da babu abinda zai hana ta fita su ci uban juna ita da Abbas,sai dai a yi kare jini-biri jini ita da shi amma ba za ta yarda ya dinga zaginta ba har yana kiranta da ƴar iska. Ƙwafa ta yi ta share hawayenta sannan ta rife ƙur'anin ta hau addu'o'i. Ta na kammalawa ta tashi ta haye gado ta kwanta ta yi shiru ta na saƙe-saƙe a zuciyarta. Fauziyyah kuwa kallon hanyar da Abbas ya bi ya fita daga ɗakin ta yi ta na ci gaba da risgar kuka kamar ranta zai fita. Kanta har wani sarawa yake yi kamar ana buga mata guduma. Dafe ƙirjinta da ya yi mata nauyi ta yi ta na jin iska ta yi mata kaɗan. A hankali ta miƙe tsaye ta kunna fanka kaɗan ta kwanta kanta na kallon sama. Ƙarar buɗe kwano ne ya tabbatar mata da Abbas na parlour babu inda ya je. Hawayenta ta share ta ci gaba da sauke nishin wahala a hankali. Shi kuwa zama ya yi ya jawo plate da spoon ya kwashi naman miya son ransa,ya buɗe tuwo leda biyu ya ci ya ƙoshi. Ruwa ya huda na pure water ya sha ya ƙoshi sannan ya miƙe a doguwar kujera ya kunna TV. Tashar da ake raye-raye na kudancin Nigeria ya kai ya na kallon mata tsirara-tsirara ya na gyaɗa kai kamar ƙadangare. A haka bacci mai daɗi ya ɗaukesa. Lokacin da Shehu ya dawo Barirah ta labarta masa kaf abinda ya faru faɗa ya yi mata,ya ce da ta sani da bata yi hakan ba,domin garin taimakon Fauziyyar gashi ta jawo mata duka da zagin iyaye a wajen miji mara daraja kamar Abbas. Sannan nan gaba ba a san me zai yi mata ba. Jikinta ne ya yi mugun sanyi,nan da nan ta hau nadamar biyewa zuciya har ta zuga Hajiya akan Abbas ɗin,gashi yanzu ya saka ƴar mutane a gaba da azabarsa. Da dare ruwan sama aka lema musu mai yawan gaske,sai garin ya ɗauki sanyi sosai,dan haka Abbas na parlour a kujera bai san cewa Fauziyyah na ɗaki ta na fama da mummunan zazzaɓi ba,haka yarinyar ta dinga tsala kuka ba tare da ya ji ba ballantana ya leƙa su. Kafin safiya Fauziyyah ta fita hayyacinta ta yi zuru-zuru. Sai da aka fara kiran sallar asuba ta samu wani irin bacci mai daɗin gaske ya sace ta. Washegari da asuba Barirah ta tashi da wuri ta ɗora girkin safe. Ta na gamawa ta saka ruwan wanka. Sai da ta zubawa kowa abincin sannan ta ɗauki nasu ta fara kaiwa ɗaki. Ganin ƙofar su Fauziyyar a buɗe sai ta yi zaton Abbas ya samu zuwa masallaci,shi yasa ya bar ƙofar buɗe,murmushi ta yi ta ce. "Ohh yau wacce rana,dama shi ibadar ma kamar fushi yake da ita,lokacin da ya huce ya je masallaci,idan kuma yana dokin fushi sai ya fi wata bai leƙa masallacin ba. Allah Ya kyauta." Kanta tsaye ta nufi ɗakin Fauziyyah,sai dai kafin ta ɗaga labulen ta jiyo munsharin Abbas ɗin,cikin sauri ta koma baya,kyaɓe baki ta yi ta ce. "Kai jama'a,Allah ka shirya wannan bawa naka." Kitchen ta wuce ta ajiye musu abincinsu wanda ta rabawa mazubi,saboda sanin halin mugunta irin na Abbas da haɗama da son kai,shi be ƙi a dinga kwashe masa naman miyar ba kaf ya zamo abincinsa shi kaɗai. Abbas bai fito daga ɗakin ba har sai da tara na safiya ta buga,a wannan lokacin Barirah ta gama yanke hukuncin zuwa ta doka musu kofa,dan kuwa ruwan wankan da ta sake ɗorawa a karo na biyu ya kusa hucewa. Miƙa ya fito yana yi ya wuce banɗaki, yana shiga ta shige ɗakin sai ta tarar da Fauziyyah kwance bakinta ya kumbura,ga jaririya kwance tana bacci,miƙa hannu ta yi dan ta ɗauke hannun Fauziyyah dake kan jinjirar,sai ta ji hannunta da zafi zau,tausayinta ne ya kama ta,sai ta ɗauki yarinyar ta tashe ta. A hankali ta furta. "Ki shirya ki shiga wanka,dan ruwan ma ya kusan hucewa,bari na je na yi mata wanka,idan kin fito ki ci abinci ki sha maganin zazzaɓi,Allah Ya baki lafiya." Murya a dashe Fauziyyah ta ce. "To Aunty na gode." Barirah waje ta yi, ta na jin kamar ita ce sanadiyyar shigar Fauziyyar cikin wannan ƙunci da zazzaɓin da take ciki. Jiki a sanyaye ta yi wa yarinyar wanka,ta na shiryata ta tina kalaman Shehu kafin ya fita kasuwa. 'Ki tabbata kin bata haƙuri ko ta ji sanyi a ranta.' Ajiyar zuciya ta sauke mai ƙarfi ta ƙarasa sanyawa yarinyar kaya. Ta na jin Abbas ya shiga kitchen ɗinta ya juye mata ruwan zafi saboda tsabar neman magana da gadara. Gyaɗa kai ta yi cike da takaici ta saɓa yarinyar a kafaɗa ta fita tsakar gidan. Kallon ta ya yi ya watsar ko nauyin abinda ya aikata bai ji ba,wanka ya shiga ya yi,sannan ya fito ya dangwarar da bokitin a tsakar gida ya shiga ɗakinsu. Har ƙasa Fauziyyah ta durƙusa ta gaida shi,sannan ta sake bashi haƙuri akan abinda ya faru jiya,ko kallon inda take bai yi ba,ballantana ta saka ran zai amsa ta. Gajiya ta yi da durƙuson ta miƙe ta wuce zuwa wanka. Sai da ta gasa jikinta sannan ta yi wankan sabulu ta fito,ko da ta koma ɗakin ta tarar da ya cinye abincinsa sannan ya ɗebi nata ya ƙara da shi. Girgiza kai ta yi ta hau shiri,kayan ta ta saka tsofaffi ta saka kwalli. Sabon pant da pad ɗin da su Shehu suka kawo mata da shi ta kintsa jikinta. Tana tsaka da cin abinci Barirah ta shiga ɗakin,kallon juna suka yi suka saki murmushi. Cikin sanyin murya Barirah ta ce. "Don Allah ƙanwata ki yi haƙuri da abubuwan da suka faru jiya. Raina ne ya ɓaci har na yi wa Hajiya magana akan halin da kike ciki na rashin kayan aiki,ban zaci hakan zai jawo matsala har haka ba,na zaci faɗa kawai zai yi komai ya wuce." "Uhumm babu komai Aunty,Allah dai ya sa ya gane ya dena abubuwan da yake yi." "Amin Ya Allah,ɗazu yayanki ya kira Hubby,yana so ku gaisa,sannan ya sanar dake Auntyn ki za ta zo saboda a yi suna da ita." Gaban Fauziyyah ne ya yanke ya faɗi,cikin sauri ta ce. "Me kuka ce masa to?" "Ah hukunci na wajen ki mana. Idan ya dawo sai a kira yayan naki ku yi magana. Amma dai kin san idan kika hana ta zuwa baki kyauta ba ko? Wai me yasa ke ba za ki iya tsayawa kan ki bane ki ƙwaci ƴancin ki?" Murmushi kawai Fauziyyah ta yi, ta ci gaba da cin abincinta. Tana kammalawa ta sha magani ta kwanta ta na tunanin hanyar da za ta bi ta hana Auntyn nata zuwa gidan,dan kuwa ta san muddin Abbas ya ƙyalla ido ya ganta a gidansa sai ya yi mata ruwan rashin mutunci

Chapter 5 of 12