Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
11 / 12
biyu zuwa uku bai zo ba,da tafiya ta tafi kasuwanci ya bunƙasa ma sai yake komawa gida duk ƙarshen shekara. A wannan lokacin ne Fauziyyah ta kai aji uku na ƙaramar sakandire. Wata ranar Litinin da safe,ranar da ta shiga kundin tarihin Fauziyyah da Abbas. Rana ce da kowannen su ba zai taɓa mantawa da ita ba. Yara ne cike da harabar makarantar cikin tsafta da annashuwa,kasancewar ta ranar da aka dawo makaranta daga hutun mako. Fauziyyah na ɗaya daga cikin ɗalibai masu hazaƙa sosai a makarantar,tsaye take a gaban assembly ta na karanta addu'o'i ya shiga makarantar. Hayaniya ce ta kaure a tsakanin malamai da ɗaliban makarantar. Tsananin kyawu da ɗaukan wankan  Abbas ne ya ja hankalin mutane. Shi kuwa Abbas tinda ya doso makarantar yake jin zazzaƙar muryar Fauziyyah na tashi ta na karanta ayatul kursiyyu. Gaba ɗaya zuciyarsa ta ƙagu ya ƙarasa cikin makarantar a saman machine ɗinsa wanda ake kira da tsuntsun soyayya a wancan lokacin. Ya na shiga ya ɗora idanunsa akan kyakkyawar halittar dake riƙe da abun magana ta na karatu. Ta cikin baƙin gilashin da ya saka ya ƙare mata kallo. Fara ce tas doguwa,ta na da siranta sosai ta sama,sai dai daga ƙasanta a buɗe take sosai ta yanda yake iya gano tudun ƙugunta a cikin hijabinta da ya kula ya fi na sauran ɗalibai girma. Yawu ya haɗiya tare da lashe leɓen bakinsa na ƙasa. A daidai wannan lokacin ne ya ajiye machine ɗinsa ya ciro jakarsa baƙa ya rataya a kafaɗarsa ya tako zuwa wajen assembly ɗin. Ya na zuwa sai ya cire tabaran idanuwansa ya miƙawa malami mafi kusa da shi hannu suka gaisa. Ba ƴan mata kaɗai ba hatta da matan auren malaman makarantar sai da suka ji wani abu game da kyawun Abbas,ga wani irin ƙamshi mai sanyi sai tashi yake yi daga jikinsa. Fauziyyah kuwa saboda yanda yake kallonta da idanuwansa wanda cikinsu yake baƙi sosai, farin ma fari fat,sai cikakken gashin ido da gira  mai kyau kamar an zana masa ita,sai ta rikice muryarta ta hau rawa,babu shiri ta yi saurin kammala addu'ar ta bar wajen,cikin ɗalibai ta shige ta rage tsawonta tana dafe saitin zuciyarta dake harba mata da sauri da sauri. Kawarta Fatima ce ta dafa ta ta durƙusa saitin kunnenta ta ce mata. "Kinga yanda kyakkyawan malamin nan ke kallon ki kuwa? Har yanzu fa leƙen ki yake yi. Kaiii amma Fauzy kin yi sa'a ina ma ni yake kallo haka,ina ga da mutuwa zan yi tsabar daɗi." Dukan wasa Fauziyyah ta kai mata suka saka dariya a tare. A haka aka gabatar musu da Abbas a matsayin sabon malamin ƴan SS 1 to 3;wanda zai dinga ɗaukan su darasin turanci. Daga nan kuma aka rufe da waƙoƙin yau da kullum na turanci kowa ya wuce ajinsu. Tinda Fauziyyah ta koma aji ta ke faman tunanin idanun Abbas da ke binta da kallo. Ajiyar zuciya mai ƙarfi ta sauke ta na ayyanawa a ranya. 'Anya tinda uwata ta haife ni na taba ganin idanuwa masu kyawun na bawan Allah'n nan? Kai inaa ko a films ɗin larabawa da indiya ban taɓa gani ba. Ohh Allah mai halitta,ji hancinsa sai kace dogon karas,ga leɓensa masu kyau da faɗi gwanin sha'awa. Gaskiya duk wadda ta auri malamin nan ta gama dacewa a duniya,sai dai ta yi fatan Allah ya bata ƙiyama kuma. Allah ka sa ni zan aure shi.' Cikin sauri Fauziyyah ta buɗe idanuwanta ta damƙe bakinta kamar wadda ta furta kalamanta a fili. Kallon gefe da gefenta ta yi ta ji ajin ya yi tsit alamar malami ya jima da shiga ajin ba tare da ta sani ba. Ta na ɗaga kai ta yi ido biyu da Abbas ya zuba mata idannuwansa da ke rikita ta. Nan take ta rikice ta daburce ta rasa inda za ta saka kanta. Murmushi ya sakar mata wanda ya sanya numfashinta ɗaukewa na wucin gadi. A rikice ta sake ware idanuwanta a kansa ta na kallon mutanen ajin,sai ta ga kowa ita yake kallo,sai dai kallon nasu ya sha banban da nata,domin kuwa da damar matan ajin harararta suke yi,wasu kuma sai suke murmushi suna jin daɗi tare da jin cewa dama su Abbas ya yi wa murmushin da ya yi mata. Ƴan mazan ajin kuwa ƙunshe dariya suka dinga yi,dan sun gano Abbas dai ya faɗa soyayyar Fauziyyah kamar yanda da damar malamai da wasu ɗaliban suke ƙaunarta. Gyaran murya Abbas ya yi sannan ya ce. 'Who is your monitor in this class?' (Wanene monitan ku a wannan ajin) Cikin sauri suka hau nuna Fauziyyah. Kallonta ya yi da idanuwansa da ke sumar da ita ya ce. 'Ok. Come here, come and tell me your name please.' (Ok. Zo nan,zo ki ɗan faɗa min sunan ki) Jiki babu ƙwari Fauziyyah ta fita ta tsaya a gaban Abbas,kallon yanayin tsayuwarta ya yi kawai sai ya juya ya saki murmushin da haƙoransa farare tas suka bayyana,gefen kuncinsa na hagu ya ɗan loɓa. Ihu ajin ya ɗauka da sowwar yara,shi kuwa Abbas tsananin kyawu da yanda Fauziyyah ta burge shi ne ya sanya shi sakin murmushi mai sauti. Kallon da ya yi musu ne ya sanya kowa haɗiye dariyarsa. Cikin muryarta mai daɗin saurare ta sanar da shi sunanta. Sake karkata kansa ya yi kamar bai ji ta ba sannan ya ce. 'Go again please. What did you say your name was?' (Ɗan maimaita. Me kika ce ma sunan ki?) 'My names are Fauziyyah Aliyu Mai Almajirai.' 'Wow what a nice name you have there. Ok you can go back and sit down. Thank you for your time,i think i am going to be your english teacher for today,as your english teacher Malam Hakim is sick. So where did you stop at?' (Wow lallai kina da suna mai daɗi. Ok za ki iya komawa ki zauna. Na gode da bani lokacin ki .Ina tinanin ni ne zan zamo malamin ku na koyon turanci na yau,kasancewar malamin ku Hakim bashi da lafiya. A ina kuka tsaya?') Ya ƙarasa maganarsa ya na kallon Fauziyyah da ke sunne kai saboda tsananin kunyarsa da take ji. Bayan sun sanar da shi inda suka tsaya ne Abbas ya ɗora da koyar da su darasin turanci na wannan ranar. Wanda da damar su sun fahimta sosai,domin ya iya koyarwa ƙwarai da gaske. Aikin gida ya basu kafin ya fita yana yi musu sallama. Tinda ya fita mazan ajin suka miƙe suna ta gwada yanda yake abubuwa cikin ƙwarewa da mazantaka. Fauziyyah kuwa hankalinta ya tafi wajen tunanin kyakkyawar fuskar Abbas,wadda take jin tabbas ko bai furta yana sonta ba,to fa ita za ta iya zuwa ta sanar da shi irin kamun da soyayyarsa ta yi wa zuciyarta a kallon farko da ta yi masa. Ta bangaren Abbas ma tinda ya fita ya kasa moruwa,saboda yanda yake jin matsananciyar sha'awar Fauziyyah na bijiro masa, domin shi kyawun da yake da shi bai bashi damar gina soyayya a zuciyarsa ba,duk macen da ya ji ta burge shi sai ya san yanda ya yi ya kawar da kwaɗayinsa da maitarsa akanta,sannan hankalinsa ke kwanciya, ballantana mata da dama su ke kai kansu da kansu dan ya biya musu bukatar sha'awar da suke yi masa. Dan haka Abbas ya ɗarsawa zuciyarsa sha'awar Fauziyyah, sha'awa mai tsanani wadda bai taɓa jin irinta akan kowacce mace ba,kuma ya lashi takobin sai ya kawar da kwaɗayinsa akanta sannan hankalinsa zai kwanta........... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: *MUGUN MIJI* *RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨* *PAGE 20.* *Kina ɗaya daga cikin mutanen da ke da sha'awar karanta labaran marubuciya HAMIBRAH/HAERMEEEBRAERH? Ko yanzu kike son farawa? To ki matso kusa,domin ta kawo muku wani sabo mai ɗauke da manyan darussan zaman gidan aure. Ina mata masu nuna tsananin soyayya ga namiji,musamman mijin da bai damu da su ba ko da kuwa za su cire fatar jikin su ne su shimfiɗa musu dan ya taka ya ji daɗi? Ina mata masu jin haushin duk wanda ya ji haushi akan mugunta da zalincin da mijin su yake yi musu? To ku matso kusa ku ji labarin yayar ku Fauziyyah matar Abbas. Domin duk yanda kike ji da ganin labarin MUGUN MIJI a duniya,to Abbas ya dasa wa dukkan maza aya. Idan kina so ki tabbatar ki biya 500 kacal ta 0006366584 Ja'iz bank Hamida sanusi Ahmad. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423 ta wannan layin. Kada ku bari a baku labari,domin gani ya kori ji.*✍️✨ Abbah bai tsaya a ko'ina ba sai a ƙofar gidan Baba Ilyas. Sallama uku kawai ya yi,da ya ji muryar Baban sai kawai ya kutsa kai ciki. A zaune ya tarar da Baba Ilyas ya na cin abinci,dan bai jima shima da komawa gida ba daga kasuwa. Zama Abbah ya yi a saman rijiyar su da ke rufe ya zabga tagumi,cike da damuwar ganin halin da Ɗan'uwansa ke ciki Baba ya zare hannunsa daga kwanon da yake cin abinci ya ce. 'Ah ah Ali lafiya ka zo ka tasa ni a gaba ka zabga tagumi haka? ' Ajiyar zuciya Abbah ya yi kafin ya ce. 'Ina fa lafiya Yaya? Ni ina can baki buɗe ina ta yabon yarinyar nan Fauziyyah akan bata kula samari,ashe wani na gefe yana hure mata kunne da kalaman ƙauna,bai sarara ba har sai da ya kurmantar da ita tare da yi mata ginin soyayyarsa a zuciyarta. Yaya wai kana da labarin jinya da jelen asibitin da muka dinga yi da yarinyar nan duk akan soyayya ne? Yanzu don Allah da wanne ido zan kalli Abdullah idan ya dawo?' Murmushi Baba ya yi ya koma ya zauna da kyau,domin tinda ya ji kalmar ana jelen asibiti hankalinsa ya tashi,dan ya zaci ma ciki za a ce Fauziyyah na dauke shi,sai ya ji saɓanin abinda ya yi zato. Suɗe hannunsa ya yi tas sannan ya muttsike su guri ɗaya,sai da ya kora ruwa sanna ya ce. 'Inaa Ali?.' Gyara zama Abbah ya yi ya ce. 'Gani Yaya.' 'To ka bani hankalinka nan ka ji me zan sanar da kai da kyau. Ka ga yaran zamani musamman mata,idan suka ce maka ba sa son aure,to ka dakanta,ka ƙyale su ka basu wanda suke so,idan ba haka ba,abinda za su yi maka sai ka gwammace ka bi son zuciyarsu akan taka tin farko. Yanzu zamani ya sauya,ba irin da bane da za a aurar da yarinya ko mijin bata gani ba kuma ta zauna,ta kyautata masa har su hayayyafa ko da bata son sa. Yanzu suna da wani abu da turawa suka ƙaƙaba musu mai suna ƴanci. Dan haka kar mu matsawa yarinya,a bata abinda ranta ke so kawai. Ko babu komai bamu taso da yaran mu akan matsanta musu da tilasta musu su yi abinda basu da ra'ayi akai ba,kuma ko a ƙa'idar islama ai ba a son yiwa yara auren da basa so gudun faɗawa halaka.' Baki sake Abbah ke kallon Baba,saboda gaba ɗaya maganganunsa basu wani shige shi ba,cike da ta'ajibi Abbah ya ce. 'Kai yanzu Yaya da bakin ka kake faɗar wannan maganar? A zato na kai me iya tsayawa Abdullah kai da fata ne ya samu abinda yake so. Lallai Yaya ka bani mamaki.' Miƙewa Abbah ya yi ya shuri takalman sa ya bar gidan. Duk kiran da Baba yake yi masa bai juya ba,domin kuwa zuciyar Haidara ce ta motsa a wannan lokacin. Murmushi kawai Baba ya yi sannan ya ƙwalawa Mama kira,ta na fitowa ya ce. 'Malam ai duk na ji tattaunawar ku da Baban Abdullahin,ni yanzu babbar damuwata yanda ya ɗauki abun nan da zafi,suna iya sakawa yarinyar nan damuwa,ka san duk son da suke yi wa Fauziyyah Abdullah a gabanta yake. Basu haɗa lamarinsa da komai ba.' 'Wannan dalilin ne ma ya sa nake so ki je da kan ki zuwa dare ki lallashi ita uwar,domin kin san ku mata da an shawo kan ku,to shawo kammu bashi da wuya. Duk abinda kuke so sai kun san yanda kuka yi kuka saka mu fara son abun. Ko bamu so abun ba to za mu yi muku biyayya.' 'Au haka ne Malam.' Murmushi Baba ya yi ya ce. 'Ke za ki faɗa wa wani yanda halinku mata yake.' Hira suka ci gaba da yi,tare da fatan idan Fauziyyah matar Abdullah ce ta alkhairi Allah ya yaye mata son duk wanda take so su yi auren su su zauna lafiya. Da dare Fauziyyah na zaune ta saka wayarta a silent suna parlour suna cin abinci gaba ɗayan su,kowanne fuska a ɗaure kamar gidan makoki, wayar Fauziyyah ta fara ringing. Daga yanda ta hau rarraba idanuwa ta na ɓoye wayar ne ya tabbatar wa da Ummi ba Abdullah ke kiranta ba. Cikin zafin nama Ummi ta warce wayar ta na kallo. Sunan Rayuwata ta gani a jiki,dariyar takaici ta saki sannan ta ce. 'Umm lallai ne Fauziyyah sarauniyar masoya. Wato shi wannan ɗin da ko iyayenki bai nema ba dan ya nuna maki cewa babu maganar aure a gabansa,shi ne kika mayar ya zama rayuwarki. To kuwa kina gab da barin duniyar,domin kuwa babu ke babu shi,ba ki da mijin da ya wuce Yayanki Abdullah. Gwanda ma tin wuri ki sanar da shi ya kama gabansa.' Tura baki Fauziyyah ta fara yi,abinda bata taɓa yiwa mahaifiyarta ba kenan,wato gardama da faɗi in faɗa. Cike da tsiwa da tabbatar wa da Ummin ita idan ba Abbas ba ba za ta auri kowa ba ta ce. 'Allah ni shi nake so,idan dai ba shi za ku aura min ba to ku barni a gaban ku kawai na ƙare rayuwata babu aure.' Dukan da Ummin ta kaiwa bakinta ne ya sanya ta ƙwalla ƙara mai ƙarfi,Abbah na zaune ya dafe goshinsa da yake jin yana sara masa da ƙarfi. Shi abinda ya fi bashi mamaki shine yanda Fauziyyah ta yi nisa da zurfi a son wanda ko ƙyallin ƙeyarsa basu taɓa gani ba. Hakan na nufin duk ƙoƙarin bata tarbiyyar da suke ta yi sun gaza kenan? Babu abinda take nema a wajen su ta rasa,daidai gwargwadon ikon su sun nuna mata daidai da ba daidai ba. Sun sanya ta a makarantar boko da ta arabiyyah,ƙarshe ma Fauziyyah mahaddaciyar ƙur'ani ce da sauran litattafan addini. To ta ina suka gaza a tarbiyyarta? Sallamar Mama ce ta katse Ummi daga jibgar da ta rufe Fauziyyah da ita. Da gudu Fauziyyah ta nufi Mama ta faɗa jikinta ta na gunjin kuka tana ci gaba da nanata bata son auren Abdullah Abbas take so,ita Abdullah Yayanta ne,ta ya za ta auri Yayanta? A hasale Ummi ta ce. 'Ta yanda akai na auri Ubanki gashi nan,ko kin manta alaƙar dake tsakani na da shi ne na tuna miki?' Dafa kafaɗar Ummi Mama ta yi sannan ta ce. 'Haba Zuhairah,ke fa mace ce mai tsananin haƙuri da kawaici,me yasa za ki dinga tada jijiyoyin wuyanki akan wannan lamarin? Kina da ilimin addini,kin san ƙaddara,to meye na ɗaga hankali? A matsayin mu na musulmai kamata ya yi mu bi yaran nan da addu'a tare da fatan alkhairi. Daga nan sai mu zuba wa sarautar Allah ido mu ga me zai zaɓa mata. Babban abinda nake son su Malam su yi shine,a kira yaron da ta ce tana so har gida a ji daga gare shi. Sannan daga nan a yi bincike akansa a ga dacewa ko rashin dacewar auratayya a tsakaninsu. Wannan shine mafita,ba wai ki kama yarinya kina duka ba kamar kin samu ganga.' Jikin Ummi ne ya yi sanyi,gashi har a wannan lokacin zuciyarta zafi take yi mata sosai akan abinda Fauziyyah ta aikata,sai kawai ta shige uwar ɗaka ta bar Mama da Abbah suna ci gaba da tattaunawa akan lamarin. Fauziyyah kuwa maƙalewa Mama ta yi da za ta tafi gida. Dan Ummin nata ta tsorata ta matuƙa,tinda suke bata taɓa dukanta ba sai yau. Shi yasa take tsoron zama kusa da ita. Gani take yi za ta iya zane ta a cikin dare. A ɗakin Abdullah Fauziyyah ta kwanta,cike da kewar sa. Ta tabbata idan yana nan babu mai dukanta. Ƙarshe sai dai ma ya shiga mata faɗan ya raba gardama. Allah Allah take yi gari ya waye ta sanar da Malam Abbas Abbahn ta yana nemansa. Da ƙyar ta samu bacci ɓarawo ya sace ta a wannan daren. Washegari da asuba bayan ta yi sallah,ta yi azkar da karatun ƙur'ani da ta saba yi,sai ta fita tsakar gida ta gaishe da su Baba,ta kama wa Mama aikin gida,nan da nan suka yi suka gama. Sai da ta ci ta ƙoshi ta yi wanka,sannan ta koma gida ta saka uniform ta shirya ta wuce makaranta. Ko kuɗin break Ummi bata bata ba,itama kuma bata nema ba,domin tana da sauran kuɗin da Abdullah ke bata a duk sanda ya zo. A makarantar ta tarar da Abbas,ya ɗauki wanka mai ɗaukar hankalin mai kallo kamar wanda za shi wani muhimmin taro ko walima. Murmushi suka sakarwa junan su,da ƙyar Fauziyyah ta sauke idanuwanta ƙasa daga barin kallonsa. Duk abinda suke yi Fatima na kallon su tana yi wa Fauziyyah dariya. Domin kuwa ta riga ta gama da Abbas ragowarta za ta je ta tarar. Ana gama assembly kowa ya wuce ajin su. Abbas da sassarfa ya bi bayan Fauziyyah yana kiranta. Ta na juyawa ya dafe saitin zuciyarsa ya na faɗin. 'Wash Allah na,yanzu ke Fauzy haka za mu yi dake? Jiya na dinga kiran wayarki amma kika ƙi ɗauka. Haka na kwana ban yi bacci ba,kalli ido na ki ga yanda ya yi ja.' Kafe ta ya yi da ido,itama sai ta zuba masa nata. Wani irin shauƙin soyayya ne yake kwasar su,da ƙyar Fauziyyah ta kawar da idanuwanta daga nasa ta ce masa. 'Humm da ka san halin ƙuncin da na shiga jiya a gida saboda kai,da ka tausaya min. Tinda nake a duniya Ummi bata taɓa ko da marina ba,amma jiya sai da ta zane min jiki na,saboda ta kama ni ina waya da kai. Daga ƙarshe dai na ce musu kai nake so,kuma Abbah ya ce yana son ganin ka.' Maganarta ta ƙarshe ta dake shi sosai,amma sai ya kawar da damuwarsa ta hanyar tambayarta irin ciwon da ta ji a jikinta. Murmushi kawai ta yi masa ta ce. 'Ai idan dai a kan ka ne,na yarda zan jure kowanne irin duka da zagi,ni dai kawai a barni da kai shi ne farincikina.' 'Da gaske kina so na har haka Fauzy? Ni kuma na yi maki alƙawarin zan aure ki,zan kula dake fiye da yanda ake lelen ƙwai,zan ririta ki kamar jaririya. Sannan zan mallaka maki duk abinda kike so matsawar bai fi ƙarfi na ba. Ke kaɗai ce macen da za ta yi mulkin duniya ta. Shi yasa ma tin daga yanzu zan baki suna sarauniyata. Ko kuma na kira ki da My Queen da yaren nasara.' Dariya Fauziyyah ta yi sosai,ta na rufe fuska,saboda ba ƙaramin saka ta nishaɗi kalaman Abbas suka yi ba. Cike da jin kunyarsa ta ce. 'Na gode da wannan matsayi da ka bani,ina fatan kuma za ka cika dikkan alƙawarin da ka ɗauka bayan auren mu. Idan ka yi min haka nima zan baka sarautar duniyata, sunan ka zai tashi daga Malam Abbas ya koma sarkina,ko kuma in kira ka da My king da harshen nasara.' A tare suka jera ya raka ta har bakin ajin su,sannan ya wuce SS 3,domin lokacin su ne,amma ya tsaya zubawa Fauziyyah kalaman yaudara. Wunin ranar Fauziyyah labarin Abbas ta dinga bawa Fatima. Ita kuma ta na ta sauraronta tana bata amsa sama-sama. Lokacin tashi na yi Abbas sai ya ɗauki Fauziyyah a tsuntsun soyayyarsa wanda baya barin kowa ya hau ko ya yi aro. Yanda Fauziyyah ta koma baya ta zauna ɗororo shine ya shaƙar da Abbas takaici. A cikin zuciyarsa yake jinjina tsananin taka tsantsan irin nata,da ƙin amincewa kusantar zina da take da shi. Dole ya saki ransa ya gama yarda gwanda ya aure ta kawai ya huta. A ƙofar gidan su ya ajiye ta ta shige gidan ta na sanar da shi ya jira ta sallamawa Abbah. Dan ta san ya dawo gida cin abincin rana a wannan lokacin. Jingine machine ɗin nasa ya yi ya jirata ta dawo riƙe da tabarma ta shimfiɗa masa,sannan ta koma cikin gidan. Zoɓo da cup ɗaya ta ɗoro a faranti ta kai masa sannan ta ce masa. 'Abbahna na nan zuwa yanzu. Ga wannan ka sha na san kana jin ƙishi.' Tsiyaya masa zoɓon tayi ta miƙa masa,karɓa ya yi ya gode mata sannan ta koma ciki. Ko da Abbah ya fito Abbas miƙewa tsaye ya yi cike da ladabi ya durƙusa a gefen tabarma,da ƙyar Abbah ya shawo kan Abbas ya ɗofana mazaunansa a gefe ya sake gaishe shi. Amsawa Abbah ya yi yana yaba hankalin Abbas a ransa. Babu ɓata lokaci Abbah ya ce. 'Kai ne Malam Abbas ɗin da Fauziyyah ke magana akai kenan?' Kai Abbas ya gyaɗa yana sosa kai,gyara zama Abbah ya yi sannan ya ce masa. 'To yaro na ji duk abinda yake faruwa. Sai dai ita gaskiya ɗaya ce,daga ƙinta kuwa sai ɓata,dan haka ina so na sanar da kai cewa mun yi wa yarinyar nan miji,da ya dawo daga tafiya ma za a ɗaura musu aure. Sai bayan candy kuma za a yi biki a miƙa ta ɗakin mijinta. Dan haka ina mai baka haƙuri da fatan alkhairi,Allah ya baka wadda ta fita.' Jikin Abbas ne ya ɗauki rawa,bai san ya zube a saman guiwowinsa ba tsabar shiga damuwa da tashin hankali,nan take ya hau roƙon Abbah yana yi masa lissafin kalar jin daɗi da kulawar da zai bawa Fauziyyah bayan sun yi aure. Dariya irin ta manya Abbah ya saki kafin ya ce. 'To Yaro na gode da wannan fatan kyautatawa yarinyata da kake yi,amma maganar gaskiya mun yi mata miji, ɗan'uwanta za ta aura da zarar ya dawo. Dan haka kar mu ɓata maka lokaci ka je ka nemi wata kawai,Allah ya bamu alkhairi. Bari na shiga da kayan ciki. Yauwa, ina neman alfarma a wajen ka,don Allah kada ka ci gaba da kula yarinyar nan da sunan soyayya,saboda in ka ci gaba da kula ta ba za ta maida hankali ta yi karatu ba.' Kasa magana Abbas ya yi,sai kawai ya miƙe jiki babu ƙwari ya bar ƙofar gidan. Yana tafiya Abbah ya shiga gidan ya sanar da Ummi yanda suka yi. Fauziyyah na jin abinda ya faru sai ta hau ihu da birgima tare da kiran ta shiga uku ta lalace za a yi mata auren dole. Babu kalar faɗa da zagin da bata sha ba a wannan rana. Amma haka ta kafe ta nace ita sai Abbas. Ta na shiga ɗaki ta kunna wayarta wadda idan ta shiga makaranta take kashewa. Babu ɓata lokaci ta nemo lambar Abdullah ta danna mata kira. Ya na ɗauka ta rushe da wani irin matsanancin kuka. Cike da tashin hankali ya hau tambayarta dalilin da ya sa take kuka haka? Cikin shassheƙar kuka Fauziyyah ta ce. 'Yayahna ka dawo gida don Allah,su Ummi suna son su kassara rayuwata,kai kaɗai ne wanda za ka iya fitar da ni a halin da nake ciki a yanzu ' 'Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un. Fauziyyah wai me yake faruwa ne? Don Allah ki sanar dani mana.' Kuka sosai ta ci gaba da yi,har dai da ya ce mata. 'To na ji ya isa haka, ina nan tafe yau,zan hawo jirgi na dawo in sha Allah.' Cike da matsanancin farinciki Fauziyyah ta kashe wayar ta na fatan zuwansa ya kawo ƙarshen matsalar da take fuskanta.... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: *MUGUN MIJI* *RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨* *PAGE 19.* *Kina ɗaya daga cikin mutanen da ke da sha'awar karanta labaran marubuciya HAMIBRAH/HAERMEEEBRAERH? Ko yanzu kike son farawa? To ki matso kusa,domin ta kawo muku wani sabo mai ɗauke da manyan darussan zaman gidan aure. Ina mata masu nuna tsananin soyayya ga namiji,musamman mijin da bai damu da su ba ko da kuwa za su cire fatar jikin su ne su shimfiɗa musu dan ya taka ya ji daɗi? Ina mata masu jin haushin duk wanda ya ji haushi akan mugunta da zalincin da mijin su yake yi musu? To ku matso kusa ku ji labarin yayar ku Fauziyyah matar Abbas. Domin duk yanda kike ji da ganin labarin MUGUN MIJI a duniya,to Abbas ya dasa wa dukkan maza aya. Idan kina so ki tabbatar ki biya 500 kacal ta 0006366584 Ja'iz bank Hamida sanusi Ahmad. Sai ki tura shaidar biya ta 09031416423 ta wannan layin. Kada ku bari a baku labari,domin gani ya kori ji.* A parlour suka tarar da Ummi ta na wasar baki tare da baza ido tana dakon

Chapter 11 of 12