Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 12
buga wani dogon tsaki ya wuce ɗaki. Ya na shiga ya tsaya ya na jin ɓacin rai na yunƙuro masa. Cike da masifarsa da baya gajiya ya ƙwala mata kira. Jikinta na makyarkyata ta miƙe ta na tunanin abinda ta aikata da yake yi mata wannan kiran mafarautan. Ta na shiga ta same shi a tsaye ya na huci zufa na karyo masa kamar wanda ya haɗiyi kunama............ [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨ PAGE 12. *SANARWA.* *Masu son su siya kuma ku sanya 500 ta 0006366584 Hamida Sanusi Ahmad Ja'iz bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.* A hargitse ya ke binta da wani irin mugun kallo. Cikin dakakkiyar muryarsa da ke mantar da ita cewa Abbas fa mijinta ne ba shugaban hukumar hukunta masu manyan laifuka ba ya ce mata. "Ke yanzu Fauziyyah kin haihun ma ba za ki yi hankali ba? Ki duba ki ga yanda kika bar min yarinya very exposed to sauraye su ciji abinda za su ciza su bar na bari. To na rantse miki in ta yi rashin lafiya sai na yi miki dukan da za a kwantar da ke a ICU. Jaka kawai,dalla wuce ki ɗaura net." Cikin sauri Fauziyyah ta shige ciki ta hau kiciniyar ɗaura net ɗin ta na mai jin maɗaukakin mamaki akan yanda Abbas yake so da ƙaunar jaririyarta. Ƙwarai jaririyarta za ta kira Muhseenah,domin kuwa Abbas da bakinsa ya furta yarinya ko yaron da za ta haifa mallakinta ne ita kaɗai shi babu abinda ya haɗa shi da cikin da take ɗauke da shi. Haka ta gama daura net ɗin ta wuce ta fara shirin bacci. Abbas na zaune ya kasa rintsawa saboda tinanin halin da Hajiyansa ke ciki. Shi ya rasa dalilin da ya sa ake neman tauye masa farincikinsa akan farincikin wata banza Fauziyyah. Tsaki ya ja ya juya ya na kallon bayan ta da ta juya masa tana rungume da jaririyarta. Tudun ƙugunta ya kalla ya gan su a cike gwanin burgewa. Sabuwar rigar baccin da ta saka ya shafa,sai ya ji fatar jikinta ta yi wani laushi tuɓus,sake kai hannunsa ya yi ya taɓa da kyau dan ya tabbatar da inda ya jiyo laushin. Idanuwanta cike da bacci a cikinsu ta ce. "My king ban fara sallah ba fa." Haushin kalamanta ne suka sanya shi birkita ta da ƙarfi ya rungumeta. Nan take ta wartsake daga baccin da ke cin idanuwanta ta ce. "Da gaske nake yi ban fara sallah ba,ka yi haƙuri idan..." Bakinta ya kama ya na sumbata da ƙarfi har ta na jin zafi,da ƙarfi ta sa hannayenta biyu ta ture sa, idanuwansa ta kalla ta ga yanda suka rine suka yi ja saboda ɓacin rai. Nan da nan jikinta ya hau rawa,bakinta na karkarwa ta ce. "Ka yi haƙuri bari na yi maka irin abun nan da nake yi maka idan ina al'ada." A kausashe ya ce mata. "Bana so ! Ki riƙe abunki ki jiƙa ki sha. Saboda kin ga ma ina binki ta lallami shine za ki kawo min iskanci? To tashi ki bar nan." Cikin rashin fahimtarsa ta ce. "Ina zan je da tsohon daren nan?" "Gidan uban ki za ki je. Dalla malama ɗauki pillow ki koma parlour." "Ka manta da Muhseenah ne? Ko na bar maka ita anan idan ta yi kuka sai na shigo?" Tsaki ya ja mai tsawo sannan ya miƙe riƙe da pillow ya koma parlour. Ya na zuwa ya kunna TV ya kwanta a doguwar kujera. Tashoshin da ya buɗe wanda suke nuna finafinai na batsa ya kai. Rage volume ya yi ya kashe fitila ya yi kwanciyarsa ya na kallon su. Da abun ya yi masa daɗi sai ya nemo wayar ɗaya daga cikin ƴammatansa da yake hutawa da su. A tare suka raya daren kamar ta ɓangarenta bata da iyayen da suke kula da lamuran tarbiyyarta. Cikin yanayi na najasa Abbas ya yi bacci. Washegari da sassafe ya farka ya kashe kayan kallon sannan ya wuce ya ɗauki flask ɗin ruwan zafi domin ya juye ya yi wanka. Ya na ɗauka sai ya ji shi ƙwalam babu komai a ciki,wurgar da flask ɗin ya yi da ƙarfi nan take kuwa ya fashe. A hasale ya hau ƙwalawa Fauziyyah kira kamar wani mafarauci. Cikin bacci ta ji yana kiranta. Tashi ta yi da kumburarrun idanuwanta da suka ci kuka bayan ta jiyo abinda Abbas ɗin ya yi a daren jiya. Jikinta a sanyaye ta fita ta same shi tsaye ya riƙe ƙugunsa ya na kallon hanyar ɗakin. Ta na fitowa ta ga flask ɗin ta a fashe a kasa. Da sauri ta ɗuka ta ɗauka ta na jujjuyawa, idanuwanta cike da alamar tambaya takre kallon shi. Haɗe girar sama da ta kasa ya yi kafin ya ce. "Me yasa babu ruwan zafi a ciki? Sau nawa zan faɗa miki kar ki dinga barin buta da flask babu ruwa?" "Muhseenah fa na yi wa wanka da shi jiya My king. Me yasa don Allah ka ke fashe min abubuwan da sai na wahala nake samun kuɗin siyan su? Last month fa ka fasa wani flask ɗin,shine yanzu dan ka gama kallon iskancin ka cikin dare za ka zo ka fashe min abu na?" Mamakin kalamanta ne suka sanya Abbas tsayawa ya na binta da kallo,ita kuwa ta ji zafin kallon batsar da ya kunna da daren jiyan ya yi har ya biya buƙatarsa,dan rashin imani irin nasa kuma ya ke neman ci mata mutunci da sassafe. Murmushi Abbas ya yi,domin da alama bata ma san wayar da ya kwana yana yi ba da budurwarsa iya kallon da ya yi ta gani. Sai kawai bai tanka mata ba ya fita tsakar gida. Tsayawa ya yi yana kallon ko ina na gidan. Mamakin ganin ko ina tsaf ya yi kamar jiya ba gidan bane ya zama kamar bola dan datti. Agogon dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya kalla,sai ya ga ashe karfe bakwai da minti ashirin na safiya ta yi. Lallai matar nan akwai ta da ƙoƙari. Cikin sanɗa ya ke tafiya har ya dangana da kitchen ɗin Barirah. Leƙa kitchen ɗin ya yi kamar wani ɓarawo,gani ya yi ta ɗora ƙatuwar tukunya mai ɗauke da ruwan zafi. Murmushi ya yi ya juya zai koma bangaren su ya ɗakko bokiti dan ya kwashi ruwan. Ya na ɗaga kai sai suka yi ido huɗu Barirah ta naɗe hannu ta na kallonsa. Nan da nan ya miƙe tsaye daga duƙawar da ya yi yana sanda cike da borin kunya. Kallonsa ta yi daga sama har kasa ta kauda kai. Wucewa cikin kitchen ɗin ta yi sannan ta ce. "Allah Ya wadaran naka ya lalace, Wai raƙumin dawa ya ga na gida. To wannan ruwan zafin da kake gani ko da shi za ka wanke zunuban ka Abbas sai dai ka tafi da su ƙiyama a haka,amma ba zan bari ka ɗiba ba." Abbas da ya san bashi da gaskiya,kuma Barirah ba raga masa take yi ba,sai ya wuce ya ɗauki bokiti ya ɗebi ruwan ƙaton drum ɗin su a haka ya shiga wanka. Ya na gamawa ya fito ya na rawar sanyi kamar wanda ake bugawa ganga. A guje ya shiga ɗakin su ya nemi hijabin Fauziyyah ya rufu da shi. Ya jima a kwance a lulluɓe kafin ya miƙe ya hau shafa mai. Ya na gamawa ya sanya kayansa ya fesa turarukansa ya bar gidan a babur ɗinsa ba tare da ya yi sallar asubar da ta kufce masa ba. Kai tsaye gidan Kawu ya nufa,ya na zuwa ya tarar da matan Kawu na ta kaiwa da komowa a tsakar gida. Ƴan matan gidan da ƙananan yara suna ta shirin islamiyya. Babu wanda ya amsa gaisuwarsa a cikin matan Kawun,saboda kowa haushin halayyarsa yake ji,kyaɓe baki ya yi sannan ya nufi ɗakin da ya san idan Hajiyansa ta je gidan anan take sauka. Muryar Kawu ya ji a bayan sa yana faɗin. "Kana shiga ɗakin nan zan fashe maka kai da wannan gorar dukan ɓarayin. Kai wai wanne irin ɗan iskan yaro ne mara jin magana? Don ubanka ban faɗa maka kar ka sake ka zo inda ƴar'uwata take ba har sai ta ji sauƙi ta neme ka da kanta? Fita ka bar min gida kafin na gurgunta ka." Banda ƙunƙuni babu abinda Abbas ke yi tinda Kawun ya fara yi masa faɗa. Kan dole ya fita ya bar gidan cikin fushi. Tada babur ɗinsa ya yi ya wuce ATM ya ciro kuɗi ya wuce kasuwa. Ransa a mugun ɓace ya ke cinikin washing machine da sauran electronics appliances ɗin da Fauziyyah ke da buƙata. Shi kanshi mai shagon sai ya dinga jin tsoron cijewa da dagewar da Abbas ke yi masa. A haka aka gama ciniki ya biya komai ya samo mai ɗan sahu ya loda masa kayan. A gaba ya saka shi suka wuce gidan Kawu,suna zuwa ya roƙi mai adaidaitan ya taya shi shiga da kayan ba za su jima a ciki ba za su kwashe su kai wani gidan kuma,cikin muryar tasha mai ɗan sahu ya ce. "Alaji in dai za ka biya me zai hana a yi maka aiki?" Ganin yaron ya yaga masa a iya shege ne ya sanya shi sauke fushinsa ya ce. "Kai dai mu gama komai lafiya ka ga irin sallamar da zan yi maka." Babu ɓata lokaci matashin ya taya Abbas suka shiga da washing machine,blender, kettle ɗin ruwan zafi,iron,flask ɗin ruwan zafi,da rice cooker. Kai tsaye ɗakin da Hajiya ke kwance Abbas ya nufa,duk kiran sunansa da Matan Kawu ke yi bai sa Abbas ya tsaya sauraron ko ɗaya a cikin su ba. Ya na shiga ya tarar da Hajiyansa na zaune an jingine ta a jikin gado,gefenta kuwa duk pillow ne da aka yi amfani da su wajen tare ta. Babbar yarinyar gidan mai suna Safiyah na zaune a kusa da Hajiyah ta na bata kunun gyada. A hankali Hajiya ta ɗaga kai ta na kallon Abbas. Kuka ya fashe da shi ya kwantar da kansa a saman cinyarta ya ce. "Don Allah Hajiya ki yi haƙuri ki yafe min,na yi miki alƙawari wannan shine karo na ƙarshe da za ki sake kama ni da wani laifi. Kinga na siyo mata ma abubuwan da kika ce har da wasu ma da na san za ta buƙata. In Allah ya yarda zaman da za mu yi a yanzu sai ya fi na da daɗi. Hajiya ki yi min magana mana." Safiyah ce ta ce. "Yayah Abbas ta yaya za ta iya yi maka magana bayan harshenta ya karye,bakinta ya juye,ko baka kula bane? Yanzu haka fa kanta kawai take iya juyawa sai kuma ƙyafta idanuwa,banda haka ko hannunta sai an gyara mata." "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un. Na shiga uku,don Allah Hajiya in dai ɓacin raina ne ya jawo kika faɗa wannan halin to ki warke,daga yau na yi miki alƙawarin zan gyara halayena." Kyafta ido Hajiya ta yi sau biyu,sannan ta ɗaga masa kai. Murmushi Abbas ya yi ya tashi da sauri ya ce. "Bari na kai kayan nan gida na zo na kai ki asibiti,bai kamata ki zauna a gida ba kina a cikin wannan halin na rashin lafiya." Girgiza masa kai Hajiya ta yi idanuwanta na zubar da hawaye. Cikin sanyin murya Safiyah ta ce. "Hajiya da kanta ta ce kar a kai ta asibiti,shi yasa ma Abbah ya dawo da ita gida." "Ke dalla yi min shiru,tinda ba uwarki bace a kwance kin ce haka mana,kai shigo mu kwashe kayan nan mu kai can inda na faɗa maka. Daga nan za ka taimaka min mu zo mu kai tsohuwata asibiti." "Alaji kuɗin aikin ka fa ya ƙaru." "Kai dalla malami kar ka faɗan maganar banza mana,ce maka na yi ni daƙiƙi ne ban san ya kamata ba?" "Ai wai kar ka min eh yane ne,bani da mutunci akan sabgar nera." Tsaki Abbas ya ja ya ɗauki abubuwan da zai iya ya yi gaba. A gaba Abbas ya saka ɗan sahun bayan sun gama loda komai suka nufi gidan shi,ko da suka je sun tarar da Fauziyyah zaune Barirah na shafa mata kayan gyaran jikin da take ta yi mata a sirrance,wanda sune sanadiyyar sauyawar da Abbas ya ji ta yi a daren jiya. Kallon,Fauziyyar ya yi a sheƙe ya na jin wani matsanancin haushinta na ɗawainiya da shi. Dama wannan abubuwan take shafawa shi yasa jikinta ya ke yin laushi kamar audiga? Ƙwafa ya yi ya shige da kayan hannusa kitchen ɗin su.Ba tare da ya sanar da su za a shigo ba dan su gyara jikin su mai ɗan sahu ya afka ɗauke da washing machine a ka ya dire. Kallon Fauziyyah ya dinga yi kamar wani baƙin maye. Haka Abbas ya wuce shi ya kwaso sauran kayan ya dire ba tare da ya ji kishi ko haushin me ɗan sahu ba. Kallon mai ɗan sahu ya yi ya ce masa. "Mu je ka kai mu asibitin." Suna fita Abbas ya shigar da Machine ɗinsa ya wurgawa Fauziyyah makulli ya sake ficewa babu ko sallama ballantana ya sanar da ita inda zai je. Su kuwa su Fauziyyah basu tashi fashewa da dariyar murna ba sai da suka ji tashin adaidaita sahu. Cikin ihun murna Fauziyyah ta rungume Barirah ta ce. "Wayyoo Allah Aunty na gode miki,yau ni ce da washing machine da blender. Ohh ni fauziyyah na ci daɗi da wuya a gidan duniya." Dariya suka sake fashewa da ita sannan suka zauna suna ta duba kayan. Suna gamawa Fauziyyah ta wanke jikinta ta ɗauki skin oil ɗin da Barirah ta siyo mata na Hamibrah ta shafe jikinta da shi. Riga da skirt na atampa ta saka ta kafe ɗauri mai kyau sai sheƙi take yi ta na ɗaukan ido,nan da nan ta fito shar a mai jegonta,Barirah kuwa hotuna ta yi mata masu kyau,tace za ta ajiye saboda tarihi. Hira suka zauna suka dinga yi,kafin daga baya Fauziyyah ta hau taya Barirah kwashe kayan ta suna durewa a buhu. A can gidan Kawu kuwa Abbas na komawa ya tarar da Kawun nasa ya dawo har da babban yayansu Hajiyan,da ƙyar da siɗin goshi suka yarda a maida Hajiya asibiti kar a biye mata. Godiya Abbas ya dinga yi musu sannan ya je ya sallami ɗan sahu da kuɗi mai tsoka. Godiya ya yi masa ya wuce,a motar babban yayan su Hajiyan Abbas suka wuce asibiti,Kawu ya shiga tashi motar shima ya bi bayan su. Suna zuwa aka hau bawa Hajiya taimakon gaggawa. Har kowa ya tafi gida saboda dare da ya yi amma Abbas na nan ya ƙi tafiya,ya ce shi a wajen zai kwana da ita. Duk yanda aka so ya tafi ƙi ya yi,dole aka ƙyale shi ya kwana da ita. Fauziyyah kuwa sha biyun dare na yi ta hau safa da marwa a tsakanin ɗakinta zuwa tsakar gida. Da ta ji motsi sai ta yi zaton Abbas ne ya dawo,sai ta ji shiru take tabbatar wa da ba shi bane. Rashin waya ne ya hana ta kiransa ta ji inda ya maƙale bai dawo gida ba. Ta na so ta yi wa Shehu magana akan ya kira mata Abbas ɗin,amma ta na jin kunyar Shehun,dan ta na sane da irin takun saƙar da ke tsakanin shi da mijinta,ba zai so kira mata Abbas ɗin ba gudun kar ya yi masa haukan nasa da ya saba. Kuka ta zauna a tsakiyar parlour ta na yi. Da misalin biyu na dare ta cire ran Abbas ba zai dawo gidan ba. Dan haka sai ta je ta yi alwala ta zauna a kujera ta na ta jan Hasbunallahu wa ni'imal wakil. Fatan ta duk inda yake Allah ya sa yana cikin ƙoshin lafiya. Washegari da asuba... *To mace me miji ɗan duniya mamugunci kamar Abbas ma ta san ta yi wa mijinta addu'a, sai ke da kika rako nisa'u duniya ce baki san ki wa mijinki addu'a ba ko?* [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨ PAGE 14. *SANARWA.* *Masu son su siya kuma ku sanya 500 ta 0006366584 Hamida Sanusi Ahmad Ja'iz Bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.* "Ban gane za su tashi ba? Ina za su hau idan sun tashi tinda ni dai gidana babu bene?" Dariya Fauziyyah ta yi,domin ganin Abbas a gida ya sanya zuciyarta nishaɗi,shi yasa duk wani motsi ko maganarsa ke ƙara mata shauƙin so da ƙaunarsa. Cike da nishaɗi ta ce. "Ina nufin za su tashi su koma sabon gidan su da Yaya ke gina musu tin da jimawa." Gaban Abbas ne ya yanke ya faɗi har sai da ya ji lomar abincin da ke bakinsa na neman sarƙe shi,idan su Barirah suka tashi ai shi asirinsa ya tonu,saboda taimakawa Fauziyyah da suke yawanyi har ta kai ta kawo ko albashi aka yi sai ya ci wajen sati biyu bai kawo komai a gidansa ba,ga kuma kuɗin haya da Shehu ke cake masa babu giɓi ko fashi,banda gas ɗin su da yake mora kamar bashi da kuɗin siyan nashi.Cikin sauri Fauziyyah ta miƙa masa ruwa ta na yi masa sannu. Dakewa ya yi ya shanye damuwar dake cikin ransa ya ƙarasa danna abincin da ya jima da dena yi masa daɗi. Ya na tsaka da cin abincin aka doka sallama,mahaucin da ya kira har ya iso. Tsallake kwanikan ya yi ya fita ya na gyara wuyan rigarsa. Gaisawa suka yi da matashin mai fiɗar,Abbas ya umarci Fauziyyah da ta kai musu ƙaton buhu da roba farfajiyar gidan. Babu ɓata lokaci mai fiɗa ya hau aikinsa. Barirah na fitowa yin alwalar sallar walaha ta ga Abbas na binta da wani irin kallon da ta kasa fassara shi,sai kawai ta wuce ta na jan tsaki ta yi alwalarta ta koma ɗaki. Ta na idar da sallah ta nufi kitchen dan ɗora abincin rana. Abbas ta gani da robar kayan cikin da aka gyara ya na washe baki ya ce. "To Yayar Fauziyyah ga wannan a saka a miya. Na kula tinda ƙanwar taki ta haihu kuke ta faman ɗawainiya da ita,Allah dai Ya saka da alkhairi." Tsananin mamakin sauyin da ta gani a wajen Abbas ne ya sanya ta saurin ja da baya ta na ƙwalawa Fauziyyah kira. Cikin abinda bai fi minti ɗaya ba Fauziyyah ta isa wajen da su Barirah ke tsaye. Nuna Abbas Barirah ta yi sannan ta ce wa Fauziyyah. "Ja hannun mijinki ki kaisa ɗaki ki tofa masa addu'o'i,domin na ga alama duk inda ya je jiya ya kwana sun daki kansa,shi yasa yazo min nan yana wasu maganganu kamar wanda akai wa wankin kwanya." Murmushi kawai Fauziyyah ta yi ta na kallon Abbas wanda ya ɗaure fuska kamar bai taɓa dariya ba. Cike da ɓacin rai ya ce. "Ku dai mata akwai mashirmanta sam ba a iya muku,nan nan kike masifa ban iya magana ba,bana ganin darajar mace yen yen yen. Yanzu na zo ina yin abun arziƙi irin wanda kuke so kina yi min shirme,kar Allah Ya sa ku yi amfani da hanjin,abokaina na zuwa anjima zan juye musu su kai wa matansu." Dire mata robar ya yi zai bar wajen,cikin ɗaga murya Barirah ta ce. "To ai ɗawainiyar da kake magana muna yi ba da aljihun mu muka yi ta ba,Yayanta ɗan albarka da ya san ya kamata shine ya turo kuɗi aka yiwa ƙanwarsa duk abinda ya dace,tinda kai dai ba namijin arziƙi bane ka kasa siyan ko allura saboda ita da ƴarka." Ba Abbas kaɗai maganar ta daka ba,hatta Fauziyyah da ke tsaye a wajen ji ta yi kamar ta arta da gudu ɗaki ta kulle ƙofa. Cak Abbas ya tsaya tare da juyowa ya na ƙare musu kallo. Ransa a matuƙar ɓace ya kalli Fauziyyah dake rawar ɗari ya ce. "Da gaske ne abinda ta faɗa? Dama Abdallah ne ya ɗinka miki suturu,ya siyawa Muhseenah kaya sannan ya siya miki rigar baccin da kika saka jiya?" Cike da bashi tabbaci Barirah ta ce. "Ƙwarai da gaske shine ya sai komai,har abincin da ka kasa siya ka zauna kana lashewa da tanɗe duk abinda aka baka da wanda ba a baka ba saboda rashin zuciya da sanin ya kamata. Kai a zaton ka ga abincin maƙota ya samu bari ka ci banza ko?" Ba tare da Abbas ya ce komai ba ya wuce cikin ɗaki ya ɗakko kuɗin sallamar da zai bawa mai fiɗa,sai da ya sallame shi sannan ya koma ɗaki ya kwanta a saman gado. Fauziyyah na can wajen Barirah ta na kiran ta shiga uku ta lalace. Barirah kuwa cike da jin haushinta ta ce. "Ai fa sai ki shiga ukun,tinda shi ɗin ɗaukan rayuwarki zai yi tinda ɗan'uwanki ya yi miki abinda ya gaza a matsayinsa na mijinki. Ke yanzu Fauziyyah ba zaki miƙe ki ƙwatarwa kan ki ƴanci ba ko? Ta ya zaki zauna namiji ya dinga juya ki haka har ya raba ki da ƴan'uwanki?" "Haba Aunty me yasa kike faɗar haka kamar baki san halin kishin Abbas ba?" "Kishi fa na ji kin ce Fauziyyah? Abbas ɗin ne yake kishin ki? Lallai kuwa idan haka ake kishi Allah wadaran kishi. Mutumin da bai ƙi abokansa su gan ki tsirara ba shine yake kishin ki? Wukaƙanci ne kawai da raini yake damun Abbas ba komai ba,dan haka idan zaki miƙe ki nuna masa mahimmancin dangin ki da ya raina ki miƙe,in ba haka ba to zai yi ta cin zarafin ki da nasu ya ɓata guntuwar alaƙar da ta rage a tsakanin ki da su. Yanzu tinda Aunty Khairi ta tafi kin kirata kin gaishe ta? Ko kin yi mata bangajiya? Girgiza kai Fauziyyah ta dinga yi kamar ƙadangaruwa. Ganin yanda hankalinta ya tashi ne ya sanya Barirah wucewa ta ɗauki kayan cikin ta fara sarrafawa,domin a haukan Abbas sai ya kwashe ya bayar ɗin kamar yanda ya faɗa. Fauziyyah kuwa kasa komawa ɗaki ta yi sai da ta jiyo muryar Abbas a waya yana ɗaga murya ya na faɗin. "....ka ji dai na faɗa maka,idan ka sake shiga sabgar iyalina kotu ce za ta raba ni da kai,sai in ga ni da kai wa yake da iko da Fauziyyah." Kashe wayarsa ya yi ya na huci. A parlour Fauziyyah ta tsaya ta kasa shiga ɗakin. Cikin hargowa Abbas ya ce mata. "Baƙar munafuka annamimiya,zaki shigo ne ko sai na fito na karya ki?" Da sauri ta ƙarasa shiga ɗakin ta zauna a bakin gado,kallonta Abbas ya yi kafin ya ce mata. "Wato kina da masaniyar Yayanki da na tsana ne ya kashe maki kuɗi a asibiti da duk wata cima da sutura da na gan ki da ita amma baki sanar da ni ba ko? Ce miki na yi ba zan iya kula da gidana ba sai wani banza ya saka min hannu?" Da sauri Fauziyyah ta ɗaga kai ta kalli Abbas wanda idannuwansa suka rine suka koma jajaye. Cikin ɓacin rai itama ta ce. "Na amince ka yi min duk abinda ka ga dama,amma kar ka sake ka ƙara zagin yayana." Ja Abbas ya yi da baya yana kallon fuskarta da ta ɗaure ta tamau kamar ba Fauziyyar da ya sani ba. Dariya ya yi yana tafa hannu,cike da mugunta ya daki ƙirjinta kamar yana magana da sa'ansa ya ce. "Idan na sake zagin yayan naki me za ki yi min,uhumm tell me,me za ki yi min!" Ture hannunsa ta yi a jikinta sannan ta raɓe shi za ta wuce,damƙo wuyanta ya yi ta baya ta koma tsakiyar ɗakin,tsayawa ya yi yana binta da kallo,wani irin kyau ya ga ta yi masa kamar ba Fauziyyan da ya sani ba. Sakinta ya yi ya juya ya na magana cikin wani irin amon rashin kirki ya ce. "Daga yau sai yau,kar na sake ganin kin saka ko da tsinke ne wanda Abdallah ya siya miki,idan kuma kika kuskura kika saka a bakin wannan ƙaddararran auren da na rasa me yake riƙe da shi bai tsinke ba har yau." A gigice Fauziyyah ta juya ta na kallon Abbas. Gira ya ɗaga mata sannan ya ce. "Ina nufin kowacce kalma da kika ji ta fito daga baki na. Dan haka zaɓi yana wajen ki. Ko ki ajiye masa kayansa ki bayar,ko kuma ki yi amfani da shi a bakin auren ki." Hawaye ne masu mugun zafi suka hau zubar mata,ji

Chapter 7 of 12