Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 12
ta yi kamar Abbas ya ɗauki wuƙa mai kaifi ya kafa mata a ƙahon zuciyarta. Ba maganar amfani da kayan da  Abdallah ya siya mata bane damuwarta. Babbar damuwarta yanda ya kira auren su da ƙaddararran aure,duk ƙoƙarin da take yi wajen riƙe musu auren,shi ne ya zamo ƙaddararran aure har yake neman kai da shi? Hawayenta ta share ta kafe Abbas da ido,cikin wata iriyar murya ta ce masa. "Na amince zan ajiye duk wasu kaya da Yah Abdallah ya yi min,amma dole sai ka sama mana abinda za mu saka a madadinsa,saboda bamu da ko allurar sakawa daga ni har Muhseenah,tinda baka siyo mana ba,ni kuma na bayar da dika tsofaffin nawa. Sai kuma wata tambaya da nake son na yi maka." Kallonta ya yi da alamun yana sauraron duk abinda take faɗa. Cikin shan majina ta ce. "Don Allah ina so ka faɗa min gaskiya. Shin ka taɓa so na kuwa a rayuwar ka? Ka taɓa jin cewa idan babu ni ba za ka taɓa rayuwa ba? Ko sau ɗaya ne ina son sanin amsarka please." Ta ƙarashe maganarta cikin wani irin rikitaccen kuka. Jikin Abbas ne ya yi mugun sanyi,rayuwarsu ta baya ce ta bijiro masa a cikin ƙankanin lokaci,cikin sauri ya kau da tambayar da ta yi masa ya ce. "Matsa min na wuce,in dai sutura ce yanzu zan kawo muku,ki tabbata baki sake sakawa ƴata kayan wannan yayan naki ba,kin ji na faɗa miki dai." Alwala ya yi ya koma ɗaki,ya jajjefa sallah,tin daga ta asuba da bai yi ba har azahar da ake kiran sallarta a wannan lokacin. Yana idarwa ya bar gidan ya nufi kasuwa. Sai da ya kashe wa Fauziyyah kuɗaɗen da bai taɓa kashe mata irinsu ba ita da Muhseenah sannan ya koma gida. A gidan ya tarar da su Salman suna zaman jiransa,suna ganinsa suka tashi suna yi masa surutun sun jima suna jiransa amma bai dawo ba. Tambayar su ya yi ya ce. "Kun ci abinci?" "Eh Madam ta cika mana ciki da abinci da ruwa,har da ƙullin naman suna an bamu,Allah Ya raya mana takwarar Hajiya." Murmushi ya yi sannan ya shige gidan da kaya niƙi-niƙi,cike da mamaki Fauziyyah ke bin Abbas da kallo. Kaya ya hau fitar mata ready made,da kuma dogayen riguna,sai da ya fitar da kala goma sha biyar,sannan ya koma kan na Muhseenah,ita kuwa har da na gwanjo ya ƙaro mata saboda zaman gida,su pampas da fida da sauran tarkacen kayan yara. Cikin ranta Fauziyyah ke ayyana. 'Akan na saka kayan da yayana ya yi min gwanda ya kaso waɗannan maƙudan kuɗaɗen? Hakan na nufin kenan ba zai taɓa barin zumuncina da Yah Abdallah ya dawo daidai ba?' A tsawace Abbas ya maimaita mata tambayar da ya yi mata da farko. "Na ce ina kayan da wancan ɗan rainin wayon ya siya miki suke? Tattaro min su nan ki kawo." Cikin sauri Fauziyyah ta ɗebo kayan ta saka a jakar da aka kawo mata su ta miƙa masa. Ba tare da ya sake cewa komai ba ya fita ya bar gidan tare da su Salman. Kai tsaye gidan kawu ya nufa ya damƙa kayan a hannun uwar gidan Kawu ya ce a bawa yara. Nan da nan kuwa ta hau washe baki ta na zuba masa godiya da sanya albarka. Daga nan kuma sai suka wuce asibiti bayan sun tsaya a hanya sun siyawa Hajiya abinci da kayan marmari. A can gida kuma Fauziyyah ce ta ke ta ɗaga kayan da Abbas ya siyo ta na mamaki,kaya ne masu kyau da tsada,wata leda babba ta gani a gefen kujera,sai ta miƙa hannu ta ɗauka. Ta na buɗewa ta ga kayan bacci masu ɗaukan hankali da kuma rigar mama da ɗankamfai kowanne shida-shida. Tsananin mamaki ne ya sanya ta kiran Barirah ta na nuna mata kayan da Abbas ya siyo mata. Kyaɓe baki barirah ta yi sannan ta ce. "Sannu ƴar daɗi miji,sai ya raba ki da Ɗan'uwanki sannan ya siyo maki kayan da basu kai tsadar na yayanki ba,saboda ke kuma kina tsoron rasa shi sai kika bi umarninsa kika bayar da kayan Ɗan'uwanki ya tafi ya zubar ko? Hummm Fauziyyah ni kam ina ga zan matso da ranar tashin mu daga kwana uku ta koma kwana biyu ko gobe ma,idan ba haka ba baƙincikin da kike ƙunsa min shine zai yi ajalina." Dariya sosai Fauziyyah ta yi, ta faɗa jikin Barirah ta na faɗin. "Auntyna ba zaki gane irin son da nake yiwa Abbas bane. Ni fa akan shi zan..." "...Zaki iya rabuwa da kowa. Na shaida kuwa,tinda kika rabu da iyayenki Fauziyyah wanene ba za ki rabu da shi ba? Da an yi magana ki hau kiran soyayya soyayya kamar mu zaman ƙiyayya muke yi da mazajen mu." Dariya Fauziyyah ta yi cike da wauta da shiririta ta ke ƙoƙarin kare kanta. Gajiya da jin shirmenta Barirah ta yi sannan ta ce. "To tinda dai king ɗin naki ya siyo miki wannan rikitiɓar kayan arziƙin,kuma mun gama suyar nama ai yau sai a yi masa kwalliya ta musamman ko? Nima kuma daga yau na gama aikina na gyaran jiki,Allah ya sa king ɗin naki ɗan wulaƙanci ya yaba." "In Allah ya yarda zai yaba Auntyna. Kafin nan na tabbata Allah Ya yaba ƙoƙarin da kike yi akaina,ni ma kuma na yaba,ina fatan Allah Ya biya ki da babban rabo. Allah Ya sa kuna komawa sabon gida a samarwa Muhseenah ƙani ko ƙanwa." Fara'ar Barirah ce ta ƙaru,cikin jin daɗin addu'ar da Fauziyyah ta yi mata ta ce. "Amin Ya Allah,ina fatan Allah ya kawo muku ƙarshen wannan mugun zaman da kuke yi ke da mijinki Fauziyyah,ban taɓa jin ƙaunar wata halittar da bamu haɗa jini da ita ba sama dake Fauziyyah,ina jin ki a raina kamar ƙanwar da muka fito ciki ɗaya da ita. Shi yasa ko na yi fushi dake nake haƙurewa na dawo na ci gaba da taimaka miki. Ina fatan zumuncin mu ya ɗora har aljannah." "Allah Ya sa Auntyna." Da wannan hirar Fauziyyah ta wuce ta yi alwala ta yi sallar azahar. Ta na idarwa ta fara gyara ɗakinta,gyaran da ta jima bata yi irinsa ba saboda girman ciki. Tsayawa tayi tana kallon saman madubinta ta ga yanda ta jera kayan kwalliya da turaren da Abbas ya siyo mata gwanin sha'awa. Wani irin farinciki ne ya lulluɓe ta. Wajen kayan sawarta ta duba,ta hau ɗaga rigunan baccin da ya siyo mata guda shida ta hau dubawa. Wata fara sol da aka yi da yadi mai santsi ta ɗauka tana kallo. Hango kanta a cikin rigar kawai ya sanya ta jin ƙaunar kasancewa da king ɗin nata. Murmushi ta saki ta ajiye kayan sannan ta koma ta zaɓarwa Muhseenah wanda za ta saka. Abinci ta je suka ci da Barirah suna gamawa Barirah ta bata haɗin da ta yi mata na rake,kankana,ɗanyar citta,kaninfari, na'a-na'a, zuma,madarar shanu,abarba,da lemon zaƙi. (Zaki gyara kowannen su yanda ake gyara su,sai ki haɗe su waje guda bayan kin yanka rake ƙanana sosai kin markaɗa da ruwa kin tace. Sai ki zuba madarar shanu da zuma ki shanye.) Banda lumshe ido babu abinda Fauziyyah take yi. Ita kanta Barirah santin haɗin take ta yi. Suna gama sha Barirah ta je kitchen ta tafasa musu ganyen na'a-na'a da kaninfari,ganyen magarya da ƴar bagaruwa kaɗan da rabin lemon tsami. Sai da suka tafasa sosai sannan ta tace ta zuba wa kowaccen su a buta ta ajiye. Barirah ce ta fara shiga ta yi wanka ta yi amfani da wannan ruwan wajen wanke gabanta da shi,sannan Fauziyyah ma ta shiga ta yi aski na hammatarta da gabanta,sannan ta wanke wajen da ruwan nan da Barirah ta gama haɗa musu. Wani irin natural ƙamshi ne ke tashi a wajen. Ita kanta ta ji sauyi a jikinta sosai saboda haɗe-haɗen da Barirah ta dinga bata tana sha. (Idan kina son kayan gyara na ciki da waje natural,wanda ba za su kawo miki illa a jikin ki ba ko bayan kin gama amfani da su,to ki nemi Littafin MAIDA TSOHUWA YARINYA wanda yake akan farashi 1500. A ciki za ki samu sana'ar da za ki riƙe kuɗi su dinga shigo miki.09031416423) Har dare ya rufa matan biyu basu zauna ba,suna nan suna ta shirin tarbar mazajen nasu. Da misalin takwas da rabi Shehu ya dawo da matsananciyar gajiya. Barirah bata yi ƙasa a guiwa ba wajen raka shi har banɗaki ta taya shi wanka suka koma ɗaki. Fauziyyah na zaune ta ci ado tana zuba ƙamshi sanye da sabuwar rigarta ta na jiran dawowar nata gwarzon. Sai dai har ƙarfe sha biyu na dare ta gota babu Abbas babu labarinsa. Gajiya ta yi da kallon ta kashe komai ta koma ɗaki bayan ta ajiye masa abincinsa da duk wani abu da zai buƙata. Fatan samun sauƙi ta yiwa Hajiya ta kwanta tana tinanin duk yanda akai Abbas a wajenta yau ma zai kwana. A ɓangaren goga Abbas kuwa tinda suka duba Hajiya suka kama hanya sai gidan wani abokinsu mai suna Babson. Babson babban manemin mata ne,kuma ɗan shaye-shaye na gaske. Shi ne yake gayyatowa su Salman ƴan matan da suke hutawa da su a duk lokacin da suka zo wajensa,sannan yana samar masu da ƙwayoyin da suke afawa a farashi sassauƙa. Shi yasa idan ba sanin Salman ka yi ba sosai ba za ka taɓa cewa yana shaye-shaye ba. Dan baya busa kowanne irin hayaƙi ballantana ya nuna a jikinsa. Abbas dai iyakarsa hutawa da ƴan mata,babu ruwansa da shan duk wani abu mai saka maye. Dan haka yana gama abinda zai yi da su ya yi musu sallama ya buga machine ɗinsa ya wuce gida. Ko da ya isa gida sai ya ga ƙarfe ɗaya na dare ta gota. Yana shiga ya kafe machine ɗinsa sannan ya buɗe ɗakinsa ya shige,ganin ko ina da duhu ne ya sanya shi haska wayarsa,naman da ya hango a soye a babban roba,ga kuma abincinsa a gefe ne ya sanya shi sakin murmushi. Zama ya yi yai nak ba tare da ya nemi Fauziyyahn ba. Ya na gamawa ya zaro wayarsa ya kunna data,nan fa ya hau karo da messages ɗin jama'a ciki har da na su Nana da ƙawayenta da yake mu'amala da su. Message ɗin Nana ya fara buɗewa. Nan take ya yi karo da hotunan ƙirjinta da gabanta ta tura masa. Ji yayi kamar bai huta da kowacce irin mace ba saboda tsananin sha'awar da ta taso masa. Sake nutsewa ya yi a kujera ya na sake playing videon da take wasa da sassan jikinta ta na wani irin kuka kamar babu kowa a gidansu. (Ina mamakin videos ɗin yara maza da mata da ke yawo na maganganun batsa da nuna tsiraici,wanda da ka gani za ka san a cikin gidan iyaye aka yi su,amma iyayen sam basu san an yi ba. Me yasa kuke warewa matasa ɗaki su kaɗai ba tare da an haɗa su da ƙannen su ba? Idan ta kama dole sai su kaɗai za su kwana me yasa ake basu waya? Na san wani gidan da duk dare sai sun miƙawa mahaifiyarsu wayar su suke tafiya bacci. Ko da da rana ne yarinya bata isa ƙulewa a ɗaki daga ita sai waya ba. Banda addu'o'i da nemawa yaran tsari da iyayen ke yi,sai suka zamo abun kwatance da buga kyakkyawan misali har aka aurar da biyu a cikin su. Ya kamata iyaye su dage su miƙe tsaye su cire son gayu da nuna suma masu kuɗi ne sun siyawa yaran su waya me tsada. Kowanne abu akwai amfani da rashin amfaninsa,idan kun saya musu ku tsaya tsayin daka ku ga me suke yi,kar ku zamo daga cikin iyayen da sai dai ma su ga yaran da waya ba su san wa ya basu ba ballantana har su iya hana su ko su nuna musu yanda za su yi amfani da wayar.) Sosai Abbas ya shagala da kallon videon har ta kai shi ga buɗe nashi jikin yana ɗaukan kansa hotuna yana turawa Nana. A daidai wannan lokacin ne aka ɗauke wuta,Fauziyyah dake bacci ta ji nishi ya yi yawa,nishi kuma irin na mace da namiji. Cikin sauri ta dire ƙafafuwanta ƙasa daga gado ta fara taku cikin sanɗa ta nufi parlourn ta. Abinda ta ga Abbas yana aikatawa ne ya sanya numfashinta ɗaukewa gaba ɗaya,cikin ƙanƙanin lokaci jiri ya ɗebeta ta faɗi ƙasa,a razane Abbas ya juya ya kalli inda Fauziyyah ke kwance kamar matacciya,yana miƙewa nepa suka dawo da wutar,cikin sauri ya hau neman abinda zai goge hannunsa da ya ɓata kace-kace sannan ya yi kan Fauziyyah yana kiran sunanta...... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨ PAGE 13. *SANARWA.* *Masu son su siya kuma ku sanya 500 ta 0006366584 Hamida Sanusi Ahmad Ja'iz bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.* Washegari da asuba suna tashi daga bacci sai Fauziyyah ta sa Barirah ta zuba mata ruwa mai kyau ta yi wanka,saboda ta daina ganin jinin biƙin da take yi. Bayan ta yi sallah da addu'o'i ne ta saka ƙaton hijabi ta isa ƙofar ɗakin Barirah ta durƙusa. Gaishe da Shehu ta yi sannan ta ɗan yi jim kamar mai tunani,shirun da ta yi ne ya sanya Shehu cewa. "Kin shirya yin waya da Yayan naki ne ki yi masa godiya, ko har yanzu baki nemi izinin king ɗin naki ba?" Sadda kanta ƙasa ta yi,a daidai lokacin da ta tuna dargar da Shehu ya yi da ita akan ta gaishe da Abdullah ta yi masa godiyar ɗawainiyar da ya yi da ita da jaririyarta. Cikin sanyin murya ta ce. "Uhumm dama zuwa na yi na ce don Allah Yaya ko za ka kira wo min shi na ji inda yake,saboda jiya bai kwana a gida ba." A matuƙar hasale Shehu ya ce mata. "To shi jariri ne da zan kira na ji inda yake? Fauziyyah ki fa kiyayi zurfafawa a soyayyar Abbas..." "To Hubby in banda abunka zurfafawa ta nawa kuma? Idan za ka kirawo mata shi kawai ka kirawo shi,dan wancan ragon yana buƙatar dusa,gaba ɗaya ya addabi kunnunawa da kuka." "Gaskiya Fauziyyah ki yi haƙuri,ba zan kira shi ba ya faɗa min baƙar magana mu zo mu na bala'i da sanyin safiyar nan. Ai shi ba yaro bane,duk inda ya je zai dawo gida." Jiki a sanyaye Fauziyyah ta miƙe ta nufi ɗakinta,ta na shiga ta fashe da kukan da har su Barirah suna iya jiyo ta. Wani mugun haushinta ne ya kama Barirah,ji tayi kamar ta fita ta bita har ɗakin ta zane ta. Cike da takaici ta ce wa Shehu. "Hubby kira mata shi kafin ta haddasawa kanta ciwon kai,dan ita bata san ciwon kanta ba sam." Ba dan Shehu ya so ba ya sa hannu a aljihu ya lalubo wayarsa,zai kira Abbas din ne kawai saboda umarnin da Barirah ta bashi,shi kuwa yanda take kyautata masa da girmamasa tare da ganin mutuncinsa bai ga abinda zata ce ya yi ba,bai yi mata shi ba,sai dai idan ya saɓa wa Allah,to anan ne za su raba hanya. Shehu ya jima ya na kiran lambar Abbas ta na ta ringing bai ɗaga ba, ƙarshe ma idan ya kira sai ya ji an saka masa User busy. Ƙwafa ya yi ya ce. "Ai dama na san ɗan rainin hankalin nan ba zai amsa kirana ba." Cikin ɗaga murya Barirah ta ce wa Fauziyyah. "To sai ki dena yi wa mutane kuka,tinda an kira ɗan rainin har sau biyar yaƙi ɗaga wayar,karshe ma kashe kiran yake yi,kin ga kenan duk inda yake yana cikin hayyacinsa." Wani sabon tashin hankalin ne ya dirarwa Fauziyyah da ke sauraron Barirah. Cikin zuciyarta take ayyana. 'Kar dai wani mummunan abun ne ya same shi? Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una na shiga uku ni Fauziyyah. To ko gidan Kawu zan je na sanar da su abinda ke faruwa ne?' Kukan Muhseenah ne ya dawo da ita daga duniyar tunanin da ta shiga. Cikin sauri ta nufi inda yarinyar ke kwance ta na ta tsala kuka ta ɗauketa ta hau jijjigawa.  Ƙarshe sai da ta zauna shayar da ita sannan ta samu ta dena kukan. Ragon suna na can ɗaure sai kuka yake tsagawa,tin jiya da aka bashi ragowar abincin suna bai sake ganin abinci ba. Ruwa kawai Barirah ta ajiye masa ta tafi,dan bata da dusar bashi ballantana ta bashi ta huta da kukan da ya cika gidan da shi. Ta ɓangaren Abbas kuwa,da ya farka ya ga Hajiya na ta shan bacci cikin kwanciyar hankali,sai ya miƙe tsaye yana miƙa bakinsa wangale ya na zabga hamma. Yunwa yake ji sosai,dan haka sai ya sanar da nurse cewar zai je gida ya yi wanka ya dawo. Kai tsaye yana fita abun hawa ya hau, ya ce ya kai shi makarantar da yake koyarwa. Ya na zuwa ya tarar da har an fara assembly,yara sun taru kowa yayi fess. Ƴan matan da yake rage zafi da su kuwa kafe shi suka yi da ido kamar su cinye shi. Haka ya dinga ɓata rai ya tsaya a gaban assembly har aka gama kowa ya kama hanyar ajinsa. Kai tsaye office ɗinsa ya nufa ya na sanya hannu a aljihunsa ya na nemo kuɗi. Wani yaro ya kira ya aika ya siyo masa waina da miya,sai ya siyo masa shayi da bread ya kawo masa office. Cikin sauri yaron ya karɓa shi kuma ya shige office ɗinsa. Ya na zaune yana danna wayarsa tare da jera tsaki saboda ganin Lambar Shehu da ya yi cikin jerin mutanen da suka dinga kiransa yana katsewa, Nana ce ta shiga office ɗin ta na wata iriyar tafiya kamar za ta karye saboda yanga. Kai tsaye gaban desk ɗinsa ta tsaya tana wani kwantawa a desk ɗin tana yi masa shagwaɓa. Cikin zazzaƙar muryarta da take ƙara kashewa ta ce. "Haba Malam Abbas me yasa ka ke wulaƙanta ni ne? Ko dan ka ga na mace akan son ka shi yasa kake yi min haka? Na tabbata tin daren jiya ka ga kira na amma ka share ni,ɗazu da safe har video na tura maka ka ƙi hawa online gaba ɗaya,ko na yi maka laifi neee." Ta ƙarasa maganarta da wata iriyar shagwab'ar da ta sanya Abbas janta jikinsa ya hau shafata. Nan da nan suka hau aikata abinda suka saba a duk lokacin da suka haɗu. Nana na daga cikin yaran da Abbas ya fi samun natsuwa da su a kaf ƴan matan da ya buɗewa ido a makarantar. Domin kuwa yarinyar dama a waye ta shigo makarantar,ta san kan yanda ake sarrafa maza,shi yasa ta matsu Abbas ya zarce daga wasanni da yake yi da ita su mori soyayyar su. Sai dai shi kuma Abbas ya na mugun tsoron maimaita abinda ya faru a baya. Shi yasa ya tsaya a iya shafe-shafe da tsotse-tsotse. Sun yi nisa ba sa jin kira,su na gab da cimma burin su yaron da Abbas ya aika ya dawo,buga ƙofar da yayi ne ya sanya Abbas saurin sakin Nana ya koma ya natsu a saman kujera,ita kuma sai ta koma gaban desk ɗin ta na maida numfashi kamar wadda tai gudun tsere. Yaron na shiga ya gansu sun yi wuri-wuri da idanuwa kamar marasa gaskiya. Miƙawa Abbas abincin ya yi sannan ya ce. "Malam Abbas ba a samu shayin ba,shine na siyo maka kayan shayin." Murya a shaƙe Abbas ya ce. "Ok na gode. Je ka aji." Sai da yaron ya sake kallon Nana sannan ya bar office ɗin,ya rufe musu ƙofar kamar yanda ya ganta. Cikin sauri Nana ta nufi Abbas dan ta sake birkita shi,amma ya dakatar da ita. Cike da haɗe fuska Abbas ya ce. "Kinga Nana tafi aji,yunwa nake ji rabona da abinci tin jiya." "To ka bari na baka a baki mana." Ba tare da ya yi mata musu ba ta zauna ta bashi abicin a baki har ya ƙoshi suka koma ruwa,Abbas na gama samun biyan buƙatarsa da ita ya kore ta kamar koda yaushe. Shi mutum ne wanda da ya biya buƙatarsa to abokin mu'amalarsa sai ya san yanda zai yi da kansa. Wannan na daga cikin abinda ke haɗa shi da Fauziyyah,domin ita tana daga cikin mata masu ɗaukan lokaci kafin su kai ga buƙatar su. Shi kuma baya jiranta ballantana ya samar mata mafita. Shi yasa kusan koda yaushe Abbas ke gama bidirinsa ita kuma ya barta da ciwon jiki da na mara. Wani lokacin kuma wulaƙancin da yake yi mata da mugunta ke hana ta samun biyan buƙatarta a kusa. Yana nan zaune yana tinanin yanda zai saci jiki ya gudu gida ba tare da kowa ya kula da yanda ya ɓata jikinsa ba Salman ya zo. Bayan sun gaisa ne ya ce masa. "Yanzu na ga mutuniyar taka ta fita ta na fushi,ko dai faɗa kuka yi ne?" "Humm wanne irin faɗa kuma? Yarinya ce yanda ka san mayya,ita fa wannan ɗan romance ɗin sam baya isarta,so take yi ta jawo min magana. Na kula zan yanke alaƙa da ita tin kafin kwaɓata ta yi min ruwa." "Haba abokina,ya kake yin abu kamar ba ɗan hannu ba? Harkar nan fa mun jima muna buga ta,me ya sa itama ba za ka dinga ɗaukanta kuna barin makarantar nan ba ku keɓe,idan yaso da kun gama sai kowa ya kama gabansa." Shiru Abbas ya yi yana nazari,ya jima bai ce komai ba,kafin ya girgiza kai ya ce. "Kai rabu da ƴan sakandiren nan,idan ina son yin harka da kyau na san inda zani,waɗannan ƙwailayen ƙiris suke jira su nasa ƙwai. Ba zan iya da tone-tone ba. Ka zo da babur ɗinka ne?" "Eh na zo da shi." "Ara min na je gida na dawo,a asibiti na kwana wajen Hajiyata,bata da lafiya." "Subhanallahi, Allah Ya bata lafiya,ga makullin,amma don Allah ka dawo da wuri kafin a tashi,idan kuma ka dawo an tashi kawai ka kai min gida." "Ko kuma ka biyo ni gidan ka karɓ ba." "To shikenan sai na zo." Cike da dabara Abbas ya miƙe zai fita,dariya Salman ya fashe da ita kafin ya ce. "Malam Abbas kana lokaciiii " Haɗe fuska Abbas ya yi ya leƙa waje,bai tarar da kowa ba sai wani matashi a ƙofar office ɗin malamai,cikin ɗaga murya ya ce. "Hey ! Why are you not in your class room? Stand up and go to your class." (Kai ! Me yasa baka cikin ajin ku? Tashi ka tafi ajin ku.) Cikin sauri matashin ya ruga zuwa ajin su yana murna,domin dama laifi yayi ake hukunta shi,sai kuma headmaster ya ce ya tafi aji. Abbas na ganin waje ya yi wayam ya ɗale machine ɗin Salman ya buga ya bar makarantar. Gidansa ya nufa kai tsaye cike da fatan an yi abinci mai rai da lafiya ya sake loda,dan ɗazu da Nana suka ci abincin nan shi yasa sam bai ji ƙoshi ba. Tin daga jin ƙarar machine a ƙofar gidan Fauziyyah ta miƙe da sauri,ta na jin ana ƙoƙarin shiga da shi kuwa ta fito tsakar gidan fuska ɗauke da fatan ta yi tozali da masoyinta. A gefen inda yake ajiye nashi machine ɗin ya ajiye na Salman. Babu sallama ya faɗa gidan kamar koda yaushe. A guje Fauziyyah ta isa gabansa ta rungume shi da ƙarfi. Muryarta na rawa kamar mai shirin fasa ihun kuka ta ce. "My king ina ka shiga tin jiya baka dawo gida ba? Na shiga damuwa da tashin hankali saboda rashin ganin ka, me ya same ka? Daga ina kake?" Ture ta ya yi daga jikinsa da ƙarfi kafin ya nuna ta da yatsa ya ce. "Wai ke me yasa baki da hankali ne dan Allah? Ni ƙaramin yaro ne da zaki saka ni a gaba kina yi min tambayoyin ina naje? Ko kuma aike na kika yi?" "Ah ah wai dama saboda na ga komai dare kana dawowa gida,amma jiya baka dawo ba. Na zaci wani abu ne ma ya same ka." "To ai gani ki gani idan na yi miki kama da wanda wani abu ya same sa. Ina ce ke ce kika yi sanadiyyar da uwata ta kwanta jinya? Ko kuwa har kin manta da hakan?" Jiki a sanyaye Fauziyyah ta janye gefe ta na murza damtsen ta da ya damƙa ya wurga ta gefe,haƙuri ta bashi sannan ta ce. "Ashe wajen Hajiya ka je,to ya jikin nata?" "Da sauƙi." Shine abinda Abbas ya faɗa ya wuce ɗakinsu. Binsa ta yi a baya tana yiwa Hajiya fatan samun sauƙi. Kayansa ya cire ya cukuikuye wandon ya

Chapter 8 of 12