da rashin hankali. Ita kuwa ba za ta so hakan ta faru ba. Gwara ta yi yanda za ta yi ta hana ta zuwa kawai,maganin kar a yi to fa kar a soma.
Har dare ya yi Fauziyyah bata samawa kanta mafita ba,sai kawai ta fawwalawa Allah komai. Fatan ta shine kada Abbas ya yi abinda zai sake nesanta ta da danginta. Washegari Shehu ya bawa Barirah ɗinkakkun atampopi uku shadda ɗaya,sai leshi mai kyau da tsada,ya ce ta bawa Fauziyyah,Yayanta ne ya ce a bata su a ɗinke gudun kada Abbas ya hanata amfani da su ya siyar. Da yammar Barirah ta shiga ta kai mata kayan,sannan ta bata shawarar kar ta sanar da Abbas daga inda kayan suka fito,idan kuma tana ganin babu matsala sai ta sanar da shi. Godiya ta yi mata sosai,sannan ta leƙa ƙofar ɗakin Barirah ta yi wa Shehu godiya. Ta juya baya ta na ta zabga godiya Abbas ya shiga gidan kamar ko da yaushe babu sallama. Hannu ya naɗe a ƙirjinsa ya na kallon ta har ta gama ta miƙe tsaye za ta koma ɗaki. Kallon kallo suka tsaya yi wa junan su. Jiki na rawa Fauziyyah ta shige ɗakinta ta tsaya a tsaye ta na jiran ta ji tijarar da Abbas ɗin zai yi mata idan ya shigo,sai dai ganin da ta yi ya gegare ta ya wuce uwar ɗaka ya barta ba tare da ya ce komai ba ne ya sanya ta shiga damuwa. Da sauri ta bi bayansa,ta na shiga ta tarar da shi ya na ɗaga kayan da aka kawo mata ya na kyaɓe baki,yana gama gani ya wurga su saman gadon sannan ya ce.
"Daɗin abun dai ni ne mijin ki,kuma ni ne uban ƴar ki,dan haka duk wata rawar kai da shisshigi da wani zai yi ba zai sauya hakan ba."
Parlour ya je ya ja abinci ya hau ci ya na kallo,hankalinsa kwance ba tare da ya ji takaicin kansa ba na rashin siyawa matarsa koda adiko ne dan ta ci suna da shi. Ajiyar zuciya mai ƙarfi Fauziyyah ta sauke,godiya ta yi wa Allah da faɗan nasa ya tsaya a iya haka. Cike da farinciki da ɗoki ta hau ɗaga kayan ta na kallo,ƙarshe sai ta cire na jikinta ta na gwadawa. Yanda suka yi mata kyau,suka fito da farar fatarta ne ya burge ta,kallon kanta ta sake yi a madubi ta na tina rayuwarta ta baya,hawaye ne masu zafin gaske suka hau zubo mata. Da sauri ta share su ta cire kayan ta ninke,a zuciyarta ta gama sanin ba zai yanka ragon suna ba,shi yasa ma ko zancen bata taɓa tinkarar sa da shi ba.
Ranar suna mutanen unguwa sun shiga sun taya Barirah aiki. Masa da miyar gyaɗa suka yi,sai kuma shinkafa dafaduka da ta ji naman rago da kayan lambu,har rana ta take Abbas bai kawo ragon suna ba,sai da Hajiyansa ta gaji da jiransa da kuma surutan mutane da ke ta ƙusƙus akan ba a yanka ragon suna ba sannan ta shige uwar ɗakin Fauziyyah da ke zaune ta ci ado suna hira da Auntynta. Gaishe ta suka yi ta kalle su ta ce.
"Kuna nan kun ƙunshe a ɗaki mutane na tsakar gida. Haba ai ba a haka,ku je ku gaisa da mutanen da suka zo taya ku murnar samun ƙaruwa mana."
Aunty Khairi ce ta ɗauki Muhseenah ƴarta Nooratu na biye da ita, suna zuwa parlour mutane suka hau yaba kyawun da Fauziyyah ta yi,ita kuwa murmushi kawai take zubawa ta na jin kanta kamar wata sabuwar halitta,kunya ta dinga ji musamman idan ta ga mutane na kallon ta,ko ana satar ɗaukan ta a hotuna.
Hajiya kuwa Abbas ta kira a waya ta hau zazzaga masa masifa,cike da bada umarni ta ce.
"Ka tabbata ka shigo da ragon suna cikin gidan nan kafin nan kafin la'asar,idan kuma ba haka ba Abbas sai dai ka nemi wata uwar ka ƙarasa rayuwa da ita,amma ba ni ba,shashashan yaro wanda bai san halacci ba."
Zama ta yi a bakin gado ta na maida numfashi,cike da ɓacin rai ta zaro maganinta na hawan jini a jaka ta sha da ruwan da ke cikin gorar ta wanda ba ta rabuwa da shi. Babu jimawa bacci ya fara fisgarta,a ƙasa can gaban gadon ta yada pillow ta kwanta ta hau yin abunta.
A can ɓangaren Abbas kuwa ha'incin da ya so yi ne ya tashi. Domin kuwa so ya yi ya siyo kan rago da ƙafafuwa a gyare,sai ya siyo nama mai yawa ya kawo ya ce ai an gyara tin a can,sai dai wayar da ya yi da Hajiya da umarnin da ta basa ne ya sanya shi siyan wani ƙarmasasshen rago,rai a ɓace ya samu abun hawa ya dawo gidan. Ya na zuwa ya nemi waje ya ɗaure shi ya wuce matan dake zaune suna ta hira ko amsa gaisuwar su bai yi ba. Ganin Auntyn Fauziyyah a kusa da Fauziyyah da Barirah ne ya sanya shi ƙara tsamke fuska tamau. Ba tare da ya gaishe ta ba,ko ya tsaya amsa barkar da take yi masa ba ya wuce ɗakinsa ya na huci. Tsaye ya yi a tsakiyar ɗakin ya na jiran Fauziyyah ta shiga ya sauke mata tijarar da ya ƙunso. Idanuwansa sun rufe bai hango ƙafafuwan Hajiya da ta yada pillow ta gaban madubi ba tana bacci. Fauziyyah na shiga ɗakin ya watsa mata mugun kallo ya ce.
"Me waccan matar take yi min a gida? Dama kun shirya ta zo ta ɗauki hotunan ki ta tafi da su ta nuna wa wannan munafukin ko? To ki je ki sanar da ita ta gaggauta fita ta bar min gida na idan kuma ba haka ba,ni da kaina zan shiga cikin taron munafukan matan da kika tara min a gida na kore ta. In banda baƙin munafurci me ya tara su basu tafi ba har yanzu la'asar ta wuce? Ohh suna jiran a kawo ragon suna kowacce shegiya ta yagi rabonta kan ta tafi ko? To ba zan yanka shi yanzu ba sai bayan magariba. Sannan kar ki sake na fito na ga wannan munafukar a gidana na faɗa miki."
Tinda ya fara magana Fauziyyah ke zubar da ruwan hawaye,shin ta ya za ta je ta ce wa Aunty Khairi ta bar gidan? Sannan maganar ragon suna ita ai ta cire rai ma ba zai siyo ba kamar yanda ya ce a baya. Sannan yanda ta ci nama daga haihuwarta zuwa yanzu ta tabbata ta cire mugun kwaɗayinsa da take fama da shi na shekara da shekaru. Nishin da suka ji a ƙasa ne ya yi mugun tsorata su,sai dai suna dubawa sai suka ga Hajiya na kokawa da numfashinta. A gigice Fauziyyah da Abbas suka yi kanta suna rige-rigen taimaka mata. Ganin yanda idanuwan Hajiya ke ƙafewa ne ya sanya Abbas fita waje da gudu dan nemo abun hawa,ganin shi ya fita a guje da kukan Fauziyyah ne ya jawo hankalin mutane zuwa ɗakin,Aunty Khairi da Barirah na shiga sai suka tarar da Hajiya a sume,cikin sauri Aunty Khairi ta ce.
"Ku kama min ita mu kai ta mota na kaita asibiti."
Babu gardama Barirah ta samo wasu matan suka kama Hajiya suka kai ta motar Khairi suka kwantar,Barirah ce ta shiga gaba bayan sun rufe motar Khairi ta ja suka wuce asibiti. Suna tafiya Abbas ya dawo da ɗan sahu ya na ta yanka zufa. Cike da bala'i da masifa ya kalli matan da sukai carko-carko a cikin gidan suna maida yanda akai ya ce.
"Kai dalla malamai kowa ya wuce ya bar gidan nan gulmar ta isa haka." Dogon tsaki ya ja ya shige ɗaki, yana shiga ya tarar da Fauziyyah idanu sun yi mata jawur,alamar ta ci kuka ta gode Allah. Ta na ganinsa ta miƙe ta nufe shi ta ce.
"Yanzu su Aunty suka wuce da Hajiya asibiti a....."
Marin da ya wanke fuskarta da shi ne ya sanya ta gimtse sauran kalamanta,nan take bakinta ya hau zubar da jini,matan da basu ƙarasa fita bane suka hau faɗin.
"A yi haƙuri Malam Abbas."
A zafafe ya yi kansu kamar zai dake su,suka kuwa kwasa a guje ana rige-rigen barin gidan,banda ashar da fatali da kwanikan da mata suka ci abinci babu abinda Abbas ke yi. Sai da ya tabbatar ya kore su ya koma ɗakin ya na masifa kamar zai haɗiye harshensa ya ce.
"Idan wani abu ya samu Hajiya sai na yi shari'a da kaf zuri'ar ku da ta yi saura. Wanne shegen ne ya ce a ɗaukar min uwa a kai ta asibiti? Ko baki ga na fita samo abun hawa bane?"
"My king gani muka yi kafin ka dawo ta wahala,domin kuwa har ta suma a bayan fitar ka."
"To yanzu wanne asibitin suka tafi?"
"Ban sani ba nima."
Kaiwa da komowa ya fara yi a ɗakin. Sun jima a zaune kowa da abinda yake saƙawa Shehu ya dawo. Abbas na jin shigarsa gidan ya fita waje,a harzuƙe ya ce wa Shehu.
"Maza ka kira matar ka ka tambaye ta ina suka kai min uwata?"
Cikin rashin fahimta Shehu ya kalli Fauziyyah da ta fito tana gyara mayafin kanta,a sanyaye ta yi masa bayanin abinda ya faru,kallon Abbas Shehu ya yi,ji ya yi kamar ya shaƙe matsiyaci ya huce takaicin faɗar masa da gaba da ya yi,ai shi a zaton sa kidnapping ɗin Hajiyar Barirah ta yi,ashe ma taimakon ta suka yi yake wannan iskancin,sai kawai Shehu ya wuce ɗakinsu ba tare da ya ce wa Abbas komai ba. Idan Hajiyar ta ji sauƙi ta dawo lafiya shikenan,idan kuma sa'inta ne ya yi Allah Ya jiƙanta,dama ta gaji da halin ɗan nata. Ganin Shehu zai shige ɗaki ba tare da ya bawa Abbas amsa ba ne ya sanya Abbas ya cewa.
"Ka san Allah Shehu Usmanu idan baka kirawo matarka ta faɗa min inda suka kai min uwata ba sai na yi ƙarar ku gaba ɗayan ku."
"Idan ka tashi ka kai ni barikin ladi a kulle,mahaukacin banza mahaukacin wofi kawai."
Ɗaki Shehu ya shige ya na jin zuciyarsa na tafasa. Ji yake yi da yana da iko da Fauziyyah da ya raba auren ta da Abbas. Domin Abbas bashi da maraba da dabba. Halayensa kaf babu na tsinta. Suna nan zaune Aunty Khairi da Barirah suka yi sallama suka shiga gidan,fuskar su gaba ɗaya ta sauya. Leƙen bayan su Fauziyyah ta hau yi ta na neman Hajiya,sai dai shiru babu ita babu bayanin ta. A kiɗime Fauziyyah da Abbas suka haɗa baki wajen faɗin.
"Ina Hajiyar take?"
Kallon juna Barirah da Khairi suka yi,sannan suka maida kallon su zuwa ga Fauziyyah da ƙafafuwanta ke rawa da Abbas da idanuwansa suka firfito waje. Shehu kuwa jin tambayar da su Abbas suka yi ne ya sanya shi fitowa ya na mayar da botiran rigarsa da ya fara cirewa. Kallon sa ya kai wajen Barirah,nan take ya gano tsananin kiɗima da tashin hankalin da take ciki, cikin sauri ya nufi inda take,tana ganinsa ta fashe da wani irin kuka mara sauti. Nan take Fauziyyah ta zube a ƙafafuwanta jikinta ya ɗauki wata iriyar rawa. Shin me ya samu Hajiya ne? Idan wani abu mummuna ya samu Hajiya ina za ta saka ranta ta ji sanyi?
*Wai shin makaranta wacece Fauziyyah ne?*
*A ina ta haɗu da Abbas har suka ƙulla soyayya suka zamo ma'aurata?*
*Menene ya jawo wannan zazzafar ƙiyayyar da Abbas ke nunawa Fauziyyah?*
*Wanene Abdullah a wajen Fauziyyah?*
*Ina iyayenta suke suka bar Abbas yake gasa ƴarsu kamar balangu?*
*Me zai faru da Barirah da Shehu saboda yawan taimakawa Fauziyyah da suke yi?*
*Shin wacce rayuwa Fauziyyah za ta yi anan gaba ita da king ɗinta da ƴar lelensa Muhseenah?*
*Kuna son ku san ya labarin mugun miji zai ƙare? Ku saka 500 ɗin ku a 0006366584 nan. Sai ku tura shaidar biya ta 09031416423.*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨
PAGE 11.
*SANARWA.*
*Masu son su siya kuma ku sanya 500 ta 0006366584 Hamida Sanusi Ahmad Ja'iz bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.*
"Ki natsu don Allah ki sanar damu abinda ya samu Hajiyan."
Cikin sauri Abbas ya isa gaban Aunty Khairi ya na huci ya ce.
"Me ya samu Hajiyata? Idan wani mummunan abun ya same ta na rantse da...."
A hasale Aunty Khairi ta ce wa Abbas.
"Dakata mara mutunci ! Ai duk abinda ya same ta kai ne sila,tinda ko da ta farfaɗo kafin bakinta ya juye sai da ta roƙi alfarmar kar a sake ka je wajen ta,babu ita babu kai,tinda kai dai ba ɗan goyawa da zani bane. Sannan ina mai yi maka albishir da cewar Hajiyanka ta samu cutar shanyewar ɓarin jiki,tinda dama buri da fatanka kenan a rayuwa,shi yasa ka ƙi ka tausayawa marainiyar Allah ka riƙeta amana ku zauna lafiya. Ke kuma ki wuce ki haɗa kayan ki mu tafi,domin Yayanki ya yi waya ya ce na tasa ki a gaba mu tafi ƙafata ƙafar ki."
Wani irin tashin hankalin da ya fi wanda Fauziyyah ta shiga ne ya ruguzo ya rufta mata,a gigice ta kalli Aunty Khairi dake kumfar baki ta na ciwa Abbas mutunci,shi ma yana masifa ya na faɗin su sanar da shi inda suka kai masa mahaifiyarsa. Gida ya rikice da hayaniya har ba su ji kukan da jaririya ke ta tsalawa ba. Sai da Shehu ya kama Barirah za su wuce ɗaki ne ya jiyo kukan Muhseenah,juyawa ya yi ya sanar da Fauziyyah wadda ke saƙa yanda za ta bijirewa umarnin Yayan nata. Cikin azama ta miƙe jikinta na rawa ta nufi ɗakinta,ta na shiga ta saka sakata ta kulle ƙofar,wajen jaririyarta ta nufa ta ɗauketa. Bugun ƙofar da ta ji ana yi da ƙarfi kamar za a cire ta ne ya sake tada mata da hankali. Rungume jaririyarta ta yi ta fashe da wani sabon kukan. Muryar Aunty Khairi ce ta daki dodon kunnuwanta. Cike da jin takaicin Fauziyyah ta ke faɗin.
"Au yanzu Fauziyyah saboda wannan ɗan wulaƙancin kika shige ɗaki kika saka sakata? Kina nufin kenan ba za ki bini mu koma can Abuja ba ko? To ina mai tabbatar maki da cewar idan har na tafi ba zan sake zuwa inda kike ba,sannan zan sanar da Honey ya cire hannunsa akan ki,sai ki je can ki ƙarata da wannan mara mutuncin. Za ki buɗe ƙofar ki fito mu wuce ko kuwa?"
Cikin kuka Fauziyyah ta ce.
"Dan Allah Auntyna kar ki yi ɗaya daga cikin abubuwan da kika lissafa akaina....ki...ki ji tausayi na...ki tausayawa rayuwata da ta ƴata...don Allah kar ku raba ni da masoyina....ina...ina son Abbas fiye da yanda...nake...son raina...ba zan iya rabuwa da shi ba...don Allah ki faɗawa Yah Abdullah ya ci gaba da yi min addu'a amma kar ya raba ni da gidan aure na. Na amince zan jure duk wani ƙunci da azabar da Abbas zai yi min..amma ba zan iya rabuwa da shi ba."
Wasu irin zafafan hawaye ne suka zubo wa Aunty Khairi. Cike da tsananin tausayin Fauziyyah ta juya ta na kallon Abbas wanda ke tsaye ya na sakin wani shu'umin murmushin nasara. Nuna shi ta yi da yatsanta manuni,muryarta na rawa ta ce.
"Na taya ka murna Abbas ka yi nasara. Ka yi nasarar nakasa zuciya da ruhin Fauziyyah,gashi kana ƙoƙarin nakasa gangar jikinta,domin kuwa na tabbata nan ba da jimawa ba zata rasa wani sashe na jikinta saboda sakarcin son ka da take yi. Ruwanka ne ka ji tsoron Allah ka kyautata mata,ruwanka ne ka ci gaba da zaluntar ta yanda ka saba. Amma ina so ka sani,shi Allah baya bacci,kuma baya barin azzalumai a doron ƙasa ba tare da ya hukunta su ba,duk daren daɗewa za ka girbi abinda ka shuka."
Hannun Nooratu ta kama tana share hawayenta za su bar gidan. Cike da isgilanci da wulaƙanci Abbas ya ce.
"Sai ki koma ki sanar da munafukin mijinki da ya aiko ki ki kashe min aure,saboda shi ya aure min mata,haƙonsa ba zai taɓa cimma ruwa ba. Sannan ko mutuwa na yi Fauziyyah ta haramta a gare shi,kamar yanda naman jaki yake haramun a bakin dikkan musulmi na gari."
Murmushin takaici Aunty Khairi ta sakar masa sannan ta ce.
"To alhamdu Lillahi tinda dai ka danganta lamarin da musulunci,ina so ka sani idan lalura ta kama mumini an halatta masa cin naman jakin. Ballantana ma da izinin Allah sai ka rabu da Fauziyyah itama ta samu inda za ta huta ta manta da takaicin ka. Shashashan namiji kawai."
Jan hannun ƴarta ta yi suka bar gidan tin kafin ta kai wa Abbas mari,domin a yanda take jin zuciyarta na tafasa,ko daki in doka tana iya yi da shi. Ta jima zaune a mota ta na risgar kukan baƙin cikin halin da Fauziyyah ke ciki kafin ta ja motarta ta wuce gidan su da ke cikin garin Kanon.
Abbas kuwa ƙofar ɗakin Barirah ya je ya tsaya ya ci gaba da yi musu rashin mutunci yana faɗin su fito masa da mahaifiyarsa ko ya yi ƙarar su. Babu wanda ya kula shi a cikin su,haka ya karaci masifarsa da zage-zagen sa babu wanda ya kula shi. Fauziyyah kuwa da ta tabbatar da tafiyar Aunty Khairi sai ta lallaɓa ta buɗe ƙofar ta fita tsakar gidan riƙe da yarinyar su. Cikin sanyin murya ta ce wa Abbas da ke ta safa da marwa a tsakar gidan.
"My king ko za ka gwada kiran Kawu? Wataƙila ya san inda take tinda ba zai yu su kaita asibiti su barta ita kaɗai ba tare da wani ba."
Kamar wanda ta bugawa sandar tina abu a kai,cikin hanzari ya zaro wayarsa daga aljihu ya kirawo kawunsa. Daga jin muryar kawun nasa jikinsa ya sake ɗaukan rawa. Murya a sarƙe ya ce.
"Kawu Hajiya na wajen ka ne?"
Daga can ɓangaren Kawunsa ya ce.
'Idan tana wajen nawa sai me? Ko an faɗa maka muna son ganin ka ne? Wato Abashe ka dage sai ka kashe min ƴar'uwa da baƙin cikin ka ko? To ka tsaya ka saurare ni da kyau ka ji,idan wani abu ya sameta sai na yi shari'a da kai. Shashashan yaro kawai.'
Kashe wayar Kawu ya yi,jiki a mace Abbas ya ce.
"Na ji hayaniya a inda Kawu yake,sannan na ji wata na kiran likita,duk yanda akai ta na asibitin da ta saba kwanciya,bari na je na dubo jikin nata."
Da sauri Fauziyyah ta ce.
"Don Allah mu je tare,ina son ganin Hajiya nima."
"To Hajiyan kallo-kallo ce da za ki je ganinta da ɗanyen jego? Dalla malama ki koma ciki,duk ba ke ce kika jawo min wannan masifa da bala'in da nake ciki ba."
Jiki babu ƙwari Fauziyyah ta koma gefe,Abbas kuwa sai ya ja machine ɗinsa ya bar gidan. Ya na fita Barirah ta fito tsakar gida da gudu ta na kelaya amai. Ta jima ta na yinsa kafin Shehu ya taimaka mata ta wanke bakinta. Fauziyyah da ta fito ta na ta jera mata sannu na tsaye riƙe da ruwan sha mai sanyi. Miƙawa Barirah ta yi ta ce.
"Sannu Aunty,ina ga har da stress ke damun ki fa,Allah Ya baki lafiya."
Kallon Fauziyyah ta yi da wani irin yanayi mara fassara,domin kuwa ita kanta ta rasa me take ji akan yarinyar,shin tausayinta za ta ji ko haushinta? Ko kuma rufe ta da duka za ta yi ko abinda ya danƙare mata a makoshi zai wuce? Ruwan sanyin ta kurɓa ta na zaune a kujerar robar ƙofar ɗakinta. Wani irin sanyi me daɗi ne ya ratsa ta. Shehu kuwa hijabinta ya miƙa mata sannan ya ce.
"Tashi maza mu je wajen Sammani me kemis ya duba min ke,idan kuma ba haka ba mu wuce asibiti kawai."
Babu musu Barirah ta saka hijabi suka hau machine suka bar gidan. Fauziyyah na nan zaune a tsakar gidan aka fara kiran sallar magariba. Ciki ta shige ta dafa kan Muhseenah ta karanta mata.
"U'idhuki bi kalimaatillahittammat,min kulli shaiɗanin wa hammah,wa min kulli ainin lammah."
(Idan yaron ki namiji ne sai ki ce,U'idhuka.... Idan kuma yaran ki da yawa ne sai ki ce. U'idhukum....)
Ta na gamawa ta juye ruwan ƙaton flask ta yi mata wanka kamar yanda ta ga ana yi,sai ta shiryata da kayan da Hajiyan Abbas ta kawo mata. Abincinta ta bata ta lallaɓa ta ta yi bacci. Zama ta yi a gefen gado ta na ta tasbihi ga Allah,tinda ba sallah take yi ba jini bai ɗauke mata ba. Sai bayan magariba su Barirah suka dawo gidan, hannun Shehu riƙe da ledar magunguna da fruits guda biyu. Ɗaki suka shige, suka zauna Shehu ya bawa Barirah ayaba ta ci ta ƙoshi,sannan ya bata magungunan da suka dawo da su ta sha da ruwa. A wajen ta kwanta ta na maida numfashi. Shehu na fita sallah Fauziyyah ta shiga duba Barirah. Cikin murya irin ta marasa lafiya Barirah ta ce.
"An gwada ni an ce malaria ke damuna."
"Allah Ya baki lafiya Aunty,sannu kin ji? Ina ga har da aikin da kika sha ya motso ta."
"Da alama kam. Ga wannan ledar naki ne,idan za ki tafi ki je da shi."
"To Aunty baku gajiya da hidima da ni,Allah Ya saka muku da alkhairi."
"Amin Ya Allah."
"Uhumm ni kam Aunty na ce to a wanne asibitin Hajiya take?"
Gyara zama Barirah ta yi idanuwanta na kawo ruwa ta ce.
"Jikin Hajiyan Abbas ya tina min da mahaifiyata,itama hawan jini ne sanadinta. Sai dai ita tin a haihuwar autarmu da bata zo da rai ba ta same shi,amma ba sanadiyyar ɓacin rai ba. Abbas na cikin masifa da bala'i Fauziyyah,domin kuwa kalaman Hajiyansa akansa sun fi kama da wanda aka tsinewa albarka. Me yasa baki bi Auntyn ki kun wuce ba da ta buƙaci ki yi hakan? Me yasa kike son nima sai kin saka min hawan jini Fauziyyah? Ba ki tausayawa kan ki ne wai? Kin rasa iyayenki kin ci gaba da rayuwa,sai ɗa namijin da bai san darajar ki bane ba za ki iya rabuwa da shi ba?"
Murmushin takaici Fauziyyah ta yi. Zazzafan hawayen da ya gangaro mata a idonta na dama ta share kafin ta ce.
"Aunty ban san da wanne irin yare zan yi miki bayanin yanda nake son Abbas ba. Hakan ne ya tabbatar min da cewa soyayya ba yare bane,ba kuma ta da rai,domin da tana da rai da tawa ta mace daboda halin ƙuncin da take ciki. Aunty don Allah ku ci gaba da taya ni da addu'a,ita nake buƙata,ba ƙoƙarin raba ni da farincikina ba."
Wani mugun kallo Barirah ta sakar mata wanda ya sanya ta saurin sadda kanta ƙasa. A sheƙe Barirah ta ce mata.
"Farinciki? Wanene farincikin naki? Ke a haka kike samun naki farincikin kullum kina cikin kyara,hantara,masifa da bala'i tare da musgunawar abokin rayuwa? Lallai to ni ina nema maki tsarin Allah da wannan wahalallen farincikin da kike samu. Kin ga Fauziyyah bani da lafiya,tashi ki tafi ɗakin ki ki huta kema."
Babu musu Fauziyyah ta miƙe hannunta ɗauke da ledar fruits ɗin da Barirah ta bata zata fita. Har ta kai bakin ƙofa Barirah ta ce mata.
"Ranar asabar mai zuwa za mu koma sabon gidan mu da Shehu ke ginawa tin da jimawa. Na san kin san cewa yana gini dan na sanar da ke komai."
Ledar hannun Fauziyyah ce ta suɓuce ta faɗi ƙasa kayan cikinta suka zube,cike da tashin hankali take bin fuskar Barirah da kallo. Kasa furta komai ta yi sai ta ruga da gudu ta bar ɗakin tana risgar kuka kamar wadda ake yagar naman jikinta da ƙarfe.
Barirah ma kuka ta sanya,saboda ta shaƙu da Fauziyyah ƙwarai da gaske. Lokacin da suka shiga ɗaki da Shehu tana bashi labarin abubuwan da suka faru a ranar ne takaici ya lulluɓe shi. Nan take ya sanar da ita ko basu gama kwashe kayan su dika ba tinda an gama gini har ya zuba kaya a sabon gidan jerawa ne kawai ba su yi ba,to za su tashi ranar asabar. Ya gaji da rikicin dake tsakanin Fauziyyah da Abbas ɗin nata,gashi ta sanadin su farincikin nashi iyalin ya yi ƙaura, kullum sai Barirah ta zubar da hawayenta akan macen da bata son a raba ta da MUGUN MIJI irin Abbas.
Abbas bai dawo gida ba sai ƙarfe sha ɗaya na dare. Jiki na rawa Fauziyyah ta kawo masa abinci ya ci ya ƙoshi,jin bai ce mata komai ba game da jikin Hajiya ne ya sa ta tambaye shi cike da ladabi. Ko kallon inda take bai yi ba ya miƙe tare da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 12