sannan ta yi shafa'i da wutiri ta yi addu'a sosai. Sai ta sauyawa Muhseenah kaya ta saka mata pampas ta ɗauketa ta kulle ɗakinta ta nufi ɗakin Abbas. Abincinsa da ta kai masa ta kalla ta ga ta ajiye komai yanda ya dace,sai ta kutsa kanta cikin ɗakin da ya hana ta shiga ko da da leƙene. Wannan ne karon farko da ta shiga har uwar ɗakin tin bayan da ta haɗa masa shi. Shi yake gyara abinsa ya fito da sharar ƙofar ɗaki ita kuma ta kwashe. Akan disk ɗin da ke ɗauke da tsiraicin maza da mata idanuwanta suka sauka. Cike da takaici da baƙin ciki ta kwashe su ta zuba masa a drower. Tana nan tsaye tana dube-dube ta hango wandunansa da ya tara gajeru wanda ya ɓata su da abinda ya fitar daga jikinsa. Hawayene suka zubo mata ta kwantar da Muhseenah a gado ta kwashe su. Waje ta kai ta jiƙa a bokiti sannan ta koma ɗakin ta kwanta a gado tana tina rayuwar su ta baya.
*Tina baya.*...........
*Don Allah ku yi min alfarma ku bari na kammala labarin nan kafin ku fitar da shi,idan ƙawayen ku ke so ku turo min su su saya. Idan kuka min haka zan ji daɗi kuma zan gode muku. Amma idan kun ga za ku fitar babu komai ƙofa a buɗe take, haƙƙin ku ne. Allah Ya bamu rabon alkhairi.*
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨
PAGE 18.
*SANARWA.*
*Masu son su siya kuma ku sanya 500 ta 0006366584 Hamida Sanusi Ahmad Ja'iz Bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.*
Kasancewar Abbas Malami ne shi da ya san makamar aikinsa,sai sunan sa ya watsu a ciki da wajen makarantar gwamnatin da yake aiki a cikinta. Jajircewarsa da yanda ya sa yara suka fara iya yin magana da turanci ne ya sa har principal ɗin makarantar ke jansa a jiki kamar ɗansa. Ganin haka ne ya sa Abbas sauya taku,sai ya dena tinkarar yaran mutane da muguwar soyayyarsa da ke ɓata musu rayuwa. Duk wadda kuwa ta yi kuskuren kawo kanta ta nuna tana son sa sai ya ja mata aji sosai,ta yanda za ta matsu da kanta ta bi shi duk inda ya kwatanta mata. Yara da dama sun lalace ta sanadiyyarsa, ta yanda wasu iyayensu na gane halin da suke ciki sai su sanar da shi akwai matsala. Daga nan su roƙe shi akan ya aure su, shi kuwa sai ya ƙi ya sanar da su cewa shi fa babu lissafin aure a rayuwarsa ta yanzu,sai dai be sani ba ko a gaba idan ya samu wadda ta dace da tsarinsa. Ana haka har tsautsayi ya faɗa akan wata yarinya ta samu juna biyun Abbas, wanda har Hajiyansa sai da ta sani ta hanyar wayar da ya yi da yarinyar a cikin gida. Haka ta yanke jiki ta faɗi aka kaita asibiti,ta sha jinya sosai kafin ta ware ta dawo daidai. Bayan an kwana biyu Abbas bai yi kasa a guiwa ba ya haɗa yarinyar da Babson suka je aka cire cikin,a cikin sirri ba tare da iyayenta sun sani ba. A tsarin Abbas kuwa duk wadda ta yi ciki koda ba shi ne ya yi mata ba baya sake waiwayarta,shi yasa ma ya fi son ƴan shilan da babu wanda ya taɓa mu'amala da su. Haka zalika idan ya gaji da yarinya zai kirata ne kai tsaye ya yanka mata warning ya ce zai tona mata asiri tinda ita ta maƙale masa take neman lalata masa sunan da ya sha wahala wajen ginawa,daga nan yaran suke tsorata gudun tonuwar asirinsu su ƙyale shi ba dan sun so ba.
A ɓangaren soyayyarsa da Fauziyyah kuwa ya na nan yana ƙara hurawa mata wutar soyayyarsa a cikin ranta. Lokacin da ta shiga SS 1 shi yake ɗaukan su English,haka zai fito da ita gaban aji ya na bata littafin Romeo da Juliet ta dinga karantawa a gaban aji,ko kuma ya bata wani littafin da ya ƙunshi soyayya ya ce ta karanta wa ƴan aji. Idan Fauziyyah tana karantawa ji take yi kamar ita ce ke zubawa Abbas kalaman ƙaunar dake jikin littafin. Shi yasa ta dena jin nauyi da kunyar tsayawa ta karanto littafin soyayya ko da kuwa akwai wuraren da basu dace ɗalibai su saurara ba. Haka Abbas zai zauna sanye da baƙin gilashi yana ƙare mata kallo ya na jin wani irin shauƙin kasancewa da ita na ɗibarsa. Wata rana da rana an tashi,wanda ya yi daidai da ƙarewar period ɗin Malam Abbas. Sai da ya bari kowa ya fita ya kirawo Fauziyyah. Tsayawa ta yi ita da Fatima suna jiran su ji dalilin kiran Fauziyyah da ya yi. Sai dai Abbas bai tanka su ba sai ma haɗa jakarsa da ya yi ya hau ƙoƙarin barin ajin fuska a haɗe. Ganin yanayinsa ne ya sanya Fauziyyah isa gabansa da sauri ta durƙusa ta ce.
'Malam Abbas gani,ko ka manta ka ce na tsaya?'
'Eh ina sane da na ce ki tsaya,gani na yi rashin yarda da ni ya sa har kin tsayar da ƙawarki kamar wadda zan yi wa wani abu. Ko kin taɓa samun labarin na yi wani mummunan abun ne a makarantar nan da wajenta?'
Cike da damuwa Fauziyyah ta kalli Fatima da ke tsaye ta na aikawa ƙeyar Abbas harara. A hasale ta bar ajin ta kama hanyar gida. Ganin haka ne ya sanya Abbas miƙawa Fauziyyah hannu akan ta miƙe tsaye. Yatsunsa ta kalla ta na jin nauyin miƙa nata hannun. A zuciyarta kuwa yaba kyawun yatsun nasa take yi,ga wani zobe mai kyau na azurfa ya saka. Agogonsa da ke ƙyalli ta kalla ta ga lokaci ya tafi,cikin sauri ta dafa desk ta miƙe tsaye ta na karkaɗe guiwarta. Hannunsa ya yarfe sannan ya ce.
'Na gode da shanya min hannuna da kika yi. Na kula tsorona kike ji Fauzy. Ko kina ganin kamar zan cutar dake ne? Kin taɓa ganin inda ruhi ya cutar da gangar jiki?.'
Da sauri Fauziyya ta kalle shi,cike da mamaki ta ce.
'Malam Abbas me kake nufi da kalaman ka? Don Allah kada ka yaudari kunnuwana,idan ka yi haka za ka fasa jaririyar zuciyar da ta kamu da zazzafar soyayyar da bata san yanda za ta yi da ranta ba.'
Matsawa Abbas ya yi gaban Fauziyyah yana jin kamar ya jata jikinsa ya rungume,ko zai samu sauƙin abinda yake ji game da ita,a hankali numfashinsa yake sauka a saman fuskarta,cikin muryar da ya tabbatar da zata kashe mata jiki ya ce.
'Kina nufin kema kina jin abinda nake ji akan ki? Me yasa baki taɓa bani alama ba?'
Jiki a mace ta ɗan ja baya,cike da kasala ta ce.
'Malam Abbas ina jin abinda kake ji akaina,sai dai dole ne na jure na barwa zuciyata,saboda na san ba zan taɓa samun abinda nake so ba.'
'Me yasa zaki yanke hukunci bayan baki gwada ba?'
'Malam Abbas ka fi ƙarfina,ka kalle ka fa.'
Haɓarta ya ɗaga ya sauke idanuwansa masu rikitata a saman fuskarta da ta fara zubar da zufa, idanuwanta masu tsananin kyau ta zuba masa itama. Nan take zuƙatansu suka tsananta bugawa. Numfashin bakin Abbas dake dukan fuskar Fauziyyah ne ya sanya mata kasala mai tsanani,yana ganin ta shiga wannan yanayin sai ya sakar mata murmushin da ya sa jikinta fara ɗaukan rawa. Da sauri ta ƙwace fuskarta ta ɗauki jakarta ta fita da gudu daga cikin ajin. Waje ya samu ya zauna ya na maida numfashi da sauri da sauri. Lallai wannan karon ya tabbata bai je wajen da ya saba zuwa ba. Fauziyyah bata daga cikin matan da ya saba mu'amala da su. Domin kuwa abinda ya yi mata a yanzu babu yarinya ko babbar macen da ya taɓa yiwa hakan ba tare da ta maƙale masa ba kamar ta cinye sa. To ya zai ya shawo kan wannan ƴar shilar dake ta tsinka masa yawu? A haka ya tafi gidan Babson saboda ya samu wadda za ta ɗebe masa kewar abinda bai samu ba a wajen Fauziyyah. Sai dai ranar sai da ya sauya mata har huɗu bai gane komai ba. Zuciya da ruhinsa Fauziyyah kawai suke so. Ita ce wadda yake muradin ta kashe masa wutar dake ci a cikin zuciyarsa. Haka ya kai dare babu biyan buƙata ya wuce gida. Hajiya ya tarar zaune ta na ta addu'a tana kuka. Jiki a mace ya shige ɗakinsa ya hau cin abinci kamar wanda ya shekara bai ci komai ba. Washegari da safe da ya gaishe ta sai ya ji ta amsa masa fuska sake kamar babu abinda ya faru. Shi ɗin ma sai ya saki jikinsa ya taya ta ayyukan cikin gida ya wanke machine ɗinsa ya shirya dan tafiya makaranta. Sai da ya hau machine zai tafi ne Hajiya ta ce masa.
' Abbas ka ji tsoron Allah a duk abinda kake yi, bana jin daɗin labaran da nake samu akan ka,da an tashi daga wajen aiki ka dawo gida kai tsaye kar ka biyewa wannan shashashun abokan naka. Ka riƙe maraicin ka Abbas ko Allah Ya yi wa mahaifinka rahama a cikin ƙasa.'
Jiki a mace ya bawa Hajiya haƙuri akan laifin da ya aikata tare da alƙawarin zai dawo gida da wuri a wannan ranar ya buga machine ɗinsa ya tafi makaranta. Yau ma kamar kullum ya shiga ana assembly,wanda yana sane yake yin hakan,domin yana jin daɗin yanda mata ke zuba masa ido suna kallon sa. Yana kafe machine ɗinsa ya hau wara ido yana neman inda zai hango Fauziyyah,sai dai haka ya gaji da nemanta a cikin dandazon yara bai sata a idonsa ba. Wunin ranar haka ya gama aikinsa ba tare da ya saki jiki ya yi walwala kamar yanda ya saba ba. Daga ƙarshe dai ya gaji ya karya billensa bayan an tashi daga makaranta ya tambayi Fatima inda Fauziyyah take. Cike da yanga da yauƙi ta ce masa.
'Malam Abbas kenan,ina ce jiya korata ka yi saboda kana so ka gana da Fauziyyah? To kamar yanda ka kore ni ban tsaya ba kai tsaye na wuce gidanmu,yau kuma da safe na taho makaranta. Ka ga kenan ban da hanyar sanin inda Fauziyyah ta ke. Sai dai....'
Cikin zaƙuwa tare da shanye ɓacin ran da Fatima ta fara dasa masa ya ce.
'Sai dai me?'
A hankali ta taka kusa da shi ta riƙe hannunsa ta ce.
'Sai dai idan nima za ka yi min irin na su Fadila,babu abinda zai hana na shigar da soyayyarka wajen Fauziyyah.'
Wani mugun kallo ya watsawa Fatima,domin sam bata daga cikin irin matan da yake so, amma dake ɗan duniya ne,yana son ya ji wasu daga halayen Fauziyyah a bakinta,sai ya murza hannunta ya kashe mata ido ɗaya ya ce.
'Ina son wayayyun mata,ashe kema ƴar yi ce ban sani ba nake ta ture ki? To yanzu ya za a yi? Ta ina zamu fara,taki buƙatar za a fara kawar wa ko tawa?'
Murmushi sosai Fatima ta yi,har sai da haƙoranta farare tas suka bayyana a fili. Zama ta yi a gefensa ta ce.
'Kamar yanda na sanar da kai,Fauziyyah ba ƴar harka bace,sannan ta tsani duk wani namiji da zai zo mata da sigar iskanci,dan haka ina mai baka shawara da ka neme ta da aure kawai,idan ta amince kafin auren ka samu abinda kake so shikenan,sai ka ci moriyar ganga ka yada kaurenta,idan kuma bata yarda ba,kana iya aurenta,daga baya da ka samu abinda kake so ka sake ta. Dabara ta rage wa mai shiga rijiya. Ni kuma tawa biyan buƙatar ina jiranka a wannan address ɗin daga nan zuwa ƙarfe huɗu. Sai anjima.'
Tsananin mamakin halayyar yarinyar da ba za ta wuce shekara sha shida zuwa sha bakwai bane ya daskarar da Abbas a inda yake tsaye. Tinda yake lamuransa bai taɓa tunanin yaudarar wata da zummar zai aureta ya fasa ba. Kaf yaran da ke bashi kansu ko ya neme su sun san babu maganar aure a tsakaninsu,sai gashi yarinya ƙarama na bashi shawarar yanda zai yi dan ya samu biyan bukatarsa.
Ɗaukan takardar da ta ajiye masa ya yi ya ga adireshin da ta bayar,murmushi ya yi sannan ya ninke takardar ya saka a aljihunsa ya bar ajin,domin kuwa ba zai karya alƙawarin da ya ɗaukar wa Hajiya ba akan yarinyar da bata yi masa ba. Ko zai je gare ta sai ya ɗan bada ƙafa hankalin Hajiya ya kwanta.
A ɓangaren Fauziyya kuwa,tinda ta koma gida ta kasa moruwa. Da ta tina kusancin da suka samu da Abbas sai ta fashe da kuka,tinaninta ya gama bata ta zama ƴar iska tinda har ta ji wani abu da bai dace ba akan ɗa namijin da babu aure a tsakaninsu. Wunin ranar da kuka ta ƙarasa shi. Ummi ta yi tambayar duniya har ta gaji ta ƙyale ta. Haka Abbanta ma da ya dawo da dare sai da ya tasa ta a gaba amma ta kasa faɗa musu komai. To ta yaya za ta fara sanar da su itama ta iskance kamar yanda yarinyar maƙotansu ta zama ƴar iska? Kullum faɗa da nasihan Ummi baya wuce na yanda za ta kare mutuncinta har sai bayan ta yi aure. Sai kawai ta watsa musu kasa a ido da wannan mummunan labarin? Da kanta ta ke sanar da zuciyarta dole ne ta haƙura da Malam Abbas,gudun kar ta kai su ga aikata haramun. Wannan dalilin ne ya sanya ta tashi da zazzaɓi mai zafi da safe. Har sai da aka kaita allura Abbah ya siya mata magunguna. Washegari da safe ta tashi jikinta da ƙwari amma sai ta ce ita ba ta jin ƙarfin jikinta babu inda za ta je. Ummi bata matsa mata ba saboda tana buƙatar ta a gidan, kasancewar Abdullah ya yi waya ya sanar da su zai zo ganin gida a wannan shekarar. Murnar da Fauziyyah ta hau yi ce ta tona mata asiri wajen Ummi,sai kawai ta yi murmushi ta ƙyale ta suka hau aikin girkin tarbon babban baƙon nasu.
Da yamma sakaliya suka kammala komai har da wanka da kwalliya sun yi tinda sai ya fara zuwa gidan iyayensa kafin ya zo wajensu. Sai kawai suka zauna suna ta hira Ummi na tina wa Fauziyyah rashin jin da ta dinga yi lokacin tana ƙarama,Abdullah na bin bayanta tare da kare mata faɗa. Suna tsaka da dariya suka ji ƙarar mota ta tsaya a ƙofar gidan nasu. Da sauri Fauziyyah ta zari hijabinta ta saka ta fita da gudu ƙofar gida ta na murna. Ido huɗu suka yi da Abdullah wanda ya fito a wata baƙar mota mai kyau,sanye da farar shadda ƙal tana ɗaukan ido. Murmushi suka sakarwa junansu wanda ya bayyana tsantsar kamannin da ke tsakaninsu. Fitowar Mama Sumayyah mahaifiyar Abdullah a mota ne ya sanya Fauziyyah saurin zuwa ta rungumeta ta na ihun murna.
'Mama wannan motar Yayahna ce ko?'
Fauziyyah ta faɗa ta na ci gaba da tsallenta. Cikin tsananin farinciki Mama ta ce.
'Motar yayanki ce Fauziyyah,tin azahar ya iso ai ya tsaya muka taɓa hira sannan ya zaga dani na ɗana,daga nan na ce ya kawo ni nan na koma gida da ƙafa,dan na san yanzu lokacin ki ne,ba zai sake bi ta kaina ba.'
Cike da dariya da jin kunya Fauziyyah ta sunne kai a jikin Mama tana faɗin.
'Kai Mamaaa.'
A tare suka shiga gidan da Mama,Abdullah kuwa sai ya tsaya yana bin duk wani taku na Fauziyyah da kallo cike da burgewa. A hankali ya furta.
'Shikenan Abdullah ƙorafin Baba da Abbah ya ƙare akan ka ,yau dai ka samu matar aure.'
Murmushi ya yi ya kulle motar ya bi bayan su cikin gidan........
[20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI.
RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEEBRAERH ✍️✨
PAGE 17.
*SANARWA.*
*Masu son su siya kuma ku sanya 500 ta 0006366584 Hamida Sanusi Ahmad Ja'iz Bank,ku tura shaidar biya a 09031416423. Ina fatan za ku yafe min idan har Allah bai bani ikon kammala labarin MUGUN MIJI ba lokaci na ya yi. Allah Ya sa mu amfana da abinda ke cikin wannan labari na alkhairi.*
Zuri'ar Malam Aliyu Mai almajirai, zuri'a ce babba a cikin garin Kano,wadda ta tara manyan malamai da ƴan kasuwa. Mahaifin Fauziyyah da Abdullah sun fito cikin wannan kyakkyawar zuri'ar mai nagarta da sanin ya kamata. Mahaifin Fauziyyah Aliyu ya ci sunan kakansu ta ɓangaren Uba wato Aliyu Mai almajirai. Inda Yayansa Ilyas kuma ya ci sunan Kakansu ta ɓangaren Uwa. Mutanen nan biyu sun taso da tsananin so da ƙaunar junan su tare da yin riƙo da zumunci yanda ya kamata a tsakaninsu. Ilyas da yake babba shi ne yake fita kudu ya saro kayayyakin da mu hausawa muke da buƙata wanda ya danganci abinci,irin su garin kwaki,manja,agushi da sauran su. Shi kuma mahaifin Fauziyyah yana zaune a babban shagon su da sauran ƴan'uwansu suna siyarwa tare da kula da dukiyarsu. A haka har Ilyasu ya haɗu da Sumayyah suka ƙulla soyayya mai tsafta,iyaye suka shiga maganarsu aka ɗaura musu aure. A cikin shekara ɗaya da yin auren su Sumayyah ta haifi Abdullah tin daga kansa bata sake ko da ɓatan wata ba,haka suka ci gaba da bashi kulawa da soyayya kamar su mayar da shi ciki. Abdullah ya taso abun so ga kowa kasancewarsa yaro mai ladabi da biyayya,ga uwa uba riƙo da addini,domin tin yana ƙaraminsa yake bawa mutane mamaki da dariya. Lokacin sallah na yi zai tada mahaifiyarsa ya kafe sai ta yi sallah,idan kuma lalurar mata ta sa ba zata yi sallah ba sai ya yi ta kuka shi fa dole sai ta yi sallah. Haka zai je ya jiƙe jikinsa da sunan alwala ya dawo ya ce sai sun yi sallah, tare,da wannan take yi masa dabara ta saka hijabi ta tasa shi a gaba ta ce shi ne liman,ita kuma sai ta yi zamanta,inda sallar tasa ta tiƙe itama sai ta zauna ta ce ta idar. Lokacin da Aliyu ya auri ƴar ƙanin babansa Zuhairah kuwa sai Abdullah ya tare a gidan,domin gidajen ƴan'uwan basu da wata tazara mai yawa a tsakaninsu. Zahairah na matuƙar ƙaunar Abdullah,ko bai zo ba ita za ta saka hijabinta ta leƙa ta kira shi su koma gidanta tare. Shaƙuwa ce mai ƙarfin gaske ta shiga tsakanin su ta yanda har ta kai Sumayyah ta saddaƙar da soyayyar da Abdullah ke yi wa Zahairah mai ƙarfi ce ba za ta iya raba tsakanin su ba,shi yasa duk sanda suka yi faɗa ya gudo ya dawo har ya ce ba zai koma ba,sai ta ce.
'Humm ni dai yanzu babu abinda zan iya furtawa a wannan lamari naku,domin duk abinda nace da kun shirya za ka kwashe ka sanar da Babarka,dan haka kun fi kusa,idan kun shirya ka koma.'
Shi kuwa Abdullah sai ya dage akan ba zai sake komawa gidan ba,Babar shi ta yi masa faɗa har ta dungure masa kai. A haka Abdullah ya girma sosai aka sanya shi a makarantar boko da kuma ta allo. Ya na da shekaru goma sha biyu a duniya Zahairah ta haifi ƴarta kyakkyawar gaske mai kama da iyayenta,ranar suna na zagayowa aka sanya mata suna Fauziyyah. Tin daga wannan rana Abdullah ya kwaso kayansa gaba ɗaya daga gidansu ya koma gidan Baba Ali da zama. Idan Zahairah na so ta huta sai ta goyawa Abdullah Fauziyyah ta kwanta ta sha baccinta,a inda ta zaunar da shi ta kwanta,a wajen take tashi ta tarar da shi. Tin Baba Ali na yin faɗa akan yawan goyon da take bawa Abdullah har ya haƙura ya dena.
Har Fauziyyah ta girma ta fara takawa Abdullah bai dena kula da dikkan lamuranta ba,shine mutum na farko da ya fara bata abinci,sannan shi ne ya fara kama hannunta ta taka a duniya,Abdullah ne ke kula da yi mata wanki,domin idan ya je makaranta ya dawo ya ga Zuhairah ta yi wa Fauziyyah wanki,to fa ranar haka zai wuni ƙunci,banda sharar hawaye da shessheƙar kuka babu abinda zai wuni yi ta yi. Tin daga wannan ranar ta ɗaukewa kanta wankin kayan Fauziyyah. Wanka da tsarki ma dan ta dage ba zai yi mata bane,saboda bai dace ba ko uwa ɗaya uba ɗaya yara suke a dinga barin yaro namiji yana yiwa yarinya tsarki da wanka,tin daga wannan stage ɗin tarbiyya ke samun matsala,ke kuma uwa za ki dinga ganin ai ba komai bane,ba tare da kin san kin gama gurɓatawa tare da lalata tarbiyyar ɗanki ba.
Bayan shekara biyar,Fauziyyah ta shiga nazire. Abdullah kuma ya tafi makarantar gaba da primary yana JSS 1. Kullum Abdullah ne ke kama hannunta ya kaita makaranta ya ajiye ta, da lokacin tashi ya yi yake roƙon malamansu a bashi dama ya ɗauketa ya mayar da ita,ya na kaita gida ko ruwa baya tsayawa sha yake komawa makaranta,da an tashi ya ke komawa gidan iyayensa ya gaishe su,ya taya mahaifiyarsa duk abinda take da buƙata,daga nan kuma idan dare ya yi sai ya wuce gidan Baba Ali ya kwana.
Bayan tsawon shekaru,sai Sumayyah ta samu ciki mai tsananin laulayi,bai rufa wata huɗu ba ta yi ɓarinsa,tin daga nan ciki ya dena zama a jikinta,da ta samu ciki da ta yi ɓarinsa,a haka har mahaifarta ta gaji likita ya basu shawarar kawai a juya mata mahaifa ta huta. Da ƙyar Baba Ilyas ya yarda aka juyawa Sumayyah mahaifa. Ita kuwa daɗi ta ji da hakan ta faru,domin ita kaɗai ta san azabar da take sha idan ta samu juna biyu har zuwa lalacewarsa da wankin mahaifa da ake yi mata.
Ta ɓangaren zuhairah ma shiru babu wani bayani,sai kawai suka riƙe abinda Allah ya basu suka ci gaba da basu tarbiyya da kulawar da ta dace. Fauziyyah ta taso yarinya mai farin jinin mutane,kowa so yake ya ɗauke ta,mata kuwa har so suke kitson kanta ya tsufa su rangaɗa mata wani,lalle kuwa da wannan ya fita za a ɗora mata wancan. Sai ta taso da tsananin iyayi da manyance,tare da shegen son girma,rashin ji kuwa a wajenta kamar jinjirar biri. Duk abinda aka ajiye shi sai ta zubar,ko ta ɓata shi,wannan hali nata ke sanya mahaifiyarta da take kira da Ummi ta kama ta ta zane ta. Idan Abdullah ya dawo su zauna su ci kukansu a tare,haka zai ta alƙawarin duk abinda ta ɓata da ya gama makaranta ya yi kuɗi zai biya. Yanda Abdullah ya tsaya mata a gidan ne ya ke ƙara rura wutar rashin jin Fauziyyah. Idan ta fita kuwa har hawa bishiya yi take yi ta tsinko duk abinda take so da kanta. Ita ce hawan keke kamar namiji. Babu kalar fitinar da bata yi,sai wadda idonta bai kai kanta ba. Tsokana da dukan yaran mutane kuwa ya zame mata abu mafi sauƙin aikatawa. Kullum sai an kawo ƙararta,ba dan iyayen yaran na son ta saboda kyawunta ba da nagartar iyayenta,wataƙila da kullum sai anji kan su da Ummi.
A shekarar da Abdullah ya gama sakandire a shekarar Fauziyyah ta shiga aji huɗu a primary. Bayan ya zana JAMB jarabawarsa ta yi kyau ne sai ya nemi karatu a jami'ar BUK ɓangaren kasuwanci. Cikin ikon Allah ya samu gurbin karatu a jami'ar. Babu ɓata lokaci ya fara zuwa ɗaukan karatu ba tare da fashi ba. Abdullah na daga cikin ɗalibai masu hazaƙa sosai a lokacinsa. Shi yasa ya riƙewa Fauziyyah wuta ta iya abubuwan da ƴan sakandire suka san shi,shi yasa idan ƴanmatan unguwarsu na hirar makaranta take shiga tayi baƙe-baƙe a tsakiyarsu ta na mayarda nata bayanin. Su kuwa saboda su samu shiga a wajen Abdullah ko ta kunyata su ba sa jin haushi,haka za su yi ta lelenta suna saya mata abubuwan daɗi tare da bata saƙo ta kai wa Abdullah.
Abdullah na kammala karatunsa na jami'a Fauziyyah ta shiga sakandire,tana aji biyu ya fara bin mahaifinsa kudu suna ɗakko kayan abinci kamar yanda suka saba,a hankali Abdullah ya faɗaɗa kasuwancin nasu ta hanyar shigar da saye da siyarwar sutura da takalma da jakunkuna. Wani lokacin ma yakan sari atampopi irin wanda inyamurai ke sakawa a kwari,sai ya kai kudu,mutanen can kudun tinda suka gane kayan Abdullah na da kyau kuma ga sauƙin kuɗi sai suke siyan nashi sosai,a haka har ya buɗe shago nashi na kansa ba tare da taimakawar kowa ba. Sai ya zamana Abdullah ya dena zuwa gida akai-akai,ya na iya ɗaukan watanni
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 12