Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 12
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ RUBUTAWA :HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✨ ✍️ Wannan littafin na kuɗi ne,idan kina son karantawa har ƙarshe biya #500 ta wannan account ɗin 9031416423 Opay Hamidah Ahmad Sanusi ko kuma 0006366584 Ja'iz Bank Hamidatu Sanusi Ahmad. Ki tura shaidar biya ta,09031416423. Mutanen Niger kuma za ku iya biya ta 96988833 Soueba sani idi,sai ku tura shaidar biya ta 09031416423. *Na san makarantan da suka jima suna bibiyar littattafaina sun san labarin MUGUN MIJI,wanda na rubuta shi a shekarar 2017/18. To gashi ya sake dawowa a shekarar 2025 da sabon salo tare da manyan darussa. Kar ku bari a baku labari.* PAGE 1. Idanuwanta da suka yi mata nauyi saboda baccin dake cikinsu ta murza. Cikin sanyin jiki ta miƙe tare da ɗaukan fitilar ƙwai ta ƙara haskenta. Saita wa tayi a daidai wajen da agogon bangon ɗakin yake a kafe,cikin sauri ta ƙoƙarta tashi da ƙyar ta na faɗin. "Innalillahi wa inna'ilaihirraji'una,na shiga uku ni Fauziyyah, har ƙarfe biyar ta yi ina kwance ban sani ba?" Cikin hanzari ta zari ɗankwalinta da ya faɗi ta ɗaure kanta mai yalwar gashi,sannan ta fita zuwa tsakar gida. Da ƙyar ta duƙa tana kwasar itace a ƙasa,ajiyar zuciya ta sauke a lokacin da ta ji danshi a jikinsu. A haka Fauziyyah ta duƙa a saman guiwowinta ta hau kunna wuta,sai dai duk da leda da buhun da ta ƙona wutar nan bata kama yanda take so ba. Cike da dauriya tare da juriya ta ɗakko mafici ta zauna ta na firfitawa. Ganin itacen ya ɗan kama ne ya sanya ta murmusawa,cikin jin daɗi ta miƙe tsaye da ƙyar ta nufi kitchen ɗinta ta ɗakko tukunya ta sake ɗaurayewa sannan ta zuba mata ruwa a cikinta. Sai da ta ɗora tukunyar ne sannan ta damo kamunta ta koma ta zauna a gaban murhu ta na ci gaba da hura wutar dan ta yi saurin tafasa mata ruwan zafin da ta ɗora. Hasken da gari ya yi ne ya sanya ta shiga tashin hankali da matsananciyar damuwa tare da fargaba,a gaban idanuwanta Abbas ya fito daga ɗaki ya wuce ta kamar zai tashi sama,ruwa ya ɗiba a bokiti da buta tare da ɗaukan kwandon wanka ya na doka tsaki da mitar sakarcin Fauziyyah,wadda a cewarsa bata san ta kai wa miji ruwan wanka ba,a haka ya shiga banɗaki yana surutai. Jiki na rawa Fauziyyah ta miƙe ta shiga ɗakinta ta fitar masa da wankakku kuma gogaggun kayansa da bata gajiya da yi musu bauta,jera masa kala biyar ta yi a saman gado saboda idan ya zo ya zaɓi wanda yake so,daga baya sai ta mayar da sauran mazaunin su. Turarukansa da yake amfani da su shi kaɗai ta ɗakko ta ajiye tare da man shafawarsa na musamman ta ajiye kusa da kayan nasa. Tsayawa ta yi tana tunanin shin menene bata gabatar masa ba gudun kar ta yi laifi? Ganin ta kammala komai ne ya sanya ta komawa kan wutar da ta kunna wadda take ƙoƙarin macewa,hankali a tashe ta duƙa ta na firfitawa kamar numfashinta zai bar jikinta. Babban tashin hankali ta ko sallar asuba ma bata yi ba ta fara aikin bautawa miji,gashi kuma da alama shi ɗin ma ba burge shi za ta yi ba,domin kuwa idan bai samu abinda zai karya da shi ba har ya gama shiri ta sani kashinta ya bushe. Barirah ce ta fito daga nata ɗakin ta shiga kitchen ɗinta ta kunna gas ta ɗora ruwan kunu,nan da nan ya tafaso ta dama kunu a babban bokiti ta ɗebi wani a jug ta zuba sugar ta ajiye,ɗumamen tuwo ta yanka a miya sannan ta ɗora. Fitowa ta yi ta kalli inda Fauziyyah ta buga uban goho a gaban murhu ta na ta hura wuta ko ɗaga kanta bata yi ballantana ta ga waye tsaye a kan nata. Ta na nan tsaye ta na kallon Fauziyyah Abbas ya fito daga wanka,kallon Fauziyyah ya yi cike da takaici ya ajiye bokiti da buta tare da kwandon wankansa ya nufi inda take,cikin zafin rai da masifar dake cin zuciyarsa ya kifar da tukunyar da ruwanta ya kusan tafasowa,a zabure Fauziyyah ta ja gefe,hakan ne ya bawa ɗan cikinta damar dunƙulewa a waje ɗaya ya tokare mata kahon zuciya. Wata iriyar azaba ce ta ziyarce ta,nan take ta rintse idanuwanta ta na cije leɓenta na ƙasa. Bata dawo hayyacinta ba ta ji saukar ranƙwashi a kanta da zafafan kalamansa a cikin kunnuwanta. "Kin san Allah Fauziyyah kika bari har na gama shiryawa baki sama min abinda zan ci ba kafin na fita, sai na lahira ya fiki jin daɗi, shashasha mara tinani kawai." Ya na gama maganarsa ya sa kai ya shige ɗakinsu ya na ci gaba da zazzaga masifa son ransa. Kasa tashi Fauziyyah ta yi daga wajen da take zuciyarta sai harbawa take yi,cikin zuciyarta take ayyana. 'Na shiga uku ni fauziyyah,yanzu ya zan yi tinda ya kashe min wutar da na tashi tin asuba ina hurawa?' Jug ta gani a gabanta da madaidaicin kwano mai murfi,kanta ta ɗaga ta ga Barirah na kallonta,cikin sauri ta ƙaƙalo wani busasshen murmushi sannan ta miƙe da ƙyar ta ɗauki jug ɗin da kwanon,murmushin yaƙe ta sake sakarwa Barirah a karo na biyu saboda ta sani ko me zai faru a daidai wannan gaɓar ba za ta iya buɗe baki ta yi magana ba, ballantana har ta iya yin godiya. Cikin sassarfa ta isa ɗakin nata ta tarar da Abbas zaune ya gama shiryawa ya na fesa turarensa mai bala'in ƙamshi da daɗi. Lumshe idanuwanta ta yi ta na binsa da wani mayen kallon da ke fitar da sirrin dake zuciyarta. Tsaki ya ja sannan ya karɓe jug da kwanon da ya san daga inda suka fito,zama ya yi ya janyo spoon ɗinsa a inda take wankewa ta ajiye masa da cups da plate gudun kar ya tashi nema idan ya zo yin ƙurmusun dare bai samu ba. Abincin ya buɗe,nan take tuwon shinkafa da miyar gyaɗan da ya ji kifi ya bayyana,yawu suka haɗiya a tare. Babu bismillah Abbas ya saka cokali ya hau cin ɗumamensa ya na korawa da koko. Yawu Fauziyyah ta haɗiya saboda yanda take jin bakinta cike da tsinkakken yawu. Ɗan cikinta ne ya hau bundul-bundul ya na juyawa kamar mai neman wani abu a duhu. Ƙara da ƙugin da cikinta ya yi ne ya tona asirin matsananciyar yunwar da take ji. A hasale Abbas ya daka mata tsawar da ta sanya ta saurin miƙewa tsaye,cikin ɓacin rai ya ce. "Za ki tashi daga gabana na ci abincin nan cikin kwanciyar hankali,ko kuma saka ni za ki yi a gaba kamar tsohuwar mayya ki na lasar leɓe?" Da sauri Fauziyyah ta miƙe ta bar wajen ta shiga store ɗinsu. Wajen da Abbas ke ajiye takalmansa ta nufa ta ɗakko masa wanda yake sakawa da kayan jikinsa ta hau gogewa. Ta na gama goge ɗaya ta ajiye a ƙasa,sannan ta kama ɗayan ma ta na ta guga kamar ta na son hango maƙerin takalmin. Ba tare da sanin lokacin da ya fito tsakar gidan ba ta ji ya fizge takalminsa daga hannunta,cikin tsautsayi da rashin sa'a takalmin ya tsinke. Tashin hankalin da Fauziyyah ta shiga ne ya yi sanadiyyar zubewarta a saman guiwowinta ta haɗe hannayenta waje guda ta na kallon Abbas bakinta na rawa ta kasa furta ko da kalma ɗaya ne saboda tashin hankali. Wani irin mugun kallo yake wurga mata wanda ke sake faɗar mata da gaba,cikin wata iriyar murya Abbas ya ce. "Malamin makaranta ne ni fa Fauziyyah for God sake,ta ya ya zaki yi sanadiyyar tsinkewar takalmin da kika san shi zan saka yau? Dika-dika takalman nawa nawa ne? Takalmi guda takwas a ganinki sun ishe ni fita cikin jama'a? Duk yanda nake lallaɓa rayuwa amma sai kin nemi tozarta ni da tona min asiri? To na baki daga nan zuwa na dawo gidan nan,idan baki gyara min takalmi na ba sai na lahira ya fiki jin daɗi,na faɗa miki." A hasale Barirah dake zaune a ƙofar ɗakinta ta ce. "Ba sai na lahirar ya fita jin daɗi ba tinda kai ka halicceta? Azzalumi mamugunci kawai,ka tsinka takalminka da kanka sannan ka ɗora mata laifi har ka dinga kurarin banza kamar kai ka halicceta,idan ka cika namiji ka fita waje mana inda mazaje ke tuɓewa su daku dan tantance wanda ya fi wani ƙarfi(filin dambe) amma ba ka zauna kana baje basirar muguntarka akan mace mai rauni ba." A hasale Abbas ya ce. "Barirah ki fita daga idona na rufe,babu ruwanki da sabgar iyalina,ke dai tinda kin shanye mijinki to ku je can ku ƙarata,amma kar ki sake ki dinga sanya baki a sabga ta da ta iyalina." Har Barirah ta buɗe baki za ta bashi amsa,mijinta Shehu Usmanu ya fito daga ɗaki,cikin muryarsa mai taushi ya ce mata. "Shiga ciki ki rabu da shi Gimbiya. Kar ki manta na sha faɗa miki,ki taimaki baiwar Allah'n nan iyakar taimakon da zaki iya bata,amma ban amince ki dinga karɓa mata faɗan da ya kamata a ce ita ke yin abunta ba,dan haka shige mu je." Wata dariyar rainin hankali Abbas ya yi kafin ya ce. "Ai da ka barta mana ta gama yi min tijara ta ga idan zan barta da haƙoranta a bakinta,idan kin shanye wannan gajeran mijin naki,ni baki isa ina magana kina mayar min ba,maganinki zan yi a cikin gidan nan,mara kunya kawai." Wani irin kallo Shehu ya hau bin Abbas da shi wanda ya shiga lungu da saƙo na jikinsa. Cikin muryar gargaɗi ya ce. "Kul Abbas ! Ko da wasa,ko da ganganci kar ka sake hannunka ya yi kuskuren taɓa mata ta da sunan lallashi ma ballantana duka,idan haukanka da rashin hankalinka ya sanya ka taɓa min matar da duk tsawon shekarun da muka yi tare da ita ban taɓa dungure mata kai ba,ban taɓa ɗaga mata murya ba,sai na jiyar da kai azabar da tinda uwarka ta haife ka ba ka san da zamanta ba a duniya. Wuce mu je ciki kar ki sake kula shi kin ji?" Ɗaga kai Barirah ta yi ta shige ɗaki ta bar Abbas tsaye ya na cizon yatsa,domin kuwa bashi da bakin da zai buɗe ya furta wata kalma saboda tsoron da Shehu ya dasa masa a zuciyarsa,sai kawai ya juya kan Fauziyyah ya na huci ya ce. "Kin gani ko? Saboda jakancinki da iskanci tare da sakarci kin jawo wata busasshiya na ci min mutunci a gabanki,to ki rubuta ki ajiye wannan abun da ta yi min ba zai tafi a banza ba,za ki biya duk wani bashi da ta ɗaukar miki." Bangaza ya kai mata ta faɗi ƙasa ta bugu da jikin ginin da take tsaye a jiki,a hasale ya ɗauki jakarsa ya rataya yana saka baƙin tabaronsa da ke ƙarawa kyakkyawar fuskarsa kwarjini da kyau. Cike da masifa ya kalli agogon hannusa ya doka tsaki ya fara tafiya ya na faɗin. "Macen kirki ƙoƙari take yi ta taimakawa mijinta ya fita da wuri ya isa wajen aikinsa akan lokaci,amma ke da yake jaka ce ballagaza baki da burin da ya wuce na ki bar mijinki ya makara." Fauziyyah na nan kwance a inda ya wurgar da ita ta na ganin dishi-dishi saboda yunwa,damuwa,ƙirshirwa tare da azabar da ɗan cikinta ke gana mata ya bar gidan. Ya na fita Barirah ta fito da sauri ta kalli Fauziyyah wadda bakinta yake a bushe babu alamar ɗigon yawu a cikinsa. A hankali idanuwanta ke lumshewa fuskarta ɗauke da busasshen murmishi ta kwantar da kanta a ƙasa. Cikin sauri Barirah ta ɗago kan Fauziyyah ta ɗora a saman cinyarta idanunta na zubar da ruwan hawayen tausayawa Fauziyyah. A hankali ta kafa mata kofin koko a bakinta ta na zuba mata,rashin ƙarfin jiki da zuciyar da zai bata damar haɗiyar kokon ne ya sa ya fara bin gefen bakinta ya na dawowa,cikin kuka Barirah ta ɗaga kan Fauziyyah sama ta buɗe bakinta ta na zuba mata kokon,a hankali ya ke wucewa zuwa maƙoshinta ta na haɗiyewa da ƙyar. Cikin ƙanƙanin lokaci ganinta ya fara dawowa daidai,kafin ta shanye kokon hankalinta ya fara dawowa jikinta. Shehu ne ya miƙa wa Barirah kwanon ɗumamen tuwon da ta zubawa Fauziyyah ya ce. "Ni zan fita sai na dawo,ki zauna ki kula da ita yanda ya kamata. Allah Ya baki lafiya ya kawo miki mafita a wannan ƙaddararran auren naku. Na ajiye kuɗi a saman madubi ko da za ki sayi wani abun." Cikin muryar kuka Barirah ta ce. "Allah Ya kiyaye ya bada sa'a,Allah kuma ya dawo min da kai lafiya." Kanta ya shafa a hankali kafin ya ce. "Amin Ya Allah,a dena min asarar hawayen nan don Allah,sai na dawo." Murmushin yaƙe kawai Barirah ta yi masa sannan ya fita daga gidan. Fauziyyah kuwa tuwonta kawai take ci a yunwace kamar wani zai ƙwace mata. Ta na gamawa jikinta ya dena rawar da yake yi kamar mazari, ruwa Barirah ta ɗebo mata ta sha ta yi hamdala,sai a lokacin ne ta kalli Barirah ta share mata hawayenta da hannunta me kyau tana murmushi ta ce. "Na gode sosai da ɗawainiyar da kuke yi da ni Aunty,Allah Ya saka da alkhairi ya jiƙan magabata " Hawaye Barirah ta share kafin ta ce. "Don Allah Fauziyyah ki gudu wajen danginki ki rabu da wannan ƙaddararran auren da ba kya tsintar komai a cikinsa sai azaba." Wani irin kallo Fauziyyah ta hau bin Barirah da shi,kallo ne na kin san kuwa me kike faɗa? Kallo ne na jin zafi da ciwon kalaman Barirah akan aureta da take zugata ta guntule. Cikin ranta take furta. 'Kin san kuwa irin son da nake yi wa Abbas? Idan na bar sa to na zauna da wa? Da kin san wanene Abbas a zuciyata da baki yi min wannan maganar ba,akan Abbas zan iya barin kowa na duniyar nan.' A zahiri kuwa sai kawai ta saki wani irin murmushin da Barirah ta kasa gane manufarsa,a hankali ta dafe ƙasa da niyyar tashi,cikin sauri Barirah ta taya ta ta ƙarasa miƙewa tsaye,ba tare da ta sake cewa komai ba ta wuce wajen butocinta ta ɗauki ɗaya ta shiga bayi ta yi tsarki,ta na fitowa ta hau ɗaura alwala. Barirah na tsaye ta na kallonta ta kammala alwala ta shiga ɗaki ta tada sallah. Cikin sujjadarta ta farko ne ta fashe da wani matsanancin kukan da ya sanya ruwan hawaye yin ambaliya a idanuwan Barirah,a guje ta wuce ɗakinta ta rufe ƙofa ta faɗa gado ta na kukan tausayawa rayuwar Fauziyyah........... [20/10, 7:52 am] HAERMEEEBRAERH ✍️✨: MUGUN MIJI. RUBUTAWA HAMIDAH SANUSI AHMAD HAERMEEBRAERH ✍️✨ PAGE 2. Kasa furta komai ta yi a cikin sujjadarta saboda bata da sauran kalaman da suka rage wanda bata roƙi Allah da su ba. A cikin zuciyarta ma bata iya ayyana komai ba,domin gani take yi idan ta roƙi Allah akan zamantakewarta da Abbas za ta yi saɓo. Ta jima ta na kuka kafin ta ɗaga ta ci gaba da yin sallar,ta na idarwa ta fara yin azkar,bacci ne mai daɗi ya ɗauketa a wajen. Ta na nan kwance ta na bacci Barirah ta fita tsakar gidan ta hau sharewa har cikin kitchen ɗin Fauziyyah. Kasancewar gidan na Abbas ne haya suke yi a ciki sai ya zamana kitchen ɗin Fauziyyah shine asalin ginin bulo da siminti,na Barirah kuwa Shehu ne ya nemi izinin Abbas ɗin ya yi mata shi da katako da langalanga,aka buga masa kanta tare da saka tayal a ƙasa sai ya dawo sak irin na Fauziyya. Kashe kuɗin da Abbas ya yi wajen ginin gidan shi ne dalilin da ya sa yake sanya mata ido sosai dan ganin ta tsaftace gidan a koda yaushe gudun kar ta lalata masa wahalarsa. Barirah na kammala shara ta haɗe kwanukansu ta wanke musu tas,sannan ta leƙa ta samo mai ruwa ya cika ko ina ta biya sa kuɗinsa ya tafi. Ganin ta rage wa Fauziyyah ayyukanta ne ya sanya ta shiga ɗaki ta duba wayarta,gani ta yi sha ɗaya na rana ta yi,gashi ranar Juma'a ce Abbas da wuri yake dawowa,cikin sauri ta isa ɗakin Fauziyya da niyyar tashinta dan ta ɗora abincin rana. Ta na shiga ta ganta kwance ta na ta sharar bacci har da munsharinta,da dikkan alamu baccin ya yi mata daɗi. Cike da tausayawa ta duƙa ta hau taɓa ƙafafun Fauziyyar a hankali ta na kiran sunan ta. Sannu a hankali take buɗe idanuwanta har ta sauke su a saman fuskar Barirah,bakinta ta share wanda yawun bacci ya ke kwaranya tsabar daɗin da baccin ya yi mata ta na lumshe ido,fuskarta ɗauke da murmushi ta ce. "Na dame ki da munshari ko Aunty? Kwana biyu My king na faɗa sosai akan hakan,wai idan ina bacci komawa nake yi kamar rago." Wani baƙin ciki ne ya tokare wa Barirah wuya,dan ganin yanda take bayyana mijinta na aure yana danganta ta da rago kuma tana bada labari har tana dariya,cikin haɗe fuska Barirah ta ce. "To ni ba wannan ne ya kawo ni ba,ki tashi ki samarwa ɗan jarabar naki abinci,idan kuma babu ne tin wuri ki sanar dani." Murmushi Fauziyyah ta sake yi,domin tinda ta ci kukanta a sallah ta yi bacci,sai ta tashi zuciyarta wasai babu wani sauran ƙunci. Cikin muryarta mai sanyi da daɗin sauraro ta ce. "Akwai abinda zan dafa mana Aunty,na gode Allah Ya bar zumunci." Miƙewa Barirah ta yi ta na amsa addu'ar da Fauziyyah ta yi mata ta wuce nata ɗakin,domin ita nata mijin sai yamma yake dawowa,ɗan kasuwa ne a kwari ya na siyar da kayan shafe-shafe na mata,har haɗa na sakawa lefe yake yi. Fitar Barirah ke da wuya Fauziyyah ta dafa ƙasa ta tashi da ƙyar ta hau gyaran ɗakin,duk da cewa ba wani datti ya yi ba,amma idanuwan Abbas kamar na mayen dake gani har hanji suke,duk inda datti yake ko da ƙura ce idan ya gani sai ya yi faɗa,haka zalika idan abu aka ajiye a inda bai dace ba komai ƙanƙantar abun nan ya gani sai ya yi masifa,wani lokacin ma har hannu yake kai mata. Ta na kammala gyara ɗakinta da parlour sai ta fito hannunta riƙe da ɗankwalinta ta wuce kitchen ta na ɗaurawa a saman kanta. Waken da ya rage musu ta ɗakko,wanda ko kofi biyu be kai ba,tsincewa ta yi ta wanke ta shiga kitchen ɗin Barirah kamar yanda ta yi mata izinin duk sanda za ta yi girki Abbas baya nan ta dinga amfani da gas ɗinta,cikin sauri ta zuba waken a tukunya ta zuba ruwa ta saka gishiri kaɗan ta jefa kanwa ta rufe. Waje ta koma ta shiga kitchen ɗinta ta ɗakko wani ragowar barkonon da take da shi da maggi biyu da ya rage sai uban gishiri da ya siyo leda baƙa guda dan ganin arharsa. Ɗiba ta yi ta hau dakawa,sai da ya daku ya yi luƙui sannan ta kwashe. Ci gaba da aikace-aikace ta yi har waken ya dahu ya yi laushi tuɓus ya farfashe. Manja ta soya da albasar Barirah sannan ta samu mazubi mai kyau da take zuba masa abinci a ciki ta kai kitchen ɗinta ta rufe. Godiya ta leƙa ta yi wa Barirah wadda idan da sabo ta saba,shi yasa kawai bata amsa ta ba sai ta tambaye ta ko akwai wani abu da take so? Girgiza kai Fauziyyah ta yi tare da cewa. "Bana buƙatar komai Aunty na gode Allah Ya jiƙan magabata." "Amin Fauziyyah." Cikin gaggawa Fauziyya ta shiga ɗakinta ta cire kayanta ta fito da wanda Abbas ya cire kafin ya fita,wanki ta tsugunna ta yi ta ɗauraye su ta shanya,ta na gamawa ta ɗebi ruwa ba tare da ta koma ta sanya hijabin da zai rufe mata jiki ba ta faɗa wanka. Ta jima tana dirzar fatarta kafin ta fito. Ruwan dake jikinta ne ya bawa zanin jikinta damar mannewa a manyan mazaunanta da ke ɗauke da cinyoyi manya,gashin kanta mai yalwar tsawo da cika ta ɗaure shi a bayanta har ruwa ya taɓa shi yana ɗiga,wasu daga cikin gashin nata ne suka manne a dokin wuyanta da gefen fuskarta,farar fatarta mai ɗaukan hankali sai sheƙi take yi,gashin fuskarta duk ya kwanta gwanin burge mai kallo. A haka ta duƙa ta yi alwala sannan ta miƙe dan komawa ɗaki. Kamar daga sama aka wurgo su babu sallama sai hayaniya da darerekunsu. Wata iriyar faɗuwa gaban Fauziyyah ya yi,nan take ta gane wautar da ta tafka na rashin sanya hijabi dan suturce jikinta. Nasihar da Barirah ke yawan yi mata ce ta faɗo mata a rai. 'Fauziyyah ina mamakin yanda kike zama ki saki jikin ki a waje,bayan kin san kina da sura mai ɗaukan hankalin mace ƴar'uwa ki ma ballantana namiji wanda dama mace ce abokiyar jin daɗin rayuwarsa. Ko baki san cewa duk shaƙuwa da zaman da mukai dake ba be kamata ace Shehu na ganin jikin ki ba? Kar ki ɗauka wai kishi nake yi da ke,ah ah gaskiya nake faɗa miki. Matsalar mu hausawa muna ɗaukan zama babu hijabi har wani wanda ba muharramin mu ba ya ga surar jikin mu ba a bakin komai ba,musamman yaran maƙota da mijin maƙota,sai mu dinga ganin ai an saba,ko kuma haya muke yi to ya zamu yi ai dole a gauraye.' A nutse Fauziyyah ta ce. 'Aunty shi ne ke hana ni saka hijabi ko mayafi,wai a cewarsa yana alfahari da kyauna,yana so duniya ta san wace iriyar mace ya aura.' 'Lallai kuwa zai kai ki wuta idan baki gyara ba,domin za a wayi gari tin kina son suturce jikin ki da kan ki,kema zaki saba da zama babu suturar arziƙi.' Lallai wannan lokacin Barirah ke jiyewa Fauziyyah zuwansa,gashi har ta saba da rashin rufe jikinta. Sauri ta sanya za ta gudu ɗaki don ta rufe jikinta. Abbas

Chapter 1 of 12