се, "Ва уа ce kar a gaya mata ba?"
Та сe, "Au haka ne? Mu dai mun san sunanta,
amma Little za mu riga ce mata".
Ta zauna dabas ranta ya fara baci, ta се, "То
amma me ya sa ni yake boyc min bayan ni na fi cancanta
137
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
da na sani kan kowa, ni na sha wuyar cikinta na haife ta,
don me ba za a sanar min ba, akwai wanda ya haifar min
ita, ko shi ya haifar min bare ya ki fada min sunanta?"
Rafi'atu ta ce, "Ya yi kyau, dole ki fada mana kin
haihu. Kan wani suna can za ki runtse ido kina fada masa
maganganu haka? In ya dawo za ki masa kiri-kiri ba za
ki lallaba shi ba?"
Ta ja tsaki tare da cewa, "Kar ya fada mana, ya je
ya yi ta riko. Suna dai dole a kira ta da sunanta, in kuma
ba ya sonta ba zai iya sa mata ba. Ni ina son 'yata, zan sa
mata sunan, ba shi kenan ba?"
Ta dauki 'yar da wayarta ta fice cikin bacin rai.
Dakinta ta shige ta haye kan gado, sai kumburi ta ke.
Tsam Rafi'atu ta mike ta biyo ta, ta shigo ta
zauna kusa da ita tana kallo. Ta kama 'yar ta kankame
kam, Rafi'a ta ce, "Me ke damunki Mabaruka? Kin san
me ki ka ce kuwa?"
Ta dago ta kalle ta, ta dauke kai tare da cewa,
"Na sani mana, sai me? Na fada, karya na yi?"
Ta ce, "Ina ga kin samu matsa! wajen haihuwar
nan, har za ki iya cewa Ya Imran ba ya son 'yar nan duk
kin manta baya, kin manta dawainiya da wahalhalun da
ya sha a kanki wajen rainon cikinki? Kin manta yanda ya
aje komai yana kula da kc, akwai imagine kan ya boye
sunan 'yar bai gaya miki ba, wasu sun sani me ke
damunki Mabaruka? Har ashe za ki iya fada masa
138
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
maganganu irin haka ko kunya ba ki ji ba, kin manta irin
soyayyarsa a gare ki?"
Hawaye suka zubo, ta dube ta a marairaice, ta ce,
"To amma me ya sa ya min haka Rafi'a? Ya daina sona
kenan?"
Ta ce, "Ni kau haushi ki ke ba ni wallahi, kin
manta halinsa ne?"
Ta ce, "A'a". A sanyaye.
Та се, "То ki sa ido ki gani mana".
Ko da ya kira ta tamkar ta masa kuka a kan ya
fada mata sunan. Ya yi dariya, ya ce, "To mene ne na
damuwar za ki ji mana, ke da 'yarki? Kada ki damu kin
ji ko my Mabaru, gobe kamar yanzu muna tare".
Kwana biyu da haihuwar ya dawo. Tun a airport
suke waya, ku zo ku ga kwalliya tamkar ranar ne suna ita
da Baby sun cancada ado, kowa yabawa yake.
Ya shigo gidan a kagauce da nufin tunkarar
dakinta, jikinsa na rawa. Aunty Luba ta tare shi, ta ce,
"To tsaya azarbabi, surukanka na ciki, wallahi in kuma
a ka nuna musu halinka to".
Ya yi turus ransa ya baci, ya ce, "Su waye su
din?"
Ta ce, "Yan uwan Babanta mana".
Bai ce komai ba ya yi kwana, tare da cire hula ya
wurgar. Ba haka ya so ba, first Mabarukarsa ya so ya
fara gani sannan 'yarsa, 'Little Mabaruka'. Ya fada kan
gadonsa tare da lalubo lambarta. Mutane na zazzaune ta
139
WAYE ANGON?-4 Maryanı Jafar Kaduna
yanko da gudu, jikinta na rawa da doki ta iso. Ya bi ta da
kallo, lokaci guda ta canza masa. Ta kara kyau duk ta
sabe.
Da zuwa ta fada jikinsa, shi kuma ya rufe ta da
hannuwansa yana murnar ganinta. Ya dago ta yana cewa,
"Fada min lafiyarki kalau, ba abin da ke damunki?"
Ta daga kai tare da cewa, "Lafiya ta lau".
Ya če, "Ina 'yata?"
Ta ce, "Tana can wajen su Rafi'atu".
Ya koma ya zauna tare da cewa, "Maza dauko
min abata".
Ta yi dariya tare da juyawa ta dauko masa din.
Ya tsura wa yarinyar ido a nutse yake kallonta, wata
soyayyarta ya ji tana shigarsa a hankali. Ba zai iya
misalta shi ba, gefe kuma mamaki ya hana shi magana
inda yake tambayar kansa, shin wannan 'yata cе
Mabaruka ta haifa min? Allah ya ba ni, ni ne babanta?"
A hankali ya sulale ya zauna bakin gado, kwalla
na taruwa a idonsa na farin ciki. Ya kankame yarinyar a
kirjinsa har da lumshe ido, yana cewa, "Allah na gode
maKa".
Mabaruka wacce ke tsaye kyam tana kallonshi,
fuskarta dauke da murmushi, dadi da zakwadinshi ya
hana ta magana, gefe kuma soyayyarshi da ta 'yarsa na
kara shigarta
Ta tsugunno gabansa taro da dora hannuwanta
kan pwiwarsa, har lokacin idonsa a lumshe yake.
140
WAYE ANGON?-4
Ta ce, "Y a Imran?"
Maryam Jafar Kaduna
Ya bude idon kyam a kan nata, ya amsa, "Na'am".
Ta ce, "Kai ma kana sonta?"
Tambayar dariya ta ba shi, ya kalli babyn da ta ke nade cikin shawul tana baccinta a nutse, sai kamshi da yake tashi jikinta mai nutsuwa. Ya dago ya kalli Mabaruka, ya ce, "Why not Mabaruka?"
Ba ta iya amsawa ba, sai dai dariya.
Ya dago habarta tare da cewa, "Yes I love her
alots, and you?"
Ya tambaye ta yana kallonta.
Та сс, "Саb! Sosai ma, ka ji yanda nake jinta a
raina kuwa?"
Ya yi dariya sosai, ya ce, "I know, mamaki ya
ishe ni Mabaruka, dubi fuskarta, idonta, hancinta da
bakinta duk irin na Mabaruka ta ne ba bambanci".
Ta ji dadi sosai, ta yi dariya tare da leka fuskarta,
ta ce, "Kowa haka yake cewa, amma me ya sa haka?"
Ya yi murmushi, ya ce, "Ikon Allah tamkar ke
kina yarinya. Mun yi waya da Mommy ta ce haka ta
haife ki, sam babu bambanci, kamannin ma har ya baci.
Ban taba ganin kamanceceniya irin wannan ba, sak! Ke
се.
Cikin doki tana dariya ta ce, "Dadi nake ji Ya
Imran, ban san me ya sa ba".
141
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya nutsu yana kallon yarinyar, ya ce, "Dole ne,
na san za ki ji. Ni ma haka ne a gurina".
Ta sake cewa, "Amma na so a ce da kai ta yi
kama Ya Imran".
Ya-aje yarinyar tare da kamo. ta zuwa jikinsa kan
cinyarsa suka kura wa juna ido tsawon dakiku kowa da
yanayin da yake ji game da dan uwansa.
Ya ce a hankali, "Me ya sa Mabaruka?"
A sanyaye ta ce kwalla na cika idonta, "Saboda
ina sonka Ya Imran, zaan so a ce na haifi mai kama da
kai, don koyaushe in dinga kallonta ina jin dadi".
Ya nutsu yana kallonta, can ya tallafo fuskarta da
hannuwansa biyu yana jin saukar numfashinta, ya ce,
"Na fi sonki Mabaruka, hakan ya sa na fi farin ciki da
haihuwar;ya mace, kuma copy din Mabaruka ta".
Ta yi dariya sosai, har sai da hakoranta suka fito,
ta ce a marairaice, "Amma me ya sa ka ki fada min
sunanta Ya Imran? Ka daina sona ko?"
Ya yi murmushi tare da shafar gefen fuskarta, ya
ce, "Wai da ba na son sanar miki ne 2 yi laifi?"
Haushin da ya dawo mata ta hade fuska, ta ce,
"Saboda ban kamata na sani ba ko ba ni da
muhimmancin sanin?"
Ya yi shiru yana kallonta ba amsa.
Aunty Luba ta kwala mata kira, "Ki fito ga baki
nan sun zo sauri kuma suke za su tafi”.
142
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta yi saurin mikewa daga jikinsa tare da ture hannunsa. Cikin haushi ta ce, "Kar ka ſada, ka yi ta riko bana so".
Daga haka ta juya, ya kwalo mata kira, "Z.o mana".
Dode kunnuwanta ta yi tare da wucewa da sauri
ta bude kofar ta fice tare da banko masa.
Murmushi kurum ya yi, tare da cewa, "Allah raya
mana ke my Mabaru". Ya fada yana kallon 'yar.
Rafi'atu ta ci karo da ita ta debo kunu, ta bi ta da
kallo bayan ta wuce ta gabanta fuu zuwa dakinta.
Da sauri ta sha gabanta tana cewa, "To me kuma
ya faru?"
Ta ja ta tsaya tare da sakin tsaki, ta hararo
dakinshi ta ce, "Ni da wancan mutumin mana".
Kunun ya kusan biyo wa Rafi'ar ta hanci don
razana, ta samu ta hade shi da kyar, ta ce, "Waye
mutumin can Ya Imran din?"
Ta ce tana harararta, "To da wa nake in ba shi ba?
Ni son ma sai na fasa gabadaya, 'yata ishe ni".
Ta jinjina kai, ta ce, "Da kyau, gaskiya dole ki ce
haka tunda ya taimaka miki kin samu 'yar son kuma ki
bar yi masa sai me kuma, shi ma Mabarukar ta ishe shi,
ba ke kadai ki ka haife ta ba".
Ta saki baki tana kallonta, ta ce, "Wacce
Mabarukar ni kuwa?"
143
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta kurbi kunun, sannan ta ce, "Yarsa mana,
wacce ki ke fada kan bai gaya miki sunanta ba".
A dan tsorace ta ce, "Su... su... sunanta kenan?"
Ta ce, "Kwarai sunan da ya sa mata kenan tun
ranar da aka haife ta. Ba don komai ba sai don son da
yake miki".
Daga fadin haka ta juya ta wuce kununta a hannu.
Gabadaya ta birkice ta rasa wane tunanin za ta yi, wani
tsoro da firgici ya kamata, da dafe kai tana salati tare da
tambayar kanta, "Me kenan na yi ni Mabaruka? Butulci
ko gajen hakuri?"
Ta ba kanta amsa. Ta juya tana kallon dakinsa,
wata kunya ta kamata. Ta yi saurin juyowa tamkar yana
gabanta, ta ce, "Ba ka cancanci halaccin nan ba Ya
Imran, ka so ni, kana sona, soyayyarka daban ce. Ta
bambanta da ta kowa don me na maka haka? Me yasa?"
Hawaye suka zubo mata na bakin ciki. Ganin
tahowar Aunty Luba ya sa ta yi saurin juyawa da
gogewa. Ya zama dole ta koma gurinsa ta ba shi hakuri,
ba za ta iya fushi da shi ba, don haka ta juya tare da
tunkarar dakinsa.
Suka ci karò da Auntyn har ta wuce idonta a rufe
ba ta ko ganin hanya, ta jawo ta ta dawo ta baya. Ta tsura
mata ido tana kallo, sai can ta ce, "Me ke damunki
idonki ya rufe ko?"
144
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta dauke kai lokacin da hawayen da ta ke
makalewa suna shirin zubowa, ta sake cewa, "Lafiyarki
kuwa ina miki magana?"
Ta juyo a marairaice ta ce, "Please Aunty kar ki
tsayar da ni, gurin Ya Imran zan je".
Та сe, "Ya Imran kuma, ba yanzu na kira ki ba
daga gurinsa kin je ma gurin bakin ko ko, kin nace
gurinsa?"
Ta ce, "Ban je ba, amma ki bari na koma gurinsa
ina zuwa".
Daga haka ta wuce da sauri ta barta sake da baki
tana kallonta. Sai da ta ga shigarta sannan ta jinjina kai,
ta ce, "Turkashi! Kuna da abin kallo".
Yana nan dai zaune makale da 'yarsa jikinsa yana
kallo, ya ga ta shigo ta ja ta tsaya bakin kofar tana
kallonsa. Nan da nan kwalla ta ciko idonta taf, ta kasa
motsi sai dai kallon da ta ke masa, sonsa na kara karuwa
a ranta.
Ya nutsu yana kallon yanayinta, ya ce, "Mene
ne?"
Shiru ba magana. Ya aje 'yar tare da mikewa
yanayinsa ya sauya, ya sake cewa, "Lafiya kuwa, me ya
same ki?"
A hankali ta fara takowa ta kasa dauke idonta a
kansa, shi kuma ya yi tsaye yana kallonta bar ta karaso.
145
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Gaf da shi ta tsaya idanunta na kara cikowa da
hawayc, ya dafa kafadunta cikin kulawa, ya ce, "Fada
min mene ne?"
Bakinta ya fara rawa, tana son cewa wani abu
kukan da yake kokarin zubowa ya hana ta.
Ya sake cewa a dan rikice, "Why Mabaruka, tell
me woo.
Kukan ya kufce mata, taffada jikinsa tana kukan
mai sauti. Ya sa hannuwansaya rike ta sosai yana
lallashinta, ta kasa barin kukan sai kara karuwa yake.
Ya yi kokarin dago ta, amma ta rike shi gam. Ya
sa hannu yana shafa bayanta, tare da cewa, "Is ok, is ok
Mabaruka, please stop cry am with you.
Ba ta fasa ba ta ci gaba da kukan. Ya dago ta tare
da tsura mata ido, ya ce, "Kin ganki kuwa?"
Cikin kukan ta girgiza kai alamar a'a.
Ya ce, "Ban taba ganin mummuna ba irinki
tamkar biranya, kin ga yanda ki ke?"
Ya kwabe fuska gwanin tsoro yana nuna mata. Ba
ta san sanda dariya ta kufce mata ba, a fada jikinsa. Shi
ma ya yi dariyar ya ce, "Is ok Ya Imran dinki ne mai ya
rage kuma?"
Ya ja ta suka zauna bakin gadon tana dai jikinsa,
ya ce, "Fada min wa ya sa min ke kuka?"
Ta marairaice fuska tana kallonsa, ta ce, "Ni
kaina na ba kaina haushi".
Ya zaro ido ya ce, "Saboda me?"
146
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "Gajen hakurina mana, na manta waye kai
da soyayyarka har na runtse ido na gaya maka magana
son raina tun bayan idonka don shirmena. Tambayar ni
mana don me na aikata haka?" Ta langwabe kai tana kallonsa.
Abin dariya ya ba shi, ya ce, "Ya isa kowa ma zai
yi haka ba ke kadai ba, ke ya kamata ki sani kan kowa".
Та се, "А'a kar ka ce haka, ka yi haka ne don
kana sona, soyayyata ce ta sa haka, ni kuma na maka
יי butulci, na...
Ya yi saurin sa yatsansa kan la66anta tare da
cewa, "Shisssh! Kar ki sake cewa haka, ba ki laifi ba.
Yes ina sonki hakan ne ya sa na zabi sunanki tunda na
samu copynki ai sai na sa sunanki na kara tabbatarwa
kaina yes you are my own'.
Dadi ya kamata, ta ce tana kallonsa, "Ni ma ina
sonka Ya Imran, ba zan daina sonka ba har abada, har
bayan raina kai kadai nake so, I am really love you.
Ya kai bakinsa kan nata yana ba ta wani sako.
"Rufe idonku!"
*** ***
Ranar sunan Little Mabaru ku zo ku ga yanda ake
wadaka da abinci, kaji bankararru sai tafiya suke da
kafafunsu. Gida makil da jama'a don ma akwai yalwa,
masu hotuna da bidiyo sai haska su suke. Ku zo ku ga
mai jego, wayyo! Masha Allah! Abin da kowa ke cewa
147
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
kenan, ta sha lasa-lasai ubansun da manyan atamfofi,
shaddoji ko ba a magana an zuba mata surfani, sai
walainiya ta ke cikin gwalagwalai zobba da awarwaro.
Tabbas Imran na son Mabaruka duniya ta shaida,
haka masu karatu sun shaida don ya fito da ita da
dukiyarsa, ya cancade ta. Hakà zalika 'yarsa Little
Mabaruka ta sha kwalliya da irin kayanta manya masu
tsada da daukar ido, duk wanda ya dauke ta kamar kar ya
aje. Ta ci sunan mamanta saboda soyayyar Babanta ga
mamanta.
Shi kanshi ku zo ku ganshi. Abin ba ya
kwatantuwa naira ta yi kuka, duk inda ya yi ana cewa,
jarumin Mabaruka, Baban Mabaruka. Tabbas ya burge
kowa.
Kowa ya tafi da sam-barka, jakarsa dam da kayan
suna aka bar Little da iyayenta suka sa ta gaba, wannan
ya dauka, wannan ya aje.
Ikon Allah aka ce a tafi da ita gida ta huta ko ya
ya ne, sai ta sa kuka ta fadi kasa tana rokon ita a barta
don Allah, a nan ma za ta huta tunda ga Umma nan, bare
shi gogan fada ya kama, wai don me ake son fauke min
mata ina sonta fa sai na zauna ni kadai, ta je can ta yi
me? Tunda ta haihu lafiya to a bar min abata".
Simi-simi aka daye aka barsu, ba wanda ya sake
tada zancen.
148
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Sai da ya dauke hutun sati biyu gurin aiki, shi ma da ya cika da kyar da kyar ya koma ya tafi da kewar Mabarukarsa da Little.
Haka abubuwa suka ci gaba da tafiya, Mabaruka
na rainon 'yarta sun yi kyau sosai da kiba, sumulmul abinsu. Kamarsu kuwa kullum kara fitowa ta ke, har abin
ya koma ba mutane mamaki, sak! Mabaruka ba maraba. Lokacin da ta fara zama idan tana wasa ko tana
dariya abin har kada Momy yake, ta kan ce, "Wallahi da dariyar da kukanta duk na mamanta ne, ita gani ta ke ma tamkar Mabarukar ce ta dawo yarinya.
Shi kam gogan hakan wani farin ciki yake sa shi da karuwar śoyayyarsu, mai kama da Mabarukarsa sak!
Tana da wata shida Nafisa matar Sulaiman ta
haihu, ta samu 'yarta mace. Komai ya wuce don haka Mabaruka kullum tana can sai yamma ta dawo gida har
ranar suna. Ita da inna ko abin kamar a mafarki sai su
wuni suna hira, Little Mabaru na hannunta.
Ranar suna tana shigowa tun kan ta shigo dakin
suan da ta ji yara na fada na yarinyar ya kidima ta, Samira ta tare ta da murna ta dauki Little da ke wasa a
hannunta an mata kwalliya da riga da siket short, pink
colour an sa mata socks da takalma cover. Gashinta
kuma an mata kitso kanana, an sa mata beat yarinyar mai fara'a ba kwiya akwai son wasa. Sai zuba kamshi ta ke
na turaukanta.
149
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta dubi Samirar cikin wani yanayi, ta ce, "Da
gaske sunan yarinyar Mabaruka?"
Ta yi dariya ta cc, "Sosai, kin yi mamaki ne?"
Kada kai ta yi alamar aja a sanyayc, samirar ta
wuce da Little hannunta, yara suka bi ta yuu don Allah ta
ba su ita, yayin da ita kuma sai wangale musu baki ta ke
tana dariya, gani ta ke abin wasa ne. ko ba komai ta biyo
mahaifinta fara'a, son mutane gabadaya halinsa ne
kamar kuma na mamanta.
Ta shiga dakin Nafeen ta sha kwalliyar suna ta
zauna bakin gadon tana kallonta, ta ce, "Wai sunanta
Mabaruka?"
Murmushi ta yi ta ce, "Ba gaisuwa abin da ya
dame ki kenan?"
Ta ce, "Ina mamaki ne me ya sa Sulaiman zai sa
sunana?"
Ta ce, "Saboda yana sonki har gobe, ba don za ki
dawo masa ba sai don kawai son daga Allah ne. Ni ma
na karfafa masa gwiwa saboda matsayinki gurina, ke се
sanadin dawowata gidan nan, ga shi har na haife ta, me
zai sa ki yi mamaki to don mun sa sunanki?""
Kwalla ta ciko idonta, ta ce, "Haka ne, na gode
Yaya Nafee, Allah raya mana takwara ta".
Mutanen dakin suka bi ta da kallo suka ce, "Da
man wannan ce mai sunan?"
Nafeen ta ba su amsa, "Ita ce kuwa".
150
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Jinjina kai kurum suka yi ba magana saboda naira
da suka gani jikinta, uwa-uba kyau wanda ya sake nuna
ta.
A gaida 'yar gidan Y a Imran Baban Littlc.
Ba da dadewa ba iţa ma Rafi'atu ta sunkuto da
nata dan, hula tsakanin dankwali. Abin da kowa ke cewa
ya aka yi ya yarda matan suka riga shi zuwa?
Kam Mabaruka ta rungume shi, soyayyarsa na
shigarta, yau ga dan Rafi'a a hannunta, me zai sa ba za ta
so shi ba? Ya ci sunan Alhajin su Dr. Faruk Usman, don
haka suka nada masa Ameer.
Ba ta huta ba, kullum tana zarya gidan Rafi'ar,
har sai da aka gama suna. Da rana da su Momý suka zo
da Sharifa ita ma ta zo tun bayan kammala karatunta,
don haka Little ta makale musu har da kuka da za su tafi,
dole suka tafi da ita tana rungume jikin Sharifa.
Ranar asabar ne Imran yana gari, don haka sai can
dare ya zo daukarta. Ta fito da tarkacen kayansu ita da
Little ta zuba a mota, lokacin yana waya hankalinsa na
kau wayar har ta gama ta shiga ya ja suka efi.
Har suka shigo harabar gidan sannan ya gama, ya
gama yin parking ya juyo yana kallonta lokacin da ta ke
kokarin fita.
Cak! Ya ja ya tsaya tare da sakin baki ya bi
cinyarta da kallo, bai ga Little ba ya kalli bayanta, nan
ma. Ya juya da sauri baya ko tana baya. Ya juyo da sauri
zai mata magana ya ga ta fice. A gaggauce ya fito tare da
151
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
rufa mata baya. A falo ya cimmata ya juyo da ita da karfi
yana cewa, "Ina Littic?"
Ta yi taga-taga za ta fadi, ya tarbe ta tare da kura.
mata ido, ta ce, "Shi ne za ka kada ni don ba ka ganta
ba?"
Ya ce, "Sorry, amma tana ina?"
Ta ce cikin ko'in kula, "Na baro ta gurin
Rafi'atu"
Ya rike baki a tsorace da zaro ido, ya ce, "Kut..."
Maganar ta koma masa ganin yanda ta zaro ido
tana kallonsa, ta ce, "Zagi kuma Ya Imran?"
Ya canza maganar da cewa a zafafe, "Kin baro ta
gurin Rafi'atu ta yi musu me? Ni na kwana haka babu
ita?"
Ta ce a marairaice, "Haba my Imran, kwana daya
fa kadai, Rafi'ar ta nuna tana so a bar mata don Allah sai
na hana ta?"
Ya ce, "Yes". Yana zaro mata ido tamkar zai dake
ta, "Ba zan iya bacci ba sai da 'yata, ban yarda ta rabu da
jikina ba, ba zan taba bari ta kwana a veni wuri ba, ki zo
mu koma mu dauko ta?"
Ta ce da sauri, "Ina? Gurin Rafi'ar?"
Ya yi kicin-kicin da rai, "Eh ko ma ina ne dauko
yata zan yi, don me ki ka barta bayan kin san ba zan iya
ba?"
152
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "Rafi'atu fa na ce ba wata ba, yanzu har za
mu iya wa Rafi'a haka? Ka manta halaccinta a gurinmu
da soyayyarta?"
Ya fada cikin tabbaci, "Ko ma wace ce na fada
miki wallahi sai na dauko 'yata, ki zo mu je".
Ta juya za ta shige daki tana cewa, "To ba da ni
ba, kai ka je ba zan iya ba".
Cak ta ji ya kamo ta tare da janta. Ta hau tirjewa
da kwakule hannunta daga nashi, ko motsi hannunsa bai
yi ba bare ta iya kwacewa.
Ransa ya gama baci har huci yake, idonsa ya rufe
shi dai 'yarsa kawai, ikon Allah.
Ya tura ta mota tare da zagayawa ya shiga ya ba
ta wuta tare da janta da karfi suka wuce. Ta ce tana
kallonsa, "Ikon Allah, tafi da mu a hankali ba bacewa za
ta yi ba".
Bai saurare ta ba ya ci gaba da tukinsa.
Sai da ta ga sun kusa gidan sannan ta ce, "Na
manta ba gidan Rafi'a ba ne, Momy ne suka tafi da ita".
Ya ci uban birkin da bai yi niyya ba, ya ja ya
tsaya cak! Tare da kallonta. Ta dauke kai tare da hade
rai.
Ya ce, "Wai me ke damunki, lafiya ki ke?"
Ta ce, "Oho". Kanta a window.
Ya jinjina kai tarc da cewa, "Ok za ki sani". Daga
haka ya juya a fusace ya tunkari gidan Momy, ta bi shi
153
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
da kallo ta sa zai hakura, ta cc, "Au ba za ka barta ba har
gurin Momy haka za ka ce a ba ka 'yar?"
Kansa na kan titi cikin masifa ya cc, "Ko ma
wane gida ne dauko 'yata zan yi".
Ba ta ce komai ba ta dauke kai ita ma.
Ita kuma lokacin Momy tana ta jaje da fada cewa
ta ke, amma yarinyar nan akwai mara hankali, cowa nake
ta biyo ta tafi da ita in za ta tafi gida, ina ga wucewarta ta
yı. Yarinya mai shan Mama yaushe za ta kwana wani
guri?"
Rufe bakinta kenan ta gansu a hargitse, bare shi
ya sha kunu ya ce wa Momyn, "Ina Little".
Ta bi shi da kallo, ta ce, "Hala da ba ta yi niyyar
zuwa daukarta ba?"
"Eh". Kawai ya ce a takaice.
Ta ce, "Allah shirya ki Mabaruka, to ga ta can
gurin Antynta har sun kwanta ita atafau in barta ta
kwana, wai Mabarukar ta ce mata cikin dare ba ta neman
Mama".
Fit! Ya wuce zuwa dakin Sharfar.
Suna kwance tsakiyar gadon sun rungume juna,
bacci ya fara daukarsu ta ji ya sa hannu ya zare 'yarsa.
Ta tashi cikin bacci, ta ce, "Please Bigbro ka bar min ita
mu kwana tare, ka ga har mun yi baссi".
Ya watso mata harara tarc da rike 'yarsa gam
wacce ta ke bacci, ya ce, "Gwanda ki ce ni na kwana a
nan a kan na bar miki ita".
154
WAYE ANGUON?-4
Daga haka ya wuce a fusace.
Maryam Jafar Kaduna
Ba ta taba ganin fushinsa ba irin yau, duk kan
'yarsa. Ta saki baki har ya fice, ta ce, "Cab! Lallai Little har ta fi ni kenan?"
Ko sallama bai yi wa Momy ba ya fice ya barsu tsaye ita da Mabarukar da ta ke turo baki. Momy ta kalle
ta ta ce, "Kin ga daga yau kar ki sake bar masa 'ya wani
gu in ba iaka ba za ki ja mana har ni, ki duba ki ga
fuskarsa ba haka yake ba, amma kan 'yarsa ya birkice ba
ta ce komai ba". Ta juya ta fice tana turo baki.
Momy ta bi ta da kallo tana cewa, "Haka ita ma 'yarki ta ke ta yo gadonki, tun kina yarinya ki ke da
dabi'ar turo baki, ga ta nan ita ma in an mata laifi ta turo
baki tana fushi, ku ku ka sani kar ku sake kawo min ita nan".
A mota ya sha fama da ita atafau ba za ta dauke ta
ba. Ta yi fushi ya je yai ta riko shi mai diya, shi kuma so
yake ta rike ta ya yi tukin. Ya tsgunna gabanta tare da
cewa, "Please my Mabaru, am very sorry, ba zan sake
ba. Wallahi soyayyarki ce ta sa min haka, don ina sonki
da yawa ya sa nake son takwararki, har ba na iya hakuri
da rashinta".
Ta turo baki tana cewa, "Ni ina ruwana? Ka rike
kayanka bana so, na bar maka".
155
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya yi dariya ya ce, "Dole sai da ke gwanda na
rasa ta a kan na rasa ki, you know, am rcally really love
you Mabaruka". Ya fada kwalla na taruwa a idonsa.
Tsakanin mata da miji sai Allah, tausayinsa ya
kamata wani sabon sonshi ya rinjaye ta, ita ma kwalla ta
taru idonta. Ta sani duk saboda ita ne yake son 'yarta,
Imran mutum ne cikakke har da rabi, yana sonta fiye da
kansa, shin me zai sa za ta yi fushi da kayanta?
Ba ta san sanda ta jawo shi ba, ya fado jikinta ta
rungume shi kyam tare da cewa, "Love you too my
Imran, you are my world'.
Ya rike ta sosai, soyayyarta na kara zafi a ransa
fiye da na 'yarsa Little.
Abubuwa sun ta tafiya, soyayya kullum karuwa ta
ke da 'yarsu da suke ji da ita kamar ransu ba ma su kadai
ba, kowa ma. Soyayyar Little ta darsu a zuciyar Momy
kamar me, in suka je wuni kamar kar ta barsu su