Ya dan yi jim!
Ya tashi ya zauna kusa da ita ya tallafo ta, ya ce, "Mene
ne Mabaruka?"
Ta kalle shi, ta ce, "Kwalliyarka ta yi yawa Ya
Imran, me ya sa ka yi har haka?"
Abin dariya ya ba shi, ya bi jikinsa da kallo. A iya
ganinsa bai ga yawanta ba, amma lura da kishi ne ya sa
ta ce haka ya sa ya tsokane ta, ya ce, "Laifi ne don na yi
kwalliya mai yawa? Daurin aure fa za mu je, kin fi son a
gan ni firi-firi bayan kin san dole mu hadu da 'yammata?
Kin fi son a kushe Imran din naki a ki kula shi?"
119
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta yi tsam tana kallonsa cikin matukar zafafa da
maganarsa, wani abu ya tokare mata makoshi bakinta ya
yi daci, hawaye suka dinga kokarin zubowa. Ta yi maza
ta danne su. Mikewa ta yi tana cewa, "Mu je rana tana
yi".
Ta sa hannu tana gogewa a wayance.
Ya yi dariya tare da mikewa shi ma ya juyo da
fuskarta tare da tallafo habarta suka hada ido, nan da nan
idon ya sauya zuwa ja, kwalla ta taru taf! Suka tsare juna
da ido. Yanayinsa ya sauya, ya ji ba dadi a ransa. Ko da
wasa ba ya son damuwarta bare kukanta, yakan birkice
ya rasa nutsuwarsa. Tsawon dakiku suna haka, can ya сe
a kasalance, "Me ye na kukan Mabaruka? Kina so na
rasa kaina ko?"
Ta yi shiru bakinta na rawa, kukan na son kufce
mata, ya ce, "Har abada ke ce kadai babu wata a raina,
ke kadai nake so, daga ke ba wata kun ishe ni ke da
babyna, wallahi ba zan taba son wata ba bayanki, duk
irin matan da zan gani ba za su taba burge ni ba. Ke
kadai ke burge ni duk duniya Y Imran naki ne ke da
'ya'yanki, yana sonki yau, jiya ya so ki, gobe ma yana
sonki har karshen rayuwarmu".
Ya sake rike ta gam, kwalla ta ciko idonsa, ya ce
cikin rawar murya, "I love you a lot Mabaruka, don't
leave me".
120
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Kukan da ta ke rikewa ya kufce mata, ta fada jikinsa tare da cewa, "I love you too Imran, I can't Icave
yo". Ta ci gaba da kukan mai sauti.
Ya rungume ta kam yana jin soyayyarta a ransa. Haka ita ma ta rike shi kam sonsa na kara shigarta. Ya dade yana kwantar mata da hankali da daddadən
kalamansa masu sa ta nishadi da nutsuwa. Daga bisani
ne suka fito a rantsetsiyar motarsa suka nufi gidan Momy
kamar yanda suka tsara ya kai ta ta wuni, idan ya dawo
ya biya ya taho da ita.
Bai bata lokaci ba bayan sun gama gaggaisawa,
Daddy ma ba ya nan ya yi tafiya. Har bakin motarsa ta
raka shi kamar ba tare suka kwana ba, sai da su Ibrahim
suka fara kiranshi suna masa tsiya sannan suka iya
bankwana. Har sai da ya fice da motar sannan ta juyo
tana masa fatan dawowa lafiya, ta juyo ciki tana cewa,
"Allah dawo min da kai lafiya Ya Imran”.
A ranar ita ma Momy ba ta huta ba, rigimar
Mabaruka da yawa ta ke, wannan dan cikin duk ya sake
shagwabar da ita, daga ta ce wannan, sai ta ce wancan
har wajen kallo suka fara rigima da ita.
Ta ce, "Ke na gaji, ciki hauka ne, kin fa wahalar
da ni gidan nan, ya zo shi wanda ya sabar miki ya miki,
ki tafi haka nan, dan ciki ba wani ba".
'Ta zaro ido, ta ce, "Da ne ma Momy? Ni fa ji
nake duk cikin duniya a jikina yake, kowa ma a cikina ya
fito".
121
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Dariya Momy ta yi, ta ce, "Za ki sani ne yarinya,
akwai ranar bayani".
Tuwon da Momy ta yi a ranar tuwon dawa, miyar
kuka sabuwa ta sha daddawa da citta, ai fa nan ta ec da
wa Allah ya hada ta in ba da shi ba? Tun tana ci tana
karo mata, har abin ya korna ba ta tsoro.
Da yamma ta ce, ai ita atafau sai Momy ta mata
shi da yawa ta tafi da shi ta sa a firij na kwana biyu,
daman ba abin da ta ke ci ya zauna daga ruwa sai fruit
Haka ko Momyn ta tashi ta sa mata katuwar tukunya ta
juye mata a roba ta barshi ya huce, miya ma ta yi ta
daidai yawan tuwon.
Tun yana mota suke waya, haka da ya iso waya
na makale a kunnensa. Karshe su Dr. Faruk suka amshe
wayar, gabadaya suka kashe. Daya daga cikin abokansu
ya tilla a motarsa ya rufe, cewa suke, "Kanka aka fara
aure? Mu nan duk ba matan gare mu ba?"
Ya yi dariya ya ce, "Ina! Tawa daban ce ba irin
taku ba ce, Mabarukata fa?"
Nan fa kowa da abin da yake cewa wajen kare
tashi, ba su bata lokaci ba ana daurawa suka juyo.
Bangarenta ita kuma ta dinga lalubensa shiru, ce
mata ake ma a kashe wayar, hankalinta ya tashi ta dinga
sintiri ko ya ta ji motsin mota.
Momy ta ce, "Kin ga Mabaruka tashin hankali ba
naki ba ne, kin san hanya akwai matsalar network yanzu
122
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
za ki ji ya iso insha Allah, ki je ki zauna kina fama da kanki".
Sam ba ta nutsu ba, Imran dinta fa me zai sa ta ji shi shiru?
Bangarenshi shi ma hankalinsa na kanta, ya damu kwarai ya san ta neme shi ba ta same shi ba. Karshe ya
karbi wayar Ibrahiı ya tura mata sakon.
‘Muna kan hanya My Mabaru, insha Allahu nan da minti hamsin ina tare da ke. Ki shafa min babyna.
Ta saukar da ajiyar zuciya tare da murmushi, ta ce
a bayyane, "Allah kawo min kai lafiya Baban Baby". Ta
shafa cikin, ta ce, "Babanka na kan hanya, kar ka damu
ka kusa jin duminsa".
Tana alwaiar magriba ta ji dirin motarsa.
A gaggauce ta fito suka ci karo a falo, shi doki ita
doki, da zuwansu suka rungume juna cikin farin ciki,
lokacin Momy tana daki tana sallah. A nan ya ci abinci
ya huta sosai, har dare ba su tafi ba suna hira da Momy.
Ganin ta fara gyangyadi a jikin Mommyn ya sa ya mike
yana cewa, "Mu je gida ko, na ga kit fara bacci".
Ta mike tsam da ma a kagare ta ke su tafi, ta ji
dumin jikinsa.
Ko da suka je sai da ya mata wanka, ya yi shi ma
sannan suka kwanta.
Mabaruka da rigima karfe biyu na dare ta tashi
cikin salon shagwabarta ta fara tada shí, "Hearly".
123
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya tashi zaune idonsa da baссі, уа сс, "Mene
ne?" Yana kallonta.
Ta turo baki cikin shagwaba ta cc, "Ni... ni fa na
gaji".
Ya zaro ido, ya ce, "Da me?"
Ta ce, "Da baccin mana, ka tashi mu zauna". Та
fada tare da jingina jikinsa.
Ya rungume ta sosai jikinsa don ma tulelen
cikinta. Ya lakace mata hanci, ya ce, "Rigima ko?"
Ta ce a shagwabe, "To ba kai ba ne?"
Ya ce, "Me na yi?"
Ta nuna masa cikin gabanta.
Ya yi dariya tare da sumbatarta a kan lab6anta, ya
ce, "Ina sonku Mabaruka ke da abin da ke cikinki"
Ta shafa sumarsa tana murmushi, ta ce, "Mu ma
muna sonka Ya Imran".
Ya kara matse ta jikinsa yana jin sonta na kara
shigarsa. Ita kuma ta lafe jikinsa tana jin nishadi da
nutsuwa kasancewarta tare da Imran dinta. Ta kalle shi,
ta ce, "Ya Imran na gode da soyayyarka gare ni, da irin
hakuri da juriya da ka yi a kan soyayyata ka dage a kaina
har sai da ka same ni".
Ya dago yana kallonta, ya ce, "Ni ne mai godiya
Mabaruka da irin soyayyar da ki ke min, ban taba
tunanin haka ba a kullum ina mamaki wai Mabarukar da
da ta tsane ni, ta kyamace ni, ta yi kuka a kaina, ta yi
bakin ciki da aurena ita ce yau mai kukan tana sona, ta
124
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
damu da ni a yau ga ni a tare da ita a gidana a matsayin
matata, tana mai sona har ga ta dauke da cikin dana.
Shin me zai sa ba zan nuna godiyata ba?"
Ta yi murmushi tare da shafo fuskarta, ta ce, "Ка
daina tunawa, ya wuce. Ni ma ba da gangan na ki ka ba,
yarinta ce ke dawainiya da ni, ban san ma me nake ba
bare na san shi kanshi son. Sai da na sha wuya sannan na
tantance wa nake so".
Hawaye suka ciko idonta, ta ce, "Na gode Allah da
ka ganar da ni da wuri, tun kan Yá Imran ya kufce min".
Ya ce, "Har abada ko bai same ki ba ba zai kufce
miki ba, ke kaďai yake so. A rayuwar Imran Mabaruka
kadai yake so".
Wannan ke nan.
"RAFIATU FA?
Allah sarki baiwar Allah kenan, halayenta abin
sha'awa da koyi, mai sanyin hali da saukin kai. Tabbas Dr.
Faruk ya yi mata matukar jin dadi da nutsuwa yana
samunta a gurinta, biyayya da hakuri ga shawarwari masu
kyau da yake samu gurinta, duk abin da zai yi sai ya nemi
shawararta.
Tun da safe ta ke kicin tana fama da girki kokarinta
kafin ya tashi ta gama samar masa abin da zai ci, don farin
cikinsa da jin dadinsa.
a
Ta yi kwalliya tana sanye da shadda pink colour,
riga da siket sun mata cas kyawun dirinta ya bayyana
ciki, duk da ba fara ba ce wankan tarwada ce, kasancewarta
125
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ba mai sha awar surfani ba amma duk da haka an dan zizirа
mata shi.
Tana aikin tana dafe da kai, tun jiya yake damunta,
ta sha magani amma dai bai bari ba, zuwa yau da safen ma
ya fi takura ta. Idanunta har rufewa suke tamkar zai fado, in
ya saro mata sai ta nemi wuri ta tsaya, in ya lafa ta koma
sıkinta, ba ta sare ba. Duk dai kokarinta ta masa abinci, duk
da sam abincin ba ya ba ta sha'awa, ba ta jin cin komai.
Gefe kuma Mabaruka ta tsaya mata a rai tunda
cıkinta ya shiga wata tara ta daina baccin kirki, da ita ta ke
kwana, da ita ta ke tasho, sallolinta, addu'o'inta duk a kan
mijinta da Mabaruka ne sai iyayenta. Wani lokacin har
kuka ta ke a kan Allah ya sauke ta lafiya, Ya raba su lafiya.
Ta fara tashi cikin dare tana gaya wa Allah, Dr.
Faruk ya kwantar mata da hankali insha- Allahu za ta sauka
lafiya da gani ya san suna cikin koshin lafiya ita da babyn
ta daina damun kanta. Hakan ya sa ta ke boye damuwarta,
fatanta dai Allah ya sauke su lafiya.
Ta samu ta gama da kyar, ya gama shirinsa tsam na
cikakken likita ya shigo kicin din yana fara'a, idonsa kur a.
kanta cikin soyayyarta.
Hajiya ta bi shi da kallo cikin yabawa da
kwalliyarsa, 1a ce, "Masha Allah likitan nan nawa ya yi
kyau, Allah tsare min kai, Ya ba da sa'a".
Ya ji dadi sosai, addu'arta kenan a kullum.
Ya riko kafadunta, ya ce, "Ke ma haka, Allah kara
bar min ke, ya kara miki lafiya".
126
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta ji dadi sosai, ta ce, "Amin likita, na gode, mu je ka karya'.
Ta dauki lask suka fito tare. Duk abin da yake
bukata ta zuba masa, ta dan yafito wanda za ta ci a faranti
ba don komai ba sai don kar ya tambayi dalili. A hankali ta ke juyawa tana tsakura tan dan matse ido saboda kan.
Ya gama fahimtarta, ya santa in wani abu na
damunta ba za ta taba fada ba, kar ta tayar masa da hankali,
sai dai ta yi addu'a kurum.
Ya ajiye cokali yana dubanta cikin kulawa, ya cе, "Rafi'a?"
Ta dan dago tana amsawa, "Na'am", cikin dakiya.
Ya ce, "Me ke damunki?"
Ta dan yi murmushi cikin kwantar da hankali, ta ce,
"Ba komai".
Ya ce, "Ban yarda ba, fada min, mene ne?"
Ta ce a sanyaye, "Kaina ke damuna tun jiya har yau
da safe".
Ya nutsu yana fahintarta, ya sake cewa, "Bayan
wannan fa?"
Ta ce, "Shi ke nan, sai ko dan zzabin da nake
tsaitsaye tun satin da ya wuce".
Ya nisa tare da cewa, "Allah sauwake, zo mu je in
miki gwaji akwai abin da nake zargi".
Ta mike din tare da mika masa hannunta ya rike
suka wuce dakinsa, inda kayan awonsa suke. Duk gwajin
da ya kamata ya mata, ya yi mata abu daya yake nuna masa
127
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ciki ne tare da ita na 'yan kwanaki. Bakinsa, ya kasa
ruluwa, can ya dube ta ya ce, "Alhamdu lillahi"
Ta ce, "Mene ne?" Cikin nata zargin.
Ya ce cikin foki, "Kina da ciki Rafi'a".
Ta bude baki cikin wani farin ciki, dadi ya hana ta
magana, sai can ta ce, "Allah Doctor ina da ciki?"
Ya ce, "Sosai, zo ki gani".
Duk ya nuna mata result.
Fadowa ta yi jikinsa cikin wani farin ciki da
nishadi, shi ma ya rike ta yana nasa farin cikin.
MABARUKA
Cikinta ya shiga wata tara, har watan yana kokarin
fita. Hankalinta ya nutsu guri guda a kullum addu'a suke
har ta kagara ita ta yi ta sauka ko ta huta, matuka nauyi ta
ke ji, musamman Imran da ya fi ta zalama, a kagarce yake
a yi ta ta kare, ya gaji da ganin Mabarukarsa cikin wannan
halin, kullum kukan da ta ke masa ita ta kagara ga idan
yaron na motsi kamar zai fasa ta cikinta ya fito.
Kwantar mata da hankali yake a kullum ga shi yana
Lagos wani aiki me zafi ya rike shi, in son samu ne ya zo
ya ganta zai so ta haihu yana nan, yana tsoron matsala duk
yanda ya so ya zo abu ya faskara, kamar ya mata kuka. Ya
daina bacci sai addu'a da salloli. Bangarenta ita da man ta
daina bacci tunda ta shiga watan sam bai barinta bacci duk
a birkice ta ke in ta zauna ta ji kamar kan ta tashi a ce ta
hathu, ko ko ta rufe ido kan ta bude ta haihu.
128
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Zuwan da ta yi gurin Momy na karshe ta dan kwanta a falo ta ce, "Momy zan yi bacci idan haihuwar ta zo ki tada ni".
Ta saki baki tana kallonta abin ma ya hana ta magana, sai ta ce, "Shi kenan kwanta yarinya ki sha baccі,
zan tada ke. Bari ma in dauko miki filo".
laka ko ta kwantan har ta tashi ba ta ji haihuwar ta
zo ba.
Ranar juma'a bayan ta yi sallah da kyar dai a zaune
Umma matar da ke kula da ita, in dai ba ya nan to tare suke
kwanciya, umarnin Imran din kenan saboda kar ta zo cikin
dare.
Dattijuwar mata mai kirki da hankali, jika ce
Mabaruka gurınta, tana samun alkhairi gurinta sosai. Ta
kan tausaya wa Mabarukar sosai ganin yanda ta ke wahala,
gabadaya cikin rinjayarta yake, sai dai ta dinga koya mata
addu'oi tana yi da wacce za ta kasance bakinta a kullum,
har ta hardace su suka zauna bakinta.
Tana zaune kan daddumar tana azkar, da ta ji
wani abu ya tunkare ta cikin wata azaba kamar an kai
mata duka a mararta, ba ta san sanda ta iasa ihu ba tare
da kiran, "Ya Imran".
Bigit! Umma ta mike a dan kishingiden da ta yi,
ta yo kanta tana cewa, "Ya dai Mabaruka, abin ya zo ne?"
Ta runtse ido gam tana yarfa hannuwa, cewa ta
kc, "Eh ya zo... ya zo... ya zo Baba, taimaka min ki
tare".
129
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Та се, "Subhanallah, Mabaruka wane irin
sambatu ne? Ina addu'o'in da na koya miki?"
Cewa ta kc, "Na ina? Suna ina? Koya min".
A haka dai ta dinga karantowa ta dinga amsawa
da karfi tana salati. Cikin kankanin lokaci da ikon
Ubangiji sai ga Mabaruka ta zankado kyakkyawar 'yar
Imran katuwa, mai kuzari da zuwanta ta canyara kuka
mai karfi da zakin muryarta da ji da kuzarinta ta zo.
Ita kanta Mabarukar duk da halin da ta ke ciki ta
bi yarinyar da kallo, ta yi dariya ta ce, "Na shiga uku
Umma, kin ga yarinyar nan yanda ta ke canyara kuka, ko
dai ba ta da lafiya?"
Ta yi dariya tana kokarin gyara ta, ta ce, "Ina?
Kina kallor yarinya dakckiya mai lafiya da kuzari ki се
ba ta da lafiya? Ai lafiyar kenan, kin ganta nan ta fi ki
lafiya, masha Allah tamkar ta yi wata. Dubi fa yanda ta
ke ware idanu".
Ta jinjina kai cike da gamsuwa, wata soyayyar
yar tana ratsa ta marar misaltuwa, farin ciki ya darsu a
ranta. Ta ji kaunar 'yarta ta yi kane-kane a ranta, ta tune
Babanta yaña can bai san me ke faruwa ba, kila ma baccі
yake, amma tabbas ta san suna ranshi.
Ta ce, "Ba ni ita Umma in ji duminta".
Ta miko mata ita saman jikinta, ta fara goge ta da
zaitun. Ta matse ta a kirjinta tana jin nutsuwa na ratsa ta,
wasu hawayen farin ciki suka zubo mata, ta bude idon
130
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
tare da kura wa 'yar ido, ita ma ta kura wa Maman nata ido kur, ta bar kukan.
Hawayen suka sauka jikinta, ta ce, "Ilove you Ya
Imran, I love you too much, kana ina, ka zo ga ‘yarka ta
iso tana bukalar ta ji duminka, tana son ta ji ta jikin
Babanta da kullum maganarsa ita ya sota ya mata gaya
tun kan ta iso duniyar".
Ta share hawayen tare da murmushi, ta ce, "Ina
sonki 'yata, Allah ya raya min ke, Ya miki albarka".
Ta daga ta tare da sumabarta a goshi, ta ce, "I
love you'. Ta sake rungume ta kyam jikinta kamar za a
kwace mata ita.
Umma na gefe tana kallo, ta cika da sha'awarsu.
Ta yi ajiyar zuciya ta ce, "Allah sarki 'ya da uwa kenan,
soyayya ce ta musamman da Aliah ke sa musu, Ya Allah
wadanda ba su yi ba Ka ba su masu albarka, karkashin
rainon musulunci".
Та се, "Тo kawo ta a gama goge mata jikin, ai
mata wanka sannan sai ki ta fada mata sakon zuciyarki".
Ta yi murmushi kawai, haka nan ta ji ta sakayau
ta nemi ciwukan da ta ke ji a da ta rasa, ta mike tsaye
tamkar za ta fadi saboda yanda ta ji ta shalau, Umma ta
taimaka mata zuwa bandaki tana fitowa wayarta na ruri.
Ta yi murmushi ta karaso, tabbas ta san gogan nata ne.
131
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Haka kuwa, ta zauna tare da karbar wayar daidai sanda
babyn ta callara wani kuka.
Sai a kan kunnensa, ya yi kasakce ya kasa ccwa
komai, ita ma ta yi shiru, dariya na son kufcc mata tana
jiran ta ji me zai ce.
Ya ce a kagauce, "Mabaruka, me nake ji ne?"
Ta yi dariya, ta ce, "Ka gane mana da kanka".
Ya ce cikin sauri, "Fada min mana my?"
Та сс, "То 'yarka ce ke ba ka labarin ta iso fa
kana ina?"
Ya lumshe ido cikin wani farin ciki, ya rasa wane
dadi ne ya ji ya saukar masa. Can ya ce, "Kin haihu
Mabaruka?"
murya?"
Ta ce, "Kwarai ga shaida nan tana fada maka".
Ya ce, "Amma wannan muryarta ne haka ta ke da
Ta ce, "Sosai, ka ji kai ma da ka ke nesa, da
wannan kukan ta iso.
Ya ce, "To ya ki ke, lafiya lau ki ke ba abin da ke
damunki?"
Ta сe, "Ya ka ji murya ta Ya Imran? Wallahi
lafiyarmu lau cikin kuzari, bare ita ma".
Ya ce, "To amman ya aka yi haka? Yaushe ne?"
Ta ce, "Wallahi Ya Imran 'minti sha biyar ban yi
ba da nakudar da haihuwar, kawai sai na ga 'ya".
Ya ce cikin nişhadi, "Allah my Mabaru?"
Ta ce, "Wallahi".
132
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya yi dariya ya ce, "Fada min da wuya?"
Ta harare shi kaınar yana ganinta, ta ce, "Ka ji ka
da wata magana, dadi mana wa yake maganar wuya?"
Ya yi dariya jin ta ba shi amsa yanda ya tambaye
ta, ya ce, "I love you my Mabaru, Allah miki albarka, ua
gode. Allab ya raya mana babynmu".
Ta ce, "Amin". Cikin wani nishadi, "Fada min
yaushe za ka zo?"
Ya yi dit! Wuta ta dauke masa.
Ta dan fahimce shi, ta ce a dan firgice, "Mene ne
Ya Imran?"
Ya ce, "Ba wani abu, calm down, ba na kasar ne,
saukarmu kenan yanzu haka ina airport'.
Yanayinta ya sauya, kwalla ta ciko idonta, ta се,
"Why Ya Imran, ka san muna bukatarka daidai wannan
lokacin".
Ya сe, "Ba don kaina na tafi ba Mabaruka, dole
aka tura mu. Akwai aikin da za mu yi jibi za mu dawo,
don kar ki tayar da hankalinki ya sa ban sanar miki ba,
amma insha Allahu jibi a nan zan sauka ko office ba zan
je ba, yanzu in ga our new baby, please ki kwantar da
hankalinki Mabaruka, kuna raina, ni ma ba haka na so
ba. A son samuna ki haihu ina kusa da ke, amma
albamdu lillahi tunda kin sauka lafiya".
Ta nisa ta ce, "Shi kenan, Allah maida ku lafiya,
za ınu yi ta jiranka, Allah ba da sa'a".
133
W
ti
f
S
1
t
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya ji dadi sosai, ya ce, "Good, that's my wife, I
love you".
Ita ma ta yi dariya, ta ce, "I love you too".
Ya sake cewa, "Dr. Faruk zai zo ya duba ku, inda
matsala ya sanar min".
Ta ce, "Shi kenan mun gode".
Kan su kashe sai da aka kanga mishi yarinyar
lokacin ta yi shiru, sai dai saukar numfashinta. Nan fa ya
shiga gaya wa mutane, nan da nan zance ya bazu, Imran
ya yi diya zankadediya, abin da yake cewa kenan tun
kan ya ganta.
Rafi'atu ita ce wacce ta fara fadawa ita ce kuma
ta fara zuwa jikinta na rawa ta shigo, gurin 'yar ta nuſa ta
dauke ta, ta rungume kyam tana juyi a daki har da
kwalla cewa ta ke, "Sannunki da zuwa my daughter
muna murna, mun yi dokin zuwanki ki ka daďe ba ki zo
ba".
Ita dai yarinya sai baza idanuwa ta ke, yayin da
Mabaruka na kishingide kan gado taną kallonsu, farin
ciki na ratsa ta soyayyar Rafi'ar na sake shigarta.
Ta zagayo ta zauna tana cewa, "Sannunki da gani
kin sha wuya, dubi idanunki".
Ta yi dariya ta ce, "Za ki sani ne ke ma kina
hanya".
134
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Та сс, "Fada min ina Babanta, sarkin 'yan doki duk in ya je mana Mabaruka kaza, in Mabaruka ta haihu.
Ta ce, "Um ba ma ya kasar sai jibi zai iso".
Nan fa mutane suka dinga tururuwar zuwa, tabbas yarinya za ta sha gata, kowa rawar jikin daukarta yake
har da kokowa tamkar nama a miya. An shirya ta cikin
kayanta masu kyau a kudundune kayan sanyi milk colour
sai kamshi ta ke duk bayan mintina Babanta zai kira ina
'yarsa? A ba shi ya ji numfashinta.
Su Aunty Karima suka dinga masa tsiya suka ce,
"To ya ishe ka zakakke, mutane cike a daki ana zuwa
ganinta, ka bari su dauke ta ba tafar maka za a yi da ita
ba, za ka zo ka tarar da ita".
Ya runtse ido ya cc, "Ya isa Anty, ba ruwanki
wannan tsakanin uba da da ne, ni na haifi kayana nake
iko da ita. Ni kadai na san wuyar da na sha kan na same
ta da rainon da na yi, ke in miki mai gabadaya uwarta ma
na sha wuya kan na same ta, don haka a barni in ji a bata,
mi: sha wuyar rainon cikinta".
Abin ya fi karfinta, dariya ta yi ta ce, "Ka fi
karfina, ka yi sai anjima a tura maka ma ita ta mota".
Da suka yi waya da Mabarukar ta ce, "Kai Ya
Imran ba ka da kunya ko kai kadai ne ka taba haihuwa?"
Ya ce, "Saurara min, ke ma wace wuya ce ban
sha ba lokacin cikin wane kuka ne ba kya min, ki tura ni
135
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
nan, ki tura ni can. A tsaye nake kanki don haka a bar ni
da vata.
Ta yi dariya, ta cc, "Shi kenan Allah ya raya
maka ita, za ka kuma dawo ni da kai ne, za ka sha wuyar
da ta fi wannan".
Ya yi dariya ya ce, "Na sani, sory, wasa nake
miki, ko me aka haifa min ke ce dai 'ya'yan ba gabanki
suke".
Ta zaro ido ta ce, "Au gabana ma suke ko Ya
Imran?"
maka".
Ya yi dariya, ya ce, "Sorry bayanki zan ce".
Та се, "Кomai ma za ka ce ai tunda na sauke
Lokacin da Momy ta zo ganin jika ta yi tsam tana
kailon 'yar, matukar mamaki ya hana ta magana. Tа
zauna a sanyaye ta rike yaerinyar tana kallo, can ta ce,
"Ikon Allah”.
Mabarukar ta dube ta a tsorace ta ce, "Mene ne
Momy, kin ga wani abu ne?"
Ta juyo tana kallonta tare da murmushi, ta ce,
"Sam! Mamaki ne ya ishe ni, yarinyar nan ta tuno min
sanda na haife ki. Wallahi tamkar ke, kin ga haka wallahi
haka na haife ki, bambanci ke da wannan yarinyar
tamkar ke ce ki ka dawo Mabaruka".
Ta nutsu tana kallo, sai sannan ta yarda da abin da
su Aunty ke cewa, wai copy dinta ce tamkar an sa ta a
computer duk ba ta yarda ba sai da Momyn ta fada, ta
136
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
tuno hotunanta na yarinta, tabbas haka ne tamkar ta yi kaki.
Ta yi dariya, ta ce, "Haka ne kam, wallahi sai
yanzu na gani.
Ta jinjina kai, ta ce, "Ikon Allah ke nan, Allah sarki"
Daddy shi ya yi wa yarinyar huduba ya rada mata
sunanta da Babanta ya sa mata. Ta yi murmushi ta dubi
Daddyn, ta ce, "Wane suna ya sa mata?"
Suka kalli juna shi da Momy suka yi dariya, ya
cc, "Tsakaninku ne wannan ba ruwana a ji mutuwar sarki bakina".
Abin ya ba ta mamaki, ta ce, "Cewa fa na yi wane
suna aka sa mata, ba wani abu fa na tambaya ba?"
Mommy ta mike tana cewa, "Kira ki tambaye shi
mana, mu kin ga tafiyarmu". Suka wuce.
Duk iya naci da rokonsu ta yi har bakin motarsu
amma sam sun ki gaya mata, ta dawo ciki inda su Rafi'a
suke ita da Auntyn, ta ce, "Wai ko kun ji sunan da Ya
I..ran ya sa wa yarinyarsa?"
Suka haďa baki suka yi dariya, Auntyn ta ce, "Au
ba ki sani ba?"
Rafi'atu ta