ita za ta nemi
maida auran. Na ji dadi sosai da abin da uwar ta yi ta koro
ta gwanda ta dawo nan din ta tantance rayuwa ba kamar
can ba. Ina fatan ka fahimce ni?"
Ya daga kai alamar gamsuwa.
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya ci gaba, "To za ta so komawa dakinta, ka ga in
ta koma din za a samu abin da ake so ta zauna idan ta tuna
zaman da ta yi a gidan nasu".
Tabbas ya gamsu da maganarsa, hakan na iya
yiwuwa. Amma yanda Mabaruka ta tsane shi anya akwai
ranar da za ta so zaman gidanshi, za ta so shi har gidanshi
ya fi gidansu? Baban ya fahimci kamar bai gamsu ba, ya
ce, "Kada ka damu yaro an yi haka ba sau daya ba, ba sau
biyu ba. Matsa mata da za a yi ba zai ba da ma'anar abin da
ake so ba, ka bar ni da ita zan yi maganinta. Idanuna za su
tsaya kanta, da kaina zan sake daura maka auranta tana
farin ciki na fada maka, insha Allahu'.
Sosai ya ji dadin zancen har ya samu nutsuwa. Ya
yarda da Baban dattijon arziki ne, ya ce, "Shi kenan Baba
zan je ni ma in dage da addu'a Allah ya taimaka mana".
Ya ce, "Amin. Amin yaro, babban abin da za ka yi
kenan. Ni ma zan yi nawa, za ka gani insha Allahu”.
Yana murna ya ce, "Allah sa Baba, Allah kara
girma".
Haka dai suka bar zancen ya masa alkhairi, amma
sam Dattijon ya ki karba, dele ya kyale shi suka rabu ya
shige motarsa. Yana kallon Baban Mabarukar yana ta dana
yara a motar, ya jinjina kai.
Inna Binto ko da aka zo mata da labarin motar, ai
sai rawa lana juyi kudi sun zo, fada ya kare yau Mabaruka
ta huce musu takaicin rashin sana'a sai la yayimi zani sai
waje don duba sabuwar motarsu, har da d'ani.
18
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Daidai fitowar Mabaruka daga bayi rike da buta
tana fama da atini, gefe kuma duk ta fada, ta yi zuru-zuru
iamkar mai azumi.
Та се, "Кan uba! Mota? Ka ji dan rainin wayau,
dan ubansa cewa muka yiba mu da abin sana'a da zai kawo
mana motar haya, wato mu ci abinci ko?"
Ta yayimi hijabi ta fita tana bala'I, "To wallahi ba
ka isa ba, sai dai ka juya da ita dan rainin wayau".
Ta fice sai dai akasin da aka samu tana fita yana jan
motar ta kalli motar; ta kalle su yanda suke rawar jikin
motar. Ta ja tsaki tare da hararar motar ta ce, Dan iska".
Tare da shigewa gida.
Ai a ranar bai jira ba ya shiga gari yana cewa Inna
Binto, "Ki je ki wanke tukunya kan rana ta yi zafi. zan
dawo".
Ta yi guda tare da cewa, "Allah tsare ka, Allah
dawo da kai lafiya, a samo da yawa".
Ya ce, "Amin".
Ya ja cike da farin ciki, ai tun kan ya bar unguwarsu
ya fara samun. fasinja, har ba wurin sa wasu.
Kan ya dawo ta yayimi gyale, farin cikinta bai
misaltuwa sai gida gurin Inna.
A kofar gida ta hadu da Sulaiman, ta yi guda tare
da shewa ta ce, "Albishirinka?"
Ya dube ta, ya ce, "Mene ne haka? Sai ihu ki ke
saman titi, mene ne ya faru?"
Та сс, "Кai dai albishirinka?"
Ya ce, "Goro".
19
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "To Mabaruka ta lito, mijinta ya sake ta".
Ya dube ta sake da baki cike da mamaki, ya ce,
"Wacce Mabarukar, tawa?"
Ta ce, "Taka ko, yau kwananta hudu a gida, yau
tunda safe kuma sai ga dalleliyar mota ta kabu-kabu an
kawo wa Malam daga mijinta. Ta kaso auran ita lallai kai ta
ke so
Wani tsalle ya yi tare da fasa ihu tamkar zararre, har
da taka rawa, ya cc, "Allah Binto?"
Ta ce, "Alkur'an da gaske nake, ka je ka gani, ita
lallai sai kai".
Ya dinga juyi tamkar zai hau bori, sai da ya nutsu
sannan ya dube ta, уa сс, "То bakinki alaikum mu bar
maganar nan kar ki sake Inna ta ji zancen nan, sai dai ta ga
ana shigowa da amarya".
Ta dube shi galala, ta ce, "Kamar ya? Kana nufin ba
za ta sani ba?"
Ya ce, "Sosai, kin manta yanda aka yi da ita wancan
karon? Na santa sarai za ta iya min bakin ciki, sam ba zan
sanar mata ba".
Ta ce, "Anya ba na zaton haka, saboda ko wancan
karon da na sa ta hanya ta gane amfanin abin ina da
tabbacin ba za ta ki ba wannan karon".
Ya ce, "Oh Binto, na fada miki na fi ki sanin halin
Inna, wallahi tamkar birkitatta ce tana iya cewa ina! Ba ta
yarda ba, musamman yanda ta ga hankalina yake kan
Mabarukar da ma sai' da ta dinga amso min rubutu sannan
na dangana, yanzu ga Nafisa nan ta korar min, Ja ga na
20
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
nutsu da ita, ita ma tunda na rasa Mabarukar ta shiga ta fice
ta raba ni da matata. To yanzu dama ce ta same ni, da ma
ba ni da mata, zan auro Mabaruka sannan in dawo da
matata
Та се, "Нaka ne kam, na goyi bayanka na yi gum!"
Ya ce, "Yauwa, kin ga ni ko mahakurci nawadaci,
ga shi nan Allah ya ga zuciyata ya dawo min da 1ta. Ya san
ba ni da hakki cutata aka yi, aka nuna min karfin mulkin
kudi, ga shi nan za ta dawo hannuna. Allali na gode maKa,
yau ina cikin farin ciki har.sadaka sai na yi":
Та се, "Ai ko ni ma ina taya ka, ai ina son
Mabaryka gwanda ta dawo hannunmu".
Ya ce, "Bari ki gani, ai ba zama zan yi ba". Sai ya
kwasa da gudu dafe da hula.
Ta shigo cikin gidan daidai Inna na cizgar fada da
yara, ta shigo tana cewa, "Laſiya tun daga zaure ana jiyo harshenku?"
Та се, "Bar ni da su in ci mutuncinsu tun shekaran
jiya waccan suka ze suka sayi koko, sai suka bar canjin
ashirin ba su zo sun karba ba, ke sai yau wai a bada canjin,
ki ji fa rainin wayau da ajiya suka va ni?"
Та се, "Кai Inna rigimarki yawa ne da ita, to ba
kudinsu bạ ne, don ba su zo sun karba ba sai ya zama laifi?
Ke dai tunda ba naki ba ne gurinsu ba shi kenan ba, duk
sanda suka shirya sun zo su karba. Nauyi ne ma za ki
sauke
Ta dawo kanta, "To ba zan bayar ba, sanin kanki ne
ba a bar min canji in kana son kudinka ka isaya kı karbа.
21
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
amma in ka nuna min ba ka so sai ni kuma na nuna maka
ina so, don haka alkur'an ba zan bayar ba".
Ta murtuke fuska, "Kun ji fa karfin hali?)
Yaro ya turo baki ya ce, "To ai ta ce in da sauran
koko ki zubo mata na ashirin din".
Ta ce, "Shi ma ba a bayarwa, daga yau ba za ta sake
ba". Ta shige daki abinta.
Inna Binto ta dube su, ta ce, "To ku kun ji ba za ta
bayar ba, ku yi hakuri da ina da dan canji da na biya,
maigidan yau ya fara fita kasuwa”
Suka juya suka fice da dan kwanonsu suna
gungunai. Innar ta fito tana cewa, "na suke, sun tafi din?"
Ta ce, "Sun tafi, amma dai don allah in sun dawo ki
ba su kudinsu, alkur'an in ba ki biya a nan ba za ki biya a
can
Та се, "Ко daya ba zan biya ba, na rantse".
Binto ta ce, "To shi kenan, ni dai ba ruwana, kin
gan ni na zo da farin cikina in gaya miki Malam an samu
sana'a, yau mijin Mabaruka sai ga shi da dalleliyar motar
kabu-kabu ya ba shi, ya je ya nemi kudi”.
Ta dube ta, "Allah Biniu? Na sanki fa da -shegiyar
karya, wa ke iya yin kyauta har haka? Ba na ji an ce
kudinta da yawa ba?"
Ta harare ta, ta ce, "Lallai to shi an gaya miki
matsiyaci ne, mai rowa? Su da kudin yayo su suke".
Ta jinjina kai, “Lallai na jinjina masa, kun gode. To
na sanki in za ki zo haka ki ke żuwa hannu biyu in na miki
magana sai ki ce ina kudin, to yanza miji ya samu abin yi
22
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ya bar kashe wando, in za ki zo ki dan yo min dage-dagen
nan.
Ta ce, "Za ki sha ko kin san ni in ina da shi zan yi,
ba ni da rowa. Musamman ma na abinci ban sha nono ba"
Ta sani sarai da ita ta ke, ta ce, "Za ki ci ubanki
yanzun nan, an yi rowar na ji ba ki sha nonon rowa ba,
amria dai kin yo gadon tsiya gurin ubanki da mutuwar
zuciya".
Tsam ta mike tana gyara zani, ba za ta iya zaman
fadansu da Inna ba, gwanda ta tafi-ko tukunyar da za tai
dage-dagen ta wanke.
Ta daga kai tana kallonta, ta ce, "Ko za ki dake ni
ne?"
Та се, "A'a ban kai wannan matakin ba, amma in
dai ana tafiya a haka watarana za a iya jarabta haka".
Daga baka ta wuce ta bi ta da kallo, ta ce, "Eh lallai
na gani, dote tunda mijinki ya samu sana'a dole ki yi min
iskanci za ki sani da ni ki ke zancen".
Ta juyo ta kalle ta tare da daga mata kafada, la
wuce abinta cikin isa.
Baban Mabaruka ko dam ya Jawo da aljihu, ciniki
sosai. Sai da ya dangana da kasuwa ya yo cefane ledoji har
da kaji ya yo gida jikinsa na rawa.
Da guda ta tare shi hannu biyu ta karbi ledojin cewa
yake, "Allah ya yi wa Mabaruka albarka da mijinta".
Ta ce, "Amin, amin Maiam, dage-dagen za a yi?
Ya ce, "Kwarai, a raba biyu rabin a yi farfesu da
d'an attarugu, ya yi yaji sosai
23
WAYE ANGON?-4
Ta ce, "An gama Malam
Maryam Jafar Kaduna
Mabarukar ta fito daga daki fuska a dukunzune tana
fushi, ta dube shi, ta ce, "Kai yanzu Baba da gaske ka karbi
motar bayan ya sako maka ni?"
Ya dube ta galala, ya ce, "Kanbu, amma ke 'yar
rainin wayau ce, don ubanki an min kyauta sai in mayar,
wato in ci gaba da zama cikin talauci ko? Ke uwarki tana
can cikin daula ta canza wannan ta maida wannan tana
zaune iska na kadata tana kallon kasashen waje, ni dai da
ba ki so in zauna a tsiya? Wallahi Mabaruka sam ba ki
Kaunata. Kin fi son uwarki, facaka nawa ki ka yi da kudi
kullum sababbi dal! A jaka, amma rana daya ba ki ce bari
ki sai min ko mashin ne in dinga haya ko na samar wa
Kannenki abinci ba. Shi ne an ba ni ki ke min bakin ciki
irin dai na uwarki wanda ki ka sha nono ko?"
Ta turo baki tana kumburi, kan me zai dinga zagar
mata uwa? Duk sanda ita ta masa laifi in ba yana hake da
ita ba.
Ya ce, "To wallahi zan ci mutuncinki a gidan nan
'yar bakin ciki, mota na karbe kin ga ni ma daga albarkarta
ga kaji can za ai miya, da ke kuma za a shanye ta. Aure
kuma ina ruwana yai ta mutuwa tunda kin ce ba ki sonsa
kin fito, to ni kam ba zan miki dole ba, da ma ke ce mai
zaman, don haka kina gama idda zan aura wa Sulaiman ke,
shi ke nan magana ta kare in ce dai shi ki ke so ko?"
Ta daga kai alamar ch, ya ce, "To an gama. Ban
wuri in wuce.
24
WAYE ANGON?-4 Maryani Jafar Kaduna
Татабс уa wuce yana cewa, "Ni dai tunda ya ban
abin sana aa ya gama min komai, me ya rage?"
Inna na fama da yanka kaji, ta ce, "Babu zance ya Kare".
Ko ba komai ranta ya mata dadi tunda ya ce zai
aura mata Sulaiman to alhamdu lilla, tabbas tana ji a jikinta
ta rabu da Imran kenan har abada, nanatacce kawai za ta je
ta yi rayuwarta mai dadi da 'yanci gidan masoyinta
Sulaiman, sai dai matsalarta daya fushin Mommynta yana
damunta, dole sai ta nemi yafiyarta da amincewarta da
auran Sulaiman din, sannan ta lalubo aminiyarta Rafi'a su
shirya.
Wannan ke nan.
BAYAN KWANA ARBA'IN
Kadan ya rage ta gama iddarta har zuwa lokacin ba
ta samu saukowar Momyn ba, abin yana damunta, yakan
hana ta sukuni, ko ya ta ke farin cikin ta bar gidan Imran,
shi kanshi imran din ya dauke kafa daf! Tamkar ba a yi shi
ba. Yana can yana addu'a duk da har yanzu Mabaruka na
ransa, duk bayan second sai ya tuna ia a kullum tamkar ana
Kara masa sonta. Jefi-jefi yakan leko Baba Hamza a
kasuwarsa su gaisa yana kara ba shi kwarin gwiwa.
Yau tana da lecture don haka ta alkawarta wa kanta
tana fitowa za ta dangana da gidan Momy kamar yanda ta
ke kusan kullum, a yau ta bambanta da sauran żuwan da ta
ke, don a yau sai ta baro gidan da yafiyarta. Mamanta ce
tana sonta, tana ranta ta tabbata don haka kuka za ta mata
25
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ba za ta kuma bar gidan ba ko da za ta kore ta, don haka da
shirin haka ta fito.
Abin ya zame mata biyu, ita kanta Rali`a fushifushi ta ke da ita, sama-sama sukė gaisawa duk da wajen
zamansu daya, sai ta kirga maganarta da ita kan su fito
school, daga ch, sai a'a. ita ma sai in ita ta tambaye ta, sosai
Rafi'a ta yi baya da ita, ta daina sakar mata fuska, wai duk
don ta bar gidan Imran, wannan wane irin so suke masa?
Rafi'ar da labari gurinsu kamar ba zai kare ba, a da da kyar
suke rabuwa, wani lokacin ma sai daya ta bi daya gidansu
don su karasa labarinsu, kowa ya sansu ya san kusancinsu,
suna ba mutane sha'awa da dama, amma lokaci guda Imran
ya shiga tsakaninta da makusantanta wadanda ta fi kowa
sonsu, ga Baba Hamza sam ba ya amsa gaisuwarta fushi
yake da ita sosai.
Ta ja tsaki cike da jin haushin Imran din, tsanarsa
na kara karuwa a ranta, ta furta, "Allah ya isa". A fili,
yayin da idanunta suka yi kwalkwal har mai adaidaita
sahun da ya dauko ta ya juyo ta yi saurin dauke kanta zuwa
gefe don ma kar ya lambaye ta dalili. Ta dawo da kudi
sosai gida, amma saboda makarantarta 'yan hidimomin
abin hawa duk sun kare, sannan in ta dawo gidan ta tarar an
yi abincin da bai mata ba, musamman ma Inna Binto ba
wani gogewa ta yi da girke-girke ba. Ita ko ta saba cin
abinci kala-kala mai dadi, wanda an kashe masa kudade,
amma wannan a yi dai en wai nan ma an yo cefane kenan,
don haka ta gwammace ta bada a siyo mata ko indomie ce
da kwai ko kayan tea. Duk a haka ta karar da kudin,
26
こ
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
yanzun ne da ba ta da su in za ta tafi makaranta Baban ke
ba ta naira dari kullum. Sosai yana ganin kokarinsa har
naira dari kullum? Don haka ta fara gane kurenta, sai dai in
za ta je ta hau adaidaita sahu naira saba'in ba maganar shan
cock ko Maltina da ta ke a makaranta, wannan ka'ida ne
kafin a tashi ta sha robobi in ta ji yunwa ne sosai ta ci
chiefs. Abincinsu kenan ita da Rafi'a, to yanzu ba kudi sai
dai ta dinga hade miyau in wasu na sha, ga rashin koshi da
ba ta ji ba ta fito haka nan ta ke shan kokon Inna ta hada da
alalar ashirin ta fito, har ta koma ba za ta sake cin komai
ba, ko za ta kai yamma. Sai in za ta dawo ta hawo bus naira
talatin a sauke ta bakin titi can-can nesa da gidansu, sai dai
ta tako a kasa, ga rana ga yunwa hade da gajiya. Hakan ya
sa duk ta yi baki ta fada zuru-zuru sai dogon hanci kamar
an dasa shi, fuskar ta rage kumari da dan taushi-taushin
nan, wanka ta koma da sabulun wanka dan ashirin bare a
zo ga wanki, sai ga ta da durkuso tana wanki da kyar da
kyar a ta gama dafe da kugu, tunda ta ke rayuwarta sai dai
ta wanke under wear dinta ta koma ta kwanta tana canza
channel gefe ga drinks mai sanyi tana kurbawa.
Shara, wanke-wanken Inna da Fan karan wanki duk
ya koma kanta. Ta ci wuya da rana, da dare ta kasa bacci
saboda sauro ga dankaren zafi, gefe kuma zarnin fitsarin
kannenta da tusoshinsu mai kumbura ciki. A haka ta ke
bacci mawuyaci, sai ga ta da gyangyadi a school ana tsaka
da lecture, ta sha iskan fanka. Gefe kuma Baban da ya shigo korafinshi duk ita ke cin kudinsa, a ce kullum sai ya
ba ta har naira dari ga na siyen alalarta naira ashirin, gefe
27
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ga omo da sabulun wankinta, shin karatun ma dole ne, ba
za ta bari ba?
Ta kan shiga daki ta ci kuka ba wacce ta ke tunawa
ssai Momynta, rana daya ba ta taba gajiyawa da ita ba. In
za ta je school kullum sai ta ba ta dari biyar kawai don shan
coca cola dinta da ta sanda shi ba don lalurar makaranta ba,
ko shan mai ga motarta nan na jira an wanke an goge dal
tana dalle ido, idan ko Daddy ne zai mata sallama dubu uku
ec zir! Wai ko da wani abu ya taso a kullum kenan. Bayan
hidimar makaranta yana yi tun tana nursery, sannan duk
wata sai ya aje mata dubu ashirin saboda bukatuwarta a
matsayinta na 'ya mace, bayan haka nan ma sai ya ba ta
dubu biyar ko goma wai ta sai cakulet, sutura ko sai dai ya
dauke ta a mota in yana da lokaci ta yo shopping kowane ta
ke so, mai tsada. Zuwa yanzu ga kayan nan duk sun dafe
don ba ta iya wanke su su fita.
Haka Mommyn kullum da abin da za ta kawo mata,
kyalkyal ne ko ko na ci ne, har tambayarta ta ke, ba abin da
ta ke bukata ko na makaranta? Rana daya ba ta taba gajiya
da ita ba duk da wasu ba hakkinta ba ne na ubanta ne,
amma shi don yana ba ta naira dari jal ba ma isarta suke ba,
haka nan ta ke jalaulautawa har sai ta hada da Allah ake
daukarta, amma gani yake duk ta takure masa, bayan kudin
da yake samowa a sanadin motar da aka kawo masa duk
sanadinta yakan samo sama da dubu biyar a rana,
musamman akwai shi da naci sai ya kai sha daya na dare
bai dawo ba, ga shi ba raina fasinja yake ba, ko kudin da za
28
WAYE ANGON?-4
a
Maryam Jafar Kaduna
ba shi ba su kai sun kawo ba shi dai kar ciniki ya wuce
shi, amma yana ganin naira dari ta tsaya masa a rai.
Ta sa hijabin jikinta ta goge hawaye tare da cewa,
"Allah ka yafe min, ka sa mahaifiyata ta saurare ni ko na
samu saukin masifar da nake ciki".
Ta dubi kafarta har ta fara kaushi, ga kanta duk ya
dankare ya karairaye saboda arshin saloon din da aka sabar
masa akai-akai.
Bayan sun iso ta fito da kyar ta karaso class saboda
azabar ciwon kan da ke damunta na rashin bacci, ga kokekoke. Rafi'atu ta riga ta zuwa don har an fara lecture, ta
sani in dai an riga shiga in dai uncle Tukur ne to dole ka
!saya waje sai ya ſito, don haka ba ta ma nemi ya yi hakuri
ba ta ja baranda ta rakube, hawaye na on zubowa in ta tuno
yanda ta ke żuwa da wuri har maigadin da ke bude musu
classes ta kan riga shi zuwa, don haka key din class dinsu
ya komä hannunta. Duk wani lecturer yà santa da kokari, a
nan za a same ta ta kwakkwafe wa books cinta, ita ce ta
farko a class din, haka tunda ta zo makarantar har tana
shekarar karshe a digirinta ba ta taba samun carry over ba
ko test ba ta taba faduwa ba bare a ce ta yi missing dinta,
haka assignment amma a yanzu ta kai kan ta iso wani
lokacin an gama test ko summiting assignment, saboda in
dai ta ce tun a cikin unguwarsu za ta hau adaidaita sai dari
amıma, in ta tako zuwa titi sun dauke ta saba in da rokonta
kamar la musu kuka. To kan ta iso titin sai ta ci minti
ashirin, shi ko Baban tunda asuba ya fice ba ta ma tarar da
shi bare ya rage mata hanya. Ilawayen suka ci gaba da
29
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
zuba, Uncle Tukur ganta sosai ya yi mamakin
canzawarta test da ašsigment dinsa duk ba ta yi ba zai yi
sammako ya yi saboda 'yan latti to duk ba ta a ciki, sabanin
da ko ma dai mene ne akwai dalili, ya bar wa kansa. Don
haka ya leko ya kira ta.
Ta yi saurin goge hawayen, ya ce, ta shigo kawai.
Ta masa godiya ta shige da sauri, ta zauna scat dinsu ita da
Rafi'a. ta dube ta, ta ce, "Ashe kin zo?"
"Um!" Kawai ta ce, tare da maida kanta zuwa
window saboda tausayi da ta ke ba ta in har ta kalle ta za ta
iya mata kuka.
Ba ta ce komai ba sai ta rausayar da kai tare da
dauke kanta zuwa jakarta tana lalubo handout idanunta na
shirin sake zubo da hawayen na tausayin kanta, ganin
yanda Rafi'a ta sauya mata sosai.
Har aka gama lecture magana ba ta hada ta da ita
ba, sai lokacin da suka samu dan hutu duk aka fita zuwa
capteria. Rafi'a ta mike tana cewa, "Matsa na wuce".
Ba ta ce komai ba ta rabe ta wuce abinta. Ta yi
zaune jugum, yunwa na kwakwalarta, ta san ba ta da ko
biyar bare ta iya fita ita ma, sai ta kalli can ta kalli can
kwalla na taruwa a idonta. Ta kalli hijabin jikinta duk ta yi
yaushi ba wankin kirki bare maganar guga, tuni ta aje
gyaluluwa a ganinta ba kwalliya jiki duk rame me za ta sa
wa gyale ai mata dariya, ta gwammace ta zura hijabi.
Can bayan an daddawo sannan Rafi'ar ta dawo, kan
desk ta dire mata robar cock kamar yanda ta sani lana
30
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
sonta.
31
Kallonta ba ta yi ba ta zauna tare da cewa, "Ga shi
nan
Ta kalli cock din ta kalli Rafi'ar, tabbas tana
bukatarta kwananta nawa rabon da ta sha? Tana
wkadayinta amma yanda aka mata kyautar ya sa ta fitar
mata a rai tamkar ta roka ita da ta ke kusan sayen katan
tana rabarwa duk kawayensu, yau ita ce a ke ba a
dangware? Ta share hawayen tare da duban Rafi'ar ta ce,
"Ban cancanci haka ba Rafi'a, ba Cock nake bukata ba,
fuskarki nake so da dariyarki na fi bukatar hakan. Amma
Rafi'a duk kin canza min, kin dauke min fara'arki da
tausayinki, kin manta ni Mabarukarki aminiyarki, komai na
yi ya kamata ki min haka ko kowa ya ki tausaya min ya
kamaia ke ki tausaya min, in kin luna soyayyar da ke
tsakaninmu. Kar ki manta haka, dubar ni fa, dubi yanda na
dawo na lalace na rame, duk sanadin fushinku ke da
Momy
Ta fashe da kuka, "Wallahi ina bukatarki Rali’a, ina
son kulawarki".
Ta dora kanta saman kafadar Rafi'ar tana ci gaba da
kukan.
Tun sanda ta fara maganar Rafi'ar ke kuka, kukan
tausayin aminiyarta har ta gagara rike kukan ta fara yi da
sauti. Ba Mabarukar ba ita kanta tana bukatarta kusa da ita,
ba ta saba da rashinta ba. Ta juyo cike da kukan ta rungume
ta Kam tare da cewa, "Ni ma ina sonki, wallahi ina
bukatarki kusa da ni
Suka rungume juna tare da kukan.
31
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Esawon lokaci ta daga ta tana share mata,
liawayen ya isa haka nan Mabaruka, kar kanki yai miki
CIWO
Ta dube ta da jajayen idanunta, ta ce, "In ba ki son
kaina yai ciwo me ya sa ki ka min haka, kin daina damuwa
da ai ko?"
Ta kamo hannuwanta cikin kulawa ta ce, "Ko kadan
kuilum kina raina, ya ki ke, me ki ke yanzu? Abin da ki ka
yi ne Mabaruka ban ji dadinsa ba, Imran ya wuce ki masa
haka idan ki ka tuno halaccinsa gare ki ko ba ki sonsa kin
zauna ko don haka, in ba ki wa Momy biyayya ba. lyayс
daraja gare su da girma Mabaruka, ban taba tunanin za ki
ki abin da Momy ke so ba har ki fito gidanki duka yaushe
ki ka je, kwananki nawa? Kin manta irin wahalhalun da aka
sha kafin auran? Ta tsayu a kanki ta dage ba ta huta ba duk
don ta kai ki gidan da ba za ki da kin sanin zuwansa ba.
Bayan kin je din zagi, rashin tarbiyya, gallazawa da danne
hakki ba abin da ba ki ba. Momy ta fada min komai, ki
duba irin zagi na rashin tarbiyya da ki ka dinga masa tun
daga Mamansa wacce ba ta da rai a halin yanzu, har zuwa
gurin Babansa wanda ya miki abin d.. ita kanta Momyn ba
ta miki ba, ke ma ba za ki iya wa kanki ba. Ya dago
rayuwarki, ya so ki, ya gatanta ki, ya ba ki duk jin dadin
rayuwa bayan ya hada ki da `ya'yansa bai bambance ba,
amma ki ka zage tas! Kan lallai sai an sake kı, haba
Mabaruka ina tarbiyyar da Momy ta dade tana ba kı, kin
watsar duk don an daura miki Imran wanda bar yau ban ga
35
3
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
aibunsa ba, ban ga abin kinsa ba, me ya sa haka? Me ya sa?
Ko yana da wani aibu?"
"A'a".
Ta girgiza kai da sauri tana kuka tare da cewa,
Та сс, "Тo don me ki ka ki zaman gidansa? Don kin
fi son zabin zuciyarki a kan na Momyn?"
Nan ma ta girgiza kai, "A'a".
Та се, "Don ki bata masa, ki bata mata ko
Mabaruka?"
Ta kara fashewa da kuka, ta ce, "A'a na tuba Rafi'a,
na yi nadama wallahi na yarda zan koma gidansa duk da ba
na sonsa ko da zan