sai na koma na ci gaba da zawarci, ba lallai kuma na
kirki ya zo ya aure ni ba, wani ma in ya ji aurena biyu
shekaruna kuma kwana na daya gidan mijin, ba zai yarda
ya aure ni ba, don duk me za a ce ni za a ga ban kyauta ba,
ni ke da laifi".
Ta ce, "Haba! Haba ba ma fata ma, insha Allah ba
inda za ki, kina nan gidan Sulaiman tunda yana sonki, ba
zan yarda ya yi sakin ba”.
Ta dube ta, "Mata nawa ya saka kafin ni, kuma
yana sonsu?
Ta kasa cewa komai, ta bi ta da ido, haka suka wuni
tare, Rafi'ar na kokarin kwantar mata da hankali.
Yayin da Sulaiman tun fitarsa bai dawo ba, ya yi
nesa da gidan, ya yi wa kansa alkawarin sai dare zai dawo
sannan ya san Innar ta yi bacci.
Haka kuwa aka yi, goma ta wuce sannan yà shigo
gidan. Ya maida kofar gidan ya rufe da sakata, ya cire
takalma ya sadada ya shigo, Inaa na kwance tsakar gida
tana shan iska da dakun shigowarsa. Ba ta sani ba bacci ya
yi awon gaba da ita, zuruf! Ya shige dakin Mabaruka ya yi
azamar murza key har da sakata.
Firgigi Mabaruka ta bude ido daga wahalallen
baccin da ya fara daukarta, ya zauna kusa da ita yana
fara'a.
"Har kin fara bacci ne Mabaruka?"
83
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta tashi zaune tana murje ido, ta се, "Еh".
Ya ce, "Ki yi hakuri don Allah Mabaruka ba haka
na so mu kasance ba daren farkonmu, wallahi wata matsala
ce ta sha kaina tsakanina da Inna, amma komai ya yi daidai
za mu ji dadin aurenmu kin ji ko?"
Ta yi kasa da kai kurum tana sauraronsa ba ta се
komai ba.
Ya leka fuskarta, "Ba ki ce komai ba Mabaru?"
Ta ce, "Na ji, shi kenan".
Ya yi dariya, "Yauwa amaryar, me ki ka ci ne?" Ya
Tada yana waiwaye ko zai ga alamar wani abu.
Ta ce, "Ba na jin yunwa, ban ci komai ba".
Ya ce, "Haba dai, kin ci dai wani abu ko ya ya ne,
ga kazarki ma ban kawo ba, ta jiya matsala aka samu da
ila".
Та се, "Ва komai”.
Inna kuwa a cikin baccinta ta fara mafarki kusan
irin na jiya.
Mabaruka bakin rijiya tana jan ruwa za ta shiga
wanka.
Inna na zaune tsakar gida duk tana kallonta, ganin
ta sungumi bokitin ne za ta shiga wanka ya sa ta mike ta
tare ta tana cewa, "Ke tsaya!"
Ta isaya tana kallonta bayan ta aje bokitin, ta ce,
"Na tsaya me ye?"
Та сс, "Ме ki ke nufi ne? Kin gama tuwo kin
kwashe da kanki alhalin kin san ba tsarin gidan nan kenan
ba?"
84
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta kalle ta a wulakance, ta ce, "Tsarinki na da
kenan, kin wa wasu, amma ni na rantse ba za ki min haka
ba"
Ta сe, "Karya ki ke, ba mai ikon yin wani abu gidan
nan sai da amincewa ta”.
Ta ce, "Ai kuwa sai ni Mabaruka, kuma za ki gani"
Samira ta shigo tana cewa, "Ya ya dai, me ke
faruwa?"
yi".
Inna ta ce, "Yauwa shigo ki gani, wai dukana za ta
Samira ta ce, "Ita din wa? Yo akwai mai taba min
ke na kyale shi ko wane ne?"
Ta ce, "Sai ni kuwa, matukar ba ta daina shiga abin
da babu ruwanta ba".
Fada ya kaure tsakanin Samirar da Mabaruka,
karshe Mabaruka ta daga bokitin wankanta da nufin ta
tsiyaye shi a kan Samira, ba tai aune ba sai a jikin Inna.
Ta yi tsamo-tsamo cikin ruwa, dukkansu suka bi ta
da kallo.
A firgice ta tashi daga baccin tana cewa, "Ina! Kai
wallahi 'yar nan kashe ni za ta yi in har ta ci gaba da zama
gidan nan, akwai mugun nufi a ranta".
Ta sa hannu tana sharce gumin da ta yi, ta saurara
da kyau tana jiyo 'yan maganganu a dakin Mabaruka. A
firgice ta mike ta nufi dakin tana cewa, "Ba dai yaron nan
ya dawo ba ya shiga dakin, ina nan baki hangame ina
bacci?"
Ta fara dukan kofar iya karfinta.
85
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Dukkansu suka zabura, musamman Sulaiman ita da
ma ta san sai an yi haka, sai ta zo. Hai kuwa ta fara fada,
Waliahi, wallahi idan ba ku bude kofar nan ba sai na tsine
maka albarka".
Tsam Mabaruka ta mike ta je ta zare sakatar, shi
kuwa zuwa yanzu ya sadakas ya bar wa Allah, Inna ba za ta
taba barinshi da Mabaruka ba, in dai yana son zama lafiya.
Ya dafe kai yana jimami, ta bi Mabarukar da harara,
"Kauce ban wuri munafuka, kin kurmuso min da ciki ko?"
Ta kauce a sanyaye.
Inna ta wuce ciki, ta tsaya gabanshi tana kallo, shi
ma ita yake kallo.
Ta miko masa hannu, "Ba zan ce da kai komai ba,
ba ni takardarta".
Ya kalle ta da mamaki, "Inn..."
Ta katsc shi, "Wallahi! Wallahi sai ka sake ta
yanzu, ni za ka raina wa wayau Sulaiman, ina kwance
hagaga da baki ka safado ka shigo gurinta bayan na yi
maka iyaka da ita?"
Ya yi shiru dai dafe da kai.
Ta ci gaba, "To ida.. har ni na haife ka ka dauke ni
uwarka ka sake ta tun kan na tsine maka albarka".
Ya dube ta, "Amma Inna..."
Saukar mari da ya ji shi ya rufe mishi baki. Ta се,
"Bana son jin wata kalma daga bakinka face furta mata
saki, in kuwa ba haka ba na ji wata kalmar tsinuwar Allah
da ta ma'aikinSa su tabbata a kanka".
86
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Jikinsa ya yi sanyi, zuciyarsa ta karaya, wasu hawaye masu dumi suka zubo masa.
Ya jinjina kai alamar gamsuwa da zancen Innar don
haka ya mike tsaye, ya tunkari gurin Mabaruka da ke rabе jikin kofar, "Mabaruka?"
Ta kalle shi a tsorace idanunta sun sauya zuwa ja, ta
ce, "Na'am?"
Ya ce, "Ki yi hakuri ya dube ta,, haka Allah ya tsara
mana rayuwarmu, za mu yi aure anuna ba za mu kasance
tare ba".
Ta sunkuyar da kai hawaye na zuba.
Ya ce, "Ki je na sake ki saki daya, in kin samu miji
ki yi aure". Daga fadin haka ya fice daga dakin da sauri.
Mabaruka ta dafe kai tare da runtse ido da karfi
hawaye suka zubo.
Inna ta matso gabanta tana dariya, "To oya-oya a
iattara kayan tsafi a bar mana gida tun kan a fara aiki da su,
nan ba a samu wuri ba bare a hallaka ni, tsinanniya".
Ta kalle ta kurum tare da dade bakinta saboda
tahowar kuka mai sauti. Innar ta fice tana murna.
Sakan goma ba ta kara ua ta yayimi wayoyinta da
jakarta, ta sanyo hijabinta ta fice daga gidan ba tare da wani
ya ga fitarta ba. Ta yi sa'ar samun napep har kofar gidan
Momynta.
Kasancewar Daddy na garin ya sa ba su yi bacci ba
da wuri, tsulum suka ganta ta shigo falon. Ta ja ta tsaya
bakin kofa kanta a sunkuye.
87
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Kiaban Momy ya yanke ya fadi, ta kalli agogo, sha
daya da rabi, ta ce, "Ke daga ina ki ke ke da wa?"
mala.
Ba ta ce komai ba sai kukan da ke kokawar kwace
Daddy ya ce, "Come on Mabaruka, fada min mana,
me ke faruwa? Ke da Sulaiman din ne?"
Ta tako ta tsugunna gaban Momy tare da fashewa
da kuka mai karfi tana cewa, "Ki yafe min Momy,
hakkinki ne ke bina sakamakon saba miki da na yi, don
Allah ki yafe min ko na zauna lafiya".
Momy ta ce, "Ni na kasa gane me ki ke nufi,
wannan zancen ai mun dade da yinshi, na kuma yafe miki
to kuma me ya kawo zancen again?"
Daddy ya dube ta, "Ke Mabaruka me ya fito da ke
daga gidan mijinki a wannan daren, ko kuwa tare ku ke?"
Ta kalli Daddy, "A'a, ya sake ni".
Suka fada a tare, "Saki?"
Ta daga kai, "Eh".
Salati Momy ta ke nanatawa in ta sauke wani ta
dauki wani.
Daddy ya ce, "Saki, kwananki daya? A kan me? Me
ki kai masa?"
Momy ta ce, "A kan rashin mutunci, halaccin da zai
mata kenan?"
Mabaruka ta ce, "A'a ba laifinsa ba ne,
mahaifiyarsa ce ta tursasa shi".
Ta ba su labarin yanda abin ya faru.
88
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Daddy ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Well, Allah
kyauta gaba. Kar ki damu, ki kwantar da hankalinki je ki
abinki ki kwanta ki huta"
Ta mike a sanyaye ta shige ciki.
Cikin damuwa Momy ta ce, "Yanzu wannan wane
irin aure ne kwana daya? Ka ga abin da na gudar mata
kenan, kadan daga cikin halr matar kenan".
Ya yi murmushi, ya ce, "Ni wannan ko kadan bai
dame ni ba tunda ki ka ga haka akwai abin da Allah ya
shirya da hakan, ke ma bai kamata ki damu kanki ba".
Ta yi shiru tana kallon Daddy, ta yi dai murmushi,
ta ce, "To Allah ya shige mana gaba”.
Ya ce, "Shi kenan kuwa".
Kafin ka ce me, zance ya bazu ai Mabaruka ta dawo
gida, Sulaiman ya sake ta abin mamaki, kowa sai ya ce
gwanda haka, babu wanda ya yi bakin ciki, haka ita ma
wani farin ciki da walwala ta ke ji a ranta, tana ji kamar ta
rabu da kaya.
Imran kuwa ya ma fi kowa, jikinshi na rawa ya nufi
garin, ko da ya zo Daddy da Momy suka tsayar da shi kar
ya sake ya tunkare ta da wata magana, kawai su gaisa
akwai abin da suke shiryawa. IHaka kuwa ya shigo har
dakinta, sam babu fara'a, ya 6oye murnarsa da zumudin
ganinta, ya dube ta, ya ce, "Sannu, ya gida?"
A sanyaye cikin rashin jin dadin yanda yai mata, ba
ta tsammaci haka ba, da tana murna ga shi ya zo kila ma su
89
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
daidaita, dole murnarta ta koma ciki, ta ce, "Lafiya lau,
ashe ka zо?"
Cikin ko'in kula ya ce, "Eh, an ce kina gida kin
dawo, da zan wuce Momy ta ce in zo mu gaisa".
ko?"
Ta ce, "Eh haka ne, na gode".
Ya ce, "Ba komai, Allah kyauta gaba. Sai anjima
Bai saurare ta ba ya fice, da ma a tsaye yake.
Ta yi kuka tamkar ranta zai fita, ta yi nadamar da ba
ta yi ba a da, sai a ranar ta sake tabbatarwa ta yi babban
rashi, Imran yanzu ba nata ba ne. haka Rafi'atu ta zo ta
same ta, magana daya ce dai Rafi'ar ta ce, "Me na taba
fada miki? Watarana sai kin yi kuka matukar ki ka yarda ya
kubuce miki. Ya Imran ba na yarwa ba ne, amma ke a
kullum cewa ki ke ba kya sonsa, ba kya sonsa, ke..."
"Ina sonsa yanzu". Ta katse ta.
Ta bi ta da kallo.
Mabaruka ta kara cewa, "Wallahi ina sonsa sosai,
ina jin kamar-zan mutu idan na rasa shi, amma shi ya daina
sona, na san kila wata yake so
Та се, "Ai kuwa don un gaisa ma da matar а
waya, ba ki ji ta ba muryarta mai dadi".
Ta birkice, ta kasa sarrafa kanta sai kuka. Duk
yanda Rafi'ar ta so ta lallashe ta amma ina! Kan dole ta
kyale ta a haka ta fita.
A falo ta same su dukkansu, Daddy da Momy,
Imran din ta shaida musu yanda sukai. Abin yai musu dadi,
90
17
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
musamman Imran wani bangare kuma ya ji tausayinta har abada ne son Mabaruka a ransa.
BAYAN WATA DAYA
Gidan. Momy kacame yake da 'yan biki, har
Sharifa. Su Rafi'atu ba zama, karfe biyu aka daura wa
Iran aure da amaryarsa. Hauka, kiris Mabaruka ta kusa yi,
ta tsure, ta rame karshe ma ta kulie kanta a daki tana kuka
cike da nadama babu wanda ya kula da ita, sai hidimarsu
suke.
Sai da magriba Imran ya iso a shigarsa ta ango, har
dakinta ya shigo tana kwance a gado ta ci kuka har ta gaji
ta kode, sai ajiyar zuciya ta lumshe idanu.
Babban yatsanta ya ja yana dariya, a firgigi ta bude
ido ta tashi zaune. Ta bi shi da kallo cike da mamakin
ganinshi a dakin. Za ta yi magana ya katse ta, "Shissss".
Dole ta yi shiru ta bi shi da kallo.
Hannunta ya jawo yana cewa, "Zo mu je ki raka ni
wani wuri".
Ba ta yi musu ba ta bi shi suka fita, har ya sa ta a
mota, ta dube shi, ta ce, "Ban fada wa Momy ba".
Ya ce, "Kar ki damu, ta san da fitarmu".
Ita dai abin ya daure mata kai, ta dai shiga ya ja
suka tafi.
Gidan da ta tsana ta kyamata a da, wato gidan da ta
taba zama nan ta ga ya tsaya da mota. Ya fito ya zagayo
bangarenta ya miko hannunsa, ya ce, "Zo mu je".
91
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ba ta musa ba ta mika masa ya kamo ta, da za su
shiga ya dube ta yana dariya, ya ce, "Ki shiga da kafar
dama ki yi bismilla".
Ta kalle shi da sauri da mamaki.
Ya ce, "Eh, ko ba haka tsofafli ke cewa ba?"
Zuwa lokacin ta gama ganewa, don haka ta yi
dariya ta yi yanda ya се.
A bedroom dinsu suka tsaya ta yi mamakin yanda
aka sauya gidan, haka kayan dakin duk an sauya sabbi.
Ya zaunar da ita yana cewa, "To Mabaruka, Ya
Imran yau ga ki a gidansa a matsayin mijinki karo na biyu”.
Kawai sai ta ji hawaye na zuba. A rude ya tsuguna
gabanta ya ce, "Kuka kuma Mabaruka? Na mene ne?"
Ta ce, "Na dadi Ya Imran, ban cancanci haka ba,
kai wane irin mutum ne mai mantuwa da cin fuska da
wulakancin da nai maka?"
"Mutum kamar kowa sai dai mai tsananin sonki fiye
da kowa, ba zan iya daina sonki ba ne Mabaruka bare na
kyale ki, shi ya sa na dawo karo na biyu, ban kuma samu
matsala da su Momy ba suka goya min baya. Kowa na farin
ciki da aurenmu Mabaruka, ya ka:nata mu fi kowa".
"Na gode Ya Imran, ni ma ina sonka so mai tsanani,
na shiga damuwa da jin wai ka samu wata, bare yau da na
tsammaci da wata aka daura maka aure".
Ya ce, "Har abada ke ce kadai ba wata, daga mu sai
va'yanmu.
92
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Farin ciki ya cikata, da gudu ta fada jikinshi tana
dariya. Ya maida hannaycnsa bayanta ya rungume ta kam a
kirjinsa.
Wani farin ciki ya dinga ratsa kowannensu, a
wannan daren sun raya shi da farin ciki cike da kewar
junansu, tare da yi wa junansu alkawurruka na har abada.
Sun bar su Momy da kowa cikin farin ciki da
komawar aurensu, kasancewar babu iddar Sulaiman a kanta
ya sa aka maida auren bayan wata daya da fitowarta daga
gidansu.
*** *** ***
Labari sabo mai dadi ya barke tsakanin Rafi'a da
Mabarukar da yanda aka daura auren duk ba ta sani ba.
BAYAN WATA BIYU.
Cikas daya da suke samu shi da Mabaruka da ya yi
nisa a Lagos sai lokaci-lokaci yake zuwa, amma dai suna
kasancewa a waya koyaushe. Satin da ya zo sun sha bikin
Rafi'atu sun gaji, a falo suke kwance yana mammatsa mata
jiki har wani zazzabi-zazzabi ta ke ji.
A talabijin kamar a mafarki ta ga an nuno Inna ba
don ta gane ta ba sai don hotonia da aka nuno, gabadaya
halittunta sun sauya.
Mai labarin yana cewa, sun samu labarin matar
danta ce ta yi yunkurin hallaka ta da ruwan zafi sakamakon
takura musu da ta ke, don haka ta gaji ta tanadi hukuncin da
za ta mata duk da ita ta sa aka auro ta. Aurer dai bai wucе
93
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
wata daya ba, a yanzu tana cikin wani halin neman taimako
ga duk wanda Allah ya hore wa don yi mata aiki.
Mabaruka ta sauke ajiyar zuciya, ta dubi Imran, ta
cc. "Yanzu me ye ranar wayonta da dabararta na ba za ta
bar danta ya zauna da matar da yake so ba? Ga shi dai
yanzu ita ta kawo matar.
Imran ya ce, "Allah kyauta, izina ne ga masu irin
halinta"
Ta dube shi a sanyaye.
"Please my Imran, inda abin da za ka iya ta
Gangarenka ka yi don mu taimake ta ba don halinta ba".
Ya nutsu yana kallonta, ya sauke ajiyar zuciya, ya
ce, "Well Allah ba ni iko".
Ta yi dariya, "Amin, ni kuma ta. bangarena insha
Allah sai na yi iya. kokarina na dawo masa da matarsa
Nafisa"
Mikewa ya yi ya sunkuce ta zuwa bedroom dinsu
yana cewa, "Amin to".
WASHEGARI
Har sha daya na safe ba a tashi ba sabanin da da ta
ke riganshi tashi don shirya musu abin kari. Bai damu ba ya
fice falo yana kallo, a tsammaninsa gajiya ce.
Ganin lokaci ya ja ne ya sa ya mike ya shiga dakin
ya ga lafiyarta
Da sauri ya karasa gurinta yana cewa, "Lafiya ki ke Mabaruka?"
94
WAYE ANGON?-4
Imran"
Maryanı Jafar Kaduna
Tana karkarwar sanyi ta ce, "Zazzabi nake ji Ya
Ya birkice cikin damuwa, "Zazzabi kuma yanzu da safen nan?"
Ta ce, "Eh". Kanta cikin bargo.
Da sauri ya fice falo ya dauko wayarsa, ya kira Dr.
Faruk. Da jin wannan kiran ya bar abin da yake ya iso
gidan da 'yar jakarsa.
Ba tare da bata lokacinsa ba ya fara aikinsa duk
wani gwaje-gwaje da ya kamata ya mata, musamman
zargin da yake. Ya dago yana kallon Imran da ya yi kuri
yana kallonsa duk a birkice, kwakkwaran moisi ba ya yi. А
kagauce ya ke ya ji me ke damun Mabarukarsa.
Dariya ta so kufce masa, ya danne ta don ya san
matukar ta fito nausarshi zai yi, don me zai dinga masa
dariya, Mabarukarsa ba lafiya, farin ciki ma yake ko abin
bai dame shi ba? Don haka ya fauze tare'da saukar da ajiyar
zuciya har da yarfe guni, ya rike kugu ya yi shiru.
Ya kalle shi a fan firgice bakinsa na rawa ya ce,
"Me... me ke damunta?"
Gabadaya yanayinsa ya sauya ya birkice, kana
ganin kwalla na son taruwa a idonsa.
Ya dafa kafadarsa cikin rarrashi ya ce, "Calm dowп
my friend ba wani abin tashin hankali ba ne, ka sa Allah a
lamuranka zai kawo muku da sauki, amma sai ka fa dage
da addu'a".
Ya sake rudewa, ya juya yana kallon Mabarukar da
ta ke kwance sharaf ba karfi jikinta, baki ya bushe, уa се,
95
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
"To amma me ke damunta, wacce cuta ce ta kama min
Mabaruka?" Ya fada kwalla na cikowa ta?
Ya kasa cewa komai ya dai tsura masa ido, ya sake
rike shi a gigice yana cewa, "Fada min Docter, ina son
Mabaruka, bana son na rasa kanta, zan iya ba da komai da
na mallaka don lafiyarta raina fansa ne gare ta, amma ka
fada min wacce cutar ta kamata?"
Ya saki huci ta baki tare da cewa, "Na sani za ka iya
komai don ita, kowacce kasa za ka iya zuwa ba wani kasa
za ku je ba illa India don su ke da wannan kayan aikin
lalurarta, bana son fada maka Imran, don na san kunnenka
ba zai iya dauka ba, yanayin da za ka shiga ina tsoro ka
kwallafa wa ranka Mabaruka da yawa, ka dinga ragewa
saboda irin haka.
Hawaye suka zubo masa, ya ce, "Ba zan iya ba,
Allah ne ya sa min sonta da kwallafarta, kuma Shi zai ba ta
lafiya insha Allah yanzu muka fara rayuwa sai mun jima ni
da ita kafin Allah ya dauki ranmu”.
Tsoro ya kama likitan, ya baza idanuwa yana
kallonsa, can dariyar da yake rikewa ta kwace masa ya
fashe da dariya tare da dukewa dafe da ciki. Ya fada kujera
ya zauna yana ci gaba da dariyar.
Gogan naku ya zo wuya matuka, ya dinga kallonsa
kamar zai makure masa ashe akwai mai dariya idan
Mabarukarsa ba ta da lafiya? Ya taso yana kallonsa, ya cе,
"Haba abokina, haka ka ke son Mabaruka, ba fa mutuwa za
ta yi ba. Tabbas na san in ka ji abin da ke faruwa da ita za
96
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ka shiga wani yanayi, amma me? Sai ka ba ni goron albishir kato kuma".
Ya ce, "Look Faruk, bana son wasa, just ka fada
min matsalar matata in ba za ka yi ba zan kira wani
simple.
Ya yi murmushi, ya ce, "Ok, congratulation!" Ya
mika masa hannu suka yi musabaha, ya ce, "You'll become
father, your Mabaruka she's pregnant 9 weeks". Ya
karashe yana kallonsa.
Sakin baki ya yi yana kallonsa, ya kasa sakin
hannunsa, ya rasa wane yanayi yake ciki, mamaki ko farin
ciki? Da kyar cikin nauyin baki ya ce, "You mean my
Mabaruka tana dauke da cikin dana?"
Ya jinjina kai tare da cewa, "Ofcourse, zan tabbatar
maka shi a takarda".
Wasu hawayen dadi suka zubo masa, ya lumshe
idon yana murmushi. Ya yi godiya ga Allah marar adadi, a
ransa shi kadai ya san me ya ce, ya juya yana kallonta,
wacce ta ke a kwancen har lokacin, ta lumshe idanu. Ya
karaso inda ta ke tare da durkusawa gabanta.
Ya yi tsai yana kallouta tamkar ranar ya fara
ganinta. Wani sabon sonta na kara shigarshi, tausayinta da
kaunarta na kara shigarshi, farin ciki ya cika shi, shin wace
murna zai yi a rayuwarsa Allah ya sa masa masifar son yara
a ransa, duk inda ya ga yara suna burge shi, to ina ga nashi
ne, kuma sun fito daga jikin Mabarukarsa? Wannan wane
irin dadi ne? Yana son duk abin da ya shafi Mabaruka to
ina ga ita ta haifa masa yaronsa? Hawayen dadi suka zübo
97
WAYE ANGON?-4 Maryamı Jafar Kaduma
masa masu dumi, ya sunkuyo daidai labbanta ya sumbace
ta, ya yi jim idanunsa a rufe, hawayen na zuba, ya kasa
janye bakinsa a kan páta. Ganin haka ya sa Dr. Faruk ya
fice yana dariya. Tabude idon a kasalance ta ganshi ta sa
hannunta cikin sumarşa, ta ce, "Mene ne?"
Ya janye Bakinsa tare da kallonta çikin sabon
yanayin soyayyarta, ya ce, "I love you Mabaruka
Ta yi murmushi takaitacce, tana kallosa a kullum
tana karbar wannan kalmar a gurinsa fiye dr sau dubu, kai
ba ma za ta iya lissafawa ba, motsi kadan zai ce ina sonki
Mabaruka.
Тa сс, "Na sani Ya Imran, kullum haka ka ke fada
bayan ka yi shi a aikace ina ganin son a kwayar idonka".
Ya sa hannu yana shafa fuskarta, ya ce, "Na yau
daban yake Mabaruka, ya fi na kullum, kin sake samun
wani gurbin da matsayi a gurina na har abada wanda ba zai
taba kankaruwa ba, sonki hade yake da numfashina da
raina".
Ta sake murmushi, ta ce, "Mene ne ya Imran, me ya
sa haka?"
Ya tashi daga tsugunnen ya hayo kan gadon tare da
tarairayota ya rungume ta jikinsa kam, ya cc, "Mabaruka
kina da juna biyu har tsawon sati tara, yanzu Dr. laruk
yake shaıda min".
Ta dago tana kallonsa tsawon dakiku farin ciki ya cikata, dadi ya hana ta magana kawai sai hawayc 'yan sirara suka sirnano. Ta tsayar da idonta kyam kan nasa lana
aasa kallon ina sonka. Ya nutsu shi ma yana kallonta
98
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
tsawon dakiku, ya sa hannuwansa ya tallafo fuskarta ya ce,
"Fafa min mene ne ya sa ki kuka?"
Bakinta ya fara karkarwar son yin kukam yayin da
hawayen ke kara zubowa ta buda baki za ta yi magana,
kukan ya ci karfinta ba shiri ta fada jikinsa, tare da fashewa
da kukau tana cewa, "I love you Ya Imran".
Ya rungume ta sosai jikinsa tare da lumshe idanu
yana jin nutsuwa na sake shigarsa da kaunarta, уа сс, "I
know love you too my Mabaru').
Ta sake shigewa jikinsa tana cewa, "Ba zan iya
rabuwa. da kai ba, kai kadai nake so, ina son danka Ya
Imran.
Ya dago ta yana share mata hawayen, ya ce, "Is ok,
na sani ni ma ina son dan da za ki haifa min, haka ya sa ki
ka sake samun wani gurbin a raina. Ke kadai nake so, kin
ishe ni har abada ba zan rabu da ke ba, rabuwa da ke
tamkar rabuwa da raina ne"
Ta sake fadawa jikinsa tana dariya, shi ma ya sa
hannuwansa ya rufe ta tsam yana dariyar da jin dadi.
Sai daga baya sannan Di. Faruk ya rubuta mata
magungunan da za ta yi amfani da su saboda rashin karfin
jikin ya sanya mata drip.
Sun ci gaba da rainon cikinsu cikin nishadi da
walwala, kullum yana tare da ita, yayin da ita tana jikinsa
tana sake narke masa, ko ya ta motsa sai ya ce, "Mene ne?
Me ki ke so?"
1
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Wani lokaci ta kan yi murmushi ta cc, "I love
yor". Hakan ya sa ya dauki hutu gurin aikinsa don
samun kula da ita yanda ya kamata. Lokacin da labarin
ya je kunnca su Momy ku zo ku ga murna a ranar Daddy
kamar ya taka rawa don farin ciki, yau zai dauki jika.
Barc Momy har da kukan dadi ganin addu'arta Allah ya
karbo anafarkin da ta dade tana yi ya tabbata, tana ganin
soyayyar İmraa fin a idanunta.
Zamaa lafiya da kwanciyar hankali suke, abin da
ta ke so keaan. To yau ga shi har za su samu zuri'a
wannan mc ya fi shi dadi? Ta yi sujjada ta gode wa Allah
da yi wa Mabaruka fatan samun lafiya da sauka kalau.
Ganin yanda ta ke wahala ba ta iya in komai sai
ruwa a kwance, duk ta narke ai koke-koke ta ke masa,
hakan ya sa Daddy ya tausaya mata matuka, har fuskarta
ta nuna ya dubi Imran din ya ce, “Ina ganin za mu tafi da
ita gida kamar za ta fi samun kulawa a wajenmu.
Ba shi ba hatta Mabarukar suka zaro idanu a
gigice suna kallonsa cikin tsoron maganarsa. Bakin
İmran ya fara karkarwa da kyar ya iya cewa, "Am...
amma Daddy kamar a nan ta fi samun kula, za ta fi son
99
Ban
Ya juya a birkice yana kallon Mabarukar ya се,
"Ko ba haka ba?"
A kwance ta ke amma sai da ta kokarta ta tashi
zaune cikin irin yanayinshi, ta ce, "Eh...ch zan fi jin dadi
a nan". Ta karashe tana kallon Daddyn.
100
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya cc, "A'a ki zo mu je gida a nan kina wahala shi kuma ya tattara ya koma aikinsa, in kin ji kwari- kwari sai a dawo da ke.
Idanunsu suka kada jajir, ita kuma har da kwalla
duk ta birkice, sai ta kalli Dadyn cikin yanayin roko ta
kuma dubi Momy ta kasa cewa komai, hankalinta ya
tashi sosai don me za a raba ta da Imran, har akwai
wanda ya fi shi kula ma? Yayin