Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
7 / 10
da shi a rikice ya rarrafa gaban Daddyn idanunsa na son taruwar kwalla, ya marairaice ya ce, “Kar ku dauke min Mabaruka Daddy, hankalina ya fi kwanciya ina tare da ita, ina kuma kula da ita komai ina mata. Tambayarta ka ji, in mata wanka tare da brush, in shafa mata mai, in sa mata kaya. Sannan in ba ta abinci har goya ta nake in ta gaji da kwanciyar, in dinga mammatsa mata jiki duk don ta ji dadi, wallahi ina kula da ita". Mommy ta sunnar da kai tana dariya ganin duk ya fita hayyacinsa, yana ta zaro maganganun da shi kanshi bai san yana yi ba, duk don an ce za a tafi da ita, ta samu sauki. Shi kuma Daddy ya rufe ido, ya ce, ina! Sam ai shi da ita zai tafi. Sai ga Mabaruka ta sauko ta tsugunna gabansa ta ririke kafafunsa hawaye suka fara zuba, ta ce, "ba zan taba samun nutsuwa ba in har bana tare da Ya Imran, shi ne kadai mai iya kula da ni, ba wanda ya kai shi. Da shi naké samun kwari da lafiyar jikina, don 101 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Allah Daddy ka bar ni tare da shi kar ku tafi da ni, ni na ma warke kun gani?" Ta mike tana kokarin dauke kayan da ke gabansu za ta kai kicin, duk don ta musu wayau a ganinta, yayin da juwa ke son kamata. Shi ko cewa yake, "Yauwa Mabaruka kun gani ko, ta ji sauki". Daddyn ya bi su da kallo ganin duk sun birkice don za a raba su. Tausayinsu da dariya ya kama shi, sai dai ya dake ya ce, "Ban fa yarda ba da 'yata zan tafi, kai kuma ka kama aikinka". Bai gama rufe bakin ba ya tare shi, "Na hakura da shi daga yau na aje aikin gabadaya in ce shi kenan ko?" Mommy ta yi dariya tare da mikewa ta ce, "Mu jе Daddyn kyale su su suka sani". Ya mike yana gyara tabarausa, ya ce, "Well za mu gani a sha rana lafiya yanzu ku ka fara mu mun tafi". lafiya". Wani farin ciki da murna ya saukar musu. Suka fice su Daddyn suna cewa, "Allah kara Ba ko rakiya sai dai ya daga murya ya ce, "Sauka lafiya". Suka ja suka tsaya bakin motarsu suna dariya, Mommy ta ce, "Ka ga yaran nan ba ko rakiya". Ya shiga motar yana dariya ya ce, "Ai ba su yi murna da zuwanmu ba, tunda mun 6ata musu rai". Ta zagaya ta shiga tana cewa, "Allah kyauta to". 102 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Bayan fitarsu ta koma ta zauna jagwaf tare da fashewa da kuka, hankalinshi ya tashi ya karaso wajeata da sauri yana cewa, "Mene ne Mabaruka?” Ya riko ta Ta kalle shi da fuskar duk hawaye a marairaice ta cc, "Za su raba mu Ya Imran, kar ka bari haka ta faru don Allah". Ya jawo ta jikinsa ta fada jikinsa tare da sake sakin wani kukan, ta rike shi gam tamkar za a dauke shi. Shi ma ya rungume ta kam tamkar za a dauke ta ya се, "Ba mai rabá mu ina tare da ke ba inda za ki je ki bar kukan kin ji ko?" Ta daga kai alamar to, ya sa hannu yana goge mata hawayen. Abin nasa ya so ya koma kamar hauka, har ya shiga wata.na biyu a hutunsa cikin kuma ya shiga na hudu, ta fara warwarcwa abinta sai dai shagwaba da kara narke masa kullam tana jikinsa kwance ta ee wannan, ta ce wancan, shi kuma jikinsa na rawa zai mata ko ya siyo mata, sam ba ya gajiya da ita, hakan ya sa ba inda yake zuwa daga masallaci sai masallaci. Abokanansa sun zo da matayensu duba ta kowa da tsiyar da suke musu. Rafi'atu ma duk bayan kwana biyu sai ta zo. Sosai tana tafiya da tausayin Mabarukar don ma ta fara gyagijewa ta yi kyau abinta. Ras! Imran yake mata kwalliya da ado tamkar ita ta yi, hakan da Daddy ya gani ya sa ya mishi tas bai san da tafiyarsa ba, sai dai ya zo masa kwatsam karfe kaza jirginsu zai tashi. 103 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Ya saki baki yana kallonsa cikin tashin hankali, ya ce, "Amma Daddy Mabaruka fa?" Ya katse shi, "Me ke damunka ne? ina hankalinka da na sani tare da kai, zama za ka yi har sai ta haihu? Ba ta ji sauki ba, dube ta fa ka dauko hutu ka zo ka tare jikinta, motsin kirki ba ka bari ta yi, soyayyar kenan ranar haihuwa in ta zo kai za ka mata duk ka kashe mata jiki?" Ya marairaice ya ce, "Amma Daddy ka..." Ya ce, "Kada ka koma Imran, zauna da Mabaruka har ta haihu, in ta haihu ku ci gaba da rainon dan tare ka bar aikin kar ka yi". Daga haka ya juya ya fice daga gidan. Ya fada kan kujera jagwaf tare da dafe kai, ya runtse idanu. Ta matso kusa da shi tare da dafa shi cikin karfin gwiwa, ya bude idanun a wahalce ya dube ta. Ta sakar masa murmushi mai kayatar da shi a koyaushe, bai ji sautin fitar kalmar da ta ce ba, sai dai motsi da bakinta da ta yi ta ce, "Ilove you". Ya yi murmushi tare da jawo ta sosai jikinsa, ya sa hannu ya tallafo habarta, ya ce, "Love you too". Ta yi dariya ta ce, "Mu je in taya ka shiri ko?" Ya buda baki zai yi magana, ta yi saurin dode bakinst da nata cikin wani yanayi nata. Tsawon lokaci 104 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna suna haka, sannan ta mike tare da kamo hannunsa, ta ce, "Mu je". Ya yi jim yana kallonta, soyayyarta na sake fizgarta tunanin nisan da zai yi da ita yake. Ta tsugunna gabansa a marairaice tamkar za ta yi kuka, ta ce, "Please Ya Imran?" Ta hade hannuwanta biyu. Y a yi murmushi tare da shafa kanta, ya ce, "OК”. Ta yi dariya sosai, har sai da kyawawan hakoranta suka bayyana. Shi ma ya yi dariyar tare da mikewa cak ya dauke ta suka shige dakinsu. Da shirinsa tsaf suka shiga gida gurin su Mommy, Daddy ya dube shi, ya ce, "Tare za ku tafi kenan?" Ya yi dariya tare da sosa kai, ya ce, "Ina! Daddy bai ba ni wannan damar ba tukunna". Ya ce, "Kai kadai ke sonta kenan, idan ka tafi da ita mu ma muna bukatarta, Imran in kun tafi sai yaushe za mu ringa ganinku? Zamanta a nan shi zai fi alkhairi". Ya jinjina kai alamar gamsuwa, tabbas haka ne, in ya tafi da Mabaruka to zuwansa sa yanda ta yiwu amma in tana nan sun dinga ganinsa akai-akai. Ya katse shi, "Sannan in ka ce ka ci gaba da zama har sai ta warke sumul, to sai bayan haihuwarta sannan kenan ka bar aikin in kuma ta haihu dan ganinshi zai sa ka kasa bari ka ci gaba da zama. Tuni su kuma za su aiko maka da takarda don ba a haka, ba kanka aka fara ba, in ka daure 105 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna sai ka yi tafiyarka ga waya nan ka jc ku yi ta yi ko da za ku wuni ku kwana nc". Sun gamsu tabbas maganarsa haka ne, in dai suka biye wa junansu, to sun daina fita har abada barc kuma wani aiki. Sai da zai wuce ya ce, "To ga ta nan don Allah Mommy a dinga duba min ita da kyau ko sau biyu ne rana Ki dan dinga dubata in da matsala a sanar min da gaggawa don Allah Mommy". Ya fada a marairaice. Daddy ya zaro ido ya ce, "Ita kuma a kan hanyar dubo matarka za ta kare, ita nata auren fa?" Ya ce, "Ba ta da lafiya Daddy ai sai ana ziyartarta akai-akai". Ya ce, "To ga dakinta can ba a rufe yake ba, ta dawo ta ci gaba da zama har ka dawon" A nan Mommy ta ce, "A'a, wai me ya sa za mu yi ta biye musu sai abin da ske so, kowa ma haka ya zauna. Ta je ta ci gaba da kula da kanta ai ba yarinya ba ce ta zauna dakinta ya fi tsari, tunda akwai ma'aikata sun dinga duba ta ta shi kenan ba?" Da haka dai ya tafi yar. waiwayenta bare ita har da kuka ta gudu dakin Mommy jin kukan zai fito. Hankalinsa ya tashi sosai ganin haka, duk da ya saba. Kafin jirginsu ya tashi ya kira ta, ya cе, "Mabaruka!" Ta amsa can Kasan makoshi. Cikin rashin kuzari ya ce, "Kukan ne har yanzu ko?" a 106 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Тa сс, "A'a”. Cikin sanyin murya. Ya ce, "Ga shi nan kina ji kina son ki tayar min da hankali in kasa nutsuwa ko?" Ta ce, "A'a". Lokacin da ta ke rikon kuka. Ya ce, "Ki bar kukan don Allah Mabaruka, na kan birkice na rasa me ke min dadi, ga babynmu kina razana shi ko kin daina son dan Ya Imran din?" Ta yi murmushi, ta ce, "A'a ina sonsa". Ya ce, "To amma kin daina tausayinsa ko?" Nan ma ta сe, "A'a". Tana dariyar. Ya ce, "To sai kin ba shi hakuri sannan zan yarda kina sonsa. Ta yi dariya sosai har sautinta ta shiga kunnensa. Ya lumshe ido yana jin nutsuwa ya ce a ransa, "Kai Allah ka sa min son baiwar nan taKa a raina, ina rokonKa Ka karo min fiye da wannan, mu kasance tare har abada..." Ta katse shi da cewa, "To ta ya ya shi da bai san ni ba, bai jina?" Ya yi dariyar shirmenta sosai, 'a се, "My Mabaru kenan, wa ya fada miki bai sanki ba?" Ta ce, "Na ga ni ma ban sanshi ba, ta ya ya shi zai san ni?" Ya sake dariyar sosai, ya ce, "Please ki bar ni haka kar ki sa ai ta kallona ina dariya ni kadai. Ya sanki sosai, kin taba ganin dan da bai san Mamanshi ba?" Та се, "А'a". 107 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Ya cc, "To ya sanki mana, tunda yana jinki saі abin da ki ka ci yake ci, ya san Mamansa sosai". Ta lumshe idanuwa tana jin wani dadi, sonsa па kara shigarta da na dansa, ta ce, "To fada min ta ya zan bs shi hakuшi?" Ya yi murmushi, ya ce, "Ki sa hamunki a kan cikin ki ji". Ta kuwa dora hannun kanshi, ta ce, "Na dora". Ya cc, "Yauwa kin ji yana motsi ko?" Ta cc, "A'a ni ban ji komai ba". Ya ce, "A'a saurara da kyau". Ta ko nutsu, can ta ce, "Eh na ji kamar numfashi". Ya yi dariya jin ta kere shi, ya ce, "To ki sa a ranki yana numfashi, yana kuma jinki, ki ce sorry dan Ya Imran". Ta yi dariya tare da fadi, ya ce, "Ki ce ina sonka". Ta fada kamar yanda ya ce. Ya sake ccwa, “Ва zan sake kuka ba har Babanka ya dawo". Ta ce, "Kai Ya Imran, in na ji fa ina kcwarka ina kuka?" Ya ce, "To wannan karon ki daure saboda shi yana kuma jinki, in ki ka yi in na dawo zai fada min, kin ji?" Ta ce, "Shi kenan ba zan yi ba". Ya ce, "Ki ce na maka alkawari ba zan sake kuka ba har Babanka ya dawo". 108 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Nan ma ta fada tana dariya, ya ce, "Good, na san za ki cika ko?" Ta ce, "Eh mana". Ya ce, "Alright, I lovc you my Mabari". Ita ma ta fada, "Love you too my Imran". Ya yi dariya tare da huro mata iskan kiss din da ya yi. Ita ma ta mayar masa cikin kara nutsewa a sonsa. Tun daga wannan ranar waya ta kasance abincinsu, baccinsu in suka fara kamar ba za su bari ba, ko ta laptop suna kallon junansu wani lokaci sai ya dawo gida yana kwance a kan gadonsa daga shi sai boksa, ita ma tana can kwance a tsakiyar gadonsu da short gown, ya ce, "Fada min yau me Mabarukar Ya Imran ta ci?" Ya tsira mata ido yana kallo, ya сe, "Ba ki da gaskiya ko?" Ta girgiza kai alamar a'a. Ya ce, "To me ki ka ci?" Tamkar yana gabanta ta rado masa cikin sigar jan hankalinsa, ta ce, "Awara". Ya baza kunnuwa da idanu yana kallonta, ya ce, "Ban ji ba”. Ta sake turo masa baki har a screen din kamar wata yayayya, ta ce, "Awara". Ya zaro ido ya ce, "Awara Mabaruka?" Ta daga kai, "Eh". Tana dariya. Ransa ya dan baci ya ce, "Don me ba ki ci abinci ba, kin san bana son wannan ciye-ciyen ina ki ka same ta?" 109 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Ta narke fuska, ta cc, "A waje fa na ga ana soyata shi ne ta burge ni". Fuskarsa ta sauya, ya ce, "Ta waje ma, wacce yara ke toyewa ba ki san ya tsaftarsu ta ke ba, ki ka kama ci za ta yi miki illa, ko ba za ta yi ba, duk ba ki wannan tunanin ba ko?" Yanayinta ya sauya, ta yi narai-narai za ta yi kuka tare da sunkuyar da kai. Ya ce, "To mene ne kuma? Dago fuskarki". Тa ce, "Ba komai". Ba tare da ta dago fuskar ba, "Ka yi hakuri ba zan kara ba". Ya ce, "Na ji, amma in ga fuskarki". Ta yi shiru ta ki dagowa. Ya tashi zaune cikin damuwa, ya ce, "Mabaruka?" Ta amsa, "Na'am". Ya ce, "Am sorry kin ji ko?" Daga kai kurum ta yi, amma dai ba ta dago din ba. Ya sake birkicewa ya ce, "Ki yi hakuri please, amma kar ki boye min fuskarki, ba zan jura ba, please kin gani, kalli na ma kama kunnuwa na. Ya kama kunnuwan. Ta make kafada ta се, "Umum na ki na dago, ni bacci zan yi". Ya ce a sanyaye, "Kar ki min haka My Mabaru, sau daya ki bari na ga fuskarki don Allah ko kina son in yi kuka?" Ta daga kai alamar eh, ya zaro ido yana son yin dariya, ya ce, "Kina son ganin kukan Ya Imran din?" 110 لن WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Та сс, "Еh". Duk dai kanta na kasan. Ya yi dariya sosai, ya ce, "Ok to bari in yi kin gani na fara". Ta ce, "Ina kallonka ba ka yi ba, sai na ga hawayen". Ya sa miyau ya goggoga a bakin idon ya ce, "Kin gani har da hawayedago ki gani". Ta ce, "In ban gani ba fa sai na ci ka tara ka yarda?" Ya yi saurin cewa, "Eh na yarda". Та се, "То shi kenan". Ta dago tare da kura masa ido don ta ga hawayen, shi kuma ya kura mata ido yana jin wani nishadi da kallonta a kullum idan ya kalle ta sonta na kara fizgarsa. Ta yi dariya ta ce, "Ni ban ga wani hawaye ba, kuma na fada maka sai na ci ka tara". Ya ce yana kallonta, "Na yarda fada min, mene ne tarar?" Ta yi dariya ta ce, "Ka yarda za ka iya bayarwa". Ya daga kai, "Sosai ma, komai ma zan ba Mabaruka ta". Ta ce, "Sharadin jinsa ba yinsa ka yarda?" Ya ce, "Na yarda fadi ke dai". Та се, "Ok". Ta yi dariya tana kallonsa. Ya ce, "Fadi mana, ke nake saurare". Ta juyo da kumatunta saitinshi tana dariya. 111 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Ya ce duk da ya gane me ta ke nufi, amma уа сс, "Ban gane ba?" Ta kalle shi da sauri, ta ce, "Ba ka gane ba?" Ya girgiza kai alamar a'a yana kallonta. Та се, "То miko min kunnenka in rada maka". Kamar suna kusa ya turo mata kunnen kan screen din. Ita kuma ta turo bakinta a kan nata screen din, ta rada masa "Kiss". Ya janye kunnen yana dariya, ya ce, "Kawo to da sauri ma. Ita ma ta yi dariyar tare da miko masa kumatun, ya dora bakinsa kan screen din sai ya yi kamar a kan kumatun nata ya mata kiss kan ta janyc ta nuna masa da hannunta, sau shida zai yi. Ya zaro ido, ta marairaice kamar za ta yi kuka. Ya yi dariya tare da cewa, "Is ok kar ki yi Sai da ya mata sau shidan, har tana umshe idanuwa dadi na ratsa ta kamar gaske. Ya ci gaba da kallonta cikin burgewa komai ta yi burge shi ta ke. Ta nutsu tana kallonsa tsnvon dakiku, shi ma haka dukkansu fuskokinsu dauke da murmushi, ta ce, "Zo ka ji". Ya matso da fuskarsa har gaban screen din, ita ma ta matso inda a tare suke za su iya jin saukar numfashinsu, ta ce, "I love you'. Tana dariya mai kayatarwa. 112 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Ya yi tsam yana kallonta, sannan ya ce, "Love you too". Ta cc, "Ka yi hakurin ko?” Ya daga kai, ya ce, "Tuni ma na yi, amma kar ki kara in kina son ci ki sa a miki a gida". Ta ce, "To ba zan sake ba". Ya ce, "Yanzu ki ci wani abu, sai ki kwanta". Ta turo baki ta cc, "Ni fa na koshi, bana jin yunwa". Ya ce, "Ban yarda ba, zan kira Umma (mai aikin da aka samo mata kenan, dattijuwar mata) ta hado miki lipten ta dan soya miki kwai ki ci'. Ta make kafada ita ba za ta ci ba. Ya ce, "Please Mabaruka ba don ni ba, don dan Ya Imran". Ta yi dariya, ta cc, "To na yarda kai ma za ka ci ka hada naka, ni ma a hado min". Ya yi jim, ta ce, "Plcase'. A marairaice. Ya ce, "OК”. Da kanshi ya tashi ya hado kan dole ya koyi dan girki don samar wa cikinsa abincin da zai ringa ci. A tare suka gama, ya ce ta fara ci, ta ce, "Um-um kai za ka fara". So yake ta ci ba don yana jin yunwa ba, don haka ya fara shan lipton din, ya ce, "Na sha, saura ke". Ita ma ta daga ta dosana kofin a la66anta ba don ta sha ba ya tsura ido yana kallonta har da lekawa. 113 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Ya ce, "Ban yarda ba yarinya, ni za ki wa wayau ba ki sha ba?" Ta yi dariya ta ce, "na sha fa". Ya ce, "A'a ban gani ba, sake sha in gani". Dole ta daga ta sha, don sanin Imran din akwai wayau. Da wayau da hikima sai da ta shanyc tas, shi ma ya shanye in ya sha ta sha, suka dawo kan plate din in ya ci ta ci, suna kirga lomominsu. Sai da suka kusa cinycwa ta turo baki, ya ce, "Menc ne?" Ta ce, "Ni fa na koshi". Kamar za ta yi kuka. Ya cc, "Plcase Kara loma hudu shi kenan sai ki kwanta". Ta ce a shagwabe, "Amai fa zan yi". Ya cc, "Ba za ki yi ba, na rage daya to yi uku". Ta tsikaro shi za ta kai baki, ya tsayar da ita tare da ccwa, "A'a ban yarda ba, babba za ki yi". Ta marairaice fuska tana kallonsa za ta yi kuka, ya ce, "me ye?" Та се, "Кuka zan yi". Abin ya ba shi dariya, ya es, "Dan Ya Imran yana jinki, kuma dariya zai miki idan ya ji kina kuka. Yi sauri ki cinye kar ya miki dariya". Ta kalle shi a nutse ta ce, "Yana ganina ne?" Ya zaro ido har da rike baki, ya ce, "Cab! Ganin ma duk abin da ki ke yana ganinki". Kamar yarinya ta sake cewa, "To ta ina yake ganina, amma ni ba ni ganinshi?" 114 と WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar kaduna Ya сс, "Ta idonsa da ya daga ido daga cikinki yana ganinki, har dariya idan ya yi za ki ji". Та се, "Го ya ya zan ji sautinsa nc?" Ya cc, "Wani lokaci ba ki jin yana yawo a cikinki kamar zai fito?" Kasancewar cikin ya shiga wata shida yana motsi sosai, ya sa ta ce, "Eh wallahi sosai, ni har tsoro yake ba ni. Ya ce, "To dariya yake yi, kuma ma yanzu zai iya miki. Ke dai ki yi sauri ki cinye". Abin dariya sai kawai ta kama ci hannu baka, hannu akushi, tas! Ta cinye. Ya tsura mata ido yana kallo tare da dariyar wautarta, 'yar fari, auta kuma. Ta cinye har da haki, ta dube shi, ta ce, "Na cinye to". Ya ce, "Yauwa ko ke fa? Saura me kuma?" Та се, "Вассі". Ya ce, "Yauwa to mu yi addu'ar bacci sai mu kwanta, amma matso in ba ki sakon kullum”. Ta sani kullum sai ya ba ta wannan sakon har sun saba, ta yi dariya tare da matsowa n har kan screen din ta turo masa bakinta, shi ma ya turo mata nasa. Tsawon lokaci suna haka ji suke kamar a tare suke, idanuwansu a lumshe suna nishadantuwa da hakan. Sai da suka gamsu don kansu, sannan suka janyc, ya rada mata, "I love you'. Ita ma ta mayar masa, "love you too myImran". 115 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Ta gyara filon tare da kwanciya duk yana kallonta suka fara addu'a yana karanta mata tana amsawa har suka gama. Ya cc, "To rufe idon za ki bacci mai dadi, Ya Imran dinki zai taya ki". Ta rufe idon kuwa, a hankali ya fara ba ta labarin tatsuniya masu dadi kamar yanda ya sabar mata, da sannu bacci ya dauke ta mai dadi, ta barshi nan yana labarin sai da ya fahimci baccin ya kamata sosai sannan ya dakata ya nutsu yana kallonta, sonta na ratsa shi da tausayinta, musamman ganin yanda cikinta ya turo ssosai, har cikin ransa ya ke jin nauyin kwalla ta ciko idonsa, ya sa hannu ya goge tare da cewa, "Allah ya sauke ki lafiya Mabaruka, ina sonki". a Ya sa hannu yana shafa fuskar zuwa cikin duk kan sakon din, sai da ya gama sambatunta sannan ya kashe ya koma ya kwanta shi ma da tunaninta bacci ya dauke shi. Wannan hira da suke ita ce ta sa suka samu saukin kewar junansu, suna ji kamar tare suke, lokaci zuwa lokaci yake zuwa ya kwara biyu ko uku ya koma. In za ta fita unguwa ba zai dai wuce gurin Momy ba ko gurin Rafi'atu da Babanta, ya hana ta tuki sai dai direba da ya daukar mata ya kai ta, in ta gama ya koma ya dauko ta Hankalinta kwance da lafiya ita da babyn, yana da kuzari sosai musamman yanda yake harbinta har tsoro ta ke. Ta kan kira shi a birkice tana fada masa. Ya kwantar 116 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna mata da hankali, ya ce, lafiya cc ta sa haka, yana da kuzari. Tana exersice sosai safe da yamma, hakan ya sa ta ke jin dadin jikinta. Ta je gidan Babanta ta wuni, ta samu labarin ya sai wani fili yana kokarin ginawa, nan ya musu kadan. Ta yi murna sosai, a nan Inna ke ba ta labarin gidan Sulaiman duk da ba son labarin ta ke ba. Babban abin da ya mata dadi jin Nafcesa na da ciki har wata uku. Kai ta yi murna matuka, sun sha hira da Nafeen ta kan ce, "Kila ba ni da rabo Mabaruka, shekarunmu bakwai da Sulaiman ko bari ban taba yi ba". Ta kan ce, "Haba Yaya ki daina damuwa, za ki samu mana, ni ma ba ga shi ba ban taba samu ba, duk da ban shekara ba kuma kin ga shi yana haihuwarsa bare mu ce bai yi, lokaci ne kurum. Don Allah ki kwantar da hankalinki insha Allahu za ki haihu, ina nan da ke". Ta yi murna matuka da hakan, sannan Inna zaman lafiya kamar me? Nafisa ta koma abokiyar shawararta har ta fara koya mata karatu, irin su ahlari da fikhu, kur'ani kuma daga alamtarakaifa suka fara. Alhamdu lillah sun samu nutsuwa da kwanciyar hankali, yayin da Samira ke fafutuka hankalinta ya tashi a kan aure ta ke so. Nafeen na kwantar mata da hankali lokaci ne bai yi ba. Bangaren Sulaiman har gobe bai daina kuka da abin da yai wa Mabarukar ba, ya yi nadama ba iyaka. Ko ba komai ta ji dadin gyaruwar gidan hankalinta ya kara kwanciya. Ta dawo gida da kudirin za 117 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna ta canza wa Baban motar kabu-kabun ganin wannan ta fara shan jiki, ba komai ya sa ta wannan kudirin ba sai ganin yanda Allah ya sa masa albarka da ita sosai, yana samu fiye ma da wani ma'aikacin gwamnati, ga cima mai kyau da dadi. Suka fara canzawa daidai rufin asiri ba talauci, kannenta suka koma makaranta mai kyau, tun safe har yamma. Ya ba wa Innar jari ta ci gaba da kasuwancinta. Wani zuwa da Imran ya yi suna kwance kan gadonsu, a hankali yake mammatsa mata jiki tana narke masa, a nan ta ke ba shi labarin kudirinta na son sake masa mota. Ya yaba da hankalinta, ya dade yana tunanin gidan da Baban yake zaune yana gani a takure yake, inda za a ba shi dama shi kam da ya gina masa wani daidai Karfin. Amma a yanzu tunda, ga dama ta samu insha Allahu zai yi wani abu a kai. Ya bar wa kansa haka ba tare da ya sanarwa da Mabarukar ba. Washegari ranar asabar tunda safe suka tashi, shi da kansa ya shirya ta ganin nauyin da ta yi sosai, da kyar ta ke cira kafa cikin ya turo sosai har kamanninta sun fara sauyawa ta fara fuskantar haihuwa. Karin zuwansa ya ganta ya je daurin auren abokinsu a can Sokoto. Ya shirya tsaf cikin dogayen kaya shadda milk colour mai matukar laushi, kamshi na musamman ta ke saboda kudinta ta masa kyau kamar me, ga dinkin da aka zuba masa. Ya dora bakar hula kube mai tsadar, har kyalli ta ke. Ya kawo takalma sau ciki su ma bakake 118 WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna masu sheki ya sa bayan ya sa socks ya makala glass dinsa a idonsa kyam, kan dogon hancinsa. Kana ganin kwayar idonsa ciki tar! Kwayar baki sidik masu lullunishewa, yanayin yankan idon ya yi kyau. Duk tana zaune bakin gado tana kallonsa ta sanya less mai kyau, hijabi ta sanya saboda mayafin ya fi fiddo mata girman cikin, fara da flat shoe farare zaune ta ke tana jiransa, wannan kwalliyar tasa ta dauki hankalinta, har ta dinga jin wani karsashi a ranta. Ya tsaya gabanta yana murmushi, ya tura hannu cikin aljihu yana kallonta, ya ce, "Ya dai Maman Baby na gama". Ta kasa cewa komai, ta dai kura masa ido tana kallo, yanayin fuskarta ba annuri. Fahimtar akwai wani abu ne ya sa ya tsuguna cikin kulawa ya kamo hannunta, ya ce, "Fada min, mene ne?" Ta dauke kai cikin dan jin haushi.

Chapter 7 of 10