kai alamar gamsuwa, ta sa hannu tana
share mata hawayen, "Kukan ya isa yau ba ranar kuka ba
ce, an gonki na nan tafe kar ya zo ya tarar da ke kina kuka,
ga kwalliyar duk ta goge. Ki saki ranki ki nishadi, ki manta
da wani Imran can da zaman gidanshi, ki ci gaba da kallon
Sulaiman dinki za ki samu nutsuwa".
Та се, "Tо". A sanyaye, "Allah ya sa Rafi'a".
Ta amsa, "Amin".
Ba da jimawa ba ango ya iso tare da abokanansa,
bayan sun zauna an yi addu'o'I da fatan zaman lafiya, tare
da zuri'a dayyiba, suka dube. t.. iare da cewa cikin sigar
zolaya, "Amaryar nan mai tsada ce da wuya, wancan karon
mun sha wahala a kan samunki, mu'ne har da kwana a cell
bayan mun sha dan karen duka, har da fitar da jini".
Kowa a gurin sai da ya yi dariya, bare ango an wani
washe baki, amma ban da ita sai ma hade rai da ta yi ba ta
taba ganin abokanan ango marasa kunya ba sai su, sun yi
66
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
wani nade-nade kan gado tana ganin wani har da kwanciya
ya cire hula yana cewa, "Ni a nan zan kwana".
Wani kuma ya ce yana shafa bargon, "Kai wannan
bargon ya yi laushi, tabbas zai yi dadin bacci, anya ba za a
ara min ba?"
Duk suka kama dariya. Ta ja tsaki a ranta tare da
Sauke kai. Ta tuno abokan Imran masu hankali da nutsuwa
sam ba irin rashin kunyar nan. Ta sa gefen gyalenta ta goge Kwalla.
Suka gama surutansu na rashin kamun kai, daga
karshe suka mike tana kallon faya daga cikinsu yana ta
tsokanar Rafi'a duk ya kura mata ido, bayan sun fita suna
bankwana da ita, ta dube ta, ta ce, "Kar ki sake ki saurari
daya daga cikinsu, duk marasa kunya ne, ban ga abin
sha'awa tare da su ba, ki wucewarki ga kudi zan ba ki ki
hau adaidaita sahu”.
Ta yi murmushi tana kallonta, ta ce, "Mabaruka
rigima, kin ce kar na kula Faruk duk 'yan iska ne da shi da
abokansu, ba kya son na yi aure da shi, yanzu má kin ce kar
na saurari daya daga cikinsu, ban san me ki ke so ba, ko ba
ki so ri ma in yi aure kamar ke?"
Ta karasa tana dariya. Ta ja tsaki tare da cewa, "Me
ye abin sha'awa gare ni, wai ke ba ki ganin yanda suke.
sam ba su dace da rayuwarmu ba? Na amince da FFaruk shi
ne daidai da ke, mai hankali da nutsuwa da kamun kai
kamar ke".
'Ta yi dariya, ta ce. "Yau kenan?
67
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "Gaskiya ce dole na fade ta Rafi'a, wallahi
har cikin zuciyata
Rafi`a ta ce, "Shi kenan, Allah ya tabbatar mana da
alkhairi. Ni ma zuciyata ba wanda ta ke so sai Faruk din,
shi kađai nake so, bana jin zan iya sauraran wani.".
Ta kalle ta, ta ce, "Ke dai in yi sa'a Rafi'a, Allah ya
ba ki miji wanda za ki samu nutsuwa da shi".
Та сс, "Кс ma haka Mabaruka, za ki samu nutsuwa
da mijinki insha Allah”.
Ta nisa tare da cewa, "To Allah ya sa, na gode
Rafi'a, godiyata gare ki ba ta da iyaka, kin sha dawainiya
da hidima duk a kaina, ban barki kin huta ba, insha Allah
ba wata matsalar da za ta taso bare ki zo ki ta wahala haka
ya isa, idan na kwana biyu zan zo ban gajiya".
Ta mike tare da cewa, "Kada ki damu kawata kaina
nai wa, ke din ce kina da girma a gurina, ki zauna ki nutsu
gidanki, ki huta sosai kafin ki fara fita kin ji ko?"
Ta daga kai alamar to. Har sai da ta yi kuka sannan
suka rabu, ta fice da gudu idanuwanta ita ma na son kawo
ruwa.
Yau fa farin ciki guri.: Sulaiman ba iyaka, yau
Mabaruka ce a gidansa a matsayin tasa? Kai gaskiya yau
zai shana. Ya dawo daga rakiyarsu ledojinsa a hannu.
Duk abin da suke Inna na jinsu, tana jin shigowarsa
ta kwala masa kira, "Sulaiman!"
Ya share yana saurin shiga daki, ta sake kwala
masa kira, "Sulaiman?"
68
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ilabawa tuni ya shige dakin da sauri har yana sa
sakata. Tana zaune inda suka barta, ta dube shi tare da
cewa, "Lafiya na ga ka shigo da sauri haka, bayan na ji kamar ana kiranka?"
Ya zauna yana cire malum-malum, ya ce, "Ke rabu da ita Inna ce".
Та ce, "Кamar ya a rabu da ita, kana ganin ka
kyauta kenan tana kiranka ka share ta?"
Ya ce, "Ke rabu da ita ba ki san dawan garin ba,
uwana zai haifar da gagarumar matsala"
Та се, "Л;a ba da ni za a yi haka ba, daga zuwana
ka fara bijire mata? Ka tashi ka je duka minti nawa ka dawo?"
Ya zaro ido, "Minti kadai? Kira min awoyi, kila ma har sai kin yi bacci sannan zan dawo".
Kan ta ce wani abu suka ji ana kKwankwasa kofar
tarc da kwala masa kira, "Sulaiman!"
. T'a mike tana cewa, "Ka gani ko har ta boyp ka, kila
ma tana bukatar wani abun ne, bari in bude mata".
Ya tashi tsaye da sauri yana cewa, "A'a kar ki bude, in ta ji shiru za ta gaji ta tafi”.
ai
ta
Та се, "Пaba dai, Allah ya sauwake Sulaiman, Allah ya kama mu, mahaifiyarka na kiranka mu share alhalin muna ji? Uwa na da girma sam ba za mu fara ba". Ta wuce tan Kokarin budewa.
Ya tare gabanta da sauri yana cewa, "Kada ki yi
wannan gangancin Mabaruka, na san komai, na san halinta
69
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
za ta iya jawo mana matsala tun daga yau, mafi alkhairi kar
ki bude Kofar nan".
Za ta yi magana, maganar Inna ta hana, "Na rantse
da Allah Sulaiman idan ba ka fito ba sai na tsine maka, dan
iska kawai bijirarre!"
Ta zaro ido a tsorace tare da cewa, "Subhanal!ahi,
ba da ni ba".
Kawai ta cire sakatar sai ga Inna gabanta tana
hararta tamkar za ta kai mata duka.
Ta dan rankwafa cikin ladabi, ta ce, "Sannu da
fitowa".
Ta ce, "Kauce ki ban hanya, ba gurinki na zo ba
Da jin haka ya yi saurin fitowa yana cewa, "Ga ni,
mu je ba sai kin shigo ba”.
Ya ja hannunta suka wuce. Ta bi su da kallo cike da
mamaki har suka shige dakin Innar, ta rike baki tare' da
cewa, "Ikon Allah, kin ji wani sabon abun kuma". Ta yi
kwafa tare da juyawa ciki abinta:
Lokacin da suka shiga dakin ta dube shi cikin
masifa ta ce, "Yanzu Sulaiman kana jin-ina kiranka ka
share ni don ka auro waccan figaggiyar da ta fi ni, har aka
daura maka aure ban sani ba ko”.
Cikin gajiyawa ya ce, "Haba Inna tun dazu ki ke
fada ina so na ba ki hakuri kin ki hakura, haba?"
ni".
Та се, "То isa ce ta sa ina kiranka ka yi banza da
Ya ce, "Ni ban ji ba, kin san na gaji, ina son hutawa
in yi bacci ke kuma kin fitine ni".
20
WAYE ANGON?-4
haka?"
Maryam Jafar Kaduna Та се, "Au ni na litine ka don ubanka, har ka zama
Ya turo baki yana gungunai.
Ta zauna tana cewa, "To na ji me na gani ka shigo da shi a leda, ka shiga dakinta da shi?"
Ya dube ta, ya ce, "Me fa, dan abu ne fa abokaina suka szi min na kai wa amarya".
Ta сe, "Ban da ni sai amarya kawai?"
Ya ce, "Ni dai amarya suka ce, ke kullum muna
tare, ita ko kyautatawarta ce da Annabi ya umarci ango ya kawo wa amaryarsa".
Та се, "Тo alkur'an sai dai a raba biyu ni rabi ita
rabi, ai ba fina ta yi ba don ubanka".
Ya zaro ido, "laba Inna, me ye haka? Yau ki ka saba ci?"
Та се, "Кo ba yau ba ne don ubanka sai ka rabo ko
mene ne, maza tashi kar ya huce".
A kan dolensa ba don ya so ba ya fita ya je ya dauko ledojin ya kawo mata.
Ta bude ta bi kajin da kallo, ta kalle shi, “Sulaiman,
yanzu duk iyayen kajin nan za ka kai mata, uwarka ce ita ko wa?"
Ya bata fuska yana ciccijewa.
Ta сe, "Da kyau, to zauna zan ga inda ma za ka
shiga dakin bare ka kai mata kajin, har a yi wani amarci".
Ya zaro ido a tsorace, "laba Inna, me ki ke fada
haka?"
71
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
T'a harare shi, "Abin da ka ji, idan kuma/ ba nina
haife ka ba ka sa kafa ka fa in gani".
Ta jawo ledar tą lizgo cinya tare da dangwalo yajin,
ta kai baki har tana lumshe idanuwa, ta ce, "Don ubanka ni
ina nan zaune baki a bushe ban ci ba, za ka kai wa wata?
Haramiyaria, gidan ma ba ta ga wajen zama ba, billahillazi
sai ka sake ta".
Ya tsorata ainun, ya tsugunna gabanta a marairaice,
"Kar ki min haka Inna, don Allah ki tausaya min na sha
wuya kafin na same ta, don Allah ki bar mu tare"
Ta aje kashin da ta fara gwigwiya ta dube shi, ta
zare ido, "Ka dubar ni nan Sulaiman ka san ni sarai ba na
magana biyu, daya ce idan kuma na fada ta zauna kenan"
Ya ce, "Amma Inna in ki kai min haka ba ki min
adalci ba, kin shiga hakkina da yawa...
Ta katse shi, "Ni adalcin kai min, a matsayina na
uwarka hakkina ka ba ni da ka yi auren ko na sani ne bá sải
dai na ji ana shigowa da amarya ba? Don haka alkur'anin
Allah sai ka sake ta Sulaiman, ka ji na fada da kakkausar
murya. Ai kyale ka na yi sai ka zo kana rawar jikin shiga
dakinta in maka iyaka da ita én.on
Ya fara kuka, "Wai me ya sa ba ki tausayina Inna?
Ni fa danki ne, sai yaushe zan samu nutsuwa da matana?"
Ta ce, "Sai ranar da ka auro wacce ba ka rawar kafa
da ita, don ka ji dadi ni ma na ji, ba zan taba gigin barinka
ka zauna da wacce ka ke so ba, don na san za ka mika
kanka ne gabadaya, a koma ana juya ka, sai yanda aka yi
da kai. ni uwarka da na sha wuyarka ina nan hangame da
72
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
baki ban isa da kai ba, juyawar ma har ni sai ta shafa. To ba
zan zama sakarya ba, na san me nake don haka ba zan
saurara ba, bare irin wannan matar da maza ke rawar jiki da
su ga kyau ga ilimi ga dukiya, in ka zauna da ita yo ai ni
sorina Sulaiman, in ji ku 'yan boko. Don haka wallahi
billahil azim sai ka sake ta, daura aure ai ba zaman aure ba
ne, na kyale ka ne".
Kuka sosai Sulaiman ya sa yana ahi da magiya a
kan ta barshi da Mabaruka, amma ina! Inna ta yi fafur ta yi
masa ahir da ita. Bakin kofa ma ta hana shi zuwa bare ya
fita daga dakin.
Ta mike tana gyara zani ta nufi wajen kofa tana
cewa, "Don haka zauna ka yi amarcinka a nan, ka yagi
kazarka nı ma na yagi tawa, mu sha lemun in mun rage ma
ajiye wa Samira da safe".
Bam! Ta datse kofa, ta sa key tare da sakata
Mabaruka wacce ta ke jikin kofar tana saurare, sakamakon fitowarta daga daki za ta yi fitsari ta jiyo kukan
Sulaiman, don haka ta aje butar ta lafe tana saurarawa. Ta ja baya da sauri saboda yanda iskan rufe kofar ya dake ta a
fuska. ilannu ta dora saman kai Ga nufin fasa ihu, tuna za a
iya jiyo ta ya sa ta juya dakinta a guje ta sa sakata ta fada
gado tare da fashewa da kuka. Ta yi iya yinta iya iyawarta
tamkar ranta zai fita, ta zubar da hawaye ba adadi har suka kafe, ta koma tana ajiyar zuciya.
Ta yi lamo, nadama, da na sani da bakin ciki suka
cunkushe mata rai, tun yau kenan, tun kafin ta kwana gidan
ma ta fara cin karo da matsalolin da aka dinga gudar mata,
73
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
amman ta dage, ta kafe lallai sai ta zo gidan Sulaiman, ta ki
Imran mai sonta tsakani da Allah, wanda ya dace da
rayuwarta. Yanzu me ye amfanin kafiyarta da rashin jin
maganarta? Auren Sulaiman me ta karu da shi, rana ta
farko, daren farko bakin ciki da dana sani tare da nadama
marar amlani sun dabaibaye ta.
Shin wai ina son da ta ke masa, ina kaunar ta ko? Ta
dale zuciyarta tana nazari, ta fada a fili, "Babu! Wallahi
babu tun ranar da aka daura min aure da Sulaiman na neme
ta na rasa, me ya sa na gaza farin ciki tun ranar da
Sulaiman ya zama mijina? Shin da ma yaudarar kaina nake
da nake cewa ina sonshi? Me ye aibun Ya Imran da na ki
shi? Wace karuwa na samu da na rabu da shi, wace
walwalar da farin ciki hadi da nishadi na samu bayan
rabuwa da shi?" Hawaya suka zubo mata.
"Babu, wallahi babu sai bakin cikin rabuwa da kai
Ya Imran".
Kukan ya ci karfinta, ta duke ta ci gaba da yin
abinta.
Sulaiman ya mike ya nufi kofa zai bude ya fita,
lana ta dube shi a kaikaice, "Za ka fita ne ko? Ni ban isa
ba?"
Ya yi shiru yana kumburi.
Та се, "Тo wallahi idan ka taba kofar nan da sunan
budewa ka fita sai na tsine maka billahil azim, kuma ka fita
دو ka gani.
Ta daure fuska tamau.
74
WAYE ANGON?-4 Marryam Jafar Kaduna Ya dawo-cikin takaici yana wurga hannuwa, "Kai! Kai!! Kai!!! Haba wannan wace trin cutarwa ce, anya ke ki ka haife ni Inna? In har ke ki kathaife ni za ki san ciwona da ciwon hana ni abin da nake so, don..."
Saukar mari ya ji ba shiri ya yi shiru, ya dafe kunci yana kallonta.
Cikin bakin ciki ta ke cewa, "Yau ni ka ke fada wa haka Sulaimanu? Ni har ka ke cewa ban san ciwon haihuwa
ba, ni Sulaiman?"
Ya sunkuyar da kai cikin damuwa.
Та се, "Ya yi kyau, to wallahi ka sake tunzura ni,
sai ka sake ta wallahi ba za ka zauna da yarinyar nan ba, in
har ni na haife ka, idan kuma ka ki hakan ya nuna min ba
ka dauke ni uwarka ba".
Ta miko masa hannu, "Ba ni takardarta yanzuyanzu ba sai gobe ba"
Ya ja da baya a tsorace, "Kai ina! Ba zan iya ba".
Та се, "Вa za ka iya ba? Kai tsaye ba za ka iya ba?
Faďa min uwarka ce ita da ba za ka iya rabuwa da ita ba?"
Ya ce, "Kawai ba zan iya ba ne".
Cikin fada ta ce, "Wallaini karya ka ke, ba ka isa ba
sai ka sake ta don ubanka".
Daren farkon kenan, sun raba dare suna wannan
kicimilli ba tare da ya-yi sakin ba, kan dole.ya hakura da
zuwa dakin amarya Mabaruka, ya yi kwanan zaune,
kwanan bakin ciki a dakin Inna, yayin da Inna ta kafe a kan
lallai gobe sai ya sallamata ta koma gidansu.
75
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Haka zalika amarya Mabaruka ta yi kwanan kuka
da takaici, hade da tunanin tsohon mijinta mai sonta Ya
Imran.
Tuni Imran ya yanke wa kansa abin da ya fi masa,
wanda zai iya dauka bayan ya warware, sam garin ba ya
masa dadi matukar kuwa ya ci gaba da zama cikinsa
tunanin Mabaruka ba zai barshi ba, gwanda ya nesanta da
ita ya ga ko zai manta da ita, don haka bai sha wahala ba
wajen neman transfer ba, saboda kwazonshi don haka ya
samu, amma sun tura shi Lagos. Ya yi farin ciki sosai da
hakan.
Ko a ranar da ya sanarwa Momy da daddynsa,
Momy ta so ta ki, amma Daddy ya karfafa masa gwiwa
saboda tunaninsu daya da Imran din, kamar nesanta da gida
zai samar masa da kwanciyar hankali, don haka bai yi wasa
ba ya tunkari garin Lagos, bayan ya yi bankwna da garinsa
ha ya jin zai iya dawowa.
A cikin Baccin da ya fara daukar Inna na 'yan
mintoci a tsakar gida, yayin da Mabaruka ta ke kai kawon
abincin rana.
Bayan ta gama ta zuta na Sulaiman a flask dinsa ta
hada da faranti da cokali ta sa a tire ta shiga da shi dakinta.
Ta dawo sauran ta juye a babban flask ta aje a kicin ta debo
wani bai fi ludayi biyu ba a wata cinyayyar roba ta turo wa
Inna inda ta ke zaune, ta ee, "Ga shi nan sai a yi ta ci".
A tsorace Innar ta jawo ta fara ci hannu baka hannu
akushi. Nan da nan ta cinye tas ba don ya ishe ta ba, iya
76
WAYE ANGON?-4 Maryan Jafar Kaduna
wannan shne rabonta, sai kuma dare a sake yafito mata irin wannan.
A daidai wannan lokacin Sulaiman ya dawo, ya shigo yana kiran Mabarukar, "Hello my dear, am back". Ва tare da ya kalli Innar ba.
Da gudu Mabaruka ta fito daga daki tana sanye da gownshout ta nade gashin kanta da ribbom yana reto a
baya, fuskarta ta yi kwalliya sosai. Ta dane jikin Sulaiman, yayin da shi ya tarbe ta suna murnar ganin junansu. A
shagwa6e Mabarukan ta ce, "My dear ka dade yau, ina ta missing dinka".
Ya ce, "Ayya sorry my dear, aiki ne ya rike ni,
amına ga ni na dawo, zan kasance tare da ke har gobe".
Ta ce, Allah my dear?"
Ya ce, "Sosai ma, amma me ki ka shirya min?"
Ta ce, "Abun dadi sosai, baki ba zai iya fada ba.
Amma dai zo mu je ka gani".
Ta kama hannunshi suka shige daki.
Inna ta dago murya a marairaice, "Sulaiman,
Sulaiman ina maka magana amma ka kyale ni? Yanzu ko
kallona ba za ka yi ba ka dawo.
Yafito cikin gajiyawa, "Oh kai wallahi tsohuwar
nan da takura ki ke, ni ban ma ganki ba"
BТа ce, "Ai da man haka za ka ce, ni ba ni da wata
daraja a idonka kenan, duk kana kallo ake min cin kashin
nan ana zaluntataiw FIORH
Ya ce, "Kai Inna, ke dai da tsogumi kike, duka me
akai miki don dai fitina? Gaskiya kauye zan maida ke na
77
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
gaji da litinarki, kullum da korafin da za ki? Kin sa mana
ido da yawa, haba! Ina dalili?"
Mabaruka ta fito tana cewa, "Haba my dear ya ka
ke sa wa ranka damuwa? Ka je ka wuni aiki ka gaji ya
kamata ka kwanta ka huta, zo mu je in taya ka". Ta ja
hannunsa
Ya yi dariya, ya bi ta, "Yauwa yar MabaruMabaru".
Bam! Suka datse kofa, Inna ta sa kuka.
Firgigi! Ta mike cikin fada, ta yi zufa sharkaf cikin
tashin hankali, "Ina! Wallahi ba zai yiwu ba, karya ku ke".
Sulaiman ya bude ido firgigi yana kallonta, da ya
fahimci shirmen baccinta ne ya share ta ya maida kafada ya
ci gaba da baccinsa. Hankalinta ya tashi matuka, tsoro ya
sake kamata, ta kuma kara zagewa a kan burinta lallai sai
ya sake ta, hakan ba za ta yarda ya faru da ita ba, ina!
WASHEGARI
Tun da asuba da Mabaruka ta fito ta yi alwala ta
shige faki, ba ta sake fitowa ba, ta sayo kofarta. Har zuwa
lokacin ba ta daina kukan Ja na sani ba, bakin ciki ya
cunkushe zuciyarta, Allah ya ba ta dama, amma ba ta yi
amfani da ita ba, har ta wuce ta. A yau me ye aibun Imran?
Me ya gaza da shi? Shi Sulaiman din da ta ke wa mai ya fi
Imran din? Yanzu ga irinta nan jiya ta shigo gidan a
matsayin amarya, amma ba angon, uwarsa ta hana shi zuwa
wurinta, karshe ma tana yunkurin sa wa a sake ta.
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Hawaye suka zubo mata, ta fada a fili, "Yanzu haka Tayitwalaza ta dinga tafiya, ina Karamal yarinya amm? aure biyu, saki biyu alhalin mazajen da rahsu ba mutuwa suka yi ba, wannan wace irin rayuwa ce, me utane za su kira ni?" Sabon kuka ya dawo, ta ci gaba da yi.
Yayin da Sulaiman har gari ya waye Inna falur ta han shi fita bare ya shiga gurin Mabaruka, ko sallahą
akinla ya yi ta hána shi zuwa masallaci bare daga nan ya
zame gurinta.er
Sai da gari ya waye tangaram sannan ta dube shi, ta
ce, "Yanzu za ka iya rubuta mata takardarta ka ba ni in kai
mata, ko kuwa da baki za ka fada in je insanar mata?"
uYa mike tsaye yana fushi, "Ni dai bà zan iya sakinta
ba, don Allah ki kyale batun rabuwar nan, ina son malata".
Ta ce, "Kai tsaya ka ji wawa, wannan da ka ke gani
ba sonka ta ke ba, masifa ce za ta zamar maka a gida,
karshe sai ta farraka mu, ni na ga abin da na gani. Allah ya
kara haska min a mafarkina na jiya, don haka saki dole ne
babu matar da za ta shigo gidana ta juya ni ta juya ka, Allah
sai ka sake ta".
ngz Ya ce, "Gaskiya ba zan iya ba, ni Mabarukata ba ta
da mugun nufi a kan kowa bare ni, tsakani da Allah ta ke
sona, don haka ki bar wannan batun".
Daga haka ya fice daga dakin, ta biyo shi da sauri
tana fadar, "Ina za ka? Kar ka sake ka shiga dakin nan,
wallahi in har ka shiga a yanzu a gabanta zan titsiye ka sai
ka furta mata saki, wallahi!"
79
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Jin haka ya sa ya fasa shiga, ya juya cikin bakin ciki
ya bar gidan gabadaya.
Ta сe, "Ya yi daidai, gwanda da ka bar gidan, amma
ai za ka dawo ina nan kan bakana".
Ta juyalashige daki.
Mabaruka tana jmsu, don haka kukanta ya Kara
tsananta. Ta lalubo Rafi'atu a waya, bugu daya ta dauka da
fara'a ta ke cewa, "Ya dai amarya, kar ki ce min har kin
lashi?"
Cikin damuwa ta ce, "Bar wannan maganar Rafi’a,
ina son ganinki don Allah”.
Rafi'ar ta yi jim cikin mamaki, "Yanzu kuma
Mabaruka? Lafiya kuwa?"
Та се, "Вa lafiya Rafi'a, don Allah ki zo da wuri".
Rafi'a ta ce, “Allah ya kyauta, bari in zo to"
Та сс, "Yauwa Rafi'a, na gode. Sai kin zo
Bayan awarsu biyu da gama wayar Rafi'ar ta iso.
Tun a tsakar gida ta ke kwala sallama ba wanda ya amsa,
don haka ta wucewarta dakin Mabaruka. Ta yi sallama ta
shiga tare da bin Mabaruka da kallo, wacce take
kudundune kan kujera, hijaii sanyc a jikinta.
Ta zauna a sanyaye tana cewa, "Jikina ya yi sanyi
Mabaruka, yanda na barki jiya haka na zo na same kı, ko
kayan jikinki ba ki sauya ba, me ke faruwa ne?"
Kwalla ta ciko idonta tana kallon Rafi'ar, "Na yi
nadama Rafi'a, na yi da na sani, na yi bakin ciki. Kaliyata
da taurin kaina ba abin da ya jawo min face hasara".
80
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Rafi'a ta dube ta da mamaki, "Ban gane ba, hasarar
me ki ka yi?"
Hawaye suka zubo mata, "Kin dade kina min fada Rafi'a. Kin dade kina nuna min gaskiya na yi amfani da
damar da na sanu, Ya Imran baiwa ne a wurina, Allah
min rahmar kasancewarsa mijina babu rashin kunyar a
ban yi ba, da taurin kai a kan sai na auri Sulaiman na bijire
wa mahaifiyata, haka aka kai ni gidansa.
Babu kalar tijara da rashin kunyar da ban mishi ba,
na cutar da shi, na shiga hakkinsa a kan don ya ce yana
sona, karshe na dage sai ya sake ni don na cimma burina na
auran Sulaiman ya sake ni".
Ta dubi Rafi'a, "Wallahi Rafi'atu tun daga sanda
Ya Imran ya sake ni na fara sonshi, sai dai na ki yardar wa
zuciyata da hakan, na ci gaba da yaudarar kaina har na fita
daga iddarsa. Mahaifina ya cika min burina, ya aura min
Sulaiman. Ban taba jin kunci da damuwa ba irin na wannan
lokacin ba Rafi'a, na nemi farin cikin da nake hasashen zan
yi yau idan aka ce na zama matarshi na rasa, komai ya
koma min ba dadi, a lokacin na tabbatar wa kaina lallai na
fara son Ya Imran, amma to ya na iya?-Ba ni da wani zabi a
yanzu matar Sulaiman ce ni, Ya Imran ya yi min nisa sai
dai wata ba ni ba. Na cuci kaina, na rasa nagartaccen miji.
Yau ga ni a gidan Sulaiman Rafi'a a matsayin
matarsa, burina ya cika, amma sam ba farin ciki sai bakin
ciki Rafi'a"
Kuka ya fara cin karfinta.
81
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Rafi'a ta dafa kafadarta cikin kulawa, "Fada min to
me ya faru yanzu?"
Ta share hawayen, "Tunda ku ka kawo ni Rafi'a
bayan fitarku da angwayen har zuwa yanzu ban sake ganin
Sulaiman din ba, ko leko ni bai yi ba".
A tsorace Rafi'a ta ce, "Saboda me?"
Та се, "Мahaifiyarsa ta hana shi zuwa wurina a
yanzu haka halin da ake ciki, takardar sakina ta ke nema a
gurinsa, tun jiya ta ke fama da shi har yau da safe, karslhe
ya bar mata gidan".
Rafi'a ta tsorata ainun, "subhanallahi me hakan ke
nufi kenan?"
A fili ta ce, "Sakamakon abin da na yi kenan, shi
kenan na zama mai aure-aure ina karamar yarinyata na fara
lalata rayuwata da kaina. Ki fada min Rafi'a da na yi wa
mahaifiyata biyayya, da zan ga haka?"
Ta girgiza kai a sanyayс, "A'a".
Та се, "То yanzu a halin da nake kenan zaman jiran
takarda ta, in kaına gabana. Na sani wannan karon ma
Momy ba za ta karbe ni ba, korata za ta yi".
Та се, "Kai amma abin nan bai yi dadi ba
Mabaruka, auren kwana daya?"
Ta kalle ta, "Laifin wa? Laifina ne duk mai na gani
ifina ne, ban ga laifin Inna ba".
Та се, "Мatsalarmu kenan a koyaushe Mabaruka,
sai mun ji wuya sannan muke nadama, ba ma karbar
kuskurenmu sai muń sha wuya, yanzu ga illar rashin
82
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
biyayyarki ba abin da ta ja miki sai da na sani da kin yi zamanki gidan Ya Imran da ba haka ba Mabaruka".
a
Ta goge hawaye, "Ai shi kenan kurunkus in ya sake
ni