mutu a kan na ci gaba da zama da
fushin Momy. Ki taimaka min Rafi,a Momy ta sauko don Allah"
Ta yi jim tsawon lokaci, sannan ta ces "Shi kenan.
amma ya zama dole sai kin kiyaye sake bata mata a gaba".
Ta ce da sauri, "ch... eh na yarda".
Haka dai suka kasance har sai da suka gama lecture,
kai staye suka nufi gidan Momyn, sai dai Rafi'ar ta biya mai adaidaita sahun.
Da Momy da Daddy ne a falon, sana zaune suna
hirarsu suka shigo hade da sallama, Rali'atu ita ce gaba
yayin da ita tana bayanta tana rabe-rabe.
Kallo daya da Momyn, ta mata sai da gabanta ya
yanke ya fadi ganin yanda ta dawo, duk ta fige ta lalace,
anya Mabarukarta ce? Amma a zahiri ba ta nuna ba, sai ma
la murtuke fuska tare da dauke kai. A sapman kafet suka
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
durkusa dukkansu bayan sun gaida Daddy ya amsa cikin
kulawa.
Rali'atu ta dubi Momyn a marairaice ta ce, "Ga mu
mun zo Momy, mun zo muna neman afuwa, mun yi laili
amma mun yi nadama, mun tuba har abada ba za mu sake
nanaia kwatankwacin laifin nan ba, za mu yi hiyayya a kan
ahin da ki ke so ko da ba ma sonshi ba mu da kamarki, ya
zama dole mu yi biyayya amma don Allah Momy ki yi
hakuri ki sauko, wallahi fushinki masifa ne gare mu". Ta
karasa fada idanunta sun ciko dam da hawaye.
Ta juyo ta kalli Mabarukar da tuni ta ke kuka, ta yi
mata nuni da ta yi magana. Ta dubi Rafi'ar tare da jinjina
mata kai alamar to. Da rarrafe ta karasa gabanta tana сі
gaha da kukan, hawaye wani na tunkuçfo wani, ta cc, "Na
tuha Momy, na yi nadama, na gane kuskurena, saba miki
masifa ne gare ni, ba van iya jurar fushinki ba. Ga ni gare ki
cikin nadama da neman yaliya, wallahi na yi da na sani
Momy don son Annabi ki karbe ni ki yafe min ko na samu
ingantacciyar rayuwa. Dubar ni, dubi yanda na dawo duk
sanadin fushinki, wallahi na yi alkawarin ko yanzu ki ka ce
in koma dakina zan koma in masa Biyayya, na karbi
zabinki ina facin ciki da shi ko da bana sonsa, amma ki yafe
min Momy, wałłahi na tuba na yi nadama".
스
Ta dora kanta saman cinyarta tana ci gaba da kukan
da roko. Ita kanta Momyn ta sauko, fushita ya tafi,
zuciyarta ta huce tausayin 'yarta ya čika mata rai. Kwalla la
taru a idonta, ta kasa cewa komai matukar ta yi magana
kukan da ta ke rikewa zai fito, ta kasa cowa komai.
WAYE ANGON?-4 Maryam uafar Kaduna
Daddy ya fahimce ta, ya yi murmushi tare da
mikewa ya zagaya bayan kujerar da ta ke zaunc ya sunkuyo
da kansa daidai yanda ita kadai za ta ji me zai ce, ya cе,
"Ya dai kina son yi wa 'yar taki kuka ne?"
Ta kalle shi da sauri. Ya daga mata kai alamar ch,
sannan ya ce, "Is ok, kar ki gaza tana neman afuwarki ki yi
kakuri ki saurare ta ki danne zuciyarki dubi yanda ta dawo
tana bukatar kulawarki, kar ki kasance mara yafiya kin ji ko?"
Ta daga masa kai alamar, "To".
Ya ce, "Yauwa, to saurararta".
Ta juyo tare da kallon Mabarukar da kanta ke kan
cinyarta tana kuka, hawayenta ya jika mata zani, ta dafa
kanta tare da cewa, "Na yafe miki, komai ya wuce, Allah
yai miki albarka".
Ta dago da sauri tana dariya, ta ce, "Kin yafe min
Momy, kin bar fushi da ni?"
Ta daga kai, "Eh na yafe miki".
Da sauri ta fada jikinta tana kukan farin ciki. Kowa
abin ya masa dadi, tarin ciki ya bayyana a fuskokinsu. Ta
aubi Daddyn ta ce, "Na gode Daddy da sa bakinka, kai ma
ina neman afuwarka".
Ya yi dariya tare da cewa, "Is ok, ya wuce ban rike
ki da komai ba, kuruciya ce ke damunki".
An samu wuri fa sai labari suka ci abinci kala da
kala, ta yu santi sosai yaushe rabon da ta ci abinci irin
wannan, musainman na Momynta me zaki da lafiya. Ta vi
35
WAYE ANGON?-4 Maryamı Jafar Kaduna
wanka tare da wanke kanta da shampoo masu kyau da
Kanıshi, ta yi fes abinta, farin ciki Kwal a ranta.
Sai yama lis suka yi shirin tafiya, Daddy ya dube
la tare da cewa, "Ina za ki? Na sha kin dawo mana?"
Ta yi murmushi, ta ce, "A'a, gwanda in zauna can,
zamana a can shi zai ci gaba da koya min darasi a
rayuwala. Ina son na kara lantance rayuwa ko na yi
hankali, in na ci gaba da zama a nan ba zan san me ye
rayuwa ba, in na samu lokaci zan ziyarto ku insha Allah”.
Sam bai gamsu da tsarinta ba, har gobe 'yarsa ce
yana ci gaba da kallonta kamar da, don me za ta guji
gidansu? To amma kamar yanda ta ce din zamanta a can
zai sa ta ta san rayuwa sosai, hakan yana da kyau, zai ba ta
dan lokaci daga bisani la dawo nan din.
Ita kam Momy hakan ya mata, ta san har da zaman
gidansu din ya sa ta yi nadamar, tana son ta ga ta yi hankali
sosai. Daddy ya yi musu alkhairi na kudi sosai, ko sabodа
makarantarsu. Sun yi godiya sosai, sannan suka fito. Suna
fitewa harahar gidan Imran na shigowa da motarsa.
Rafi`atu ta dube ta, ta ce, "Ga ma Imran nan bari mu gaisa
ko
Ta yi tsaye cak sam ba ta so haduwarsu ba, har da
shi va sa ta ki gidan, gwanda ta yi nesa da shi can har ta
samu ta yar da iddarshi. Yana nan dai ba wai canzawa ta yi
bz. Lar gobe ba ta kaunarsa ta li tunanin Sulaiman, amma
sa hun kunya insha Allabu ta bar masa sai dai magana mai
dad: ko don Momy, sannan lokaci guda da shirvawarta da
1ny da Rafi'a bai kamata su fara nusu da Rati'ar ba,
36
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
don haka ta ce, "To". Kurum zuciyarta a kuntace. Kagare ta
ke ta bar gidan.
Ya karaso har inda suke tsaye ya yi kyau sosai,
yana sanye da farin yadi mai kyau da daukar ido. Manne da
tabarau fari, ya gaji da haduwa. Kallo daya ta masa ta
dauke kai. Ya yi murmushi idonsa a kanta tamkar ya jawo
la su koma gidansa yake ji, ya ce, "Hajiya Rafo'a ya gida,
kwana biyu?"
Ta ce, "Ai ko kwana biyu ka buya".
Ya sake murmushi idonsa a kan Mabarukar, ya ce,
"To alhamdu liliah, ofis ne ke boye ni. Kenan ku kuma
school ko?"
Ta yi dariya kawai, ya cc, "Malama Mabaruka
barka da yamma".
Ta juyo ta kalle shi, ta ce, "Ina wuni?"
Ya amsa, "Lafiya lau, ya makaranta?"
Ta ce, "Lafiya lau". Kanta na kasa.
Ya ce, "Allah ya taimaka.
Ta ce, "Amin".
Ya so ya rage musu hanya, amma Rafi'atu ta ki
sa, dole ya kyale su suka yi sallama suka wace.
Rayuwa ta fara mata sauki ba don komai ba sai con
saukowar: Momynta gefe kuma ga aminiyarta sun koma
kamar da, karatunsu lafiya lau yana tafiya. Kudi kuma na
zuwar mata ko ba ta je ba Daddy zai aiko mata dubu goma
duk sati, don haka ta koma facaka da kudi kamar yanda ta
saba. Sam ba ta iya rikon kudi, jakarta sai ta cinye su, ko
37
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
da can Rafi'a ke dauke su tana boye mata. Ko ba ta sani ba
sai kudi sun taru sosai ta nuna mata ta kan yi mamaki sosai
ganin kudadan. Ta kan rankwashe ta, ta ce, "Da an bar
miki duk a cikinki za ki cinye su, karshe dai Momy suke
kai wa
Tana nan da kudinta kashi-kashi, to yanzu ma haka
ne ta kan rage mata wasu a jaka ta боус.
Abin da ya rage mata na iddarta sati biyu, sai dai
abin da ke damunta ya kan tsaya mata a rai yana cinta.
IHaka-nan tana zaune sai ta ji tana tunano Imran, wasu
abubuwa nasa da ya mata ko na kulawa, ko kuma dariyarsa
wani lokacin har tsintar kanta ta ke tana murmushi duk
sanda ta dawo tunaninta abin na ba ta mamaki da tsoro, sai
ta bi ta damu kanta, wai don me ta ke yawan tunaninsa
haka, ko suna tare da Rafi'atu idan ta ambace ko ba shi ba
ko mai irin sunanshi sai gabanta ya yanke ya fadi. Fuskarsa
ta fara zama a kwakwalwarta, ko kuma ta dinga auno shi in
ya yi kwalliya. Kai abin nan fa yana damunta sosai, idan ta
gaji sai ta watsar ta ce, don ta dan zauna da shi ne tsawon
wasu kwanaki shi ya sa, amma ta san za ta bari ne.
Bangaren Sulaiman kuwa ya yi .atiri gurinta, sai
dai duk sanda ya zo kan ya ganta Baba Hamza zai kora shi,
ya ce idda ta ke, ya bari sai ta gama. Ya yi rokon amıma
sam ba ya kyale shi, gefe kuma duk sim dinta Baba Hamza
ya karbe duk kokarinsa kar ta hadu da Sulaiman din a
koma yar gidan jiya ta ki komawa gidan Imran din. IMa
kanta tana son ganin Sulaiman ko sun yi maganar ya auran
38
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
nasu zai kasance, har yanzu ba ta yi magana da shi ba, duk da Inna Binto ta ce ta sanar mishi ta fito.
Ranar asabar ne da yamma lana wanke-wanke Baban ya shigo ya dube ta, ya ce, "Ke ki je wancan yaron na son ganinki Sulaiman".
Tsam ta mike da sauri ta yayimi hijabi ta fice, bayan ta wanke hannunta.
Tana fara'a ta dube shi, shi ma ita yake kallo cikin farin cik da sake ganinta, sonta yana dawo masa a rai, ya ce, "Mabaruk a?"
Та се, "Na'am Sulaiman?"
Ya yi ajiyar zuciya, ya ce, "Sai yau Allah ya yarda
zan ganki, tuni nake zarya gidan nan amma Baba Hamza sai ya hana ni ganinki, wai kina idda ne, sai kin gama. Na ga dai ai gaisuwa ne".
Ta сe, "Пaka ne, ni ma haka ya takure ni ya sa min ido sosai, tuni dama nake son ganinka in maka albishir na fito".
Ya ce, "Na ji zancen nan, Yaya Binto ta sanar min
na yi favin cikin da ban taba yinshi ba. Daman haka nake ba
mata
Ta zaro ido, ta ce, "IHaba, ina Nafeen?"
Ya ce, "Inna mana ta kore ta tuni, amma ina sa ran dawe warta kusa-kusa".
Ta ce, "Gaskiya kam ka kokarta, mai hakuri da
biyayya".
39
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya ce, "Sosai zan dauki mata biyu, kina gama iddar
zan turo insha Allah ba zan sake yarda ai min sakiyar da
babu ruwa ba"
Ta yi dariya tana jin wani dadi, ta ce, "Allah ya kai
mu, sai kai wa Baba magana".
Ya ce, "Insha Allahu kar ki damu".
Sun dade suna hira, daga bisani ne suka yi saliama,
daidai fitowar Baban. Suka koma gefe da Sulaiman, ya
shaida masa shi fa har yanzu yana nan kan bakansa. Baban
ya ce, "Kar ka damu, wannan karon ma na maka alkawari,
ka jinkirta ta gama idda, ka san ba a neman aure ana idda.
Zuwan naka ma bai dace ba, don na tabbata ka furta mata
kana nan dai, amma dai zan ga waliyan naka kar ka damu".
Ya ji dadi sosai har alkhairi ya masa, sannan suka yi
sallama ya tafi cike da farin ciki.
RANAR FITA IDDA
Sululu ta tashi shin me za ta ce, farin ciki ko bakin
ciki? Babban abin da ya staya mata a rai mafarkin da ta yi
da lmran, a cikin mafarkin ta ganta tare da shi cikin wani
kayataccen gida mai kyau da tsari, wa. suna rayuwa mai
dadi ita da shi, kowannensu yana cikin farin ciki da dan
uwansa. Wata irin soyayya ta ga suna yi mai tayar da
hankali, wannan abin ya tsaya mata a rai, haka nan kuma
sai ta ji tana jin dadin tuno mafarkin da ma ba ta farka ba,
A wannan ranar haka ta kasance cikin rashin kuzari
da tunane-tunanen mafarkin.
40
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna Bangaren Imran kuwa ya yi bakin ciki sosai, a ranar bai so a ce ta fita iddar ba tare da ta dawo gidansa ba,
amma kamar yanda Baba Hamza ya kwantar masa da hankali, sai ya samu nutsuwa ya bar wa Allahı, idan har
Mabaruka za ta sake zama matarsa ko bayan ta fita iddar za
ta dawo gare shi. Yana fata ta dawo masa da alkhairi.
Ita ko ko da suka je school ta fada wa Rafi'atu
mafarkin da ta yi, dariya ta dinga yi har da tafi. Ta kalle ta
galala ta ce, "Ban gane ba fa Rafi'a, me ye abin dariyar a
nan? Na fada miki ne don ki kwantar min da hankali ba wai
ki min dariya ba".
Та се, "Тo Mabaruka abin naki ya zama na dariya
ke kanki abin a miki dariya ne kin tabbata 'var Tari, har ma
za ki damu kanki ga abu nan kiri-kiri ya nona kuna
soyayya da Imran, wallahi ina ji a jikina za ki koma
gidansa kina mai masifar sonsa fiye da yanda yake miki,
wallahi Mabaruka”.
Ta yi jim tana tunani, can ta ce tana kalkonta, "Ta ya
haka za ta kasance alhalin ba na kaunarsa ko kadan har
yanzu Sulaiman kadai nake so".
Mikcwa ta yi tare da daukar wayarta ta jawo
hannunta, "Kin ga taso mu tafi capteria mu sha cock za ki
ban labari, yanda hakan zai kasance. Kar ki damu my.
friend".
Ba ta iya mikewar ba sai dai ta jawo ta suka fice
jikinta a mace, abubuwan fa suna son faure mata kai.
ン
WAYE ANGON?-4 Maryam Jatar Kaduna
Ranar kwanapta biyu da fita daga iddar da asuba ta
tashi sallah, tana zaune kan dadduma tana lazimi., Baban ya
shigo ya shiga kwala mata kira, "Mabaruka! Mabaruka!!
Da sauri ta fito da ji wannan kiran ba na lafiya ba
ne. ta fito tana cewa, "Na'am Baba, ga ni”.
Ya ciro goro daga aljihunsa manya-manya уa.
damka mata, “Amshi nan".
Ta sa hannu biyu ta karba tana cewa, "Na me-ye
Ya ce, "Na daurin aurenki ne, yanzu aka daura da
asubar nan shi ya sa ma na dan jima ban dawo baR
Gabanta ya yanke ya fadi, ta dube shi da sauri tare
da cewa, "Aurena? Da wa? WAYI ANGON?” Bakinta na
rawa.
Ya ce, "Wa ki ka ce min kina so, tun yaushe ki ke
fada min kina son wannan yaron?"
Bakinta na rawa cike da fargaba ta ce, "Su..su
lai... lai... man?"
Ya cc, "To da shi aka daura mana, shi kenan na
huta".
Goron da ke hannunta ya sulale ita ma-ta bi shi a
sulale tana salati, "Lalilaha illallahi vuhammad rasulillahi
sallaliahu alaihi wasallam, na shiga uku ni Mabarukaa
Ya dube ta sake da baki, ya ce, "Ban gane ba, me ye
na huga ukun? Ba fa tsokon mijinki na ce ba, Sulaiman
aro dan gidan su Binto da ki ke nacin soV
Ta dube shi cikın tashin hankali, ta ce, "Yaushe na
cmaka ka daura min aure da shi don kawaj na ce ina
wosh
42
WAYE ANGDN?-4 Maryam Jafar Kaduna
a
Ya tago cikin bala'i, "Kundun babarki, don ubanki
tun yaushe ki ke cewa shi ki ke so, kuma shi ki ke son aure
tun kan ki auri wantan ba irin kuka da haukan da ba ki ba
kan an ki daura miki aure da shi, yanzu na yi bajinta na
daura miki aurenshi shi ne za ki canja batu? Karya ki ke wallahi".
Hawaye suka fara satata, ta ce, "Amma Baba haka
kwatsam ba shawara da ni, aure haka ban sani ba, ba wanda
ya sani sai kawai ka je ka daura min aure tunda asuba?
Aure fa ba abin wasa ba ne, ya kamata ka yi gaban kanka?"
Ya taso zai dake ta, ta kauce ya ce, "Wallahi yanzu
zan miki shegen duka a gidan nan, 'yar banzar yarinya
tunda aka haife ki ki ke wahalar da ni, ki ce wannan ki ce
wannan wai me ki ke so ne? So ki ke a sa miki ido?"
Ilawayen tashin hankali suka ci gaba da zuba, miyan bakinta ya kafe har wani daci-daci ta ke ji, ta се,
"Amma komai da shawara yana da dadi, sannan koda yaushe mutum yana iya canza ra'ayi don me za ka daura
min aure da Sulaiman?"
Ya daga hannu zai kai mata duka, Inna Binto ta fito
jin hayaniyarsu ta dube shi, ta ce, "Mala.n aure?"
Ya ce, "Eh, ko na yi laifi?"
Ta ce, "Da wa aka daura in ji?"
Ya ce, "Sulaiman".
Ta yi shewa da guda har da juyawa ta ce, "Alkawarin Allah ya cika, ka yi daidai Malam”.
Ya ce, "To ke ma kin gani, amma ja'irar ba ta gani ba".
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Mabaruka ta dubi Innar a gigice, ta ce, "Kar ki ce
haka Inna, kina ganin an yi daidai-kenan a daura min aure
ban sani ba sai bayan an daura, ba a tuntube ni an ji ina da
ra`ayi a kai ba ko na canza
Ta ce, "Amma Mabaruka tun yaushe ki ke cewa
Sulaiman ki ke so, kin sha mana kuka a nan ke shi ki ke so,
don an daura sai ranki ya бaci? A ganina farin ciki za ki
yi
Ta сe, "Ki gane Inna ba kowane lokaci mutum ke
kan ra`ayinshi ba, zai fa iya canzawa".
Ta ce tana kallonta a nutse, "Me ki ke so ki се
kenan?"
Ta yi shiru tana kallonta, ta rasa me ma za ta ce ita
dai sam ba ta yi murna da daura auran nan ba, haka nan
kuma ta rasa dalili. Amma can kasan zuciyarta akwai abin
da ta ke so, ba haka ba. Amma ta rasa mene ne wannan
abin da ta ke so. Sam ko kadan ba ta ji farin ciki ba da
auran ba ta murna duk da tana ikirarin tana son Sulaiman
din.
Ganin ta rasa ba ta amsa ya sa Innar ta dube shi, ta
ce, "Amma Baban Mabaruka ya aka yi haka,yaushe
wakilan namu suka zo ku ka yi maganar?"
Ya ce, "Jiya da dare suka zo, mun dade muna
magana. Sun zo sun kawo sadaki, ni kuma kawai na ce to
gobe su zo nan da asuba sai a daura kawai, magana ta kare.
Ba su yi musu ba kuwa suka amince, a haka muka rabu da
su. Na shigo na tarar kina ta shirma bacci, ban tayar da ke
44
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ba na kyale har da asubar nan na fice masailaci muna sallah
aka daurа".
Mabaruka ta dora hannu saman kai tare da afshewa
da kuka, "Na shiga uku Mabaruka, me ya sa ka min haka?
Wallaki bana murna, ya zan yi kenan?"
Inna ta dube ta cike da bacin rai, ta cе, "То... ko na
gano ki yarinya, ba komai a cikinki sai munafunci, ashe
Karya ne bakinki, karya ki ke cewa kina son dan uwana,
ashe ba haka ba ne saboda shi talaka ne so ki kai ki koma
gidan tsohon mijinki yaudararriya, to Allah ya kama ki,
inda ba ki so din can za ki je gidan talaucin, sai dai ki mutu
ba yanda za ki tunda an daura aure, mu ba kya sonmu, ban
taba zaton haka daga gare ki ba, na gode".
iDaga haka ta wuce, shi ma ya dube ta, ya ce, "Sai
dai ki mutu aure dai an daura, munafuka!" Ya wuce daki
yana cewa, "Kan na fito in tarar da gawarki:
Ba ta saurara ba ta shige daki tana kuka tamkar
wacce aka aiko wa da mutuwa: Ta dauko abin da za ta
dauko ta fito daga gidan, tana tafe tana kuka har ta samu
adaidaita sahu sai gidan Momynta. Da kuka ta shiga idan,
iun daga daki Momy ta jiyo kukanta, a rice ta fito. A falo
suka hadu, da zuwanta ta fada jikinta tana kuka har suna
kokarin faduwa. Ta ja ta suka zauna cikin wani yanayi,
Allah sarki uwa hankalinta ya tashi iaatuka da ganin yar
lata haka duk ta birkice ita ma, ta ce, "Ya isa ki bar kukan,
fada min me ya faru?"
45
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Kukan ya hana ta fada, da ta zo za ta fafa sai kukan
ya hana ta. Ta dafa kafadarta cikin kulawa ta ce, "Nutsu
Mabaruka ki fada min me ya same ki".
Cikin kukan ta ke fada mata bayan ta riko
inunta, ta kankame ta ce, "Baba ne ya daura min aure da
Sulaiman yanzu".
Ta dube ta a zabure tare da faduwar gaba, ta ce,
"Aure? Ya aka yi haka?"
Ta ce, "Ban sani ba, wai... wai jiya suka zo masa da
sadaki da dare, shi ne ya ce wai yau su zo kawai a daura.
Na shiga uku Momy, wallahi bana murna da auransa, ya
zan yi?
Ta yi jim wuta ta dauke mata, shin me za ta yi ne?
Anya za ta yarda 'yárta ta shiga mawuyacin halin gidan
Inna? A wahala da rashin daraja za ta yarda rayuwar 'yarta
kare a haka da wahalar surakkuwa? ia
Ta dafa ta, "Momy ki taimake ni, ki yi wani abu ban
san me ya sa ba bana farin ciki, ban shirya ba yanzu".
Ta dube ta cikin damuwa, ta ce, "To me zan yi
Mabaruka tunda an riga an daura, Babanki ne ya za mu yi?
Dole ne ki je ki zauna ki ta addu'a ita e mafita, Allah ya sa
can ya fi zama alkhairi gare ki, ki yi farin ciki a can ina
miki fatan alkhairi".
Ta dube ta galaia da baki cike da mamaki, ta ce,
"Kina nufin ba abin da za ki iya yi sai dai na yi hakuri na
je?"
Та сe, "A'a ikon Allah, nan fa ki ke min kuka da
ihu, kaliya da raci ba wanda ba ki min ba ke iallai
46
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Sulaiman ki ke so, shi za a daura miki, ba kya son Imran.
To yanzu me ya canza miki, kar fa ki manta Sulainman dinki
ne?"
Ta fada jikin kujera ta jingina tare da dafe kai, ta ce,
"Kina son ki ce min kin daina son Sulaiman akwai wanda
ki ke so?"
Ta tashi zaune sosai yana kallon Maman nata, ita
kanta tambayar kanta ta ke ta daina son Sulaiman kenan?
To wa ta ke so? Amsar tambayar ta gagara ita kanta ba ta
san me ye amsar ba, me kenan hakan ke nufi?
Momy ta ce, "Kin ga Mabaruka ki nutsu ki fahimce
ni, ba wani abu ba ne don kin auri Sulaiman tunda da ma
kina sonshi, kawai abin da ki ke ji don ya zo miki kwatsam
ne ba tsammani shi ya sa ki ke jin haka, ba ki shirya wa
abin ba. Amma ki saki ranki zan miki duk wani shiri da ya
dace da ke, za ki je gidan mijinki kina mai farin ciki, ku
zauna lafiya insha Allahu za ku zauna lafiya, kin ji ko? Ki
nutsu ba wani abu ba ne".
Ta yi shiru tana juya maganar, anya haka ne ba
kawai don ba ta shirya ba ne, akwai dai wani abun? Ta
katse ta, "Ki yi addu'a, Allah yana sane za ki ji dadi insha
Allahu kin ji ko 'yata?"
Ta daga kai alamar to, da gamsuwa da zancen
Maman, ta ce cikin nauyin baki, "Shi kenan kimin addu'a
Allah ya sa haka shi ne mafi alkhairi, in daina jin abin da
nake ji a raina.
47
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "Insha Allah ina miki fatan alkhairi, addu'a
kuma ina miki koyaushe duk inda ki ka shiga za ta bi ki,
kin ji ko?
Ta daga kai alamar to.
Ta mike tare da jan hannunta ta ce, "Zo mu je ciki".
Ta mike din ta bi ta jiki a mace da rashin kuzari.
Duk maganar da suka yi a kunnen Imran tun
shigowarta tana kuka ya mike daga kan gadonshi a
kokarinshi na ya fito, amma jin wannan bakar magana
mummuna ya jingina da bango tare da lumshe ido yana
kiran sunan Allah don samun nutsuwa har suka gama. Yana
tsaye dafe da kansa cikin wani tashin hankali, jikinsa ya
hau rawa zufa ta keto masa da kyar ya iya jan kafafunsa
zuwa gadon ya fada a rigingine ya dafe kansa da ke masifar
sara mishi. Ya runtse ido gam wasu hawaye masu dumi
suka zubo, ya furta a fili, "Ya haka? Me ya sa haka? Ina
sonki fa Mabaruka, me ya sa za ki aure gidan wani ki bar
ni? Ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba, kullum ana kara
min sonki, rasa ki tamkar rasa numfashina ne, ba zan iya
jure rashinki ba, zan cutu matuka. cutuwa, don Allah ki
dawo gare ni Mabaruka".
Ya fara kuka tare da buge-buge tamkar mace, duk
abin da ya zo gabansa zai buge cikin kankanin lokaci
72zzafan zazzabi ya rufe shi, jikinsa har karkarwa yake, ya
Kudendune cikin bargo idanunsa na zubar da hawaye.
48
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Sai can rana ta kira Rafi'atu a waya ta sanar mata ta
same ta gidan Momy akwai matsala. Da hanzari ko ta zo, ta
dube ta, ta ce, "Lafiya Mabaruka, me ya faru?"
Ta tashi zaune daga kwanciyar da ta yi a kan gadon Momy, a marairaice ta ce, "Rafi'atu Babanmu ya min
katsalandan, ya gutsire min rayuwa ba tare da na tsammata ba".
Ta dube ta cikin kaguwa ta ji mene ne, ta ce, "Fada
min Mabaruka, hankalina a tashe yake".
Ta ce, "Rafi'atu Baba ya daura min aure da
Sulaiman yau da asuba ba tare da shawara da ni ba".
Ta dafe kirji tare da salati saboda faduwar gaban da
ta yi, ta rike ta da sauri a firgice, ta ce, "Ya aka yi haka
kwaisam, me ya sa bai ba ki lokaci ba?"
Ta ce, "Ban sani ba Rali'a, shi dai ya yi amfani da
tunda da nake cewa ina sonshi”.
Ta dube ta da sauri, ta ce, "Me ki ke so ki ce min,
kin daina sonsa kenan?"
"Ta kalle ta jim tsawon lokaci, sanman ta се, "A'a
ban daina sonsa ba, ni dai kawai abin da ke zuciyata nake ji
bana farin ciki da auransa, ban yi mura ba da auransa".
Та се, "Тo da wa ki ka so ki ąura?"
Ta sake yin-shiru, can ta ce, "Ba kowa, Sulainan
din dai naké son aure, amma a yanzu ban ji dafin auran
nasa ba, ban san dalilin hakan ba".
Ta