yi jim tana kallonta tana mamakin yanda
Mabaruka ta ke yarinya, sam wasu abubuwan ba ta sansu
ba ko don tana 'yar fari, auta kuma gurin Mamanta? Amma
49
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
a ce takamaimai ba la san me ta ke so ba, kuma ta rasa
dalilin hakan? Ta kalle ta, ta ce, "Magana ta Kare
Mabaruka, an riga an daura a nan ban ga wata shawarar da
zan iya ba ki ba face in ce ki saki ranki ki karbi auran
tsammanin da aka daura miki, ki zauna lafiya da mijinki
abokiyar zamanki, uwa-uba sarakkuwarki. Ki rike addu'a
wannan ita ce shawarar da zan iya ba ki, al'amurranki
Mabaruka ban san me ya sa suke zuwa haka ba, anya
Mabaruka kina kuwa yawaita addu'a komai sai ya zo da
matsala?"
Ta yi narai-narai da idanu, ta cc, "Ina tsoro Rafi'a,
bau san me gaba za ta kasance a rayuwata ba".
Ta nisa tare da daſa kafadarta cikin kulawa, ta се,
"Kar ki damu Kawata, ki rike Allah ba abin da zai same ki
sai alkhairi, za ki yi murna gaba, za ki farin ciki. Idan kin
samu sukuni ko a gidanki ne ki shiga islamiyya za ki samu
addu'o'in da shawarwari gurin malamanku, ki kuma san
yanda rayuwar 'ya mace ta ke a musulunci".
Ta dube ta tana fadin, "Ina da karancin ilimin
addini ko Rafi'a?"
Ta daga kai, "Sosai Mal.a.uka, kina da karancin
hakan kin fara ki ka watsar da kin dage kin yi wallahi da
abubuwa ba su zo miki haka ba. Kar ki sake Kawata”.
Ilawaye suka zubo mata, ta jinjina kai cikin
gamsuwa, "Insha Allah na miki alkawari zan shiga,
sannan zan je gidan aurena in zauna inda Allah ya kai ni in
yi biyayya ga mijina, amma ki taya ni addu'a Allah ya yaye
50
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
min kunci da rikitaccen al'amarin da ke damuna don Allah
Rafi'a".
Ta riko hannunta daidai sake zubowar wasu
hawayen, ta roke ta ita ma, ta ce, "Insha Allah zan taya ki
Ta jawo ta jikinta, ita ta san me ke damunta, amma
fadin ba shi da mana'a tunda gidan wani za ta je magana ta
kare, dole ne ta yi iya bakin kokarinta kan kwantar mata da
hankali duk da ba ta so ta yi aure a gidan Inna ba, tana
tausaya mata. Ta sososai ta koma gidan Inran, a ganinta
shi ne mafi dacewa da rayuwarta, ba za ta taimaka ba wajen
tayar mata da hankali ba, kamar yanda Maman ta yi kowa
ya san ba ta son ta auri Sulaiman ko da ba za ta koma gidan
Imran din ba ita ta san matsalarsa, to amman tunda an
daura babu amfanin ta tayar mata da hankali kamar yanda
ta tayar da hankalinta. In har tana son farin cikin 'yarta da
nutsuwarta to dole sai dai ta goyi bayan Baban don ta sa
mata nutsuwa, zance dai ya kare tunda an riga an daura,
amma tana bakin cikin auranta gidan Sulaiman.
Ranar a nan ta wkana duk da yanda Sulaiman ya so
ya ganta saboda azarbabin zuwanta kwana uku ya sa
tariyarta, sam ta hana masa ganinta. Jin aa ce nan da kwana
uku ya sa ta dinga wa Momyn kuka don me nan da kwana
uku, a bari sai bayan sati biyu ita fa ba ta shirya ba. Tа
dube ta cikin damuwa ta ce, "Haba Mabaruka me ye kwana
uku an fa yi mai wuya, ba ki da wani shiri ki yi hakuri ki
tafi gidan mijinki tunda an riga an daura duk wani abu da
ya kamata zan miki insha Allah kar ki damu, ke dai ki je ki
ta addu'a.
51
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta kwanta jikinta tana cewa, "Shi kenan Momy,
Allah ya kai mu
Та се, "Amin". Tana shafa kanta, "Allah miki
albarka".
Baban kam da man tunda ya duba ya ga ba ta nan
ya san tana can dòn haka bai damu ya san ina ta tafi ba.
Shi ko ango yana can yana ta hidimar tarbar
amaryar kamar yanda yake ziyartar Nafisa gidansu ya same
ta ya shaida mata batun auransa da Mabaruka. Sosai ta yi
murna ta dade tana son auranshi da Mabarukar, ta kara
masa kwarin gwiwa, ya shiga fito da duk tarkacen da ke
dakin ainahin dakin da aka taba ba Mabarukar.
Inna ta ga ana fito da kaya zuwa wani dakin, ta fito
fana kallonsa, ta ce, “Sulaiman?"
Ya dago yana kallonta tare da amsawa, ta ce, "Ina
za ka kai min kaya ka ke ciro min, me za ka yi da dakin?"
Ya ci gaba da aikinsa tare da cewa, "Wai dan fenti
za a yi muku, duk wannan ya tsufa”.
Ta dube shi da kyau, ta ce, "Anya? Na fa sanka kar
in ji wani zance can.
Ya ce, "Wane zance? Ki yarda da ni mana"
Ta rausayar da kai tare da cewa, "To shi kenan, ai
za mu ganı
Bai ce komai ba ya share ta ya ci gaba da aikinsa.
Aka yi wa gida ras!
Ana gobe tariyar aka zo jere, sai dai ta ga mala na
shigowa da kaya, manyan mata masu ji da naira 'yan gayu.
Kaya na lada da ba da labari ba komatsai ba. Bayan sun
52
WAYE ANGON?-4 Maryam Jatar Kaduna
gaisa cikin mutunci suka ce, "Mu ne iyayen amaryar, mun
zo jere ne, ko ina ne dakin da aka ba ta?"
Ta dube su daidai, ta ce, "Amarya? Nan gidan?
Anya ba kuskure ku ka yi ba? Ba nan ba ne za a kawо
mana amarya ba".
Suka hau kallon-kallo suka ce, "Ba nan ba ne gidan
Sulaiman ba?"
Ta ce, "Tabbas nan ne”.
Suka ce, "To ai nan din ne, shi ne mai auran".
Ta ce, "Sulaiman shi ne zai yi aure ban sani ba?"
Suka yi shiru suna kallonta cike da mamaki, ta ce,
"Shi kenan ya kyauta tunda ba ni da wani matsayi da zai
fada min sai ya san mai ba shi daki, ba dai a nan gidan ba".
Suka ce, "Amma Inna an riga an daura ya za a yi
haka? A yi hakuri dai, me yiwuwa da dalilin rashin sanar
miki din".
Ta taso cikin fada, "Kai kar ku gaya min maganar
banza, dalilinsa na banza? Ina uwarsa amma don ubansa ya
ki sanar min, wato har an daura aure? To wallahi ba dai a
nan ba".
Abu fa yana kokarin zama fada, tamkar ta dake su,
kamar su suka yi laifin. Samira ta ja hannunta tana cewa,
"Zo ki ji Inna".
Ta ja ta gefe ta dube ta, ta ce, "Haba Inna ke kuwa
sai kin nuna masa halinki a tafi ana yi da ke duk sai bakin
mutane ya kama ki?"
Ta ce, "Na yi din, su cinye ni. Gaskiya ce nake fada
ban yarda da karya ko munafunci".
53
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
a
Ta ce, "To ki yi hakuri ba dai sun zo da kaya ba, to
ki barsu su jera gida ai namu ne, mun ga yanda za a yi
kawo amarya, da guda-guda in dinga dauka iba sayar mana
muna cin balangu".
Ta washe baki, "Allah 'yar nan?"
Ta ce, "Wallahi, to ki kyale su su jera za mu yi
maganinsu, kin manta wadancan muka fara saidawa sai
daga baya suka zo suka kwashe?"
Ta сe, "Пaka ne fa".
Та сс, "Тo kyale su su yi, in ya zo ki ci
mutuncinsa.
Ta ce, "Shi kenan, zai hadu da ni, ni ya maida za a
mana fenti wancan ya tsufa, ashe amarya ya yo, zai cі
ubansa.
ke". Ta yi tafi, "Yauwa Innarmu, Allah bar mana
Ta ce, "Amin, ai ke rainona ce, ba mai raina ki ko
kin yi aure.
Ta ce, "Haka ne kam, mu je kar su ji shiru".
Ai ko haka aka yi suka jera daki ras da kaya masu
tsada da kyau, tabbas naira ta yi kuka, sai dai kash! Duk
kyansu ba su kai wanda aka kai nata gidan Imran ba,
wannan ga shi ba shiri, ba kuma murna ake da shi ba
sannan ba guri daki daya ja! ko kicin babu. Wannan kenan.
Imran ko yana nan kwance lokaci guda duk ya bi ya
fige, tamkar wanda ya shekara kwance, to ba ci ba sha, su
Momy da Dady suna tsaye kansa gidan koda yaushe cike
yake da mutane 'yan dubiya, daga Mommy sai Daddy suka
san ciwonsa, gwanin tausayi kai so masifa ne wani lokacin,
54
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Allah ya jarabce shi da soyayyar Mabaruka ta barshi cikin wahala.
Dr. Faruk ya zo duba shi, shi ne likitansa yana tsaye
yana sa masa drip ya dube shi cikin rashin kuzari ya сe,
"Ka daina wahalar da kanka, ka je ka huta wannan duk ba
shi zai sa in warke ba, ba ku da maganina. Mabaruka се
kadai maganina, in har za ku kawo min ita ni na san zan
tashi, kuna wahalar da kanku ne Doctor".
Ya zauna gefensa yana kallonsa, ya ce, "Haba
Imran, kar ka ce haka. Mabaruka ba ita ba ce maganinka
ba, ka sha magani za ka samu sauki. Ka yi kuskure da ka sa
soyayyarta a ranka bayan ka san ba ta sonka, yanzu me ye
amfanin ci gaba da soyayyarta har kana kokarin rasa
lafiyarka alhalin tana matsayin matar wani?"
Tamkar ya watsa masa ruwan zafi ya ji, yanzu
Mabaruka matar wani ce ba matarsa ba, ta fita sunan
matarsa kenan.
Ya yi dif takaici ya hana shi magana, likitan ya ci
gaba da rarrashinsa, amma sam ba ya jinsa, dole ya gaji ya
kyale shi.
Ana gobe za ta tare suka fita kunshi da saloon ita da
Rafi'a an zuba mata kunshi mai kyau da gyaran kafa.
Rafi'a ta dafa ta, ta ce, "Kin yi kyau kawata, kin ganki
kuwa?"
Ta yi murmushi iyakarsa fuska, ta ce, "Ban manta
ba, haka aka yi wancan karon ana min kunshi da gyaran
jiki, amma sam ba na cikin farin ciki da murna kamar
55
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
yanda sauran amare ke yi, suna farin ciki da walwala,
nishadi saboda za su tafi gidan masoyansu. Wannan karon
ma ga shi nan haka ne, ba na farin ciki har yanzu kuma ban
san dalilin hakan ba".
Ta dago ta kalle ta, "Sai yaushe ne zan yi farin ciki
da aurena kamar kowa?"
Ta zauna tana kallonta cikin damuwa, "Ilaba
Mabaruka, me ya sa ki ke furta haka? Kowa fa da tsarin
rayuwarsa ba iri daya ba ce da kowa, mene ne ciki nan to
za ki yi farin ciki idan ki ka je, Sulaiman dinki ne fa".
A sanyaye ta ce, "To Allah ya sa ina fatan hakan ya
kasance".
Ta ce, "Insha Allahu kawata kar ki damu, za ki
farin ciki a gaba".
Sai ranar da za ta tare sannan Sulaiman ya kawo
mata kayan sawa, atamfofi biyu, leshi daya sai shadda an
dinka biyu da 'yan tsiraran kayan kwalliya.
Rafi'atu ta ja ta dakin Imran su gaishe shi da jiki, ta
dube ta a marairaice ta ce, "A'a Rafi'a bana son haduwa da
shi".
Ta dube ta da sauri ta ce, Caboda me?"
Ta yi jim sannan ta ce, "Kawai dai ban san dalili ba,
ni dai kar mu je".
Ta jawo hannunta ta ce, "Kar ki damu Mabaruka,
ganinshi za mu yi da jiki, ba za mu jima ba".
Kan dole la biyo Rafi'atun har dakinsa, suka
kwankwasa. Daga shi sai Dr. Faruk, suka shigo tare da
zama a kan kujerar da ke gefe. Rafi'ar la taso har zawa
56
A
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
bakin gadon inda yake cike da tausayi ta dube shi, "Sannu
Ya Imran, ya jikin?"
Ya dan dago ya kalle ta ya maida kansa tare da
cewa, "Alhamdu lillahi".
Duk da ta ga alamar sauki a jikinsa ya yi kyau
sosai, to amma yanayin yanda ya amsa mata kamar yana jin
haushinta. Abin da bai mata dadi ba, ta ji wani iri, ba haka
suka saba gaisawa ba, duk sai ya sage mata gwiwa. Ta nisa
tare da cewa, "To Allah ya kara sauki".
Bai ce komai ba, haka ta dawo jiki a sanyaye ta
dubi Mabaruka wacce da ganin fuskarta ka san akwai
dumbin damuwa a tattare da ita, kamar har da dan tsorotsoro.
Ta ce, "Ki je ku gaisa".
Ta kalle ta tare da girgiza kai alamar ba za ta iya ba.
Rafi'a ta ce, "Saboda me? Ba gaishe shi ki ka zo yi
ba? Ki je ku gaisa bari in fita".
Ta yi saurin riko ta alamar rokonta, ta ce, "Mene ne
haka Mabaruka? Ki je mana".
Ta janye jikinta tare da duban Dr. Faruk ta се, "Mu
je waje".
Tamkar jira yake tsam ya mike suka fice, ya zamto
daga ita sai shi a dakin. Yasan tana dakin amma yai shiru
ya share ta, ganin babu amfanin zamanta a gurin ya sa ta
mike tsam za ta lita tana cewa, "Da ma na zo na gaishe ka
da jiki, Allah ya kara sauki, sai anjima".
57
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Har ta kai bakin kofa ya tsayar da ita, "Na san kina
farin cikin kin rabu da ni nanataccenki kamar yanda ki ke
cewa, za ki je gidan masoyinki zuciyarki".
Ta juyo da sauri cikin marairaicewa, za ta yi
magana, "Ba haka ba ne wallahi, ban..."
Kan ta karasa ya mike da sauri cikin tsananin tashin
hankali da tsawa ya katse ta, "Ba ki da abin da za ki ce,
muguwa marar imani da tsoron Allah. Burinki ya cika ni da
ba ki so na bar miki rayuwarki, karshe ma bar miki duniyar
zan yi ke ko za ki je ki rayuwarki da masoyinki. Na gode
Mabaruka, na gode da tsanar da ki ka min". Ya fada daidai
zubowar hawaye.
Hankalinta ya tashi tunda ta ke ba ta taba ganin
babban mutum na kuka gabanta ba, kalaman da ya fada
tamkar ba daga bakinsa ba, ya juya sam daga Imran mai
hakuri da sanyin hali, har yana kiranta muguwa? Kalaman
sun tayar mata da hankali.
Ta dube shi ya zauna bakin gado yana kuka, kuka
mai karfi da sauti hawaye wasu na tunkudo wasu sai a yau
ta ke ganin abin da yake fada a idonsa a yau ta ke jin
kwatánkwacin abin da yake ji tsanisár kaunarta ta gani a
idonsa.
Wannan shi ne karo na farko a rayuwarta da ya fara
ba ta tausayi tamkar tai masa kuka, ta fadi gabansa tare da
durkusawa hawaye suna zubowa masu zafi da daci, ta
kama kunnuwa cikin tsananin nadama da matukar tausayin
kanta da nasa.
58
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya dube ta, ta dube shi dukkansu hawaye na zuba,
ita tana yi shi yana yi cikin wani yanayi iri daya da zafi da
zukatansu ke musu.
Da kyar ta iya buda baki ta ce, "Sorry! Sorry!!
Sorry!!!"
Ta ci gaba da kukan, "Na yi nadama, na yi nadama
Ya Imran, ina cike da dana sani da rashin sanin me zan yi,
na cuci kaina Ya Imran, na wulakanta kaina ba kowa ba ce
ni face butulu. Na bijire wa kyautar da Allah ya min,
mahaifiyata ta min gatan da duk kowacce uwa ta ke son tai
wa 'yarta ta ko ina an min gata, an min halacci, amma na
kasance butulu na runtse idanuwa, zuciyata ta kurumce
baua jin komai, bana ganin komai da kowa sai abin da
zuciyata ta ke so".
Ta sake fashewa da kukan tana kallonsa, "Sai a yau
nake nadarna da dana sani ranar da ba ni da sauran dama,
lokacina ya wuce, damata ta kare. Ranar da ba ni da sauran
daraja ko kima da zan dawo da su sun guje ni. Ban san da
wane ido zan kalle ka ba, ba ni da bakin ba ka hakuri,
nadamata ba ia yi amfani ba lokacin da ba zan iya maka
maganin abin da ke damunka ba, ni ma yake damuna a
yanzu in..."
Da sauri ya katse ta yana kallonta da idanunsa da
suka sauya, hawaye na zuba.
"Ba ki da abin da za ki ce har abada, ba ki da wata
magana da za ki in yarda da ke. Ina nan a yanda nake
gurinki na san ba zan taba canzawa ba, mutum daya ki ke
59
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
so, kuma bukatarki ta biya shi ke nan ki je ki tashi ki tafi
gıdan masoyinki ni ne daman ba ki so
Ta kalle shi da hanzari ta ce, "Wallahi ina..."
Ya katse ta, "Kina me? Karya ko ko yaudara
lokacin da ki ka san ba yanda zan yi na sake takura miki, ba
na tunanin haka har abada".
Ta ce, "Wallahi Ya Imran ka yarda da ni-na..."
Ya katse ta, "Don Allah ki tashi ba na son ganinki,
ba zan taba manta ki ba a rayuwata kin min tabon da ba zai
taba gogewa ba, ki sa a ranki koda yaushe ina tuna abin da
ki ka min da tsanar da kika min, tashi ki je".
Z.a ta yi magana ya daka mata tsawa, "Bana son jin
komai, tashi ki je”.
Ta sake fashewa da kuka tana kallonsa, tana son yi
masa magana amma ya hana ta.
Karshe ma bandaki ya shige yana cewa, "Idan kin
gama ki rufe min kofa".
Kai wannan abu na da takaici da bakin ciki,
mutumin da da yake rawar jiki da kai yake son koyaushe
kana kusa da shi, amma yau wai shi ke korarka?
Ta tashi ta fita da gudu íana kuka, ta gaban su
Rafi a ta wuce suka bi ta da kallo. Rafi'ar ta kwalo mata
kıra ganin ba ta da niyyar amsawa ya sa ta mike ita ma ta bi
ta da gudu, dakinta ta shige da zuwa ta fada gado tare da
fashewa da kuka mai tsanani.
Rafi'ar ta zauna kusa da ita cikin damuwa tana
cewa, "Mene ne Mabaruka?"
60
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta dago fuska share-share da hawaye ta ce, "Na
shiga uku Rafi'a, Imran ya canza min, ya daina sona,
tsanata yake yi
Rafi'a ta dube ta tana fadin, "Me ki ke son ce min,
kina bukatar son nashi ne da za ki damu kanki?"
Ta ce, "Ki fahimce ni Rafi'a ko ba na bukatar ya so
ni bai kamata ya tsane ni ba, me ya sa zai ji haushina?"
Ta ce, "Kina jin ciwo ke nan?"
Ta daga kai alamar eh.
Та се, "То kar ki manta wannan shi ne kadan daga
cikin abin da yake ji lokacin da ki ka tsane shi".
Ta yi jim kanta a kasa, sai can ta dago ta dube ta, ta
ce, "Na yi nadama Rafi'a da ina da hanyar da zan gyara
kuskurena wallahi da na yi, sai ya yi mamakina da kowa
ma, sai dai kash ba ni da wannan damar-nai wa kaina
Rafi'a".
Ta ce, "Ba komai, Allah ya ga zuciyarki, ki je gidan
mijinki ki masa biyayya ku zauna lafiya shi ne babban abin
da za ki yi yanzu, kuma shi ne a gabanki".
Ta koma ta kwanta lamo tana jin kunci a ranta,
hawaye na ci gaba da zuba.
Yamma lis aka zo da motar daukar amarya, bayan
ta koma gidan Baban ta sha. kuka sanda za ta bar gidan
Momy duk abin da ya kamata Momy ta yi ta mata, bayan ta
damka mata kudade saboda toshe matsalolin da ko da za su
taso tamkar za a cire mata rai ta ke ji.
61
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ga ta a mota zuwa gidan Sulaiman wanda ta nemi
farin cikin da ta ke tsammani za ta yi idan aka ce yau ga la
za a kai ta gidan masoyinta, kunci ya mamaye ta miyan
bakinta ya kafe har daci-daci ta ke ji, har aka iso lokacin da
za ta shiga gidan ta runtse ido gam tare da ambaton Allah ta
ce a zuciyarta, "Ya Allah ka sa min farin ciki da wałwala а
cikin gidan nan da na shigo, Ka yaye min duk wani kunci
da damuwa da nake ji. Ka ba ni ikon yi wa mijina biyayya
kamar yanda ka umarta".
Ta zauna kan tumemen gadonta da ya sha
shimfidun alfarma masu tsada da kyau, kanta a lullube.
Nan fa aka dinga shigowa ganin amarya, wannan ya
shiga, wannan ya fita. Tabbas duk wanda ya shigo sai ya
fita da gulma yana jinjina kai, lallai ba 'yar kananan
mutane aka auro ba, kusoshi ne kaf kayanta sabbi dal daga
waje, ko cokali ba a kawo ta da shi ba tsoho wanda ta yi
amfani da shi gidan Imran ba.
Sai dai kash duk irin yanda mutane ke zuzutawa har
a gaban idonta da irin bajintar da Momynta ta yi, babu daya
daga cikin kayan da suka burge ta sam sai a yanzu ta ke
ganin duk na gidan Imran sun fi yau da ma su -aka kawo
mata, me yiwuwa ma ta fi murna da su.
Shi kanshi dakin duk ta ji ya kuntace ta ba wata
yalwa da gadon da kujeru duk a daki daya tal komai а
kukkutse ba abin da ya wala yanda ya kamata. Ta tuno
gidan Imran tamfatsetse mai yalwa, ko ina kal-kal tar
gadonta a tsakiyar dakin yake bare kuma girman falon.
Idanunta suka ciko kwalkwal, ta dubi Rafi'a ta tura
62
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
hannunta cikin nata, ta ce, "Ki taya ni addu'a kawata Allah
ya yaye min masifar da ke damuna”.
Saboda mutane ya sa ba ta ce komai ba, ta jinjina
mata kai alamar gamsuwa. Ta dora kanta saman kafadarta
ta yi lamo.
Sai da aka shigo da amaryar sannan Inna ta gane ko
wace ce, ta shiga daki ta dinga-cizgar fada inda ta ke shiga
ba nan ta ke fita ba, "Ashe wannan yar mahaukatan ya
sake aurowa? Sai da ya kashe mata aure kenan saboda naci,
ashe bai hakura ba? Sai da ya yi yanda ya yi ya auro ta kenan?"
Samira da ke gefe ta ce, "Haba Inna, me ya sa ki ke
son damun kanki, me ye ita din? Ta zauna mana da kanta
ma za ta gudu, nawa muka fitar bare wannan lakasun ba
abin da za ta iya".
Та се, "Кс yarinya ce ba ki san komai ba, iyayenta
kudi gare su, idan har kana auren 'yar masu kudi kai kana
talaka to juya ka za a dinga yi, saboda kudin mai yiwuwa
gidansu ake mata komai har kai ka ci albarka, sai ka koma
sakarai iyayenta na juya ka, ba ka da iko da ita".
Ta ce, "Amma me Yaya Binto ta ce? Mu ma fa za
mu lasa"
Та се, "Кe banni da zancen nan, ban nutsu da shi
ba. Ina nan ina lasa za a lashe min da in zama ba ni iko da
shi, ai ta juya min da, abin da kuma ba zan yarda da shi ba
ke nan
63
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta ce, "Ni ban ga wani abu nan ba, ki kwantar da
hankalinki kawai".
Та се, "Кoma dai mene ne ban cancanci ya min
haka ba, a dauro masa aure ban sani ba, sannan ban san
wace ce amaryar ba? Dole ne in yi fada, wallahi ba za ta
sabu ba".
Kowa ya daware an bar amarya daga ita sai 'yar
wuarta, kawarta kuma aminiyarta Rafi'a suna dakin an
gyara shi fes, an saki labulayen masu kyau da kauri an saki
turaruka masu rikita kwakwalwa, babu wuta sai dai aka
kunna lenter ba laifi dakin ya haske tarr! Duk Rafi'atu ke
aikn yayin da ita tana zaune kan kujera ta yi shiru, tunanika
kala-kala ba wanda ba ta yi, sai dai ka ji ta saki ajiyar
zuciya tare da share kwalla.
Har Rafi'atun ta gaji ta dawo kusa da ita ta zauna
tare da riko hannunta cikin kulawa ta ce, "Mene ne
Mabaruka?"
Ta kalle ta tsawon dakiku kwallar na sake ciko
idanunta, ta ce, “Ba komai". Tare da dauke kanta gefe.
Ta ce, "Amman ba komai ki zauna kina ta ajiyar
zuciya?"
Ta yi shiru, ta sake cewa, "Haba kawata za ki manta
ni ne? Ni ce fa Rafi'atu, ba za ki iya sanar min damuwarki
ba matsayina ya canza kenan?"
Ta kalle ta da sauri, "A'a har abada kina nan a
matsayinki ba za ki taba canzawa ba, ke 'yar uwata ce babu
abin da zan boye miki".
Ta ce, "To na ji me ye dalilinki na ajiyar zuciyar?"
64
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta kalle ta a marairaice, ta ce, "Ke ma kin sani
Rafi'a, har yanzu haushin kaina nake ji. Ban taba ganin
marar sala irina ba, mai makauniyar zuciya. Rafi'atu na yi
bakin ciki na yi asara tunda har na bari Imran ya kufce min,
ina cike da tausayinshi, Rafi'atu ya cutu daga wurina duk
lunanina gidan Sulaiman kadai zan samu farin ciki da
wałwala a nan nake zaton zan nishadantu hankalina ya
kwanta, amma sai na ga akasin haka.
Wallahi Rafi'a ranar da na je gidan Imran ina ganin
ina cikin kunci, ashe farin ciki ne, ashe walwala nake
sabanin nan. Gani nake kamar a birsin nake, an kuntace ni
tsananin kunci ya cika min zuciya, kuncin da nake ciki a
yau da aka ce an daura min aure da Sulaiman ya lunka
ninkin ba ninkin a kan sanda aka cc an daura min aure da
ímran. Wallahi na ſi murna da auran Imran a kan na
Sulaiman, amma saboda rashin rabo na take na ki karbar
kyautar da Allah yai min, na dinga hango nan, ga shi na zo
nan din ban ji wani sauyin da nake tsammanin zan samu
ba, sai ma bakin ciki da takaici na kasa nutsuwa, ba abin da
nake hangowa a yanzu sai Imran".
Rafi'a ta ce, "Sai yau ki ke gani, kin manta lokacin
da nake gaya miki ina tunasar da ke akwai irin wannan
ranar, ki ka nuna min ke kin fi son hakan don kin san za ki
farin ciki. Yanzu ga ranar ta zo kin baro gidan da ba ki so
kin dawo gidan da ki ke so, amma ba wani nutsuwa me ye
ribarki, me ye abin burgewarki a nan?"
Ta fada lokacin da hawaye yake zubowa, ta ce,
"Babu illa ma bacin rai da hasara, na yi kaico da kaina".
65
Maryam Jafar Kaduna WAYE ANGON?-4
Ta dafa kafadarta cikin kwantar da hankali, "To ya
isa, komai ya wuce a duniya ba wanda ba ya kuskure, abin
da ake so ga dan Adam da ma ya tuba ya gane abin da ya yi
baya kuskure ne ya bari, alhamdu lillahi kin yi wannan, na
tabbala gaba za ki kiyaye da duk ma wani wanda ya ji
labari.
Akwai addu'o'in da zan ba ki ki dinga yinsu insha
Allah za ki samu nutsuwa da kwanciyar hankali, duk
damuwarki za ta tafi soyayyar Sulaiman kuma za ta dawo
sabuwa, ku yi zamanku mai dadi da farin ciki insha Allah”.
Ta jinjina