An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
WA ANGON
4
Maryam Jafar Kaduna
HAUSAВООК.СOM
WAYE
ANGONZMARYAM JA AFAR KADUNA
(MTs Khabeer Abdullahi),
WAYE ANGON?-4
GODIYA
Maryam Jafar Kaduna
Ina godiya ga Allah (S.W.T) wanda Ya
ba ni damar kirkirar wannan littafi mai suna
WAYE ANGON? Tsira da aminci ga
shugabanmu Annabi Muhammad (S.A.W) da
alayensa da sahabbansa da dukkan mabiyansa.
Typesetting:-
NURA SADA NASIMAT KT
08131994808
BUGAWA DA YADAWA
DANEJI PUBLISHERS
08037968900/08029035187
2
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
ت
WAYE ANGON?-4
okacin da Imran din ya shiga Momy na Lzaune falo cikin takaicin wannan abin.
Sallama ya yi ya shigo har kasa ya tsugunna ya gaishe ta, fuskarsa ba walwala ba kamar da ba. Bayan
sun gaisa ya mike, ta tashi tsaye tare da kiransa. Ya ja ya tsaya tare da juyowa ta ce, "Ka fada min gaskiya, na sanka ba ka min karya, me Mabaruka tai maka?"
Ya yi shiru sam ba ya jin zai iya fada mata zancen
nan. Ta katsc shi, "Kar ka boye min Imran, ni mahaifiyarka ce, ka kalle ni a haka, kar ka kalle ni matsayin mahaifiyar Mabaruka, ko ma mene ne na san
kai ne da gaskiya, amma me ya faru?"
Matar tana da matukar girma da kima a idonsa,
yana kallonta a matsayin mahaifiyarsa, bai so tona
wannan zancen ba, amma ganin sun dade a tsaye tana
rokonsa ya sa ya zauna ya fede mata duk gaskiyar abin
da ya faru, tun daga kai ta gidansa har jiya cikin dare
zuwa yau da safe, da ta nemi ya sake ta.
a
Kunya ta kama ta, ta gagara haga ido da shi,
Mabaruka ta gama ba ta kunya, da kyar ta iya cewa,
"Allah yai maka albarka, Ya yi maka zabi mafi alkhairi,
Ya zabo maka wata wadda ta fita. Na san ka yi hakuri,
amma ka kara hakuri, ina mai rokonka. Ba zan tilasta
maka ba, haka ma ya isa, insha Allahu za ka ga sakayya
mai girma a wajen Ubangiji".
Maryam Jafar Kaduna WAYE ANGON?-4
Sun dade suna tattauna maganar, ya nuna mata
bai rike ta da komai ba, da man ta fada ta ce ba ta sonsa,
dolc aka mata don haka duk abin da ta yi kar a ga
laifinta, bacin rai ne dole sai ya yi shi, amma zai wucc,
shi ya ci gaba da kwantar mata da hankali.
A firgice ta isa gidan Babanta, sai dai suka ganta
kwatsam. Inna na bakin murhu tana kwalkwale
gwangwanayen alale ta ganta, ta wuce ta samu kujera
'yar tsugunne ta zauna, tare da rafka tagumi hannu biyu.
Inna ta taho tana cewa, "Mabaru lafiya dai ko?"
Ta daga kai ta kalle ta, ta watsar ta ce, "Lafiya".
Ba ta sake cewa komai ba.
Baban ya fito daga daki yana cewa, "Wa nake ji
kamar Mabaruka?"
Ta ce, "Ni сe".
Y a ce, "In ce dai lafiya wannan sammakon?"
Ta turo baki tare da cewa, "Yo ya sake ni".
A tare suka rafka salati, Inna har kwano na kufce
mata, ta ce, "Saki? Y a sake ki?"
Ta ce, "Eh mana”.
Baban ya yi shiru jim, can ya ce, "Amma ya aka
yi haka?"
Ta ce, "Ni da man fa ba sonshi nake ba, na gaji
shi ya sa kawai ya sake ni".
Ya ce, "Au ke ki ka nemi sakin kenan?"
Ta ce, "Eh".
E
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ya cc, "Amma yau an yi ja'ira, da ma haka ki ke ashc ba ki da wayau don ubanki wa ke kin mai kudi? To kin zo nan in miki mc a nan?"
Ta kalle shi cikin jin haushi, ta ce, "Yo ba gidanmu ba nc, ina zan je to?"
Ya ce, "Dole ki yo nan kam ‘yar bakin ciki, ki
zauna can mu dinga lasar arziki shi ne ki ka kaso auran ki ka dawo min nan ki tsugunna ke babu ni babu? To kin kyauta, ga gidan nan sai ki ci tsiyar da za ki ci a cikinsa,
na koko ma yau babu, dan jarin da za a ba ni kin yi
bukulu shi kenan, zauna ga gidan nan".
Ya shuri takalman ya fice yana bambami duk
bakin cikinsa da takaicinsa ta datse masa hanyar samun
'yan sulalla. Inna ta daga murya ta ce, “Yo ka fita ai
mijin za ka sa a kira maka ka ji dalili, su sasanta ta koma dakinta in ba uku ba ne".
Ta kumbure fuska, ta ce, “Ni ba inda zan je na
fito kenan, kar ma ki fada masa haka, uku ya min".
Ta zaro ido, "Uku?"
Ta cc, "Eh, sai me to?"
Ta ce, "Amma Mabaruka ba Babanki kaďai ki kai
wa ba, har ni. Ina nan ina shirin zuwa in jc mu dan gaisa,
fan jarin alalar ya yi kasa Babanku ya amshe tas sai
kamc-kame nake".
Ta turo baki tare da mikcwa ta shige tsohon
dakinta tana ccwa, "Ku kullum zancenku kudi, Allah sauwakc".
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Lambar Rafi'atu ta kira, ta cc ta zo yanzu-yanzu
ga ta a gidan Baba. Ai ko ta taho don jin kiran ba na
lafiya ba ne. bayan ta iso ta shigo hankalinta na kan
Mabarukar ta shigo dakin, tun kan ta zauna ta ke ccwa,
"Wai lafiya ki ka kira ni haka, me ya faru?"
Ta tabe baki ta ce, "Um wai Imran ya sake ni".
Saboda faduwar gaba ba ta san sanda ta kai kasa
ba, tana jan dogon salati kan ta gama ta ce, "Saki? Me ya
faru haka har ta kai ga saki?"
Та се, "Ke ma kin sani, sau nawa zan fada ba na
sonsa, zan bar masa gidansa?"
Ta zauna sosai tana kallonta, ta kasa cewa komai,
ta ci gaba yayin da idanunta sukai rau-rau, ta се,
"Rafi'atu Imran ya cuce ni, ya lalata min rayuwa bà zan
taba barinshi ba wallahi, yana sane ni ba matarsa ba cе
ya kusance ni jiya, ya keta min haddi". Ta karasa da
kuka.
Rafi'a ta saki baki tana kallonta, mamakinta ya
ishe ta, da kyar ta iya cewa, "Wai me ki ke nufi, kina son
ki ce min tunda ki ka je gidan mu'amaler auratayya ba ta
hada ku ba har sai jiya?"
Ta ce, "Eh, mijina ne shi da zan biye mishi? Me
ki ke nufi ne?"
Tsaki ta ja tare da cewa, "Ban taba sanin ke
bululu ba ce sai yau. Sam ba ki san halacci ba wallahi,
Mabaruka ba kya jin magana, kina son zuciyarki, kin ki
wa mahaifiyarki biyayya kin runtse ido ba kya ganin
6
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
soyayyar da mijinki ke miki wanda har abada ba za ki
taba samun irinsa ba, aurc kuma kin san Imran mijinki ne
ba ki da hujjar karyata haka, kin dauki alhakinsa har
tsawon wannan lokacin bayan kin sha tsinuwar mala'iku
karshc kin 6allo auran. To ni da ki ka kira ni me zan
miki bayan kin gama yanke hukunci, in zo in taya ki
zaginshi ya yi miki fyade, ko ko in fada miki abin da za
ki yi gaba?"
Ta dube ta a sanyaye, ta ce, "Ya kamata ki
tausaya min Rafi'a, dubi halin da nake ciki, na je gurin
Momy ta koro ni, ta yi fushi da ni. Ina cikin musiba fa".
Та се, "Ke ki ka sa kanki ciki, ke ki ka sani
wallahi ba ruwan Rafi'atu, tuni nake ba ki shawara
amma kin yi biris da ni, to tukunna akwai ranar kuka da
dana sani”.
Ta marairaice ta ce, "Sanadin ciwon yatsa na ma
manta da wani ciwon, tuni na neme shi na rasa bala'in da
nake ciki Rafi'a ya hana ni nutsuwa, bana son fushin
Momyna, me ya sa ba za ta fahimce ni ba?"
Tsam ta mike tana cewa, "Kin ga Mabaruka a nan
ba mai fahimtarki, hada da ni ba ni da lokacin wannan
maganar, kin ga tafiyata. In kina son dariyar Momy ni
ma na kasancc da ke, wallahi ki nemi mijinki ku sasanta
tun kan ya miki nisa, in kin dauka to kin min waya in
samc ki gidanshi".
Ta ja tsaki tare da cewa, "Allah ya kyauta! Tir!"
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Та сс, "То shi kenan a sha zama lafiya, sai
anjima". Daga haka ta fice da sauri.
Ta dago murya tana ccwa, "Ko kowa ya gujc ni
bai kamata ke ki barni ba, wallahi ina bukatarki Rafi'a".
Haba! Tuni ta fice, gabadaya ta fice mata a rai.
A nan ta kife tana kuka tamkar ranta zai fita,
wanda ba shi da magani (mu dai sai mu ce Allah ya
kyauta).
A wannan ranar haka ta kasance cikin kunci,
kuka, damuwa ba abin da ta sa a cikinta. A daki ta wuni
har dare aka koma 'yar gidan jiya, kannenta suka
yayumo tabarmarsu mai cike da zarni saboda ruwan da ta
kc sha har kakkaba ta kc. Ta bi su da kallo cikin fargabar
ya darenta zai kasance, ba damar hana su, dakinsu ne,
nan ta tarar da su. Ta dafe kai cike da takaici, haka dai
suka kwana
GIDAN INNA
Ya fara şamun sauki har yana zancen zai dawo da
Nafisa, Inna ta yi tsalle ta dire ta ce, a!Çur'an ba zai yiwu
ba, ba inda za ta zauna tunda ta ga hankalinsa ya karkata
gurinta ba matar da ya taba aure ta shiga ransa irinta, don
haka ta ce ba ta yarda ba, sai dai ya auro wata.
Ya ce, "Ni kuma wannan nake so, ba macen da
zan sakc aurowa, wannan din ita ce kadai me iya zama
da ni, kuma kina nan za ki ga ta dawo". Daga haka ya fice.
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta dago murya a rikice tana cewa, "Sulaiman!
Sulaiman!! Kana jina ka fice ko?"
Haba turi ya yi nisa, ta cc, "Shi kenan za ka dawo
ka sane ni gidan, da ni ka ke zancen".
Kwanania hudu kenan da baro gidan Imran,
babban abin da ke ci mata tuwo a kwarya fadan Babanta
da Inna, kullum da fadan da za su yi harshensu sama ana
jiyo su a makota, har da buge-buge kan naira goma sai su
tashi kura yanzu-yanzu, dole ta ke raba fadan da biyan
wanda aka ci wa ko ba ta yi niyya ba. Gefe ga sauro da
dan banzan zarnin fitsarin kannenta duk da yanda ta ke
gyarawa, gefe kuma ga fushin Momy, har yanzu ba ta
sauko ba, sai na karshen bakin ciki da takaicin, sanin da
Imran din ya mata a matsayin 'ya mace. Ta kan yi kuka
kamar ba za ta yi shiru ba, idan bakin cikin nan sun mata
yawa.
Shi ko Imran ya dawo tsohon dakinsa na gida, ba
ya jin farin ciki idan ya zauna a wancan gidan duk abin
da ya faru za su dinga dawo masa, musamman kwana
daya jat! Da ya yi ba tare da Mabarukar ba duk kuncin
duaiya ya baibaye shi, kai so masifa ne. Allah ya jarabce
shi da son Mabaruka, soyayyarta a cikin jininsa ta ke, da
ita aka halicce shi. Ya yi tunanin duk zagi da cin
mutuncin da ta masa ya manta da ita, ta fita ransa amma
ga mamakinsa kullum da ita yake kwana yake tashi,
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
rashinta kusa da shi masifa ne, yana sonta ainun, anya zai
iya hakuri da soyayyarta? Idan ya duba Mabaruka
yarinya ce har zuwa yau ba ta san mene ne so ba, haka
nan ta ke fadarsa, sannan in ma ta sanshi tuni ta ke fada
ba ta sonshi kar a aura mata shi za ta cutu, sannan abin
da ya faru da daren zai bakanta mata kamar yanda ta ke
cewa ba shi tai wa tanadin kanta ba, dole ne idonta ya
rufe ta caka masa son ranta.
Ya juya kan gadon da yake kwance, daga shi sai
boska a jikinsa, ya fada a fili, "Ina sonki Mabaruka, har
gobe ke ce a raina, ba zan iya son wata ba in ba ke ba, sai
da ke zan iya rayuwa. Rashinki mutuwa ce gare ni don
Allah kar ki guje ni, ki dawo gare ni wallahi zan kare
duk hakkinki, zan kula da ke in ririta ki fiye da kowacc
mace a duniya. Don Allah kar ki guje ni".
Ya sa hannu ya share kwallar da ta fara zubowa.
Wayarsa ta dauki kuka, ya jawo ta cikin mutuwar jiki,
hoton Mabarukar ne a fuskar wayar tana murmushi, ta yi
kyau sosai, ya shafi fuskarta, sannan ya dauka.
Daga can akai magana bayar mai wayar ya gaishe
shi cikin ladabi da girmamawa, ya cc, "Yallabai sakon
nan re ya iso yanun haka muna tare da shi".
Ya cc, "Ok, zan turo maka address din da za kai”.
Ya rankwafa kamar yana gabansa, ya ce, "Shi
kepan Yallabai, an gama, sai na gani".
Ba tare da ya ce komai ba ya kashe, tare da tura
14-a address din. Ya dade a kwance yana juyc-juyen
10
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
tunanin Mabaruka, daga bisani ne ya mike ya shiga
wanka. Kwalliyarsa kamar kullum mai kyau da daukar
hankali, ko ya ya yi ado sai ya haska kuma sai ya burge,
sai dai kwalliyar tasa ta yanzu ba walwala a fuskarsa,
zuciyarsa a cunkushe ta ke, Mabaruka ta hana masa
nutsuwa.
Daddy da Mommy suna zaune kan dinning din
break fast ya fito, har kasa ya tsugunna yana gaishe su ba
annuri a fuskarsa. Bayan sun gaisa Daddy ya dube shi
cikin kulawa da dan nasa, ya ce, "Har yanzu damuwar
ce?"
Ya yi shiru kansa a kasa.
Ya mike daga kan kujerar ya nufo shi, ya taso shi
daga tsugunnen suka mike cikin kulawa ya ce, "be ginat
and patient my son, na san Mabaruka ta shiga rayuwarka,
amma ka daure ka cire sonta a ranka idan da alkhairi
gaba Allah ya hada ku ko kuma kowa ya masa zabin da
ya fi zama alkhairi gare shi".
Ya dube shi cike da mutuwar jiki, ya се, "То
Daddy".
Daga haka bai sake cewa komai ba ya fice daga
falon, Mommy da Daddyn suka saki ajiyar zuciya, yayin
da ita Momyn ta dafe kai ta tsura wa farantin gabanta
ido, shi kuwa Daddy ya bi shi da kallo cike da tausayin
dan nasa, har ya fice. Ya dawo ya zauna yana cewa, "Sai
addu'a ba damuwa za mu taya shi ba".
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta dago ta kalle shi cike da dauwa har ta fada, ta
ee, "Ban san me Mabaruka ta ke nuli ba, taurin kanta yanа
ba ni mamaki. Ni yanzu ban isa da ita ba kenan sai abin da
zuciyarta ke so?"
Ta fada hawaye na son zubowa. Ya dube ta cike da
kulawa, ya ce, "Sai yaushe ne wai za ki bar damun kanki
ne? Na fada miki duk a nan ban ga laifinta ba, babu masu
laifi sai mu da muka nace sai mun aura mata shi alhalin ba
ta so. Mun manta sai da soyayya auran zai yi karko ta
zauna, ta kyautata masa. Sannan zamanin nan an daina yi
a yara auran dole, don samun zaman lafiya da kwanciyar
hankali da gudun fitina ba daidai yake da namu zamanin
ba. Amma muka dage a kan lallai sai an yi, to an yi din ga
shi nan ba wani abu da suka karu da shi sai tashin hankali
da rashin nutsuwa, to bare mu kuma. Ita a kuntace shi a
kuntace, tunda ya gaza samun soyayyarta, don haka ban
matsa ba a kan lallai sai ya dawo da ita ba, su je kowa ya
nemi zabin Uhangiji fakat! Magana ta kare. Ke ma na gaya
miki ki daina tayar da hankalinki, ki bar komai hannun
Allah, Shi ya shirya hakan, kuma Zai kawo mafita".
Ta numfasa tare da share hawayen ta ce a sanyayc,
"Shi kenan, Allah ya shige mana gaba".
Ya ce, "Amin”. Cikin farin cikin saukowarta.
Imran din ya shiga mota ya yi shiru, sam ya gagara
tashin motar, wai sai yaushe ne zai samu nutsuwartsa? Sai
yaushe zai samu soyayyar Mabaruka? Da ma haka soyayya
ta ke da daci idan ka rasa masoyinka? Ashe zaman da sukai
tare duk da ba sonshi tá ke ba ganin da yake mata ko da
12
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
harararsa ne ashe ya li dadi da farin ciki, da samun
nutsuwa? laka Mabaruka ta shiga ransa anya zai iya
rayuwa babu ita? Jerin tambayoyin da yai wa kansa, amma
amsarsu ta gagara.
Kiran Sharifa ya shigo wayarsa ya duba sunan My
Sis, ya jawo wayar ya dauka cike da mutuwar jiki ya kai
kunne tare da cewa, "Sis ya ki ke?"
Da jin maganarsa ta gane ba lafiya ba, kamar yanda
ta ke tunani da man, ta ce, "Yes bro how are you?"
Ya amsa tare da lumshę idanu yana jingina jikin
kujera, "Thank God"
Ta ce, "Bigbro da gaske kun rabu da Mabaruka?"
Ya yi jim yana jin kamar ta watsa masa ruwan zafi,
duk da haka ne amma sai ya ji maganar ta dake shi, wai ya
rabu da Mabaruka? Ya jinjina kai cikin takaici ya ce, "Haka
ne".
Ta yi shiru daga can, ba farin ciki ba, ba bakin ciki
ba. Babbar damuwarta Yayanta ta san irin zafin son da
yake wa Mabarukar zai shiga mawuyacin hali, ba ta son
damuwarsa, ta ce, "Na sanka Bigbro kana nan cikin
damuwa, ka bar wa Allah komai, Yana sane, Shi zai kawo
maka sauki a cikin lamuranka. Kar kai ta damuwa da
tunane-tunane don Allah Bigbro, ni ma zan shiga damuwa
na kasa karatu".
Ya yi murmushin jin dadin kulawarta gare shi, ya
ce, "Shi kenan kada ki damu, ni ma ina nan lafiya ba abin
2
da ke damuna".
Ta ce, "Ban yarda ba Bigbro ka dai kiyaye".
13
WAYE ANGON?-4
Ya ce, "Shi kenan zan kula
Ta ce, "Promise?"
Maryam Jafar Kadunа
Ya daga kai kamar tana gabanshi tare da cewa, "Shi
kenan na ji.
Ta yi dariya daga can, ta ce, "Thank my bro, Allah
tsare mu, kai muna exam da zarar mun kammala zan zo".
Ya ce, "Shi kenan ki dage ki karatu sosai".
Ta juya rigingine cike da jin dadin kasancewarta da
dan uwanta, ta ce, "Zan yi Yaya insha Allah, sai ka yi alfahari da result dina".
Ya yi murmushi, ya ce, "Ni kuma za ki ga kyautar
da zan miki, katotuwa, tuleliya".
Ta yi dariya sosai, ta ce, "Shi kenan ka tanadar min
tun kan ka gani, na maka alkawarin ba zan ba ka kunya
ba.
Ya ce, "Shi kenan, ki je ki karatu, zan gani din. Sai
anjima
Тa сe, "To by my dear bro, love you.
Tare da hura masa iska. Ya yi dariya shi ma, ya ce,
“Love you too”. Suka kashe wayar.
Ta rungume filo tare da lumshe ido tana jin dadin kasancewarta da dan uwanta.
Balarabiyar mata ta shigo tare da sallama, ta yane kanta da irin shigarsu ta Larabawan asali, Momy Pateema
kenan kanwar Mamansu uwa daya uba daya. Ta zauna tana kallon Sharifar, ta ce, "Manillazi tatakallam fil hatif?"
Ta yi murmushi, ta kalle ta, ta ce, "Ana wa aki
14
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
Ta jinjina kai tare da cewa, "A'alam huwallazi
takallama wa Anti ariha”
Ta yi dariya tare da tasowa ta rungume ta, ta ce,
"Haza huwa ya Ummi li anna ni ahabbahu ma ahabbu
nafsi".
Ta jinjina kai tare da murmushi, ta ce, "Barakallahu
fikum fi hayatikum".
Ta сe, "Ameen wa fiki barakallah shukran”.
Da kyar ya iya jan motar ya fice, kai tsaye gidan su
Mabarukar ya nufa.
Sabuwar dalleliyar adaidaita sahu ce a kofar gidan
an riga an gama hada ta, ja kawai za a yi. Baban Mabarukar
ne tsaye jikin motar, sai washe baki yake yana zazzagaya ta
tamkar an ce tashi ce, shi dai dan aiken yana kawo wa ya
wuce yana cewa, "Maigidana ne ya ce a kawo".
Ya fito daga motar, ya iso inda yake. Ai yana
ganinshi ya taho yana cewa, "Shi kenan ma ka zo, da ma
tun dazų nake jiranka, na ga an kawo motar kabo-kabo in
ce dai tawa din ce ta iso?"
Ya dan yi murmushi yana kallonsa, ya ce, "Пaka ne
Baba, ta sana'ar ce ka fara ja mu ga ya abin zai kasancё".
"Yihuhu! Allahu akbar". Ihun da ya buga kenan tare
da tsalle ya nufi gurin motar har yana tuntubе ya се, "ka ce
tawa din ce? Hamza! Haruna!! Ku zo ku zo da gaske dai
tawan ce kamar yanda na tsammata"
15
WAYE ANGON?-4 Magyam JatanKedana
Ya kira `yan uwan nasa. Da sauri suka karaso cioke
da farin ciki. Ya ce, 'Kun gani ko, da ma na fada muku kila
tawa ce, ashe kwa hakan ne.
Suka dubi mran suka ce, "Allah saka da alkhairi,
Allah kara arziki".
Ya ce, "Amin, amn".
Sam bai ma tsaya suka gaisa ba yana ta rawar kan
motar da kiraye-kirayen abokansa, to bare kuma ya mishi
maganar ya aka yi, me ya faru har abu ya kai ga saki, in
mai daidaituwa ne a daidaita ta koma dakinta, in babu
kuma a san me za a yi, amma sam bai tsaya ba, a tunanin
shi kanshi Imran din zai masa magana, amma sai ya ga
kamar motar ta fiye mashi komai ma har shi mai kyautar
motar. Ya jinjina kai cike da mamakinsa, wannan wane irin
uba'ne Mabaruka ta ke da shi? Tunda yake masa rawar kai
da maula-maula, roko-roko bai taba ba shi haushi ba sai
yau, don me ba zai yi kokarin dawo mishi da matarsa ba,
motar ta fi kenan da man don motar yake masa sintiri?
Haushi ya kai shi wuya, ya juya kawai zai shige motarshi.
Baba Hamza wanda shi ne madaurin auren ya kira
shi suka rabe gefe, ya dube shi cikin kamala na dattijai, ya
ce, "Na san Mabaruka ba ta jin magana, za ta iya yin komai
don son zuciyarta, yarinya ce mai kafiya da taurin kai.
Haka aka dinga fama da ita kan auran nan aka samu aka yi
da kyar tana ciccijewa, shi kuma Babanta ba girma shi ne
babbanmu amma bai maida hankali a kan abin da ya
kamata ya yi. Yau kwananta hudu da dawowa gida ta ballo
auran ía dawo, amna shi Baban nata bai sanar min ba, sai
16
WAYE ANGON?-4 Maryam Jafar Kaduna
dai gurin yara na ji. Jiya nake cewa zan kira ka ka zo in ji
me ya faru, sai dazu da safe da ka yo aikc yake cewa ai kai
ka aiko masa, kilan ka zo. To sai na jınkirta ka zo din na
kuma sa masa ido in ga zai maka magana, ko ko nai ko
haka na gani bai yi maganar ba sam. Abiu bai dame shi ba,
murnar niotarsa yake abinsa, mutuwar auran 'yarsa ba ya
gabansa, don haka na kira ka ina son in ji daga gare ka, me
ya faru har aka kai ga saki?"
Sosai ya ji dadin abin da mutumin ya yi, hakan ya
sa ya kara ganin girmansa da gemansa yana sa rai kila a
dawo masa da matarsa tunda manya sun sa baki.
Bai yi kauron baki ba ya fada mishi komai, har duk
zagi da rashin kunyar da ta ke masa, har na ranar da ya yi
sakin.
Baban ya dinga fadin, "Subhanallahi! Subhanallahi,
assha ba ta kyauta ba, amma ka yi hakuri yaro, zan ci
mutuncinta, ba za ta sake ba. Amma yanzu ka jinkirta ka
koma ka gaya wa Allah, idan da alkhairi a komenta Allah
ya maida auranku ta fahimce ka ku zauna lafiya. Ba zan
sake matsa mata ba lallai sai ta koma ba kamar yanda na
mata na farko ga abin da ya haifar, kar ta koma ta yi abin
da ya fi wannan kyama, abin da za a yi ka kyale ni da ita,
zaman da za ta yi gidan musamman nan gidan Baban za ta
gane kurenta, sai ta yi kuka da idonta, karshe