tsoka abar tayar da
husuma da shasha shai 'wadanda basu san ciwon kansu ba
in.... kan ya karasa yaji sauar kulki saman kansa ta bayansa
wanda ke hade da saukar gigitaccen mari a kunne ba shiri
ya dafe kai yayi luu yafadi anan yana shure shren kafato
tamkar ransa zai fita saboda yanda yake jin azabar dukan
har a kwakwalwar sa kan ya dawo hayyacinsa ya sake jin
saukar wani, wani irn ihu ya saki tamkar zararre suka
cigaba da dukansa ta ko ina ajikin sa kafafunsa da hannuwa
gwiwo duk suka sagar masa kafafuwa suka kuma dinga
sararsa da wukansu masu tsananin kaifi da tsafi, ya dinga
ihu yana kiran sunan allah.Cikin baccinta ta dinga jin ihu da
hayaniya ga alamar ana dukan wani abu sai taji tim a rikice
cikin tsananin tsoro ta mike sai sannan ta tuna bayi take ta
fito daki jikinta narawa ta sadado tad an leko ta kofa ganin
ma'aikatan tayi daddaure a kasa sunyi plate ta saki kofa tare
da bude baki idanuwa suka fito jinta ya kara rawa ta dafe
kai tare fashewa d kuka tace na shiga uku ba dai yan fashi
b? Saukar wani dukan da taji ne yasa ta firgita ta koma a
guje fitsari na son zubawa ta hau karkarwa ta rasa me zatayi
180
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
sai sintiri a daki tabbas ta gane muryar wake ihu makiyin ta
ne imran Sai da suka tabbatar baya motsi ya mutu sannan
suka kyale shi yayi jina jina da jinni kwance suka bincuka
dakin tas suka dauki abinda suka dauka suka fito da sauri ta
leko kenan tad an hudar kofar ta hangosu suna fitowa da
sauri su da yawansu, Tasa hannu tad ode baki gam kar wani
sautin ta ya fito tare da runtse idanuwa gam tana kiran
sunan allah tuni fistarin dake kokawar zubowa ya fito, said
a taji tashin motarsu sannan ta dafe kirji tare da silalewa
kasa saman tails ta kifa kanta jikin kofa ta fashe da kuka oh
ni mabaruka da zuwana gidannan wallahi sam nan gidan ba
alkhairi bane gidanmu zan tafi bazan iyaba azo a kasheni a
banza haka kawai ya jawo minmasifa.Shi kam yana can
kwance baisan inda yake ba cikin jinni shin a mace ko
araye? A wannan daran batayi bacci ba, kuma taji bazata
iya duba shiba taga yana lafiya ba mussamman da taji shiru
tun bayan fitarsu, tayi zaune gari ya karasa wayewa ta ware
gida, sai gaf da asuba sannan bacci ya dauketa dukn da
tsoron da ta ke yi. Jin ana dukan kofa tane yasa tashi a
hanzarce jiki na rawa ciki tsoro a tunaninta ko sune suka
dawo taja da baya tana cewa waye? A storace akace mune
181
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
hajiya ma'aikatan ki bata dai gamsu bat ace ya akayi ne?
sukace alhaji ne fa ba lafiya kamar ma ya mutu dn baya
motsi "yan fashinnan sun dakeshi sosai yana can kwance
cikin jini ta nanata cikin mamaki tace ya mutu? Suka ce eh
bude kigani. Wani tunanin ta shiga kar dai sakayyar da take
nema ce tun yau allah ya saka mata ya dauki ran imran,
kenan zata sakata ta wala ta samu sukuni? Tayi wani
murmushi tace shikenan ina zuwa ta wuce ta bude kofar
sun dauko shi daga dakinsa sun kwantar dashi a falo har
yanzu baya motsi tabi jikinshi da kallo yanda suka raunaka
shi sosai gashinan dai bako matsi anya ma yana da rai
kuwa? Gabanta ya yanke ya fadi hakannan tajijikin ta ya
mata sanyi ta gaza daga kafa sai dai ta sulale ta zauna tana
innalillahi wa inna ilaihirrajiun. Tsawon dakiku tana kallon
sata rasa wane tunanin zatayi murna ko bakinciki jiya jiya
fa suka rabu me hakan ke nufi ya mutu kenan abinda
takeso? Daya ya katseta muyi gaggawa madam yana
neman taimako idan yanada rai kar mu jnikirta tace to a
sanyaye ta mike ba jiki ba kwari waya ta dakko ta rasa ama
zata kira da wannan mummunar labara. Mommy tabbas
itace mafi kusanci gareta gwanda ita akan ta kira 'yan
182
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
uwansa don haka nambobinta ta daddana ta kira. Ta dade
tana ringing sannan ta shiga cikin muryar son kuka tace
mommy imran ya mutu? Wayar saida kusa faduwa a hannu
mommyn a kidime tace lafiya kike kuwa ko kina mafarki
ne? Tace wallahi da gaske mommy 'yan fashi ne suka shigo
jiya suke kasha shi gashi can a kwance a mace, zufa ta keto
wa mommy jikin ta yah au rawa ta gigice rasa me zatayi
tayi sai subhanallah take daddy ya shigo dakin ya dawo
daga masallaci ya yajiyo salatinta yace lafiya me ya faru
ne? hankalinta ya kara tashi ta rasa mezata ce masa yayinda
ta manta da wata waya ya sake nanatawa ki nutsu ki min
bayani me ya faru da kyar dai bakinta na rawa ta fada masa
ya zauna baking ado yayi shiru yana tunani tsawon lokaci
ya mike ya dubeta tare da cewa zo muje da sauri ya fice don
fito da motor. Ta jajumo hijabin tad a ta idar da sallah ta fi
fito kafar ta sanye da silifas sharifa tana dakinta bata san me
ake ba suka shiga motar a rikice, tan agama wayar ta dawo
farkur ta tsirawa gawansa ido, mahakacin gudu daddy yayo
nan da nan sai gasu a bakin gate ya aje motar suke shigo.Da
zuwansu suka nufi inda yake daddy ya daga hannunsa
sharaf ya sakihannun ya dago yana kallonsu musamman
183
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
mommy da tafi kowa rikicewa itako mabaruka tana kan
kujera tana kallonsu dai dai ita ba murnaba ita ba bakinciki
ba Yacewa mommy inaga zamu je asibiti tace to to to
amman lafuya ko? Yace ina sa ran haka. Haka suke
kinkimeshi zuwa motar. Itama ta sanyo hijabinta ta biyosu.
Nan da nan suka iso asibiti ingantacce lafiyayye me
kyau da kulawa sai dai akwai bayanin kwandala,
emergency aka nufa dashi likitoci suka taru kansa sunyi
nasara kam don an same shi da sauran numfashi sai dai ba
yanda ake sonsa ba yafita sannan raunukan dake jikinsa
abin y abaci anyi sa'ama ba karaya tabbas sun so daukar
ransa allah bai basu nasara ba, sai dai aka sa masa odygen
don ya taimaka masa duk wani treatment an masa aka sashi
special room, likitoci sun tabbatar musu da zai sami lafiya
su kwantar da hankalinsu insha allah. Daddy ya samu
nutsuwa sosai amma mommy still bata nutsuba ita ko
gimbiya ko a jikinta wani gefen zuciyarta bata so bayanin
likitaba ba haka taso jiba suka tsura masa ido. Ahankali ya
fara samun sauki amman dai bai farfadoba mommy ta kira
sharifa tana fada mata tazo asibitin amma bata sanar mata
me ya faru ba don tazo a nutse tace amman mommy waye a
184
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
asibitin tace kizodai tace asanyaye to shikenan mota ta
dauko ta taho, mabaruka kuwa ta basu labarin iya abinda ta
sani lokacin da tai so idonta kan gadon dan son ganin gano
waye wani ihu ta sulale anan ganin dan uwanta mutu kwa
kwai rai kwakwai. Da daddy da mommy ke bata hakuri
amman sam taki nutsuwa tana cewa na shiga uku meka
tarewa wasu da suke shirin daukar mana kai waHahi muna
sonka kada ka tafi ka barmu bazan iya jure rashinka ba don
allah ka tashi big bro, A wannan ranar haka suka kasan ce
cikin tashin hankali da damuwa kowa jugum jugum. Sunyi
waya da rafi'a take fada mataa suna asibiti ga abinda yafaru.
Ba shiri ta nufo asibitin ita da mamanta maman ta jajanta
ainun ya basu tausayi matuka. Haka mutane suka mutane
suka dinga turereniyar zuwa ganinsa duk wanda yayi
labarin abin nan take zai saki abinda yake ya taho a rikice.
Hana shiga akeyi dinga yi sai dai majinya tansa asibitin
makil da jama'a yan dubiya, sai dare sannan daddy da
mummy suka tafi da sharifa damuwa dam aransu bad an
sunzo bad an dole ka'I dar asibince mutum daya zai kwana
dashi itace kuma mabaruka. Ranta ya. sake baci saboda
barinta de akaji dashi meyasa ba;a bar sharifa ba kamar
185
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
yanda taso daddy yace a'a ita yafi cancanta saboda itace
matarsa.
Sai washe gari sannan ya fara dawowa hayyacinsa
lokacin da taga yana motsa kafarsa ne ta fita ta sanar da
likita tare suka shigo. Alhamdulillah jiki yayi kyau sosai
nunfashinsa ya daidaita har likita ya daga masa odygen din
sai dai tsami da jikinsa yake ga kansa har yanzu bayajin
dadinsa ya bude ido yana kallon inda yake asibitin yayi
shiru yana tunano abinda ya faru da sauri ya juya kansa
wajen mabaruka ya dubeta cikin murya can kasa yace basu
miki komai ba mabaruka ko sun tabaki? Ta murtuke fuska
tare da cewa a'a can ciki ya lumshe idanuwa yana jin wani
dadi tare da hamdala likita ya leko fuskarsa yace to kakejin
jikinka yanzu? Yayi murmushi yace lafiya lau ba wani abu
kainane kawai ya jinjina kai cikin gamsuwa that's good zai
saki insh allah sannu ko, ya daga kai alamar amsawa ya
juya yana kallon mabarukar yace idan wani abu ya faru ki
nemeni tace to ya juya ya fice yana cewa allah ya sawake
tace amen can ciki:
Ya juyo yana kallon ta fuskarsa da murmushi yace
sannu mabaruka tayi masa banza tana turo baki ya sake
186
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
cewa ba dai abinda abinda suka miki ko? Tace eh cikin
gajiyawa yace ka basu gankiba ta sake cewa eh, yayi shiru
yana kallonta ganin yanda take fushi bayansa yayi duk ya
sandare yana son ya dan tashi zaune ya yunkura zai tashin
duk jikin ya masa nauyi yayi yayi ya tashi ta kasa tashi,
tana kallonsa sai ma ta juya kanta ta zaro waya tana game
ya dan dubeta a sanyaye yace kidan taimamin inshi na gaji
da kwanjiyar, tamkar ta kwadeshi da mari don me wai yake
son takurawa rayuwarta? Taki ta matsa. Ya sake nanatawa
don allah ki taimaken na tashi ta wuce fou tana turo baki ta
nufoshi ya dubeta da kyau yace bashshi kawai kije ki kira
min nurse inaga akwai matsala ko? Banza tayi masa tana
kokarin dagashi din ta taimaka masa din tad an dungurar
dashi don ba zaunar dashi tayiba yasa filo ya dan jingina
yana lumshe ido cikin jin jikinsa, ya dubeta yace dan snmin
ruwain kuskure baki.Tayi kyam cikin takaicinsa wallahi fa
tagaji bazata iya da dawainiyarsa ba don ba dolensa bace ya
bari wadanda suka zama dolensa suzo su masa yasake cewa
kiyi hakuri daga wannan shikenan ta wuce ta dauko ruwa
tare da dungura masa ya bude bakin ya kurba yana
kuskurawa ta dauko container ta tare masa tare da kauda
187
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kanta tana yastina fuska tamkar me shirin amai. Ya zubar ya
sake kuskurar wani ya zuba yace shikenan na gama
nagode, ta wuce ta zubar harda toshe hanci ta dawo ta aje ta
koma inda ta tashi taci gaba da gaba game din fuskar babu
annuri, sai can sannan su mommy suka zo hade da nau'ikan
abinci kala kala da kayan fruit.Suka tambayeta me jiki a
can makosh ta basu amsa sunyi murna sosai da ganin
tashinshi, sharifa ta dan hada masa tea ta bashi ya shad a
danwani abu marar nauyi, har hira akai dashi aranar da
labarin abinda abinda ya faru daddy yace wallahi bazan yar
daba sai na dauki hakuri zan hada shi da commissioner yan
sanda don gobe ko hanyar gidan bazai biyo ba bare yasa a
shigo gidan dukkansu sun gamsu da hakan. Gabadaya
asibitin ya gundureta ga jikinta baya mata dadi inda son
samu ne tad an yi wanka, wajen yamma ta dubi mommy
tace in son naje gida indanyi wanka tayi shirutana kallonta
can tace a'a wane waka ki jira dai, tahade rai tamkar ta fasa
kuka ya dubeta ya dubi mommy yace kibarta taje din nasan
mabaruka tana da jumirin wanka bata zama haka a rana
nasan ta kanyi har uku to bare kuma batayiba zataji jikinta
ba dadi.Tayi jimm sannan tace yo shikenan kije amman
188
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
1
a
a
n
awa biyu na baki kije kidawo kafin magriba, batare da amsa
ba tawuce tana kumburi mommy ta bita da kallo hart a fice
tace allah ya shirya, madadin tawuce gidanta sai tawuce gidan mommy ma'aikatan gidan suka bita da kallo basu
gabanta ta wuce tsohon dakinta ta nufa ansa masa key, keyn
na jikinsa ta murza ta bude tashiga kan gado ta fada tayi
lamoo gaba daya rayuwarta bata mata dadi wallahi da tayi
farinciki amman ya akayi sulaiman ya samo wadannan yan
daban suka shigo gidan imran da gaske neman ransa sukayi
koko suzo su dakeshine? Tace ina sulaiman bazai hakaba
ninasan sulaiman dina bame kisa bane, karshe dai bayi ta
fada tayo wanka tare da sallar da batayiba gado ta fada da
tawul din jikinta bacci me matukar dadi ya dauketa.
Bangaren sulaiman kuwa suka koma masa washegari suka
tabbatar masa da lalle ya mutu don sun baro shi kwance
babu rai, yayi farin ciki sosai ya kawo saran kudinsu yabi
yasu suka wuce abinsu. Awannan daren yayi farin ciki sosai
don gani yake mata ta zama tasa lallai mabaruka tashice ya
godewa yayar sad a ta kawo masa wannan shawarar da
bebiba da yanzu yana nan cikin bakincikin karshe ya mutu
ahaka haka washegari ya saurara yaji anzo masa da labarin
189
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
jan'izar imran din, amma har rana ta take bai ji kishin kishin
bay a shiga kokonto kwatam yaje gidansu mabaruka, inn
ace ke cewa wai sulaiman wana irin ganganci kay me nace
maka ba cewa nayi kasa asace imran dinba shine suka dake
shi suka baroshi kwance? Yace eh wani abnne ya kikaji?
Taja tsaki tare dawcewa kai dai wallahi baka jin shawara
sam way ace maka ya mutu? Yayi wuri wuri da idanuwa
yace wayanda nasa mana sun tabbatar min da cewa ya mutu
dan baya motsi tace to bai mutu ba yana nan da ransa yana
gado asibiti saidai bamusan ko zai tashiba ko ba zai tashiba
don baisan indaa kansa yake ba tunada aka kaishi, zufa
taketo masa ya ciro hankachief yana share gumin
hankalinsa ya tashi tsoransa daya kada a damkoshi
musamman da said a ska sanarwa imran din daga gareshi
ne shi ya turosu. Yace na shiga uku kada fa su kamani tace
su sun fada masa kai ka turosu?, yace sosaima mdanhar
fada na musu kan katobarar da sukayi yanzu gashi sun sani
a masifa. Tace ah to kai ka sani ai kin bin shawara ta yajawo
maka gaka ba mata ba biyan bukata saima jefa kanka
dakayi a bala'I, mikewa yayi yana cewa ina zuwa Sai da
tasha baccinta ta matse sosai sannan ta tashi ta dauko daga
190
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kayan data bari nata ta saka tare da dako hijabi ta fito, a
hanya rafi'a ke kirana zantafibaki dawoba tace ina kan
hanya ki jirani tace to saikin iso ta hau adaidaita sahu har
asibitin ta sallameshi tashiga mommy ta dubeta tace sai
yanzu kika dawo? Batace komai bat a nemi wui ta zauna
shikuwa idonsa a kanta yana jin dadin ganinta musamman
da tayi wankannan duk dab a wata kwaliya me zafi tayiba
suka rabe ita da rafi'atu tana cewa banson zaman asibitin na
rafi'a duk ya gundureni, ta dubeta tace toya zakiyi
mabaruka ya zama dolene ki jure mijinkine dolenkine kima
godewa allah da ba kashe shi sukayi bad a yanzu anski
takaba tsaki taja tare か
da dauke kai tace da kasheshi sukayi BUIH!
ISWS134 da naïf farinciki 15 wallahi da sauri ta rufe mata baki kar ajita,
ta mike da jan hannunta suka fita zuwa baranda ta dubeta
tace baki bari bako mabaruka har yanzu kina nan akan
bakanki dukda kin aureshi a yanzu kina matsayin matar fa? 25D
Tace dam dan wannan ne kika fito dani to bari kiji so daya
ne haka kiyayya daya cee ba wata tunda ina kinsa baШОК abinda В КОШЕ 19
zai canza da kiyayyarsa aka halicceni don haka har gobe
ban sansa bazan taba sonsa ba hakan yasa na gwammace
mutuwar sa akan rayuwarsa. Tace wallahi kiji storon allah
191
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
mabaruka ki san me kie yanzu ba lokacin cigabda sakarcin
nan bane dole kisan me kikeyi ki tallafi aurenki ki rumgumi
mijinki don shine tsirarki kar kice zaki ja da ikon allah
kinutsu mabaruka ina fada miki tun kina dadama kar tazo ta
wucemiki kizo ranar dazaki fara kuka da idon ki imran ba
kamar kowa bane baa bin yarwa bane idan kika yarda kika
rasashi har abada bazaki samu kamarsa ba wallahi wallahi,
Taja tsaki tareda wucewa tana cewa saiki tayi na fada bana
sonsa saime ya mutu ma meye ruwana.Binta da kallo tayi ta
rasa me zatace al amarin mabaruka ya fara bata tsoro tafaje
kafiyada naci. Wucewa kawai tayi ta hau mota ta tafi gida
tunda ta riga tagama bata mata rai. Haka dai suka kasance a
asibinn ahankali yana samun sauki sosai saboda kulawar
likitoci ga ingantacan magunguna abinci sai wanda likita
tace abashi don hake ya samu kafiya sosai da rana zai wuni
dasu momy da sharifa sai daddy sannan gimbiya mabaruka
yan dubiya suna ta zuwa ganinshi. In dare yayi abarshi daga
shi sai mabarakar ta koma gefe ti kyaleki tana kumburi
komai ya mata kunci in zai ta Magana bazata amsa masa ba
sai dai ya giji ya hakura. Satinshi biyu asibitin aka sallame
shi ba abinda ke damunsa ya warware sosai. Sulaiman
192
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kuwa aranar da akayi sallama. A ranar ake damkeshi inna ta
fito waje tana ta bala'i da basase zaga wai sharri akawa
danta akalin taji maganar abakin inna aka sashi mota suka
tafi. Inna ta bisu da dawatsu tana jifa tamkar mahaukiya
tana allah ya isa shegu masu bakaken fuska da zuciyoyi
masifa da bala'i ya sauka kanku tunda kun daukar min da....
Ku biyo ni a 3 za ku ji duk yanda hakan zata kasance,
karan batta tsakanin Inna da Mabaruka, haka nan
soyayyarta da Imran duk ta ya ya? Ku biyo ni za kuji, akwai
labari.
Kuyi hakuri mu tara a cikin littafi na uku (3) da yardar.
Allah, zai fito nan ba da jimawa ba, na gode sosai Makaranta.
Sai mun hadu a (3)
193
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
DANDANO DAGA
'WAYE ANGON?'
(Kashi Na Uku)
Tunda ta gama abin da take ta shiga wanka, bayan ta
turara duk gidan da nau'in turarukansa, tun daga dakuna,
toilet har da harabar gidan.
Sannan ta hada na wankanta wanda yasha turarukansa
masu kama jiki, ta fito. Ta dade gaban mirror tana lindar
jikinta da nau'ikan mayukanta masu daddadan kamshi da
sa nutsuwa.
Fatarta har sheki take, tayi laushi jajir tamkar jini zai
fito, musamman diga-digan. Ta nade gashinta bayan ta
turara shi da turarukansa, ya yi baki wuluk da laushi sai
Kamshi ke tasowa, ta sake shi baya yana reto.
Fuskarta tasha kwalliya me kyau da tsari, sai walwali
take irin kwalliyarsu ta matan zamani, ko ina ta gyara shi na
jikinta. (2) subari minisa
Tayi tsaye gaban wordrove tana tantance kayan da ya
kamata ta saka, duk kayan da ta daga sai taga sun kaskanta
tasawa Imran dinta, darajarshi ta wuce haka.
Da kyar dai ta zamo wasu wadanda tasan sune yafi son
tayi masa kwalliya da su, yakan rude ya rikice ya yi ta
sabbatu, yana cewa "Kin min kyau my Mabaru."
194
WAYE.ANGON? Maryam Ja'afar
Tayi murmushi ta dauko su tare da shinshina kamshin
turaransa wanda suke amfani da shi, ita da shi.
Ta lumshe ido tana jin wani dadi da farin ciki ta ce "Ina
sonka my Imran, Allah dawo min da kai lafiya."
Tasa kayan ta tsaya gaban mirror a kullum idan ta sa su
takan tambayi kanta anya ita ce ba canzata aka yi ba?
Tamkar 'yar baby kayan suna karfarta wando baki
shortniker.
Ko cibiya bata rufe mata ba.
Ta saki gashin a baya yana reto, tayi murmushi ta ce,
"Nasan za ka yi farin ciki da ganina, haka nima ina tayaka."
Ta Kara turare jikinta da nau'ikan turaran daidai sanda
take jin hon dinsa.
Da sauri ta aje abin da ke hannunta tana murna ta fallo
da gudu cikin kuruciyarta 'yar shalau-shalau marar nauyi
kamar budurwar Turawa,a kagare take ta ganshi tana
masifar kewarsa.
Yayin da shi ma bangarensa kamar ya fita jikinsa har
rawa yake kasa rufe motar ya yi don son ganin
Mabarukarsa da tun a jirgi take matsa masa da kira.
Na gaji da jira fa my, na kusan kuka fa? Cikin
shagwabarta me rikita shi. Ya taho da hanzari a daidai kofar
suka ci karo, kowannensu bakinsa ya kasa rufuwa don jin
195
1
1
t
j
k
t
t
S
WAYE ANGON?
dadin ganin dan'uwansa.
Maryam Ja'afar
Da zuwansa ya buda mata hannuwansa don fadawa
kirjinsa, kamar yanda suka saba. Ta fallo a guje tana zuwa
tayi tsalle ta fada jikinsa tana cewa.
"Welcome back my desire." Cak ya dauketa ya rufe ta
da hannuwansa yana jin wani nishadin jin dumin jikin
matarsa da ya yi kewarsa kwana biyu.
Suka lumshe idanuwa a haka kowa yana jin nutsuwa na
shigarsa da nishadin, kasancewa da juna.
Sannan ta diro bakinta washe tana dariya ta kasa cewa
komai, sai tsalle-tsalle take.
Shi ma dariyar yake yana kallon yanda take zumudi, sai
ya ce yana kallonta bayan ya dan rankwafo.
“Fadi mana menene?" Tayi dariya ta ce "Ina murna my
one, naji dadin ganinka."
Ya ce yana dariya "Ke kadai ko?" Ba amsa sai dariya
kina jin dadin ganin Imran din ki ko?" ta daga kai tana
kallonsa.
Ya ce, "Good! Zo muje ciki yau zamu sha hira ko?" Та
ce, "Eh." lokacin da take tura hannunta cikin nasa "Eh
mana, na tanadar maka labarai masu zaki da dadi."
Yace, "Allah?"Ta ce, "Allah my." Ta langabar da kanta
196
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
jikinsa suna karasa shiga zuwa dakinsu, tana jin wani farin
ciki da walwala, Imran dinta ya dawo daga tafiyar da ya yi
kwana uku.
Shima bangarensa yana jin dadin dawowarsa gareta,
wacce ya yi missing ta na kwana uku sai dai waya.
WANI BANGAREN
Tun safe take tsaye ba ta huta ba saboda aikin
kasancewar ranar girkinta ne, ta gama kwashe tuwon dare a
flask dinta masu kyau da tsada ta juye miyar a flask ta aje a
kitchen.
Wajen rijiya ta nufa don ta debi ruwan wanka ta sirka da
na zafin da ta dafa, bayan ta dauro zani da tawul wajen
Magriba kenan don har an fara kiran sallah.
Inna na zaune tsakar gida duk tana kallonta ganin ta
sungumi bokitin ne zata shiga bandakin yasa ta mike ta tarė
ta tana cewa ke tsaya! Taja ta tšaya tana kallonta, bayan ta
aje bokitin tana cewa, "Na tsaya, meye?"
Ta dubeta ta ce, "Me ki ke nufi ne? kin gama tuwo kin
kwashe da kanki alhalin kin san ba tsarin gidannan kenan
ba?"
Ta kalleta a wulakance ta ce, "Tsarinki na da kenan, kin
wa wasu amman ni Mabaruka na rantse ba za ki min haka
ba.
197
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ni nayi girki kuma ni zan raba in ba kowa, yanda naga
dama kuma ba wanda ya isa ya hana ni, ehe!
Ta dube ta da kyau ta ce, "Ai ko za ki ci ubanki wallahi,
ba ki isa ba ba tsarin gidana ba kenan. Yau kwananki tara
gidannan amman har kina wani gadara, sai nasa ya sake ki
walłahi shegiya 'yar gidan mahaukata wacce ake aura mata
maza biyu."
Ranta ya bace sosai, ta ce "Tsohuwa ki iya bakinki, ki
san me ki ke fada, na rantse zan daka ki a gidannan ba a min
wasa fa!"
Samirá ta shigo jin hayaniyarsu tana cewa "Meye?
Meye nake jin hayaniya?"
Mabarukar ta juya tana kallonta ta ce, "Ki shigo kiga da
دو
wa ake yi mana.’
Ranta ya baci itama ta ce, "Au! Da ke ne kenan tun
zuwanki gidannan ki ka fitine mu." Inna ta ce, "Wai dukana
zata yi."
Samira ta zabura "Me? Ita din banza, yo akwai me taba
min ke in kyale shi, ko shi dan gidan uban waye?"
Ta ce, "Ai ko za ki gani matukar ba ki gargade ta ba a
kan karambaninta gare ni." Inna ta ce, "Sannan kin san ba a
wankan dare gidannan amman ke naga kina son ki raina
min wayo ko?"
198
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Tayi dariya ytare da dukan cinya ta ce, “Wallahi har na
cikin dare za ki gani ba ma na dare ba, tunda kin san auro ni
aka yi."
Ta ce, "Da kyau fitsararra! Zan yi maganinki." Та се
tana zaro mata idanu "Sai dai muyi maganin juna
tsohuwa."
Ran Samira ya 6aci ta daga hannu zata kai mata duka,
caraf! Ta rike hannunta tana kallonta ta ce, "Karya ki ke 'yar
marassa kunya, kin yi kadan ki dake ni, dubi fatata da
kyau."
Ta ce, "Za ki gani kuwa na rantse." Ta fincike hannunta
ta sake dagawa zata mareta, kan ta sauke hannunta jikinta
ita ta kai mata nata gigitaccen marin.
Ai fa kan ka ce me? Fada ya kaure tsakaninsu, dan
bokitin wankan aka daga sai jikin Inna aka watsa mata shi
tas, tayi jagab.
A wannan halin ne Sulaiman ya shigo, idonsa ya sauka
kansu, ya zaro ido ganin faruwar abin yayin da Nafisa tana
daki abinta ranta kwal.
Tana godewa Allah da ya kawo musu Mabaruka
gidannan, damuwarta tazo karshe ko ba komai dai ta koshi.
199
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
TSOKACI
A cikin wari dare, lokaci daya ba zato babu tsammani, wata
Kasaitacciyar gobara ta tashi a wasu gidaje uku, wutar da ke ci ta
samu makamashi mai girma wanda yasa ta bunkasa.
Tun kafin zuwan 'yan kwana-kwana, hasashe ya tabbatar da
cewa koda ruwan KOGI ba za su iya kashe wutar ba, to ballantana
kuma ruwan RIJIYA.
Duk a cikin littafin WAYEANGON? Tirkashi!
Labarin BABANA DAMIJINA ya zamo tauraron fito da wani
salo mai matukar ban sha'awa da birgewa.
Makaranta sun yaba, sun kuma jinjinawa Marubuciya
MARYAM JA'AFAR.
Na tabbatar wasu za su yi tunanin daga shi ba za ta iya rubuta
littafin da ya kai shi dadi ba, wasu kuma za su yi tunanin ta juye
dukkan basirarta a cikinsa.
To amma lokaci daya sai ga shi ta faso da babban labari,
littafin da ya ce wa BABANA DAMIJINA kauce ba ni wuri.
'WAYE ANGON?'.
Labarin ya yi matukar kayatar da ni, don kuwa basirarta ta
kara bayyana a cikin labarin mutane hudu da suka zamo taurari
mafi shahara a cikin labarin, wato MABARUKA, IMRAN da
SULAIMAN, a gefe kuma ga babbar kawa RAFI'ATU.
WAYE ANGON? Ya fito da sabon salo na daukar hankali,
akwai babban darasi a cikinsa.
A gaida 'yar JA'AFAR (Maryamu)
-NAFI'U SALISU (Marubuci/Manazarci)
200
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na