Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
8 / 10
har kike wa wani gadara kina masa gorin arziki to dame gidanku yafi nasa me zaki nuna masa? Tayi tsuruu tama kallanta. Taci gaba to tun wuri ma gwande ki koma gidan yayanki kije ki tallafesu wallahi tun kan kwanon abinci ya gagare ki a gidannan. Wake yarda yaya ya taho don rashin hankalinki hadda na goyan. Ni kaina nan ba farinciki nake da aurennan ba saboda haukan nan da sukayi na daura mata maza biyu sam bazata zamo mana alkhairiba: Inna an bashi matar binshi za'aji da mugun asiri harmu nan yasha femu hakanan muna zamanmu ya jawo mana ja iba gayi yayi da zatukanta mikewa yayi da kyar ya fice kofar gida. 158 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Inna binta tace ke inna baki ganewa bakisan liki mar hakan ba. Yarinyar nan uwarta kudi kegareta ina ganinta da manya manyan kadade bandir bandir sannan yarinya ce me kyuta ba kananan alkhairi nake samu dagareta ba. Ta ya kike gani idan ta shigo gidanmu kanina na auranta bafa karamin warwarewa zamu yiba. Inna fa tayi sukuti tana sauraro jin labarin kwandala tace Allah "yarnan? Ta mike kafa sosai tace habawa sosai mana wallahi duk yan cefanan da kikaga ina yomiki daga kudin tane duk in tazo ina da dubu biyu. Tace Allah binto harda rike haba. Tace wallahi inna. Kinga tana san sulaiman haka zata dinga kwakwakwa gun uwarta tana bashi muma muna samun na batarwa zama da talauci bashi da dadi inna da zama da matsiyaci gwara zama da me arziki. Tace hakanan fa yarinyar nan kinyibasira meyasa tuni baki sanarshe niba? tace ai nasha kin gano hikimata da dagewata. Tace ina sam wallahi face to kinji hikimar alkalinnan ya mana kancal. Tace sasai badan kadan ba. To yanzu ya za'ayi ta tabe baki yo ni nasan ya za'ayi bayan an yanke hukunci mu gashi ba kudi ba bare mu daga kara. Tayi jimm sannan tace ke binto shegen son kudinki ina 159 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar tsoron kar ya kaimu gahalaka muzo mu sa kanmmu a wahala. Tunda an yanke hukunci shikenan muhakura mun dace gaba. Tayi shirun tsawo sakwanni sannan tace shikenan amman wallah idan na şamu dama zanyi dun ta dawo mana nan amman dai zan dinga kai mata ziyara ina dan samo wani abun. Ta Harare ta tace meye hadinki da ita da zaki dinga zuwan mata gida. Bayan kin kwanto aurannaki ta yaya. Tace nifa bai sake niba zai zo ya maidani nima ina zanyi wannan sakacin wane gida ne zanyi abinda nake agidansa ni kadai abu na. Tace ko da naji gwanda ki kuma gidanki kar nauyin yayi yawa tace to ai zan koma daman nasan tunaninki kenan kar na cinye muku abinci. Tace in hakane naji laifi ne yaro na shan wahala na nemo wa kizo ki saki ciki ki cinye nasa ke kinbaro naki auran tace naji naji haba zan koma shikenan ko? Tace shikenan hakan ai yafi agaisa nesa nesa dai. Anan ta kwana ranar inna nate tsegumi kan abinci lokacin da nafisa tagama wahalar aikin tuwo duk tayi gumi ga fama da itace saboda damina idanunta. Sun rikide hakan yasa kanta ke masifar 160 WAYE ANGON? juyawa. Maryam Ja'afar Sai bayan isha tagama ga tabatar kokunya inna batajiba wanda ya zamar mata ka'ida duk dare. Ta sungumo tukunyar tuwon gabadaya ta kawo gaban innada ta kafa kujera tasa ta tsare tana ganin aíkin duk dan kar asa ma danta magani amakke ko ta debi wani ta baje kafin ıkasa abata nata. Ta toma ta dauko kwanukan da maara duk ta aje gaban innar. Sınnan tabar gun ta koma kan miya. Ita ma miyar koda akagama aka kawo mata aka dire ta koma kan tatar kokan tarayi tana dafe kai. Aka yafuto dan tuwan mara daya aka ofka miya ciki wacce bata fi rabin ludayiba duk yawanta kuva aka dangwarar dashi gaban inna Binta akace gashinan ta lalli tuwan to kalli innar tace dan wannan kefa inna rowar tsya ji yar miyar kamar na roko itama ta fusata ta miko hannı tana cewa bani kayana me rainuwar tsiya. Kefa binta cin araba ne dake tace cikin jin haushi ai daman haka kike cewaduk sanda irin haka ta kasance ke dai kar azo a cinye muu abinci sabode bakar rowa. Yanzu ya zanyi da wannan bincin wallahi ba inda zai je min. Cikin gajiyaw tace ke bani kayana don ubanki maras 161 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar godewa Allah ina naki wannan din ke ke nemo masa? Tace bani ke nemo masa ba amman dai ai abincin dan uwa nane. Tace to bigeni ki kwata marar tausayi ko tausaya masa bakiyi ki saukakwa cinki in kinje can gidanki kyaci yanzu da safe ma jira zaki abaki amman duk da haka baki ga kokarinsa ba. To naki na kara din in zaki ci wannan din kici in bakici bani kayana gobe mun kara muyi dumame. Harara innar tayi yayinda ta luma hannu ciki tuwan taci gaba da silbarshi rantabace dajin haushin rowata. Sulaiman ya fito daga bandaki ya aje buta da yar cikin jin jikinsa yace to meye na hana abincin aba lowa mana yaci ya koshi meye amfaninsa. Tace to ubana ko miyina anki aba din aci yako shi biyewa binta zakayi in dan ita ne akwanaoiyu zata iya cinye mudu sam bata iya tattaliba saian binzan a! munbazaranci tsiya sambata san darajar abiciba. Yace to bata nawa mana kinsan dai ya rata kadan kuma tunda an karu ai sai a kara awo ko? Tace an kara fa gwangwanin garin daya iakin yande ak dafa wa kullum sannan da safe ma ci zatayi. So tace ta yafi kafinta tai ta uban kashi me shegen wari da karfi. Kude kansa yayi ya 162 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar wuce ya gaji da maganganun in dai innace zata iya kwana da ita ana abu guda sabode nacinta duk ka gaji ka sakar mata ga nuna iko. Dakin matarsa nafisa yadosa zai shiga ta daka masa tsawa kai ina zaka je? Yace batare daya juyoba so nake na kwanta bana jin dadin jikina yau ta zaro masa ido tareda nuna masa dakinta zo nan ka kwanta tun yanzu ka saba shiga ka kwanta ko sabon gulma ne. yace kai inna ki tausaya min mana banajin dadin guntu guntun baccin danake im son na kwanta gabadaya don na huta sasai. Tace anki din dawo nan ka kwanta nace. Wucewa yayi kofar gida ya bar mata gidan gabadaya tace hakan yafi yaushe zan barka ka shiga tun yanzu. Binta dake gefe tana jinsu tace umku dai kuka sani shi kafiya ke kuna takura da shiga hakki ta uyo tana kallonta baki cike da tuwo har yana fadawa wanda t tauna tace. Kinsan bintc na kusan fasa miki baki saboda rashin kunyarki, ina ruvanki ne yau daga zuwanki zaki fara sa min idao da surutaito gobe ki tattara ki koma gidanki bazan iya ba kin naji duka. Samira ce ti fito laga daki hannunta rike da waya tasa 163 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ear phone kunnanta tana bin wakar dake aiki daga ita sai daurin kirji kai ba dankwali hannunta rike da indomie da kwai ta shige kitchen inna ta bita da kallo harta shige ta fito da yar karamar tukunya tana kokarin wankewa tace kinsan idan na kara ganinki da wannan taliyar ta leda sai na dandakaki a gidannan keda ita waa ya waifeki da bazakici tuwo ba shi muma mukaci sai shegen feleken bazakici tawo ba. Bata san me fake cewaba saboda tadode kunnen saida ta jefeta da marfin kwano sannan ta cire tana cewa inna me nayi kike jifena? Tace Amadu na jefa ba kebadan ubanki. Tace to me ya kawo kuma na sako ubana cki yana kasa kwance kina zaginsa. Tace na zaga zo ki ama mai tayi shiruu tana gun guni ta wanke ta shige kichen Binta tad ago murya tace munci indomie in kin gam: kanwata daman ban koshi ba. Ta kalleta tace kwadayayya ahaka zaki kare kina bin kannaki kina lashe musu dan abinda uka samu. Mikewa tayitabar gun wanke hannu tana rarlawa. Nafisa baiwar Allah tana daki duk tana jinsu bayanta idar da sallar isha'i. Jikinta duk kaikayi yake mata ga kaari duk sabode aikin da 164 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar tayi da son samu ne tayi wanka amman jarabar inna bazata bartaba bata isa tayi wankan dace ba yanzu zata hau masifa da zaginta. Wankan me zatayi da dare in ba sako gulma ba da makirci don haka tana ji tana gani ta kashemata wankan dare sai dai ta kwana da kaurin danko da kaikayi. Da tage tana cutuwa ne bata iya baccin kirki sai ta dinga shiga da baho. Daman tana ajiyar ruwa a daki na bokitai sai ta shiga cikin bahon tayi wankanta abinta sai ta daidaici inna ta shige daki bazata ji matsin ruwa ba. Ahaka take samu tana bacci me dadi da tayi sti gado nan da nan sai dacon me dadi ya kwasleta bata sanin shigowar sulaman din dan sai dare yayi sosai sannan yake samun shigowa. Tana zaune tana laziminta inna ta kwalo mata kira har tana tuntube dan saurin fitowa kartace wani abu. Ta fito hijabi jikinta ta tsugunna tace gaani tabita sama da kasa tace matar limin anan sanye da hijabin an shige daki anyi shiru. Kunne na nade duk abinda akace saboda muna kicin ba'a ko jin sai kin kasa kunnuwa. Ta sunkuyar da kai dai cikin ladabinta gantalallen tuwonta aka turo mata wanda baifi na bintanba mara guda duk wahalar aikinta shine rabonta. A kace dauki gashi nan 165 WAYE ANGON? yau Binta tasa miki rani na dan rage zubi. Maryam Ja'afar Tace ba komai an gode Allah kara rufa asiri daga haka ta dauka ta wuce daki. Daman yunwar na kwakwalarta ba wani koshi takeba don haka minti biyar yawa ta muke. Tamkar bataci komai ba haka taji. Sai dai ta kora da ruwa ta kuma tayi zaune jugum tana cigaba da lazimin. Itake dai abin ya kasance har washe gari. Shi kuma Baban mabaruka ahaka ya kasance awannan daren sai dai ya tura gidan matan kanin saya basủ nair hamsin su sai wani abu. Shi kad'ai ya kwana a gidan cikin takakin tsiyar da binta tamasa na barmas a yara. Ranar da za'a tafi da mabaruka gidin imran kansa Binta ta shigo dakin inna tana cewa zanje fa in gano makwam in gano gidin mabasuka inzo in baki labari. Tace aifa ke akwai tsinannen yawo hake kake so kit a gantali a gari zini na kodewa. Kije. Sai kin dawo bata damu da maganar innanba ta wuce fakam fakam. Tamkar mahaukaciya. Kode taje bata iya shiga gidanba musamman da me gadin gidan yake mata kallen almajira san ya hanata shiga duk irin bayanin da take masaa amman yace ina wallahi 166 WAYE ANGON? bazata shiga ba. Maryam Ja'afar Ta ciji yatsa matuka saboda takaci taso ta shiga don ta bada labari kuma akai rashin sa'a ba ubanda ya ganta cikin wadanda suka santa kota sansu su shigar da ita. Shi dai tadinga dogin wuta tana jin jina gidan mamakinta wai duk mabaruka ke da wannna gidan ita kadai har yafi gidan mamanta? Duke hasashenta bai hakaba ayande take tsammanin ganinsa kash! Ina ma ta shiga taga ya cikinsa yake tamkar ta kaiwa maigadin duka take ji. Sai dai tawuce ta zagaye duk bayan gidan tana kara tu'u jibin tsaruwar gidan. Karshe dai ta tattara ta komo a kasa a zatonta daa ta shiga ciki mabarukar zata bata kadi harta hawo mashin. Daman akasa tazo don haka takaici biyu ga na rashin shiga ga na rashin samun kudin don tason ta samo tun a hanya zatayo cefanan ta me rai a lafiya har da nama ko kifi taso. Tazo ta girka ta baibaye gida da kanshi tahana inna gabanta ma zata zauna tacita taune kashin don ta rama. Sai dai hakan baiyuwu ba. Itaka ta dawo gida wurjanjan kafafuwa sunyi lu hu luhu yar yarkace yirkace tana zuwa randa ta nufa ta kwan kwadi 167 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ruwa kan tsohuwar yunwarta dasa bawa sannan ta shigo daki tana cewa wash. Ta fadi kasa tana maida numfashi inna tabiya ta da kallo tace sannu kinsha wuya hala. Tace ke dai bari ba kadan batace ya akayine ta bata labarin komai. Tace Allah ya kara maganin ki kenan kinje inda baa gayyaceki ba saboda yawonki da kwadayi gashinai kinci bakarwuga kin dawo a bama gobe kya sake. Cikin jin haushi innar da gajiyarta tace ke kiji inna ya mabaruka ba yata bace ubantafa nake aure har sai an gayyace ni don naje gidan 'yata? Tace lallai kam tunda de kika je an bude miki kafa kin shiga saboda kin haifeta. Wallahi nasan baki ma me gadin kama de mutu niyar arziki ba wacce za'a kiraki da uwa yasa yace bude miki mu samman de yasan ita mabarukar wane gida ta fito gida no na masu kudi tsaffta da hankali, amma ke wa zai saki a lissafi mahaukaciya kawai maganganun inna suna mata zafi matuka wallahi ba dan matsayinta agunta ba wallahi da yau saita mata dukan tsiya ta barta kwance ko dan tahuce gajiyarta da haushinta mata sai fadan tsuya dagori juya mata baya tayi ta kwanta shame shame a kasa tana jin kafafinta na dandaka. 168 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar afTace ki tashi fa ki tafi gidanki yau bakida wuri anan bare ki samu kwanan abinci ki tafi can. Aranta tace sai ki tayi tayi kwanciyarta abinta. Baban mabaruka kuwa tunda safe yara sukazo ya basu na koko. Ishirin kadaice jikinsa ya mika musu su biyar sai nag aye ko shi zar shana takhin. Haka suka siyo suka kukkurba harda kokas yayi jigum yana kallansu shikanshi inda son samu ne suidan.san masa haka ya kwanta jiya baci komai ba koba kamai da Binta nanan da ta danyi danyi dabararmu ta mata tadan girka wani abu ko dan ya yenta harta sammasa to bata haka kokon safe in ya bada ko talatinne ta kan cika a asiyo dadan yawa har shi ya kurba da aka zo na rana suka sa masa kuka su yunwa suka ji shi kanshi na gayen ya galabaita sai dai dan Babban wande bufi shekara gama shaba yake ta jigik dashi. Kwandala bashi dasu da yai basu suci kode awara ne ya fita ya bubbuga bai samoba sai gama. Ya siyo musu kuli ya kawo musu suka tattauna saka sha ruwa. Allah ya jefo masu sijan kwalabe jikinsa har rawa yake yakwaso duk kwalabanta da take Tarawa din ta sayar ya fice dasu. Daya daga cikin yaran yace ka na inna nefa ita ke 169 tanaaa WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Tarawa zata saida. Yace itama sai na sa yar ba kwalabe wa zai amfana da kudin idan baku ba marar kunya? Suka yi --shirų suna kallansa ya fice da sauri kar me kwalabin yatafi tana cewa in sake jin bakinka marar kunya. Anyi sala kam kwakben da yawa duk ya siyar ya wuce shago ya siyo mu su gari da siga ya kawo ya jika ya basu suka kume.. Yamma lis sulaiman ya shigo ai de sauri tafice ta tareshi tana cewa kai sulaiman ba dole ba akin baka mata ba kaga kerarren gidan da aka gina ma mabaruka? Ransa ya bace sosai ya dubeta yace yaaya banason maganar nan kar ki sake yi min ita. Tace kai sakarai shawara nazo maka da ita. Wallahi har gude ina son mabaruka ta shigo gidammu. Kuma kaima nasan har ynazu kana santa koba haka ba? Yace to meye na tambayar alhalin kinsan haka ne ina santa man azan dana ne. Taa to ga shawara ya baza kunnuwa yana saurare tace dayan bayun wallahi ko ka sace mabarukar ko kuma shi ANGON. Buta ke hannunsa ba shiri ya salata yana kallanta yace 170 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar r 1 sata wannan cace irin Magana cemarar dadi yaaya. Tace ka fahincce ni mana yanzu zaka ta zura ido kabar wani kato ya kusanci matarka alhalin kowa yasan matarkace akwai fa auranka a kanta fa kausu maida kai gara fa. Yayi shiru yana tunani tabbas yana son gasgata maganarta tabbas mabaruka matarsace tunda an daura mashi aurența ya bada sadaki kuma babanta ya daura masa. Ya za'ayi yabar wani sakarai can tare de matarsa alhalin shine ANGON. Jikinsa yahau rawa sabode kishi ayaune komai zai iya faruwa idan yayi sake tabbas dole ne ya dauki mataki ayau ya kamata ya raba mabaruka da wannan mugun me kwace matar mutane a yande yake jin kansa har kisa zai iya indai mabaruke zata zama matarsa ya tabbata itama aduk inda take hankalinta tashe yake tana cikin damuwa. Tabbas bazai bar rayuwaisu ta surkur kuce haka har a rasa rayukansu gwanda a kawar da imran din don cetan rayuka biyu. Yadubeta yace ya kike ganin za'ayi kansa? Taji dadi sosai tace yawa kanina yan daala zaka samu da yawa ku dira gidan da wukake da dare bayan an kaita daki ku gudu 171 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar da imran din kuyi nisa dashi sosai kuna azabtar dashi har sai ya rubuta takardar saki gareta. Kuji hikimar dane kata ga mabarukar a tabbatar da eh lallai ya saketa din kaya tana nan tana idda har ta gama nasan to a wannan lokacin za'a baka auranta tunda wanda suka ba ya wulakantata ya sakar musu ita bayan ya gudu. Bazaku sake shi ba har sai bayin aurenku. Jikinsa na rawa idanunsa sun sauya yana jin ya gamsu de bayaninta yace zan iya kawar da shi gabadaya dan samun kwanciyar hakalinmu. Tace a'a bance haka babande kisa bai saurareta ba ya wuce da sauri yana cewa ba abinda zan fasa. Idanunta suka fito hankalinta ya tashi ta dinga kwala masa kira amman ina yayi nisa da gudu ta fada dakin inna tana rawar jiki a tsorace. Inna ta bita da kallo ta tashi zaune daga kwancan tana cewa meye haka wane kaka haukanne? Ta zauna tana cewa da sulaiman mana tace. Tace en me yayi? Ta bata labarin abinda ta tsara masa da yanda suka rabu na kudirinta. Inna tace ke dai akwai shedaniyar mata kinta dan uwanki kika tara yayi kisa kan san kudinki? Tayi tsuru tana kallanta. Tace to wallahi ke 172 WAYE ANGON? za'a kama ba ruwana. Ke kika turashi. Maryam Ja'afar Idanunta suka fito ta fara rantse rantse ita batace yayi kisa ba shine yace zaiyi. Inna tayo kanta zata daketa har zani na fajuwa. Rufe min baki makira ke dai fitinace duk ranar da kikazo gidannan sai kin haifar da tashin hankali karshe ma yau kisa zaki jawo mana muna zaman lafiya. To tashi maza maza ki bargidan na gaji kikama can gidan mijinki, tace cikin jin haushi nifa ki bar gańin laifina kome nayi ranonki ne kika bani ahanja kika koya min dan na kwatanta kadan daga abinda kikayi sai kiga laifina ta kara zafafa to naji tashi tashi haka ta dinga korata har zaure tamkar akuya tasa sakata ta datse gidan ta juya tana masifa haka kawai yarinya taja mana jafa'i ina dalili. Shima zai dawo ya taras shine mu zuba dani kuke zance ta shige daki taja tayi tsaye tana hararan gidan tamkar bazata tafiba. Daga karsle dai ta zuciya fuu ta wuce azuciyarta tai alwashin bazata sake yin yaji ba tazo wajen inna gari da yawa ga gidajan kawayanta. Don haka can ta fara nufa gida gida duk in taje da niyar zama zasu canza mata fuska ba arziki ta fito tayi nan tayi nan ba inda ake ganinta da daraja. To wa zai jawa kansa 173 WAYE ANGON? bak'i taje ta kashe dan makalallen auren. Maryam Ja'afar Baban mabaruka kuwa yana can yana fama da yara har dare yayi ya rasa sukuni. Tabbas ya fara nadamar barin binta da yayi ta tafi. Dole sai ita gidannan wa zai iya rike yarannan: shi dai kam ko da kudi be iyawa don haka ya kudiri aransa tunda safe zai yo bikonta ta dawo su zauńa ahake kawa ai shegen kansa ne. A nata bangaren itama hakane har daren bata sanu inde zata raba ba. Ga yanwa dake damunta sannan mamanta sun cicciko sai tsiranta suke tun jiya idan tayi wasa zasu zame mata ciwo gwanda ta dawo gidanta kawai in ya mata ta masa. Yafi wulakancin da ake mata ta kanta inna walakancinta dabian ne ga ruwar masifa sam baka koshi agidanta ko da da ziyara ne wuni daya waima ita don an santa "yace amman bakihaka ko a "yan uwa ne ba wanda take ba sai dai a dafa abarshi a tukunya ya dankare. Don haka tasan gidanta ya fiye mata koba komaidai ko sana'arta tayi taci ta koshi tabawa yaranta amman a haka batasan halin da suke cikiba. A wannan daran yaron na gaye ya kima kashi ga zazzabi da yake na maracin mamansa sar amai shaa ga dankaren 174 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar far kuka shima haka yayayyen kuka da kashin tsaye duk sukabi suka rikitashi saurankuma kuka wai yunwa sukeji. Ji yayi bazai iya hakurin safe ba takalma kawai ya shura yayi gaba dan yo bikon matarsa binto. A kafar gida sakaci karo da juna. Ta doka masa harara tare da tsaki ta wuce cikin gida ta barshi tsaye. Wani farinciki ya saukar masa ganin dawowarta dai dai sande yake bukatarta. Yabita da kallo har ta shige yana dariya yace oho dai ai kin dawo kije ga aikin can na jiranki ni nayi nan yawuce da sauri. Da wannan tilin kashin da amai tayi maraba ga kukansu sun birkita gidan taja tayi tsaye tan a kallo cikin tsananin masifa tace kam bala'i kunyi kashi shine ya kasa wankewa zai fita ya barku anan. Suka yi shiru suna kallonta na goyon ko koda ya ganta yah au zillo yana dariya ta fito da sauri don ta sauke masa kwandon masita sai dai wayam. Tajuyo tana bak'i zaka dawo ka sameni wallahi ni kadai na haifi "ya "yanne. Ko zama batayi ba ta hau wankin kashi. Suka isheta da inna yanwa mukeji ta tasomusu nima banciba kukaki garkwa wanda ya ajeku eye? Suka yi shiru suna kallonta a tsorace ganin yanda ta taso musu tamkar 175 も 1 1 1 1 WAYE ANGON? zata cinye su. Maryam Ja'afar Sai da ta kammala sannan ta dubą tsohuwar ajiyarta sabode irin hake kanzo adaran ta daka ta murza musu da gishiri suka ci suka koshi. Ta dade tana jiran dawowarsa har bacciya kwasheta bai dawo ba. Sai day a tabbata tayi bacci ya dawo ya shigon sadaf sadaf ya kwanta. Shawarar de ta bashi tabbas ya dauka dan haka yayo hayar "yan kato da gora ko nace kauraye ko "yan daba ya tanade su su kuma suka tanadi makamansu. Sai da dare yayi sosai misalin karfe daya na dare sannan suka tinkaro gidan imran. Lokacin kowa yana cikin halin da muka barsu ita tana bayi shi yana dakinsa kwance suna bacci ta kan me gadi suka fara suka daure shi suka kwantar dashi suka shigo cikin gidan duk ma'aikatan suka daddaure su hanyar hanyar sadarwa na gidan suka daddatse suka tunkaro dakunan. Kamar cikin bacci imran ya dinga jiyo tashin maganganu a babban falo ya mike da sauri dọn dubawa har lokacin yanajin zafi akansa. 176 F WAYE ANGON? Maryam Ja'afar far a Ta window ya leko abinda ya gani ne ya ya storatashi a ganinsa yan fash duk sun rurrufe fuska sai bindigogi da wukake hannunsu Ya saki labule yana salati hanlinsa ya tashi ainun ba abinda ya fado masa sai mabaruka kada su shiga dakinta sú lalata masa mata itako su kasheta. Jikinsa yah au rawa bata kanshi yakeyiba ita kadai ya keji Daga cikin ma'aikatan gidan ya nuna musu dakinshi kamar yadda suka bukata don haka suka tukaro dakin da zuwa suka fara dukan kofar tamkar zasu karyata. Ya runtsa idanuwa yana ambaton sunan Allah sukace kabude kofar nan tun kafin mu shigo da kanmu. Yayi addu"a de neman tsarin ubangiji ya dogara gareshiya nufi drower don ya dauki waya babu ita a dakin yayi shiru yana tunani sai sannan ya tina yasata charge a dakin mabaruka ya dafe kai yana salati suke sake dukan kofar tamkar zasu budo su shigo. Wucewa kurum yayi yana addu'a yasa key ya bude kofar suka bankado shi dakin ya fadi ta baya saman karpet duk suka shigo sannan babban cikinsu yayi dariya tare da cewa barka da dare oga ya kasa cewa 'komai yana kallonsu 177 n E E E 1 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ya sake cewa ango ango kai da zamu tarar da kai a dakin amarya ya akayi muka tarar da kai a dakinka?Yace kansa tsaye haka nake sha'awa ko akwai laifi? Yace no no no ka kyauta that's gud haka muke so daman damun tarar da kai adakinta da hukuncin da zamuyi maka sai yafi wanda muke tsaro ya dubeshi cikin jarumta pls ko zaka fada min me kuka zo gidana a wannan lokacin? Yace kana mamakin ganinmu ne? yace sosai ma kuwa yace ok amma bamuyi maka kama da masu neman nadare ba? Yace bazan iya ganewa ba sabida bansan kamanninsu ba don basu taba zuwa min ba Yace good good kasan dalilin rashin zuwan su? Yayi masa banza yace saboda baka da dalilin azo maka gida, kasan meye dalilin ya girgiza kai a'a yace to amaryar da aka kawota maka zo maka gida sai sannan ya fahimce su da nufin su yaja tsaki tare da mikewa tsaye yana kakkabe hannu yana hararansu duk suka bishi da kallo da mamakin karfin halinsa. Daya daga cikinsu yace cikin maganar su ta dabanci wai ya hakane oga wane irin gaye ne shi yaa muna Magana yanayi kana tsaye oga yana tsaye ai aika mar kawai ko? 178 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar 'afar Yayi dariya ogan ya fara zagaye shi sannan ya dubeshi yace dan Shafa min shi malana yakai masa duka aikuwa ya daga hannu zai kai masa duka caraf ya rike hannunsa cikin tsananin bacin rai yace kada ka kuskura ka kai hannunkajikina dan wallahi lallai zan kar yaka idan kai karamin dan iska ne hannunsa ya kama rawa da jikinsa karshe ya sake shi. Ogan tafa ya masa yana cewa good good ka birgeni abokina haka nake son namiji, ya dubeshi cikin bacin rai yace ka ka fadaman me kake so me zan baka ku fitar min daga gida, ya juya yana juye juye adakin sannan ya tsaya gabansa yace anan banga abinda zaka bamu ba nasan baka ajiya a gida, bakudi muke nema ba kawai dai munzo daukar ranka ne simple ka bamu kawai mukara gaba. Yayi dariya ya kalleshi yace daukar rai ko? Yace yes yes yace daga cikinku nan bame iya daukar raina allahi ko don irinku allah sai ya barni da tsawon rai don ku dinga ganin takaici mata ni allah yaba don nine alkhairi gareta ku fadawa wanda ya turoku 'yasa ido yagani zaiyi mamain irin zaman da za muyi me sha'awa da birgewa bai taba ganin ma'aurata ba irimu ahaka zai mutu dabakin ciki kufada masa kukuma 179 ta an Ka ta la ni n d a h も t 1 1. WAYE ANGON? Maryam Ja'afar sakarkaru dakikai marasa aikin yi idan zaman ya gagareku kuzo zan baku aiki da albashi me

Chapter 8 of 10