ke gani shi ke da mata?"
Ya nutsu tsawon dakiku.sannan ya ce "Kai! I can't, ban
san wa zan ce shi ne angon ba, wannan sai mai shari'a."
Ya yi jim sannan ya ce "Ka taya ni addu'a abokina a bani
45
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
matata, zan iya mutuwa idan a ka ba wancan, ko kuma na
kashe shi wallahi."
Ya buda baki yana salati, cikin tsorata da mamaki yake
kallonsa. Ya ce, "A'a kar ka fara wannan tunanin, ka bar wa
Allah komai kar ka bi son zuciyarka, Allah shi zai ba mai
mata matarsa."
Bai iya cewa komai ba, ya yi daijim yana sauraronsa.
Koda suka shiga daki ta zaunar da ita bakin gado tana
dubanta.
Ta сe, "Me ki ke tsoro ne?" Tayi shiru tana kallonta ba
amsa. Tayi murmushi ta ce; "Na fahimce ki abin da ki ke
tunani ba haka ba ne.
Ki kwantar da hankalinki, Sulaiman dai mijinki ne ba
komai yasa ya bukaci haka ba sai don samun nutsuwarki da
tasa, don farin cikinku.
Don kin kwana a nan ba wani abu ba ne, kowa yasan
kina tare da mijinki ne bare ba wanda yasan kina nan..."
Ta katseta a sanyaye "Amman wannan ha'inci ne bai
kamata na ha'inci Mahaifiyata ba. Sannan ba ni da tabbacin
waye mijina tsakaninsu.
Ina tsoron sabawa Mahaliccina, haka nan idan
46
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar far
a
Mamana taji ina tare da Sulaiman bare na kwana da shi na
rantse sai ta karya ni."
Ta zauna tare da dafa kafadarta cikin lallashi.
"Ba abin da zai faru da ke, kiyi tunani tun yaushe ku ke
cikin rashin nutsuwa da fargaba? Yau kadai idan ku ka
wuni da juna ku ka kwana za ku sami nutsuwa ku shiryawa
tanadin gobe.
Ki nutsu da kyau hakan babu aibu, don shi mijinki ne ya
bada sadakinki an kuma daura muku aure yana da ikon fita
da ke duk in da ya so."
Tayi shiru tana tunanin maganarta, wani gefe na
zuciyarta yana son amince mata wani gefen kuma yana
hanata.
Da dadin bakin Basira da lallashi ta shawo kanta a kan
eh zata kwana din amman a kan sharadi.
Ta dubeta ta ce, "Wane sharadin kenan?" Ta ce tana
kallonta "Ba zan kwana tare da shi ba a daki daya, sai dai su
kwanta da mijinki ni kuma na kwana tare da ke."
Tayi dariya ta ce, "Wayo ko Mabaruka?" Murmusawa
kawai tayi ta sunkuyar da kai ta ce, "Shi kenan kada kiji
komai hakan za a yi, amman muje muci abinci muyi hira
47
WAYE ANGON?
yau sai mun kái dayan dare muna hira."
Maryam Ja'afar
Haka kuwa ta kasancen, sun dade a falo suna labari gefe
kuma da dan abin sa wa a baki.
Bai ce komai ba suka shige shi da Mansur din wani
dakin su kuma suka shige dakinta.
Can ma suka dasa da ita, musamman hirarmu ta mata da
Karin shawarwari.
Taji dadi kam da sukuni ta dinga nishadi musamman
kasancewarta da masoyinta ga abokanan hira masu
mutunci da ban dariya.
Sun ba su shawarwari a kan addu'a ce kadai mafita gare
su. Ta kwnata tana nishadi tana cewa a ranta me ake da
wnai Imran can! Ina! Ai sai Sulaiman.
Haka zalika ta tashi da farin ciki, sai dai kash! Tuna yau
za ayi ta ta kare yasajikinta ya yi sanyi kalau.
Fargabarta ta dawo sabuwa, addu'ar da su Mansur suka
bata ita take ta nanatawa a baki, har suka baro gidan karfe
goma.
A hanya Momy ke kiranta ta ce tana kan hanya. Can
nesa da gidan ya ajeta a kan sai sun hadu a kotu, ya juya ya
wuce.
48
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ifA harabar gidan suka hadu da Imran.
Ya yi kyau sosai yasha dream yard ya yi matual dress,
fuskarsa manne da glass fari yana kokarin shiga motarsa
wacce a ka wanke masa tana ta sheki.
Suka hada ido biyu ya sakar mata murmushinsa mai
kyau.
Yayin da tayi saurin dauke kanta ba ta dai harare shi ba
ta shige ciki da sauri tamkar wacce a ka ce a kamo.
Ya yi siririyar dariya tare da fadawa mota yana ambaton
sunan Allah, ya ja motar ya fice zuciyarsa cike da tunanin
'yar Mabarukarsa.
la112
1Karshen tika-tika-tik!
**
A KOTU
Kamar yanda Alkali ya ce a yau zai yanke shari'a, zai ba
mai mata matarsa a yau dinnan.
Kuma koda aka fara tasu ce kan gaba ya kara
jaddadawa lallai a yau zai yanke hukunci.
'Yan cikin Mabaruka suka hautsina, zufa ta keto mata,
49
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
jikinta ya yi sanyi kalau, gabanta ya dinga dukan tara-tara,
fargaba ta cikata dam.
Har sai da Rafi'a dake gefenta ta riko hannunta tana
cewa, "Ki nutsu Mabaruka ki ta ambaton sunan Allah, za ki
samu nutsuwa."
Ba ta iya amsawa ba sai dai ta daga kai saboda yanda
bakinta yai nauyi ta baza kunnuwa da idanu tana kallon
Alkali.
Imran kuwa da Sulaiman ban san wa ya fi shiga fargaba
da zullumi ba, sai kallon kallo suke.
Ita kanta Momy a zulumce take, tana tsoron kar 'yarta ta
shiga gidan Sulaiman ko ba lallai Imran ba tana tsoron
matsalar gidansa, sabanin Babanta da fargabarsa ba wata
ba ce.
Da farko Alkali ya faro da nasiha da wa'azi, ya kawo
ayoyi da hadisai a kan yanda aka ce mu Musulmai muyi
aure.
Maza an ce su aura daga bibbiyu zuwa uku har hupu,
idan sun ji tsoron ba za su yi adalci ba to su tsaya ga daya.
Babu wata aya ko hadisi da aka ce mace ta auri fiye da
miji daya, sai dai ko in auren ya mutu ko mutuwa ko
50
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
rabuwar aure shi ne mace zata sake auren wani namijin.
Ba don komai ba kuma sai don adalci ne hakan. Kai
kanka ka nutsu kayi tunani a kan abu daya ma kawai mu
dauke shi dangane da daukar ciki.
Yau in tana dakin wannan gobe tana dakinw anna sai ta
sami ciki, to ta ya ya za a gane cikin wannan ne 'ya'yan
wannan ne? Ba yanda za a yi hakan ta faru.
Don Allah bai ce ayi haka ba, ba wata dabara ko hikima
da zai sa mace ta auri maza biyi, yin hakan kuma babban
zunubi ne, rashin tsoron Allah ya shigo da rashin tsoran
azabarsa.
Duk wanda ya yi haka kuma ya sabawa Allah da
Manzonsa, sannan akwai tsantsar jahilci da isa, don sai
jahili zai yi haka, kai ko jahili in dai ba mahaukaci ba ne ba
zai yi irin haka ba.
Babu inda ake auren maza biyu, mace namiji daya take
aure, don haka iyayen wannan yarinyar sun aikata babban
sabo da zunubi, dole ne su nemi gafarar Ubangiji suyi ta
istigfari.
Idan rashin jituwa ce su sasanta kansu, an haramtawa
Musulmi gaba da junansu, an fi so su kasance ma su yafiya
51
afar
la
Li
a
1
WAYE ANGON?
da hakuri ga dan uwansu.
Maryam Ja'afar
In ita mahaifiyarta tana jin haushinsa ta rike abin da ya
mata sai tayi hakuri ta dubi matsayin da Allah ya bata а
yanzu ba don yinta ba shi ma yasa wa kansa dangana.
Su daidaita da junansu don zaman lafiyarsu da
kwanciyar hankalin yarinyar da suka haifa, don a kullum
da ba shi da kwanciyar hankali matukar iyayensa ba sa
jituwa, ya kan rasa nutsuwarsa.
Sannan duk wannan abin da ya faru rashinjituwarsu da
hadin kansu ne ya jawo haka, in akwai jituwa da
kyakkyawar fahimta sai su tattauna su shawarta a kan wa
ya fi cancanta su ba auren 'yarsu?
Sai su tantance su aura mata a nutse da aiki da ilimi
amman a haka kowa yana ji da kansa shi fa ya haifi 'yarsa
don haka shi zai aurar da ita ga wanda yaso, shi yasa hakan
ta faru."
Alkalin ya dan tsahirta tare da yin wasu rubuce-rubuce
sannan ya ci gaba.
"Don haka zamu yanke hukunci mu ba mai mata
matarsa."
Dukkansu suka kwalalo idanuwa da kunnuwa, yayin da
52
C
WAYE ANGON?
ita kuma faduwar gabanta ya karu.
Maryam Ja'afar
Ya dubi takardun da ke gabansa sannan ya dago ya cсе,
"Imrana Umar shi ne a ka fara daura mata aure da shi a kan
sadakin da ya bayar lakadan, shaidu sun shaida an yi addu'a
kuma kanin Babanta wanda suke Ummi wa Abba shi ya
daura mataa matsayin waliyyinta tare da nashi.
Don haka ya tabbata lallai babu mai mata face shi,
kasancewar shi aka riga aka daura kafin wancan."
"Innalillahi wa'inna ilair'raji'un! Hasbunallahu
wani'imal wakil! La'haula wala kuwwata illa billah!"
Abin da take nanatawa kenan, ta dora hannu saman kai.
Alkali ya ci gaba.
"Daurin auren da ya biyo baya ya zama shirme, harbin
iska ba shi da mata saboda akwai mai matar an riga an kuma
daura din. Don haka sai ya nemi wata.
A yau muka kawo karshen wannan shari'a, idan kuma
akwai mai son daukakata yana iya daukakata daga nan
kotun Musuluncin zuwa wata kotun ta gaba."
Wannan kenan.
Tsalam! Ta mike ta dubi Alkali fuskarta da niyyar kuka
53
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ta ce, "Babana shi ya daurawa Sulaiman aurena, kuma ya
ce shi yaba kowa kuma ya san uwa ba ta daura aure, ya za a
yi a ba shi?"
Ya kalle ta tsaf ya ce, "Yarinya na riga na yanke
hukunci, ga mijinki nan." Ya nuna Imran. "Saboda kanin
mahaifinki zai iya daura miki aure kuma kasancewar shi ya
daura yasa a ka ba Imran din.
Kamar kuma yanda na ce idan bai yi muku ba za ku iya
daukakawa."
Ta fashe da kuka ta haďa hannuwa tare da cewa "Don
son Annabi don iyayenka ka canza ka ba Sulaiman, wallahi
ba na son Imran din."
Bai saurareta ba ya buga abin da ke gabansa alamar ya
tashi, duk a ka mike ana amsa masa daga nan ya wuce
abinsa. Dogaransa suka bi shi da takaddun da ya bari.
Ai fa nan kotu ta hau kace-nace, ayarin Sulaiman da shi
kanshi Sulaiman din sai bala'i suke, yayin da shi gogan ya
yi tsaye ya kasa cewa komai.
Sam bai yi tunanin haka zata kasance ba, tuni ya barwa
kansa shi za a ba mata saboda uba ke daura aure.
Imran kuwa da ayarinsa sai murna da farin ciki, bakinsa
54
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ya kasa kullewa, hatta Momy tana cikin farin ciki sabanin
Sharifat.
Daddy da Rafi'a ma ba a bar su a baya ba.
Ita kuwa ta juya nan ta juya can, duk ta kidime ta rasa a
ina take, ta manta komai.
Jiri ya dinga kwasarta, ta dinga yi luu-luu ana juyata
idanunta suka rufe, kafafunta suka kasa daukarta. Sai dai
aka ji rijib ta zube a nan.
Nan fa aka yo kanta a rude, musamman Imran din shi
kanshi Sulaiman ya runtumo da gudu da Momy da Rafi'a ke
mata fifita.
Cak! Imran ya daukota tamkar jinjira a gigice ya nufi
waje da ita zuwa mota, sauran kuma suka rufa masa baya.
Wani abu ya tokare makogwaron Sulaiman, ransa ya
baci ya dinga huci tamkar kumurci, idanunsa suka kada
jajir.
Ya yunkura zai bi shi ya kai masa duka, abokansa suka
rike shi tare da tunasar da shi wancan dukan abin da ya
jawo masa.
Sam ba ya jin su ba ta wannan yake ba, ya dinga kokarin
kwace kansa, ko da ya kwace din yana zuwa suna barin
55
WAYE ANGON?
wurin da motarsu, suka Ôace masa 6at!
Maryam Ja'afar
Ya dinga kuka yana dake-daken duk abin da ya tari
gabansa, tamkar zai cinye mutanen da ke gurin, idan kaga
yadda yake yi kamarwani sabon hauka.
Asibitin suka nufa da ita, da zuwansu a ka ba su gado, ba
da jimawa ba ta farfado kasancewar bata yi nisa ba a sumar.
Ba kowa dakin sai Rafi'a ta shiga wuwwurga idanu don
son gano a ina take, ta daga kai ta kalli karin ruwan da ake
sa mata, ta gane a asibiti take sai a sannan komai ya dawo
mata.
Ta dubi Rafi'ar cikin yanayin mutuwa jiki.
"Ba da gaske ba ne ko Rafi'a?"
Ta ce, "Ba da gaske ba me?"
Ta ce, "Sulaiman shi a ka ba ni ko ba Imran ba ne?" Tayi
shiru. Sam ta kasa cewa komai bata san me hakan zai jawo
ba, idan ta fada.
Kafin ta ce komai Momy da Sharifa suka shigo suka
hau mata sannu, binsu da ido dai take tana son karyata
abinda zuciyarta ke son tuna mata.
Kamar hadin baki Daddy da Imran suka shigo suma.
Da zuwansa ya hayo kan gadon a dan birkice yana mata
56
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar rsannu ta bishi dai da ido ta kasa amsa masa, so take a bata
amsar abind atake zargi.
Ya hau rawarjiki da ita me take so me zata ci ba dai in da
ke mata ciwo? Sam taji bakinta ya kulle, sannan idonta ya
kasa daukewa daga kansa.
Likita ya shigo ya duddubata tare da tambayoyi gareta,
jikin ba wata matsala, amman ya ce tana bukatar hutu sai.
gobe zai sallame ta.
Ya rubuto wasu magunguna da za su sa ta kuzari da
karin lafiyarta. Imran din ya fita don nemo su.
Dady ya dubeta ya ce, "Sannu my doughter ta daga kai
ta kalle shi tare da amsawa a hankali." Ya ce, "Kin tabbata
ba wani abu da yake damunki ko?"
A can kasan makoshi ta ce, "Eh Daddy." Ya ce "Good,
idan kina bukatar wani abu ki sanar da ni kin ji ko?" Та
daga kai alamar 'To.'
Ya ce, "To zan wuce sai anjima zan dawo." Ta се, "To a
dawo lafiya." Ya dubi Momy yana cewa "Zan je wani guri
دو idan na dawo zan biyo ta nan."
Ta ce, "To shi kenan a dawo lafiya."Ya amsa amin.
Sharifa ta mike tana cewa "Nima zan bika Daddy."
57
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Yanayin fuskarta ba annuri, ya ce "Don me ke da za ki
zauna kuyi jinya.
Ta yatsina fuska tare da turo baki ba tare da ya ce komai
ba. Mommy ta riga ta gama fahimtarta, sam ba son auran
take ba da Yayanta, duk saboda yanda Mabarukar take nuna
kiyayyarsa a zahiri kuma bata da laifi, waye zai so dan
uwansa ya cutu?
Tayi murmushi ta ce, "Me yiwuwa ta gaji ne tun safe
fa." Ya ce, "Amman ai dole ce zata sa ta tsaya din."
Ta ce, "Ka barta dai taje din da dare ta dawo."
Ya yijim sannan ya ce "Shi kenan muje."
Tayi dariya ta dubi Mommyn ta ce, "Thanks Momy."Ta
rufawa Daddyn baya.
Ita ma tayi dariya ta fita don raka su.
Dakin ya rage daga Rafi'a sai Mabarukar ta juyo ta kalli
Rafi'ar, ta ce "Fada min gaskiya Rafi'a, waye Angon? Wa
kotu ta ba?"
Tayi jim tana kallonta, dole ne ma ta sani yau ba sai
gobe ba, ta kamo hannunta cikin kulawa ta ce, "Komai ki
ka ga ya faru ga dan Adam daga Allah ne, Mabaruka me
58
WAYE ANGON?
kyau ko akasinsa.
Maryam Ja'afar ar
Ba kuma don ba ya sonka ba sai don ya jarabaka kuma
me yiwuwa shi ne mafi alkhairi gare ka...'
Ta katseta "Ki fada min kawai bana son sharar fage, duk
nasan wannan, ki fada min waye mijina?"
Ta kalleta da kyau, ido cikin ido ta ce, "Mabaruka Allah
ya yi miki baiwa, ya zabe ki a cikin dubban mata, ya azurta
ki da miji na kwarai mai addini da kamala.
Ba kowacce mace ba ce take samun irin mijin da ke ki
ka samu ba, kin yi miji ba ki da bakin cikin gidan aure, za ki
yi rayuwamai kyau da dadi."
Ta dai tsura mata ido tana kallo, ta kasa cewa komai. Ta
ci gaba da magana a tausashe, duk a kokarinta na kwantar
wa kawar tata hankali don ta nutsu ta gane abin da take fada
mata gaskiya ne.
"Mabaruka! Imran shi ne Angonki, shi ne kotu ta ba."
Tamkar wacce a ka dasa, ta zamo a kan gadon tare da
kurawa Rafi'ar ido tamkar yau ta fara ganinta.
Ita ba tunani ba ita ba kallonta ba, ba ta ce kuma komai
ba. Har sai da ta taba ta, amman ko motsi.
Sai da ta jijjigata daidai zubowar wasu hawaye masu
59
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
dumi daga idanunta wadanda ba su nuna alamar zuwansu
ba.
Ta ee, "Mabaruka kuka kuma?"
Tà kalle ta ta ce, "A tunaninki dariya zan yi ko shi yasa
har ki ka yi mamakin ganin hawayena?"
Ta ce, "In ba ki dariya ba kuka bai kamace ki ba, godiya
za ki yi wa Allah, don hakan ya fi dacewa."
Ta ce, "Dag ayau na fara kuka a rayuwata Rafi'a, har
daukewar numfashina na har abada. Kukan zahiri kukan
zuci wanda za a gan shi ko ba za a ganshi ba."
Ta ce, "Don me Mabaruka? Sai ka ce wacce a ka hadata
da mugun abu?"
Ta ce yayin sakkowar wasu hawayen.
"Ai wannan yafi mugun abu a guna, gwanda a hada ni
da mutuwata a kan nayi rayuwa da shi saboda ba na sonsa!
Ba na sonsa!!."Ta fada tare da fashewa da kuka, sannan ta
kife a nan tana rizgar kukan.
Hankalin Rafi'ar ya tashi, ta birkice ta dinga kokarin
dagota.
"Haba Mabaruka, kina son jefa kanki a tashin hankali?
Duk fa abin bai kai haka ba. Meye laifin Imran da har za ki
60
WAYE ANGON?
bakin ciki da auransa?"
Maryam Ja'afar
Tan dago ta dubeta fuska share-share da hawaye,
"Gwanda a hada ni da mutuwata yafi min farin ciki da
nutsuwa, koda kullum tana daukar numfashina.
Na fada miki ba na sonsa Rafí'a, amman kińn kasa
ganewa, wallahi mutuwa zan yi."
Kasa furta komai tayi sai dai ta bi ta da kallo, abin nata
ya fara wuce misali sai kallo.
Kan ta ce wani abu taga mikewarta, tana kokarin sa
takalma idonta a rufe.
"Mabaruka ina za ki je?" Rafi'a ta tambayeta a
hanzarce.
Ba ta jin za ta iya bata amsa, ta wuce ta gabanta da sauri.
Ba ta tsaya ba itama ta rufa mata baya.
A baranda ta samu cimmata, ta juyo da ita da karfi tana
cewa "Wai lafiyarki, ina za ki je?" Yanayinta ya sauya
gabadaya.
Ba abin da ka ke gani a idonta sai bakin ciki, idanun
nata sun sauya launi, hatta fuskarta ta sauya.
Ta tsura mata ido cikin tsananin fushi tana kallo, uffan
taki cewa. Ita ma ta kura mata idon tana jiran amsarta.
61
E
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Tsawon dakiku suna haka, kawai sai ta sake juyawa tayi
gaba a hanzarce. Ita ma Rafi'ar ta sake binta.
Wani mai adaidaita sahu yana sauke wata mata da sauri
ta shige cikinsa, ganin yana kokarin jan mashin din ya tafi
Rafi'a tayi saurin shigewa itama.
Mai Adaidaita sahun ya ce, "Ina za ku je?" Rafi'ar ta bita
da kallo don son jin ina zata je. Ta yi masa shiru.
יי Ya sake nanatawa, ta ce "Kai ni ko'ina ma."
Ya juyo yana kallonta cikin mamaki, "In kai ki ko ina?
Lafiya ki ke?"
Ta ce, "Lafiya nake, ka kai ni duk in da ya maka."
Rafi'a ta dube shi ta ce, "Yi hakuri Mallam, bari mu
sauka bata da lafiya."Yaja ya tsaya.
Ta jawo ta da karfi ta fito.
Suka yi cirko-cirko suna kallon-kallo a tsakaninsu.
Tsaki kawai taja tare da wucewa.
Tamkar za su tashi sama tana tafe tana biye da ita suna
fada, ta ce "Wai har ina za ki je Mabaruka? Ya kamata ki
saurare ni." Ta tsaya tare da juyowa a fusace ta ce "Ai bina
ki ke, ki sa ido ki gani." Daga haka ta juya ta ci gaba da
tafiya abinta.
62
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ar
Abin da ta gani ne ya girgizata, idanunta suka fito, tsoro
ya bayyana tattare da ita.
Ganin Mabarukar tayi tsakiyar titi, manya-manyan
motoci da mashina sun sa ta tsakiya sai faman horn suke
mata. Ta hada go slow, amman ko a jikinta taja tayi tsaye
tamkar mahaukaciya.
Da wani irin gudu ta falla wanda ba ta san tana da shi ba,
da zuwa ta fincikota da wani irin karfi suka dawo bakin
titin, mutane daga ma su zaginta sai masu tir da ita.
Ita kuwa Rafi'ar saboda tsabar haushi ji take tamkar tai
ta falla mata mari. Ta dubeta cikin fushi ta ce da ita.
"Ba ki da hankali ko kina hauka? Auren dole hauka ne
ko kanki aka fara? Kina son ki kashe kanki ko Mabaruka?"
Tanke ta kasa cewa komai, illa wani takaici da take ji a
ranta, me yasa Rafi'atu take son zama matsalarta?
Ta ci gaba "Wallahi na kusa raba hanya dake tunda kin
canja kin juya halinki, kawai don an aura miki wanda ba
kya so, meye laifin mahaifiyarki har za ki ga laifinta? Bа
zan iya hada hanya da marar biyayya da da'a ba."
Dòn fadin wannan maganar kawai sai ta fashe da kuka,
taja da baya ta fadi kasa tim! tamkar karamar yarinya
63
WAYE ANGON?
yayayyiya.
Maryam Ja'afar
Nan ta hau shure-shure tana kuka, abin ya daina ba
Rafi'atu haushi illa takaici da jin haushi. Wai me Mabaruka
take son zama? Tsakiyar titi cikin mutane take nuna
halinta?
Momy kuwa tunda ta fita sai kawai ta hau motarta ta
wuce gida, a kokarinta na ta dan samawa Mabarukan wani
abu don jin dadinta, musamman abin da tasan zata bukata a
asibitin, ba da jimawa ba tajuyo.
Zata shiga dakin suka hadu da Imran da ledar
magungunansa, sai wata ledar shake da su fruits jikinsa har
rawa yake yi.
Suka tura kofar dakin da Mabaruka ta ke suka shiga a
tare, amma suna shiga suka ga wayam! Dakin babu kowa.
Suka bi junansu da kallo cike da mamaki, kowa so yake
ya tambayi dan'uwansa ina Mabarukar?
Wata Nurse ta shigo ganin shigowarsu, ta ce "Marar
lafiyar nan ku ke nema?" Suka hada baki da sauri suka ce
"Eh." Ta ce, "Yanzunnan naga sun yi na ita da wacce ku ka
zo tare, har sun shiga mota naga sun sauka sun wuce
64
WAYE ANGON?
kuma."
Maryam Ja'afar
aBai san sanda ya saki ledar ba ya runtuma a guje har
yana ture Nurse din. Mamaki ya cika Momy, tayi sake da
baki tana tambayar kanta ta fita ina to za ta je?
Su kuwa suna can tana ta bige-bige da ihu saman titi,
mutane sun mata caa kowa na kallonta, wasu na tambayar
Rafi'ar me ya faru?
Ba ta jin za ta iya ba daya daga cikinsu amsa, takaici ya
cika zuciyarta, ta dinga zubar da hawaye tana gogewa,
saboda abin da Mabaruka take ja musu saboda shegiyar
kafiyarta.
Ta tsaida Adaidaita sahu, da kyar ta samu ta tura ta ciki
ta rirrike ta tamkar hauka sabon kamu, a kan ita wallahi ba
in da zata je sai ta kyaleta an kasheta a wannan titin.
Gidan Momyn suka sauka, ta jata suka shige ciki. Still
dai ba ta fasa shure-shuren ba, ita a lallai sai ta mutu.
Koda ta shigar da ita dakinta bata fasa ba, taja ta jingina
da bango ta dubeta ta ce, "To ci gaba da yi har ki kashe kan
naki don Allah."
Karshe ma fitowa tayi ta dawo falo tayi zamanta tare da
65
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
rafka tagumi tamkar tana jira, tana fita ta maida kofa ta
бame бam!
Ta ci gaba da buge-buge duk abin da ya tari gabanta sai
ta kai masa duka.
Hankalin Rafi'ar ya tashi, tsoro ya kama ta kar fa ta
kashe kanta kamar yanda take bukata, tayo dakin tana
bubbuga mata ta bude, tamkar ba ta dakin bare ta amsa.
Tana jin ta tana kashe glass din mirror da na drower,
'yan kwalaban turaranta su Humra ta dinga kashe su.
Ta ci gaba da rokonta a kan ta bude don son Annabi,
ganin ba za ta bude ba yasa a rikice jikinta har rawa yake ta
lalubo lambar Imran.
Shi kuma a lokacin ya fito sai wiage-waige yake, ya yi
nan ya yi can yana son gano ina suke? Sam babu nutsuwa a
tare da shi.
Kiran da Rafi'ar tayi masa ne a waya yasa da sauri ya
dauka ya kai kunne don yasan suna tare da Mabarukar.
Ta fashe da kuka tana cewa "Ka zo ga Mabaruka nan a
daki ta rufe kanta tana ta buge-buge, wai sai ta kashe
66
.
WAYE ANGON?
kanta."
arMaryam Ja'afar
Ya kara rudewa, jikinsa ya hau rawa ya ce "A wane
gidan?" Ta ce, "A nan gidanku." Bai sake cewa komai ba ya
tura wayar aljihu ba tare da ya ko katse kiran ba saboda
tsananin firgita da tashin hankali, da gudu ya shige mota ya
jata a guje.
Mintuna kadan suka kai shi gidan, Momy ta fito kenan
taga jan motarsa. Tabbas tasan ba lafiya ba, hankalinta ya
kara tashi. Cewa ta ke "Oh ni! Me ke faruwa kuma ina zan
yi?" Duk ta birkice ta rasa me zata yi.
Shi kuwa Imran ya isa gidan a gaggauce ya shige falon.
Yana shiga ya kwankwasa mata kofar tare da cewa "Bude
دو mana Mabaruka ni ne."
Tana jin muryarsa, sai ta kara wuta a kan abin da take yi.
Ya sake cewa, "In dai ni ke şa ki wannan tashin hankalin
zan kyale ki Mabaruka, ba na son kiyi asarar ranki, ki yiwa
mahaifiyarki ke kadai ke gareta, ki tausaya mata ko don ita
kadai ki bari kada ki kashe kanki.
Ba zan zama masifa a rayuwarki ba, amman ki bude zan
miki duk abin da ki ke so.
Iya nacin ya yi mata amman ta ki sauraronsa, ji yake
67
E
i
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kamar ya fasa bangon ya shiga ya daukota, har cikin ransa
yake jin kukanta wanda da jinsa ta gaji da yinsa, ga fashefashen abubuwa da take idan ta fasa wani abu har sai ya
razana, ji yake kamar a jikinta take fasawa.
Ya ci gaba da dukan kofar yana mata magiya, ya damu
kwarai duk a kansa take wannan haukan, har take kokarin
rasa ranta, meye laifinsa? Meye illarsa? Ko dai yana da
wani abu ne na aibu wanda ba kowa ke gani ba sai ita?
Rafi'atu ma bata gaza ba, wajan bata hakuri da lallashi.
Tun suna jin motsinta da gunjin kukan har suka ji dif!
Hankalinsa ya kara tashi, tsoro ya bayyana a tare da shi,
zufa ta keto masa, ya hau tambayar kansa meye ma'anar
shirun da tayi?
Tsawon awa kenan ana abu guda.
Kai da yaga abin ya wuce misali, ficewa ya yi da sauri
ya nemo masu kwance kofa. Nan da nan kuwa aka kwance
kofar, har yana buge mai aikin ya fada dakin a rikice.
Kwance ya ganta saman tayils, gabansa ya yanke ya
fadi. Ya hau jijjigata. Can ta bude ido a wahalce, idanun
nata sun rine sun kankance saboda kuka, muryarta ta dishe
ta kasa tsayar da idonta.
68
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
a
A rude yake cewa, "Lafiya Mabaruka menene?” Ba ta
iya ba shi amsa ba, yum! yum! haka take jin kanta wani iri.
Rafi'atu ta fashe da kuka tayi tsaye ta kasa karasawa
kusa da ita, tsoronta kar dai wani abu taci ko ta sha.
Shi ma haka ne a ransa, a tsorace ya ce "Me ki ka ci
Mabaruka?" Ta kasa ba shi amsa bata san ma da wa take
magana ba.
Ya sake nanatawa