Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
1 / 10
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels HNL WAYE ANGON Maryam Jafar Kađuna HAUSABOOK.COM WAYEANGON? 2 Na Maryam Ja'afar Kaduna Mrs: Khabeer Abdullahi WAYE ANGON? ne yabaku girman. M. umma Muhammad M. khadija Musa Rimi M. rukayya madani Maryam Ja'afar Ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi yaja kwana Ameen. NIMA GA NAWA ANGON In har mabaruka tasan angonta ta kuma rike gam ni me zai hana bazan rike nawa ba, ya zama dole inyi Babbar gaisuwa da jinjina in bada girman ga wanda Allah ya ba. dukkan alkhairin duniya da na lahira Allah ya baka Angona Muhammad Kabeer Abdullahi, Ubangiji Allah ya bar kauna Ameen. INA YA “YANA? Umar, Muhammad, Aisha, sahalu, khairat da yusra. Allah ya rayaku bisa tafarkin gaskiya ya albarkaci rayuwar ku da sauran yayan musulmai Ameen. BABBAR KAWA Hauwa'u Muhammad godiyata ba adadi kin zama yar uwa Allah ya kara dankon zumunci ya yara mana su husna Ameen. 4 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar 1 WATA JINJINAR Dole ne in yi godiya da jinjina ga yar uwa abokiyar aiki bisa kokarinki gareni da soyayya bazan manta ba ubangiji Allah ya cika mana burinmu Ameen Humaira khalil Adam marubuciyar INA SIRRIN YAKE? ALKALAMAWA (gidan fasaha) Ban cire kowa ba gaisuwa ta musamman da jinjina gareku marubutanmu bisa kokarinku na dabbaka harshen hausa da gyaran zamantakewa. Allah yaja nisan kwana ya daukaka aikalummanku Ameen "YAN UWA DA DANGI Ga gaisuwata gareku na miko da fatan alkhairi jerin sunayenku bazai jeru ba ana idan ko harnace sai haka to tabbas zan cika littafin wani mabai samu shigaba ga adduar zumunci nan soyayya da kaunar juna Allah ya karo mana ya hade kawunanmu ya dorar da zumunci me dorewa Allahumma Ameen. 5 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar wana daya ya rage a koma kotu, don haka a nan Kta kwana daga nan suka wuce kotun ita da Maman Rafi'ar sai Rafi'atun. MUJE ZUWA MU JI ME ZAI FARU A KOTUN? WAYEANGON? WA KOTU ZATABAMATA? A KOTU Bayan an gama sauraron Karar wasu an kammala, sannan aka gabatar da tasu. Alkali ya bukaci ganin amaryar wacce kanta ake wannan hargitsin, ina ma amaryar take? Jikinta ya hau rawa zuciyarta ta karye, a marairaice ta dubi Rafi'atu dake gefenta ta ce, "Ina jin tsoro Rafi'a ba zan iya fita ba in tsaya gaban dubban mutanennan duk a tsira min ido wallahi ina jin kunya Rafi'a. Ta riko hannunta ta ce "Ki nutsu Mabaruka, ki cire komai a ranki ki dauka ba kowa a nan ke kadai ce. Ki fita ki bayyana gaskiya da abin da ke ranki, kar ki 6oyewa kotu komai don za tai miki adalci ta ba ki mijinki da ya fi dacewa da ke, kilan ma kiga Sulaiman za a ba. Amman idan ki ka yi sanya ki ka tsaya kunya ko tsoro zà ki rasa shi, ki rayuwa da makiyinki. Fadin hakanne yasa ta 6 WAYE ANGON? samu kwarin gwiwa, zuciyarta tayi kwari. Maryam Ja'afar Don haka bata jin komai ta mike ta tunkari inda ake tsayawa, Alkali ya dubeta ya ce, "Ko za ki gaya mana sunanki da ko waceсе?" Ta ce, "Eh! Sunana Mabaruka, kuma ni ce amaryar da ake rigima a kanta. Na taso karkashin kulawar iyayena guda biyu, Mamana da Babana, a gun matar Babana na taso amman na kan je gun Mamana. Nayi karatun Firamare da Sakandire masu kyau da tsada, duk daukar nauyin mijin Mamana, wato Baban su Imran har zuwa yanzu da nake karatuna a Jami'a, ina kuma shekarar karshe a karatuna. Na taso cikin gata da jin dadi, komai na rayuwa ina samunshi ba na rasa komai. Na kan je gidan Mamana nayi kwana biyu ko uku, haka gidan Babana har zuwa yau da nake kusa da gamawa Babana bai taba ba ni ko Naira goma ba in sayi fensir. Duk wani abu na dawainiyar karatuna ba ya yi, duk idan na bukaci wani abu gun sa sai ya kama fada, in bar shi ya ji da dawainiyar gabansa na kannena, dangane da ciyarwarsu 7 WAYE ANGON? me zan ji da karatu ni da nake mace aure zan yi. Maryam Ja'afar Haka dinki ko silifas, ko da da sallah ne yanda uba yake dagewa kan kayan sallar 'ya'yansa, to ban da Babana komai sai Mamana ita ke min ko mijinta Baban Imran, hakan yasa nafi zama a gidansu Imran din. Ya yi karatunsa a Ingila na Pilot tun kafin ya tafi muka shaku da juna, Imran ya koya min cin dadi da 'yan tandetande duk in da yasan idan ya kai ni zan ji dadi, to zai yi kokarin kai ni,ga sayen abubuwa na yayi ko naci ko na ado. Lokacin da zai tafi karatunsa nasha ciwo bayan tafiyarsa ban saba da rashinsa ba, zan wuni 'ba kuzari in wuni a kasalance, ba zan ci komai ba duk sanda na dauko abinci zan ci na kan tuno shi, hakan yasa sai in ta kuka saboda dashi muke cin abinci plate dinmu daya cokalinmu daya. Na koyi abubuwa sosai gun sa dangane da karatuna, boko da Islamiyya, shakuwa sosai mu kayi dashi. Gefe ita ma Sharifa 'yar uwa ce kawa ce aminiya ce gare ni, duk idan tazo muna tare ina jin dadi idan Sharifa tazo sai in rasa inda zansa raina don dadi su sani tsakiya kowa ya na bani tashi kulawar, 8 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Shi kuma Sulaiman tashin farko yakan zo gidanmu kusan kullum yana yawan tsokanata da dan min tsaraba, da dama yakan kira ni da matas! Daga haka abin ya faru, ban san ya aka yi ba na fara son shi ba har muka yi nisa. Gefe kuma muna tare da Imran amman har lokacin ban san me yake nufi da ni ba. Koda Babanmu ya ji magana ta da Sulaiman ya yi farin ciki da murna yaiwa Sulaiman din albishir da ya bada ni gare shi ko bayan ransa. Inna ma tayi murna matuka da hakan ko don ta sanni na kan yawaita mata alkhairi in dai ina gidan, musamman idan tana wa Babana tijara kan kudi nakan biyata fiye da yanda yaci hakan yana mata dadi sosai, shi yasa muke shiri da ita. Ni kuma abin da take ma Babana bana jin dadinsa hakan yasa na ke maganinta da kudi. Wata rana Imran ya dawo ofis, kamar yanda na saba da zaran ya dawo zan taro shi in raka shi har daki tamkar wani mijina in ya cire riga in rike masa muna yi muna hira muna dariya. Ranar ma haka ta kasance ya dube ni cikin fara'a ya ce, 9 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar "Lallai kina ji da ni, sai ka ce wani mijinki irin na dawo dinnan ko?"Ya fada yana kallona yana dariya. Ban fahimce shi ba nima nayi dariyar nace manta da wannan maganar yau ne zamu je wajennan da ka сe ko?" Ya zasro ido ya ce "Ina?" Na turo baki cikin shagwaba na ce, "Kana sane fa tun yaushe muka yi maganar nan don Allah?" Ganin kamar zan yi kuka yasa ya ce, "Is ok, naji na sani tsokanarki nake, zamu je anjima. Nayi dariya tare da cewa, "Thanks my dear bro." Ya yi murmushi kawai yana kallona cike da sha'awar yanayi na gefe kuma yana wani tunanin. Na katse shi "Ka san me?" Ya bazo kunnuwa ya ce, "A'a menene?" Nayi dariya na ce "Ba ka tambaye ni me na girka maka ba?" Ya ce, "Sorry, na tambaya yanzu me ki ka girkawa tumbin yayan naki?" Nayi dariya tare da make kafada na ce "Um'um idonka zai baka labari, amman nasna za ka yi farin ciki." Ya ce, "Na sani duk abin da za ki, za ki yi don farin י cikina, zai sa ni farin ciki am sure. 10 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Tare muka ci abincin yana santi, a kullum yakan tambaye ni wai ina na koyo girke-girke, shi wallahi bai taba cin abinci irin nawa ba. Na kan ce abin sirri ne amman zan fada maka. A kan hanya muna mota shi ke tuki, ina gefe dukkanmu mun sha kwalliya, labari muke amman naga ya yi shiru. Na dube shi na ce, "Ya Imran!" Ya nisa tare da kallona na ce "Lafiya, me ke damunka?" Ya kalle ni da kyau ya ce, "Kina son ki sani?” Na daga kai tsaye ya ce "Aure nake son yi Mabaruka." Na fito da idanu da bude baki cikin murna na ce "Aure Ya Imran?" Ya ce, "Sosai, kin yi mamaki?" Nayi dariya na ce "Dole abin mamaki ne mana, nifa ban taba jin kayi maganar mace ba bare aure, a tunanina ko ma ba za kayi auren ba a rayuwarka." Ya zaro ido ya ce, "So ki ke in mutu kenan? Ina! Ba zan iya ba." Nayi dariya ina kallonsa cikin mamaki na ce, "Don ba ka yi aure ba sai ka mutu?" Ya ce, "Of course! Son da nake wa yarinyar zai iya hallakar da ni." Na kalle shi na ce, "Wannan wace 'yar baiwar ce ka ke so har haka daidai da ranka?" 11 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ya yi dariya sosai tare da dukan sitiyarin motar ya ce, "Kina son sanin wacece?" Na ce, "Eh!" Ya ce, "Kin santa ai." Na ce, "Na santa! Wacece?" Ya kalle ni a nutse kamar ba zai fada ba sai dai naji kamar daga sama, ya ce "Kе се mana." Na kalle shi da sauri na ce "Ni kuma big bro?" Ya ce, "Ke Mabaruka." Yanayina ya sauya na ce "Please! Ya Imran ka daina tsokanata, ka san ba ma haka da kai, ka faďa min kawai wacece?" Na karasa ina dariya fuskarsa ba wasa ya dube ni ya ce, "Mabaruka!"Na kalle shi tare da amsawa. "Na'am!" Ya ce "Ba wasa nake miki ba, tunda kin ga ban taba miki irin wannan wasan ba." "Wallahi da gaske nake, ina sonki tun ba yau ba, tun kina Sakandire aji daya (SS1), kusan shekara shida kenan, kuma wallahi aurenki zan yi serious (da gaske)." Fuskata ta sauya sosai, na ce “Ka bari Ya Imran, bana son wasa fa." Ya ce, "Na fada miki da gaske nake, kina maida magana baya. Cikin week din nan zan kai maganar nan gun su 12 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Daddy, ba wani bata lokaci za a yi ba in aure ki in kai ki gidana. Kin ga shi kenan hankalinki kwance kin san wa za ki aura, Imran din ki ne da ki ke tattali, tun-tuni sai ki zarce na tabbata hakan ba zai miki wuya ba tunda kin saba." Tun da ya fadi maganar nan bakina ya kulle, jikina ya mace, na rasa me ke min dadi. Har muka je muka dawo ba ni da kuzari. Na zo kwanciya tunanika suka rufe ni, wai me hakan ke nufi? Shin anya Imran yasan so ma kuwa? Kawai don yaga muna dan raha da wasa sai ya ce so wai yana sona? Kai! Ina bai san so ba, ni dai nasan ina son Sulaiman don haka gwara tun wuri ta taka masa burki kar abun ya yi nisa a ransa bare su Daddy su sani. Ban yi tunanin komai ba na tunkari dakinsa ya fara shirin kwanciya ya ganni. Na wuce shi inda ya bude min kofar na zauna kujerar da ke dakin na zauna a sanyaye. Ya dawo ya zauna kan gado yana facing dina ya ce cikin damuwa my dear me ya faru? Kalmar ba ta min zafi saboda haka muke kiran junanmu 13 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar amman wannan lokacin sai naji zafinta sam bata dace ba, ta fito daga bakinsa ba na ce a tausashe. "Ya Imran!" Ya ce, "Na'am, menene?" Na ce, "Magana nazo muyi da kai."Ya ce, "Ok, ina jin ki menene?" Na daga kai na kalle shi ganin yanda ya maida hankalinsa gabadaya gare ni yana saurare. "Maganar da ka min dazu ce nake son mu tattauna." Ya ce, "Ok." Na ce "Maganar gaskiya Ya Imran ba ka fahimci so ba, ko don baka taba yin shi ba, amman wallahi ba sona ka ke ba kawai dai mun shaku ne, nima haka ba na sonka." Maganar ta ba shi mamaki, amman ya ce "Mabaruka kenan! Ke yarinya ce, a tsawon zamanmu da ke ya kamata ki fahimta ko don wasu abubuwa da nake miki, amman da yake yarinya ce ke kin gaza fahimta, har na fito yau na fada miki. Tabbas ina sonki, kuma kema kina sona." Na dago ina kallonshi na ce, "A'a Ya Imran ba haka ba ne, kar maganar nan tayi tsawo mu barta a nan, ka cire maganar so tsakaninmu, don ba zai kasance ba, bana jin sonka a raina, wallahi akwai wanda nake so, don Allah ka fahimce ni." Idanunsa suka kaďa jajir, ni nasan bacin rai ne amman 14 S WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ya dake ya ce "A'a Mabaruka, to ba wani wanda za ki so sai ni, in ma ba ki so to ki kokarin sa shi a ranki, don jin dadinmu ni da ke, wallahi da gaske nake ni dai ina sonki." Na mike tsaye na ce, "Don Allah Ya Imran ka bar tsokanata, wallahi akwai wanda nake so." Shi ma ya mike yana cewa "Ba na tsokanarki ni dai ina sonki zan aure ki kema za ki gane hakan a hankali, zan koya miki." Wucewa nayi ina cewa, "Ni dai na fada maka ka daina daukar abin wasa, wallahi da gaske nake." Ya biyo ni zai rufe kofar yana cewa, "Ni ma ba da wasa nake ba, ina sonki ki sa haka a ranki." Ban iya cewa komai ba na juya nayi wucewata zuwa dakina, ya rufe kofarsa ya koma ya kwanta hankalinsa kwance., Tun daga wannan ranar alakarmu ta canza da shi, muka rage walwalar da muke da shi duk da yanda yake kokarin ja na. Abu kamar wasa ganin yanda ya dage yana sona. Hakan yasa na dage nima ina nuna masa ba haka ba ne ni ba na sonsa, bai gane ba, har na fara nuna masa tsantsar tşanarsa, kamar yanda nake jinta a raina, har kawo yau ba 15 WAYE ANGON? abin da ya canja. Maryam Ja'afar Alakata da shi ta roshe haka, alakata da Sharifa bayan tazo bikin, yayin da soyayyarmu da Sulaiman take karuwa tsakaninmu mahaifiyata ta dage a kan lallai sai na aure shi. Yayin da shi ma Babana ya dage lallai sai na auri Sulaiman, saboda shi ya ba aurena. A tunanina jahilci ne ke dawainiya da su har suke son aura min maza biyu da kafiyarsu, sam ba sa jituwa motsi kadan zai zagi Mamana, duk bakin cikinsa ta bar gidansa ta koma gidan wani Alhaji tana more rayuwarta me dadi da nishadi ta bar shi a wahala da talauci. Ita kuma take jin haushinsa a kan wuyar da tasha gidansa da wulakancin da ya mata, kamar yanda take fada min kullum, amman bata taba fada min ya aka yi suka rabu ba, amman takan ce ta sha wuya gidansa. Nayi iya bakin kokarina na fahimtar da su a kan abin da suke kokarin yi ba kyau, ba a taba yi ba, sam ba su saurarona kowa ya dage a kan burin shi a ganinshi shi ke da gaskiya. Hakan yasa nayi yunkurin kai su kara kotu, tunda ba su da magabatan da za su musu fada, kawata Rafi'a ita ta hana 16 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ni sannan naso na gudu shima nan ta hana ni ta tsare ni a gidansu. Yayin da su kuma suna can kowa na kokarinsa suka kuma sa ranar auren duk rana daya. Har dai suka daura min aure da maza biyu har zuwa yanzu." Ta kalli Alkalin ta ce, "Wannan shi ne cikakken ko ni wacece da yanda abin ya faru gare ni." Nan fa kotu ta hau kace-nace. Bayan an nutsu Alkali ya fito da angwayen, Sulaiman da Imran, kowa yai ma kotu bayanin wanda ya daura mai aure, kuma ya bada sadaki. Duk tambayoyin da ya kamata kotu tayi musu tayi ta gamsu da duk bayanansu. Ta bukaci a bata kwana biyu kan ta yanke hukunci, don haka a haka aka tashi kotun. Wannan karon ma gidan Momy ta koma, a mota ta ci gaba da yiwa Rafi'a, korafi kamar zata yi kuka. "Wallahi na gaji Rafi'a, na kagara a yi ta ta kare, in san matsayina, na gaji dajelangen nan na kotu." Ta ce, "Haba! Kada ki damu, jibi ne fa kawai. A jibin kai tsaye gidanki za a zarce da ke, magana ta kare ko gidan 17 rו WAYE ANGON? Sulaiman ko gidan Imran." Maryam Ja'afar Idanunta suka fito hankalinta ya tashi, idanunta suka yi rau-rau, ta ce "Ya Allah kada kasa aure tsakanina da Imran, Ya Allah ka sa Sulaiman shi neANGON Ya Allah." A haka suka isa babu kuzari jikinta, ta haye gadonta tayi lamo zuciyarta da sake-sake dankare da zullumi. A nan suka wuni da Rafi'a tana kara kwantar mata da hankali, sai gaf da Magriba sannan Rafi'ar ta tafi gida. Bayan ta rakata ta dawo, daidai kofar falo suka ci karo da Imran ya tare mata kofar yana kallonta fuskarsa dauke da fara'a. Tayi kicin-kicin da fuska tamkar bata taba dariya ba, ranta ya baci matuka ta dago tana harararsa, yayin da shi yake dariya shi kansa yasan ya jawa kansa fada ne. Ta ce cikin fushi "Matsa ka bani guri." Ya dage kafada alamar a'a bata saurare shi ba tayi kokarin rabewa ta gefensa ta wuce. Nan ma ya tare, ta dawo ta dayan gefen nan ma ya fake. Tazo iya wuya, ji take kamar ta shake shi ta huta gabadaya. Tsawon mintoci suna haka, ganin da gaske yake ba zai matsa ba ga wani tukuki da take ji a ranta tsayawa kusa da 18 ン WAYE ANGON? shi da tayi, kawai ta juya baya abinta. Ya bi ta da kallon ina zata je. Maryam Ja'afar farGefe ta koma ta zauna a harabar gidan tana 'yan harareharare da fushi, bai daddara ba ya kara binta can din. Tsugunnawa ya yi gabanta har suna jin numfashin junansu, kamshinsu ya hade da juna ta dago tana kallonsa cikin tsananin tsanarsa shi ma ita yake kallo cikin yanayi na kaunarta ya ce da ita. "Wai menene haka Mabaruka? Guduna ki ke don ba kya sona ko?" Kai tsaye ta ce, "Eh, amman ka kasa gane hakan bare ka kyale ni na huta, zuciyata ta huta da matsananciyar tsanar da take maka." Ya yi shiru yana kallonta zuciyarsa tana masa ba dadi, ya ce "To me yasa? Meye abuna me na rasa da har zuwa yanzu na gaza zama masoyinki. Kullum kina furta min kiyayya, ina ganinta a idonki me yasa Mabaruka?" Idanunta suka kada kamar zata yi kuka ta ce, "Haka nan babu wani dalili Allah ne yasa min haka ba daga ni ba ne amman ka ki fahimtar haka ka kyale ni don ba mu dace da 19 1 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar juna ba sam bare zamantakewar aure ta yiwu tsakaninmu." Zuciyarsa ta kara yin daci bakinsa ya yi nauyi da kyar ya iya cewa "Mabaruka, Allah ya jarabce ni da matsanancin sonki ban san ya zan misalta miki ba bare ki tausaya min yanda zuciyarki take miki ba dadi da . azalzalarki a kan kiyayyata. Haka nima tawa take azalzalata da sonki, a kullum kara min sonki ake, wallahi Mabaruka ba zan iya rayuwa idan ba ke ba, bare na iya hakuri da ke ta harararshi tamkar ta kife shi da mari, sannan ta ce "Kana Kara wahalar da kanka ne ka sawa kanka hakuri da dangana, aure tsakanina da kai ba zai taba yiwuwa ba, har abada saboda Allah bai rubuto hakan ba tsakaninmu." Cikin kwarin gwiwa ya ce, "Ni kuma ban taba sawa raina ba, ba zan same ki ba a kullum ganina nake tare da ke muna rayuwar aure tare da 'ya'yanmu cikin farin ciki da walwala. Ta kalle shi da kyau ta ce "Ba za ka taba ganewa ba, zuciyarka na yaudararka da mahaukacin tunaninka, ni dai nasan ba zan aure ka ba, kaje kai ta haukanka." Daga haka ta mike ta wuce cikin gidan da sauri tamkar 20 WAYE ANGON? wacce za a kamo. Maryam Ja'afar Far Ya bita da kallo cikin sha'awar tafiyarta, musamman da take saurin nan sai tai masa kyau a ido matuka, yayi murmushi tare da mikewa ya wuce inda motarsa take yana cewa, "Zan kama ki yarinya." Ya shige abinsa ya fice daga gidan. Da dare wajen karfe tara har ta gota sannan ya dawo. Momy ce a falo, ita kuma Gimbiyar tana dakinta ita ba bacci ba ita ba kuka ba. a Haka zalika ba tunani ba, zuciyarta taki ta barta ta huta saboda zullumi bata san me jibin zata haifar ba, meye cikinta? Farin ciki ko bakin ciki, rayuwarta ko mutuwarta? Ba abin da ke mata dadi tun tsawon ranar bata sa ko kwayar ruwa a bakinta ba bare abinci, haka take. Ko kadan ma bata jin yunwar. Ya zauna cike da gajiya yana fadin wash! Ya cire hula yana sosa kai, Momy ta bishi da kallo tana cewa "Gajiya ko?" Ya ce, "Wallahi amman yunwa tafi yawa." Ta ce, "Ah lallai kam ai ga abinci can a dinning ba ma wanda ya tabа shi tunda aka gama." 21 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ya dubeta yana cewa "Saboda menene ba kowa a gidan, ina Mabaruka?" Ta cě, "Tana cikin daki, tun dazu nake fama da ita taci abinci, ta ki har na gaji na kyaleta, idan ta tantance ta fito ta nema don kanta." Sam baiji dadi ba, jikinsa ya kara mutuwa. Mikewa ya yi yana cewa zan shiga ciki in dan watsa ruwa, ki sa Mabarukar ta kawo min abincin da dan lipton, ta ce, "To." A daki ta samu Mabarukar kwance ta taso ta suka fito. Tana zama kan kujerar ta ce "Kije ki hado abinci a tire da lipton. Ta kalli Momyn fuskarta da fushi ta ce nifa bana jin yunwa. Ta ce, "Na sani daman ba ke nace ki hado kanki ba, kije kiyi abin da na saki." Ta amsa da "To." Sannan ta wuce. Tayo yanda ta sata, ta kawo mata. Ta dube ta ta ce "Kije ki kaiwa Imran dakinsa." Ta kalleta da sauri cikin tsoro ta zumburo baki tamkar zata yi kuka "Ni fa Momy..."Ta katse ta "Ba dole, idan ba za kije ba aje ni sai na kai masa." Tasan gatse ta mata. Ji take tamkar ta fasa ihu wai me 22 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar fara yasa ita aka tsaneta ake son kusantata da wannan makiyin nata? Ko dai ba a san numfashinta. Yanzu abincin ma sai an sa ta ta kai masa bayan a dinning ya saba ci kawai don a fata mata rai. Ta wuce kamar zata yi kuka, idanunta sun taru da kwalla, ta shiga kwankwasa kofar. Ya fito daga wankan daga shi sai short niker yana sane ya ki suturta jikinsa sabanin da da ba zai taba yarda ta same shi a haka ba, yanzu ta zama matarsa, kun ji fa! Ya zo ya bude mata fuskarsa dauke da murmushi, bata ko kallonsa bare tasan ya yake ta zunguro masa tiren tana kumburi ta ce, "Gashi ya yi tsayen yana kallonta ya ce "Kije ki aje ciki mana, ai ba lallai sai na karba ba." Ranta ya kara 6aci yana raina mata wayau. Ina laifin da ta kawo masa ma yasa hannu ya karba ba zai yi ba, sai ita ta karasa masa da shi bai ma ga kokarinta ba? Don haka taji ba za ta iya ba. Tsugunnawa tayi tana kokarin dire masa a nan bakin kofar, kafin ta aje ya ce, "Wallahi ki ka aje shi a nan ba zan dauka ba, a nan zan bar shi har sai wuce ta turoki ki kawo tazo ta gani inda ki ka aje na gwammace na kwanta ban ci 23 WAYE ANGON? komai ba." Maryam Ja'afar Kwallar da ta taru a idonta ta sauko, tasa hannu ta goge ta riga ta barwa kanta ba a sonta, so ake kawai ta mutu ko ta ina mużguna mata ake ana cutarta. Ba ta ce komai ba ta mike da abincin bata ko kalle shi ba, ta rabe ta gabansa ta wuce cikin dakin. Ya yi dariya yana kallonta gefe kuma ya ji tausayinta, amman duk da haka bai

Chapter 1 of 10