saboda
ba baki sai hawaye dake zubowa saboda takaicinta tayi ta
kasa kwatar kanta saida yaga dama badon ya gajiba ya
saketa shima din saida ya tara miyanshi. Kan ya dau ke
bakinsa ya tofa mata abaki ya kuma denne hancinta kamar
yanda ake wa yara in za'a basu magani ba shiri suke
hadewa. Itama hakace ta faru da ita ba shiri tahade saboda
ko kowa da numfashinta yake tas ta hadiye. Sai daya
tabbatar ta hade sannan ya dagata yana dariya yace see
aikin namiji kenan ba kuma kowanne zai iya haka ba.
Kaki ta hau dan san kakalo amai tanayi tana kuka
sabo mai sauti tamkar yayayya har yatsa ta dinga sawa dan
ta ameyo miyansa. Rike hannunta yayi cak yana kallonta
yace kada ki fara wallahi. Idan ba haka ba zaki wahalar da
kanki ne dan in kin amayo shi sai kin kuma shan wani
wanda ma yafi wannan yawa. Ta dago tana kallonshi da
jajayen idanta wadanda suka kankance saboda kuka.
137
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Bakinta kuma yana zubar de yawu ta saki bakin kamar
shanyayyan mutannen nan da basa iya rike miyau duk dan
saboda miyansa ya shiga bakinta yasa ta kasa hade
miyannata ta kalleshi da kyau tace Allah ya isa mugu dan
iska wallahi sai Allah ya saka min.
Ya tsugunna gabanta yana dariya yace me mukayi ma
tun yanzun kin fara kai karata wajen ubangiji ki bari in mun
kasance tare dake mana sannan. naga shin Allah zai saka
miki, sannan ke kika fara kika watsa min miyau a fuska.
Kika kuma min gadara akan me zan iya me zanyi hakan
yasa na nuna miki abinda zan iya fiye ma da haka zan iya
zaki kuma gani hakan yasani firinciki matuka.
Mikewa tayi daf da nufin shiga bayi tajecan tayi kale-kalen
amanta. Shima mikewa yayi ya tare gabanta tare da cewa
ina zakije? Bata bashin amsa ba. Ta koma gefansa
zatawuce ya sake tare wurin ta kama daya gefan nanma ya
tare tadago ta kalleshi cikin gajiyawa tace ka matsa ka bani
guri yace naki bigeni kiwuce batace komaiba ta sake yin
gefe zata wuce nan ma yabi ta tare.
Cikin masifa tadago tana wallah zan maka rashin
kunyar da har ka mutu bazaka manta ba. Yace ok yi mana
138
1
WAYE ANGON?
ina jiranki.
Maryam Ja'afar
Sun dade a haka ta kuma kasa wucewa din duk in da tayi
nan zai tare, Tayi amman ta kasa, Karshe dai kuka ta fasa
masa tana rokansa ya bata wuri bazata iya jure miyansa
abakinta ba. Ya riko hannunta yana dariya yace to meyasa
ki kukan dan yawun mijinki na bakinki sai ki damu tana
kallansa tace dan san Annabi kadaina tabani wallahi bana
so. Taci gaba da kukan yace is ok is ok bana san kukannan
pls, share hawayenki sai in baki hanya.
Da sauri ta share don ya matsa din hannunta yaja ya
zaunar da ita yana kallonta yace Meyassa kike kyamata
mabaruke alhalin ni mijinki ne yanzu bazaki iya shan
yawonaba? A marairaice tace saboda bana sonka ina
kyamar duk abinda zai fito daga gareka. Kai wallahi zama
ma da kake kusa dani ina cutuwa na kanji kunci da damuwa
ya lullubeni hakanan saina rasa sukuni da walwala komai
ya cunkushe min ba abinda ke min dadi maganar da nake da
kai ma wallahi daurewa nake amman kunci ne azuciyata
bana san hakan. balle har na lya hada yawunka wallahi
bazaniyaba. Don Allah ka kyaleni kabarni na huta? Ta hada
hannu wa tana rokonsa wasu sabbin hawaye na zubowa ya
139
WA
B
sl
Si
n
t
1
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kalleta a tsanake yace to amman kinsan ni mijinki ne dole
in zauna tare dake dole kiyi Magana dani bare azo ga mu
amalar aure kinsan haka dole ne. ta kalleshi da kyau tace
amman kana ganin idan ka min haka ka min adalci ka
kyauta min kenan baka ganin cutar ta min yawa dame
kakeso naji? Yace mabaruka ba cutarki nayiba sanki nake
fa kuma tunda an daura aure ai kinsan dole hakan zai
kasance ko zami yi ta kallonjuna ne. tace asanyaye amman
kasan niba dawwama zanyi da kai ba tafiya zanyi wani
gidan meyasa to zaka kusance ni alhalin ba samu na zakayi
gabadayaba indai har da gaske kake zaka sawwake min
nanda wata uku. Ya kalleta a nutse sannan yace kina nafin
na aureki ne kodai don in ganki agidan har zuwa wannan
lokacin batare da wani abu ya kasance tsakanimmuba ke
bazaki min adalici ba ki tausaya min tunda har nina miki?
Ta kalleshi tace bazan iya ba wallahi bazan iyaba. Inajin
kamar zan mutu idan har ka tilastamin yin hakan wallahi
numfashina zai dauke.
Abin ya soma bashi haushi matuka wannan maganar
banzace don ya kasance da ita a matsayin matarsa sai ta
mutu wannan wace irin tsana ce haka? Amman duk da haka
140
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Σ
zai jarabata ya gani don haka yace ba abinda zai faru dake
zaki samu nutsuwa da hakan duk damuwarki da bacin ranki
zasu tafi. Ya fada sanda ya cire dankwalinta ya wurgar ta
tsorata ainun jikinta ya fara rawa ya kara matsowa kusa da
ita ya jawota zif din ri garta taji ya zuge bayan ya bude
gabadaya saboda har kasa ya dirishi.
Ta rikice ainun ya fara yawo da hannusa duk illahirin
jikinta. Ta runtse ido gam tana jin wata masifar kunci aranta
jikinta na rawa ganin ya fara nisa yasa ta dubeshi da
rikitatun idanunta acikin tsawa tace ka janjanye hannunka
daga jikina Baima san me takeba inma daji baya tunanin zai
iyabata amsa ta sake naąnata masa ganin zata bashi matsala
yasa ya tarata tsakiyar gadon ya kwantar da ita shi kuma
yana kwance kan jikinta bayan ya kashe hasken. Bala inta
ya karu da masifa ta hau dakansa ta ko ina tana ihu tamkar
wacce zai wa fyade maganinta yayi sai ya hade bakinsa da
nata saidai gunjida take da halbe halbe. An dade ahaka iya
abinda zataji taji amman bata ci nasarar tureshi ba.
Zuciyarta tana jinta tamkar zata fashe saboda takaici da
bakinciki.
Tuna takalminta masu kwaras kwaras na gefen gado
141
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
tunda aka shigo da ita suna karkashin gado da haka ta wajau
da hikima ta tura hannunta ta dauka daya batayi tunanin
komaiba. Ta dage iya karfinta ta kai masa duka a kai a
jejjere har so biyu.
Ba shiri cikin tsananin azabar radadi da zafi ya saketa
yamike dafe da kai yana juyi a dakin dake karshe ya
durkushe agun dafe da kai hankalinsa ya gushe ita kuma
tana kwancan tamkar wacce aka dasata gun hawaye na
zarya. Ta mike zaune tana gunjin kuka. Ko kallansa batayi
ba ta shige toilate zaune tayi dabas a bandakin ta saka kuka
mekara bayan ta tabbatar tasa wa bayin key.
Bakinciki takaici kunci suka dameta wallahi tayi bakin
cikin da har ya tabbata ya hadata da jikinsa bayan yasa
mata miyanshi. Tayi Allah ya isa ya a kirga tacigaba da
kakolo aman tana kuka har saida ta amayo duk abinda taci
sannan ta hakura badan ta yadda harda yawun ta amayar ba,
ta dinga wanke bakin tamkar zata karar da duk ruwan
bayin duk ganinta bata wanke kazantar bakinsa ba daya
goggo ga mata.
Taci kuka iya karfinta karshe dai ta bige da wanka dan
wanke dattin jikinsa à ganinta. Shikuma yanacan dafe da
142
:
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kai yana juye juje tsawon wasu lokuta sannan ya fara
samun sauki yaji yadawo hayyacinsa da kyar yamike
saboda ji yake tamkar kansa zai fado ya shiga juye juyen
ina take bai gantaba ya lelleka ko ina. Sai a bandakin yaji yo
motsinta ya samu nutsuwa sannan. Yadan daga murya yace
kiyi hakuri daman kin fada nine nakiji zan kiyaye ki daga
haka ya juya yana cewa saida safe. Dakinshi ya shiga kan
gado ya fada Takaicinsa ya karu a yau yakara tabbatarwa
kansa mabaruka bata sansa tunda har tayi yunkurin daukar
ransa. Babu abinda zaiyi taso shi dole ne yahakura da ita
yasawa kansa hakuri da salama ba tasa bace zuciyarta ba'a
gunsa take ba hakuri da ita shi ya zama dole. Amman ta
yaya zai iya hakuri da ita yana fa sonta? Ya zaiyi da ransa ya
zaiyi da zuciyarsa yana jin tamkar nunfashinsa zai dauke
idan har bat-tare dashi ba idanko har ya ralu da ita tabbas
mutuwa zaiyi. Kansa ya matsa masa da rarrae ya mike ya
nufi drower dan samun tamakan gaggawa. Duk da tasan ya
fita tayiwa kanta alkawarin bazata fito ba a bayin zata
kwana tuned shi mugu ne. don haka anan taji zamanta tana
share hawajen takaici said a y agama ya dansha magunguna
sannan ya kuna ya kwanta da ruki har idacin kan dummm
143
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
yakeji juyi ya dinga yi hawaye na zubowa na tausayin
kansa a wannan daren yaiwa kansa alkawarin har lokacin
da ya jiba sawake mata bizai sake nemanta ba a matsayin
matarsa tundahar bataso bazai sake marmarin hakanba har
abada yahakura da ita. Daire iren wadannan alkawurin
bacci ya kwasheshi me matukar wuya.
Shi yana kan gadinsa yana bacci daciwo jikinsa sam
baya jin dadinsa. Yayinda ita tana bandaki zaune kasan tails
baccin wuya wanda bataso tayi shi agidan bay a kwasleta
daga zaune kawannensu zuciyayinsu basu musu dadi ba
abinda ke musu dadi.
Shin ahaka wannan daren nasu zai kasance darenfarko?
Masu karatu ku min afuwa zan dan dawo baya zamu so
muyi wanehali baban mabarukar yake tun bayan barinsa
kotu sannan shi kanshi sakishi sakiman zamu so muji wane
hali yake.
Tun lokacin da alkali yagama yanke huknci ba ban ya
fice daga kotun zuwa gida. Isarsa kenan sai ga inna ta iso
yayi zaune tsakar gida yayishirun bawai yaji zafi sosaiba
amman inda ace anbawa sulaiman ne da yafi farinciki don
haka damuwarsa ba wata bace.
144
.
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ta rife kugu tare da tsayawa saman kansa tace to kazoo
ka zauna me kake nufi? Ya dago yana kallonta yace name
kenan? Tace au bakasan ma me nake nufi ba ko? Yaja tsaki
tare da cewa ki tayi ni nasan me kike nufi ya dauke kai cikin
gajiyawa da'ita.
Tace to maganar kotu bazakayi wani kokari ba na daga
kara ba don ni wallahi ban yardaba an cikiwa alkali kudi ya
yanke shari'a yanda yakeso amman kowa yasani kanina ke
da mata amman antake gaskiya anba wani wallahi mallam
ana guje maka kada mabaruka tayi zaman zina. Ya dabeta
da kyau yace kei binta bana san jaje jajen jifa'i naki ke
kullum bakinki båya furta alkhairi sai sharri sannan da kike
cewa in daga kara in kai ina san nan da wani kudin ban
dagata ke nifa na karaya shari'a da masu kudi yana da wuya
bazan iya ba ni ka kace kullum ina zarya kafa duk taji
kaushi yanda akeji wannan haka zaayi idan na yi kamar
yanda kikace zuwa za'ai a sake akalin dan haka bazan
iyaba. Taje shi Allah ya zaba mata Allah sa alkhairi ya basu
zaman lafiya shikuma sulaimanun yayi hakari ya nemi
wata ba matarsa bace shikenan Magana ta kare.
Cikin fada tace iyye! Hake kace ko. Daman na dade ina
145
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
zarginka bason aurennan kake da sulaiman tinda saboda
talakane kafison kaba me kudi. Ina lura da kai bawani
bibiyar sahun da kayi idanka yana a kwadayi ranshi ya baci
sosai ya mike ya nunata da hannu yace Binta! Binta ina
hanaki baka ji bakisan me zaki fadaba. Wallahi kada ki
cikani kuma kwadayin ne nefiki ne inda yarkice na tabbata
wallahi bazaki bata ga talakaba ko da yakike da talakan
saboda shegen kwadayinki. Sai ni nana yi kokari wajen
ganin sulaiman din shi ya aureta duk saboda ke amman
baki ganiba to kije kiyi abinda zakiyi nabada ita saboda
kudin sai me ai "ya ta ce ke ina taki yar? Aifa ta kara hawa ta
dinga huci wallahi karya kake. Kai kasanni bani da shegen
son abin duniya sai kai duk abinde yarin-yar nan ta shigo
dashi idanka na kai har rokanta kake kana aikawa gun
uwarta tabaka ya kaleta da sauri cikin mamakin jin
sharrinta ya jinjina kai yace mata shedanu Allah ya shiryaki
binta wallahi kiji tsoron Allah ke zaki iya sa akama mutum
saboda mugun makircinki. Itama ta taso kaine babban
shedan kwada yayye me son abin duniya ba hakuri da
abinda aka samuAllah yasa kada ka dinga mata zarya agida
dan nasan dali linka kenan na bashi don kadinga zagajawa
146
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
anki mu talakawa an bashi waya sani ma kila dan yankan
kaine watarana kanka zai fara yankewa kwadayyace ya
juyo ya kalleta yace ni dake ke kwadajayya ni kwadajayye
kinga anyi daidai zanga dani dake wa zaifi mata zarya
agida sannan in kinji haushi kingara hakura da hukuncin ki
daga karar ke na bar miki ita taso kayi cika baki kamar har
zuciyarka alhalin munafunci ne. ayi dai mugani in tusa zata
hura wuta kuma ni da kai cikin gidannan ka gama samun
hutu kaine Babban makiyina aduniya tunda kaki jini na.
yace eh naji din marar godiyar Allah kar in zamo maso
yinki in dawwama amakiyinki din rashin hutu kuma na
nawa ai ni kullum acikin rashin nutsuwa nake a gidana bani
da sukuni kin fitine ni a gidina taaji haushi sosai tace to abu
me sauki ka sawwake mun mana in tafi gidammu sai in bar fitinarka daman me nake karuwa da kai in banda bakin
talaucinka kowa yana cigaba a rayuwa amman banda kai
haka zaka mutu a talaucinka cikinsa ka taso cikinsa zaka
kare ahaka na sameka amman yau tsawo shekaru ishirin
babu rana daya da naga sauyi da kai gakanan riga kullum
daiya sai shegen datti da warin jiki takalma a huhhuje. Yace
sosai kince haka mana tunda na raboki da gidan ku masu
147
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kudi marassa talauci game da arziki na dauko ki.
Tace koma dai aja ka dauko ni kasan gidammu yafi
gidanka so dubuwallahi.
Yace to shikenan kina iya tafiya gidannaku ki rabuda
talauci ko na huta. Ki hada duka da fitinannun "ya "yanki ki
tafi bazan iya da fitinarku ba rashin me kula dasu yasa tuni
ban sallama maki ba dan ba me iyawahalarsu. Sakarya
kawai me dogan baki silifas din kafarta ta cira sun koma jaa
saboda bakin datti duk sun cinye harda kullin leda in da
hancin ya cire ta jefe shi dasu tana cewa katon banza me
gadan talauci tun iyaye da kakanni. Shima ya ciro na
kafarsa yajefota dashi yana cewa sai kin bar gidinnan yau
me kashin tsiya jarababba. Kai fada dai tsakanninsu ya
kaure da buge buge ya daketa ya zageta itama ta rama "ya
"ya duk sun kewaye su suna dariya idan ya kada innar su ce
ka dubi inna ta fadi. Sai su kyalkyale da dariya. In kuma
baban aka yar saibu kyalkyale da dariya suce shima baba ya
fadi.
Sakarcin fadannasu ya dinga nishadar da "ya "yan suka
dinga tsalle suna tafi karshe suka fita waje suka yo gayyar
yara suna cewa kuzo kuga su Babammu na fada har suna
148
WAYE ANGON?
faduwa.
Maryam Ja'afar
Nan fa yara suka cika gida suna ta tsalle abin na burge
su wani yaron na cewa nima sai nacewa su iya muma suyi
miyi ta kallo har ni fita in kira ku kuma ko? Sukayi tsalle eh
eh wallahi mayi ta jin dadi nan kowané yaro zake shima su
innarsu zasuyi yazo ya kira abokanansa.
Su kuwa basu fasa ba suna yi suna zagin junansu har da
gari karshe dai saidai makota suka shigo rabo duk akabi aka
kwakkwade su wajen rabo. Maza dai su suka iya rabawa
suka janye shi da iyar yana bala'i sai kin bar gidennan
tsinanniya "yar matsiyaata.
Itama ta taso ana rirrike da ita yome zan zauna inyi
gidanka matsiyaci talaka me kashin tsiya duk na kare
agidanka ba cigaba sai shegen faso duk ka yaga min zanin
gado katon banza me tusa cikin dare duk ka kumburamin
ciki daga yau na huta Ahaka dai aka rabasu aka fice dashi
yana ta bala'i sai tabar masa gida kafin ya dawo ta tattara ta
bar masa gida harda "ya "yan duka baya so.
Itama cikin gida tana baka'i har ni zai wulakanta cikin
mutane in ni shegiya ce zan kara zama gidansa me ma zai sa
na nace agidansa. "ya "ya kuma anan na same su dan haka
149
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
nan zan barsu nima banso me zanyi da "ya "yansa.
Akece haba "ya "ya ai basu da laifi dole ko ki tafí dasu
taçe Allah ba inda zanje dasu aishi ya haifar nan da nan
tahau hada kaja-minti biyar hart a fito yaronta nagoye na
jikinta yana shan maama ta cireshi tana cewa zauna nan dan
iska ai nanon da nake bake ba biyana ake ba.
Yaro ya canyara kuka tace kafara kenan shi yazo
yacigaba da baka bazan iyaba. Mutanen nakotan dake
wurin suka zaro ido tare da cewa a haba dai kanki daya yaro
yana yan watanniki cireshi? Bakya fara ba wallahi.
Ta hararesu san ranta tace da daya daga cikinku wacce
ta haifa min shi? Sukace a'a ke kika haifi kayanki tace to
naki na tafi dashi din magulmata kawai sai aje giba a yada.
Suka daddubeta ta taso zaku fice mindaga gida ko sai na
fasa kan daya kinibabbu kawai sirin sirin suka mike suka
fice ba wanda yace komai taja tsaki ta kalli "ya yan" tace ku
kuma don ubanku zaku gane kuranku kokon safe sai ya
gagare ku indai na barku a gidan ubanku marar zuciyar ne
matsiyaci.
Daya yace inna ina zaki je? Tace gidan uba na nima
suka ce zamu biki muma ta zaro musů ido babu wanda
150
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
D
ubana ya Haifa cikinku kuma kuji zamanku a naku gidan
daga haka ta dauki ledar gari yayi zafinta ta wuce fuu fuu
suka biyota suna zamuje inna taci karo da kara ta dauka ta
biyo su da gudu duk wanda ya biyoni sai na fasa masa kai.
Suka koma da guda suna kuka ta yarda karan ta wuce tana
cizgar fada sake sake biyota itama ta biyo su tana karasu
suka gudu suna kuka tamkardai mahaukaciya harta samu
nesarar fita.
A fafar gida suka ci karo dashi zai shigo ta dillah masa
harara shima ya dallo mata tasa. Suka ja tsaki a tare da cewa
can a karata gayyar tsiya ta sake cewa mahaukacin banza
marar zuciya durkusawa yayi zai dauki duwatsu habawa da
gudu ta falla. Shikuma ya dinga jifanta da dawatsun. Ita
kuma ta gudu tana cewa Allah ya isa ka jefi uwarka sahura
me tuwo.
Ya yunkura zai biyota mutane suka rikeshi suna haba ba
girmanka bane kana barin abin kallo dubi yanda mutane ke
kallonku. Sai wurge wurgen idanuwa yake karshe dai ya
denna kai gida taras da yaran yayi sun hada kai suna kuka
ga me shan maman yana ta canyara kuka.
Tsaye yayi ya rike kugu yana kalkasu tare da cewa wato
151
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
wannan matar bata tafidakuba anan ta barku? Sukayi
tsuruu suna kallonsa. Yace harda na gayonma. Amman
wannan matar akwai makira to ni ya take son nayi daku?
Sulaiman kuwa ko daya samu sauki yabi duk ya rikice
yafita hayyacinsa sai surutai yake shi kadai inna ta shigo
dakin tabishi da kallo tanacewa sanbatunne angon
mabaruka? Ya daga kai ya kalleta da jajayen idonsa cikin
takaicin maganarta yace duk wama yaja min inba keba
daman kinmin baki ba ba dani za'a ba alhalin NINE
ANGON haka kawai an ba wani sakarai can. Wallahi sai na
daukaka kara. Taja tsaki tare da zama tana tabe baki tace
sakarai kawai iska na wahalar da me kayan kara baka gaji
da wahalarka. Kaje kaine kaa wahala. Babban abinda ke
damunsa da bashi tsoro idan ya tuna hankalinsa ke tashi
jikinsa ya dinga rawa duk tsikar jikinsa ta mike saboda
kishi. Kar imran ya kusantar masa mata.
Wannan tunanin da yayi yasa ya rike ya fasa ihu tare da
hargagi tamkar wani zaki idanunsasu ka kada jikinsa yah
au karkarwa.
Inna tajabaya tana kaponsa tace o o o o meje haka sai
kace wani kura waa zakaci anan? Sakarai fankan feyau.
152
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Kana nan kana hauka zaka haukatar de kanka abanza badai
baka matar za'ayiba tana can tare da nijinta taama manta da
kai kwanukanta na gefe ya wani juya tareda baro duka
kwanikan suka tarwatse masu jamba sukaji yacigaba da
hargagi idanunsa suka rikide.
Tace to ko zanci ubanka dan banza lalatacce me
shegiyar zuciya da ubanka kwanukan nawa zaka fasa kan
wata shegiyar yirinya "yar mahaukata? Tun kan na haife ka
nake da kwanu kannan gadansu naci gun uwata itama gun
uwarta taci gadonsu. Shine zake min sanadi fitsararre me
zuciyar kare.
Daman hada hanya ake da talake bare masu kudima
hauka suke su dauki "yarsu su baka? Shima uban nata ba
abakin komai yake ba gunsu sunan ya Haifa ne ba wai cin
galaba zaiyi akinsu ba don sunfi karfinshi tunda suna da
kwandala. Shi ko ko tsiya anan ta ganshi ta barshi tun
sanina dashi matalauci ne kuma har yanzu bata canza
zaniba uwarta taci wuya gunsa da halinsa da takaicinsa.
Ahaka zata yarda taba ka auren "yarta ta lalace gunka tana
kallen dan masu dashi danshi. Duk bata lokaçinku ku kayi
da kuke zarya kita haka shima ubanka da talaucinsa ya
153
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
mutu yabarni daku ba wuyar rayuwa da ban shata ban a
talaucine gashi nan har yau bai sakeniba kuma gaka nan
cikinsa riga kwaya guda baka da wacce za'a kalla aso.
Banga ma abinda ta gani baya burgeta harta kwallafa ranta
a gunka tamkar dai ubanka. Wata tsawa yayi tare da cewa
ya'isa zata kara masa takaici ga na abinda ke damunsa
amman tanakara masa zafi.
Tayi shekeke tana kallansa tace to nayi ubana. Kar ka
kai min duka sullutun banza kawai ka gaza kwace mata
kazoo nan kana min hargagi bashi da abincewa don in ya
fada zaka kara masa zafi.
Saminra ta shigo gidan tana yafe dadan gyale tasha
kwalliya irin nasa nayan zamani ana tafe ana taunar
cingum. Ta zauna tana cewa wash na gaji inna tabita da
kallo tace aikin me kikoyi in ba shegen yawo ba. Kara yau
baki dauke be agidan sai gantalin banza da na wofi.
Ta dubeto tace ke dai kin faye tsegumi wallahi duka
yaushe na fita rana daya idan banyi wani abu gidannan ba
sai kiga kamar na shekara banyi ba duk bakya ga nin
kokarina a gidanan ba.
Ta daga hannu zata kai mata duka. In baki min shiru ba
154
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
sai na kwadeki maras kanyar yarinya afada ki fada mikewa
tayi gabadaya ta fice daga dakin tana turo baki. Nafisa na
tsakar gida na shara har tana bangajeta amman ko tsayawa
batayi ba bare ta bata hakuri ta dago tana kallonta tace
amman kina ji kina bige ni ko? Tsaki taja bayan ta juyo ta
shige daki.
Inna dago daki tad ago murya tace to to me kum aka
miki maras hakuri ke dai a kullum sai kince an miki wani
abu yaushe ta bangajeki din "yar gidan marassa hakuri?
Tace a sanyaye ba komai daga haka taci gaba da sharar
ake da taikaici a ranta.
Tace au da kyau kin kyauta wato ina miki Magana shine
kika dago kika harareni kika shareni kika cigaba da sharar
wato ga mahaukaciya tayi tayi ko mirewa tayi daf daga
dugen tazo harkofar dakin ta durkusa cikin ladabi da sanyin
halinta tace kiyi hakuri ban kyautaba zan kiyaye gaba.
Taja tsaki kawai tare da dauke kai sai don kanta ta mike
tacigaba da aikinta innar ta dubeshi tace kai sullutun maza
wadanan tarkacan da kasa aka zo aka cika mana daki dasu
kasa suzo su kwashe tsiyatakunsu.
Ya dago ya dubeta da jagajen idanunsa yace amman
155
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
meyasa samira take shigar dakin alhalin tasan akwai me
dakin tunda akwai kaya.
Ta taso masa cikin bak'i wacece me dakin duk nan bame
dakin gidana ne babu wacce ta mallaki daki a gidannan sai
dai aro. Ita wacce kake maganar tun yausle ta kama gidanta
har kake fadan akwai medaki samira kuwa daki nata ne
tunda asalinsa anan take kwanciya kinibabban aurenka ne
yasa ya fito to tunda basu zo sun kwashe tarkacansu ba me
zai hana bazata dinga shigaba tana huce gajiyarta akan
gadon. In sun kwashe shikenan idan kuma basu kwashe
bamu munyi namu wallahi sadakinka kuma kaje ka anso
kayanka da duk kayan auran de ka dankara musuhar zanin
da kawa yarinyar ka amso yau ba sai gobe ba. Nafada maka
yayi tsaki tare da cewa banajin bazata dawoba zata dawo ta
taras da kayanta.
Tace alko zanci mutuncinka wallah, ba dai a
gidannanba na rantse kai ba waccema zata sake shigo gidan
anba waccan figaggar ta iskka. Bazan sake ganin wani
tashin hankalinba na fada maka Allah.
Zaiyi Magana kenan suka dinga jiyo kuka daga waje
kuma cikin gidan ake shigowa. Suka saurara de kyau.
156
2
2
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Inna suke gani ta shigo tana kuka wi wi wi fuska share
share harda majina hijabin farace amman tayi dakan dekin.
Suka bitade kallo cike da mamakin wannan sakaren
kukanta. Har ta zauna ta mike kafafuwa tamkar me shirin
bori..
Inna ta saki baki tana kallanta harta zauna din tace wai
me nake gani haka wane irin sakarci ne haka kin shigo kina
kuka tamkar akuya yaragaje yargaje ina taron ko ya muta
ne.
Ta cire hijabin tana cewa yo inshiya muta ai dasauki
aurennawa ne yą mutu.
Inna tazabura tamkar an watsa mata ruwa ta dafe kuji na
shiga uku me nake san ji ya zamuyi dake? Tace ba gwanda
ya sakoni ba de wal kancin dayamin bayau. Tace be dai sako'ki din ba daiko ko abinci aka barmu dashi mun shiga
uku ince dai bai yi saki da dai ko? Tace kai kaji inna da wata
Magana kinsan zagin daya mine da cin mutuncine? Tace
ince dai baki rama ba kar yaji haushi in aka sako ki kika
dawo min nan ai tawa ta kare yausle zan iya ciyar dake niba
karfi ba me ya faru ne. ta zauna nan fata fara zuba karya da
gaskiya wanda akayi da wanda ba ayiba. Saida tagama tas
157
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
sannan inna tace bayan taja tsaki ta dauke kai ai kinji
sakarcin ke a kallum baki da wajau awannan zamanin wa
ke fada da miji ai lallabawa ake inba hakaba wallahi yaa
sakoki ki dawo gida ki jera da kannanki suna rainake.
Sannan da kika dage kan auran dan uwannaki wani tsine
daku me ke gareke da har za'a baku ina zaku kai "yar
mutane kema din haka tsiya ta ganku ta barku tunda nakeda
ubanku ban taba ganin ya tsinanawa kansawani abuba
ahaka ya mutu ya barni daku. Mutum ne marar zuciyar
nema. Shine