Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
5 / 10
take sai kumbure-kumbure tana turo baki 91 WAYE ANGON? motsi kadan taja tsaki. Maryam Ja'afar A ganinta suna 6ata lokacinsu ne da asara bata jin zata yarda ya ganta da kwalliyar bare ya ji dadi. Sannan duk yanda aka yi da ita sai tayi musu kamar dai yanda aka yi da ita wancan karon, dole a haka ake mata kwalliyar. Aka ciro mata rantsattsen leshi din da zata saka jikinsa har rawa yake saboda tsada ga kyalkyali yana kashe ido, tsadarsa ya kai. Komai sabo aka ciro mata, duk kayansa ne tun da aka fara bikin sai yau zata sa kayansa, don ya gani ya ji dadi. Nan fa aka dinga yi ta ce ita atafau ba za ta saka ba, wallahi kyamarsu take tir ta sa su, har ya mutse fuska take wai zuciyarta na tashi saboda ganin kayansa, har tana tsirtar da yawu. A ka taru kanta ana abu daya, amman ta ki sauraron kowa, ga motar daukarta tazo ita kadai ake jira. Momy bata gun sai da aka je aka fada mata tare da dan aiken suka shigo. Koda taji ga Momyn nan zuwa gabanta ya fadi, ta tsorata. Nan da nan kwalla ta taru a idonta taf! Ta riga ta 92 WAYE ANGON? sani dole sai tasa kayan tunda Momy taji labari. Maryam Ja'afar Tasan Momynta sarai, tana masifar tsoronta, sam ta canza mata tunda aka fara maganar aurannan ta sauya. A da tamkar ba Mamanta ba, mai sakar mata fuska suyi wasa suyi dariya tayi mata rigima da shagwabarta son ranta. Ko dunguri bata taba mata ba sai a kan Imran, har ta kai jiya da duka da dorina. Don Allah me zai sa ba z ata kara tsanarsa ba? Duk shi yaja mata haka. Me ake dashi? Tasa hannu ta goge kwallar daidai shigowar Momyn. Ta dubeta fuska a hade babu alamar dariya ta ce, "Me yasa ba za ki sa kayan ba?" Tayi shiru tana kallonta ba amsa. Ta sake nanata mata "Da ke nake, me yasa ba za ki saka kayan ba, bayan kin san tun dazun ake jiranki, ko a kanki za su kare?" Ta girgiza kai "A'a." Ta ce, "To dauki ki sa minti biyar ina jiranki." Ta juya hawaye suka dinga kokarin zubowa saboda takaici. Zata yi magana "Momy ni..." kan ta karasa ta juyo a 93 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar fusace ta ce, "Kin san Allah Mabaruka ko ki kiyaye ni, ko ko kafin ki bar gidannan in miki karo na biyu, na rantse." Ta sauko daga kan gadon a marairaice ta durkusa gabanta tana rokonta. "Don son Annabi ki min afuwa kar ki tursasa ni sa kayan nan, ki bari nasa daga cikin wadanda ki ka dinka min, don Allah Momy." Ta ce, "Wallahi ba za ki saka ba, wadannan za ki saka kuma kije da su har gidansa, kuma ya gan ki da su. Idan kuma har ba ki yi haka ba Allah ya isa. Kin nuna min ban isa da ke ba, ba ni da wata kima da muhimmanci a gurinki, sannan ki sa ni yin kaffara." Daga haka ba ta sauke saurararta ba, ta juya a binta a fusace ta bar dakin. Ta dafe kai tare da zubowar hawaye ta ce, "Na shiga ukuna!Wayyo Allahna!" Ita kanta Rafi'a abin ya bata haushi, taja tsaki tare da dubanta ta ce, "Wallahi ba ki jin magana Mabaruka, kin cika kafiya. Sa kayan kawai sai an ta fama da ke kina sa ta rantsuwa, meye wuyar a ciki?" Ta dawo ta zauna bakin gadon tana cewa, "Imran! 94 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Imran!! Wallahi ka shiga uku a hannuna, sai ka gwammace ba ka kawo ni gidanka ba, dan iska kawai mugu." Kwaraf! Taji an buge mata baki, ta daga kai tana kallon aikin waye wannan? Anti Karima ce ta gani a tsaye tana huci ranta a басе, tana kallonta ta ce "Ke dai 'yar wulakanci ce wallahi, fitsararra marar kunya. Don ubanki mijin naki ki ke cewa haka?" Tayi shiru tana zumburo baki, ta ci gaba da cewa "To don Allah mu zo mu tarar da gawarsa tunda ba kya sonsa, sakarya mararwayau." Ta juya ta fice ita ma rai a bace tana fada. Rafi'a ta kalleta cikin fushi ta ce, "Gaskiya ina ganin zan tafi gida ni ma, na gaji da ganin wannan fitsarar taki wallahi. Tunda ba ki jin magana nayi iya bakin kokarina kin ki ji, gara in je gida in huta da bakina." Ita ma ta kalleta tare da harararta ta watsar ta ce, "Ki tafi mana sai me? Tunda daman ba goyon bayana ki ke ba, bakinku daya." Abin ya ba Rafi'a mamaki, bata yi zaton zata fada mata 95 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar haka ba. Taji haushi sosai, don haka ta zuciya sosai. Ta mike tana cewa "Haka ki ka ce ko?" Mabaruka ta cе, "Haka na ce'mana, ai ba tsoronki nake ba, na fada dukkanku a bayanshi ku ke ba kwa sona, sai me kuma don kin yi tafiyarki?" Ta kara zuciyà, ta wuce a fusace ta figi gyalanta ta fice cikin fushi. Tabi ta da harara tana tabe baki. Mai yi mata kwalliya ta ce, "To yi maza ki sa kayan in karasa miki kwalliyar." Tamkar ba zata tanka ba ta ce, "Je ki ba sai kin karasa ba, wannan ma ta isa." Zata yi magana ta dakatar da ita, "Kije don Allah bana so." Ganin kanta na rawa tana yi wa kowa rashin kunya tayi wa wadancan to ina ga ita! Don haka da sauri ta bar dakin kartayi mata tata rabon. Taja tsaki tare da fadawa gadon tana gunjin kuka. Koda Rafi'a ta fita a falo suka ci karo da Momy, ta fahimceta sosai saboda bayyanar fushinta a fili. Ta ce, "Rafi'atu lafiya, me ya faru?" Ta dan kakalo murmushi ta ce "Ba komai." Daidai fitowar mai yi wa Mabaruka kwalliya, ta ce "A'a 96 WAYE ANGON? tsakaninta ne da kawar tata." Maryam Ja'afar Momy ta ce, "Me ya faru?" Ta fada mata duk abin da ya faru. Ran Momy ya kara бaci. Mabaruka ba ta jin magana, kan aurannan duk ta fitsare. Taja hannun Rafi'a ta ce, "Yi hakuri 'yata kar kiyi fushi, zata gane muhimmancinki, ki dan saurara ki rakata gidan mijin." Ta ce, "Shi kenan Momy, ya wuce." Tayi murmushi ta ce, "Na gode." Suka wuce cikin dakunan, kan hakan sai da Momyn ta ci mutuncinta ta zazzageta. Mabaruka tasha kuka, don dole ta shirya cikin kayan makiyinta tunda take ma a rayuwarta bata taba kyau irin na yau ba. Kayan sun zauna mata, sun karbeta sosai kowa sai yabawa yake yana daukarta hoto, tana ta walwali. Ita kuwa sai botsare-botsare take tana turo baki, gabadaya kyamar kanta take kamar tasa kayan da suka taба kaşhi, ta tara miyau bakinta taf! Aka yi mata kwalliya mai gigita mai kallo, gabadaya ta sauya tamkar ba ita ba. Masha'Allah kawai ake cewa. Aka shiga da ita gun 97 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Momyn don suyi bankwana, tasa mata albarka sosai tare da yafe mata duk abin da tayi mata. Ta kara ja mata kunne sosai da sosai. Tun a nan ta fara kuka tan'aihu bare da taga an fito da ita an sakata a motarta wacce ya bata a lefenta. Ta dinga shure-shure tana kuka tamkar zata buge mutane ta fito. Abokanan Ango suka dauka irin kukannan ne na barin gida, a haka dai aka dauki hanya da ita zuwa rantsattsen gidansa inda ya tamfatsa mata don ita kawai. Har suka iso tana kuka, musamman da taga an tsaya bakin gate a na yi wa Maigadi horn wanda ya fara aikinsa tun bayan gama ginin. A ka shiga da ita cikin motarta. Runtse idonta tayi gam! Don kar taga gidan, aka fito da ita tamkar makauniya. Anti Karima ta ce lokacin da za su shiga falon "Ki ambaci sunan Allah don shiga gidanki." Tsaki taja a ranta, bata jin zata iya don ba alkhairi take nema ba cikin gidan. Aka shiga da ita falon wanda sassanyar iska da kamshi ke bankadowa mai dadi da sa nutsuwa, dole in ka shake shi 98 WAYE ANGON? ka lumshe idanuwa, aka wuce da ita dakinta. Maryam Ja'afar A dosane ta zauna kan tafkeken gadon nata wanda ya dago yasha lallausar katifa tumemiya, ga shimfidu na alfarma. Shi kanshi kamshi ba iyaka, kayanta wayyo Allah! Sun dauki hankalin kowa, kamar kayi ta zama cikinsa. Komai yayi cas-cas wallahi, yayi kyau. Lallai Momy tayi kokari, kuma dai Daddy shi ya bada kudin komai, sai dai ita ta shige gaba kan shigowar kayan. Kowa yana cikin farin ciki saboda shigowar wannan kerarren gidan da dakuna kamar a kasar Turai, ga kamshin gidan na dukan hancinansu. Amman ita sam haushi, bakin ciki da takaici sun cika mata rai, tayi tsuruu, bakin ciki ya hanata magana. Wai yau ita a gidan Imran? Kai jama'a wannan wane irin bakin ciki ne? 'Yan rakiyar duk na gida ne, sun saba da angon. Shi ma haka cikinsu ba wacce yake jin kunyarta, haka suma. Don haka da shi aka shigo dakin da abokanansa. Suna ta tsokanar juna. Ya shigo kansa ba hula, hannunsa rike da waya da charger yana cewa, "To-to-to a tashi a tafi gida 99 WAYE ANGON? haka nan mun gode." Maryam Ja'afar Samira daga cikinsu ta ce, "Lallai ma! A nan za mu kwana ba ka san in an kawo amarya ana kwana tare da ita ba?" Ya zaro ido yana cewa, "Wallahi ba zai yiwu ba, ba mai kwanar min gida tunda dai kun kawo min ita to kuje na gode zan neme ku." Aka yi dariya. Anti Karima ta ce, "Ai ko ba ka isa ba sai mun huta gajiyarmu a wannan lallausan gadon dukkanmu." Ibrahim daya daga cikin abokansa ya ce, "In kuma ki ka ce haka Gwaggo ba ki tausaya ba, tun yaushe yake tsaye ita kanta Amaryar ya kamata a bar su su huta su san sun angwance. Duk maganganun saman kanta suke yi, fuskarta a rufe da mayafi. Haushi ya cikata, sai jan kananan tsaki take tana harare-harare cikin gyale ba wanda ke ganin me take yi. Don me zai shigo mata har nan yazo suna mata rashin kunya saman kai? Taja tsaki tare da dauke kanta, dan iska kawai! Ta fada a ranta. Anti ta ce, "Kai-kai-kai kalle ni da kyau Anti ce ba 100 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Gwaggo ba, baka ganni ba ne ban yi kama da Gwaggo ba da saurana?" Dukkansu suka yi dariya, Imran ya ce "To sorry Anti, ni dai bari in sa chaji kafin ku tafi."Ya wuce yana jonawa. Rafi'a ta ce, "Duk ba in de za ka sa sai a nan?" Ya ce, "Wallahi socket din duk basa aiki sai an duba min su, na nan ne kawai ban san ya aka yi ba." Dayan abokin ya ce, "Ai ba laifi tunda dakin Amarya yana yi, ai faduwa tazo daidai da zama, kaga shi kenan." Ficewa ya yi yana dariya, suma abokan suka rufa masa baya suna dariya, ba don komai ya yi haka ba sai don lura da ya yi da Gimbiyar tasa maganganunsu sun isheta, tsoron kar ta ba shi kunya ne yasa ya fice. Sauran 'yan kawo Amarya duk sun tafi sai su Anti Karima da Anti Luba, sai kuma Rafi'a. Sai da suka yi sallar Isha'i sannan suka yi shirin tafiya, bayan sun gama santin gidan suna ta zuzuta shi, ina ma su ne. Ita kuwa Gimbiyar ba abin da take yi sai gatsine-gatsine a cikin lullubi babu mai ganin abin da take yi. Da taga za su tafi da gasken, idanunta suka yo 101 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Kwalkwal, ta tuno inda take gidan Imran daga ita sai shi, a wannan makeken gidan. Hankalinta ya tashi, kuka ya dawo sabo. Ta dube su ta ce, "Anti Luba don Allah kada ku tafi, ku zauna tare da ni." Suka yi dariya ta ce, "Lallai Mabaruka! Har yanzu yarinya ce ke, yaushe za mu zauna nan godai-godai da mu, Allah ya tsare. Anti Karima ta ce, "Ai ko dubi tun dazu yake cewa mu barmasa gida, ina ga yazo ya tarar da mu a nan?" Ta mike tsaye hawayen suna fara zuba ta ce a marairaice "Wallahi Imran zai cutar da ni in dai daga ni sai shi ne, don Allah Anti ku..." Anti ta katse ta, "Mabaruka ki cire komai a ranki, ya riga ya zama mijinki ba zai taba cutar da ke ba saboda yana sonki. Ya sha wuya kan ya same ki, kin ga ko ba zai yi wasa da יי ke ba, zai rike ki da kyau.' Ta ce, "To amman kin san bana sonsa Anti, ya zan zauna da shi?" Ta ce, "Wannan mai sauki ne, ni nasan Imran Jarumi ne tsayayye, za ki sha mamakin yanda za ki fara sonsa, ke dai kiyi biyayya." 102 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ta ce, "Ba zan iya ba Anti, ina ji kamar zan mutu." "Za ki iya Mabaruka, kowa da haka ya faro, kuma ya saba, kema hakan zai kasance a gare ki, za ki gani. Mu da zamu dawo nan da wata tara daukar baby." Ta fada tana dariya.. Ta dauke kanta daga gareta cikin jin haushin maganarta. Duk suka yafa mayafansu, suka ce "To sai gobe zamu dawo, a aje mana kazar nan mai maiko-maiko, wallahi kar ki yarda ki cinye in ba haka ba ranki zai 6aci." Cewar Anti Luba tana dariya. Anti Karima ta ce, "Haba kema da wani zance a ganinki Imran zai kawo kaza daya ne, ai yasan zamu dawo zai tanade su don mu." Sam! Labarinsu ba ya mata dadi, sai ma karin takaici da bakin ciki." Ta katse su "Don Allah Anti ki fahimce ni ku zauna." Anti Luba ta ce, "Ke kina da isasshen lokaci, mu gaba muka yi ba mu da lokacin sauraron shirmenki." Tayi gaba. Da sauri ta riko Rafi'a tana kuka, ta ce "Nasan ko kowa ya guje ni ke ba za ki iya ba, kin san komai kawata don son 103 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Annabi kada ki tafi, ki zauna tare da ni don Allah Rafi'a." -Rafi'a ta zaro ido tare da cewa "Ni? Ba ruwana, so ki ke yazo yasa a fitar da ni da tsiya? Wallahi ba ruwana, kiyi hakuri dai gobe insha'Allahu zna dawo kar ki damu." Ta kara fashewa da kuka tare da kankame Rafi'a, a lallai ba ża ta tafi.ta barta ba. Ita ma Rafi'ar sai kuka, aure ne ya rabata da kawarta, su kan kwana tare suyi yawo tare, makarantarsu daya, seat daya. Kowa ya sansu tare, amma yau aure ya nisanta su, me yasa ba za ta yi kukan rabuwa da aminiyarta ba? Ta ce cikin kuka "Rafi'a ki zauna da ni kada ki manta baya muna kwana tare mu wuni tare, me yasa yau za ki guje ni? Kema ba za ki iya zama a wannan Kuntataccen gidan ba amman ni ku ka kawo ni cikinsa kuma kitafi ki bar ni?" Ta ce, "Da da yanzu ba daya ba Mabaruka, yau Imran ya kwace min ke, ya raba kwana da nake tare da ke, babu wata ranar da zamu kwana tare saboda shi. Shi zai zama madadina, wanda kuma yafi ni. Na tabbata za ki fi samun farin ciki da walwala a kan ni, za ki saba da hakan ba da dadewa ba, sannan gidan mai yalwa ne ba 104 WAYE ANGON? Kuntatacce ba, kada ki manta da haka." Maryam Ja'afar Ta rasa inda zata sa ranta, duk in da ta bullo musu sai sun zame, me yasa wai ba a sonta? Imran ya leko yana cewa, "Wai me ku ke ba ku fito ba? Kar na fito muku da halina fa?" Suka yi dariya tare da wucewa suna cewa "Sorry ango, kar muyi laifi har a wajen Allah." Ta rikice ganin za su tafi ta yunkuro zata biyo su, yana daidai bakin kofa zata wuce ta gabansa kenan. Yasa hannu ya dakatar dan ita ta hanyar rike mata hannu gam yana dariya. Taja tayi tsaye cak! Tana kallonsa, tamkar an dasata gun. Ya lakuce mata kumatu tare da cewa, "Sorry, kije ki jira ni zan raka su in dawo, ba nisa zan yi ba." a Daga haka ya wuce da sauri, ta bishi da kallo cikin kunar ran taba ta da ya yi da dakatar da ita da ya yi. Haka nan kuma taji ta kasa fita din, taji ta fasa fita din. Ta rasa dalilin hakan. Da gudu ta koma ta fada gado tare da fashewa da kuka mai karfi. 105 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Sai da yaga shigarsu mota har ihsani ya yi musu, sannan ya dawo zuciyarsa cike da farin cikin zai kasance da amaryarsa a yau. Ga ta a gidansa a matsayin tasa, mallakinsa daga shi sai ita a gidan. Ita kuma a can tana zaune sai ta tuna ta bar kofarta a bude yasa da sauri ta mike tana kokarin rufewa. A iya bincikenta bata ga key ba, tayi mamakin rashinsa. In dai ba an shirya haka ba me yasa za a dauke shi? Bayan a jikin kofa aka saba barin key kowane gida? Tayi kwafa tare da komawa tsakiyar gadon tana share hawaye wasu kuma suna yunkurin zubowa, duk takaicinta na kasancewarta ne a gidan makiyinta. Imran ya shigo da sallama idonsa a kanta yana fara'a. Ya tunkarota har kan gadon in da ta kifa kanta a kan gadon tayi ruf da ciki. Da zuwansa ya ja mata yatsan kafa, cikin wata irin fusata ta juyo da bala'i yanda ka san da ta juyo zata kife shi da mari. Sai kuma tayi sororo tana kallonsa, ba abin da ya fado mata sai maganar Momy. Tayi sukut tare da sunkuyar da 106 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar kai kasa bayan ta janye kafafunta har da nade su cikin zani. Sarai! Ya fahimce ta. Ya yi murmushi yana kallonta daidai sanda ya zauna bakin gadon kusa da ita. Da sauri taja baya ta kauda kanta daga gefen da yake tana jin bakin cikin zama kusa da ita da ya yi. Ya kirata "Mabaruka!" Tayi masa banza tamkar ba ta gurin sai bakin rai. Ya sake nanatawa, nan ma shiru. Ya ce, "Shi kenan tunda ba za ki amsa ba, ko sai na kira ki da matar?" Ya fada yana dariyar tsokanarsa. Haushi da takaici suka kara turnike ta, ji take da ma tayi tsuntsuwa ta 6ace a dakin. Tun shigowarsa ta gagari maida numfashi mai. kyau. Tana jin duk ya cika dakin da kamshinsa mai sa ta tashin zuciya da gagara maida miyau, ta tara miyana bakinta fam, bayan ta dan kara hannunta a hanci. Ya ce, "Idan ba ki amsa ba zan hayo gadon sosai in ga dalilin rufe bakin." Taja tsaki a ranta tana harararsa ta wutsiyar ido. Ya ce "Mabaruka!"Jin abin da ya fada ne yasa ta amsa can kasan makoshi "Uhum!" Ya ce, "Har yanzun fushin ne ba ki bari ba?" Tayi masa 107 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar banza dai, ya sake cewa "Zuwa yanzu ya kamata ace kin saki ranki kin yi farin ciki tunda dai fushin bai miki magani ba, ga ki dai a gidana." A ranta ta ce, "Yanzu na fara, ba ka ga komai ba wallahi tunda har ka nace sai ka zauna da ni." Ganin dai ba za ta tankan ba shi kadai ke surutunsa yasa ya ce bayan ya maida numfashi. “Well, bari in kyale ki mai yiwuwa har da gajiya, in kin huta sai muyi labarin ko?" Ba ta da shirin amsa masa, don haka ya mike still idonsa na kanta, haka nan ba ya gajiya da kallonta ko yaushe amarmarce yake da ita. In zai kalleta sai yaga kamar yau ne ya fara ganinta, ya gagara dauke kansa daga gareta. Ya ce yana kallonta "Na tafi." Ci kanka ba ta ce ba. Ya kada kai kawai ya wuce har ya kai bakin kofa ya juyo yana kallonta, ya ce "Kada ki sa ran ba zan dawo ba, zan dawo." Daga haka ya wuce a binsa. Yana fita ta juyo tana hararar kofar tare da jan dogon tsaki, 'Dan iska kawai, mugu. Naga gidan da za ka dawo, wallahi Allah sai ya nuna min karshenka azzalumi." Ta 108 WAYE ANGON? sake jan tsakin. Maryam Ja'afar Da fitarsa dakinsa ya zarce, inda shi ma haduwarsa ta wuce kwatance, kayan da ya sha tamkar ya so yafi nata. Ya cire kayansa ya fada wanka don ya ji sanyi-sanyi, ga gajiya har da alwala yayo ya maida jallabiya fara sol ya feshe jikinsa da nau'ikan turarensa yajawo kofar ya fito. Dakinta ya tunkaro, a rufe ya ganshi. Ya tura da niyyar budewa, kofar dai gata a bude amman da alama an tokareta da wani abu. Ya leko yana cewa "Me ya sami kofar ne Mabaruka?" Tayi masa banza tana harararsa. Ya fahimci aikinta ne, don kar ya dawo kenan? Ya yi dariya ya turo hannunsa ya janye abin da ta tokare din yä shigo. Tana zaune a kasan tayils ya nufota, tsugunnawa ya yi gabanta idonsa kur a kanta ya ce, "Wai menene Mabaruka? Ba kya son na dawo ne?" Tayi shiru dai, ya ce "Ba kya son angon naki ya taya ki bacci yau?" Dagowa tayi ta harare shi son ranta sannan tà sake durkusar da kanta tana kokowa da zuciyarta. Ya ce, "Sorry, ban cancanci wannan kallon ba amin 109 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar uzuri, ba daga ni ba ne laifin zuciyata ce mai naci." Ba ta dai tanka din ba. Ya ce, "To zo muje kiyi alwala muyi sallah mu yi wa Allah godiya da ya kawo mu wannan ranar, nasan ba ki ci abinci ba, in ki ka dan ci wani abin sai ki kwanta ki huta gabadaya." Kala! Ba ta ce ba. Ya sake cewa, "Mabaruka wai menene haka? In ta yi ko, ni mahaukaci?" Ta dago ta harare shi ta mayar. Ba ta yi tsammani ba taji ya riko hannunta daf! Ta bishi da kallo masifa na cinta. Zata yi magana yasa yatsa bakinsa tare da cewa “Shihh!” alamar tayi shiru, sai kuma ta gagara cewa wani abun, ta ci gaba da kallonsa din kawai. Mikar da ita ya yi tsam! Yana cewa "Taso muje in raka ki." Ta fara botsare-botsare tana ture hannunsa, bakin yayi tsini saboda zumbure-zumbure. .Shi kuwa ya rike ta gam ta gagara kwace kanta, sai guna-guni. Ya turata bandakin ya aje mata buta gabanta. Mikewa tayi ita ba za ta yi ba, ya sake durkusar da ita ta 110 愛 2 WAYE ANGON? sake mikewa. Sun yi haka ya kai sau bakwai. Maryam Ja'afar Ya dubeta ya ce, "Wai me ke damunki, lafiyarki kuwa? Ba kya jin magana ko?" Tayi tsaye tana turo baki. Ya sake ta yana cewa, "Shi kenan kada kiyi din fito."Ya juya ya fice. Taja tsaki tare da harararsa. Ba wai don ya bata ransa yasa tayi alwalar ba, sai don Momynta kawai, musamman da ta tuna bata yi sallar Isha'i ba, tayo ta fito tana zumbure-zumburen baki. Zaune yake bakin gado hannunsa rike da waya yana dannawa, wucewa tayi ta dauko Darduma ta shimfida ba ta ce komai ba ta zura hijabinta ta kabbara sallar. Bin ta ya yi da kallo yana mamakin taurin kanta, ta cika kafiya. Yajinjina kai kurum. Haka nan ransa ya ba shi Isha zata yi, don haka ya kyaleta har ta idar. Ya mike tare da shimfida wata Dardumar gabanta yana cewa "To tashi muyi nafilar ko raka'a biyu ne." Ba ta dago ta kalle shi ba, bare ta ba shi amsa. Har ta idar da lazimin ta mike. Ganin ta mike ne yasa ya kabbara sallar a zatonsa ita ma ta kabbarar, amma ita kowama tayi ta zauna abinta bayan ta cire hijabin. 111 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Har ya idar ya hau jero addu'o'in zaman lafiya da zuri'a dayyaba, duk idan ya fada zata ce a'a Ya Allah! Har ya idar yajuyo. Ganinta ya yi zaune ta mike kafafuwa tana danna waya. Ya ce "Mabaruka!" Tayi mishi banza, ya sake kiranta. Ta dago kawai ta kalle shi ta watsar. Ya ce, "Ba ki sallar ba ko?" Tayi shiru. Ya sake nanatawa can cikin makoshi. Ta ce "Eh." Ya ce "Saboda me?" Tayi shiru. b1 50 Ya gaji da maganar, don haka ya ce "Shi kenan za ki yi watarana." Ya matso kusa da ita har jikinsu na goguwa da juna. Tayi saurin matsawa, ya bita da kallo tsawon dakiku. Ya numfasa ya ce, "Ok! Akwai wata addu'a da Manzon Allah (S.A.W) ya umarta ga duk wanda ya yi sabon aure, ko ya sayı abin hawa. Saboda samun alkhairinsa da nisanta daga sharrinsa, kuma an so ga wanda ya yi sabon aure ya sanarwa amaryar da yin addu'ar saboda an so ya kama kanta ya yi addu'ar. sm Faidar hakan kuwa don kar kawai taga ya tunkarota kwatsam! Amman idan da bayanin zata fahimce shi ta ba shi hadin kai, kamar yanda muka yi sallar nan muyi 112 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar addu'o'i mu nemi rahamar Allah da tsarinshi da alkairin da ke cikinsa. Bayan haka sai wannan addu'ar da na fada miki." Ya tsaya yana kallonta kanta na kasa kan waya tana dannawa tayi kunnan uwar shegu da shi, shi kadai ke surutunsa. Ya ci gaba "Sannan an so Angon ya gabatar musu da dan abin tabawa a baki da abin sha daidai karfinsa. Bayan haka a wannan daren ana bukatar su raya shi da sunnar Annabi (S.A.W) saboda dare ne mai rahama, albarka da daraja gare su. Kar su bari wannan daren ya wuce haka nan."Ya kalleta da kyau "Ina fatan kin fahimci me nake nufi?" Ta dago kawai ta kalle shi ta watsar. Ya ci gaba da magana. "To idan kin fahimce ni ina son wannan daren abubuwan da na lissafo miki muyi su a aikace don samun ladar sunnar. Na sanki ba yau na sanki ba, tun kina yarinyarki. Nasan gwargwadon ilimin da ki ka yi na Islama, kin san komai, kin san aure kin san me ake nufi da shi da kuma hakkokinsa, haka ne?" 113 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Tayi masa banza. Ya sake nanatawa. Don ya kyaleta ne yasa tadaga kai kawai. Ya ce "Alhamdulillah." Ya mike tsaye ya tunkarota yana cewa "Bari in yi addu'ar." Kafin ta yunkura taji ya rike mata kai. Da wani azama ta mike ta tunkude shi, idanunta sun kada jajir saboda 6acin rai tana harararsa. Yaja baya hannu da baki a sagale yana kallonta cikin mamaki, da kyar ya iya cewa "Meye haka?" Ta harare shi tare dajan tsaki ta durkusa ta dauki dankwalin da ya cire ta koma kan gado ta zauna tana fushi. Ya dan tako gabanta kadan idonsa a kanta ya ce, "Anya lafiya ki ke?" Ta dago ta harare shi son ranta, ta kawai tana kara jin tsanarsa a ranta da takaicin kasancewarta a gidansa. Tsugunnawa ya yi tare da dora hannunsa saman wuyanta yana cewa, "Ina ga ba ki da lafiya don..." Kafin ya karasa ta mike da sauri tare da janye jikinta cikin masifa take cewa. "Wallahi kada ka kara taba min jiki."Ya kalleta da kyau ya'ce, "Don me?" Taja tsaki tare da rike kugu tana harareharare. 114 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ya ce, "Tunda ba ki da dalili ni kuma ba zan fasa ba, ke matata ce ya zama dole

Chapter 5 of 10