Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
2 / 10
fasa abin da ya shirya mata ba. Ya datse kofar tare da sa mata key ya dauki dan key din ya cillar bayan wordrove. Ta aje kan table din da ke gefen gadon, ta mike ta wuce abinta zuwa kofar, ta jawo ta ji ta gam da ta lura da kyau taga ansa mata key ta ji cak ranta na kara mata daci, to me yake nufi kenan? Tamkar ba za ta masa magana ba, amman dai tunda so take ta fita ya zama dole ta sauke girman kan ta tambaye shi, ya bude mata. Shi kuma ya yi zaune kan gadon yana kallonta da son ganin kokarinta. Bata juyo ba ta ce "Ka bude min kofar ina son in je in kwanta dare ya yi."Ya yi mata banza tamkar ba ya dakin. 24 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ba ta gaji a'afar ba ta sake tambayarsa din, sai sannan ya yi magana in bacci ki ke son yi ki zo ki kwanta a nan ga gado nan. Sai a sannan ta juyo cikin fushi da bala'i zata yi magana, ganinsa a haka tamkar ba kya jikinsa yasa bakinta ya kulle ta kasa maganar. Ta sunkuyar da kai wani tsoro na shigarta ga kofa a rufe wato dalilinsa kenan na rufe kofa? Tsoro ya kamata, jikinta ya dauki rawa, idanunta suka yo waje, sam ta gagara daga ido ta kalle shi. Sosai ya fahimce ta ya yi dariya ya ce, "Ina jin ki, me za ki ce da?" Tayi shiru ta kasa magana. Ya sake nanatawa lokacin da ya mike jikinta ya kara rawa. Bakinta na rawa ta ce, "Ka..ka...ka bude min...min kofa bar...barci nake ji." Ganin ta tsorata ainun yasa ya yi tsaye cak ya ce "Shi ne na ce ki zo ki kwanta a nan mana ga shimfida nan." Yana rufe baki ta dauka "Momy zata yi fada ai bai dace na kwanta a nan bа." Ya ce, "Waye zai tuhume ki don kin kwana a dakin mijinki?" Tsoron da ke ranta ne ya hanata ba shi amsa, 25 da ni a WAYE ANGON? Maryam Ja'afar amman dai ta ce "Kayi hakuri dai don Allah ka bude min." Ya ce, "A'a ban yarda ba, a nan za ki kwana musamman da naji labarin duk yau ba ki ci komai ba, shi yasa na ce a ba ki ki kawo min da kanki, kinga sai muci tare sannan muyi kwanciyarmu a nan ga gado can.' Sai sannan ta iya dagowa ta kalle shi a marairaice ta ce, "A'a ba zan iya ba, don son Annabi ka bar ni na tafi dakina kar Momy ta jiyo ni a nan dakin." Tunkarota ya yi yana cewa, "Ba abin da zata ce, nasan zata yi farin ciki idan ta ji ki a dakin mijinki, kada ki damu kina tare da Angonki." Ganin yana tunkarota ne yasa ta kara tsorata, idanunta suka fito ta faraja da baya har ta dangane da jikin kofa. Shi kuma bai fasa ba ya ci gaba da tahowa yana dariya, har ya tsaya gaf da ita suna jin numfashin juna, tayi saurin sunkuyar da kai jikin nata kuma bai fasa rawa ba. Ya ce, "Wai meye duk ki ka tsorata, me ki ke tunani? Ta ce da sauri ba komai. Ya ce, "In ma kina tunanin wani abu nasha masifarki da ki ka saba min zata kwace ki." Tayi shiru dai ta gagara hada ido dashi, kamshinsa ya baibayeta ganin ya daga hannu ne yasa tayi saurin datse 26 WAYE ANGON? idanunta da kankame jikinta gam. Maryam Ja'afar Ya yi dariya yayin da ya ke dora hannunsa, saman kofar wato bayanta sai ya sata tsakiya tsakanin jikinsa da hannuwanta jikinsu har yana ta6a juna. Jikinta ya kara rawa, ya ce yana kallonta "Calm down my angel, ba zan miki komai ba, kawai da naji baki ci komai ba ne yasa hankalina ya tashi, naji ba dadi shi yasa nake son muci abinci in ba ki tunda Momy ta ba ki kin ki ci. Ba zan iya jurar zamanki haka ba, ba tare da kin ci komai ba, don nima ba zan iya ci din ba." Ita dai ta datse idanunta gam bakinta yana ta salati, jikinta bai fasa rawa ba bayan zufar da ta lullubeta. Kamar wasa taga ya daga rigarta yana cewa, "In ga cikin ma?"” Ba shiri ta bude idon tana kallonsa, anya yana cikin hankalinsa? Kan ta gama wannan mamakin taji hannunsa saman cikinta yana shafawa yana cewa "Kin ga ni ko cikinki shafe yake alamar ba abin da ki ka сі." a Ta kalle shi cikin bacin rai ta ce, "Imran!"Ya amsa yana kallonta. Та се "Ка dauke hannunka daga jikina." Ya tsareta da ido ya ce "Why?" Ta ce, "Ni matar aure ce matar 27 WAYE ANGON? wani." Maryam Ja'afar Ya yi dariya ya ce, "Ni ba?" Ta ce, "Na dai fada maka ka cire hannunka a jikina."Ya ce, "Idan ba haka ba..." Kan ya gama rufe bakinsa a fusace zata ture hannunsa, caraf taji ya rikota yana kallonta, ta kama kiciniyar kwace kanta gabadaya ya rikota ya hadata da jikinsa ya riketa gam. Tayi iya kokarinta ta kasa, har da cizo ta cije shi ba iyaka amman ko motsi bata ga ya yi ba bare ya saketa. Ta hau botsare-botsare, idanunta sun taru da kwalla, tsawon lokaci tana kokarin kwatar kanta ta kasa, ya rike ta gam. Sai kawai ta fashe masa da kuka har da shure-shure. Ya yi tsaye yana kallonta har cikin ransa yake jin kukanta sam ba ya masa dadi ga wani sonta da ke kara damunsa, ya ce "Mabaruka wai menene?" Cikin kuka ta ce, "Ka sake ni in tafi."Ya ce, "Ba zan iya ba, ina sonki ina son na kasance da ke a yau don Allah Mabaruka." Ta kara fashewa da kuka ta ce, "Ni ma ba zan iya ba, ina da miji kada ka keta min haddi don Allah Imran." Ya ce, "Ke ba matar wani ba ce matata ce, ni ne Angonki 28 WAYE ANGON? ba wani ba." Ta ci gaba da kallonsa tana kukan. Maryam Ja'afar Ya ci gaba, "Kin san yanda zuciyata take tafarfasa na sonki Mabaruka son da nake miki wallahi wanda ki ke so baya miki ba zai baki kulawar da zan ba ki, ba zai tattale ki ba kamar yanda zan miki ni zan gatanta ni in ba ki farin ciki da jin dadin rayuwa. Saboda ni ke sonki tsakani da Allah, kuma na fi shi sonki, a gidana za ki fi jin dadi. Don Allah ki tausaya min Mabaruka ki bani hadin kai muyi soyayya me dadi, ba abin da zan miki a nan har sai kin zo gidana. Ta kasa cewa komai, illa kukan da take har kanta ya fara ciwo ta gaji da yi masa bayanin bata sonsa, ta furta masa ta masa a aikace amman ya gagara fahimta, to me zata ce masa ya fahimta kuma? Ta ci gaba da kukan tana kallonsa, ya kalleta cikin tausayawa ya ce, "Ya isa! Ya isa! Is ok, bana son kukan nan, kiyi hakuri." Taki dainawa ta ci gaba da kukan dai tana kallonsa, shi kuma har lokacin yana rike da ita. Ya ce, "Kina son nima in yi kukan ko ba kya son farin cikina ba kya tausayina ko?"Daga kai tayi alamar eh. 29 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ya yi murmushi ya ce, "Ok, naji zo muci abinci sannan ki ta fi." Ta tirje ita ba za ta tafi ba, ya ci gaba da lallashinta da yaga ba za ta je ba, ya jata da karfinsa suka wuce ya zaunar da ita bakin gadon kusa da jikinsa. Ta dinga kiciniyar kwace kanta. Ya dubeta ya ce, "Wallahi idan ba ki tsaya ba a nan za ki kwana, kinga gadon nan?" Ya nuna mata. Tabi gadon da kallo. Ya ce, "To a nan za ki kwanta, ni da ke kuma babu mai tambayata dalilin hakan, don haka gwanda ki nutsu ki ci abincin nan sai na bude miki kofa ki fita salin alin abin ki, kije dakinki ki kwanta." Tayi narai-narai da ido, kukan ya tsaya cak sai zare idanu, ganin ta nutsu ne yasa ya saketa yana kallonta. Ya yi tunanin zata tashi amman sai yaga tayi dai zaune, don haka ya jawo abincin yana zuba musu shi da ita. Yaje table din tsakiyarsu ya debo a cokali yana kallonta ya yi dariya. Ya ce, "To haa bakin in ba ki." Ta juyo ta galla masa harara tare da dauke kai tana jin wani takaici a ranta da karin tsanarsa. 30 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ya yi dariya ya ce "Sorry my Princess, juyo ki karba ki ci." Tamkar ba ta gun bare ta amsa, ba yanda ta iya ne yasa take zaune a dakin, dakin ma akan gado, gadon ma kusa da shi har tana jin saukar numfashinsa, ta ce a ranta tir! Ya ce, "Ok, tunda ba za ki yarda in ba ki ba ni ba ni." Ya juyo da ita ya mika mata cokalin, ba ta da shirin karba. Ya ce, "To idan har ba ki yarda na ba ki ba, ko ki bani wallahi a nan za ki kwana kuma abin da ki ke tsoro sai ya faru." Hankalinta ya tashi ainun idanunta suka yi rau-rau, wallahi ita dai an cuce ta tunda aka hadota da shi bayan an san bata sonsa. Kawai hawaye suka fara sintiri a kumatunta. Ta jawo cokalin tana kokarin ba shi, idanunta a rufe taf da kwalla. Ya fahimceta tabbas ba da son ranta zata yi ba sai don ya matsa mata, jikinsa ya yi sanyi tausayinta ya kama shi kanta na kasa ya dan leka fuskarta. Cikin damuwa ya ce, "Mabaruka!" Tayi shiru tana shesshekar kuka, ya sake nanatawa a dan rude ya ce, "Menene Mabaruka?" Kukan ya soma fitowa. Ya birkice ainun yana cewa, "Ni ne ko ni ne na sa ki 31 WAYE ANGON? W Maryam Ja'afar k c 2 kuka? Sorry ba zan kuma ba." Ta ci gaba da kukanta tana Kokarin ba shi hannunta na kusa da bakinshi. Ya janye hannun yana cewa "Is ok! Is ok! Sorry na fasa wallahi amjocking, please ki bar kukan kin ji ko?" Ba ta fasa miko masa ba, sam ya daina sha'awar ta ba shi din, kukanta ya birkita shi ya tada masa da hankali gefe kuma tausayinta da ya cika masa rai. Ya tsugunna gabanta tare da riko hannuwanta bayan ya cire hannun daga kan abincin ya rike ta cikin kulawa da damuwa yana cewa. "Is ok Mabaruka, ki bar kukan na fasa kin ji ko?" Ta daga kai kurum. Ya dan leko ya ce, "Kin bar kukan ko?" Ta sake daga kan ya ce, "Promise?"Ta sake daga kanta. Ya ce, "Ba zan sake miki haka ba, bana son kukanki kin ji my angel?" ta dai daga kan. Ya ce, "Please, say something mana am compused."Ta ce, "To." Kawai ya ce "Thanks my Mabaruka." Ya koma ya zauna idanunsa still a kanta ya ce, "Za ki wuce dakinki in buďe miki kofar ko za ki dan ci abincin sannan. Ta dan dago ta kalle shi second biyu ta sunkuyar, haka 32 る WAYE ANGON? Maryam Ja'afar nan taji gwanda ta ci ko ya ya ne tunda har ya damu taci kuma ya barta ta tafi din. Duk da hakan da ya yi ba burgeta ya yi ba, ta ce a can kasan makoshi “Eh zan ci."Ya ce, "Ok, to ci ki tafi dare ya yi nisa." Та се, "Тo." Kawai taja cokalin ta fara kaiwa baki tana ci don dole, sam abincin bata jin dadinsa ko don shi ya bata taci kuma a dakinsa. Yayin da shi kuma ya zuba mata ruwa a cup ya rike mata yana jiran ta bukace shi ya mika mata idonsa kur a kanta yana jin matsananciyar kaunarta na karuwa. Ta mika hannu ta karbi ruwan tasha, zata aje ya yi saurin amsa yana cewa "Kawo in rike miki." Ba ta cсе komai ba ta mika masa. Ta ci abincin sosai da ruwan, dadi ya dinga ratsa shi gashi gata ina ma a gidansa ne. Ko da ta gama taja tayi zaune ita bąta tashi ba ita bata ce komai ba, ya dubeta ya ce "Kin koshi ko?" Ta daga kai kanta a kasa. Ya sake cewa "Muje in bude miki ko?" Ta ce, "Um!" Kawai ta ce tare da mikewa tana gaba yana baya har bakin 33 1 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar kofa, ya duba baiga kayan ba ya tuna ya jefa bayan wardrove. Ya jawota ya dauko ya bude mata yana kallonta cikin fara'a sai da safe ko? Ta ce, "Eh." Ya sake cewa, "Ko in raka ki?" Ta ce, "A'a" tare da wucewarta. Ya yi murmushi kawai tare da binta da kallo har ta tura dakinta ta shige suka yi ido biyu, ya dago mata hannu. Sunkuyar da kai kurum tayi tare da jan kafarta ta datse. Kan gado ta fada tare da fashewa da kuka, kukan alakakan hada ta da shi, kukan takaicin kasancewarta da shi a dakinsa, yau cikin darennan. Duk yanda zuciyarta take azalzala akan kiyayyarsa. Ta ci kuka son ranta daga bisani ta mike ta shige toilet don wanka, a ganinta akwai datti a jikinta saboda tasata da ya yi shi kuwa a wannan daran ya yi bacci me matukar dadi da mafarkin Gimbiyar tasa cikin walwala da annashuwa. Washegari tunda safe karfe goma ta bar gidan, koda Momy ta tambayeta ina zata je tunda safe ta ce gidan su Rafi'atu. Don haka kai tsaye can ta nufa tun kan nataccanta ya tashi. Da zuwanta ta fashewa Rafi'ar da kuka tana bata 34 WAYE ANGON? labarin abin da ya farujiya da kokarin da ya yi. Maryam Ja'afar far a Ta ce, "Na shiga tara ba uku ba Rafi'a, da Imran ya cutar da ni jiya wallahi da na roki mutuwata a kan na juri kasancewata da shi, tanadina Sulaiman. Imran ba shi ba ne Angon bare ya kasance da ni." Ta dube ta ta ce, "Ni fa ba na son hauka Mabaruka da rashin hakuri, kan dan wannan abin za ki nemawa kanki mutuwa don rashin hankali?" Ta ce tana kallonta a marairaice "Har yanzu ina kara fada ba ki san kiyayya ba, ba ki san dacinta ba a rai." Gabadaya za ki rasa me ke miki dadi, musamman idan kina ganin wanda ba kya son din bare kuyi rayuwar aure tare, wallahi ba ki san sanda za ki roki mutuwa a kan kasancewarki dda shi na rantse miki." Ta tabe baki tare da kauda kai tana cewa, "Ina neman tsari da wannan tsanar ko wanda ba ya sona ba na fatan na mishi wannan tsanar." Ta ce, "Ba wannan ba ma Rafi'a, zullumin gobe nake ya zan yi idan hukuncin da Alkali ya yanke min wanda bai min dadi ba." Ta ce, "Biyayya mana, ki karbi abin da Allah ya zaba 35 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar miki da iyayenki kije ki kyautatawa mijinki, ku zauna lafiya cikin farin ciki da ganin darajar juna, wannan ita ce shawarar da zan iya ba ki." Taja tsaki tare da dauke kanta tana cewa "Ba zan iya ba, zan nemowa kaina shawarar abin da zan yi wanda ba zai nakasa rayuwata ba." Duk yanda Rafi'ar taso ta ganar da ita da tausasarta sam ta kasa cin nasara a kanta sai dai tasa mata ido. Suka yi waya da Sulaiman a kan bai zo ya ganta tana ina sam ba shi da nutsuwa a zamanta gidan Mamanta, ta dawo gidan Babanta. Ta dube shi bayan yazo a sanyaye, to ya zan yi Sulaiman Momyna ba ta min da wasa, ban isa in mata musu a kan abin da tasa ni ba, ban ma ga fuskar tambayarta ba, bare nazo nan na tare. Sannan shi kanshi gidan Baban ba dadinsa nake ji ba, matsaloli ne dankare cikinsa." Yaja tsaki tare da rike kugu ya ce "Me ake da wannan haukan haka nan an hana min nutsuwata, kowa ya sani ya gani ni ne Angon, amman ana son murkushe zance a bi son zuciya a ba wani sakarai can." 36 5 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ta ce, "Ba kai kadai yake wa ciwo ba, Sulaiman na fika jin ciwo da damuwa ni kadai nasan yanda zuciyata take min daci da radadi, ba in da nake samun sauki da walwala." Ya dubeta da kyau yana ganin abin da ta fada a idonta duk ta rame tayi zuru-zuru, idanuwa ko yaushe a rikide jajawur kamar ma suna ciwo tayi duhu, kana kallonta kasan ba ta da sukuni ya dubi mashin dinsa ya ce hau muje. Ta kalle shi da kyau ta ce "Ina zamuje Sulaiman?" Ya ce, "Ni mijinki ne kada ki tsorata da ni, ina son yau kadai ki sami walwala zuciyarki ta saki ki dan ji sanyisanyi kafin zuwa gobe, in dauke ki zuwa gidana." Ko ba komai taji sanyi-sanyi a ranta duk da a ganinta in har ba an kawo karshen rikicin ba bata jin akwai abin da zai sa ta walwala saboda zullumin da yake dankare a ranta, tsoronta daya. Ba musu kuwa ta haye ya tada mashin din suka wuce: Kai tsaye gidansu ya nufa da ita, ta dube shi ido cikin ido bayan ta sauka ta ce, "Kana nufin nan ka kawo ni?" Ya dube ta "Eh, wani abun ne?" Ta ce a sanyaye "A'a ba komai hakan daidai ne." Duk da tana jin faduwar gaba a tattare da ita, bata nutsu 37 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar da zuwansu ba, amman dai bata nuna masa ba, suka shiga tare. Inna na zaune tsakar gida tana dama fura, Samira na wanke-wanke, yayin da Nafisa na kitchen tana faman aikin tuwon dare. Inna ta bisu da kallo dai-dai. Ya shige daki ya dauko tabarma ya shimfida ta zauna cikin jin kunya. Duk bakin Inna sake shima ya zauna kusa da ita, ta dube shi da kyau ta ce, "Sulaiman." Ya ce, "Na'am Inna." Та се, "Ina ka samo wannan yarinyar?" Ya juyo yana kallon Mabarukar ita ma shi take kallo idanu sun raina fata, sannan ya dubi Innar, haka nan ya ji bakinsa ya yi nauyi yana tunanin fada mata ko wacece. Ta sake fada “kai da kai fa nake, wacece ita wannan din ka shigo min da ita har da dauko min sabuwar tabarma?" Ya ce cikin dan tsoro "Inna Mabaruka ce fa." Ta ce, "Ta ina? Ni nasan wata Mabaruka ne, ina ka samo ta?" Ya ce da kyar, "Amaryata ce fa." Tamkar wacce aka watsawa ruwan zafi, ta zabura har zani na faduwa ta ce, "Amaryarka ta gidan uban wa? Wa ya bakaiye?" Da gashi har ita sun tsorata, suka zuba mata ido ya ce, 38 5 WAYE ANGON? "An fa daura min aurenta kowa ya sani." Maryam Ja'afar ifaTa сe, "Haka ka ke cewa, amman kowa yasan ba kai za a ba ba." Ya turo baki cikin fushi "Ni fa matata ce ba me kwace min mata." Ta yunkura ta rarumo kara zata dake shi tana cewa, "Amarsu ba Amarya ba don ubanka, me na fada maka tun yaushe nake cewa ka sakar musu 'ya?" Idanun Mabaruka suka fito, ta juyo tana kallon Sulaiman din cikin tuhuma daman haka suka yi da Innarsa amman bai fada mata ba? Innar ta katseta "Gidan wa kaga ana wannan haukan auren? Ko a garin Mahaukata ban taßa jin labari ba sai a nan, shi ne ka ke kokarin kawo mana ita nan gidan ta zama tarihi a dinga zuwa kallo?" Ya dinga nuna mata da hannu ta bari tana ba shi kunya, ta ce "Na ki na bari don ubanka, in kai kana tsoronta ni ba na tsoronta, da kai da ita sai in hada in zabge ku da wannan karan don ubanku." Idanuwansu suka fito suna kallonta baki sake. Ta ci gaba "To tunda ga ka ga ta sakarta a nan ayi ta ta kare na fada maka ba kai za a ba ba, wahala kaďai za ka sha 39 lai E WAYE ANGON? sakarai." Maryam Ja'afar Daga Samira har Nafisa ido suka sa abu ya zama na kallo, ya ce "Ba zan iya ba Inna, ina son matata daga na kawo miki ita ta gaishe ki kafin a kawo ta gobe kin bi kin rude kina zaginmu." Tayo kansa "Na zage ku din, sai me? Ko za ku rama ne?" Suka yi shiru ba amsa. Ta ce, "To wallahi sai ka sake t na rantse." Ya ce, "Ba zan iya ba kiyi hakuri na..."kan ya karasa ya ji saukar karan a jikinsa, abin bai tsaya shi kaďai ba har da Mabaruka ta dinga jibgarsu. Da sun yunkura za su gudu dukanta zai maida su, suka kasa kwatar kansu. Sai da kyar sannan suka arce ba shiri a wurwurce takalma a hannu, suka tsaya a waje suna haki da maida numfashi, suka baro Inna na cizgar fada tana fadin. "Za ka dawo ka same ni a gidan, sakarai wahalalle, kai ba ka ma da wayau wa ke shari'a da ma su kudi?" Samira ta ce "Kin min daidai Inna, ke din ba ta wasa ta ce." Nafisa ko ba bakin magana, bata isa ta ce wani abu ba, abu ya dawo kanta sai dai tayi bakin ciki da aka kora su har 40 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar zuciyarta tana son karin aurenshi don samun saukinta. Mabaruka ta dora hannu saman kai tare da fashewa da kuka, "Wai wai wai ni Mabaruka na shiga uku, wai ya ake son nayi da raina?" Ya rasa ma me zai ce, wannan abin kunyar da Inna taja masa har ina? Ya dubeta ya ce, "Ya isa Mabaruka, bana son tashin hankalin nan, ba komai ba ne komai zai daidaita kada ki damu, nasan yanda zamu yi da ita." Ta marairaice fuska, kwalla ta cika a idanunta ce "Ko ta ina akwai matsala, yanzu kana nufin bata son aurenmu har tana cewa a sake ni Sulaiman?". Ya ce "Rabu da ita, wannan fadarta ne. Tun yaushe take fama da ni naki nayi sai dai taji ana shigowa da ke." Ta zauna dabas kasa ta rafka tagumi ta ce, "Ga shi nan mun sha duka karo na farko kenan ban san me zai kasance gaba ba." Ya ce, "Na fada miki ba abin da zata yi..."Ta katse shi da'sauri "Don me za ka ce haka? Bayan mahaifiyarka ce ta isa ta saka ko ta hanaka har sai da yardarta sannan zan shigo gidanka?' Ya durkusa gabanta ya ce, "Ni ne mai aurenki ba ita bа, 41 a WAYE ANGON? Maryam Ja'afar idan tayi kokarin raba ni da ke zan kaita kara ga magabatanta." Tayi jagwam tare da cewa, "Allah yasa to tsorona kar hukuncin da kotu za ta yi ya ki mana dadi, wallahi ina tsoro Sulaiman."Ta fada a marairaice tamkar zata yi kuka. Shi kanshi hakanne a ransa, damuwar kotu tafi ta Inna. Koda yaushe zuciyarsa na harbawa dankare take da tsoro, Allah ya sani yana son Mabaruka fiye da duk matan da ya aura. Kai yana jin zai iya sadaukar da komai a kan ya sameta koda 'ya'yansa karshen zance hatta Inna zai iya sadaukar da ita idan har zai sami Mabaruka bare abin duniya, ko ransa. Ya kwallafawa ransa ita. Kun ji fa! A fili ya dubeta ya ce, "Koda kotu ta yanke hukuncin da bai mana dadi ba, zna iya daga shari'a har sai naje in da za a bani ke tunda kowa yasan uba shi ke da hakkin aurar da 'yarsa ga wanda yaso ba uwa ba, don haka ina da tabbacin ni za a ba mata in dai ana bin gaskiya." Ta kalle shi kurum, ita ba haka ba ne a ranta, tsoronta ya wuce nasa. Koda ta fada masa ba zai fahimta ba, gwanda ma kawai ta kyale shi. 42 WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Ta ce, "Mu bar wa Allah Sulaiman, shi zai shige mana gaba yasan zuciyoyinmu duk wani dabara ko hikima ba zai fishshemu ba." Ya ce a sanyaye "Haka ne." Daga bisani ya dauke ta a mashin dinsa suka shiga yawace-yawace duk don ta saki ranta ta samu nutsuwa. Ba laifi dai ta dan ji dama-dama, amman da zaran ta tuno tashin hankalin da ke gaba da idan ta tuna gobe kamar yanzu an riga an yanke hukunci. Dayan cikin biyu sai taji komai ya dagule mata, har goma na dare suna waje. Tuni take cewa ya maida ta gida amman ya ki, ko da Momynta ta kirata rikicewa tayi ta rasa me zata ce, sai dai tayi mata karya ta ce tana gidan Babanta. Ba ta ce komai ba ta kashe wayar saboda ta yarda da ita ranta bai kawo komai ba. Shi kuwa Imran koda ya tashi yake tambayar Momy ina Mabaruka? Ta ce Taje gidan su Rafi'a. Ya nanata, "Gidan su Rafi'a kuma?" "Haka dai ta ce, wai." Ya jinjina kai kawai amman ba haka yaso ba, yaso ya ganta da safen nan yanda ya tashi da kwadayin son ganin matar tasa, har ya gama abin da yake 43 WAYE ANGON? ya fice. Maryam Ja'afar Har dare da ya dawo ya sake nemanta bai ganta ba, a haka dai ya kwanta yana tunaninta. Sulaiman kuwa gidan abokinsa Mansur ya wuce da ita, Mansur yana da matarsa da 'yarsu guda daya. Sun ci sun sha suna ta zolayarsu da sake labarta wannan rikitaccen auren nasu. Ya dubi Mansur din ya ce "Mu fa a nan zamu kwana sai ku bamu daki daya." Tayi saurin dubansa tare da cewa, "A nan kuma? Wasa dai ka ke." Ya dubeta ya ce, "Wallahi da gaske nake, yau a nan zamu kwana." Ta marairaice fuska ta ce, "Please, kar ka min haka Sulaiman, wallahi idan Momyna taji sai ta dake ni." Ya ce, "Ba za ma taji ba, ba kin ce kina gidan Babanki ba, shi kenan sai ta dauka kina can din, shi kuma daman ya sakankance kina gun Mamanki. Sannan ba magana suke ba bare ya tambayeta ke ko ita ta tambaye shi." Tayi tsuru-tsuru, sam ba haka taso ba, ta ya ya ma hakan zai kasance har yana wani cewa a basu daki daya. 44 S WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ar 1 Masifaffen tsoronta ya taso bata san sanda ta mike ba tsalam! Sai dai ta ganta tsaye tana wuwwurga idanuwa suka bi ta da kallo. Basira matar Mansur din ita ta fahimce ta, tayi dariya tare da mikewa tana ce musu "Ka bar ni da ita minti biyu." Da haka taja hannunta zuwa dakinta. Sulaiman din ya dago murya yana cewa, "Kar fa ki kai min mata wani gurin." Ba ta saurare shi ba suka shige daki. Mansur din ya yi dariya ya ce, "Kai mutumina ta zama matarka kenan har yanzu fa a babin-badinuhu ka ke, ba ka san tsakaninka da wancan ba,waye me matar?" Ya dube shi a natse ya ce, "In tambaye ka mana.""Ya ce "Ina jin ka." Ya ce, "A ganinka ni da wancan din waye Angon?" Ya yi dariya sosai ya ce, "My friend kenan, ni ba Alkali ba ba Lauya ba, ta ya zan san waye Angon?" Ya ce, "A'a a naka tunanin in za ka bi tsakani da Allah a hukuncinka wa ka

Chapter 2 of 10