a wahalce da gajiya ta ce, "Ba komai
ban ci komai ba, na gaji yunwa nake ji, ku bani abinci naci
yau kwanana biyu ban ci abinci ba."
Ya juyo yana kallon Rafi'a cikin farin ciki.
"Ba ta ci komai ba, ina ga kukan da ta dade tana yi ne
yas ata gaji, ba ta ma cikin hayyacinta." In ji Imran.
Ita ma farin ciki ya bayyana a fuskarta, ta durkuso tana
cewa, "Mabaruka!" Ta dago tana kallonta a wahalce, ta ce a
hankali "Rafi'a, Rafi'atu ba ni abinci." Ta ce, "Yunwa ki ke
ji?" Ta ce, "Eh."
Da kanshi ya hado mata tea ya dagata ya jinginar da ita
jikinsa kanta saman kafadarshi, a hankali yake bata tea din.
Ta ci gaba da sha, ta sha sosai har sai da yaga ta koshi
sannan ya kwantar da ita.
69
E1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Duk dakin ta birkita shi, duk wani abun fashewa ta
fashe shi tas! Koda Momy ta dawo taga abin da ya faru har
da kwance kofa. Rafi'a ta ba ta labarin yanda abin ya faru.
Ranta ya 6aci sosai, ta inda take shiga ba ta nan take fita
ba. Ta dinga wa Imran fada sosai, kan me zai biye mata ya
kyaleta mana taje ta kashe kanta mana, wa ta yi wa?
Ta san dai hukuncinta, shi dai ya dinga bata hakuri,
hankalinsa na kan matarsa wacce take barci bata san me
ake ba.
Ta shige dakinta tana fada, "Za ki tashi ki same ni,
fitsararriyar yarinya kawai marar jin magana."
** **
Sulaiman kuwa wannan ihu da ya dinga yi ba arziki aka
sa shi a mota, amman duk da haka kokari yake ya fito shi
sai an ba shi matarsa.
Gidan Inna aka kai shi, bai fasa ihun ba.
Sai da aka banka masa magunguna don ya samu bacci
ko ya lafa. Baccin kuwa ya dauke shi, nan da nan yana
sambatu.
Inna ta numfasa tare da cewa "Dankari! Nan fa ake
70
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar aryinta, so ake a zauta min da kenan? To ba zai yiwu ba."
Ita kuwa Mabaruka sai dare sannan ta farka, tun baccin
da ya dauke ta. Sayau ta tashi, sai dai damuwarta wuni daya
duk ta fada tayi zuru-zuru tayi jugum tunanika kala-kala
marassa dadi suka dameta, sai dai zaryar hawaye.
Rafi'a na gefenta duk yanda taso tajata da labari amman
sam ta kasa shawo kanta, ita kadai ce ke labarinta. Dole ta
yankewa kanta shawarar ta kwana a nan tare da ita.
Suka tsayar da magana tsakanin Momy da Daddy sai
uban gayya Imran, akan tarewar matarsa gobe
insha'Allahu.
Ya yi jim! Yana jin damuwa a ransa da tsoron abu daya
game da hakan, Daddy ya lura da shi ya ce "Akwai matsala
ne?"
Ya ce, "Um to! Akwai Daddy."Ya ce, "Me kenan?"
Ya ce cikin damuwa yana kallonsu.
"Ban san ya zamanmu zai kasance da ita ba. Ina tsoron
kar ta hallakar da kanta a kaina kamar yanda take fada. Na
lura har zuwa yanzu bata sona ko kadan, ko ganina bata son
yi.
171
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
A duniya bata da makiyi kamata, dubi fa irin haukan da
tayi yau duk don an tabbatar mata da ni ne mijinta? To
yanzu kenan muna nesa da juna, ina ga muna tare da juna?
Zamu yi rayuwa da ita ta kusanci kuma har abada."
Yana magana abin tausayi.
Da Daddy da Momy suka tausaya masa.Amman Daddy
ya ce "Kai namiji ne Imran me karfin zuciya, kada ganin
haka yasa ka sare. Mabaruka matarka ce an riga an daura
baka da zabi a yanzu zama da ita dole ne, sai kayi hakuri da
juriya zaka ci nasara, za ka samu abin da ka ke so daga
gareta.
Batun tsoro duk ka aje shi a gefe, ka sa a ranka zaka iya
duk kurari ne ita kuma ba za ta kashe kanta ba kasa ido
kuma ka gani."
Ya yi jim har yanzu dai yana jin shakku a ransa,
soyayyar nan fa ba dole zai iya hakuri da ita koda hakan shi
ne ajalinsa ya gwammace farin cikinta a kan nasa, gwanda
ita taji dadi a kansa.
Daddy ya katse Imran.
"Calm down my son, ka zamajarumi mana ba komai ba
ne hakan anyi ba iyaka, kuma abu ya zama tarihi."
72
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar ar
Kafin ya ce wani abu Momy ta ce, "Kada ka ce haka
mana Imran, tunda har an zo wannan matakin kar ka sare ka
ci gaba da hakuri nayi maka alkawarin Mabaruka zata
zama yanda kake sonta. Maganar hakuri ma bata taso ba a
יל
nan.
Duk yanda za su kwantar masa da hankali da ba shi
kwarin gwiwa sun yi har ya ji kwarin gwiwar yasa a ranshi
yanzu ma ya fara sonta da nacin zama tare da ita har abada.
TO MU SAI DAI MU CE MUJE ZUWA, MUGA
WANNE IRIN ZAMAN ZAAYI?
A haka dai suka tsayar da maganar gobe za a kai masa
matarsa, don ma rikicin da aka samu ai da ta dade a gidanta,
Yanzu kuma tunda abu yazo karshe ba wani 6ata lokaci
gobe a tattarata akai masa shi kenan, don ma tsiyar da tayi
ai da yau za a kaita daga kotun direct.
Dare har ya fara, Momy ta shigo dakin ta dubeta fuska a
daure ta ce, "Ki biyo ni dakina." Daga haka ta ficewarta.
Ta tashi zaune tana turo baki cikin fushi da kumburi, sai
da ta gama jan jiki sannan ta mike ta fice. Rafi'a ta bita da
kallo.
Momyn na zaune bakin gado ta shigo ba tare da ta
73
E
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
kalleta ba ta ce "Rufe kofar ki shigo." Ta tura kofar tare da
Karasowa, taja ta zauna dosane bakin gadon ta sunkuyar da
kai, can kasan makoshi ta ce cikin fushi "Ga ni."
Ta kalleta da kyau ta ce, "Aina ganki maganar ke banga
damar yi miki ba, yanda ki ke jin kin isa da kanki nima haka
nake jin na isa da kaina, bare gidana ki ka same ni gidan
mijina, karkashin mijina wanda karkashinsa nake sa ran
samun Aljannata. Ko nan gidanku ne ke?"
Ta dago tana kallonta da sake nanata maganar a ranta, ta
katseta "Da ke nake nan gidan ubanki ne?" Tayi jim sannan
יי
ta ce "A'a gidanki ne ba gidanmu ba ne."
Ta harareta sannan ta ce, "To kin san gidana ne ki ke min
iko da isa kina nuna min tamkar gidan ubanki ne nan?"
Ta dago da sauri tana kallonta cike da mamaki, anya
Momynta се?
Ta ce, "Kalle ni mana! Na fada nan ba gidanku ba ne
kara ki akai har ki ke zaune cikinsa kici abinci mai kyau
wanda ki ka zaba, ki sa tufafi mai kyau da tsada irin wanda
ki ke so, duk kuma ba gumin Babanki ba, ko nasa ne?"
Ta ce, "Mom..."Ta katseta "Ba ni amsa kawai."
Ta ce, "A'a ba nasa ba ne." Ta ce, "Da kyau! Kin ga
74
WAYE ANGON? ANGON Maryam Ja'afar
kenan a matsayin agola ki ke ba 'yar gida ba ce kara ki aka
yi."
Maganganun sun mata zafi matuka, amman
kasancewar mai fada mata ba ta wasa ba ce ko musu bata
isa tayi mata ba, dole taja tayi shiru zuciyarta tana mata
zafin maganganun.
Momy ta ci gaba da cewa, "Shi ne kin san hakan har ki
ke iskancinki son ranki ba inda iskancinki ya tsaya sai ga
masu gidan, duk halaccin da suka miki da gatan da suka
miki, don kin samu ko?
Ki dube ki ki gan ki, kin san matsayinku ba daya ba da
su bare shi makiyin naki, gabansa gaban mahaifinsa gaban
'yar uwarsa da shi ne mafi soyuwa a gurinsu sun
gwammace su rasa komai a kan su rasa shi, amman ke shi
ne abin wulakantawarki.
To dubi kanki ba ki fi shi komai ba, kyau, asali, ilimi da
kudi sai ma shi ya fiki duka hudun bare ki masa isgili, har
yana bin ki shi yana sonki da kyautatawa amman ke kina
nuna masa tsana saboda iskanci da rashin hankali har da
kidahumanci.
Sam ba ki da godewa Allah a rayuwarki, ba ki san baiwa
75
3
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
da kyautar da ya miki ba, kin watsar. Shi wanda ki ke wa ba
shi da wani dalili da za ki nace masa face matsaloli dankare
a gidansa.
Sannan ni kin manta wacece a gurinki, kin manta
matsayinki kin fifita ra'ayinki a kan nawa, kin zabi farin
cikinki a kan nawa.
Kin fi son saurayi a kan uwarki, wacce ta sha fadi-tashi
da ke har kawo girmanki. Ko irin sadaukarwar nan ke ba za
ki iya ba saboda ni kawai don na ce ki aure shi ba don yana
da illa ba, sai ma ingancinsa da na ganar miki da irin farin
cikin da za ki samu a gidansa.
Saboda son da yake miki wanda ko rabin rabi bai kai
wanda ki ke wa wancan ba, amma kin rufe idonki kina ta
yin rashin mutunci ko a jikinki.
Tun farkon maganar nan nake fama da ke da lallashi da
ban baki amma har a ka daura aurennan ba ki ji za ki iya
min biyayya ba, sai rashin kunya da ba ni kunya gaban
mutane.
Har yau ki ka fito fili a kotu ki ka yi magana son ranki,
an kai ki asibiti ki ka baro ki ka zo tsakiyar titi ke za ki kashe
kanki saboda an hada ki da mai yankar naman jikinki
76
WAYE ANGON?
kullum, abin cutarwa gare ki.
Maryam Ja'afar
fara
Kina son ki kashe kanki ki mutu kafura, kije gaban
Ubangijinki wuta ta kasance makomarki, tun a nan kin
sabawa Mahaifiyarki kin sabawa Mahaliccinki, kin ki
karbar zabin da ya miki har ki ka kashe kanki.
Ba ki ma tsaya a nan ba, ki ka dawo bakin titi ki ka dinga
ihu kina kururuwa a cikin dubban mutane, saboda ki
tozarta ni ki wulakanta ni.
Bayan an saka ki a mota da kyar kin dawo gida kina
hauka da kashe-kashen abubuwa wanda ba ubanki ya sai
min su ba, ni nasa kudina na saya miki don jin dadinki, ki
ka kulle kanki ke za ki kashe kanki, har ta kai ga karshe aka
Balle kofar aka fito da ke..."
Ta tsagaita tare da mikewa ta durkusa ta dauki dorinar
dake gabanta ta nufota tana cewa.
"To sai kin fada min kwakkwaran dalilinki na aikata
wadannan, da kuma dalilinki na tsanarsa. Yau na gaji da
iskancinki don ubanki."
Idanuwanta suka fito, tsoro ya bayyana a tare da ita
saboda ganin wannan sharbebiyar bulalar, jikinta ya hau
rawa ta faraja da baya a tsorace.
77
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ba ta fasa biyo ta ba har sai da suka dangane da bango,
ba shiri taji saukar bulalar nan mai azabar zafi har cikin
Kwakwalwa.
Ta fasa wani ihu mai gigitarwa, a rayuwarta wannan shi
ne karo na farko da ta taba dukanta da bulala a rayuwarta.
Tamkar ba ita ta haifeta ba, ta dinga dukanta ba ji ba
gani iya karfinta, sai da tayi mata lilis duk ta fasa mata jiki,
jini ya kwakkwanta, hatta motsi ta bari bulalar duk ta
ciccire.
Ta dinga kuka kanta na masifar ciwo.
Ta jawo kunnenta ta matse tana cewa.
"To bari kiji in gaya miki, duk asarar da ki ka sa nayi yau
na kayan da ki ka fasa sai kin biya su tas! Sannan duk
abincin da ki ka ci da suturar da ki ka sa har karatun da ki ka
yi sai kin biyawa ubansa kudinsa, tunda ba na ubanki ba ne.
Me za ki yi da kayan uban makiyinki? Sakarya marar
mutunci."
Ta dinga kuka tana bata hakuri, hankalinta ya tashi.
Tunda take bata taba ganin fushin mahaifiyarta ba har da
dukanta.
Mabaruka yarinya ce 'yar fari, kuma 'yar auta. Ba ta san
78
WAYE ANGON?
FaMaryam Ja'afar
a
wani abin ba maganganun Maman suka bata tsoro, a
ganinta da gaske take don haka ta rude taci gaba da bata
hakuri kamar ranta.
Momyn ta ci gaba da cewa, "Auran an fasa, amma duk
abin da na lissafo miki sai kin biya su kayansu.
Ba za ki more su a banza ba, ke a ki morarki. Sannan ni
kaina daga yau ki sa a ranki ba ki da uwa, uba kadai ke gare
ki.
Za ki tattara komai naki ki koma gunsa can ku karata da
kannanki ba ruwana da ke zan manta da ke a rayuwata, kije
can ubanki ya aura miki Sulaiman din da ya fini."
Ai fa hankalin Mabaruka ya kara tashi, ta gigice ta
dinga gurza kuka tana rokonta tayi hakuri.
Ta durkusa gabanta hannu biyu tana rokonta.
"Don Allah don girmansa da zatinsa kar kiyi fushi da ni,
wallahi zan yi abin da ki ke so, na tuba wallahi zan aure shi.
Ba ni da kowa sai ke, ba ni da gatan kowa sai ke, don
Allah kar ki rabu da ni zan aure shin wallahi na yarda."
Sam taki sauraronta don ta kara tsoratata, daman tasan
za ayi haka, tasan Mabaruka da tsoro sam bata san barazana
ba.
i1
179
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Duk don ta rikitata yasa ta ce ta tashi ta bata guri ta gama
magana, tunda safe ta bar musu gidansu.
Kuma ta biya su kayansu. Mabaruka ta ki tashi tana
kukan tare da bata hakuri.
Ta ce, "Ki tashi ki ba ni guri na gama magana, tunda dai
ba kya sonsa zan nemo masa mata ya aura wacce ta fi ki, ke
kuma kije can gidan Sulaiman dinki."
Ta ce, "A'a Momy, na tuba wallahi na fasa na hakura
zan zauna da shi, kiyi hakuri in zauna da ke in na rasa ki na
rasa komai na duniya."
Haka dai ta dinga magiyar nan, karshe dai turata waje
tayi ta datse kofarta tana dariya.
Ta dinga dukan kofar tana rokonta, tsawon lokaci da ta
gaji da jan gwiwa ta nufi dakinta tana gunjin kuka.
Rafi'atu ta tashi a rikice ta rikota.
"Lafiya Mabaruka, me ya faru?" Kuka ya ci karfinta, ta
kasa fada mata.
Da kyar ta iya cewa "Na shiga uku! Rafi'a Momyna tayi
fushi da ni. Ta ce ta rabu da ni in bar mata gidanta kuma sai
na biya su komai da naci.
Wai in koma gidan Babana, na ba ni Rafi'a ba zan iya
80
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar Farhakuri da Momyna ba, ina son Mamana. Ki taimaka min a
Rafi'a."
Duk cikin kukan take fada, tana ji tana yarfa hannuwa.
Dariya ta kusan kwace wa Rafi'ar, saboda jin shirmen
da take karanto mata, an linketa baibai kuma ta linku duk
don a tsoratata.
Itama ta biye mata. Sai kawai ta hade rai ta ce, "Mun
shiga uku Mabaruka! Ya zamu yi idan Momy ta cire
hannunta a kanmu? Uwa fa ba abar wasa ba ce, ba abar
yarwa ba се."
Ta kara rikicewa ta ce, "Wallahi zan mata duk abin da
take so, ina tsoron kar ta rabu da ni ita ce gatana."
Tayi jim sannan ta ce "Gaskiya ni kaina na tsorata
Mabaruka, kan namiji ki rabu da mahaifiyarki, wacce tun
kafin ki zo duniya take dawainiya da ke?
Take tattalinki har zuwanki duniya, har yanzu ma rana
daya ki ka yarda namiji ya raba ku kin shiga uku, zai iya
wulakantaki ya juya ki son ransa.
Don ganin har ki ka iya rabuwa da ita don son da ki ke
mishi, ki rasa inda za ki sa ranki kiji sanyi ko ma ya sakoki
ki rasa in da za ki zauna ma.
81
i
1
1
1
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Yanzu ma to ina za ki samu kudin da za ki biya ta, tunda
dai Sulaiman ki ke so?
Kin ga sai a biya su sai kije ki auri Sulaiman din." Ta
fadi kan gado zaune jagwab tare da rafka tagumi hawaye na
tsiyaya, ta kasa cewa komai.
Rafi'ar ta zauna tare da dafa kafadarta ta ce, "To me ki
ka ce?" Ta juyo ta kalleta a natse tsawon dakiku.
Sannan ta share hawayen taja majina ta ce, "Shi kenan
na yarda."
Ta fito da idanuwa "Kin yarda da me? Kin yarda ki auri
Sulaiman din ki rabu da Momyn?"
Ta kalleta ta ce, "A'a na yarda zan zauna da Imran, zan
دو je gidansa a kan na rabu da Mamana."
Farin ciki ya sauka a zuciyar Rafi'a bata taba zaton haka
daga wurinta ba.
Ta jinjinawa Momy da wannan hikima tata, kafin ta ce
wani abu ta ce "Amman da sharadi."
Tayi saurin kallonta "Wanne sharadin?"
Ta ce, "Ba zai taba samun farin ciki na rana daya ba tare
da ni, da yin auransa da rashinsa daya ne, ba zai ga amfanin
auransa ba.
82
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Nayi alkawarin ba zan taßa ba shi farin ciki ba wallahi."
Ta fada cikin kakkausar murya, idanunta sun rikide.
Bin ta take da kallo kawai, abin ya wuce maganarta, ta
nisa can ta ce, "Amman Mabaru..."
Ta dakatar da ita ta hanyar daga mata hannu "Bana son
cewa komai dinki, amincewata ake bukata kuma nayi ba
wani abu da za kuma ku ce."
Zata sake magana kenan ta mike tare da ficewa daga
dakin cikin sauri don kar taji wata maganar.
A haka suka kwana wannan ranar, tun kuwa da asuba ta
tafi dakin Momyn a marairaice ta durkusa gabanta inda ta
sallame sallah.
Ta ce, "Don Allah Momy ki janye maganarki, wallahi
na yarda na amince da auransa, ina sonki bana son rabuwa
da ke."
Matuka taji dadin hakan, amman a fili sai ta ce, "Ni na
riga na gama maganata, ba neman amincewarki nake ba,
hukunci ne na riga na yanke.
Lokaci ya kure miki, lokacin da nake son amincewar
taki ai wulakanta ni ki kayi.
Imran dai ba zai rasa matar aure ba kusa-kusa ba da nisa
83
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ba a satinnan. Ke kuma kije ki auri Sulaiman dinki."
Ta fara rudewa, ta fashe da kuka tana rokonta. Sam!
Momy ta ki saurarenta, sai da taga da gaske har a ranta ta
amince da auran sannan ta ce da ita.
"To shi kenan, na yarda amman akwai sharadi." T се,
"Na menene?"Momy ta ce da ita.
"Zan fada miki amman sai kin je yanzu da kanki wajen
Imran din kin fada masa kin amince da auransa har
zuciyarki ba don an tilasta miki ba, kuma ba cikin fushi ba."
Tayi dif! Tana jin nauyin hakan. Ta sake cewa "Ko ba za
ki je ba kin fasa?"
Ta girgiza kai "A'a." Ta fada da sauri, sannan Momy ta
ce, "To mike kije."
Ta mike jiki a mace, zuciyarta cike da takaicin hakan.
Kan dole ta doshi dakin nasa.
Ta shiga yin knocking. Shi kuwa ya koma bacci kenan
ya dauke shi, ya ji dukan kofar.
Daga kwancen ya ce "Waye?" Ta ce, "Ni ce." Ya yi
matukar mamakin jin muryarta, amman ya sake cewa "Ke
ce wa?"
Ta zumburo baki tare da hararar kofar tamkar shi ne a
84
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
tsaye a gun. Ta ce cikin kufula "Ni ce Mabaruka." Ya yi
murmushi tare da dirowa daga gadon ya tunkarota.
Yana bude kofar ta wuto ciki da sauri, ya maida ya kulle
yana mamakin zuwanta da sanyin safiyar nan.
Ya zauna bakin gado yana kallonta, ya ce "Lafiya
Mabaruka na ganki yanzu?"
Tayi shiru kanta a kasa, sai kuma ta ce "Daman
Momy..." sai kuma ta fasa cewa daga Momyn tuna yanda
suka yi da ita.
Tayi cak! Tana tunanin ta ya za ta faro maganar?
Ya ce, "Ina jin ki, menene?" Ta dan dago ta kalle shi,
kiftawar ido ta kuma dauke kanta ta ce.
"Daman nazo in fada maka na amince." Ya ce "Kin
amince da me kenan?"
Haushi yazo mata wuya, don me yake son kureta? Ta
dai daure da kyar ta ce "Da aurenka."
Abin yazo masa kamar daga sama, ya aka yi haka to?Ya
dubeta ya ce, "Me yasa ki ka amince? Ko an tursasa miki
ne?"
Tayi saurin cewa, "A'a, don kaina ne kawai.”
Sam bai yarda ba, duk yanda aka yi aikin Momyn ne,
85
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
amma shi ya sani ba don son kanta ba ne, amman sai ya ce
da ita.
"Nayi mamakin hakan, idan na fahimce ki, kina sona
kenan?"
Sam bata da amsar da zata ba shi, ba za ta ce eh ba, ba
zata ce a'a ba kuma.
Ya sake nanatawa. Tayi mai banza kanta na kasa. Ya yi
murmushi iya fuska ya ce, "Shi kenan na gode."
Daga fadin haka tsam! Ta mike tare da cewa "Na tafi."
Ya daga kai yana kallonta tare da cewa, "To sai anjima." Ba
ta ce komai ba ta wuce da sauri.
Ya girgiza kai tare da komawa kan gadonsa abinsa.
Koda taje gun Momy ta fada mata yanda suka yi ta ce,
"Shi kenan, in ma ba haka ba ne zan tambaye shi, kuma zai
gaya min komai."Ta ce, "Eh na yarda."
Ta ce, "To sharadin da zan kafa miki ba wani abu ba ne
mai wuya, tunda har ki ka amince da auransa ya zama dole
ki siffantu da matarsa.
Ki masa aikin da duk mata take wa mijinta, ki ba shi
farin ciki ban ce ki bakanta masa ba.
Dole ne ki girmama shi da biyayya, yi masa da'a da
86
WAYE ANGON?
ganin girmansa,ban da rashin kunya.
Maryam Ja'afar
Duk abin da ya bukata kiyi masa ba cikin fushi ba, ba
kuma cikin bacin rai ba. Duk abin da yake so daga gare ki ki
ba shi, ba tare da ya 6ata rai ba.
Ko ya sake nanata miki, ai kin fahimce ni?" Ta daga kai
kurum tana kallonta.
Ta ce, "Kije ki rike wadannan, sauran kuma zan fada
miki idan naga yanayin zaman naki, da kaina zan zo."
Та се, "Тo." Can cikin makoshi.
Ta gama jaddada mata da ja mata kunne, daga bisani ta
ce "Tashi ki bani guri ki shirya duk abin da ki ke bukata da
yamma za a tafi dake."
Ta mike ta fice tana ji tamkar ta fasa ihu. Ta bude kofar
ta shigo a sanyaye ta maida kofar ta datse.
Ta jingina jikinta tare da daga kai sama tana jin wani
daci-daci a ranta, miyan bakinta ya bushe kam!
Hawaye masu dumi suka gangaro kumatunta, ta ce "Ya
Allah! Allah ka san zuciyata, ka san bana son mijin da aka
daura min aure da shi.
Allah ka san wanda zuciyata take so, Ya Allah ka kawo
min agaji cikin gaggawa kafin zuwa yamma. Allah kada ka
87
WAYE ANGON?
bari a kai ni gidansa, zan cutu wallahi zan cutu.
Maryam Ja'afar
Ba na sonsa, ko kadan ba zan yi farin ciki da auransa ba,
shima ba zai yi farin ciki da aurena ba, illa 6acin rai da
takaici.
Bana son na dauki zunubi Ya Allah ka gaggauta canza
min da Sulaiman Ya Allah. Wallahi bana sonshi." Ta fada
tare da fashewa da kuka mai karfi tare da durkushewa a
Kasa tana ci gaba da gunjin kukanta.
Duk Rafi'atu tana jin ta ta idar da sallah kenan ta koma
ta kwanta, ba ta san ma me zata ce mata ba in ma za ta ce din
ba zai wuce lallashi ba da ban hakuri.
Ita kuwa a wannan lokacin ba zata ji hakuri ba bare
lallashi, mafita take nema.
Don haka babu amfanin ba da hakurin. Tayi
kwanciyarta kawai ita kuwa tana ci gaba da kukan tayi
goho har tana hadawa da dukan tayils din.
Ganin kukan nata ya ki karewa ne yasa ta sauko daga
gadon cikin damuwa.
Ta dagota ba tare da ta ce da ita komai ba, suka zauna
tare a kan gadon. Idanunta taf da hawaye, sun yi jajur.
Hawayen na zubowa ta dubi Rafi'ar zata yi magana ta
88
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
tare ta "Ya isa, ya isa na sani nasan matsalarki ba sai kin
fada ba."
Ta ci gaba da kallonta tana rera kukan. Ta ce, "Imran
ko?" Ta ďaga kai da sauri "Eh."
Tayi shiru ta rasa ma me zata ce, tajawota jikinta ta dora
kanta saman kafada cikin lallashi tare da sa hannu tana
share mata hawayen.
"Ya isa haka nan Mabaruka, kukan nan ba shi da dadi,
kuma ba magani zai miki ba.
Addu'ar dai da ki ka yi ita ce mafitar tunda kin gaya wa
Allah ki sa ido ki gani."
Ta dago ta dubeta ta ce, "Ina jin tsoro Rafi'a bana son
zuwa gidansa, me yasa ya ki hakura da ni ya kyale ni ya
nemi wata?
Har sai da ya shiga tsakanina da mahaifiyata har tana
Kokarin fushi da ni don dole tasa na amince da auransa.
Wanne irin bala'i ne wannan? Me yasa dole sai ni?" Ta
Karasa da kukan tana kallonta.
Ta ce, "Wannan ba ni za ki tambaya ba Mabaruka, shi za
ki tambaya. Ya san me yasa ya nace sai ke din.
Wallahi Mabaruka ina yo miki wani hange a gidansa
89
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
abinda nake hasashe irin yanda zaman naku zai kasance da
shi yakan ba ni sha'awa da marmarin lokacin.
Na kan ji na kagara lokacin ya yi, ke kanki sai kin yi
دو mamakin yanda ki ka zama haka a kansa, bare mu kuma...
Ta katseta "Kina ganin har zan je gidansa ne ki ke min
wannan mugun fatan?"
Tayi murmushi tana kallonta ta ce, "Shi kenan, ba za ki
taba ganewa ba a wannan lokacin za ki same ni ni na
sani..."
Ta ce, "Ya isa Rafi'a, bana son maganar nan ki bani
mafita da shawara." Ta ce, "Ai tuni kin ba kanki tunda kin
amsawa Momy to ni wace mafitar zan ba ki ko shawara?"
Tayi jim sannan ta nisa tare da share hawayen ta ce, "Shi
kenan nasan me zan yi."Ta ce tana kallonta.
"Me za ki yi kenan?"
Ta ce, "Za ki gani." Ta ce, "Shi kenan Allah yasa in ga
alkhairi abin da nake zato."יי
Ta ce, "Wai shi ne har Momy take cewa in hada abin da
zan bukata har wnai shiri zan yi a yanda nake kawai su zo
su tafi da ni."
Ta ce, "Sosai ma shirye-shirye ga ma magungunanki
90
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
can da Mama ta dafa miki suna jiranki, jiya naji ta ce yau ko
gobe za ta dafa 'yan shilan da ciccibi."
Wani abu ya tokare a ranta, jin wannan zancan da Rafi'a
take yi mata a yanzu.
Wallahi ba abin da zata ci ko tasha, tunda ba wannan ya
kai ta ba gidan, tir! Allah ya tsare.
Mikewa tayi tsam! Ba tare da ta ce komai ba ta shiga
bayi don zubar da miyan da ya taru a bakinta.
Dariya kawai Rafi'a tayi ta bita da kallo.
**
KARFE 4:07 NA DARE
Su Anti Karima tuni suka hallara a wannan ranar tare
da wasu dangin Momy ba daya daga dangin Babanta.
Tunda safe mai gyarata tazo, tun safen take tsaye kanta
na gyaran jiki, ta zuba mata lalle aka gyara mata gashin
kanta, wanda aka nannade shi ya yi kyau sai tashin kamshi
yake.
Ballantana kuma jikinta tamkar an zubar da turaruka,
jikinta ya yi kyau jikin har wani sulbi yake.
Ba abin da