An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
HNL WAYE ANGON
Maryam Jafar Kađuna
HAUSABOOK.COM
WAYEANGON?
2
Na
Maryam Ja'afar Kaduna
Mrs: Khabeer Abdullahi
WAYE ANGON?
ne yabaku girman.
M. umma Muhammad
M. khadija Musa Rimi
M. rukayya madani
Maryam Ja'afar
Ubangiji ya saka muku da mafificin alkhairi yaja kwana
Ameen.
NIMA GA NAWA ANGON
In har mabaruka tasan angonta ta kuma rike gam ni me zai
hana bazan rike nawa ba, ya zama dole inyi Babbar
gaisuwa da jinjina in bada girman ga wanda Allah ya ba.
dukkan alkhairin duniya da na lahira Allah ya baka Angona
Muhammad Kabeer Abdullahi, Ubangiji Allah ya bar
kauna Ameen.
INA YA “YANA?
Umar, Muhammad, Aisha, sahalu, khairat da yusra.
Allah ya rayaku bisa tafarkin gaskiya ya albarkaci rayuwar
ku da sauran yayan musulmai Ameen.
BABBAR KAWA
Hauwa'u Muhammad godiyata ba adadi kin zama yar uwa
Allah ya kara dankon zumunci ya yara mana su husna
Ameen.
4
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
1
WATA JINJINAR
Dole ne in yi godiya da jinjina ga yar uwa abokiyar aiki bisa
kokarinki gareni da soyayya bazan manta ba ubangiji Allah
ya cika mana burinmu Ameen
Humaira khalil Adam marubuciyar INA SIRRIN YAKE?
ALKALAMAWA (gidan fasaha)
Ban cire kowa ba gaisuwa ta musamman da jinjina gareku
marubutanmu bisa kokarinku na dabbaka harshen hausa da
gyaran zamantakewa. Allah yaja nisan kwana ya daukaka
aikalummanku Ameen
"YAN UWA DA DANGI
Ga gaisuwata gareku na miko da fatan alkhairi jerin
sunayenku bazai jeru ba ana idan ko harnace sai haka to
tabbas zan cika littafin wani mabai samu shigaba ga adduar
zumunci nan soyayya da kaunar juna Allah ya karo mana
ya hade kawunanmu ya dorar da zumunci me dorewa
Allahumma Ameen.
5
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
wana daya ya rage a koma kotu, don haka a nan Kta kwana daga nan suka wuce kotun ita da
Maman Rafi'ar sai Rafi'atun.
MUJE ZUWA MU JI ME ZAI FARU A KOTUN?
WAYEANGON? WA KOTU ZATABAMATA?
A KOTU
Bayan an gama sauraron Karar wasu an kammala,
sannan aka gabatar da tasu.
Alkali ya bukaci ganin amaryar wacce kanta ake
wannan hargitsin, ina ma amaryar take?
Jikinta ya hau rawa zuciyarta ta karye, a marairaice ta
dubi Rafi'atu dake gefenta ta ce, "Ina jin tsoro Rafi'a ba zan
iya fita ba in tsaya gaban dubban mutanennan duk a tsira
min ido wallahi ina jin kunya Rafi'a.
Ta riko hannunta ta ce "Ki nutsu Mabaruka, ki cire
komai a ranki ki dauka ba kowa a nan ke kadai ce. Ki fita ki
bayyana gaskiya da abin da ke ranki, kar ki 6oyewa kotu
komai don za tai miki adalci ta ba ki mijinki da ya fi dacewa
da ke, kilan ma kiga Sulaiman za a ba.
Amman idan ki ka yi sanya ki ka tsaya kunya ko tsoro zà
ki rasa shi, ki rayuwa da makiyinki. Fadin hakanne yasa ta
6
WAYE ANGON?
samu kwarin gwiwa, zuciyarta tayi kwari.
Maryam Ja'afar
Don haka bata jin komai ta mike ta tunkari inda ake
tsayawa, Alkali ya dubeta ya ce, "Ko za ki gaya mana
sunanki da ko waceсе?"
Ta ce, "Eh! Sunana Mabaruka, kuma ni ce amaryar da
ake rigima a kanta.
Na taso karkashin kulawar iyayena guda biyu, Mamana
da Babana, a gun matar Babana na taso amman na kan je
gun Mamana.
Nayi karatun Firamare da Sakandire masu kyau da
tsada, duk daukar nauyin mijin Mamana, wato Baban su
Imran har zuwa yanzu da nake karatuna a Jami'a, ina kuma
shekarar karshe a karatuna.
Na taso cikin gata da jin dadi, komai na rayuwa ina
samunshi ba na rasa komai.
Na kan je gidan Mamana nayi kwana biyu ko uku, haka
gidan Babana har zuwa yau da nake kusa da gamawa
Babana bai taba ba ni ko Naira goma ba in sayi fensir.
Duk wani abu na dawainiyar karatuna ba ya yi, duk idan
na bukaci wani abu gun sa sai ya kama fada, in bar shi ya ji
da dawainiyar gabansa na kannena, dangane da ciyarwarsu
7
WAYE ANGON?
me zan ji da karatu ni da nake mace aure zan yi.
Maryam Ja'afar
Haka dinki ko silifas, ko da da sallah ne yanda uba yake
dagewa kan kayan sallar 'ya'yansa, to ban da Babana komai
sai Mamana ita ke min ko mijinta Baban Imran, hakan yasa
nafi zama a gidansu Imran din.
Ya yi karatunsa a Ingila na Pilot tun kafin ya tafi muka
shaku da juna, Imran ya koya min cin dadi da 'yan tandetande duk in da yasan idan ya kai ni zan ji dadi, to zai yi
kokarin kai ni,ga sayen abubuwa na yayi ko naci ko na ado.
Lokacin da zai tafi karatunsa nasha ciwo bayan
tafiyarsa ban saba da rashinsa ba, zan wuni 'ba kuzari in
wuni a kasalance, ba zan ci komai ba duk sanda na dauko
abinci zan ci na kan tuno shi, hakan yasa sai in ta kuka
saboda dashi muke cin abinci plate dinmu daya cokalinmu
daya.
Na koyi abubuwa sosai gun sa dangane da karatuna,
boko da Islamiyya, shakuwa sosai mu kayi dashi.
Gefe ita ma Sharifa 'yar uwa ce kawa ce aminiya ce gare
ni, duk idan tazo muna tare ina jin dadi idan Sharifa tazo sai
in rasa inda zansa raina don dadi su sani tsakiya kowa ya na
bani tashi kulawar,
8
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Shi kuma Sulaiman tashin farko yakan zo gidanmu
kusan kullum yana yawan tsokanata da dan min tsaraba, da
dama yakan kira ni da matas!
Daga haka abin ya faru, ban san ya aka yi ba na fara son
shi ba har muka yi nisa.
Gefe kuma muna tare da Imran amman har lokacin ban
san me yake nufi da ni ba.
Koda Babanmu ya ji magana ta da Sulaiman ya yi farin
ciki da murna yaiwa Sulaiman din albishir da ya bada ni
gare shi ko bayan ransa.
Inna ma tayi murna matuka da hakan ko don ta sanni na
kan yawaita mata alkhairi in dai ina gidan, musamman idan
tana wa Babana tijara kan kudi nakan biyata fiye da yanda
yaci hakan yana mata dadi sosai, shi yasa muke shiri da ita.
Ni kuma abin da take ma Babana bana jin dadinsa
hakan yasa na ke maganinta da kudi.
Wata rana Imran ya dawo ofis, kamar yanda na saba da
zaran ya dawo zan taro shi in raka shi har daki tamkar wani
mijina in ya cire riga in rike masa muna yi muna hira muna
dariya.
Ranar ma haka ta kasance ya dube ni cikin fara'a ya ce,
9
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
"Lallai kina ji da ni, sai ka ce wani mijinki irin na dawo
dinnan ko?"Ya fada yana kallona yana dariya.
Ban fahimce shi ba nima nayi dariyar nace manta da
wannan maganar yau ne zamu je wajennan da ka сe ko?"
Ya zasro ido ya ce "Ina?" Na turo baki cikin shagwaba
na ce, "Kana sane fa tun yaushe muka yi maganar nan don
Allah?"
Ganin kamar zan yi kuka yasa ya ce, "Is ok, naji na sani
tsokanarki nake, zamu je anjima.
Nayi dariya tare da cewa, "Thanks my dear bro."
Ya yi murmushi kawai yana kallona cike da sha'awar
yanayi na gefe kuma yana wani tunanin.
Na katse shi "Ka san me?" Ya bazo kunnuwa ya ce, "A'a
menene?" Nayi dariya na ce "Ba ka tambaye ni me na girka
maka ba?"
Ya ce, "Sorry, na tambaya yanzu me ki ka girkawa
tumbin yayan naki?" Nayi dariya tare da make kafada na ce
"Um'um idonka zai baka labari, amman nasna za ka yi farin
ciki."
Ya ce, "Na sani duk abin da za ki, za ki yi don farin
י cikina, zai sa ni farin ciki am sure.
10
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Tare muka ci abincin yana santi, a kullum yakan
tambaye ni wai ina na koyo girke-girke, shi wallahi bai taba
cin abinci irin nawa ba. Na kan ce abin sirri ne amman zan
fada maka.
A kan hanya muna mota shi ke tuki, ina gefe dukkanmu
mun sha kwalliya, labari muke amman naga ya yi shiru.
Na dube shi na ce, "Ya Imran!" Ya nisa tare da kallona
na ce "Lafiya, me ke damunka?"
Ya kalle ni da kyau ya ce, "Kina son ki sani?” Na daga
kai tsaye ya ce "Aure nake son yi Mabaruka."
Na fito da idanu da bude baki cikin murna na ce "Aure
Ya Imran?" Ya ce, "Sosai, kin yi mamaki?"
Nayi dariya na ce "Dole abin mamaki ne mana, nifa ban
taba jin kayi maganar mace ba bare aure, a tunanina ko ma
ba za kayi auren ba a rayuwarka."
Ya zaro ido ya ce, "So ki ke in mutu kenan? Ina! Ba zan
iya ba." Nayi dariya ina kallonsa cikin mamaki na ce, "Don
ba ka yi aure ba sai ka mutu?"
Ya ce, "Of course! Son da nake wa yarinyar zai iya
hallakar da ni." Na kalle shi na ce, "Wannan wace 'yar
baiwar ce ka ke so har haka daidai da ranka?"
11
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ya yi dariya sosai tare da dukan sitiyarin motar ya ce,
"Kina son sanin wacece?" Na ce, "Eh!" Ya ce, "Kin santa
ai."
Na ce, "Na santa! Wacece?" Ya kalle ni a nutse kamar
ba zai fada ba sai dai naji kamar daga sama, ya ce "Kе се
mana."
Na kalle shi da sauri na ce "Ni kuma big bro?" Ya ce,
"Ke Mabaruka." Yanayina ya sauya na ce "Please! Ya
Imran ka daina tsokanata, ka san ba ma haka da kai, ka faďa
min kawai wacece?"
Na karasa ina dariya fuskarsa ba wasa ya dube ni ya ce,
"Mabaruka!"Na kalle shi tare da amsawa. "Na'am!" Ya ce
"Ba wasa nake miki ba, tunda kin ga ban taba miki irin
wannan wasan ba."
"Wallahi da gaske nake, ina sonki tun ba yau ba, tun
kina Sakandire aji daya (SS1), kusan shekara shida kenan,
kuma wallahi aurenki zan yi serious (da gaske)."
Fuskata ta sauya sosai, na ce “Ka bari Ya Imran, bana
son wasa fa."
Ya ce, "Na fada miki da gaske nake, kina maida magana
baya. Cikin week din nan zan kai maganar nan gun su
12
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Daddy, ba wani bata lokaci za a yi ba in aure ki in kai ki
gidana.
Kin ga shi kenan hankalinki kwance kin san wa za ki
aura, Imran din ki ne da ki ke tattali, tun-tuni sai ki zarce na
tabbata hakan ba zai miki wuya ba tunda kin saba."
Tun da ya fadi maganar nan bakina ya kulle, jikina ya
mace, na rasa me ke min dadi.
Har muka je muka dawo ba ni da kuzari.
Na zo kwanciya tunanika suka rufe ni, wai me hakan ke
nufi? Shin anya Imran yasan so ma kuwa? Kawai don yaga
muna dan raha da wasa sai ya ce so wai yana sona?
Kai! Ina bai san so ba, ni dai nasan ina son Sulaiman
don haka gwara tun wuri ta taka masa burki kar abun ya yi
nisa a ransa bare su Daddy su sani.
Ban yi tunanin komai ba na tunkari dakinsa ya fara
shirin kwanciya ya ganni.
Na wuce shi inda ya bude min kofar na zauna kujerar da
ke dakin na zauna a sanyaye.
Ya dawo ya zauna kan gado yana facing dina ya ce cikin
damuwa my dear me ya faru?
Kalmar ba ta min zafi saboda haka muke kiran junanmu
13
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
amman wannan lokacin sai naji zafinta sam bata dace ba, ta
fito daga bakinsa ba na ce a tausashe.
"Ya Imran!" Ya ce, "Na'am, menene?"
Na ce, "Magana nazo muyi da kai."Ya ce, "Ok, ina jin
ki menene?" Na daga kai na kalle shi ganin yanda ya maida
hankalinsa gabadaya gare ni yana saurare.
"Maganar da ka min dazu ce nake son mu tattauna." Ya
ce, "Ok." Na ce "Maganar gaskiya Ya Imran ba ka fahimci
so ba, ko don baka taba yin shi ba, amman wallahi ba sona
ka ke ba kawai dai mun shaku ne, nima haka ba na sonka."
Maganar ta ba shi mamaki, amman ya ce "Mabaruka
kenan! Ke yarinya ce, a tsawon zamanmu da ke ya kamata
ki fahimta ko don wasu abubuwa da nake miki, amman da
yake yarinya ce ke kin gaza fahimta, har na fito yau na fada
miki. Tabbas ina sonki, kuma kema kina sona."
Na dago ina kallonshi na ce, "A'a Ya Imran ba haka ba
ne, kar maganar nan tayi tsawo mu barta a nan, ka cire
maganar so tsakaninmu, don ba zai kasance ba, bana jin
sonka a raina, wallahi akwai wanda nake so, don Allah ka
fahimce ni."
Idanunsa suka kaďa jajir, ni nasan bacin rai ne amman
14
S
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ya dake ya ce "A'a Mabaruka, to ba wani wanda za ki so sai
ni, in ma ba ki so to ki kokarin sa shi a ranki, don jin
dadinmu ni da ke, wallahi da gaske nake ni dai ina sonki."
Na mike tsaye na ce, "Don Allah Ya Imran ka bar
tsokanata, wallahi akwai wanda nake so."
Shi ma ya mike yana cewa "Ba na tsokanarki ni dai ina
sonki zan aure ki kema za ki gane hakan a hankali, zan koya
miki."
Wucewa nayi ina cewa, "Ni dai na fada maka ka daina
daukar abin wasa, wallahi da gaske nake."
Ya biyo ni zai rufe kofar yana cewa, "Ni ma ba da wasa
nake ba, ina sonki ki sa haka a ranki."
Ban iya cewa komai ba na juya nayi wucewata zuwa
dakina, ya rufe kofarsa ya koma ya kwanta hankalinsa
kwance.,
Tun daga wannan ranar alakarmu ta canza da shi, muka
rage walwalar da muke da shi duk da yanda yake kokarin ja
na. Abu kamar wasa ganin yanda ya dage yana sona.
Hakan yasa na dage nima ina nuna masa ba haka ba ne
ni ba na sonsa, bai gane ba, har na fara nuna masa tsantsar
tşanarsa, kamar yanda nake jinta a raina, har kawo yau ba
15
WAYE ANGON?
abin da ya canja.
Maryam Ja'afar
Alakata da shi ta roshe haka, alakata da Sharifa bayan
tazo bikin, yayin da soyayyarmu da Sulaiman take karuwa
tsakaninmu mahaifiyata ta dage a kan lallai sai na aure shi.
Yayin da shi ma Babana ya dage lallai sai na auri
Sulaiman, saboda shi ya ba aurena.
A tunanina jahilci ne ke dawainiya da su har suke son
aura min maza biyu da kafiyarsu, sam ba sa jituwa motsi
kadan zai zagi Mamana, duk bakin cikinsa ta bar gidansa ta
koma gidan wani Alhaji tana more rayuwarta me dadi da
nishadi ta bar shi a wahala da talauci.
Ita kuma take jin haushinsa a kan wuyar da tasha
gidansa da wulakancin da ya mata, kamar yanda take fada
min kullum, amman bata taba fada min ya aka yi suka rabu
ba, amman takan ce ta sha wuya gidansa.
Nayi iya bakin kokarina na fahimtar da su a kan abin da
suke kokarin yi ba kyau, ba a taba yi ba, sam ba su
saurarona kowa ya dage a kan burin shi a ganinshi shi ke da
gaskiya.
Hakan yasa nayi yunkurin kai su kara kotu, tunda ba su
da magabatan da za su musu fada, kawata Rafi'a ita ta hana
16
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
ni sannan naso na gudu shima nan ta hana ni ta tsare ni a
gidansu.
Yayin da su kuma suna can kowa na kokarinsa suka
kuma sa ranar auren duk rana daya. Har dai suka daura min
aure da maza biyu har zuwa yanzu."
Ta kalli Alkalin ta ce, "Wannan shi ne cikakken ko ni
wacece da yanda abin ya faru gare ni."
Nan fa kotu ta hau kace-nace.
Bayan an nutsu Alkali ya fito da angwayen, Sulaiman
da Imran, kowa yai ma kotu bayanin wanda ya daura mai
aure, kuma ya bada sadaki.
Duk tambayoyin da ya kamata kotu tayi musu tayi ta
gamsu da duk bayanansu.
Ta bukaci a bata kwana biyu kan ta yanke hukunci, don
haka a haka aka tashi kotun.
Wannan karon ma gidan Momy ta koma, a mota ta ci
gaba da yiwa Rafi'a, korafi kamar zata yi kuka.
"Wallahi na gaji Rafi'a, na kagara a yi ta ta kare, in san
matsayina, na gaji dajelangen nan na kotu."
Ta ce, "Haba! Kada ki damu, jibi ne fa kawai. A jibin kai
tsaye gidanki za a zarce da ke, magana ta kare ko gidan
17
rו
WAYE ANGON?
Sulaiman ko gidan Imran."
Maryam Ja'afar
Idanunta suka fito hankalinta ya tashi, idanunta suka yi
rau-rau, ta ce "Ya Allah kada kasa aure tsakanina da Imran,
Ya Allah ka sa Sulaiman shi neANGON Ya Allah."
A haka suka isa babu kuzari jikinta, ta haye gadonta tayi
lamo zuciyarta da sake-sake dankare da zullumi.
A nan suka wuni da Rafi'a tana kara kwantar mata da
hankali, sai gaf da Magriba sannan Rafi'ar ta tafi gida.
Bayan ta rakata ta dawo, daidai kofar falo suka ci karo
da Imran ya tare mata kofar yana kallonta fuskarsa dauke
da fara'a.
Tayi kicin-kicin da fuska tamkar bata taba dariya ba,
ranta ya baci matuka ta dago tana harararsa, yayin da shi
yake dariya shi kansa yasan ya jawa kansa fada ne.
Ta ce cikin fushi "Matsa ka bani guri." Ya dage kafada
alamar a'a bata saurare shi ba tayi kokarin rabewa ta
gefensa ta wuce.
Nan ma ya tare, ta dawo ta dayan gefen nan ma ya fake.
Tazo iya wuya, ji take kamar ta shake shi ta huta gabadaya.
Tsawon mintoci suna haka, ganin da gaske yake ba zai
matsa ba ga wani tukuki da take ji a ranta tsayawa kusa da
18
ン
WAYE ANGON?
shi da tayi, kawai ta juya baya abinta.
Ya bi ta da kallon ina zata je.
Maryam Ja'afar
farGefe ta koma ta zauna a harabar gidan tana 'yan harareharare da fushi, bai daddara ba ya kara binta can din.
Tsugunnawa ya yi gabanta har suna jin numfashin
junansu, kamshinsu ya hade da juna ta dago tana kallonsa
cikin tsananin tsanarsa shi ma ita yake kallo cikin yanayi na
kaunarta ya ce da ita.
"Wai menene haka Mabaruka? Guduna ki ke don ba
kya sona ko?"
Kai tsaye ta ce, "Eh, amman ka kasa gane hakan bare ka
kyale ni na huta, zuciyata ta huta da matsananciyar tsanar
da take maka."
Ya yi shiru yana kallonta zuciyarsa tana masa ba dadi,
ya ce "To me yasa? Meye abuna me na rasa da har zuwa
yanzu na gaza zama masoyinki.
Kullum kina furta min kiyayya, ina ganinta a idonki me
yasa Mabaruka?"
Idanunta suka kada kamar zata yi kuka ta ce, "Haka nan
babu wani dalili Allah ne yasa min haka ba daga ni ba ne
amman ka ki fahimtar haka ka kyale ni don ba mu dace da
19
1
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
juna ba sam bare zamantakewar aure ta yiwu tsakaninmu."
Zuciyarsa ta kara yin daci bakinsa ya yi nauyi da kyar
ya iya cewa "Mabaruka, Allah ya jarabce ni da
matsanancin sonki ban san ya zan misalta miki ba bare ki
tausaya min yanda zuciyarki take miki ba dadi da
. azalzalarki a kan kiyayyata.
Haka nima tawa take azalzalata da sonki, a kullum kara
min sonki ake, wallahi Mabaruka ba zan iya rayuwa idan ba
ke ba, bare na iya hakuri da ke ta harararshi tamkar ta kife
shi da mari, sannan ta ce "Kana Kara wahalar da kanka ne
ka sawa kanka hakuri da dangana, aure tsakanina da kai ba
zai taba yiwuwa ba, har abada saboda Allah bai rubuto
hakan ba tsakaninmu."
Cikin kwarin gwiwa ya ce, "Ni kuma ban taba sawa
raina ba, ba zan same ki ba a kullum ganina nake tare da ke
muna rayuwar aure tare da 'ya'yanmu cikin farin ciki da
walwala.
Ta kalle shi da kyau ta ce "Ba za ka taba ganewa ba,
zuciyarka na yaudararka da mahaukacin tunaninka, ni dai
nasan ba zan aure ka ba, kaje kai ta haukanka."
Daga haka ta mike ta wuce cikin gidan da sauri tamkar
20
WAYE ANGON?
wacce za a kamo.
Maryam Ja'afar
Far
Ya bita da kallo cikin sha'awar tafiyarta, musamman da
take saurin nan sai tai masa kyau a ido matuka, yayi
murmushi tare da mikewa ya wuce inda motarsa take yana
cewa, "Zan kama ki yarinya." Ya shige abinsa ya fice daga
gidan.
Da dare wajen karfe tara har ta gota sannan ya dawo.
Momy ce a falo, ita kuma Gimbiyar tana dakinta ita ba
bacci ba ita ba kuka ba.
a
Haka zalika ba tunani ba, zuciyarta taki ta barta ta huta
saboda zullumi bata san me jibin zata haifar ba, meye
cikinta? Farin ciki ko bakin ciki, rayuwarta ko mutuwarta?
Ba abin da ke mata dadi tun tsawon ranar bata sa ko
kwayar ruwa a bakinta ba bare abinci, haka take. Ko kadan
ma bata jin yunwar.
Ya zauna cike da gajiya yana fadin wash! Ya cire hula
yana sosa kai, Momy ta bishi da kallo tana cewa "Gajiya
ko?"
Ya ce, "Wallahi amman yunwa tafi yawa." Ta ce, "Ah
lallai kam ai ga abinci can a dinning ba ma wanda ya tabа
shi tunda aka gama."
21
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
Ya dubeta yana cewa "Saboda menene ba kowa a gidan,
ina Mabaruka?" Ta cě, "Tana cikin daki, tun dazu nake
fama da ita taci abinci, ta ki har na gaji na kyaleta, idan ta
tantance ta fito ta nema don kanta."
Sam baiji dadi ba, jikinsa ya kara mutuwa.
Mikewa ya yi yana cewa zan shiga ciki in dan watsa
ruwa, ki sa Mabarukar ta kawo min abincin da dan lipton, ta
ce, "To."
A daki ta samu Mabarukar kwance ta taso ta suka fito.
Tana zama kan kujerar ta ce "Kije ki hado abinci a tire da
lipton.
Ta kalli Momyn fuskarta da fushi ta ce nifa bana jin
yunwa. Ta ce, "Na sani daman ba ke nace ki hado kanki ba,
kije kiyi abin da na saki."
Ta amsa da "To." Sannan ta wuce.
Tayo yanda ta sata, ta kawo mata. Ta dube ta ta ce "Kije
ki kaiwa Imran dakinsa."
Ta kalleta da sauri cikin tsoro ta zumburo baki tamkar
zata yi kuka "Ni fa Momy..."Ta katse ta "Ba dole, idan ba
za kije ba aje ni sai na kai masa."
Tasan gatse ta mata. Ji take tamkar ta fasa ihu wai me
22
WAYE ANGON? Maryam Ja'afar
fara
yasa ita aka tsaneta ake son kusantata da wannan makiyin
nata? Ko dai ba a san numfashinta.
Yanzu abincin ma sai an sa ta ta kai masa bayan a
dinning ya saba ci kawai don a fata mata rai. Ta wuce
kamar zata yi kuka, idanunta sun taru da kwalla, ta shiga
kwankwasa kofar.
Ya fito daga wankan daga shi sai short niker yana sane
ya ki suturta jikinsa sabanin da da ba zai taba yarda ta same
shi a haka ba, yanzu ta zama matarsa, kun ji fa!
Ya zo ya bude mata fuskarsa dauke da murmushi, bata
ko kallonsa bare tasan ya yake ta zunguro masa tiren tana
kumburi ta ce, "Gashi ya yi tsayen yana kallonta ya ce
"Kije ki aje ciki mana, ai ba lallai sai na karba ba."
Ranta ya kara 6aci yana raina mata wayau. Ina laifin da
ta kawo masa ma yasa hannu ya karba ba zai yi ba, sai ita ta
karasa masa da shi bai ma ga kokarinta ba? Don haka taji
ba za ta iya ba.
Tsugunnawa tayi tana kokarin dire masa a nan bakin
kofar, kafin ta aje ya ce, "Wallahi ki ka aje shi a nan ba zan
dauka ba, a nan zan bar shi har sai wuce ta turoki ki kawo
tazo ta gani inda ki ka aje na gwammace na kwanta ban ci
23
WAYE ANGON?
komai ba."
Maryam Ja'afar
Kwallar da ta taru a idonta ta sauko, tasa hannu ta goge
ta riga ta barwa kanta ba a sonta, so ake kawai ta mutu ko ta
ina mużguna mata ake ana cutarta.
Ba ta ce komai ba ta mike da abincin bata ko kalle shi
ba, ta rabe ta gabansa ta wuce cikin dakin.
Ya yi dariya yana kallonta gefe kuma ya ji tausayinta,
amman duk da haka bai