zaizo
gurinki sai ki yayyarfa turaren nan a dakinki ki
zuba a inda kika san yana zama, to da ya zo ya shaki kamshin turaren to duk abinda kika yi
masa umurnin ya yi shi zai yi babu makawa”. Ya
kare bayaninsa yana duban Goggo sannan ya
koma da bayaninsa kan Haj. Harira.
"Ke kuma 'yarki zaki ba turaren ta sa a
jikinta duk ranar da kika tabbata zai zo gurinta
idan har ya shaki kamshin farin turaren nan to
aikin gama ya gama, amma fa ku sani matarsa
da iyayenta suna tsaye a kan 'yarsu da addu'o'I,
163
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
saboda haka sai mun hada kai mun yi musu tsaye
in ba haka ba za ku dinga tufka ne su na
warwarewa, da kunga aikinmu ta a baya sai ku
garzayo a sake sabon shiri ina fatan kun gane".
Suka ce "Eh, mun gane". Ya ce,
Idan maganar aure ta taso to kafin ayi sai
an yi wani sabon aikin don yana son matarsa
sosai yana jin maganarta baya son ranta ya 6асі,
sai na dage sosai". Sai na bashi dubu ashirin, sai
kuma sun dawo za su sake kawo wasu kudin na
sabon aiki.
Sun dawo Dukku cike da murna tare da
dokin ganin zuwan Mujceb garin, domin samu
nasarar aikinsu yana da nasaba ne da zuwan
Mujeeb Dukku.
Anyi ta samun tsaikon zuwanshi garin
sabida yanayin aikinsa har sai da ya shafe sati
hudu sannan ya zo Goggo ta aikata abinda boka
tsidigu yace ta aikata, kuma Allah ya yi mata ta
talala taci nasara don kuwa tana yi masa umurnin
auren Suwaiba ya amshi maganar har ya kara da
cewa, "Ni dama ba wai na ki bin umurninki ba
ne so nake in kammala shirye-shirye na kuma na
kamala, yanzu yaushe kike ganin ya dace a yi
bikin". Goggo cike da murna ta sake yi masa
wani umurni don ta dada tabbatar la aikin boka
tsidugu taсe,
164
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
“Za mu yi shawara amma ya kamata ka je
yanzu ku gana da Suwaibar ku fahimci juna,
tunda ku ne za ku zauna da juna ba mu ba, ko
tadinma mu zamu yi muku?" Ya yi murmushi ya
ce, "zan je yanzu in Shaa Allah".
Ko ruwa bai tsaya ya sha a gidan Goggon
ba ya nufi gidan Haj. Harira don cika umurnin
mahaifiyarsa, yana fita Goggo ta yi saurin kiran
wayar Haj. Hariran tace mata "Aminiya
albishir?" tace, "Goro sahiba ya iso garin ne?' ta
ce, "Ai na gaya miki yau zai zo, to har ya zo
mun gama komai bukata ta biya, gashi nan na
turoshi gurin Suwaibar sai ki yi, azama kafin
isowarsa ki aiwatar da umurnin tsidugu don kada
a sami mishkila mu ga tangara”. Haj. Harira ta rangwada mashahuriyar guda a wayar har sai da
kunen Goggo ya so ya dode tace,
"Godiya ta tabbata ga tsidugu
(wa'iyazubillah)) yau bukatarmu ta biya, da ya
zo za a tsaida magana kin san ba za a ja lokaci
ba, tunda tsidugu ya ce aikinmu zai dunga sanyi,
kinga gara ayi abin wuta-wuta ko?" Тасс,
"Hakan ya yi daidai ke dai je ku yi shiri". Ta
katse wayar.
Suwaiban na kwance bisa gado Haj.
harira ta sameta tace, "Ke tashi maza ki shirya
dama kinyi wanka ga mutuminki nan zuwa nan
165
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gidan yau bukatarmu ta biya aikin boka tsidugu
ya ci". Suwaiba ta mike tare da doka tsallc ta
dire cike da murna tace, "Mujeeb din ne da
kansa zai zo gidan nan yau?" tace, "Shine mana,
maza ki yi ki canza kaya, bari in dauko tiraren
nan da na gaya miki ki yi maza ki sa kafin ya
iso".
Kwalliya mai sunan kwalliya Suwaiba ta
cancada, Haj. Harira ta kawo mata turaren nan ta
gumbuda shi a jikinta, ita kanta Suwaiban karfin
turaren ya bi ya dame ta irin turaren nan ne na
'yan bori me hawa ka in banda suna neman cin
galaba a kan Mujeebu da ba bu abin da zai sa ya
sa wannan turaren da ya kusa sanya haraswa.
Gama sa turaren ya yi dai dai da jin dirin
tsayuwar mota a kofar gidansu, hakan ya ba su
tabbacin Mujeeb ya iso kenan. Wani yaro ya
samu a kofar gidan yace ya shiga ya gayawa Нај.
ga Mujeeb ya zo. Yaron yana gaya mata sakon
tace ya je ya gaya masa ya shigo.
A falo ya yi sallama ya sami Haj. a zaune
ya risina suka gaisa ta tambaye shi ya aiki da
mutanen Gombe yace, "Duk lafiya lau”. Sun yi
shiru na 'yan sakonni sannan ya cc, "Gurin
Suwaiba na zo tana nan ko?" Haj. tace, "Eh, tana
ciki" ta kwalawa Suwaiban kira, ta fito tana
rangwada, ya bita da kallo shi kam har ga Allah
166
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
bai ga abinso ga Suwaibar ba don shi ba ya son
mace mai kiba sannan kibar mara fasali irin jikin
zaki daga sama kiba kasa kuma kamar
kwankwason zaki a tsuke ba duwawu, sannan
yana auren ta idan ta ji dadin cima mai kyau
dada habakewa zata yi ta cika tayi dam, ya fi son
jikin matarsa ba rama sannan bata cika kibaba
'yar daidai da ita, ga komai nata mai kyau mai
birgewa.
Ta nemi kujera ta zauna, sannan ta gaishe
shi, Haj. tace, "Tashi ki kawo masa abin sha". Та
tashi ta fita itama Haj. ta fita ta yi, tare da Haj.
suka shirya mishi juice a jug sannan aka juye
wani garin magani me kama da busasshen jinni,
wai maganin mallaka ne Haj. Harira ta yi bibaya
ita kadai bayan zuwansu da Goggo ta amso, don
a mallake musu Mujeeb din ya kasance idan an
yjauren za su mallake ragamar rayuwarsa ta
yadda ba zai ga kowa da gashi ba ko da uwarsa
ce sai Suwaiba da Haj.
Suwaibar ta shigo da tiren ta aje a
gabansa, ta dauki kofį ta tsiyaya ta mika masa ya
amsa ya yi bisimilla sannan ya sona sha, ita
kuwa ta koma ta zauna tana kallonsa tare da yaba
kyawu irin na Mujecb wanda yike cikin flanin
ma sai an tona, ga kyau ga kyan kwalliya ga
ilimi ga kudi ga kuruciya, ko da can idan ta je
167
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gidansu sam bata gajiya da kallon Mujceb, balle
yanzu da ya dada hadewa, tamkar ka surc shi ka
saka a jaka ka boye saboda kyau, ga kayan da ya
sa sun amshi jikinsa shadda ce Galila 'yar asalin,
an yi masa dinkin boda me kalar kunun kanwa.
Ya dube ta ya cc "ya karatu ance kin
gama bana ko?" ta cc, "Eh, na gama", yace, "kin
dai cinye ko, kinga sai ki fara jami'a tare da
Munceba ita ta sami Nine credit". Cike da bakin
ciki da wai Muneeba ta sami nine crcadit ta ce
"ni ban je an duba ba, amma zan je". Ta fadl
haka ne don ba zata iya gaya masa 3 credit ta
samu ba kuma ba maths ba English kenan bata
da shiga jami'a a wannan shekarar.
Suka ci gaba da hira amma zance daya
biyu sai ya sako sunan Munceba, haushi duk ya
isheta na yadda ba ya iya wata maganar arziki in
bai hado da sunan matarsa ba, yana koda ta yana
yabon halayenta sai kace ita ce macen farko mai
kyautata wa miji a duniya. A zuciyarta ta sha
alwashin sai ta raba harshensa da Ambato sunan
Muneeba, za ta maye gurbinta da nata sunan a
bakinsa dama zuciyarsa
Bai dade sosai ba ya yi sallama da su ya
tafi bayan ya yi musu yayyafin naira, Haj. Harira
da yarta aka dunga murna har da tsalle saboda
burinsu na shckara da shekaru a cikin Mujeeb
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
yau ya cika. Koda ya koma gidan Goggo bata barshi ya tafi ba sai da ta tabbatar sun tsayar da
maganar biki da shi ana da wata biyu za ayi zai
turo da kudi su baffaninsa tunda kuma su ne 'yan
uwan ubansa sai su kai kudin duk da ake kaiwa
na neman aure
Daga gidan Goggo gidan yayarsa Adda
Fadıma ya wuce ya labarta mata komai dangane
da maganar aurensa da Suwaiba Fadima ta
jinjina maganar tace, "yanzu Goggo dai ta dage
lallai-lallai sai sun hadaka da Suwaiban nan,
yarinyar da bata da kirki bata ganin mutuncin
mutane, sannan kowa ya san Haj. Harira da bin
malaman tsubbu, kai kanka na san sunanka aka
kai aka yi tsubbu har ka amince tunda da ai baka
son auren shine ta san yadda tayi ta shiga ta fita
sai da ka amince me ake da irinsu Haj. Harira
(FA DALLU WA ADAL) ne, su bata kuma su 6atar, mu dai kada ta koyawa Goggonmu bin
bokaye don zata iya tunda ta fata itama ta batar
da ita". (Allah sarki ba su san aikin gama ya
gama ba) Mujeeb yace,
"Wallahi ni kaina ba son yarinyar nake ba, don
dai in farantawa Goggo ranta ne ya sa na amine,
ni dai ku taya ni da addu'a Allah ya sa alheri za
su kulla in kuma ba alheri to Allah ya tarwatsa
al'amarin". Adda Fadima ta ce, "Tunda ka ce har
169
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
an tsaida wata biyu, to sai ka gayawa Munccba
don ta san halin da ake ciki". Yace,
"Gaskiya saboda gudun tashin hankali Goggo
tace kada in gaya mata don ba a san ya zata kaаrбі
abinba, idan biki ya matso sosai sannan zan gaya
mata". Adda Fadima tace, "in kuwa ka yi haka
ka ci amanar zumunci kuma ka munafinci
matarka, saboda ai ba zama munafinci kuke yi ba
da zaka 6oye mata abinda yake faruwa kuma irin
wannan halayyar da maza ke nunawa su ki
gayawa matarsu zasu kara aure har sai abu ya zo
daf su gaya mata, shi yake kawo rigima a
tsakanin ma'aurata har a dinga zagin matar ace
ta cika kishi tana hauka don mijinta zai kara aure
alhalin munafincin 6oye mata da ya yi nc ya
kawo musu sabani, amma da tun farko ya gaya
mata cikin lallashi da lumana da hakan bata faru
ba. Saboda haka yau kana komawa ka gaya mata
sannan ka lallasheta, nima bayan ka gaya matan
zan kirata in kara lallashinta". Ya yi na'am da
shawarar Addanshi, shi yasa ma da ya shiga
garin Gombe kai tsaye ya zarce wani katafaren
super market ya zabgowa Munecban sayayya ta
ban mamaki sannan ya isa gida.
Gidan sai zuba kamshin turaruka yakc yi
shi kam hakan ya na masa dadi, yadda Muneeba
take dadada musu gida da dakuna da Kamshi don
170
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
babu yadda za a yi ka zo gidansu ka tarar baya kamshi, har suna ya rada mata 'yar kamshi. A
falo suka hade zata fita tarbo shi sai gashi har ya shigo. Ya jata jikinsa ya rungume yana aika mata da sumba a jikinta ta ſan janye kadan ta се, "Ка dawo lafiya ko?" ya su Goggo da sauran jama'ar Dukku?" yace, "kowa lafiya suna gaishe ki". Sai suka ji sallamar yaron da ke musu hidimar gida Jume". Suka amsa sallamarsa tare da yi masa
izinin shigowa ya shigo niki-niki da kaya a
hannunsa yace ya kwaso a mota, ya ajiye sannan
ya yi musu sai da safe. Mujeeb ya dakatar da shi
ya sa hannu a aljihu ya ciro gudar dubu daya ya
bashi ya yi godiya ya juya ya tafi, a ransa yana yaba kyawawan halin iyayen gidan na sa na kyauta da alheri da sanin darajar dan adam, har
ya kan rasa wa ya fi wani kirki cikinsu, sai dai
kawai ya yi musu kudin goro halinsu iri daya ne
shi yasa suke zaune lafiya cikin so da kauna,bai
taba jin kansu ba.
Kai tsayc bayi suka wuce, ruwan
wankansa na jiransa, duk da irin kwalliyar da tayi, bai sa ta yi tunanin kayanta za su baci ba,
ita ta yi masa wankan suka fito ya gabatar da
Sallar Isha'l sannan ya sa 'yar rigar shan iska
suka dawo falonta bisa dinning tablc don c.n
abinci. Ka'ida a dakinsa suke kwana, sai sunyi
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
nishadi ne suka kwana a dakinta. Sun ciyar da
junansu abincin da ta shirya kusan kala biyar har
da abubuwa sha, suna ta hirarsu cikin nishadI,
sai dai shi da yakc kawai yake yake yi don
magana na tsikarinsa amma ya kasa yadda zaiyi
ya gaya mata, yana tsoron kada ya ruguza
wannan nishadi da farin ciki da ciki yanzu
saboda al'amar kishi ga mata hakika babban abu
ne, maza yaki shine jihadinsu mata kuma kishi
shine jihadinsu, idan mace ta yi hakuri ta iya yin
jihadin kishin da ya tunkuro ta to za ta iya samun
aljanna.
Ita kanta Muneeba ta lura da yanayin
nishadin mijinta ya sauya a daren yau, saboda in
har zata fita ta dawo sai ta iske shi cikin zurfin
tunani har ta yi ta damunsa da tambaya yana ce
mata babu komai, duk yana kaucewa fada mata
babu komai duk yana kaucewa fada mata nc don
ba ya son abin da zai dagula zuciyarta alhalin shi
kullum burinta ta gata faranta masa, ko da za ta
takura kanta ne, shi kam in banda Addanshi tace
idan yaki gaya mata ya munafinceta hakika da
ya boye mata don ya samawa kansa farin ciki,
shi kam baima san yadda aka yi kaddara ta
kwasheshi ya amsawa Goggo cewa zai auri
Suwaiban ba. Ko wane namiji yana da hujja
kwakkwara idan kaga zai kara aure, to shi kam
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
bai ga wannan hujjar ba, don Muneeba bata
rageshi da komai ba, bata da bashinsa in dai
gurin kyautata nasa ne, ita kanta Goggon shaida
ce akan haka, sai dai ta ki fadan gaskiya, ta fake
da cewa don ya sami zuri'a takc son ya kara
aure, wai ba zai yiwu Allah ya azurta shi ba ta ko
wane fanni amma ace baya da arzikin 'ya'ya, ai
arziki bai yi ba, tunda Muneebar ba mai haihuwa
ba ce gara ya auro wata kila ita ta haihu, ya yi wa
Goggon bayanin da ake musu a asibiti idan sun
je cewa lafiyarta lau lokači ne kawai bai yi ba,
amma Goggo ta sa kafa ta yi fatali da bayaninsa
tace karya ne, boye mata ya ke yi kila ma ance
har abada ba zata haihu ba, dole yake hakura da
bayaninsa ya kyale Goggon tunda ba zata yarda
ta gane ba.
Sukan kwana cikin farin ciki da
annashuwa, har yake, tunannin shifa zai je kawai
a sami Goggo yace mata su yi hakuri ya fasa
auren don matarsa babu abin da bata yi masa,
kada ya zo ya auro wadda zata wargaza musu
zaman lafiyarsu, amma da garin Allah ya waye
sai ya ji son auren ya sakc tasiri a zuciyarsa ya ji
ba zai iya tinkarar Goggo ya ce ya fasa ba, idan
ya yi haka tamkar ya tozartata ne, duk da ba
wani son Suwaibar yake ba, zai dai aureta ne
173
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
saboda Goggon ta matsa masa, kuma don ya
faranta mata rai.
Sai da ya yi shirinsa tsaf na zuwa ofis,
sannan ne ya kira Munceba suka zauna a falonsa
yace, "Munceba ina son mu yi wata magana,
amma ina son ki yi wa maganar kyakkyawar
fahimta, kuma wallai ba da son raina hakan za ta
faru ba na yi ne don bin umürnin su Goggo,
kuma ina ganin ni da ke mun zama jinni da tsoka
don idan aka tsaga jiki na za a ga irin jininki, ke
ma idan aka tsaga jikinki za aga irin jinina, ina
son mu ci gaba da hada kanmu ta yadda ko wani
ya shigo tsakanin zaman mu ba zai ga wata
faraka a tsakanin mu ba balle ya sami kofar da
zai ci gaba da haifar mana da wata 6arakar".
Zuciyar Munecba ta soma, bugawa fat!
Fat!! Fat!!! ta soma karyata żuciyarta na irin
abinda take kitsa mata shine zai faru, kafin ta yi
yunkurin cewa wani abbu har ya ci gaba da cewa
"kin riga kin san Goggo ta na son hada ni aure
da 'yar aminiyarta Haj. Hariria, wato Suwaiba,
to sunci galaba a kaina don ban san yadda aka yi
ba na amince wa Goggo zan auri Suwaiba, har
an tsaida lokaci jiya an aje wata biyu masu zuwa
za a yi auren, shine na ke son ki kwantar da
hankalinki ki bani hadin kai, mu ci gaba da
zaman lafiyar mu,'na yi miki alkawarin in sha
174
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Allah ba za ki ga wani sauyi daga gareni ba, zan ci gaba da sonki da tattalinki har abada ba zan juya miki baya ba don na yi aure, za ki ci gaba da zama tauraruwar zuciyata".
Hawayc ne kawai ya kc ambaliya a
kuncin Munceba, ta kasa cewa komai, saboda jin
wannan bala'I da ya rufto mata, kwarai auren
Suwaiba ita bala'I ne a gareta domin ko kankani Suwaiba bata da kunya sannan ba sa shiri ko kadan, don idan ta zo gidan gurin Goggo ita kadai ko da Hajiya Harira harara ce kawai za ta dinga ballawa Munceba, bata yi mata magana sai idan ita ta yi mata, kuma ko ta yi mata ma bata cika amsawa ba, sannan acc ita ce za su yi zaman
kishi, sannan ga tarihin rayuwar auren Hajiya Harira da kowa ya sani a Dukku, har ubansu Suwaiba ya mutu bai taba tunanin kwatanta kara
aure ba duk da mai hali ne ba talaka ba, sannan
ita ce ke jan ragamar gidan, komai zai yi sai da izininta ya ke yi ta raba shi da 'yan uwansa kaf
bai zuwa gidansu, haka suka yi rayuwarsu har
Allah ya amshi ransa.. ya'ya dama kuma ta raba
su da dangin ubansu da ya rasu sai ta zamo ita cc
uwarsu itace uwansu, ko da neman aurensu aka
zo sai ta wakilta wani kawunta da yake mai son
abin duniya ne ta dan yi masa hidima to shi yake
shigewa gaba gurin auren 'ya'yanta kunga ko ta
175
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
nan manema auren za su gane ba su zo gidan
mutunci ba tunda babu dangin uba a neman
auren.
Mujeeb ya jawota jikinsa ya rungume
yana kara lallashinta, a kan wannan al'amari da
ya same su tare da tabatar mata In Shaa Allahu
ba zai wofintar da ita ba, ba zai ci amanarta ba,
ta kwantar da hankalinta.
Ta dube shi idanunta sun yi ja saboda
kuka tace, "Don Allah ina son ka yi min wata
alfarma", yace "Fadi ina jin ki in dai zan iya to
In Shaa Allah duk zan yi miki'. Ta ce "Na
amince ka kara aure amma don Allah ba da
Suwaiba ba ka canza wata, don ina tsoron
al'amuran Suwaiba da Hajiyarta, sannan kai
kanka shaida ne a kan irin alakar da Suwaiba ta
ke yi da ni idan ta zo gidan mu, ji take tamkar ta
sheka ni don na aureka, bata kaunar gani na tare
da kai sam, to ka ga ina ga muna kishi kuma ai
bani ba zai yi mini kyau ba".
Yace, "ba zai yuwu ba in fasa Muneeba
tunda na riga na anince wa Goggo, idan na ce na
fasa ke za su cc kin hanani tunda sunce sai
abinda kika ce na ke yi, abinda na ke so da ke
shine ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki,.
varinvar nan ko ta zo gidan nan ba za ta
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kamo matsayinki ba, balle har ta ce za ta zarta ki,
kuma bata isa ta zo ta raina ki ba ko ta tayar miki
da hankali, wallahi ba zan lamunta ba zan nuna
mata kurenta, saboda haka ki kwatar da
hankalinki ni da ke nan gani nan bari kuma mutu
ka raba takalmin kaza”.
Da zai tafi ta roke shi cewa tana so za ta
je gidan Inna Amina ya dan tsaya yana dubanta
cike da nazari sannan yace "Za ki kai karata ne
gurin Inna Aminan? Ki yi hakuri kada ki sa 'yan
uwanki su dinga jin haushi na, ke ma kin san bin
umurnin Goggo na yi ba don in 6ata miki rai ba,
in banda Goggo babu wanda zai sa ni in yi
abinda ban yi niyya ba". Tace,
"Ni ba karar ka zan kai ba kawai abinda dama
zai kaini, maganar maganin nan ne, ai na gaya
maka mai maganin nan ne yace dole sai nazo ya
yi mini tambayoyi kafin ya bani magani, ba zai yiwu ya bada magani da ka ba". Yace " OK na
tuna to amma na san ai sai kin gaya mata
wannan maganar, sai dai na san Mama ba zata
baki gurguwar shawara ba, za ta tayi ni
lallashinki tare da baki shawarwari na gari, kuma
dama ina so in gaya miki ina son za muje Umara
kafin bikin saboda ki ga likita, wai abokina ya
gaya mini wani asibiti a Jidda zan kaiki a duba
ki, da ban yi niyyar gaya miki ba na bari ne sai
177
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
na gama shirin komai sannan in gaya miki".
Тасс,
"Amma kana ganin Goggo ba zata ce a bata
yardaba, gani na yi ita ya kamata ka fara biyawa
aikin Hajji kafin ni in je". Yace,
"To ai ba aikin Hajji ba ne ganin likita za mu
je tunda dole har dani za a duba din ba a san wa
ke da matsaar ba, kinga a nan duk sun ce
lafiyarmu kalau a can kuma ba mu san me za su
ce ba". Tace,
"Sheke nan Allah ya kaimu, ya sa a dace".
Yace "Amin".
Ya kamamla shirinsa tsaf ta rakashi har
jikin motarsa ya shiga ya tafi, sannan ta dawo
gida ta soma gyaran gidan kamar yadda ta saba
kafin jume ya zo ya yi nasa ayyukan gidan,
kamar su shara wankin kayan shi da yin guga sai
kuma aike idan suna da shi.
Ta isa gidan Inna Amina ta iske ta yi
bakuwa, hakan ne ya sa suka shige dakin su
Khairi suna ta hirarrakinsu duk ta kosa bakuwar
Inna Amina ta tafi don su kebe da ita ta gaya
mata abinda ke faruwa, abin yana ta
tsinkunkuninta har sai da ta gayawa su Khausar,
salati suka dauka suka dire mai karfin gaske
wanda har ya jawo hankalin Inna Amina da ta
dawo rakiyar bakuwar ta, ta shiga dakin nasu a
178
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
hanzarce tana tambayarsu "Lafiya? Mutuwa aka
yi kuke salati mai karfi haka?" Khairi tacc, "Ai
mama da jin sakon mutuwa da irin wannan
mummunan labarin da Munceba ta bamu duk
daya ne a kunnen wanda aka gayawa in dai ya
shafe shi". Ta сe "kai wai me ya faru ne? ku fito
direct ku gaya min bana son shirmenku
Khausar tayi karaf ta ce,
"Hum Mama wai kinji Mujeeb aure zai yi nan
da wata biyu". Ita kanta Inna Amina zancen ya
soki zuciyarta, amma don kada ta nuna ta dada
ingiza su ta kuma karyawa da Muneeba zuciya
sai ta yi jarumta ta ce,
"To meye don zai yi aure a kanki matar zata
zauna, ta so nan mu je daki ki kyale wadannan
sakarkarun, in baki dau abin da zafi ba damuwar
da za su nuna sai ta sa ki zafafawa kanki, taso
mu je”. Muneeba ta mike idanunta cike da
kwalla Inna Amina ta ruko hannunta ta
rungumota tana share mata hawayen da hannunta
har suka isa dakinta.
Ta zaunar da ita a gefen gado itama ta
zauna sannan ta ce, "gaya mini me ke faruwa da
gaske auren zai yi ta gyada kai sannan ta
labartawa Inna Amina yadda maganar auren ia
ke da adadin lokacin da ya rage. Inna Amine.
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
tace, "Yanzu wannan yarinyar 'yar wajen Haj.
Hariran zai aure" tace,
"Itace zai aura kin san tun tuni Gggo ke son
hada auren yaron ya nuna baya so, ko lokacin
bikinmu ai rigimar da ka yi ta yi da ita kenan sai
dai ya auri Suwaiba, to yanzu sun samo kanshi
shine ya amince, ni na san zama na ya zo karshe
a gidan Mijceb, saboda halayyar Haj. Harira
kowa ya sani bata son kishiya, kin ga ba zata so
a'ce 'yarta na da kishiya ba, ko yanzu da ya
yarda zai auretan akwai abinda suka yi masa har
ya amince, Adda Fadima ta yi mini waya dazu
haka tace, amma tayi ta bani hakuri, ta ce ita sam
bata goyon bayan wannan aure don dai babu
yadda zata yi ne da ta hana shi, tunda abin hadin
Goggo ne sai dai mu yi ta addu'a duk sharrin da
zata shigo da shi gidan ya kare a kanta":.
Inna Amina ta ce "ni ma shawarar da zan
baki kenan ki yi hakuri ki kwantar da hankalinki
ki sa Allah a zuciyarki kuma ki kudirta cewa
zaki zauna da ita tsakani da Allah babu cutarwa,
sai ki ga Allah ya dube ki ya yi miki kariya idan
ita ta zo gidan da mugun kudiri, kuma kada ki sa
maganar rashin haihuwar ki a ranki ki yi ta
damuwa, Allah ya na sane da ke bai manta da ke
ba, In Shaa Allah zai dubeki ya azurtaki da
haihuvar 'ya'ya masu albarka, in ma bai bakin
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
ba kiyi godiya a gareshi da ya baki rai da lafiya,
ki na cikin rufin asirinki wani shi kuma Allah ya
bashi ‘yan'yan amma ba da lafiya, wani babu wadatar abinda zai ciyar da su, babu muhalli ba
ba ba tayi masa yawa, sai arzikin 'ya'ya amma
ba arzikin kwandala, to kowa da irin na sa
arzikin sai ki yi ta yi masa tasbihi, da tahmidi da
taklili, ki yi ta gode masa, kada ki yi kukan
rashin haihuwa ki yi wa Allah batulci don ya
baki rai da lafiya da arziki dai dai gwargwado.
Bari in kira aminiya Rahman Zaria ta sake baki
wasu shawarwarin a waya tunda ni ma mamanki
tana bani shawarwari ina amfana da su sosai".
Muneeba tace, "mama wace ce Rahma Zaria?"
tace, "Au har kin manta Rahmatu Hassan Zaria
da na baki littafinta DON MAʼAURATA da
SIRRIN GIRKE-GIRKE 1&2 ko kin watsar da
littafan ne? tace, "Lah! Mama na tuna ta wallahi
na karanta littafan su ne ma abokan huldata ko
da yaushe, na karu da littafan sosai don na koyi
girki kala-kala a ciki wanda da ban iya ba,
sannan ta fannin kula da miji na koyi abubuwa
da yawa, gaskiya ta yi mana taimako mu
ma'aurata Allah ya biya ta da gidan aljanna. Don
Allah Mama kirata na san za ta bani shawarwari
masu alfanu". Mama ta yi dailing numbarta bugu
daya biyu zuwa uku saita dauka suka yi wa juna
181
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
sallama sannan gaisuwa ta biyo baya