ko bako tayi bazata sami sukuni ba sai ta
gama ayyukan da suka zamo wajibi a kanta, idan
a haka ba to idan bakin nata suka tafi zaía zo ta
iske aikinta na nan yadda ta barshi bata samun
sukunin hutawa sai sun gama girkin dare, idan
tayi wanka shike nan ta gama na ranar sai kuma
ba gobe, yaune don yayi shigowar dare ne tabbas
da ya zo ya isketa kaca-kaca cikin aiki.
Mujecbu yayi iya kokarinsa don
Munceba ta gaya masa abinda yasa tayi rama
amma tace masa ita babu komai, kuma ba ciwo
tayi ba, sai zuciyarsa ta fara zargin to ko dai
Goggo ta fara gallaza mata ne tunda ta rigata
fada bata son aurensu? Ai kuwa a irin ladabi da
biyyar da Muneban ke masa ya kama ta watsar
da rashin son auren nasu ta rungumi Munceban
hannu bibbiyu a so ta tunda tana kyautata mata,
amma zai cigaba da bincike a hankali har sai ya
gano meke faruwa ne a gidan dangane da
zamansu.
Baisake tsinkawa da al'amarin Muneba
baya tabbatar lallai wani abu ya faru da bayanan
sai da suka zo kwanciya, sun riga sun san tare
suke kwanciya cikin bargo daya, amma yau ko
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gado daya taki yarda su hada balle bargo daya
har da ratsuwarta na ccwa ba zata kwana tare da
shi ba, za ta kwana a falo a doguwar kujcra ko, ta
kwana a kasa yayi zuru yana kallonta lokacin
tana kokarin shimfida bargo a kasa, abin duk ya
daure masa kai, tabbas wani ya zuga masa
matarsa tunda bahaka suka rabu ba, don ko daren
ranar da zai tafi ta sallama masa kanta, shine dai
ya kyaleta saboda tausayinta da yake ji, kamar
zai kwareta yake gani shiko wasannin da suke yi,
suna rage masa karfin sha'awarsa yana wadata
da hakan, to yau ta guje shi wannan matsalarma
dole ya binciketa tunda ba zai iya jurar hakan ba.
Haka suka kwana kowa ransa babu dadi,
yana gado abinsa, ita kumatana kasa nade cikin
bargo. Washe gari ma hakance ta kasance, don
ko da rana tayi mirsisi ta hana ya rabi jikinta,
abin ya dame shi kuma ya daure masa kai sosai
har ya soma bincikarta dalilinta na gudunsa da
take yi yace,
"Wai ni Munecba ko wata cuta aka ce miki ina
da ita yasa kike gudu baki son ko jikinki in goga
kada in shafa miki cuta?" tace, "ni daiban ce
haka ba, waya isa yace kana da cuta gaka nan
lafiyayyanka da kai", yace, "To meye dalilinki
na irin abinda kike mini tun jiya da na zo?" ta
soma nuku-nuku sannan da kyar ta iya cewa,
125
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
"Ni fa ba gudunka nake yi ba, ni dai tsoro nake
kada in samu ciki, idan na koma maaranta a kore
ni, kasan basa yarda da mace mai ciki
amakarantar kwana ko mace na da miji". Ya yi
murmushin ban mamaki yace,
"Nima ina son ki karasa karatunki, ai bazan
yarda ki samu ciki yanzu ba, ai babu abin da
zanyi miki, da ya wuce wasannin da kika ga ina
yi miki, ki kwantar da hankalinki bazan yi miki
abinda zaki sami ciki ba, nayi miki alkawari". Ta
soma 'yar shagwaba
"To ai shima wasan da kake mini ance in dai
mace ta yarda namiji na wasa da ita yana
tattabata zata iya ganin ta da ciki, shi yasa nake
tsoro". Dariya Mujecb yayi sosai sannan yace,
"Haba Muneeba kada ki bani kunya, yanzu duk
karatun islamiyya da na bokon da kikayi da
zanki cikin wayyayyun mutane a Gombe baki
san cewa sai ta hanyar yin jima'i tsakanin mace
da na miji sannan macen ke samun cikiba, duk
wani wasan da za a yi da mace ba zata taba
daukan ciki ba har sai jima'i ya gifta tsakaninsu.
In kuma har yanzu baki fahmci hakan ba, zan
kira Malam Ayuba na nan baya ya zo yayi miki
bayani dalla-dalla kila zaki fi ganewa. Tace,
"Ni kam bance ka kira mini Malam Ayuba ba, ka
barni zan a hankali, idan lokacin da zan gane
126
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
gane yayi".yace, "Gaskiya gara in kira shi tunda
kin nuna ke kifin rijiya ce bai san komaiba to
gara a fayyace miki abinda kika siga duhu
akansa, tundani ko nayi miki bayani ba ganewa
zaki yi ba", tace,
"Don Allah kayi hakuri karda ka kira mini
kowa in kuma ba so kake ka tonawa auren mu
asiri ba".
Ganin ta nuna ta bata son ya gaya wa
kowa, abin da ke faruwa tsakannin su, shi yasa
ya kyaleta, amma in har ta cigaba da gudunsa to
yasan dole ne aji, don da ransa da afiyarsa ba zai yiwu hakan ta kasance a kansa ba kuma ba zai
iya jurewa ba.
Kwana biyun da yayi, yayi su ne cikin damuwa da rashin gane kan Muneeban a dalilin barinsa da take yi a daki tayi tafiyarta can sasan Goggo, wanda da ba hakatake masa ba, idan
yana gida tota kan kasance ne tare da shi, amma
yanzu muraran take gudunsa, kuma iya
bincikensa da yayi, ya kasa gano ko wane ne ya
cusa mata hudubar guduns.
Da safe ranar kwannansa na uku, shi yana
daki yana nazari ita kuma tana kicin tana gyara kayan wanke-wanke da ta wanke saita ji sallama,
tana dago idanunta ta ga Goggosu Hinde, ta saki kwannanon hannunta da gudu ta fita tana
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Oyoyo Goggonmu, Oyoyo", ta rugume Goggon
tana murna. Itama Goggo Hinden cike da murna
tace,
"Sannu 'yar gidan Goggo aiki ake yi ne?" tace,
"kicin nake gyarawa, shigo faki Goggo Yaya
Mujeeb ma yana ciki". Yana jin zuwan Giggin
yay hamdala, dama yasan da zuwanta shi yaje
har gida yayi mata bayanin abinda ke faruwa
tsakaninsa da matarsa tace ya taho gata nan zuwa
zata binciki Muneeban idan ta zo sai ta ji
musabbabin daga inda matsalar ta kunno kai.
Ya mike tsaye yana yiwa Goggon sannu
da zuwa. Bayan sun gaisheta ne ta ke dubansu
tace,
"Ni ban gane ba ne, na zo inga 'yata tayi cikar
daki tayi kyau, sai naga duk kinyi dan wuya, shi
ma dan nawa naga a rame, kamar ba amarya da
ango ba, me ke faruwa ne, ko har yanzu ba kuyi
amanna da hadin auren da aka yi muku bane?"
Muneeba ce tayi karaf tace,
"Lafiyarmu lau Goggo, babu wata matsala".
Mujeebu yace,
"Gata nan Goggo Allah tunda na dawo na rasa
gane kanta ni ban sani ba ko nayi mata wani
abune, tunda satin da ya wuce da zan koma
lafiya lau muka rabu", yanayin yadoa, Mujeeb
yayi maganartamkar yanzu ne ya fara sanar da
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo Hinde matsalarsu, alhalin ta riga ta san komai.
Goggo ta dubi Munceba da ke ta zabgawa
Mujccbu harara a fakaice tace, "Gaya min me
dan nawa yayi miki? Idan na fada ne in yi masa
fada inja kunnensa in ma laifin ya kama naduka
ne sai in bugeshi gaya min". Muneeba tanoke
tace,
"Ni fa Gogga babu abinda yayi mini", tace,
"a'aMunecba kinyi masa laifi mana tunda yace
ya kasa gane kanki alhalin lafiya ya koma
Gombe ya barki ba wata matsala a tsakaninku,
kada fa ki bada wata kafar da idan baya nan wani
zaizo ya zuga ki, ya hargitsa muku zamanlafiyar
da kuka gina, ko waye ki natsu ki lura da shi zaki
ga ba mai kaunar aurenku ba ne, ba mai son ci
gaban rayuwar aurenku bane, ki yi karatun ta
natsu kada ki sake a sake yi miki wata huduba ta
banza akan mijinki tunda sai bango ya tsage ne kadangare yake samun gurin shiga". Kalaman Goggo Hinde sun sa jikinta yin sanyi lakwas, har
ta gano lallai hudubar da Goggansu Mujcebu tayi mataba abin dauka bace, kasancewar tun fil azal bata kaunar aurensu, kenan kota yaya zata iya bin duk wata hanyar da zata bi don ganin rashin zaman lafiya ya wanzu a tsakaninsu, kai
dole ne ma tayi watsida hudubar Goggon ta
129
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
rungumu bukatun mijinta don suna lafiya duk
abinda Allah ya nufa zai faru idan ma ta sami
ciki sun koreta a makaranta sai yayi mata
tiransifa ta koma wata makarantar ta jeka ka
dawo.
Wai tunanin me kike yi ne?kinga ki natsu
kiyi aiki da iliminki ki ba aurenki Muhimmanci
ki bauta masa da dukkan iawarki babu ruwanki
da 'yan boni naiya, 'yan hana ruwa gudu, su 6ata
goma biyar bata gyaru ba naga bakinki da
alamun magana, ki gaya min meke faruwa ne?"
Muneeba ta soma 'yan noke-nnoke tana son
gayama Goggo Hinde hudubar da sirikarta tayi
mata, amma tana alhinin fada a gaban Mujeeb,
sai Goggo Hinde ta dubi Mujeeb tace,
"Tashi ka tafi hidimar gabanka zanyi mata
fada da nasihohizata gyara in sha Allahu zamaku
daidaita, kuma bana son ka gayawa kowa sirinku
ne kaida matarka, ka ji ko?" ya gyada kai tare da
mikewa yace, "Shikenan Goggo mun gode, ki
gaida gida, kila kuma in dawo in sameki, ki
tsaya ki ci girkin diyarki wallahi ta iya girki,
kamar kun nin mutum zai tsinke saboda dadi".
Dukansu ukun suka kyalkyale da dariya
Goggo tace,"haka ake so mai gida ya dinga
yabon girkin uwargidansa, kinga kinci jarabawar
130
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
girki saura gurin kula da miji ma ki cinye".
Mujeeb ya fice ya bar Goggo da Munecba.
A irin hikima ta su ta manya ta lallashi
Muneeba cikin hikima da dabara Muneebanta
zayyana mata duk yadda Goggo ta gargadeta
akan kada ta saki jiki da mijinta ta yadda idan ta
kuskure ta sami ciki to karatunta zai zama asha
ruwan tsuntsaye, idan kuma ta bi ta son miji taki
yin karatun to labudda nan gaba zai auro wadda
tayi karatu, ita kuma zata zamo koma baya,
wannan kalma ta koma baya da Goggo tace zata
zama idan Mujeebu ya auro 'yar boko ita tafi
zamowa mafi tasiri da sosa mata zuciya matuka
gaya, har hakan yayi babban tasiri a zuciyarta na
abin da ta yi wa mijinta da da mara idanu, kawai
gara ta hakura ta watsar da hudubar Goggo ta
rungumi mijinta hannu bibbiyu.
Goggo Hinde ta hau tafa hannu da
sallalalimi tace, "yanzu Gogon kuce da irin
wannan hudubar da bata dace ba? To ai wannan
abinda tayi Mujeebun da take tsananin kauna shi
abin zaifi shafa ita kanta ba zata gane kansa ba
indai tace irin wannan hudubar zata ci gaba da yi
miki ta ki bijircwa mijinki, ke kuma tamkar wata
shashasha, kin manta cewa bata son aurenku,
duk hanyar da zata bi don ganin baku zauna
lafiya ba zata bi, saboda haka ki natsu ki dinga
131
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
daukar huduba ta gari ga duk wandaya baki,
wadda kika ga ba ta gari bace to kiyi maza ki
watsar da ita, bana son in sake jin wani abu mara
dadi ya shiga tsakaninki da mijinki, kada ki
zamo mace mai fallasa ssirrin mijinta, ki yi masa
ladabi iyakar iyawaki. Allah yayi muku albarka
ya baku dawwamamman zaman lafiya amen.
Haka Goggo Hinde ki tayi ta ba Muneeba
shawarwari da nasihohi da hikimomi da dabaru
na zama da miji, kafin ta tafi. Da zata tafi
Muneeba ta kawo sabulaimasu Kamshi ta zuba a
leda ta kawo mata, da kyar ta amsa suka fito
zuwa sasan Goggo.
A tunanin Goggo Rahim 'yar uwarta
ziyarar zumunci ta kawo mata bata san gyaran
auren 'ya'yanta da take son gurguntawa ta zo
gyarawa ba, kuma tana fatan ta gyara 6arakar da
Goggo Rahin din ta yi a zamantakewar 'ya'yan
nata da yarinyar Allah.
A kofar gida Goggo Hinde ta sami
Mujeeb yana dakon fitowar ta don yaji yadda
suka yi da matar sa. Ta gaya masa komai amma
ta gargadeshi da kada ya nunawa Goggon ya san
meke faruwa ya bi al'amarin a hankali kuma ya
ci gaba da yiwa mahaifiyar sa biyaya, tunda bata
son auren su dole sai ya bi ta a hankali.
132
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Tunda ya shigo gida bayan rabuwarsu da Goggo Hinde ya iske canji sosai a tare da Muneeba ta dawo da zamansu irin na satinsu na farko, tamkar ba itace ke gudunsa ba. Wannan
sauyin ne yasa a daren ranar da hikima irin tasu
ta maza wayayyau ‘yan boko ya sami kan
matarsa ta sallama masa ragamar kanta.
Kwana yayi yana lallashi da tarairayarta;
kasancewar ya san Muneeban karamar yarinya
cc, 'yar shekara sha biyar, yanzu ne ta farad
rayuwa irin ta ma'aurata kuka dai ya sha shi
babu adadi da kyar ya samu ya lallasheta tayi
bacci, amma taki yarda ya saketa taba jikinta
saboda ta riga ta tsorata da al'amarinsa, shi yasa
ta koma can Karshen gado ta dunkunkune, da
yaga haka sai ya ja bargo yalulluba mata har sai
da yaji tana sauke numfashi da ajiyar zuciya a
hankali alamun AL ta yi bacci, sannan shima ya
kwanta. La.. Co
Tun kafin tatashi da asuba shi ya rigata
tashi, ya dafa ruwan wanka a risho ya debe a
bokiti ya sirka da zafi sosai sannan yaje ya
tasheta yalallabata sukaje bayi da taga shi yake
son yayi mata wankan sai tace ya kyaleta zata yi
da kanta yace, "Zaki iya kuwa, naga har yanzu
bacci bai sake ki ba, ga jinki ba kwari? Ki bari
inyi miki sai in gasa miki jikinki", ta make
133
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
katada tace, "ni dai ka tafi zanyi da kaina", ya
juya zai fita yana janyo mata kofar tare da yi
mata bayanin yadda zata yi wankan, da
abubuwan da ya aje mata don amfanin kanta.
Kwana yayi yana lallashi da tarairayarta,
kasancewar yasan Muneeba karamar yarinya cс
'yar shekara sha biyar, yanzu ne ta fara rayuwa
irin ta ma'aurata.
Da ta fito ta wuce shi ta shige dakin
baccinsu ta shafa mai ta saka wata doguwar riga,
ta hau dadduma ta soma sallar raka'atanil fajri,
kafin ta fara sallah a masallaci. Da Mujeeb ya
leko yaga tana sallah shima sai ya fice zuwa
masallaci.
a Lokacin da ya dawo a gado ya ganta
kwance ta dukunkunne cikin bargo ya zauna a
kusa da fuskarta yace, "har kin sake kwanciya
ne?" ta dan bude ido tace, "bacci nake ji, kuma
na ji zazzabi yana son kama ni”. Ya ce, "To ki
tashi ki sha magani sannan ki kwanta", tace, "Ai
ni bana shan magani idan anyi bacci ma insha
Allahu zan tashi garau". Ya ce, "Shike nan to
gyara kwanciyarki, ki daina takura anki haka,
dubi yadda kika takure kamar alkaki, in don nine
ki saki jikinki kiyi bacinki bazan sake matsa
miki ba". Ta gyara kwanciyar ya rufa mata
134
65
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
zuwa ma mutum bagatatan daga Allah.
Mujahced ya nuna tauhidi don baiyi jayya da
Kaddarar ubangij ba a cewarsa dama Muneeba ba
matarsa bace kurna wani ai baya auren matar da
ba tasa ba.
Iyalan gidan Inna Amacena a can Gombc
kuwa basu da labarin meke faruwa a Dukku,
sannan Muneeba ta zayyanawa Innarta alakar
soyayya da suka kulla ita da dan uwanta Sadiq
dan Inna Amina, a cewar Muneeban tunda auren
zumunci ake so ayi mata ida da an daura da
Sadiq tunda shirna ai dan uwan gida ne, kuma
shi take so, shima yana sonta sabanin Mujeeb da
ba ta da tabbacin ko zaiyi amanna da wannan
hadin iyayen, shi ma ta san a can Gombe ba zai
rasa wacce yake so ba, Innan ta ce,
"Ni dai ina dada jaddada miki kiyi hakuri ki bi
umurnin iyayenki insha Allah zaki ga alkhairin
ya biyo bayan aurenku, shi ma Mujcebu na
tabbata kuma ina da yakinin akansa ba zai nuna
bijirewa ko da zai dawo ya tarar da irin bijirewan
da Guggoonku tayi, ba zai goya mata bayaba.
Maganar Sadiq kuma ni baki taba gaya mini ba
Yaya Amina ma ba mu taba zancen da itaba,
koita ma bata sani ba nc?" Munecba ta ce "Tа
sani don ta taba kirana muka yi maganaganun
akan hakan". Inna tace, "Kin gani ta yi nauyin
WATA KUSAN 1 6b Rahmatu Hassan Zaria
baki, kuma ni duk zuwan da Sdiq keyi gidan nan
ban taba lura da wani abu a tsakaninku baai da
tuni na sanar da Babanki, kinga da 'yan uwansa
suka kira shi da ya gabatar da maganar Sadiq
din, yanzu kuwa lokaci ya kure tunda har sadaki
gasu can uban dakinsa a Gombe ya bada, bakin
alkami ya riga ya bushe, sai dai mu biku da
addu'a Allah.ya sanya albarka a auren ya baku
zaman lafiya ya kauda fitintinu a tsakani. Barin
in tasht in vi shiri kinsan na gaya miki Gombe
zanje don in sanar da Yaya Amina, akwai wasu
'yan maganganu da zamu tattauna wadandaba
zai yiwu a wayaba gara in je can".
Inna a can Gombe sun kebe da 'yar
uwarta Amina ta kwance mata zare da abawa ana
abinda ke taíe da ita, da maganar daura auren
Минес за nan da kwana uku. Inna Amina ta
jinjina kai cike da al'ajabi da alhini tace,
"Iko sai Allah wannan al'amari da ban al'ajabi
yake wan ran yana nan yana nasa lissafin na idan
ya kanımala kara'u iama a lokacin zata gama
saisu yi aurensu tunda sun daidaita kansu suna
son juna, ashe ba rabonsa bacc. Haka Allah ya
Kaddara Allah yasa alarkı yaba su zama lafiya,
Mujech ai yaro ne na kwarai". Inna tace,
"Wallahi ban san da muhimmiyar magana haka
tsakanin tà da da na ba, kuma duk zuwan da
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
kwana? ta risina gaban Goggon tana gaisheta, ta
cc "Ba sai na zauna ba, dama nazo duba jikinki
ne, ya ciwon cikin ya lafa ko?" tacc, "Eh, yayi
sauki Alhamdukillahi", tace, "In dai bailafa ba
sai ku tafi asibiiti ko in tura Isah ya amso mata
na gargajiya don ya fi na asibiti". Mujeeb yace,
"Akwai maganin asibiti na bata tasha". Ta ce,
"To shike nan Allalh ya sawake" ta juya ta
koma sasanta, Mujceb yace,"Ga ruwa can nasa
miki sai ki kara yin wanka sannan ga abin break
fast can, idan kika ci sai ki sha maganni duk da
kince bakya sha dole ki sha in dai kina son
jikinki yayi miki dadi". tacc, "Wai du ina bacci
kayi ayyukan gidan nan? Lallai yau ka sha aiki
sannu da kokari", yana murmushi yace, "Ba dole
inyi ba, tunda na tabo lafiyar wanda zata yi,
nima aikinyi kokari da hidima ta koba haka ba”,
kunya ta kamata tayi saurin fitowa ba tare da
tace masa komaiba tanufi kicin, ya iske har ta
debo ruwa a bokiti tana sirkawa, yace, "Au ba
baki hutun aiki bayau? Ki tafi bayi zan kawo
miki ruwan".
Dole ta tafi shi ya kawo mata ruwan,
wankan ma dolente ya tayata shiri ma shi ya taya
ta sannan suka zauna gurin karyawa. A baki ya
dinga bata abinci yana tarairayarta tamkar 'yar
jaririya, ita kam kallonsa take cike da mamakin
137
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
irin kulawar da yake wadda ta nininka ta da ko
da yake ta san Kila hakan baya rasa nasaba da
hadin kan da ya sami daga gurinta, tunda
tsakannin daren jiya zuwa yau ba zata iya kirga
godiya da sa albarkar da ya dinga yi mataba, shi
yasa itama ta sha alwashin zata watsar da komai
ta rungumi mijinta ba zata sake daukar duk wata
huduba mara kyau daga kowa ba balle har hakan
ya kawo musu wani nakasu a aurensu.
Ranar dai Mujeeb bai fita ko inaba yana
gida tarairayar Munceba, ita ma sai ta biye masa
ko sasanan Goggo ta kasa barinsa ta fita tunda
dama Goggo yau a matsayin maralafiya
Muneeban take a gurinta, shi yasa itama ta ba
kanta hutun ayyukan da take wuni tana yi a
gidan.
Mujceb har tsokananta ya dinyi wai yau
kadai da ta kwanta taba kanta hutun ayyukan da
take yi har ta yi kiba, sannan yau ne ta fara
amarci na sosai da duk amarcin karya take yi",
tayi masa murmushi tace, "kibar ai bani kadai
nayi ba, kaima kayi har haske ka kara yi". Yace,
"Ba dole in yi kiba ba angwancin gaske wasa ne,
saima nan gaba kila sai an canza mana kofar
gida da kofar daki don ni da ke duk kadan zasu
yi mana wajen shigowa? Tayi ta masa dariyar
kalamansa.
138
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Wannan karon Mujeeb bai koma Gombe
makaranta da wuri ba ana can ana ta karatu, shi
kuma yana nan yana angwancinshi har sai da
Yusuf ya kira shi a waya yana masa tsiya a
wayar yana cewa, "Wai kai wanc irin sakaci ne
wannan ka bar karatu ka je ka makalewa
yarinyar mutanc, idan ba zaka dawo bane ka
gaya mini na gaji da karyar da nake sharawa
Alhaji cewa bakajin dadin yace yayi ta kiran
wayarka baya samu". Mujecb yayi dariya yacс,
"kai yaro karabu dani aurefa ba karya bane, gara
ma idan za ka yi ka zo ka yi shi tun yanzu da
kuruciyarka, ka aje tsarin da mukayi da na cewa
sai mun gama masters lokacin ka tsufa wallahi,
sai dai ka sami tsohuwa irinka, wallahi baka ga
yadda na zama ba na yi kiba na yi fari ba za ka
san aure rahama ke gareshi ba sai ka ganni,
hankalina kwance kamar ma kada in dawo
makarantar ashe yarihyar nan na sona haka
boyewa tayi sai yanzu take ta fito min da
6oyayyar soyayya iri-iri". Yusuf ya ja tsaki yana
dariya yace, ID
"Amma fa kaji kunya, yarinyar da ka ke cewa
Karama, kana wani babbasar da ita, harka sauko
da ajin ka kasaka yarda ta iya soyayya? Lallai ta
ci garinka dayaki ina yimata jinjina tunda har a
dalilin soyayyarta zaka iya aje karatun da ke da
039
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
muhimmaci a gareka. Yanzu dai yaushe ka
shirya dawowa, ko ingayawa Alhaji ba zaka iya
dawowa yanzu ba soyayya ta rike ka?" yace,
"Idan ka isa mara kunyar gaskc kana iya gaya
masa, kai zaka kwana ciki don Alhaji ba zai
yarda zan iya fadın magana makamanciyar
wannan ba, ya riga ya gasgata walicci na, gara
ma kayi wa bakinka linzami". Yusuf yake ce da
dariya har sautinta ya doki kunnen Mujeebu,
Mujcebu yacс,
"Ni don Allah kada ka kashe min dodon kunne
in kasa jin irin kalaman soyayyar da ake gaya
min". Yusuf yace,
"Ai dariya ka bani saboda ni na san kai ba
waliyyi ba nc sai yau, Alhaji kam yayi rashin
sa'ar wanda zai gasgata waliccinsa, gara ma tun
wuri ya kwance nadin da ya daura maka na
walicci, ko da yake babu ruwa na asirinka ai zai
tonu waliyyin Alhaji ni dai yaushe zaka dawo?"
yace,
"Idan ta sasauta min gobe zanyo sammako don
in sami test din da zamu yina goman safc",
Yusuf kashe wayar kawai yayi don yasan
Mujecb tsokanarsa kawai yake yi, don su yi ta
kwafsawa.
Washe gaari da zai tafi kuka sosai
Muneeba ta dinga yi, har sai da ya ji tamkar ya
140
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
fasa tafiya, sai daikomawarsa makaranta ya zama
dole, shiyasa yalallasheta da cewar zaiyi kokari
ba sai Kashen mako ba zai dinga zuwa duk bayan
kwana biyu.
Tunda ya tafi sai Muneebata hakura ta
saki jikinta ta ci gaba da harkokinta, amma idan
ta zo kwanciya kewar mijinta na damunta da
salon soyayyar sa da yake nuna mata wadda
tamkar soyayya yake karanta a jami'ar.
Goggo ta sa idanu sosai akan Munceba,
so take ta gano ko ciki kega Muneeba a dalilin
ciwon da aka ce tayi sannan gashi ta yi 'yar kiba
ta murje ta yi haske fatarta sai sheki baa san bata
da komai ba, tsabar kwanciyar hankali ne suka
samu da fahimtar juna a rayuwar auurensu.
141
WATA KUSAN 1
*** ***
Rahmatu Hassan Zaria
Rayuwa ta ci gaba da garawa, Mujeeb yayi cukucuku anyiwa Munecba tiransifar karatunta ta
dawo makarantar jeka ka dawo ta 'yan mata
anan garin Dukku ta ci gaba da karatunta har tayi
zana (JSCE) ta shiga aji daya na babbar
sakandare, shi kuma a nasa fannin karatun yana
shckarar Karshe. A wannan lokacin shekarar
aurensu daya da watanni.
Tun goggo na zuba idanu ta ga ciki ya
bubllo a jikin Munceba, har ta saduda sai kuma
abin ya koma tana gayawa Munccban kakkausar
magana akan bata haihu ba don akwai lokacin da
ka zo ana fadin haihuwar wata sai Goggon ta
kada baki tace, "Oh, kinga duk sa'o'in auren su
Muneeba duk sun haihu har ma wadanda aka yi
bikinsu a bayan nasu, itakam har yanzu shiru, ko
da yake ai 'yar boko ce kwayoyi zata sha bata
son haihuwa sai ta gama karatu, ko ka fada
mijnta ba yarda zaiyi ba zakiji yace Allah nc bai
kawo ba, alhalin ana cutarsa a 6oyc ne bai sani
ba saidai Allah ya saka masa kokarinsa ya tashi
a banza a sanyc shi an rufe masa baki”. Munceba
na gefe tana tankaden garin tuwo, ita kuma
Goggon na kicin tana iza wuta suke hira da
bakuwarta da ta zo take bata labarin haihhuwar
142
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
da aka yi, shine Goggo ta ke kwararo wannan
zance da bai da cc ba.
Munceba bata san lokacin da hawayc ya
balle mata ba saboda bakin cikin duk lokacin da
Goggo ta tashi zancen rashin haihhuwar ta, sai ta
danganta hakan da cewa Muneeban ne bata son
haihuwa take shankwayoyi alhalin bahaka ba ne,
ki yayya ce kawai take sa ta fadin wadanan
kalamai, ita da za a riketa da bindiga wallahi
bata sanma yamaganin tsarin iyalin yake ba, bata
san inda ake yi ba, amma ta lakaya mata har
Mujeebu Goggo ta gayawa, shi dai kullun cikin
laltashin matarsa yake yi don yasan ba laifinta
bane rashin haihuwarsu Allah ne bai basu ba,
kuma suna nan suna kai masakukansu insha
Allahu zai dube su ya basu tunda ba wai ya
manta da su bane ya hana su yana sanc da su
lokaci ne kawai baiyi bana yaba su haihuwar.
Goggo daga kicin ta hangi hawaycn
fuskar Muneeba sai ta. ta6e baki tare da sakin
uban tsaki tace, "au kuka kike yi don an fadi
gaskiya? Lallai kuwa kuka bai kare miki ba don
ba zan daina fadin gaskiya ba sai ranar da naga
jika na a hannuna in kuma ba haka ba, wallahi
kara aure zaiyi. Ya auro wanda zata haihu tunda
ke bakya son haihuwar. Ita dai Munecba ba ta ce
uffan ba ta ci gaba da sharan hawayenta ita
WATA KUSAN 1 Rahmatu Hassan Zaria
Goggo ta ci gaba da surutanta da ke bakanta
zuciyar Munceba, kuma su ke rage mata
girmanta da take gani
Da daddare da Mujeebu ya shigo tunda
yana gari sai ya kasa gane kan Muneeban ya
ganta sukuku babu walwala ya yi ya yi ta gaya
masa me ke damunta ta ki gaya masa dama idan
ya ga haka, to ya san Goggoce ta yi mata wani
abin sai taki gaya masa in ba Goggon bace ta
gaya masa ya zo ya tambaye ta sam ita bata gaya
masa kuma idan Goggon ta tashi gaya masa son
ranta take fada, da yake ya san halin
mahaifiyarsa sai ya bita yadda take so